𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam
Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, jiya na ga video clip na wani magidancin da ya
yi wa ’yar cikinsa fyaɗe,
a ƙarshe
kuma da sai aka fara mayar da maganar wasan kwaikwayo, aka fara nuna wai wanda
ake zargin yana da taɓin
hankali! Wannan ba zai yi justifying (ya gaskata) abin da wasu shugabanni suka
yanke na dandaƙe irin waɗannan
mutanen da kashe su kawai ba?! Abin yana neman ya ƙazance fa!
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Duk yadda
al’amura suka lalace ko suka ƙazance, kamar yadda ka faɗa, mafita dai ƙwara
ɗaya ce kawai:
Komawa ga hanyar da Allaah Maƙagin Halittu ya tsara. Allaah Ta’aala ya ce:
ظَهَرَ الْفَسَادُ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ بِمَا كَسَبَتْ أَيْدِي النَّاسِ لِيُذِيقَهُمْ بَعْضَ الَّذِي عَمِلُوا لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ ١٤
Ɓarna
ta bayyana a tudu da teku saboda irin abin da hannuwan mutane suke aikatawa,
domin ya ɗanɗana musu sashen abin da
suka aikata, ko wataƙila su dawo kan hanya. (Surah Ar-Ruum: 41)
Wannan nuni ne
a kan cewa:
(i) Ashe duk
abin da ya yawaita a wannan zamanin na rashin albarkar rayuwa, da karayar
tattalin arziki mai kai wa ga yawaitan talauci, da rashin tsaro da aminci da
kwanciyar hankali, da yawaitan nau’ukan cututtuka masu kai wa ga yawaitan
mace-mace da sauransu, duk tushensu abu ɗaya
ne: Saɓon Allaah
kawai.
(ii) Taurarewa
da kangare wa dokokin Ubangiji Ta’aala ta hanyar: Munafunci ko kafirci ko
mushirikanci ko fasiƙanci ko zalunci da sauran laifuffuka makamantansu, su ne
ummul-habaa’isin
dukkan bala’o’i da masifun da ake fama da su a duniyar yau.
(iii) Hikima
ko dalilin sauke wa al’umma irin waɗannan
masifun da bala’o’in ba kamar yadda waɗansu
suke tunani ba ne cewa: Wai domin sakamako ga laifuffukan da jama’a suke
tafkawa ba ne, amma dai domin fatar al’umma su tuba daga laifuffukansu ne, kuma
su dawo kan hanyar Allaah Ta’aala.
Don haka, duk
wata hikima ko dabara da mutane za su tsara ko su bi don kauce wa aukuwar irin
waɗannan bala’o’in
da masifun a cikinsu ba zai haifar musu da mafita ko ya biya buƙata
ba, in dai ba komawa suka yi ga hanya guda ɗaya
ta Allaah Maɗaukakin
Sarki ba. Duk muna ji da gani dai a yau yadda ƙwarar cutar covid-19 ta gagari manyan ƙasashen
duniya!
Kyara ko ɗauri ko duka ko tara ko
dandaƙa
ko kisa da sauran hanyoyin da hukumomi suke tunanin bi duk ba hanyoyi ne na
warware wannan matsalar nan ta fyaɗe
ba. Kuma ko da shekaru dubunnai za a ɗauka
ana kururuwar da yin amfani da ita, wannan ba zai taɓa biya buƙata ba. Domin gazawa ko zaƙewa
a cikin hukunci ko dokar Ubangiji ba sa maganin matsala.
Hanya guda ɗaya tilo kuma ƙwara
guda tak da za a bi don maganin matsalar ita ce abin da Shari’ar Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ta bayyana:
(1) Idan wanda
aka kama da laifin ya zama baligi ne mai hankali da zaɓin ransa, wanda kuma bai taɓa yin aure ba sai kawai a
tsayar da shi a gaban jama’a, a zuba masa buloli har guda ɗari cif-cif, ba tare da
nuna wani tausayi gare shi ba. Sai kuma a kore shi daga garin na shekara guda.
(2) Idan kuma
mazinacin baligi ne mai hankali mai zaɓin
rai wanda kuma ya taɓa
yin aure ko da sau guda ne a rayuwarsa, to bayan bulolin sai a ƙara
masa da wannan hukuncin: A tsayar da shi a gaban mutane, kuma a sanya su yi ta
jifan sa da duwatsu har sai ya mutu.
Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« خُذُوا عَنِّى ، خُذُوا عَنِّى
، قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلاً : الْبِكْرُ بِالْبِكْرِ جَلْدُ مِائَةٍ وَنَفْىُ سَنَةٍ ، وَالثَّيِّبُ بِالثَّيِّبِ
جَلْدُ مِائَةٍ وَالرَّجْمُ »
Ku ɗauka daga gare ni! Ku ɗauka daga gare ni!! Haƙiƙa!
Allaah ya sama musu mafita: Saurayi da budurwa: Bulala ɗari da ɗaurin
shekara guda. Bazawari da bazawara kuma: Bulala ɗari
da jefewa. (Sahih Muslim: 4509)
(i) Wannan
hadisi ƙarin
bayani ne ga ayar Surah An-Nisaa’i:
وَاللَّاتِي يَأْتِينَ الْفَاحِشَةَ مِنْ نِسَائِكُمْ فَاسْتَشْهِدُوا عَلَيْهِنَّ أَرْبَعَةً مِنْكُمْ ۖ فَإِنْ شَهِدُوا
فَأَمْسِكُوهُنَّ فِي الْبُيُوتِ حَتَّىٰ يَتَوَفَّاهُنَّ الْمَوْتُ أَوْ يَجْعَلَ اللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلًا
Kuma waɗanda suka je wa alfãsha
daga mãtanku, to, ku nemi Shaidar mutãne huɗu
daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje
har mutuwa ta karɓi
rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su. (Suratul Nisá'i : 15)
(ii) Wannan
hadisi ya ƙunshi
hukuncin da Shari’ar
musulunci ta kafu a kansa ke nan, dangane da mazinata: Ko dai bulala ɗari tare da jefewa ga
wanda ya taɓa yin
aure, ko kuma bulala ɗari
tare da ɗaurin
shekara guda ga wanda bai taɓa
yin aure ba.
(iii) Daraja
da martaba da ɗaukaka
ga kowane musulmi ita ce: Yin biyayya da jayuwa kawai ga wannan dokar, sannan
kuma da zartar da ita a kan duk wanda ya saɓa
mata, a lokacin da ya samu iko da dama a matsayinsa na shugaban ƙasa
ko shugaban jiha, ba tare da yi mata kwaskwarima ko gyaran fuska ba.
(iv) A nan
babu bambanci ko mazinacin namiji ne ko mace ce ko kuma mata-maza ne. Haka ko
ya yi zinar da baligi ne ko da wanda bai balaga ba ne. Sannan kuma ko da son
ran abokin yinsa ne ko ba da son ransa ba ne (kamar ta hanyar fyaɗe), duk hukuncin dai ɗaya ne.
(v) Abin lura
dai kawai shi ne: Ana zartar da wannan hukunci ne idan dukkan sharuɗɗa sun cika kuma dukkan
abubuwan da suke hana aukar da hukuncin a kan wanda ake zargi da laifin sun
kau. Don haka ake buƙatar matuƙar yin taka-tsantsan da zurfafa bincike
daga alƙali
kafin zartarwa.
(vi) Tsai da
wannan hukuncin daga alƙalin kotun musulunci a kan musulmin da aka bincika kuma aka
tabbatar da ya aikata wannan laifin shi ne daidai kuma kyakkyawar hanyar samun
ingantacciyar al’umma ce a duniya.
(vii) Amma saɓa wa wannan ta hanyar
yanke masa hukuncin da ya gaza hakan, kamar tara ko ɗauri kawai, wannan ba zai gyara al’umma ba
kuma ba zai hana ci gaba da aikata laifin ba, kamar yadda ake ji da gani a ciki
da wajen al’ummomin wannan zamanin.
(viii) Haka ma
zaƙewa
ko wuce-iyaka wurin yanke hukunci ga mai wannan laifin, kamar ta hanyar tsire
shi, ko dandaƙe shi, ko cire mata mahaifa. Wannan duk ba zai gyara al’umma ya sa su daina aikata
laifin ba, kamar yadda ake ji da gani a kan wasu dokokin makamantan wannan.
(ix) Harbe
mutanen da ake zargi da fashi ko ta’addanci don kawai an same su da makamai, ko
da kuwa ba a tabbatar da cewa sun taɓa
tsare hanya ko sun taɓa
kashe kowa ba, wannan zalunci ne. Ballantana kuma yafe wa mutanen da binciken
kotu ya tabbatar da cewa sun mallaki muggan makamai kuma sun yi amfani da su
wurin hallakawa da tarwatsa al’ummar da ba su taka musu ko sun zubar ba!
(x) Wanda yake
ta ƙoƙarin
cusa lomar tuwo ta cikin hancinsa, da wanda ke faman ɗura ruwan rijiya a cikin man motarsa, sannan
da wanda ya zauna yake ta nacin tura katin glo a cikin layinsa na mtn misali,
duk mun san wahalar banza kawai suke yi, kuma ba za su taɓa cin nasara ba. Kamar
haka, duk mutanen da suka kama bin waɗansu
abubuwa, suka kauce daga bin dokoki da tsarin da Ubangiji Ta’aala ya saukar
musu: Wahalar banza kawai suke yi, kuma ba za su taɓa samun cin nasara ba.
Allaah ya ƙara
fahimtar da shugabanninmu, su gane gaskiyar addini kuma su iya kafewa a kan yin
aiki da shi. Allaah ya fahimtar da mu, ya ƙara shiryar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.