Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
188. Ɗaurin ƙugiya ko ba wanda
ya korai,
An kuma fid da ƙa’ida kuma ta aurai,
Ba a hana shi ko kaɗan kuma ban sa
rai,
Harafi in da ƙugiyatai aka ɗaurai,
Dole a bar ta liƙe
nan ba a cirewa.
189. Za
ka ji ta fito cikin lafazi
sosai,
Haka nan za ka sa shi,
sai ya fita sosai,
Ba nashe shi, kana
ba a kuma yassai,
Furucin lanƙwasar
tana nan dai sosai,
Kuma
a rubuce ƙugiyar ba ta gushewa.
190. Ɗaurin in ya kama ‘ƙ’ kai dai ƙyale,
Ba a cire shi dole sai dai a yi lele,
Kalmomin da sun ka zo nan ga misale,
Ƙaton nan ƙafarsa
duk ta ƙaƙƙalle,
Kuma ya yunƙura shina
tattakawa.
191. To dai ga su yadda za ka rubutawa
Raggo in an kirai yana ɓoɓɓoyewa,
Ƙaƙƙarfan ƙanen ga nau bai ɓoyewa,
Ɓaɓatun gyaɗa wuta ƙoƙƙonewa,
Ga maciya a zaune sai ɓaɓɓarewa.
192. Riga in ta tsufa sai
ta ɓaɓɓarke,
Damma ga su ɗaure yanzu a ɗaɗɗauke,
Na ga buhuhuwan hatsi
an ɗiɗɗinke,
Wasu ɗaɗɗaure bakunan nasu a
tsuke,
Ga wata tashe yanzu sai ɗuɗɗurawa.
193. In
ka lura ƙugiya ba ta sauya ba,
An jera su ka ga
dai ba a canza ba,
Ga misalin da yat
taho in ka duba,
Kowace ƙugiya a nan ba a karye ba,
Kuma
mai ƙugiya kawai aka ɗaurewa.
194. Duk sautin da za ya ɗaure shi kalar shi,
Ba a rubuta kowane dole a sa shi,
Shi mai ƙugiya idan an ɗaure shi,
Duk harafin da kas
sani bai ɓoye shi,
Sai mai ƙugiya
kaɗai za ya biyowa.
195. Je
ka yi binciken abin ga ka tantance,
Shiga littattafai ka nemo su nazarce,
Kai nazari ka duba komi ka karance,
In ka gan shi sai ka zana a rubuce
Masana sun aminta mu ba mu musawa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.