Yauma kamar kullin tana zaune aƙofar Faculty ɗinsu ta baya tana kallon ɗaliban dake shawagi tsallaken Faculty ɗin wato geography kamar ko yaushe gurin ya kalla tana zaune shikam zai so jin meke damunta da kullun take zaune ita kaɗai cike da tunani shikam zaiso jin matsalarta ko zai iya magance mata ita ya fuskanci damuwa ce ta ke damunta har take zuwa gurin ta zauna.
Motarsa yaja acan ɗan nesa da ita ya ajiye ya tako inda take
kamar rannan sallama ya mata saidai yau ɗinma
ba ta amsa ba.
Bai damu da rashin amsawar tata ba ya sa
littafin hannunsa ya ɗan
taɓo ta tai saurin
jiwowa a tsorace sannu ko yafaɗa
yana mai nuna mata littafin hannunsa alamu da shi ya taɓata na miki sallama baki ji ba ko zan iya zama
ba ta ce komi ba iya ɗan
kallonsa da tai da alamu nazarinsa tai kamin ta ɗan
matsa alamar ya zauna batare da ta ce kasa komi ba zama yai gami da cewa na
gode ba ta ce komi ba ta cigaba da kalle kallenta.
Sunkai minti talatin kamin ta ɗan duba agogon da ke
hannunta miƙewa
yaga tayi ba ta ce masa komi ba ta bar gurin juyawa yai yabita da ido harta ƙule
sa'annan shi ma ya tashi yabar gun.
Tun daga wannan ranar kullin ya kanzo saida ba
maganar da take haɗa
su ahankula yake nazarinta so yake ya gama fahintar ta kamin yai tunanin yadda
zai shawo kanta sai dai ita ɗin
tana da wuyar fahinta har yau abu guda yakai ga fahinta game da ita wato tana
da damuwa babba.
Allah mutumina kana abin da kake so a Faculty ɗinnan tamu yaɗan murmumusa towo me nayi
kuma ai kaima kasani kagafa yadda kake jan yaran mutane aƙas yaɗan ja ƙaramin
tsaki fahintar dani nake jansu aƙas kamar yaya fa.
Ai kaima kasani ah haba na sani kamar ya fa haba
malam ai ƙarya
kasa sanin yadda ‘yan matan Faculty ɗin
nan suka gama matowa akanka.
Ni kuma ya dafe ƙirji gami da zaro ido su waye ke nan
mahamud ya sha kunu kai abin da iskanci muma mukasan suna sanka bare kai da ake
so sai kaita jan aji har ajin ya tsinke wai kai baka fahinta ba.
Ina kuwa zan fahinta ina kaima malami ne me ya
sa kai baku gano suna sanka ba ko kuwa za ka ce min sa idon naka basu gano haka
ba ko kuwa na taɓa
baka labarin wata cikinsu ta zo guna zance ko kuwa kai sun taɓa baka saƙo ka kawon
eyy yadda ya wani haɗe
rai ya tsare gida yana magana yabaiwa Mahmud dariya.
Dariyar da ya sa ce tabaiwa Deen haushi yai
tsaki kana da matsala Mahmud wallahi ya miƙe yabar office ɗin.
Farida ce zaune cikin motar ta tana duba
course ɗin D dan
Captain ya faɗa mata ɗazu wai ta zo zai mata test
ƙarfe
uku hakan ya sa take ta duddubawa tasan duk mugunta ya taka shi ya sa yaƙi fawa
Captain ɗin sai ayau ɗin wato inbata zo bama shi
ke nan se ya ce ba ta zo ba in tai kamar za ta ji haushinsa sai kuna zuciyarta
taka sa jin haushin nasa itakam gangar jikinta na faɗa mata zuciyarta cutar ta kawai take sedai ta
kasa fahintar haka.
Tana ganinsa ya fito daga office ɗin malam mahmud ta miƙe ta
bi bayansa.
Yana shiga ta kwankwasa yafi minti uku kamin
ya ce yes shigo da sallamar ta tashiga ya amsa murya ƙasa ƙasa za
ta rufo ƙofar
ya ce mene haka zaki wani rufen ƙofa tai saurin barinta a buɗe ita ɗin ba mai tsoro bace
maganar maza ba ta tsorata ta ko dan cikin masa ta tashi oho sai dai shi
kwarjinsa yai yawa muryarsa razanar mata da zuciya take.
Shigowa tai jiki a saluɓe gami da gaidashi ina jinki ya ce ba tare da
ya mata amsar gaisuwar da tai ba eh daman Captain ɗin level 2 Department of phsycology ne ya ce
in zo kana nema na.
Ɗagowa yai yaɗan kalle ta gami da faɗin ni kuma to kimin mene cikin rawar murya ta
ce nice wadda level coordinator ya ko takardar banda lafiya za'amin make up
nazo ka ce se naje gunsa ok Farida ko ya faɗa
idonsa kan takardar da yake karantawa tai saurin cewa eh tana murmushi.
Tsaki yaja shi ne kuma daga dawowata zaki wani
zo eh daman monitor ɗin
namu ya ce inzo before 3 ya ɗan
kalli agogo 3m to 3 se kuma kizo min office ke kaɗai
ki je in kin samo wanda zaku zauna sai kizo a miki 3 nayi time ɗinki ya fara tafiya 30m
kawai zan baki.
Ta buɗe
baki zatai magana ya shige ɗakin
dake haɗe da office ɗin fiska a haɗe.
Futowa tai rai aɓace
itakam yau ta shigesu Ma'u ba ta zo ba gashi time ɗin baida yawa bare ta kirata awaya ta ce ta zo
gashi ‘yan
ajinsu babu wanda suke magana ba wanda tasan sunansa mace ko namiji afuska
kawai tasan wasu....
Don't forget
to vote, comment and follow
Tsayawa tai
rai a tunkushe wani ɓarin
na zuciyarta na faɗa
mata rashin kyautawarsa inda ɗayan
ɓarin ke ce mata ai
dedai yayi in yana barin kowa sasakai bama tsari tana cikin tunane tunanen ne
ta rasa madafa ta hangi wani ɗan
ajinsu batasan sunansa ba sai dai tana ganinsa a ajin da sauri ta ƙarasa
inda yake ta masa sallama.
Ya ɗago
ya kalle ta gami da yin murmushi kamin ya amsa tace.
Sannu ko ta ce dan Allah tai mako za ka min
mamaki ya kamashi tai mako kuma fahintar mamakin nasa tai ta ce kaga wallahi
Malan Deen ne nai missing test ɗinsa
so zaimin make up ya ce sai nazo da wanda za mu zauna tare bai san mu zauna mu
biyu a office ɗin inba
damuwa ka temaka kazo mu zauna ok ba damuwa muje ko ok na gode ta faɗa.
Yai gaba ta bi shi abaya Nasir na shiga Deen
ya ce lafiya daiko tai saurin shigowa dan Namiji da sauri ya rigata shiga ta ce
danman shi ne frnd ɗin
nawa dazai tsaya ni inyi test ɗin.
Ɗan kallon Nasir ɗin yai gami da taɓe baki kai ka zauna anan ya nuna masa kujerar
da daga ita sai ƙofa ke kuma ki zauna anan ya nuna mata kujerar kusa da tebur ɗinsa tai saurin shigowa
sosai dan zama mene haka kuma zaki barmin ƙofa a buɗe
ya faɗa oh my goodness
ta faɗa ɗazu fa ya ce danme za ta
rufe ta buɗe yanzu ya
ce danme shikam mutumin nan ya cika matsala wani zubin.
Da sauri ta koma dan rufewa wasu ‘yan
mata suka shigo suna ta baza ƙamshi anci ado kai ka ce wani gidan biki
zasu gurin Dinner.
Lafiya dai ko ya faɗa yana ƙara haɗe
girar sama da ƙasa daman sir za mu wuce ne mukaga ƙofar office ɗinka a buɗe shi ne muka shigo dan
gaidaka ok ya muku kyau zaku iya tafi suka tsaya sororo cikin fishi ya kuma
maimaitawa nace zaku iya fita dasauri suka fice dan yadda yai maganar ya basu
tsoro.
Daɗi
ya kamata har hatasan sanda tasa dariya ba Nasirma ya sa dariya ya ɗan kallesu ya watsar zaki
rufe ko kuwa cikin time ɗinki
kike tai saurin rufewa ta zo ta zauna.
Question ya ba ta rubuce cikin paper ɗin da za ta amsa ya ce
inkin magana ko kika ci gaba da wannan dariyar zan yaga kinyi missing time ɗinki ya daɗe da shiga sauranki 15m nan
ta ci gaba da abin da take.
Time na cika ya amshe ta miƙe za
ta fice ya ce no ki tsaya ki tafi da abarki nan ya fara dubawa sosai yai
mamakin yadda ta amsa baiyi zatom za ta iya haka ba tai ƙoƙari ahankula ya ɗago ya kalle ta ya taɓe baki not bad ya faɗa ya maka gami da shigar
mata da marks ɗinta
computer ya ba ta ta fito ranta fes.
Ko da suka fito Nasir tama godiya kamin ta ce
in bazaka damu ba sunanka mana yai murmushi Nasir taɗan murmusa oh ashe ma Dad ne ashe shi ya sa
kamin mutunci any way zan riƙe ni am Farida na gode fa Maisunan Dad ya
ce no bakomi farida tai gaba ranta fes shi ma haka yau shikam sunyi magana da
farida ashe tana da kirki ba kamar yadda suke ganinta a class mara mutunci ba.
Tana tafe amota tana sakin murmushi yau ta ji
sunanta bakin D kai satinnan tana caɓawa
ta sami hotonsa yau kuma ya kira sunanta ai tana zuwa danja saida tai sadaka
dan ita kaɗai tasan
farin cikin da ta ji tana san sauran bayain Allah suma suji daɗi yau ɗinnan.
Ko agida kowa ya san yau Jaririn mom da Dad
ana cikin farin ciki yadda Faruk yaita tsokanar ta shi dole saita ɓata rai anman abanza.
Kwance take rungune da paper ɗin da ya marker lokaci
lokaci takan shishina ta dan shaƙar kamshun dake jikinta ayayinda
kunnuwanta ke tariyo mata da sautin sa alokacin da ya ce Farida ko tasan yanada
sanyin murya muryarsa me daɗi
ko lecture yake sedai lokacin da yake faɗin
sunan se takejin kamar Muryar ta ƙara daɗi
itaman tasan duk duniya babu wanda yafi D ɗinta
iya faɗin sunanta.
Taso ina ma ace Ma'unta ta zo ta taya ta murna
ta ji D yakira sunan wayyo me ya sa ma'u baki zo ba waya ta ɗauka ta kirata ummansu ce
ta ɗaga seda suka
gaisa ta ce tai bacci ko abata kinsan ba ta jin daɗi lah wallahi umma ban sani ba ba ta faɗan Allah ya ƙara
sauƙi
ta kashe wayar duk farin cikinta sai ya ragu Allah sarki Ma'una ko meke damunta
gobe zan je dubata ba ta san sanda tai bacci ba rungune da paper ɗin.
Washe gari ta shirya ta faɗawa ummanta za ta duba ma'u
umman ta ce ta mata sannu sosai ta ji tausayin ƙawar tata dan yarta ɗan faɗa taita mata sannu nan ta
faɗa mata ai jiya D ya
kira sunanta ma'u ta kalle ta cike da tausayi ta daure ta taya ta murna
Da yayan Ma'uɗin ya shigo ne ta ba shi
paper ɗin data ninke
tasa aleda ta ce Yah Aminu pls faɗan
sunan turaren nan ya amsa ya shinshina ya jima kamin ya faɗa mata tai godiya ta san
intace yayunta su faɗa
mata se sun isheta miƙezan wuce kar in makara se na kuma dawowa.
Kai tsaye sahad ta wuce ta siyo turaren tabbas
shi ne tai makaranta ita kaɗai
tasan me take shiryawa aranta..
💞Don't
forget to follow, Vote and comment💞
A mota tabar
turarenta tai aji dan tasan malami ya kusa shiga kasan tuwar Dr tijjani baya
jimawa hakan ya sa ba ta wani jima a sch ɗinba
tai gida ranta cike da farin ciki.
Duda tana jin yunwa kasa zuwa tai gurin
abincin tai ɗakinta na
sama bayan ta cewa mum ta dawo turarenta ta ɗauko
se alakacin ma ta rasa ya zatayi ganin duk a rufe suke ma'u ta kira dan
tambatarta nan ta faɗa
mata sukai sallama.
Roba ta samu ta haɗe turen da wanda ta siyo daɗi ya cikata inda ƙamshin
yabada wani sanyin ƙamshi nai daɗi
ji take kamar ita da shi ne suka haɗe
suka zama mata da miji farin ciki ya cika ranta.
Zaune take lokaci lokaci tana kallon gefen
kujerar da tak zaune aranta tanata tunanin ko lafiya mutumin da ke zuwa ya
zauna kusa da ita yau kwana uku baizo ba tasabs sosai da jinsa a gurin duda
kuwa ba ta taɓa ido ta
kalle shi ba bama za ta iya ganeshi ba in sun haɗu
ahanya saidai ance mutun rahama ko yaya yake duk se takejin babu daɗi fatanta de Allah ya sa ƙalau.
Ya jima a bayanta yana Nazarinta yaɗan saki murmushi kamin ya
tako ya ƙaraso
dan ya fuskanci tana jimamin rashin mai zama kusa da ita ashe dai tana sane da
zamansa a gurin dan basu taɓa
magana ba ko sallamar sa ma dabadan yakanga bakinta na motsawa in yayi da ya ce
ba ta amsawa.
Sallama yai mata kamar koyaushe jakarta ta ɗauke gami da matsawa bai
damu da jin amsar ta ba yaja ya zauna taɗan
kalleshe asaninsa tun randa ya fara zuwa gurin taɗan
kalle shi tai nazarinsa bai ƙara ganin ta ɗago ido ta dube shi ba ta ce bakazo ba kwana
biyu ta faɗa a hankula
abubuwa suka min yawa ya ba ta amsa.
Ba wanda ya kuma magana cikinsu can ta miƙe
bayan kallon agogonta gami da saɓa
jakarta da alamu gun takesan bari ɗan
ɗagowa yai daga kallon
wayar sa da yake ya ce bakya ganin dacewar cemin kin tafi.
Ta ɗan
kalle shi ai ba gida naiba zan je salla ne in dawo inda gidai nai zsnce na tafi
ok shi ke nan sunanki fa taɗan
kalle shi kamin ta ce FATIHA ok kawai ya ce gami da miƙewa ni bara inwuce ba ta
ce komi ba tai hanyar masallaci.
Shi kam yarasa meke damun yarinyar nan be san
ta ba haka kawai yake jin tausayinta tsoronsa kar damuwa ta cutar da ita.
Fatiha ce ta fito cikin shirin ta tsaf
natafiya makaranta ta dubi ummanta daketa faman fifita wutar da tun ɗazu take takesan ta kama
sai dai da alamu icen ɗanye
ne umma ni zan tafi a'a Fatiha bazaki tsaya kici ɗumamen
bane eh umma na makara toshi ke nan Allah ya tsare akula insha Allah umma amana
addu'a Allah ya bada sa'a amin umma ta faɗa
tana shirin barin sashen nasu.
A babban zaure ta ci karo da yayanta lah yah
yaushe ka dawo jiya dadaddare ayya ban saniba fatan andawo lafiya Alhamdulillah
ya faɗa badai har
anfito ba eh wallahi ayya to tsaya in shiga in gaida umma se in rage miki hanya
toyaya anman karka jima.
Ababur ɗinsa
ya ɗauke ta suka tafi
wanda tun da suka fara tafiya bawanda ya ce da wani ci kanka adaidai ATC ya
tsaya ta sauka ya zaro duku huɗu
ya miƙa
mata ki ririta na san wancan sun ƙare ko a'a yaya ka rage da saura a'a ki
riƙe
na san zan ɗanjima
banzoba in na koma to yaya na gode Allah ya saka da alkairi amin ya ce tai gaba
inda zai kaita inda za ta hau motar zuwa sabuwar jami'a.
Ya jima ya kallon ƙanwar tasa ransa fal
tausayinta kamin yaja mashin ɗinsa
yai gaba cike da fatan inama yana da arziƙi ya farantawa ƙanwar tasa sosai tun da
ya taso yake tausayin rayuwarsa sai dai randa ummansa ta haifi Fatiha sai yaga
shi cikin farin ciki mayake dan tun ranar aka fara kunsawa babyn abin rashin
kyautawa har kawo yau.
Sosai yau yai mamakin rashin ganinta a gurin
bacin kullin a irin wannan lokacin yakan ganta to ko ta daina zama ya faɗa dana fi kowa jin daɗin hakan ya san damuwarta
ta tafi ke nan dan baisan zaman da take tai tsit agun.
Tun randa ya fara zuwa earth and environmental
dan musu GSP idonsa ya faɗa
kanta ada yai zaton shaƙatawa take saidai asannu yana nazarinta ya fahinci damuwa
kawai ke kawota gurin.
Yana shirin barin gurin yaji Sallamar ta ya
amsa ba tare da ya kalle ta ba ba ta damu da hakan ba ta ce zan iya zama yaɗan matsa ga mamakin sa
murtarta ya tsinkaya tana faɗin
barka da safiyya.
Barka dai Fatiha yau bakizo da wuri ba taɗan juyar da kai gami da faɗin na makara ne ok yayu
kyau ya faɗa
littattafin ta taɗauko
ta hau dubawa yai mamaki baiyi zaton damuwar ta na barinta karatu ba.
Miƙewa tai ni bara inje za muyi test ok
anman bakya ganin dacewar ki tambayeni sunana tai murmushi akaro na farko daya
taɓa ganin tai
murmushi ta ce ai baka ce in tambaya ba shi ma yai murmushi gami da faɗin shi ke nan yau na roƙa.
Murmushi ta kumayi shi ke nan baka faɗan sunan ka ba shi ma
murmusawa yau ya ce FAJARUDDEEN zaki iya kirana Fajaru ko Deen oh masha Allah
ta ce zan riƙe
insha Allah tabar gun ya bita da ido kawai kamin shi ma ya miƙe
yabar gun.
💞
Don't forget to vote, comment and follow 💞
Deen ne zaune
yana cin abinci Mamansa na kallonsa da alama jira take yagama cin abincn suyi
magana Fatima ce ta fito riƙe da hijabi tana ƙoƙarin sawa take lah yaya baka tafi ba eh
kawai ya ce ya cigaba da cin abincinsa ta ce umma ni na tafi to Fatima Allah ya
bada sa'a Amin umma.
Har takai bakin ƙofar ɗakin
ya ce Fatima inkin je kice ma Muhammad ya riƙen ajin zanzo anjima to yaya.
Bayan ya sha
ruwa ya matsar da kwanon ya ce yawwa umma naga kamar kina san muyi magana eh na
ji kafe za ka makaranta ka je inka dawo ma tattauna kar yaran suyi ta jiranka
a'a umma ba komi na san Muhammad zai kula dasu kamin inje to yayi kyau ta faɗa.
Fajaru daman ba komi nake san mu tattaunawa ba
face batun aurenka agaskiya na gaji da ganinka babu aure sa'oinka duk sunyi
auren nan sun barka ada na ji karatu kake yanzu fa me kake eyyi.
Yaɗan
sosa ƙeya
anman mama....karka cemin komi yanzufa ka duba makarantar nan taku ta mangariba
tun kuna Ɗalibai
har kun zama ku ke tafi da ita jibi fa duk wanda kuke malinta da aurensu da
yaransu anman mama kin mance duk sun girme min dan dai kawai munyi aji ɗaya ne yimin shiru da nawa
suka girmekan eyyi jibi fa Badamasi yaransa uku fa yanzu shi ma ai tare kukai
wasa.
Kai umma dan Allah dudu fa shekaru na bawa ashirin
da takwas fa ni ban ga girman da naiba eyyi ah lallai ashirin da takwas in aƙauye
ne ai ya aurar da ɗiya
to ai umma nan ba ƙauye bane birni ne ki ci gaba damin addu'a insha Allah zan yi
aure kamar yadda kike so karma kayi kaita jamun magana gurin mahaifinka shi ke
nan ki yi haƙuri
umma zan yi ni na tafi kar yaran suyi ta jirana.
Fatima ce tafe tana ta zuba dan batasan makara
sabida yau malam Nasiru keda duty duka zai mata ba ruwansa jitai an ƙwala
mata kira tai saurin jiyawa ganin Faiza ya sa ta faɗaɗa
murmushin fuskar ta tana faɗin
anti Faiza kema kin kusa makara bari kawai Fatima inata sauri kar malan ya
rigani zuwa Fatima tai dariya baima fito ba nabar shi yana cin abinci.
Faiza ta ɗan
saki murmushi ah kice yau zai zo eh zaizo ya ce min ince malam Muhammad ya jire
ku kan ya zo daɗi ya
ziyarci faizs ta ɗanyi
fari gami da murmusawa ba tare data ce komi ba itakan ta rasa meke damunta aduk
ran Litinin take jin daɗin
zuwa makaranta muje to kar mugun can ya dake inji Faiza uhun ku da baima bama
ke nan inji Fatima sukai dariya baki ɗaya
gami da yin gaba.
Zaune suke suna muraja'a ya shigo daɗi ya cika shi aduniya ba
abin da ke masa daɗi
kamar gari ya waye magariba tai yazama yana da lokacin zuwa makarantar dan
ganin ɗalibansa na
gurfatu Aliyu bin Abi ɗalib
yana san yaran tun suna ƙana na yake koyar da su har kawo yau da duka girma aka fara
aurar da wasun su.
Suna ganinsa sukayi shiru dan gaidashi ya amsa
cike da annashuwa kai baka ce shi ne wannan Deen ɗin
da baya dariya ba.
Aisha ce ta ce malam yau ka makara yai
murmushi Aisha sarkin mita ai saiki aika a ɗauko
bulala ki daken ta dabe fuska wa ai nayi kaɗan
ah haba dai kinfa yi yawa tun da gashi ana min ƙorafi.
Ya dubu Ruƙayya ya ce ah su Rakiya ba magana ta turo
baki dan batasan sunan tun tana yarinya in yaso tsokana sai ya ce Rakiya ta ce
kai malan dan Allah idanta yai rau rau yai dariya ai na kusa dena faɗe Ɗaha ya ce ai malan ko
kadena faɗe mudai ba
za mu dena ba Ɗaha abokin faɗan
Ruƙayya
ne malan yai dariya nima ai ba yanzu ba ta watsawa Ɗaha harara ‘yan
mazan suka sa dariya.
Fa'iza da tun da ya shigo ta ɗan kalle shi gabanta ya faɗi ba ta kuma kallonsa ba ta
rasa me ya sa kan ta ganshi saita tason ta ganshi tana ɗora idonta kansa gabanta zaita faɗuwa takanas take kwalliya
ta rafi layinsu sai dai ko motar sa ta gani sai ta tajin gabanta na faɗuwa.
Ya santa tun tana ƙarama ba ta cika magana
ba sai dai ba kamar yanzu ba bai tunanin komi ba zatonsa ko nata ‘yan
matancin ya zo a haka.
Aliyu ya duba ya ce Ali wai yaushe za mu sai
banki ne Basira tai saurin rufe fuska dan tasan kan zancen bai ko kalle ta ba
ya ce zan bawa Ali ya sayo in yaso sai duk me shi ya dinga sawa nima innazo zan
dinga sa nawa suka ce to.
Al'adar ajinne duk sanda aka sa ranar auren ɗalibar ajin sukan sai banki
dan tara kuɗin mata
gudun mawa tun bai fara aiki ba har yakai ya fara in sun tara yakan shawar ce
su me zasu siya ya cika asayo abawa amarya..
Yanzu bikin Basira ya tashi shi ya sa yakesan
su fara tarin tun da sai bayan azumi.
Aimana ta dube shi ta ce malam wai kai yaushe
za ka yi aure ne mu sai aita mana gori namu baban yaƙi aure yai dariya sai na
gama aurar da ku inkuma kun gaji se ku min auren ai zainab tai saurin cewa
munbana Faiza.
Faiza tai saurin ɗagowa daka kan littattafin da take dubawa ya
ce kinci gidanku zainab maza ku ɗauko
littafin ku na muku ƙari ina da wancan ajin.
Saida ya gama biya musu ya tabbatar sun iya ya
sa suketa maimaitawa yau Babban aji.
💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞
Rubutawa
Faɗima Fayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.