Ticker

6/recent/ticker-posts

Fajaruddeen (Kashi na 4)

Saida ya gama biya musu ya tabbatar sun iya ya sa suketa maimaitawa yau Babban aji.

 Yana barin ajinsa ya wani haɗe rai kai baka ce shi ne yanzu yake ta faman dariya ba dan ya tsani babban aji yaran ko kaɗan basu da kunya ada suma yakan ɗan musu wasa saidai ko ganin fuska sukai oho sune harda kawo masa letter tun lokacin ya bar sakar musu fuska dan yaga raini na san shiga tsakani.

 Suna ganinsa suka shiga tai tayinsu sai ɗan magana da suke ƙasa ƙasa wadda duk ba ta wuce kan shigar sa ta yau ba dan kayan da ya sa sun amshe shi duda dai shiɗin ko wani kaya ya sa kai ka ce danshi akayi.

 Yana musu ƙari suna ƙus ƙus zahra tafe kinsan mai sadiyya se kin faɗa wallahi malam Fajar ya haɗu ke sai yau kika gani inji Badairiyya a'a kawai dai yau naƙara gani kudai kubari ai duk makaranta albarka ina jin malan Nasiru ne kawai zai iya takara da shi a fagen kyau shi kuma ya sa mugunta aransa Kulsum ta ce to ba gwanda mugun ba yana dariya shifa wannan shashashun ajinsa kawai yakewa dariya.

 Kai ashe kema kin sani ai inna ganshi a ajinsa se inji kamar anya shi ne kuwa bari kawai ji nake kamar in koma ajin nasa inji zainab taɓ koro ki zai yi.

 Yana ganinsu duda baya jin me suke cewa sai dai yana jin ƙus ƙus ransa ya ɓaci dan ya tsani yana ƙari ana magana ya miƙawa usama littafinsa da ya ara ya ce abin da wulaƙanci ina da abinyi na taso dan muku karatu tsabar wulaƙanci sai ku dinga surutu inkun san karatun ne bakwa so ai sai ku zauna agida ko ce muku akai banda abinyi ne to indai nine na dena shigowa ajin nan sai ku nemi wanda zaku raina.

 Mansura ta ce Allah ya isa wallahi banzaye kawai dan ita tana san karatun dan sosai take gane abin da yakeyi suka kuwa yo kanta da masifa yan maza suka shigar mata dan suma sunji haushi.

 Sabida haushi ma yana zuwa ya tashi ajin nasa yai gaba Faiza tai saurin tsai da shi tana faɗin takaddun baka amsa ba ya ce ok ba ni za ta hau duba jaka ya ce basshi gobe ki kaima ummamu ta ajiyemin in bana nan ta ce to tai gunsu Aimana da suke jiranta.

 Majalisar su ta da yai yajima baije gun ba yana zuwa suka hau masa mitar yai kuɗi ya manta dasu Mahmoud ya ce banda abinku ai ba mantawa ake da asali ba abubuwa ke yawa kuma ai kun rage zaman yawwa mutumina gane min hanya dai inji Fajar.

 Se wajen goma ya musu sallama Mahmud ma ya ce bari in gudu suka taso dan tafiya gida aiko suna barin gurin aka kafa fagen zaginsu wai dan sunga sun samu aiki shi ne suke wani shasshan ƙamshi nidai nace uh mutun.

Tun bawa ma'u motar nan kishiyoyin ummanta keta gulma dan sosai suke mamakin wani dalili ya sa Alhaji ya haƙura yabar motar bai mai da ba itadai umman ma'u daman can bamai san shiga hayaniya bace kullin tana sashenta sai lokaci lokaci ma suke ganinta.

 Tun jiya Farida ke takurawa Dad ɗinta kan ya shirya zasuje duba ma'unta ko kaɗan baya san ɓacin ran ɗiyar tasa suka shirya su huɗu harda yaya faruk da momun ta suka tafi.

 Ankoyi sa'a Abban ma'u na gida bakinsa yaƙi rufuwa daɗi ya cika shi wai yau shi ne Alhaji Nasir Dala ya zo har gidansa mutumin da seka shekara kana san ganinsa bazaka ga ko ƙurarsa ba.

Gwanda ma shi sabida yana da kuɗi ba lefi ya samu darajar ganin sakatarensa shi ma dakyar sai gashi a gidansa a ɓagas.

 Ma'u ta ji sauƙi tai mamakin ganin su farida ta ce yanzu aminiyar seda kika taso su Dad bacin nace miki gobe ma zanzo sch ta turo baki gami da hararar ta to saka su nan gaba innace muje guri suce no ƙarya nake akai dariya baki ɗaya.

 Ganin yadda mai gidan nasu yake ta girmama baƙin ma'u yaita basu mamaki dan sun san farida tana zuwa gidan saidai su basu damu da sanin ko ita ɗin wace ba dan sanin makaranta guda suke da ita ma'u ɗin.

Sai isha suka bar gidan Abban ma'u sai ziba godiya yake kai baka ce shi ne ba.

 Yau basu jima azaune ba Deen ya dubi agogo Fatiha ni zan wuce inada abinyi to shi ke nan sai Allah ya sake haɗa mu amin ya ce yabar gun baisan ya makara dan karya bawa ɗalibai ƙofar makara.

 Bai jima da barin gurin ba ta miƙe tai aji dan itama malamin su ya kusa zuwa batasan afara lecture tana waje dan malumman su na agric basu cika rufe class ba dan hana ɗalibin da ya makara shiga.

 Farida ce zaune tana duba littattafin ta lokaci lokaci tana duban hanya kar ya zo ya shiga ya hanata shiga duda taga alamar baya nan dan ba ta ga motarsa a Department ɗin tasu ba ko kaɗan ba ta cika san hayaniyar

 💞Don't forget to vote, comment and follow 👫💞

Ɗagowar da zatai idan ta kan motarsa da ke ƙoƙarin shigowa Department ɗin tasu ba shiri ta fito daga motar tai aji.

Ajin ya cika sosai wani takai ci ya kamata sai yanzu ta tuna ba ta tsari guri ba yanzu dole in koma baya ke nan ta faɗa aranta to ya zakiyi yau dai kam bake ba ganin D ɗinki sosai.

 Ji tai ance Farida ga guri muryar namiji ce jitai kamar tai halin nata ta share shi kamar karta kalli mai maganar tai baya ɗan juyawa tai dan ganin mai maganar Nasir ta gani yai tsuru yana kallon ta ayayin da duk ‘yan ajin suka zuba musu ido jira kawai suke ta dizga Nasir ɗin tai baya su sa dariya.

 Ga mamakin kowa zama tai harda ƙarin na gode Nasir ko me sunan baba zance yai dariyar jin daɗi dan ya san da ta dizgashi tai baya yau ba Department ɗin ba duk Faculty ɗin an samu abinyi ya ce ah duk wanda kika zaɓa ok shi ke nan nazaɓi Dad Name sake ɗin.

 Masu san gulma sai aka hau mamaki ashe ma har sunan sa ta sani .

 Anya kuwa zaizo inji musa ko kawai mu ware ne inji Nasir taɗan kalli agogonta gami da faɗin naganshi yana Faculty ɗinnan still time ɗinsa bai cika ba ok to mujira kawai Muktar yai saurin faɗe wai dan dai shi ma dole ace shiɗin abokin farida ne .

 Lokaci lokaci tana saka baki a hirar tasu hakan yaima Nasir daɗi ashe dai tanada mutunci tasan wanda ya mata alkairi ko kaɗan bai za ta zata iya riƙe sunansa da kaman ninta sa ba.

 Ko da aka tashi malan na fita ta fice Nasir yai saurin bin yanta saida ta kusa shiga mota ya tsaida ita ta tsaya ya ce Na gode taɗan kaɗa kai alamar godiyar me ya ce da kika zauna abin da sanda nace ki zauna ɗin ba bankuma yi tunanin ko zaki zauna ko a'a ba tai ɗan murmushi nice da godiya dan ko kaɗan abin da zaman baya yai murmushi to seda safe tai motarta.

 Tana jan motar abokansa suka ƙaraso anman wallahi Nasir kai munafiki ne ace kuna mutunci da Farida shi ne bamu taɓa sani ba yai dariya kunji ba baku taɓa sani bs inda da gaske ne muna mutuncin da ita ai da saikunfi kowa sani.

 Eh shi ya sa tasan sunanka yai murmushi kun mance a ajinmu take ne kun mance yawancin presentation ina cikin presenters kun mance ana faɗin suna anan ta san sunana ko kun taɓa ganin munyi magana da ita ne yauma tausaya mata nai naga kullin agaba take yau sai baya gabaki ɗaya sun yaddadashi.

 Kai amman kam tausayinka ya kyauta ko ba komai in kuna gaisawa muma za mu saba da sannu inji musa suka saka dariya.

 Masallaci ta parker motar sai dai ba ruwa ta tarar hakan ya sa tai central mosque wato C monque anan ƙofar shiga ta ajiye motar tasai pure water gami da shiga masallacin.

 shi ma Deen yana fitowa bai wani bi ta masallacin Faculty ba yai C monque nan tsallake ya ajiye motarsa bayan inda white bus ke ɗaukan ɗalibai ya tsallaka dan shiga masallaci.

 Kamar ance ta ɗaga idonta tana ƙoƙarin tada motarta ta gangeshi suna magana da wani aranta ta ce ko me ya zo yi oho can ta ce bazai wuce salla ba ido kawai ta tsura masa ta ma kasa tada motar tana kallo suka ƙara gaisawa da mutumin ya tsallaka.

 Ga mamakinta baya ta ga ya dawo zuwa inda ɗalibai ke zama dan jiran mota.

 Tayi zaton ko motarsa ta sami matsala ya zo hawa motar ɗalibai tana cikin tunani aranta taga yaje gaban wata dake can gefe kusa da yara masu saida goro ta ta rafka tagumi harda tsugunnawa kishi ne ya kamata to ita ɗin wace da har zai mata haka mene gamin sa da ita bacin tasan ita kaɗai ce tasa nai dariya nace eyye wato ke ɗaya ma.

 Shiko anasa ɓangaren har ya wuce idanunsa suka kai kan Fatiha data rafka uban tagumi da alama ta jima a gurin bama tasan motoci sunzo ba sunata cika.

 Ya jima a tsugunne agabanta ransa na raya masa abubuwa da dama kan abin da ke damunsa sai dai kwata kwata yaka sa gano ko mene.

 Ganin irin ɗalibansa da suka sanshi suna gai da shi ya sa ya ce ma ɗaya cikin masu goron ɗan taɓa min ita aɗan razane ta kalle shi ganin shi ne yasata ɗan murmushi lah yah Fajar kaine jin yaya bakin ta ya sa ɗalibai masu san gulma sikai zaton ko ƙanwar sa ce.

 Ina zuwa ya ce da ita motarsa ya ɗauko ya ce da ita shigo ko tsintar kanta tai da kasa ce masa a'a kawai ta shiga duda kuwa ba al'adar ta bace shiga motar wasu.

 Farida na kallon su gabaki ɗaya jikinta yai sanyi ta rasa wane irin jarabar so takewa mutumin nan hawaye kawai ke bin fuskarta.

 Ta rasa me ya sa zucuyarta ke sansa in dan kyansa ne za ta iya cewa Fatahu yafishi kyau in kuɗi ne daman tuni tasan fatahu ya kere shi in illimine tun kan ta shigo buk Fatahu yai PHD ɗinsa in ƙuruciya ce ma tasan Fatahu bai girmi D ba anman ta rasa me ya sa ko sau guda ita ba ta taɓa sansa ba sai wanda baima san tanai ba.

 Ada tanada ɗan hope ɗin ko zai so ta sai dai yau se take jin kamar bazai so ta ba ji take kamar tafi kowa rashin sa'a aduniya.

 Kuka ta saka zuciya ta why me ya sa zakimin haka me ya sa bakiyi shawara dani ba.

 Ta jima tana kukanta kamin ta fito ta wanke fuskarta ta ɗan shafa mai gami da shafa hoda da kwalli dan ko kaɗan batasan tadawa iyayan ta hankali dan tasan in ta je gida da alamun tayi kuka duk gidansu hankalin su bazai kwanta ba barima Abbanta zai shiga damuwa sosai.

 Motar ta taja tabar makarantar.

💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞

Rubutawa

Faɗima Fayau

Fajaruddeen

Post a Comment

0 Comments