Ticker

6/recent/ticker-posts

Zargi A Tsakanin Ma’aurata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, wai menene hukuncin zaman aure tare da miji mai yawan zargin matarsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

(i) Me yiwuwa tun kafin su yi aure ya san ta da hakan ne, ko kuma a hakan suka rayu kafin a ɗaura musu auren. In haka ne, wajibin abin da yake a kansu yanzu shi ne gaggauta tuba da komawa ga Allaah tare da neman gafararsa.

(ii) Dole ne shi kuma ya hana kansa yin irin wannan tunanin, kuma ya ɗauki matakan da ba su ci-karo da koyarwar shari’a ba, kamar ta hana ta fita daga gida sai tare da wani amintaccen muharraninta.

(iii) A duk lokacin da wannan tunanin ya taso masa, wajibi ne ya riƙa yin istiaazah yana roƙon Allaah Taaala ya tsare shi daga sharrin shaiɗan, kuma kar ya kuskura ya furta komai da bakinsa, ko ya rubuta shi.

(iv) Idan kuma ya furta abin da ke cikin zuciyarsa a fili ko ya rubuta shi, har wani ya ji ko ya gani, to hukuncin ƙazafi ya hau kansa ke nan.

(v) Dole ne kuma wajibi ne ya kawo shaidu musulmi guda huɗu adalai waɗanda za su yi shaida a gaban alƙalin kotun musulunci cewa, sun ga matar tana aikata wannan alamarin da yake zargin ta da shi.

(vi) Idan kuma shi kaɗai da idonsa ne kawai ya gan ta tana aikata abin da yake zargin, bai iya samo shaidun guda huɗu a kan hakan ba, to ba abin da ya rage masa a nan sai dai ya yi haƙuri, ya rufe bakinsa kawai. In ya so yana iya sakin ta shiru bakinsa-alaikum, ko kuma ya yi mata li’ani.

(vii) Idan kuma ya kasa yin ko ɗaya daga cikin abubuwan biyu, bayan kuma ya furta wannan maganar a fili, to babu abin da ya rage sai ya kwanta a gaban alƙali a zuba masa buloli har guda tamanin daidai.

Allaah Ta’aala ya ce:

 وَٱلَّذِینَ یَرۡمُونَ ٱلۡمُحۡصَنَـٰتِ ثُمَّ لَمۡ یَأۡتُوا۟ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَاۤءَ فَٱجۡلِدُوهُمۡ ثَمَـٰنِینَ جَلۡدَةࣰ وَلَا تَقۡبَلُوا۟ لَهُمۡ شَهَـٰدَةً أَبَدࣰاۚ وَأُو۟لَـٰۤىِٕكَ هُمُ ٱلۡفَـٰسِقُونَ ٤۝ إِلَّا ٱلَّذِینَ تَابُوا۟ مِنۢ بَعۡدِ ذَ ٰ⁠لِكَ وَأَصۡلَحُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ ٥۝

Kuma waɗanda suke jifar mata masu kamun-kai, sannan kuma ba su iya kawo shaidu guda huɗu ba, to sai ku yi musu buloli guda tamanin, kuma kar ku karɓi wata shaida daga gare su har abada, kuma waɗannan su ne cikakkun fasiƙai. Sai dai waɗanda suka tuba daga bayan haka kuma suka gyara, to haƙiƙa! Allaah Mai Yawan Gafara ne, Mai Jin Ƙai. (Surah An-Nuur: 4-5)

Sai kuma ya ce:

 وَٱلَّذِینَ یَرۡمُونَ أَزۡوَ ٰ⁠جَهُمۡ وَلَمۡ یَكُن لَّهُمۡ شُهَدَاۤءُ إِلَّاۤ أَنفُسُهُمۡ فَشَهَـٰدَةُ أَحَدِهِمۡ أَرۡبَعُ شَهَـٰدَ ٰ⁠تِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِینَ ٦۝ وَٱلۡخَـٰمِسَةُ أَنَّ لَعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَیۡهِ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡكَـٰذِبِینَ ٧۝ وَیَدۡرَؤُا۟ عَنۡهَا ٱلۡعَذَابَ أَن تَشۡهَدَ أَرۡبَعَ شَهَـٰدَ ٰ⁠تِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡكَـٰذِبِینَ ٨۝ وَٱلۡخَـٰمِسَةَ أَنَّ غَضَبَ ٱللَّهِ عَلَیۡهَاۤ إِن كَانَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِینَ ٩۝

Kuma Waɗanda suke jifar matan aurensu kuma bai kasance suna da waɗansu shaidu ba sai dai su kansu kawai, to shaidar ɗayansu ita ce: Rantsuwoyi har sau huɗu da Allaah a kan cewa: Lallai ne shi yana daga cikin masu gaskiya. Kuma ta biyar ita ce cewa: Tsinuwar Allaah ta sauka a kan shi, idan har ya kasance daga cikin maƙaryata. Kuma zai kawar mata da horon (jefewa) idan ta yi rantsuwa sau huɗu da Allaah a kan cewa: Shi yana daga cikin maƙaryata. Kuma ta biyar ita ce: Fushin Allaah ya tabbata a gare ta idan ya kasance daga cikin masu gaskiya. (Sura An-Nuur: 6-9)

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments