Koda mahaifin Fatiha ya dawo daga masallaci ɗakin matarsa ya shige wato mahaifiyarsu Fatihan kamar yadda ya saba yahau bincike nan ya tattara duk abin da yake buƙata tun daga kan taliya sauran man da ke cikin jarkar ya juye a leda ya ɗaure cikin huhu kamin ya fito yana cika yama batsewa cikin ɗaga murya yake kwalawa ummansu Fatihan kira.
Da sauri ta fito daga madafa lafiya dai malam
cikin fishi yake faɗin
tsabar wulaƙanci
shi ne kuka tsiri boye kaya ta daure ta ce wane irin ɓoye wa shi ke nan muke da shi abin da ƙarya
ya faɗa na san Bashir
Buhu guda yake ajiye miki gami da galan ɗin
mai.
Cikin fusata ta ce to be ajiye ba da me kake
so yaji yanzu yai aure matarsa harda ciki ga kuɗin
makarantar ƙananan
sa yaja tsaki wannan ai duk haƙƙinsa ne inji wa ya ce haƙƙinsa
ne kai yake kanka cikin fusata ya ce to gorantamin bana iya ci da ku nidai ba
goranta ma nayi ba gaskiya ce.
Tsaki yaja ya shiga ya ɗauko kayan da ya haɗa zai fice tasha gabansa me kake nufi bafa mu
da komi kai baka kawo ba shi ne za ka kwashe mana namu tureta yai yana faɗin daɗin abun hake kika kawo ba
kema ɗana ne yakawo
kuma ki faɗa masa in
ya zo lalle ya kawon dubu goma zan biyawa Salima kuɗin makaranta.
Me wallahi bazai kawo ba indai ni na haifeshi
to bazai kawo ba yadda yai ta gwannati haka itama tayi in kuma kaga bazatai ba
seka ɗauki himmar biya
mata anman ba shi ba, ya juyo zai haita da masifa tai shigewar ta bayi yai
kwafa gami da ficewa rai a ɓace.
Fatiha na jinsu tausayin kanta da ‘yan
uwanta dana ummanta ya kamata ta share hawaye gami da fitowa ta ɗau wakenta dan kai markaɗe.
Koda ta kammala komi na awarar Ibrahim ne ya ɗibar mata kaya suka fice
zuwa inda take suyar.
Tafe suke suna shida abokinsa cikin wata
tsaleliyar mota kallo ɗaya
za ka musu kasan tabbas kuɗi
da hutu yagama zauna musu kai motar kawai inka kalla se kaso ganin na ciki.
Anman wallahi Faruk kai ɗan Iska ne tsabar wulaƙanci
nazo garinku ka rasa inda za ka kawoni yawon shaƙatawa sai nai jibi dan Allah yadda motar
nan ke faɗawa
kwazazzabai Faruk ya sa dariya kaga malam karka kuma iskantani kaifa ka ce in
kaika inda baka taɓa
zuwa ba agarin kano, Msttt kamis yaja tsaki ni maidani gida na haƙuri.
What gida fa
ka ce wallahi ba inda zan koma se naje inda nai niyya inkaga za ka koma in
ajiyeka ka hau mashin ni mashin haba Allah ya kiyaye inji kamin to seka shirya
zuwa inda nai niyya tun da dai mota tawa ce daɗin
abin nima inada tawa.
Kujerar da yake zaune ya ɗan tura baya ya kwanta
yahau gami da saka ear phone a kunne ya lumshe ido dan ya san halin faruk in ya
biye masa zai iya sa masa damuwa.
Birkin da Faruk ɗin
yaja ne yai mugun tsoratar da kamis yai saurin ɗayowa
hankali tashe dan zatonsa ko sun taka ko kuma sun kusa taka wani ne sedai ganin
gaban motar da suke ciki wayam ba kowa ya baima kamis haushi Haba faruk wannan
wane irin ɗaukar
alhaki ne kaji yadda gabana ya faɗi.
Faruk bai ba shi amsa ba ya ce kalli can kamis
ya kalla sai dai shi bega abin kallo ba mene kuma zan gani ka kalla mana me ka
gani me kuwa na gani banda tarin yara pls ka dai kuma kallo wai ko dai kai gamo
ne faruk kamis ya tambaya ni ban ga komi ba sai yara da mai suyar kosai.
Yawwa pls kuma kallonta yaɗan kalle ta kamin ya ce
mene kuma pls kata tama kama da me talla sosai ma gata nan ma tana abinta mtss
faruk yaja tsaki gami da buɗe
murfin motar zai fice kamis yai saurin jawo shi me kake nufi?, Ai malam ka jira
ni kawai in sayo mana kosan can mafi jin daɗin
shaƙatawar
kamis ya ce kaime za ka ci abin kan hanya lalle yau da ruwa da ƙanƙara
mutumin da a gida ma ba kowa ke girki ya ci ba Faruk yai murmushi gami da kwace
rigar sa jirani pls.
Ba kamar yadda ya za ta ba, awara ce ba ƙosai
ba yadda ya ganta da ya matso kusa mamakinsa sai ya ninku fiye da na baya anya
kuwa idon sa gaskiya yake faɗa
masa wannan yarinyar ko kaɗan
batai kalar wahala ba ya daurewa mamakinsa ya ce aban awara.
Ibrahim dake gefenta ya ce ta nawa dubu ya miƙa masa
ta ɗari biyu ok ya ce
ya hau zuba masa ba haka yaso ba yaɗanso
yaji muryarta ko zatai masa kama da ta ‘yan talla ita kuwa bama tasan yanai ba
suyarta kawai take.
Ibrahim na miƙa masa ya juya zai tafi tai saurin cewa
baka ji ba ya ɗan jiyo
da saurin jin muryar yai ta doki kunnensa bema tsaya tan tance damuryar yan
talla ko yan ƙauye take kama ba sabida yadda yaji daɗin muryar.
ta ce ka manta baka karɓi canjin ka ba yai ɗan murmushi no bar shi kawai yai gaba. Umar
yayanta da ke gefe yai saurin amsar canjin ya bi shi dashi.
Malam bakaji ba Faruk ya tsaya hannunsa umar
ya kamo ya danƙa masa canjinsa gami da faɗin
ba bara take ba in kana san kyautata mata za ka iya sayan abin da take saidawa
zaifi wannan kuma za ka iya bawa mabarata kamar Faruk yai magana ya fasa ok tom
na gode zam kiyaye ya juya yai gun motarsa.
Yana shiga kamis ya haushi da jaraba kan ya
tsaidashi shidai yamai banza gami da juya motar dan bema jin zai iya zuwa inda
yai niyya.
Kamis ya ce mene haka kuma ina za ka kaimu
Faruk yaja tsaki pls karka dameni kadai san bazan sace kaba ko ya faɗa cikin zafin rai kamis ya
taɓe baki iyi haƙuri
gami da komawa ya kwanta a jikin kujerar da yake yabar faruk cike da tunani kala
kala a zuciyarsa....
💞Thanks for reading 😍
💞 Don't forget to vote,
comment, share and follow 💞😍
Koda suka koma gida Faruk ko takan awarar
baibi ba ya fice daga motar bare abi takan rufe motar malam mene haka kana
nufin ni zan rufe ma ƙorar faruk ya watsa masa harara kabarta a buɗe to wannan fa ya nuna masa
awarar kai na siyowa ya faɗa
yana ƙara
harararsa gami da barin gun Kamis yabishi da kallo yana murmushin mugunta.
Hannu ya sa ya ɗauko
awarar gami da rufe motar yai cikin gida kai tsaye kitchen ya nufa ya zuba a
faranti ransa fal farin ciki dan ya san zai rama takaicin da faruk ya gama ba
shi ɗazu.
Yana fitowa ya ci karo da Bilkisu ƙanwar
Faruk a'a yah me kuma zakai da awara bari kedai Faruk ya siyo tasa dariya taɓ kaima dai yaya ina Yaya
faruk ina awara yai murmushi ai wannan ta dabance towo aci lpy tai ɓangaren ummansu.
Yana shiga ya tadda faruk yai rigin gine yana
duba wayarsa ya ba shi duka abaya yaiko saurin ɗagowa
mene haka banfa san iskanci ya faɗa
Kamis ya haɗe rai
kafasan bakyau anobazzaranci ka sayo abu kaku kuma bar shi.
Nace kai na siyowa a'a in baka ci kabaiwa
almajirai ya koma ya kwanta.
Ah to na gode ke nan me awarar ma zan iya
neman aurenta ke nan ko faruk ya ce duk yadda ka gani kai anman na gode kamin
zaɓi fa me kyau kaga
malam kamin shiru fa.
Kamis ya daure
ya ɗauki awara guda ya
gutsira ya ce kai anman wannan awara da daɗi
take ga kyau a ido kamar me seda ta nifa nayi sa'a waya ganni ran bikina da me
awarar nan kai mun fa dace ko Faruk takai ci ya ishi faruk ganin yai masa banza
ya sa kamis taɓo shi
ka mance baka faɗan
sunan matar tawa ba.
A zuciye Faruk ya ɗago ya kawowa kamis naushi kamis ya kauce yana
dariya haushi ya kuma kama faruk cikin fishi ya ce agidan ubanwa ta zama
matarka kamis ya nuna masa awarar hannunsa tinda na iya cin wannan ka kuma iya
sayo min yana nufin nine mijinta.
Bani abata
inji faruk kamis ya ce ta ƙarfi ne azo a kwata faruk ya miƙe yayin da kamis yai waje yana dariya
yako bishi.
Dakyar faruk ya amso awarar yazauna yana ci
seda ya ci wajen shiga sannan kamis yako sheƙe da dariya yana faɗin woo ni gaskiya fa nai ƙoƙari
koda yake kaine kai ƙoƙari waya san ma da wane irin kwano, ruwa gami da mai akai
ledar ma fa harwa ƙarni ƙarni da wari wari take tuni amai ya tawowa faruk ya miƙe yai
toilet kamis yaita dariya ko banza ya rama.
******
Farida ce
zaune tana duba tweet da retweet ɗin
malam Fajar sosai take jin daɗin
abin da take karantawa dan ayanzu ba ta da wani abin ɗebe kewa agunta fiye da karanta tweet ɗin sa da kallon hotonsa.
Kiran Fatahu ne ya shigo wayarta wani ƙululun
takaici ya ziyarci zuciyarta yana ɗaya
daga abin da ke ba ta haushi da Fatahu baya taɓa
tashi kiranta se tana cikin nishaɗin
duba saƙon
malam ba shi da aike se katse mata jin daɗi.
Har kiran ya katse ba ta ɗauka ba ganin yaƙi dena
kira ne ya sa taja tsaki cikin dakushasshiyar murya me cike da takaici tai
sallama.
Ya amsa cike da farin cikin samun nasarar yau
anɗaga kiransa
gimbiyata abar sona gami da burin zuciyata.....bata bari ya ƙarasa
ba ta ce pls bana jin daɗi
ne ka kira wataran tuni ya rikice me ya same ki nifa ince na ji muryar abar ƙaunar
tawa wani iri ashe ba ta jin daɗi
ne.
Taja ɗan
ƙaramin
tsaki mara sauti yawwa sai anjima ban cika san jin hayaniya ba ok Allah ya ƙara
afuwa sai nazo dubiya bai jira me za ta ce ba ya kashe dan ya san cewa zatai
kar ya zo bacin ba abin da idanunsa ke san gani face fuskar faridansa sedai
baida hujjar zuwa dan baya san ɓata
mata rai dan ya fuskanci zuwansa ke ɓata
mata rai.
Ita ko tsaki taja tsabar wulaƙanci
ni zai kashewa waya ta kuma jan tsaki kawai ta cigaba da dube dubenta a waya.
Shiko fatahu ya kashe wayar ya kira abokinsa
dake aiki a airport pls Nura jirgi da zaije kano nake so ok bari zan duba in
gani ya ce ya kashe wayar gami da shiga toilet dan yin wanka.
Tsaf ya kintsa yai ɓangaren iyayansa kai tsaye falon momy ɗinsa ya nufa dan ya san
Abbansu ya fice yadda taganshi cikin walwala yasata farin ciki saida suka ɗan taɓa fira kamin ya faɗa mata yana san zuwa kano
ta masa fatan alkairi gami da kashedin karya jima sannan ya fice.
Bala driver ne ya ɗaukeshi zuwa airport yana zuwa Nura ya ba shi
komi na tafiya ya masa godiya gami da alkairi mai yawa yai jirgi.
Koda ya sauka
a kano gidan kakanninsa ya nufa saida ya sake wanka sannan ya fice zuwa unguwar
su Farida ko tsayawa hira da kakannin nasa bai ba dan hankalinsa yayi kan
Faridansa.
Tana zaune
inda tai salla tana cin abinci yayanta ya shigo jaririyar Dady kinfayi baƙo ta ɓata fuska waye shi yaɗan saki murmushi yah fatahu
ne ta waro ido wane fatahun mubasshir ya watsa mata harara ke fa baki cika M
fatahu bako kara tai murmushi ai gani nan ɗazu
mukai waya yana Abuja banyi zatonsa ba yanzu yai ɗan
murmushi to dai yana jiranki.
Abaya ta saka milki mai adon golden batai wata
kwalliya ba ta naɗa
mayafinta tai falon baƙi ga mamakinta baya ciki gashi ba ta fito da waya bare ta ji
yana ina.
Farfajiyar gidan ta fito ɗan nesa kaɗan ta hangeshi zaune bakin
bishiyar mangwaro ta ƙarasa tana murmushi tun da ta tawo yake kallon ta ransa fal da
farin ciki dan rabon da yaga murmushin Farida tun kan ya ce yana santa.
Ta ƙaraso gami da gaidashi cike da mamaki ya
amsa wai yaushi Farida ta gaida bai gama mamakinba ya tsincin muryarta na faɗin yanzu yah haka ake zuwa
dubiya me makon ka shigo seka sa patient wahala.
Cike da farin ya ce kai wani da wahalar da
patient na san patient ɗin
ba ta san motsa jiki temako nayi ko ta ɗan
motsa nan suka shiga hira ran fatahu fal farin ciki ji yake kamar addu'arsa ce
ta amsu ayayin da ita kuwa farida daurewa kawai take ganin yadda yai takakkiya
ya taso duk dan kawai ya dubata.
Tausayin sa takeji ganin tayi duk iya rashin
mutun cin da za ta iya anman ya shanye gani take inta bi shi a hankula zaifi
fahintar ta ya janye ƙudurinsa na santa.
Thanks for
reading 😍
💞
Don't forget to vote, comment and follow 💞
Rubutawa
Faɗima Fayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.