Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Rasa Sallar Juma’a Guda Uku

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Idan musulmi ya rasa sallar Jumma’a har fiye da sau uku, menene hukuncinsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Ya tabbata a cikin Hadisi Sahihi cewa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« مَنْ تَرَكَ ثَلاَثَ جُمَعٍ ، تَهَاوُنًا بِهَا ، طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قَلْبِهِ »

Wanda ya bar Juma’a har guda uku domin wulaƙantarwa gare su, to Allaah ya rufe a kan zuciyarsa.

(An-Nasaa’iy (1378) da Abu-Daawud (1054) suka riwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya ce: Hasan sahih ne a cikin Sahih Abi-Daawud: 1052).

A wani lafazin kuma ya ce:

« مَنْ تَرَكَ ثَلاَثَ جُمَعٍ مِنْ غَيْرِ عُذْرٍ ، كُتِبَ مِنَ الْمُنَافِقِينَ »

Duk wanda ya bar Juma’a guda uku ba da wani uzuri ba, to an rubuta shi a cikin munafuƙai.

(Al-Albaaniy ya inganta shi a cikin Sahih Al-Jaami’i: 6144 da Sahih At-Targheeb: 729).

Daga waɗannan hadisan da makamantansu ne malamai suka gano cewa:

(i) Zuwa sallar Juma’a wajibi ne a kan dukkan musulmi baligi mai hankali, ɗa ba bawa ba, namiji ba mace ba, kuma mazaunin gari ba matafiyi ba.

(ii) Haram ne mutum musulmi mai waɗancan siffofin da aka ambata ya ƙi zuwa sallar jumaa haka nan siddan, ba da wani uzuri gamsasshe ba.

(iii) Daga cikin uzurin da ke halatta barin zuwa Juma’a in ji malamai, akwai: Rashin lafiya, ruwan sama, sanyi mai tsanani, tsoro, tafiya, bauta da kuma kasantuwar ita mace ce.

(iv) Ƙin zuwa masallacin Jumaa haka nan kawai don wulaƙantar da alamarinta, ba da wani uzuri ko hanzari abin karɓa a Shari’a ba, ya shigar da mutum cikin jama’ar munafuƙai waɗanda kuma ake rufewa a kan zukatansu.

Allaah ya kiyaye. Allaah ya shiryar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments