Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko da So... (Kashi na 4)

Ammi na zaune cikin shaddar ta da ta ji sirfani kallo take dan ta mai da hankalin ta kan TV ɗin suka shigo suna dariya da alamu wata maganar sukai wannan ya ja hankalin Ammin kan su "a'ah yau su Hafsatu ne gidan namu?"

Hafsan ce ta ɗan ture hannun Hidaya ta yi gun Ammi da sauri, "Ammin mu ashe kina ƙasa?" Murmushi Ammin ta yi "ina nan kallo ya riƙe ni"

Rissinawa Hafsa ta yi ta gai she ta. “Inaa ba ni amsawa na yi fushi sai yau kika ga damar zuwa" Ammi ta faɗa tana haɗe ran tsokana, kamo hannun ta Hafsa ta yi " wallahi makaranta ta hana ni zuwa anma aikin san Allah bazan ƙi zuwa haka kawai ba"

Murmushi Ammi ta yi " to shike nan shagwaɓar ta mece ai tun da kin zo ɗin shike nan jiya jiyan nan Hidaya ke cewa za ta je ta ɗauko ki" kallon Hidaya Hafsa ya yi ba ni ta yi missing ba na san ta sarai yawo take so da kuma ta zo tamin ‘yan kwa she kwashe, cikin salon riƙe murya Hidaya ta ce "ah haba ai na wuce nan kedai da kike haka Allah ya shirye ki" suka sa dariya duka.

Miƙewa Hafsa ta yi na ji gidan shiru Yays baya nan ne? Ta tambaya tare da yin gaba ba tare jiran amsar su ba, ɗakin sa ta leka da alamu bayanan ledar alawa da ta gani bisa gado ta ɗauko tana sha kafin ta wuce daƙin Hidaya, hangar ta da Hidaya ta yi ne ya sa ta miƙewa da gudu ta bi bayan ta dariya kawai Ammi tasa ta ci gaba da kallon ta.

Jiyiwa Hafsa ta yi tare da tsayawa cak, tana taunar alwalar sai da ta haɗe rai kafin ta ce "Hajiya gudun mai kike haka?, Mai kika mai dani ɓarauniya ki mai dani ko ke?"

Dariya Hidaya ta sa " ni na isa in mai da ke ɓarauniya, kawai dai.."

"Kawai dai me?" Hafsa ta tambaya tare da tsare Hidaya da ido.

Hannun Hidayan ta takalla " da wannan kika zo?"

Banza Hafsa ta mata ta shige ɗakin tare da faɗawa gado, "jiya mai zaki zomin?" Ta faɗa bayan ta gyara kwanciyar ta.

Zama geren Gadon Hidaya ta yi " kawai na gaji da zaman haka shi ne na ce bari in zo mu ɗanfita ko park ne muje"

Ta shi zaune Hafsan ta yi "kamar kinsan kullum sai ƙawata da nake faɗa miki ta BUK ta ce mun yau she za mu ɗan fita indai ba har gidan su naje ba Maman ta ba ta barin ta"

Juyowa Hidaya ta yi cikin ɗoki " a beg sis ki shirya mana walllahi na gaji da zaman nan sam a Sch ni bana zama guri guda tun da muka dawo ka zama ‘yar kurku"

Dariya Hafsa tasa. “To ba ke ce kika zaɓi zariya ba da kina kano abinki ai da tare za mu dunga hutu yanzu ki bari week end mu gani zanma Bilkisu Magana..." Wayar ta da ta hau ƙara yasata duba kan screen "Momy ce"ta fada kafin ta ɗaga, " ok tom" kawai ta ce kafin ta kashe wayar duban Hidaya ta yi "ta ce ta kusa ƙarasowa bari in koma falo da sun gaisa da Ammi wai za mu tafi."

Turo baki Hidaya ta yi "wai dama kina nufin ba yini zakiyi a gidan nan ba?"

Dariya Hafsa ta yi ta ɗan dafa kafaɗar ta " karki damu ba Sunday za mu haɗu ba"

Murmushi kawai Hidaya ta yi inda Hafsa ta ɗauki wayar ta tare da sauka daga gadon littafin labarin da ke kan drawer in da ke gefen gado Hafsa ta sa hannu ta ɗauka sai kuma ta ajiye caraf ta ɗauke popcorn din sa ke ajiye da fitilar da ke Kai ta yi waje, dariya Hidaya tasa tasan babu ta inda za ai Hafsa ta zo ba ta ɗauki abu ba sedai in ta je ta ɗauko abin ta.

"A'a badai har tafiya ba me aka yi haka?" Ammi ta tambaya lokacin da taga shigowar su falon.

" Tare da Mami muke na ɗauka za ta kai yanma yanzu ta kirani ta ce tana hanya shi ya sa na san yanzu za ta ƙaraso" Hafsan ta faɗa lokacin da ta samu wuri ta zauna.

" Shi ne baki faɗamin ba ai da nasa an yi mata wani abin"

Dafe goshi Hafsa ta yi " walllahi na sha'afa..." Sallamar momy cikin falon ya sa ta yin shiru kamta ce "lah tama ƙara so"

Cikin mutunci Ammi ta amshe ta kowa fuskar sa ɗauke da annashuwa, Momy ba ta fi minti Ashirin ba suka tun a mota momy ke harar Hafsa kamar take su shiga suna shiga falo ta balbale Hafsan da Faɗa "wato Hafsa ba zaki canja halin ki na bada mu da kike ba wurin dangi ko?"

A ɗan tsorace Hafsa ta ce " Momy nai nayi kuma?"

"Au tambaya ma kike eyye sannu to, har sau nawa kike son in faɗa miki in kinje ki dinga kama kanki, ki kalli yadda Hidayan ta ke, in ta zo gidan nan ai ba ta daukan komai magana ma ɗai ɗai take, anma ke jibi yadda kike bada kanki"

Dariya Hafsa ta sa "kai Momy Hidayan ce ba ta ɗaukan komai, kuma ai magana ai kema kin san haka maganar ta take, Allah su ba su ɗauki komai ba duk ɗaya muke fa"

Tsaki Momy ta hanyar "Ɗaya a ina?, Ɗayan suka ɗauke mu shi ne dan ta ji zanzo ta ci wannan uwar kwalliyar to wa za ta nunawa kaya?"

Ajiyar zuciya Hafsa ta yi " walllahi momy ba ta san zaki zo ba tun da na shiga haka naganta ai kema kin san Ammi da gayu kullum cikin sa take"

Murmushin takaici Momy ta yi " eh kam ai na saba ƙarya"

Shiru kawai Hafsa ta yi ta ja ya zauna ta sauraron faɗan momy dan tasan in ta shige ɗaki ta kuma jawa kanta..

** ****

Da wur wuri ya tashi tsaf ya shirya ya fito tsakar gida yana ta je kan sa Hajara ce ta dube shi kai tabrakallah ma sha Allah, "ah ya ya kaga yadda ka haɗu" dariya ya yi yana kuma kallon kansa jikin glass ɗin tagar kafin ya juyo ya ce "ina tuwo na?"

Langar da ke rufe da furfin kwanon sha ta nuno masa kujera ya ja gefe ya hau ci muryar Hafsa ya tsinkaya na faɗin kuma ya ya yau she za ka koma can?

Siɗe hannun sa ya yi " kafin ya ce sai dai na je naga in da shagon da zan iya kamawa inna ji kuɗin ya yi yawa ma gwanda kawai na yi zama na anan"

"To Allah ya zaɓa mafi alkairi" Hajara ta faɗa

"Amin, in Inna ɗin ta dawo ki ce mata nake horar war da suka ce mu zo" ya faɗa yana wanke hannu.

Kai tsaye shagon Idris ya nufa, bayan sun gaisa ne ya ce "dan Allah dubu biyu za ka ranta min zuwa ƙar shen wata"

Shiru Idris ɗin ya yi kafin ya zaro ya miƙa masa " Allah dan ina ganin mutuncin ka ne in kana son hakan ta ɗore to watak na yi ka dawon da kuɗina"

Dariya Muktar ya yi kar ka damu in Sha Allah zan cika alkawarin"

Yau bakamar ranar da ya zo interview ba, babu mutane da yawa kusan ba su fi su bakwai Bama sai mai musu orientation din na takwas, hayaniyar da suka ji ce ya sa mai maganar yin shiru sautin murya ke ta shi cikin har shen turanci " abu ne mai wuya ku samu Physics teacher kamar ni ko kun samu na tabbatar ba mai yadda ya dinga muku jaki work ɗin da nake mu"

Shirun da suka ji ya sa mai maganar ci gaba da magana, sai dai kamar an hankaɗo mutumin ya shigo yana haki "waye zai ɗauki Physics ɗin?, walllahi na tausaya ma, mutanen nan mugaye ne dan kawai ba ce naje yajin aiki sai sun ƙaran alba shi suka ɗauka, Please ka nuna min kai"

School proprietor ne ya shigo kamar kullum sanye da Babbar riga haibar sa ta sa David yin shiru, bai ce komai ba ya amshi takardu hannun Muktar ya miƙawa David ganin alba shin da ke jiki ya sa David kallon school proprietor ɗin cike da mamaki.

Karɓar takardar ya yi. ka gani amount ɗin da ka yi demanding muka ƙara, “

ba wai kuɗin ne ya sa na sallame ka ba. No, baka san daraja da mutunci ba, sam baka kallon furfurata ka ba ta daraja, ni da kai da naga kun kasa resolving problem ɗin da principal na kira ka na ce ka yi haƙuri kar ka tafi yajin aikin nan our students need you, har ce ma na yi zan ƙara alba shin in ma kana tsoron principal ba za ta baka ba ni zan dinga biyan ka da hannu na amma ka ƙi sauraro na, I see no reason da zan ci gaba da zama da mutumin da zai din ga wulaƙantani. It is not like you are doing me some favour, no we are doing it for each other, kai ina biyan ka ni kuma kana yin abin da bazan iya so respecting each other is something like mandatory among us".” School proprietor ɗin ya faɗa kafin ya juya zai fice.

" But sir..." David ya faɗa ɗaga masa hannu ya yi komai ya wuce dama na baka na kaje ka samu inda bs za su dinga zaluntar ka ba" ya faɗa kan ya bar ajin David ya bi bayan sa.

Sosai mutumin ya birge Muktar ji yake indai wataran da rai shims ya zama dattijo to nutsuwar mutumin nan da halin sa zai bi.

Wurin biyu suka ta shi kai tsaye gurin dillalin da zai nuna masa shagunan ya nufa sai dai kusan ba bu wanda zai iya kamawa, wanda aka nuna masa mai sauƙin kuɗi na dubu arb'inne shi kuma ya yi nisa sosai da makarantar wannan ya sa ya yanke shawarar gwanda kawai ya yi zaman sa gida zuwa ya yi saving sai ya sayi ko mashin ne da haka ya ta ri ɗan sahu ya yi gida a gajiye.

Rubutawa

AeshaKabir
Fadimafayau

Soyayya
Credit: LuckyTD

Post a Comment

0 Comments