Hamdala

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    740. Na gode wa Jalla Sarki Mabuwayi,

     Wanda ka sa wuta ta koma ta yi toyi,

     Wanda ya ƙagi duniya yay yi Nabiyi,

     Da sahabbansa Ahlihi had da waliyi,

    Wanda ya ƙaddaro ni bokon Hausawa.

     

    741. Masana Hausa ko guda ban ɗebe ba,

     Ku duka kun yi ƙoƙari ban yada ba,

     Ba tamkar ku ni garan ba wai ne ba,

     Dukkanninku na yaba, ban ware ba,

    Nai muku godiya ga ƙwazon koyarwa.

     

    742. Ibrahim Yahaya Rabbu ka yafe mai,

     Kai rahama gare shi Rabbu ka ƙara mai,

     Dukkan ni’ima Ilahu an sa a daɗa mai,

     Sannan zuriyarsa Rabbu an ƙara ɗaga mai,

      Babban malamin Alu gun koyarwa.

     

    743. Bari in ƙara godiya gun Ɗangambo,

     Babban malaminmu malam Ɗangambo,

     Sannan Garkuwan Adab ne Ɗangambo,

     Farfesan adab a nemo Ɗangambo,

      Babban malamin da ba na mantawa.

     

    744. Bayaro Malamin Alu ɗa ga Yahya,

     Ba fa Alu kaɗai ba har ni da Ruƙayya,

     Abdullahi Bayaro, jikan manya,

     Jikan Nana ‘yar tsatson girma manya,

      Jagoran Alu ga B.A. farawa.

     

    745. Ɗalhatu na yaba da alkancin ka,

     Kai ka duba Ali ka yi hukuncinka,

     Ka lamunta, ka yaba kai aikinka,

     Ka yarda Alu ya karɓi Dakta don doka,

      Kakana na bincike gun Hausawa.

     

    746. Burina ga wagga waƙa a kiyaye,

     Ai hattara wurin rubutu kai waye,

     A bi tsari na gaskiya, kar fa a tauye,

     Kowane ɗalibi ya duba ya kiyaye,

      Dukkan ƙa’idar rubutun Hausawa.

    747. Ya zamo sun zamo jiki gun mai koyo,

     Yai ta faɗinsu ba tsayi nan gun koyo,

     Maimaicin ta ko’ina in har zai yo,

     Ɗan baiti ya zanto ita ce dai zai yo,

      Ko tafiya yakai yana iya rerawa.

     

    748. Burina ƙasar ga kamin a naɗe ta,

     Kowane yanki ya koya ya rubuta,

     Harshen Hausa yai yawa sai gane ta,

     Dukkan al’uma fa tilas su iya ta,

      Hausa ta mamaye harasan Turawa.

     

    749. Tun a Firamarenmu manyan makarantu,

     Har da sakandare mu su ne matsakaitu,

     Har taciary, shirin ya zan zai yi nagartu,

     Har can University abinmu ya ingantu,

      Turanci ya bar aji bai shirya ba.

     

    750. Nahawun Hausa ga shi dai mun waƙe shi,

     Mun yi shiri ga ɗalibanmu su gane shi,

     Su ji sauƙi wajen biɗa da karanta shi,

     Mun tsara shi mun zuba, ga adadin shi,

      Bisa baiti ɗari bakwai ga ƙarawa.

     

    751. Sa hamsin cikin ƙidar ga jimillarsu,

     Ɗauko ɗari bakwai ka sa lissafinsu,

    Sai an tattara ka san kimaninsu,

     Ka ji ɗari bakwai da hamsin ga ƙidansu,

      Ga wuturi guda na ƙarshen ƙirgawa.

     

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.