Sun ɗan jima suna hira farida duk a takure take daurewa kawai take can ta ce Yah jikin fa patient ya motsa a rikice ya ce sannu meke damunku ta ɗan ya mutsa fuska ba komi to shi ke nan Allah ya ƙara afuwa bari in gudu se munyi waya ta daure ta ce ba za ka shiga ku gaisa da mami ba bari se na kuma zuwa.
Ta ɓata
rai so kake ta ce na kwace mata ɗa
ace kazo bazaka shiga ku gaisa ba gaskiya inbaka shiga ba za mu ɓata a'a to ba za ai haka ba
muje tai gaba ya bita abaya ji yake kamar ya ce ta zo su jera sedai yana tsoron
kar aljanun masifar ta su motsa ta butse masa.
Sosai mami ta ji daɗin ganinsu tare fatan ta Allah ya sa Fatahun
yayi nasarar shawo kan faridan.
****
Shi kuwa Faruk
tun daga wannan ranar kullin kome yake duk yadda aiki ya run ca ɓe masa se ya yakice yaje
inda Fatiha ke saida awarar ta ya siyo.
Tun yana siyan ta ɗari biyu ya koma ɗari uku yanzu kullin ta ɗari biyar yake siya duda
kuwa ko da wasa baya koda ɗan
ɗannawa burin sa kawai
ya ɗora idanunsa kan
yarinyar duda kuwa magana ko kaɗan
ba ta haɗa in ka ɗauke ta nawa tashi se
anjima mun gode shi ma se in Ibrahim me zubawa baya nan.
Sosai tsarin yarinyar yake birgeshi sana'arta
kawai take gashi da wuya kazo gun ka tadda maza da sunan cin awara sedai ta
zuba maka ka tafi da ita sa'annan da wuya kazo babu wani ƙaninta
ko wanta a gurin azaune.
Tun yana ƙaryata kansa da maganar kamis har ya fara
jin tabbas kamis gaskiya ya ke faɗa
masa sedai yaka sa yadda anya kuwa ta yaya kamar shi zuciyarsa za ta so wata
yarinya yarinyar ma wai me talla a hanya anya kuwa to anman me ya sa nake kasa
samun sukuni in idanuna basu ganta ba ya tambayi kansa.
Wayarsa ya ɗauka
ya kira kamis bugu biyu ya ɗauka
a'a mutumin yadai kira da sassafe haka Faruk ya ce matsalata dakai gajen haƙuri
inkayi shiru baka tambaya bama ai zan faɗa
maka to shi ke nan ina jin ka.
Daman maganar yarinyar nan zanma kamis yai
saurin cewa me awara faruk yaja tsaki Fatiha sunanta malam kamis ya sa dariya
lalle an tafi dakai wato har sunanta ka samo tsaki faruk yai ni abin da
shiririta wallahi.
To na ji na dena shiririta me kake san faɗan tambayarka zan ina jin
ka pls da gaske san yarinyar nan nake kuwa kamis ya sa dariya lallai naka wasa
ne wallahi kaga ni ba iskanci nace kamin ba kawai kaban amsa.
Sorry sir inji kamis ya faɗa cikin dariya kaga in
bazaka faɗan amsata ba
shike nan cikin sauri kamis ya ce gaskiya ban sani ba ko san ta kake anman ka
jira zuwa anjima zan zo kanon se muyi maganar in kuma ban samu zuwan ba zan
kuma kiran ka ok se mun haɗu
faruk ya kashe wayar gami da miƙewa dan zuwa ya kintsa.
******
Tafe take
cikin nutsuwa tai kyau sosai kallo ɗaya
za ka mata kasan tana cikin nishaɗi
sanye take da doguwar riga abaya baƙa mai adon duwatsu ja sai mayafin rigar
da ta naɗa akanta
Faiza ke nan ta fito ne zuwa gidansu malam fajar dan duba ƙanwarsa
Fatima kuma ƙawarta.
Kamar ko yaushe da faɗuwar gaba ta ƙarasa cikin gidan da ummansu Fatiman ta
fara cin karo a tsakar gida tana wanki har ƙas ta durƙusa ta gaida ta gami da mata ya me jiki
da fara'a umman ta amsa ai me jiki ma ta ji sauƙi ta ma fita ayya.
Shiru yaɗan
ratsa kamin Faiza ta ce umma kawo wankin in tayaki umma tai murmushi a'a yarnan
ki bar shi ki je ɗakin
ƙawar
taki ki jirata na san tana hanya ba nisa taiba a'a gaskiya umma ki kawo in taya
ki kinga indai aiki kike san tayani to ga kwanukan nan wanke min farin ciki ya
kama faiza tai ɗakin
Fatima ta ɗauko zani
ta ɗaura saman rigarta
ta hau wanke wanke.
Sama sama suke fira da umman wanda duk dai kan
karatune sosai umma kesan yarimya dan akwai hankali tanaiwa Fajaru sha'awarta
matsayin mata dan tasan zai ji daɗin
aurenta sedai ganin shi baya tunanin haka kuma tana tunanin ko yarinyar nada
wanda take so ya sa take barin komai cikin ranta.
Fa'iza na wanke wanken ne Abbansu fajar ya
shigo a'a yau su Faiza ne agidan tai murmushi ta gaidashi aiki ake haka ne eh
to Allah yayi albarka ta amsa amin umma ta cika da mamaki yadda taga sun gaisa
faram faram da Abban su Fajar tai mamaki sosai dan sanin da tai masa tun bayan
abin da ya sameshi na biyu ko yaransa bai damu da shiga sabgarsu ba tai mamakin
har sunan yarinyar ma ya sani.
Se ta ji tabbas yarinyar nan ta kuma kwanta
mata anman zatai ƙoƙarin tambayarta inta gane ba ta da wanda take so itakam za ta
sa fajar ya nemi aurenta in anyi sa'a sun dedai ta itakam zatai farin ciki dan
ta gaji da ganinsa ba aure da uzirin da yake ba ta mara kan gado.
******
Duk yadda
farida takai ga ɓoye
damuwarta ta gaja duk ta rame hankalim iyayanta duk ya tashi musanman
mahaifinta da Allah ya ɗora
masa santa.
Mubasshir ne ya shigo ɗakin nata dan sanar mata da kiran Dad sedai
yadda yaganta yasashi ruɗewa
yai sauri ƙarasawa
jikinta zafi rau alamun zazzaɓi
se rawar ɗari take ba
shiri yai waje ya faɗawa
Dad da gudu Dad ɗin
yai ɗakin Faridan
hankalinsa ya tashi sosai mubasshir ya sa ya kira likita yadda Dad ya tada
hankalinsa ko mami ba ta damu haka ba.
Koda likita ya zo ya dubata ya ba ta magani a
falo yake faɗawa su
Dad ai jininta ya hau sai malaria kuma hankalin Dad ya tashi da jin yarinya
kamar Faridan sanace jininta ne yahau itakam meke damunta.
Abakin gadonta Dad ya zauna yana shafa kanta
tausayinta duk ya cika masa zuciya ji yake kamar ya sa kuka gani yake duk
lefinsa ne.
Koda ta farka kan dad ɗinta ta fara ɗora
idanunta tausayinsa ya kamata tasan dad ɗinta
na santa ta ji sauƙi bakamar ɗazu
ba nan dad yasata agaba yana tambayarta damuwar me tasa aranta haka tai ta ce
masa ita ba ta sa komi aranta ba seda ya ba ta abinci taci suka ɗanyi hira kamin ya fice
zuwa nasa ɓangaren.
Yana shiga kukan da yake ɓoyewa ya kwace masa akullin
baya jin sukuni in baiyi kukan nan ba sedai yau duda yanayinsa zuciyarsa ba ta
dena masa ɗacin
takaici da dana sani ba damuwarsa ba ta ƙara ƙaruwa ba seda yaga farin cikin faridansa
ya fara yin ƙaura
tun alokacin damuwarsa ta fi ta da sedai tayau tafi ta koyaushe.
Farida yake gani abaya yaɗanji sanyi sedai baisan
kuskurensa ya shafeta.
Mami ce ta shigo ɗakin danjin Alhaji shiru yadda ta ganshi ya ɗaga mata hankali tasan
lokaci lokaci yakan keɓe
yayi kuka sedai baya bari ta ganshi sedai fa yau kamar damuwarsa tafi ta kullin.
Da hanzari ta ƙarasa sedai me makon ya dena kuka kamar
yadda ya saba in yaganta sedai yau kamar an tinzirashi.
Daƙyar ta samu yai shiru haba Dadyn Farida
yanzu in farida ta zo taganka ahaka yakake jin za ta ji dan Allah ka daure ka
mance da abin da ya faru dan Allah.
Haba Bilkisu taya kike gani zan mance bacin na
san yana rubuce a littafina haka ne anman ai Allah gafururrahimu ne anman baya
yafe haƙƙin
wani kema kinsani hakane anman ya san yadda kayi nadama.
Ni tsoro na kar abin da nayi ya juya kan
yarana ina tsoron ko shike bibiyar Farida bama shi bane Allah ba ya zalunci
baya kama wani da lefin wani ka ci gaba da neman yariyar sa su kuma karka kaza
wajen musu sadaka tun da....se kuma tai shiru ka tashi ka je kayi wanka ta miƙe za
ta shiga toilet ɗin.
Hannunta ya ruƙo ta jiyo ya ce na gode Bilkisu na gode
Allah da besa nayi kuskure biyu ba kuskuren rabuwa da ke alokacin da idona ya
rufe na gode da haƙurin da kikai dani ta murmusa karkaji komi har abada ni
mesanka ce ya saketa ta shigo toilet ɗinta.
Tana shiga ta share kwallar da ta tawo mata
dan mikin da ya daɗe a
zuciyarta takejin kamar ya warke ya taso ji take kamar tasa ihu sedai tana san
kwanciyar hankalin mijinta dole ta shanye damuwarta ta fito tana murmushi oga
ruwa ya kammala ya shiga ita kuma tai nata ɗakin.
Ni kam na fito cike da tunanin ko mene suke
kokawa akai oho
💞
Don't forget to vote, comment and follow 💞
Wajan biyu na rana kamis ya iso kano saida ya
ci abinci sa'anan suka fara tattauna maganar da suka fara ɗazu a waya.
Faruk ne ya fara magana da faɗin ple kamis ka faɗan meke damun zuciyata game
da Fatiha na kasa na kasa ganewa shin san ta nake ko kuwa, dariya sosai kamis
ya sa cikin fushi fatuk ke faɗin
kaga malam abin da iskanci dan kawai na tambaye ka bayana nufin na zama shasha
ba da za ka tisa ni aga kana faman min dariya.
Cikin dariya mai ƙular da tai kamis ke
magana ai kai ɗin ne
dole ama dariya ace kaida zuciyarka baka sam me take ciki ba ina kuma gani da
ba'a jiki na take ba.
Mtsss faruk yaja tsaki gami da miƙewa
zai bar ɗakin kamis
yai saurin kamo hannunsa haba nawan da wasa nake ai kai kasan hakina sai slow
zauna mu tattauna ya fara ƙoƙarin kwace hannunsa kamis ya marairai ce haba nawankayi haƙuri
mana kazauna in faɗa
maka me na fahinta.
Fuska a haɗe
faruk ya koma ya zauna yayin da kamis ya fara da azahirin gaskiya faruk bana
jin san yarinyar nan kake faruk ya ɗago
cike da fara'a haba koda na ji nisan ba san ta nake ba wallahi shiru ya ɗan ratsa kamin faruk ya ɗago ya dubi kamis to anman
faɗan meke damuna game
da ita da kullin nake san ganinta da san jin muryarta.
Fakar idon faruk kamis yai yaɗanyi murmushi dan ya san
yanayin dariya abu zai zama rigima.
Eh to nima
gaskiya abin da meke damun zuciyar ka da ita ba ina ganin kai za ka fi kai za
ka fini sani cikin fushi faruk ke faɗin
inda na sani ai da bazan kiraka neman shawara ba.
Kasanme inji kamis duk alamu sun nuna
zuciyarka ta kamu da san ta cikin fushi faruk ke faɗin Allah ya kiyaye ta yaya ma hakan za ta yiwu
eh shi ya sa nace aɗazun
nace gaskiya abin da meke damun burnin zuciyar ka ba sabida ita soyayya ba
ruwanta da asali masoyi baya kyamar masoyinsa sai dai kai kana kyamar ta tun da
bazaka iya cin abin ta ba ni abin da meke damunka ba dole ka yadda abin dai ba
gaskiya kai za ka zauna ka gano da kanka in yaso sai mu gano mafita ya miƙe zai
bar ɗakin.
Har yakai bakin ƙofa ya dawo kasan me kamar yadda na faɗa ɗazun ina jin a jikina kamar kuma yadda alamu
ya nuna san ta kake sedai ego ɗinka
ya hanaka fahinta bai bi ta cewar faruk ba yai ficewarsa yayin da faruk ɗin ya bi shi da mugun kallo
cike da takaicin cewar da yai wai san ta mai awarar nan yake.
*******
Umman Fajar ce
zaune suna hira da mai gidanta cikin dabara ta bijiro masa da abin da ke ranta
Abban fatima ta faɗa
murya ƙasa
ƙasa
a nutse ya kalle ta na'am umman fajar cikin nutsuwa take faɗin daman maganar Deeni ce
nan da nan ya sauya fuska kardai kice wannan zsncen zaki kuma min ba shi bane
saidai zai iya shafar sa to indai ba shi bane ina jinki.
Eh to daman gani nake yaron nan ya girma ya
kusa talatin da biyu ka duba ka gani duk suna da yara shi ne nake ganin ko za
ka sa baki ya daure yayi aure ina ganin zaifi jin Maganarka tinda ni bai ɗauki maganata da mahimmanci
ba.
Cikin fushi da
faɗa yake faɗin ba nace miki ki dena
sani cikin harkar yaran nan ba inyaga zai yi aure yayi in ma bazaiba ni babu
ruwa na ya miƙe zai fice.
To shi ke nan na ji zan yi iyayi na har ya
yadda yayi auren kasan baida inda zai zauna ka ba shi izini koda iya ɗakinsa na yanzu ne se ya
zauna kafin Allah ya hore masa inma kinaso ni sai in dawo ɗakinki ya haɗa da nawa ɗakin kawai asani ciki ne
bana so yai waje tai saurin cewa dan Allah ka dawo mu ƙarasa wallahi bazan saka
ka ciki ba.
Dawowa yai ya zauna ita kuma ta ɗora da daman na yanke wata
shawara ne na san baida wata budurwa shi ne nake neman shawarar ka kan ina san
ya auri yarin yar nan ɗalibarsa
fauziyya matsayin ka na uba nakesan ji daga gareka inka amimce.
Indai yarinyar ta amince ai ba komai nima na
yaba da tarbiyyar ta shi ke nan ta ce eh ya tashi ya fice yai ɗakin sa ransa a tunkushe
shikadai ya san meke damunsa alwala yai yayi nafila gami da roƙon
Allah inda alkairi a abin da da Salima kesan haɗawa
Allah ya tabbatar.
******
Duk yadda
faruk yakai ga daurewa zuciyarsa kan bazai kuma zuwa gurin yarinyar nan mai awara
ba sai dai hakan ya ci tura kusan kullin sai yaje yake samun sukuni sai ya dawo
takaici da haushin kansa duk ya cika masa rai.
Yau kusan kwana uku ke nan yana zaryar zuwa
gurin saidai babu ita babu dalilinta hankalinsa duk ya kasa kwanciya.
Sannu a hankali ya yardarma zuciyar sa tabbas
tabbas ta kamu da san yarinyar nan so mai tsanani sai dai rashin ganin ta gurin
sana'ar ta shi yafi komai ɗaga
masa hankali gashi ko ‘yan matasan da ke zama gurin baya ganinsu bare ya tambaye su.
Kamis ya kira awaya kuka riris yake masa wai
yai gamo sosai kamis yai dariya wallahi faruk kanada matsala na rasa yaushe za
ka girma wataran in ina ma kallon gentle kawi se ka dawo sha..... Yai saurin
rufe bakinsa dan ya san halin faruk da fushi ya sauya maganar da faɗin dan baka ganin ta ai ba
yana nufin kayi gamo bane malam ka je area ɗin
ka tambayi address ɗin
gidansu cike da farin ciki sukai sallama faruk ya kashe wayar.
💞
Don't forget to vote, comment and follow 💞
Rubutawa
Faɗima Fayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.