𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam
Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wai shin yaya ake yin Sallar Istikhaarah ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Al-Imaam
Al-Bukhaariy (Rahimahul Laah) ya riwaito hadisi (lamba: 1166, 6382) daga Sahabi
Jaabir Bn Abdillaah (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce:
Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance yana koya mana yin
Istikhaarah a cikin al’amurra dukkansu, kamar yadda yake koya mana Surah ta
Alqur’ani, yana cewa:
Idan ɗayanku ya himmatu ga wani
al’amari sai ya yi sallah raka’o’i biyu ba na farilla ba, sannan kuma sai ya
ce:
اللَّهُمَّ إِنِّى أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ ، وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ ،
وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ ، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ
وَلاَ أَقْدِرُ ، وَتَعْلَمُ وَلاَ
أَعْلَمُ ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ
الْغُيُوبِ ، اللَّهُمَّ إِنْ
كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأَمْرَ خَيْرٌ لِى فِى دِينِى ، وَمَعَاشِى ،
وَعَاقِبَةِ أَمْرِى - أَوْ قَالَ : عَاجِلِ أَمْرِى وَآجِلِهِ - فَاقْدُرْهُ لِى ، وَيَسِّرْهُ لِى
، ثُمَّ بَارِكْ لِى فِيهِ ، وَإِنْ كُنْتَ
تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأَمْرَ شَرٌّ لِى فِى دِينِى ، وَمَعَاشِى ،
وَعَاقِبَةِ أَمْرِى - أَوْ قَالَ : فِى عَاجِلِ أَمْرِى وَآجِلِهِ - فَاصْرِفْهُ عَنِّى ، وَاصْرِفْنِى عَنْهُ
، وَاقْدُرْ لِى الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ، ثُمَّ أَرْضِنِى
- قَالَ - : وَيُسَمِّى حَاجَتَهُ
Ya Allaah! Haƙiƙa!
Ina neman zaɓinka da
iliminka, kuma ina neman ƙaddarawarka da ƙudurarka, kuma ina roƙonka
daga falalarka mai girma, domin kai kake ƙaddarawa ni kuwa ba na ƙaddara
komai, kuma kai kake sani ni kuwa ba na sanin komai, kuma kai ne masanin duk
abin da ya ke ɓoye. Ya
Allaah! Idan ka san cewa wannan al’amarin alkhairi ne gare ni a cikin addinina
da rayuwata da ƙarshen al’amarina,
ko kuma ya ce: - Magaggaucin al’amarina
da majinkircinsa -, to ka ƙaddara mini shi, kuma ka sawwaƙe
mini shi, sannan kuma ka yi mini albarka a cikinsa. Ya Allaah! Idan ka san cewa
wannan al’amarin
sharri ne gare ni a cikin addinina da rayuwata da ƙarshen al’amarina, ko kuma ya ce: -
Magaggaucin al’amarina
da majinkircinsa -, to ka kawar da shi daga gare ni, kuma ka kawar da ni daga
gare shi, kuma ka ƙaddara mini alkhairi daga duk inda ya ke, sannan ka yardar da
ni da shi. Sai kuma ya ambaci buƙatarsa.
Malamai suka
ce:
(i) Allaah
(Tabaaraka Wa Ta’aala) Shi kaɗai
ne ake dogaro gare shi, ake mayar da al’amura gare shi, kuma ake bauta masa,
ake roƙonsa,
domin shi kaɗai ne
ke iya sanya zukata su amince, kuma su yarda da ƙaddararsa.
(ii) Cewa: ‘Ya
Allaah! Idan ka san wannan al’amari…’ ya nuna cikakkiyar sallamawa ga Allaah
ne, ba wai shakka ko kokonto a cikin iliminsa ba, kamar yadda wasu marasa fahimta
suke faɗi.
(iii) Babu
Istikhaarah a cikin abubuwan da suke wajibai ko mustahabbai, domin dukkan su
alkhairi ne waɗanda ake
neman musulmi ya aikata su.
(iv) Kuma babu
Istikhaarah a cikin haramtattun abubuwa ko makaruhai, saboda dukkansu abubuwan ƙyama
ne da aka hana musulmi aikata su.
(v) Sallar
Istikhaarah ana yin ta ne a cikin abubuwan da mutum yake da zaɓi a cikinsu, watau
abubuwan da malamai suke kiransu: Mubaahaat, watau: Halal, kamar: Shiga wani
nau’in kasuwanci ko wata sana’a, da kamar zama a wani gari ko wata unguwa, ko
aure da wani mutum ko wata mace, da sauransu.
(vi) Dole ne
mai yin Istikhaarah ya zama ba shi da wani ra’ayi ko zaɓin ransa a cikin al’amarin da yake neman yin
Istikhaarah a kansa tun da farko. Domin in ba haka ba, ya zama maƙaryaci
ke nan a cikin maganarsa cewa: ‘Ya
Allaah! Haƙiƙa!
Ina neman zaɓinka
(vii) Kamar
yadda hadisin ya nuna a fili ƙarara: A bayan sallar nafila raka’o’i biyu ne a ke yin addu’ar Istikhaarar, ba a bayan sallar farilla ba. Kuma yana
ambatan buƙatarsa
ce a daidai inda ya ce: ‘Wannan
al’amari…’
(viii) Bayan
Istikhaarah sai mutum ya ci gaba da irin abin da yake ganin shi ne daidai, yana
mai dogaro ga Allaah, tare da ɗaukan
matakan da suka kamata kuma yadda suka dace da shari’a. Kuma yana gane abin da
aka zaɓa masa ne ta
samun sauƙi
wurin aikata shi, da kuma wahalar abin da ba shi ne aka zaɓa masa ba. Ba wai ta gani
a mafarki ko makamancinsa ba.
(ix) Yana
maimaita yin Sallar Istikhaarar ce da gwargwadon yadda ya ga buƙatar
hakan, kamar dai yadda mara lafiya ke shan magani, har sai ya ga bayyanar abin
da aka zaɓa masa.
(x) Ba daidai
ba ne a nemi malamai wai su yi wa mutum Istikhaarah, domin kamar yadda ya zo a
Hadisin, Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) koya wa Sahabbai yake
yi, ba yi musu ba!
Dubi ƙarin
bayani a cikin Tamaamul Minnah: 1/370-371.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.