Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Allah kasa yanda na fara lafiya in kare shi lafiya. Wannan labarin ya faru da gaske dan kusan Book dina da nake yi true life ne sai dai in yi masa kwaskwarima dan abun ya fi ba da citta.
Ku biyo ni ku sha labari.
Ku daure ku yi comment dan in ji ra'ayoyin
ku a kan Littafin nan......
*JARUMAI
WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta
masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa
harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
Marubuciyar
* Amince Da Ni
* KAI KA JA WA KANKA
Yanzu kuma
gani ɗauke da
ƘANWATA
Paid Book ne
Vip 300
Special 500
Acct No. 3115484026, First Bank, ko kuma Kati MTN (Ba na son VTU)
Idan kin biya
ta bank kina iya turo shaidar biyar ki ta wannan 09069080725
🌟🌟 ƘANWATA Na Ikilima Adam [Kashi na 6]🌟🌟
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah8️⃣6️⃣
Ta ce hoto
kuma ban gane ba '' Marwan din ya dauke mu hoto nida kai ''
Eh shi ne ya ɗauke mu'' matso kiga hoton'
gallery Din wayar sa ya shiga ya maida hankalin sa gun nemar hoton...
Murmushi ya yi
ya ce uhmm zo ki ga' 'matso da ita ya yi kusa da shi tare da nuna mata hoton...
Cikin gigita
take kallon hoto cike da zallan mamaki ta ce Marwan din ne ya ɗauki hoton tana kallon
hoton bakin ta abude...
Eh Marwan ya ɗauka ya turawa Salma' itakuma
Salma ta nunawa Adamu ranar daurin auren naku shikuma ya janye...
Wataran Salma ta
kira Marwan saina na dauki wayar agaban sa' 'na Daga inajin muryan mace nace
masa kenan kafara bin mata....
Wannan dalilin
ya sa nabi diddigin sa nadau wayar tasa naga hoton daya tura mata saida nashiga
shock cikin tsananin tashin hankali nasan wannan hoton' 'yana da Burin ya yada
shi duniya tagani kinga za a halin mu daya da ubana...
Goge duk wasu
hotuna nayi a wayar tasa dan kada ya yi zargin Ko angano shi ne...
Innaliahi
Rahama ta shiga maimaitawa ta ce Salma nashiga uku ƙanwata' cikin kuka ta ce
Amjad ban san menayi wa Salma ba take tsanata ba '' na dauka kuruciya ce 'Wallahi
innaga yaya da kanwa suna kusanci' 'sossai kuma suna kaunar junan su 'burgeni
suke.....
Hannayen sa ya
sa ya fara goge mata hawayen nata ya ce Hubby kiyi hakuri fa..
Azuciyar sa
sai fadi yake dan ma bakisan abun da Salma take shirin aikatawa bane''' uhmm
InshAllah zan kareki mata ta cikin maganar zuci yake Rahamaa ta zuba masa idanu
ta ce yadai Amjad tunanin me kake..
Murmushi ya
sakar mata hade da lakacar hancin ta '' uhmm Hubby kin san in inajin dumin
jikin ki..
Kashe min jiki
kike...
Zazzare idanu
Rahama tasoma tana neman hanyar guduwa cikin kukan shagwaba ta ce Amjad
dîna....
Ni ɗai ka kyaleni ba abun da
zan iya maka...
Tashi ta yi tana
kokarin zillewa hade da masa gwalo '' sossai ya ɗara
ya ce uhmm Allah yakaimu ai daren yau namu ne..
Tabe baki ta
yi ta ce uhmm ka ga bankira Asiya ba tun da ta tafi ba...
Kuma yakamata
ki kirata ita da mamar ki '' anty kike kiran ta...
Eh Anty nake
kiran ta my Amjad ''...
Kusan Azahar
Samad yana makale da Rahama a dakin Da ƙyar yabar ta '' ta shiga kitchen da kan
ta dan daura musu girki....
Isowar Karima
ne ya sa Samad barin Sashin yafita dan gudanar da wasu Ayyukan sa...
Yana Fita ya
tura wa Yusuf Sani Yaro sako a kan whsap dinsa...
Ya tura masa
da :
Salam Alhaji
yusuf dafatan kana Lafiya..
Kwana biyu ba
ka nemana ya kake yame dakin naka Sumayya...
Cikin Sa'a
kuwa yau yana online dan sai ya yi sati behau online ba '' amma datar sa tana
kunne da zakayi masa '' whsap call ze shiga amma baza a Daga ba.....
Ganin Sakon
Yarima Samad ya sa shi kai tsaye shiga cikin sakon ya san duk yanda akayi Ko
zumunci za su yi Ko kuma aiki ne yazo dashi...
Hakan ya sa ya
yi maka reply tare da bashi damar su sauka Daga kan whsap '' yakira direct..
Babu Musu
Samad ya sauka Daga kan whsap dîn..
Kiran sa ya yi
direct Daga cen ɓangaren
yana wayar amma kuma yana magana da wasu alamu cikin tarin Ayyuka yake '' kuma
manyan yan majalisu ne kusa dashi....
Cikin da fada
fada yake musu magana ya ce dan Allah ku fita '' waje ku dawo nan da Sati daya
'' Samad dake sauraren yanda yake zuba ruwan masifa acen din ya ce ka ga
namijin zaki '' wanda beson takura.....
Muryan Yusuf
yadawo da shi duniyar tunanin daya shiga..
Yusuf ya ce
dan uwa Dan Sarki. Jikan Sarki wai kana nufin har yanzu bakaga Sarkin Adalai
ba...
Samad ya ce
ban ganshi ba nasan kaine kadai za ka iya binciko mun shi..
Amma kafun nan
wannan baiwar nan wacce Al'amarin ya faru da ita '' ita nake nema ance ta buya a
garin kano.....
Kasaitaccen
Murmushi Yusuf ya yi ya ce uhmm '' lallai ta yi karamar hauka tarasa inda zata
buya sai kano..
Amerika ne
kadai zata je inkyale ta..
Tura mun hoton
ta '' kaban awa 48 duk inda take zakaji inma kanon Ko wajen kano...
Sossai Samad
yaji dadin bayanan Yusuf hakan ya sa ya rinƙa masa adu'oi a karshe ya ce shi ne baka
zo biki na ba..
Yusuf ya ce
A'h Ah kabari ta haihu mana InshAllah da Mata ta zan zo.
Sossai Samad
ya ɗara ya ce to Allah
yabata cikin da Ameen suka Amsa tare........
''
Rahama tsaf ta
shirya cikin shigar ta ta Alfarma tare da sanya Alkyabba da Karima ta daura
mata '' Kallon Karima ta yi ta ce duba kigani shigar nan tamin kyau kuwa...
Karima ta ce
sossai ma kinyi kyau shugaba ta' '' sai m'a shugana ya ganki ze kara ruɗewa '' 'murmushi ta yi saida
kuncin ta ya lotsa ta ce anjima da dadare zakiban labarin da kika sani wanda ban
saniba Karima cike da ladabi ta ce ya shugaba ta' ɗuk yanda kikace haka za ayi...
Muje ki rakani
sashin Fulani yau cen zan fara lekawa cewar Rahama....
Babu Musu suka
baro sashin nasu khadija kadai aka bari dan ba ta nemi izinin Samad ba' 'babu
halin fita harsai yadawo dan doka ya sa mata......
Koda suka fito
Farfajiyar Masarautar bayi suna ta shinmfidewa kasa dan gaishe da Rahama..
Cike da ladabi
suka fara fadin barkda da fitowa Gimbiya Rahama..
Bakin ta dauke
da murmushi take Daga musu hannu ba tare da ta yi magana ba..
Tafiya take
tamkar hawainiya duk takun ta daya sai Bayi sun Dago kai suna kallon ta ''
cikin zallan mamaki dan ba a taba yin Gimbiya wacce ta iya tafiyar Matar
sarakai Ko yarima ba irin ta...
Daidai Mashigar
sashin Fulani ta hadu da jakadiya tana horar da bayi da ba sa Jin magana...
Ganin Rahama
ya sa ta fadada murmushin ta '' tafara mata kirari......
Ita Ko Rahama
murmushi ta yi tare da da mata gaisuwar hannu ba tare da ta tsaya ba....
Kai tsaye suka
wuce dakin Fulani ita da Karima....
Bakin su dauke
da Sallama
Bayi masu mata
hidima suka gani..
Cike da
girmamawa suke gaida Rahama..
Cikin sanyin
murya Rahama ta kalli bayin dake dakin ta ce uhmm ina Mama Fulani take ne..
Baiwar dake
goge goge ta ce ta shiga wanka..
Karima kallon
Rahama ta yi ta ce shugaba ta mu je dakin nata mu jira ta Ko..
Rahama
murmushi ta yi ta ce to mu je kai tsaye Dakin Fulani suka nufa cikin azzama..
Suna shiga
dakin ganin ba ta fito ba ya sa suka fara dube dube a dakin...
Idanu Rahama
ta yi ma Karima ganin haka ya sa Karima sanda sanda take wajen kofar bandakin
da Fulani ke wanka '' Daga wajen tasawa kofar sakata ta tabbatar yarufe...
Murmushi
Rahama ta yi cike da izza tafara nuna wa Karima inda zata hau saman sif din..
Karima cikin
azzama tahau tafara dube dube tana sauko da kayan dake kai...
Saida tagama
sauko da dukan kayan har tana Zufa cikin maganar kurmanci ta yi mata alamu da
hannu ba ta ga komai ba...
..
Rahama alamu
ta yi mata data kara bincikawa hakan ya sa tabada azzama wajen bincike '' cikin
sa'a kuwa sai gashi taga layoyi guda uku ajere....
Jin karar buga
kofar bandakin ya tabbatar musu fulani ta gama wanka so take ta fito ta ji
kofar arufe gam..
Zazzare idanu suka
yi Rahamaa ta yi mata alamu data miko mata layoyin dukan su '' sunkai talatin
'' tana mika mata cikin jakar ta '' tasaka su..
Kayayyakin da
suka sauke kasa tafara mikawa Karima '' tana maida su inda suka dauko su..
Jin Fulani ta
tsananta da buga kofar bandakin ya sa..
Karima tasauko
a hankali...
Gadon da ta
taka tahau sama nan da nan tahau gyara shi tsaf yanda ka san basuyi komai
ba....
Komawa kujerar
dakin Rahama ta yi ta zauna..
Hakan ya sa
Karima taje a hankali tabude kofar...
Da karfin
tsiya Fulani da bankado kofar tana ta huci sama sama...
Rahama cikin
azzama takaraso wajen Fulani ta ce Mama yanzu muka shigo dakin naki '' sai mu
ka ga kina ta buga kofar '..
Cikin tsananin
bacin Rai ta ce kulle ni akayi ta waje...
Rahama ta ce
anya ba Jan blok bane ya shiga ba..
Ke Karima je
ki duba kigani..
Karima cikin
azzama taduba cike da dalabi ta ce ya shugaba ta' 'maganar ki gaskiya ce Jan
blok kofar tashiga
Ajiyar zuciya
Fulani tasauke ta ce haba ni nayi mamaki ashe Jan blok ya shiga Abban Marwan
ne' ɗaya shiga dazun
ya sa shi a kan Jan blok
Maida kallon
ta ta yi a kan Rahama ganin ta yi wani mugun haske fatar ta takara yin kyau
sossai..
Tabe baki ta
yi cike da Fargaba ta ce Amarya mu yau kece har dakina lallai yau kin dauke ni
amatsayin uwa...
Murmushi
Rahama ta yi ta ce mama Fulani '' yarima ya ce indai ina son insamu Albarka
dole inbiku...
Darawa ta yi acikin
zuciyar ta'tana bin Karima da kallon banza..
Ganin haka
Karima tafara sanda kanta akasa...
Uhmm damar
nace Karima tarakoni in gaishe ki akace kina daki nace bara in zo ban san wanka
kike ba zan tafi cikin gida....
Fulani dake
kallon Rahama cikin tsoron kada abun da take tunani ya tabbata inhar dagaske
Rahama ciki ne da ita Asirin nasu ze Tonu..
Mudin Sarki
yaji labari zance yakare '' zefara kokarin maida Mulkin hannun Samad...
Sossai hankalin
ta ya tashi cikin dauriya ta ce yata har zaku tafi gashi baku ci abinci ba...
Rahama ta ce
A'a nagode na koshi Daga haka suka bar dakin ita da Karima...
Kai tsaye
dakin Karima suka je tare da Rahma..
Layoyin suka
warware akasa....
Cike da mamaki
ta kirga su taga wai har guda talatin ne...
Kowani laya
saida suka warware su daya bayan daya...
Wasu layun
harda Allurai acikin su...
Wani layan
takarda ce mai dauke da sunan Salihu farraku shida Turaki...
Sossai Rahama
ta Girgiza ganin Yarima Samad '' kada ya haihu...
Batagama
mamaki ba '' taga wanda aka rubuta..
Babu Salihu
babu gidan masarauta har abada...
Sake da baki
suke kallon juna Rahama da Karima.......
Rahama da
mamaki take kallon Karima tare da mikewa tsaye zumbur kamar wata soja...
Ta ce Karima
kin san gidan Maman Maryam..
Karima ta ce
kwarai nasani shugaba na yana aikata awannan gidan..
Miko min
wayata Daga cikin jakata...
Cikin hanzari
ta mika mata...
Dannawa Samad
kira ta yi Shiko yana tuki zeje Filin airport din Samad air plan....
Ganin kiran
Rahama ya sa babu ba ta lokaci ya ɗaga...
Cikin begen
abun kaunar sa ya ce Amarya bakya laifi koda kin kashe Fulani da Marwan
Sossai ta dara
ta ce ban kashe bane 'shi ya sa...
Cikin cool
voice din ta.
Ta ce Amjad.
Naam Rahama ta
yakarashe zancen yana kokarin tusa hancin motar a airport din...
Inajinki
fadi...
Uhmm dan Allah
kamun izini zanje gidan Maman Maryam nida Karima ba zan dade ba...
Ziyara ce..
Nazarin
kalaman ta yake yanason ya ce A'a ganin wanne karo na farko data tambyeshi zuwa
unguwa ya sa shi Fadin Allah yakai ku lafiya...
Zanwa drever
magana yakai ku ya kuma jira Yadawo dake...
Sossai Rahama
ta ji dadin bayanan sa hakan ya sa ta rinƙa masa adua yana fadin Ameen ameen
hubby...
Babu ba ta lokaci
suka shirya zuwa gidan Maman Marwan..
Koda suka isa
farfajiyar gidan sun iske drever su kadai yake jira su tafi...
Ganin sun fito
ne harda khadija..
Babu ba ta lokaci
ya bude musu kofa...
Suna shiga
motar '' kai tsaye ya ja motar zuwa kan titi..
Rahama cike da
murna take kallon garin '' ba ta taba shiga cikin garin kwatano ba...
Sossai yanayi na
tsare tsaren nasu yaburgeta.....
Gani ta yi har
sun iso Gidan wanda tafiyar basu fi minti shabiyar ba...
Koda Drever ya
paka motar tasa.
Basu ba ta lokaci
ba wajen fitowa ba..
Maman Maryam
da Abban Maryam da maryam suna zaune afalo suna tattauna da alamu a kan Samad
ake magana...
.
Sallamar
Khadija ya sa suka maida kallo a kan ta....
Ganin Rahama
da Karima a bayan khadija '' ya sa suka Mike dukan su...
Maryam
cikin.........
Muje zuwa..
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah8️⃣7️⃣
Maryam cikin
mamaki ta ce wannan kamar Matar Yaya Samad...
Murmushi
khadija ta yi ta ce aikuwa ita ce ashe kin gane ta..
Maman Maryam
cikin Aro jarumta taje ta rungume Rahama cike da bakin cikin dake cin ta...
Ta ce yata
idon ki kenan lale lale da Rahamatullah..
Kallon Maryam
ta yi data zama kamar gunki a tsaye ta ce ke Maryam kallon Matar yayar naki
kikeyi ne..
Murmushi
Khadija ta yi ta ce mommy naga Alama..
Samun wuri suka
yi suka. Zauna Karima kasa ta zauna.
Cike da ladabi
Rahama ta gaishe DA MOMMY DA Maryam '' da Abban marwan dayanzu yake zama kan
kujerar sa...
Mommy ihun
kiran yar aikin ta tayi.
Nan da nan yar
aikin tazo tana sanye cikin riga da
Wando
matsassu.
Abban Maryam
yana kallon yar aikin ta kasa idanun sa ya sauka a kan nonuwan da suka ciko
rigar...sai hadiye yawu yake.....
Duk abun da
yake Rahama tana lure dashi...
Abun sha yar
aikin ta zuba musu tare da jera musu agaban su..
Mommy ta ce ku
sha lemu laifin Abdul Samad ne. '' inzaku zo ya sanar mana ayi maku girki special..
Amma yanzu ba
ta baci ba...
Rahama cikin
cool voice din ta ta ce mommy '' Mungode ahanya muke nace muzo mu gaishe ki..
Naga lokacin
lasa'ar ta gabato ina son naje 'nayi Alwala..
Mommy ta ce
uhmm kije dakin Maryam saikiyi a bandakin ta..
Maryam tabe
baki ta yi ta ce la mommy ai pampo na ya tsaya tun jiya sai dai khadija takaita
dakin naki..
Maman Maryam
ba haka taso ba' ɗan
kada su gane ya sa ta fadin uhmm kuje yata akaiki dakina...
Babu ba ta lokaci
suka Shiga dakin Maman Maryam' ɗuk
yanda Rahama taso khadija tabar dakin abun ya garara saida taje ta yi Alwala ta
fito tana kallon khadija dake latsa wayar Rahama..
Ta ce sista
jekiyi Alwala Ko muyi Sallah ina jiran ki....
Babu musu
khadija ta tashi ta shiga bandakin tana ganin khadija ta shiga taje ta dannawa
kofar shigowa key '' cikin Rawar jiki tahau saman sif din jikin ta 'na rawa
tana tsoron kada khadija ta ritsata cikin ikon Allah ba ta sha wahala ba..
Taga layun har
uku...
Cikin Rawar
jiki ta sauko tare da gyara wajen data taka' '.
Key da ta
murzawa kofar ta cire.
Sum Sum ta
dawo kan sallaya ta zauna kamar yanda khadija tabar ta..
Ita Ko khadija
har da bahaya ta yi ya sa ta dade a bandaki..
Tana fitowa
kai tsaye Rahama tajasu Sallah...
Suna cikin yin
Sallah' maman Maryam ta shigo ita da Maryam din..
Ganin Sallah
suke ya sa suka kalli juna suna tabe baki ''
Maman Maryam ta
ce in kun idar ina jiran ku...
Tare da komawa
Falon ita da yar ta.....
Rahama suna
idarwa Ko tsayawa azkar basuyi ba suka tashi daman a ujajjan tazo dan dole...
Fitowar su
Falon ya sa Karima tashi Daga zaunen tana ma Rahama kallon andace' '
Rahama gira ta
Daga mata Alamun yes..
Agogon wayar
ta' ta kallah taga lokaci ya ja gashi tanason takoma gida ta daurawa Amjad din
ta girki...
Cikin ba da uzuri
take kallon Mommy da Maryam dake hararan ta'' ta ce zamu tafi' ɗaman munzo mu. Gaishe ki
ne..
Kafun muzo
miki wuni...
Maman Maryam ta
ce haba yata ga girki nan andaura muku yakusa dafuwa..
Rahama
kasaitaccen murmushi ta yi ta ce Ayya mommy na''' zamu dawo InshAllah..
Mommy cikin
Jin haushin jiran girkin da batayi ba.
Ta ce uhmm to
nagode da ziyara yata.
Kallon khadija
ta yi da suke magana ita da Maryam.
Ta ce khadija
tashi kuje '' anty taki ta ce bazama inaga Samad zedawo yasha girki ne.....
Murmushi
Rahama ta yi tare da yin kasa da kanta dan kunya.....
Har bakin mota
suka raka su banda Maryam da bakin ciki yahanata fitowa tana ayyana irin
hukunci da zatayi m'a Rahama..
Babu ba ta lokaci
drever ya ja su Rahamaa a mota tare da nufar hanyar gidan nasu....
Ita Ko Maman
Maryam '' bakin ciki ya ishe ta kasa komawa cikin gidan take tana ayyanawa
aranta anya wannan yarinyar ba ciki ne da ita ba...
Kasa daurewa
ta yi hakan ya sa ta yi maza tadannawa bokan jeji waya..
Bugu uku ya ɗaga Daga can ɓangaren Ya ce Farida nasan
zaki kirani a daidai wannan lokacin yana tsoron gayamata '' Rahamaa ta kwashe
layoyin taki biyan sa '' sauran kudaden sa..
Kuma yanajin
shakkar Rahama ta warware layoyin ta wargaza musu shirin nasu..
Matar dan naki
tawuce Ko yau ziyara ta musamman ta kawo miki mai cike da dumbun tarihi..
Maman Maryam ta
ce ban gane me cike da dunbun tarihi ba......
Dariya ya
kekyashe da shi sossai sanna ya ce zaki gane ne Farida ba abakina amma barin
infada miki abun da kike son sani....
Matar Samad
bin Salihu tana dauke da cikin sa....
Cikin gigita
Maman Maryam ta tsala ihu ta ce garin ya haka tafaru kaida kace za ka hana ta
samun ciki...
Bokan jeji
hade rai ya yi kamar tana ganin shi '' ya ce ke banda shasha ce '' ke kinyi
sake '' bare ni da ba haduwa muke da ita ba '' saide intura dan sako....
Yarinyar ce
hatsabbiya ce ta karshe duk inda muka bi saita tare mana hanya hatta Samad ''
inmuka je masa yanda kika san a jikin ta '' haka take zaburar damu '' '..
Nan da nan
Zufa ya ketowa Maman Maryam cikin damuwa ta ce yanzu meye abun yi..
Abun yi shi ne
kawai ku ɗau hakuri ta
haife abun da ke cikin nata kinga sai ku shayar dasu guba su mutu..
Maman Maryam ta
ce kana nufin cikin yan biyu gareta ne....
Boka
tuntsirewa da dariya ya yi sanna ya ce '' wannan dai mu jira mugani dan ba zan
fadi abun da zai sa wannan bakar Mayyar Matar Samad ba tazo ta hanani barci
ba...
Daga haka suka
yi sallama.
Tana jinjina
Al'amarin nan kiran Fulani ta yi cikin sa'a ta Daga nan take ba ta labari...
Fulani cikin
salati ta ce haba biri ya yi kama da mutum shi ya sa yarinyar nan takara haske
sossai..... Ga kiba..
Shege Samad da
kike gani ya iya cike mace cikin kalilan lokaci jarababbe shida uban nasa...
Maman Maryam ta
ce ni dai kinji ya ce sai yaran sunzo duniya za a kashe su..
Amma kisan
yanda zakiyi kada mai martaba ya san tanada ciki..
Fulani ta ce
uhmm inaga Samad din ma besan da cikin ba ita ma matar batasani ba.....
Cigaba da
tattauna suke a kan yanda zasuyi kawo karshen Rahama agidan...
Adaren ranar
Rahama tagama warware dukan layoyin tasa su a wuta suna konewa.....
Zuciyar Mai
martaba da Abban Marwan '' da Baba Salihu da Marwan dake tuki yadau bugawa gab
gab gab da karfi..
Baba Salihu
Samad gado yake yana barci hakan yaji gadon na juyawa da shi cikin gigita ya
farka yana Salati..
Shima Mai
Martaba kusan da Salati ya tashi ya zauna yana Jin wani irin yanayi tattare
dashi...
Shiko Abban
Marwan zaune yake yana cin Abinci '' kansa yarike da yake sara masa...
Marwan dake
tuki kadan yarage beyi hatsari ba '' da taimakon wani soja ne.
Allah yakare
shi koda sojan ya fito zeyi fada ganin Marwan jikin Sarki ne ya sa shi fadin
Prince Marwan kayi hakuri ban san kai bane..
Marwan da Sam
baya cikin hankalin sa ya ce ataimaka akaini gida...
Sojan ya ce
subuhannalah Prince bakada lafiya ne....
Shiru ne
yaratsa hakan ya sa babu ba ta lokaci sojan ya ja motar tare da da maida Marwan
kujerar me baya..
Kai tsaye gida
ya nufa dasu babu ba ta lokaci...
Sarki Turaki
bakin sa na rawa yake kallon Mama karama ya ce hajiya Nasiba ina ɗana Salihu yake Saboda ance
Yayiwa baiwa fyade shi ne yabar gidan nan....
Mama karama da
mamaki take kallon sa '' ta ce yau kaine kake tambayar inda dan naka ya shiga
bayan da bakin ka kace yana iya barin gidan dan be iya hada idanu da Talakawan
sa...
Sarki Turaki
zazzare idanu ya yi ya ce haba Nasiba ya zaki ce haka yaushe na fadi haka......
Kuma ya'akayi
mulkin yadawo hannuna '' mikewa tsaye ya yi hakan ya sa Mama karama ta yi maza
tarike hannun sa ta ce ina za ka je ne adaren nan...
Zanje wajen
baiwa Saratu yabata amsa ataikaice....
Cike da tsoron
yanayin sa ta ce anya ba iskokai ke damun ka ba...
Saratu shekara
da shekaru ba ta gidan nan sai a yau za ka nemeta wai ma kayi mata me.....
Cikin zazzare
idanu ya ce kina son kice min Saratu ba ta gidan nan bayan nace ina son ayi
bincike ya'akayi tabar gidan nan cike da fada yake magana sossai kamar ita ce
ta yi laifin....
Mama Karama ta
ce subuhannalah Sarki me ran Karfe ni dai Kayi hakuri zuwa safiya InshAllah
zanmaka bayanin komai '' ɗakyar
ta lallaba shi yakwanta yana kukan zuci' 'babu abun da yake son gani sai mafi
tsoyuwar dan nasa..
Abban Marwan
ture kwanun abincin dake gaban sa ya yi yafadi wargas akasa da yake tangaran ne
nan da nan ya farfashewa daddaya akasa...
Fulani cike da
mamakin sauyin yanayin sa ta yi ta ce kai ta ce lafiya kuwa Sani mêke ɗamun ka...
Wani kallo
yake bin ta da shi masu wuyan fassara ya ce Salamatu me kike yi agidan nan ''
daman ke na aura...
Rau Rau da
idanu Fulani ke kallon sa ta ce kam buhu yauga rainin wayo ya za ka ce me nake
yi agidan nan..
Bayan ina
matar ka '' har da haihuwa tsakanin mu...
Abban Marwan ya
ce nasan inada da Marwan '' kina nufin kece uwar tasa...
Fulani cikin
gigita take kallon mijin nata '' ta ce Nice uwar sa kaine uban sa ya da wannan
tambayar...
A'a Salamatu
wallahi ban san na aureki ba''ni rayuwar dani dake kamar a mafarki yanzu abun
yake dawo mun....
. Kinko San
irin tsanar danayi miki kuwa....
Kokarin Fita
yake ta kamo hannun sa' 'cikin kukan dayazo mata' ta ce ina za ka je ne...
.
Zanje wajen
Yayana mana inmasa bayanin yanda akayi kika zama mata ta....
Shan Gaban sa
ta yi cikin zafin nama bakin ta na rawa ta ce yaya Salihu baya gidan nan
shekara da shekaru kai a yau ka san benan...
Cikin gigita
yake kallon ta da Idanun sa da suka kawo ruwa nan da nan ya ce ban gane yaya
Salihu baya nan ba....
Hankade ta ya
yi ta fadi kasa tare da bude kofar.....
Yana fitowa
cikin zafin nama zashi sashin mai martaba ya yi daidai da anshigo da Marwan a
ujajan kamar matacce...
Cikin tsananin
tashin hankali ya nufi inda sojan yake tare da bâyi da suka taimaka masa wajen
ciccibar Marwan....
Bakin Sa na
rawa ya ce meya Samu ɗana
ne...
Sojan ya shiga
bashi labarin abun da ya faru..
Sossai Abban
Marwan yarufe tare da tallafa Marwan din suka yi sashin Mamy dashi...
Mamy zaune
take ita da Ahmad suna hira '' turo kofar da akayi shi ne ya sa hankalin ta
yadawo a kan kofar.
Ganin Marwan a
ujajan ake kokarin shigo dasu '' cike da fargaba suka taso ita da Ahmad...
Bakin ta na
rawa take kallon Sani Abban Marwan ta ce lafiya meya samun dan namu...
Abban Marwan
cikin gigita yake ba ta labarin sojan daya kawo shi.
Babu ba ta lokaci
suka daura shi a kan kujerar falon ''..
Ganin haka
Mamy ta ce kai Ahmad maza kaje ka kira Samad shida Matar sa..
Abban Marwan
da rabon shi daya shigo Sashin mamy tun Salihu yana gidan '' cikin dauriya ya
ce Mamy dan Allah kiramun yaya Salihu mana..
Naga kamar Samad
ba zai fito dawuri ba..
Rau Rau da
idanu Mamy take kallon Abban Marwan ta maimaita Salihu cike da Mamaki ta ce
uhmm kaiko Sani yaushe rabon duniya da ayiriri yayan naka da kuka kore shi...
Murya Samad ta
ji Daga Sama yana karasowa falon ya ce A'a ba shi ne yakore shi ba...
Asali ma besan
an yi ba...
Rahama cikin
yarda da zancen mijin nata..
Ta ce Mamy
kwarai kuwa Abban Marwan besan da komai ba..
Barin zancen suka
yi tare da dukufa a kan Marwan.
Babu ba ta lokaci
Rahama ta soma yi masa ruƙya inda Yasoma gurnani Daga karshe ya rinƙa
maida numfashi ganin haka Rahama ta ce Alhmdulilah ze iya farkawa normal
InshAllah....
Komawa ta yi tazauna
tana adu'oi carbi na hannun ta...
Mamaki da
mamaki take kallon yanda Rahama ta saita Marwan har ya bude Idanun sa..
Abban marwan ya
ce Habiba yanzu kuna nufin yaya na be gidan nan wallahi da sake wai anbawa me
kaza kai.
Samad kallon
sa yake ya ce duk wannan abun daya faru Matar ka Fulani ce sila...
Abban Marwan ya
ce wallahi ban san yanda akayi na auri Fulani ba...
Mamy cike da
tausayawa ta ce Rabo ne ya kuka tsakanin ku bakada zabi dole sai hakan ta
faru....
Marwan firgit
ya tashi Daga kwance yazauna yana kallon yan cikin dakin wani sabuwar soyayyar
Samad yaji yana ratsashi ta Ko ina sassa na jikin sa...
Aguje ya tashi
ya je ya rungume Samad yana tuna baya '' lokacin daya ta aikata masa laifuka ''
cike da rashin sanin meyasa ya muzgunawa yayan nashi ya ce..
Yaya Samad dan
Allah kayafemun laifukan ɗana
aikata maka abaya..
Shiii Yarima
ya yi da yatsar abaki ya ce kada kace komai kanina bakayi mun laifin komai ba
'' Ada na daukeka mara gaskiya yanzu kuma na dauke ka me gaskiya.
Kara Rungumar
Marwan din ya yi ya ce Marwan nayi mamaki yanda Mamy ta zama uwar dakin ka
lokaci daya ka canza '' nayi mamaki yanda nake kula da kai komai naka lokaci
daya kazama mugu ashe bayin kanka bane..
Sharrin Fulani
ne.....
Marwan cikin
gigita yake kallon Abban sa ya ce Abba ka cuce ni ya akayi ka zaba min uwa kamar
Fulani...
Abban nasa
rintse Idanun sa ya yi ya ce haba Marwan nikaina ban san yanda akayi na aure ta
'' da ba mu kama nida kai tabbas zancen kai ba ɗana
bane...
Yarima Ahmad
dake kallon abun da ke faruwa tabe baki ya yi ya ce nifa bantajin kaunar Fulani
ba Mamy...
Samad kallon
Abban Marwan ya yi ya fara bashi labarin gwagwarmayan da Rahama tasha..
Dakuma zancen
layoyin data kona harda garin layoyin dasuka yi toka ya bude nan ya nuna musu..
Gabadaya wajen
aka dauki Salati..
Mamy cikin
tashin hankali ta ce meya kawo Anty Farida cikin wannan lamarin oh Allah yaya
ta mekike so ne '' meye ban miki ba'''
Kin kasa
ganewa ba laifina bane dan Salihu ya zabeni amatsayin matar daze aura ba
laifina bane dan Samad be aure Maryam ba...
Kuka take
sossai har Idanun ta sun kada ta ce wannan labarin saina gayawa mahaifin mu..
Kuma zan
sanarwa Yayyena na da autar mu '' su sani Farida gurbatacciyar jini ce acikin
mu...
Kuka take
sossai hakan ya sa Rahama zuwa soma rarrashin ta cikin kalamai masu taushi ta
ce Mamy karki fushi kibar ta ta girbi abun da ta shuka...
Mamy ta ce
wallahi tallahi tun da nake da Farida ban taɓa
yin abun da ze cutar da ita ba..
Meyesa ita ba
ta kaunar cigaba na...ɗana
zuri'a ta...
Gabadaya dakin
shiru suka yi Ko wanne da abun da yake sakawa aransa....
Abban Marwan
cikin Rawar murya ya ce Rahamaa ke yar halak ce samun ki Rahma ne a gare mu..
Ahmad ya ce
kwarai kuwa ita ce fitilar gidan nan..
Yarima Samad ya
ce ita ce hasken gidan nan..
Mamy ta ce ita
ce babban bangon gidan nan..
Gabadaya suka
hada baki wajen Fadi.
Rahama Ba gaba
da gaba ba kota baya sai an shirya...
Shiru ta yi tana
sauraren su cikin zakin muryan ta ta ce ku Ahlina na ne ku ne Farincikina ''
rayuwa ta tadawo hannun ku tabar hannun iyayena.
Dole ne inkare
martaba da mutunci ku yan uwa na...
Dan Allah bana
son godiya komai nayi ya zame mun dole ne..
Abban Marwan ya
ce A'a Rahama mata nawa ne basayin jarumtar ki '' wasu watsa gida suke yi..
Kinada Imani
ne...
Shi ya sa kika
dage a kan tono gaskiya..
Azabure Abban
Marwan ya Mike tsaye tare da kama hannun Marwan da zuciyar sa ke tafasa..
Kai tsaye
cikin hanzari suka bar dakin...
Ganin haka
Samad da Ahmad suka take musu baya sun San wajen Fulani suka nufa..
Samad Sai gudu
yake da sassarfa yana fadin Marwan ku tsaya dan Allah..
Amma ina ba sa
Jin abun da yake fade..
Kamar Daga
SAMA fulani taga an bankado kofa.
Cikin.........
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah
Rahama ta ce
yi hakuri Mamy komai8️⃣8️⃣
Cikin Gigita
take kallon Abban Marwan daya shako wuyar rigar ta '' saida Idanun ta suka
kakkafe sama..
Marwan gefe ya
tsaya yana kallon su'' ya kasa magana soyake ya kwace ta tsakanin Uwa da da sai
Allah hakanan yaji Beji dadin shakar ba...
Isowar Su
Yarima da Ahmad ne ya sa cikin zafin nama suka fara kokawa da shi wajen kwatar
Fulani da idanun ta suke asama akafe dan wuya...
Koda suka
karbe ta gefe daya takoma tazauna tana haki....
Shiko Abban
Marwan cikin ihu ya ce Salamatu kin cuce ni kin cutar da Rayuwa ta' 'sai yau
nasan Amfanin Karatun Islamiyya' Wanda naki maida hankalina akai tun ina yaro'
'' gashi sakacina a kan Addini ya sa kinyi mugun galaba akaina..
Shi yayan nawa
da yake da adu'oi a bakin sa '' kun kasa iyawa da shi '' shi ne kuka bi '' ta
makirci da tuggu..
Salamatu ban
kaunar ki bankaunar komai naki..
Amma ki sani
baki ci bulus ba.....
Na sake ki
Saki daya..
Saki biyu
Saki uku dan
uban ki..
Hannun Fulani
ta daura akai cikin kuka taje takama kafar sa'' ta ce Dan Allah Samad kace masa
ya maida auren ina zanje ina zansaka rayuwa ta.... Wayyo Marwan kayi magana
mana tashi ta yi tana Girgiza marwan din 'shiru ya yi yana kallon ta yana
hawaye...
Aguje ta yi wajen
Samad tana Girgiza shi ta ce Abdul Samad dan Allah kamasa magana' '' 'shima
shiru yayi.. Hakan ya sa taje gun Ahmad Ko kan ta karaso wajen nasa..
Hannu ya yi mata
Alamun karta kusanto shi...
Yabita da wani
mugun kallo ya ce karki kuskura kazamin hannun ki yatabani..
Cak ta tsaya
tana kallon Ahmad Idanun ta cike da hawaye...
Ganin shigowar
Mamy da Rahama ya sa ta nufe kama kafar Mamy tayi.
Ta ce habiba
dan Allah ki sa baki ya sake ni ya zanyi da rayuwa ta nasaba da gidan mulki nan
komai nakeso ina samu..
Kuka take
sossai
Mamy cike da
tausayi takama Hannun ta '' ta mikar da ita..
Fuskanta Abban
Marwan ta yi ta ce Sani dan Allah kamaida auren na kuskure yariga ya faru..
Sai asannan
yadago kai yana kallon Mamy ya ce Mamy ita jahila ce ta ina ake gyara saki Uku
banson ta ban kaunar ta....
Kuma tabar
tunanin zatabar masarautar nan ba tare da hukunci ba..
Wallahi gidan
kurku zata zauna sai yayana ya bayyana da wannan baiwar sanna za ayi shari'a
ayanke hukunci...
Mamy cikin
tashin hankali ta ce kash Sani da ina nan ɗana
hanaka yin Saki..
Kallon Fulani
ta yi ta ce Salamatu kinga yanda rayuwa ta juya miki baya Ko '' Kidau haka a
matsayin shiri'a ce Allah yake son ki dashi..
Rahama ta ce
haka ne gaskiya MAMA fulani karki gujewa hukunci
Abban Marwan
cikin ba da Umarni ya ce ina Karfin iko yake..
Ahmad ya ce
yana gidan yari..
Ina son a sake
shi dan yau da kan sa zeyiwa Fulani bulala dari sanna ya ajiye mun ita a dakin
daya zauna tare da irin horon da Samad ya bashi..
Ahmad maza je
ka kiramun gangami..
Cikin hanzari
Ahmad yafita dan cika umarni
Mamy nakokarin
dakatar da shi amma ina Ko tsayawa beyi ba....
Samad ganin
Mamy zata hana ruwa gudu ya sa shi yakama hannun ta cikin dabara ya ce Yww Mamy
mu je sashin naki '' kinde San gobe hassana zata wuce '' kince kina son tabi
Samad air plan personnel...
Mamy ta ce eh
haka nace '' bakace saida tabi wani jirgin ba ''
No Mamy baki
FAHIMCE NI bane mu je inganar dake..
Tsare shi da
idanu ta yi ganin yanda yarike mata hannayen ta...
Sake da baki ta
ce kai Yarima ya da haka inajiran inga dawowar baba na ne..
Rahama ta ce
gaskiya kam gâra muga dawowar haka kurum kazo da wata salo da dabara za ka kaita
daki...
Sossai ya yi mamaki
Mamy da Rahama da suka gano lagon sa...
Cikin da ba ta
rai ya ce Mamy nace ba za ki tsaya anan ba meyasa ba za ki gane nufi na bane..
Kama hannun su
ya yi ita da Rahama ya rinƙa jansu har zuwa sashin nata...
Yana kai su ya
ce kada wanda ya sake ya fito haka kurum...
Mamy sake da
baki take kallon sa harya fice ta ce Rahama kinga ikon Allah wai yaron nan yaki
bari na insa baki cikin lamarin ni wallahi tabani tausayi duk da muguntar ta...
Rahama ta ce haka
ne '' nima saina ji babu dadi wallahi
Koda gangami
ya iso Umarni aka bashi yatafi da Fulani gidan kurkuku daman yana cike da jin
haushin ta '' tun lokacin data sa '' Aka hanasa abinci agidan sarauta Saboda sharrin
sata...
Cikin zafin
nama yake Jan ta..
Tana ihu tana
fadin Abban Marwan Nice Fulani kar ka mun haka.
Samad kallon
Abban Marwan ya yi ya ce muyi hakuri da kaddara...
Itakuma ta
zauna nan gidan kurkuku sai anga Abbana da Saratu..
Sannan horon
yunwa da kace gaskiya babu shi zata ringa samun abinci a kan lokaci kuma irin
wanda takeso...
Gidan kurkuku
inda ake ajiye matan sarakuna insunyi laifi nan za a kaita.
Bazata yi
amfani da waya ba...
Abban Marwan
cikin takaici ya ce duk yanda kuka zartar daidai ne...
Babban bakin
ciki na wannan matar ta yi amfani dani wajen shayar da mahaifina maganin Asiri na
hana shi gane komai...hatsabibiya ce matar nan.
Sun dade suna
shawara tsakanin su..
Ɓangaren
Baba Salihu..
Kuwa yana
zaune yana salati '' gani yake inbeje gida akwai matsala..
Tun da yabar
gida be taba sha'awar zuwan ta ba..
Wayar sa ya
dauko tare da kiran mai bashi labari...
Wayar tana
ring ɗagacen ɓangaren ya ce ya shugaba na
kayi wuyar gani ygida ya Ayyuka..
Baba Salihu ya
ce lafiya lau wai ya labarin Samad da Mamy ne da Ahmaɗ ɗa
Sarki..
Uhmm ni tun da
na rakasu airport lokacin da yan uwan Matar Samad za su koma kasar su...
To bankara
zuwa gidan ba...
Shugaban
Adalai ya ce to Saboda me..
Cikin tsaita
nutsuwar sa ya ce akwai wata yarnya da nakeso' 'shikuma Ahmad yarigani har an
nema masa auren nata
Inajin kunyar
haduwa da Ahmad..
Shugaban
Adalai murmushi ya yi ya ce Ahmad dîna ne ya fito da Matar daze aura wacece
ita...
Sunan ta Asiya
ya ba shi Amsa...
Kawar Rahama
matar Samad..
Shugaban
Adalai ya ce Asiya dai ɗana
sani..
Cike da mamaki
Me bashi labari ya ce ka santa ne ya shugaba na..
Murmushi baba
Salihu ya yi ya ce uhmm naga hoton ta mana da Rahama shi ya sa nake magana..
OK yanzu na
fahimta..
Cewar me bashi
labari...
Ina son kayi
hakuri dan Allah a kan abun da ya faru '' inkana so zansa Ahmad ya janye..
A'a nifa
narabu da ita Ko yafasa ba zan aure ta ba.
Ahmad kanina
ne '' mace bazata hada mu ba...
Sossai yaji
dadin Furucin sa..
Ya ce
InshAllah za ka dace da mace mafi kyau a nagarta '' akwai yarinyar da zanbaka
tana cikin masarautar mu..
Ba khadija ba
ce kar kayi tunanin ita ce..
Dan nasamu
labarin Anyiwa Khadija miji.....
MashaAllah Ya
furta Allah yakaimu '' to wacece wannan matar da shugaba na yake son ba ni Ko
ma wacece na amince ya shugaba na...
Sossai yaji
dadi ya ce nako gode InshAllah zakayi farin ciki...
Akwai bikin da
za ayi nan da Sati biyu..
Zanje kano kai
Amarya dakin mijin nata..
In Allah ya yi
zamu hade a kanon.
Me bashi
labari ya ce ai Samad ya ce akwai bikin surukin shi baban matar sa zekara aure
zamuje bikin harda su Mamy kowa ma zeje.
Yayi daidai da
zuwan ka kenan...
Nan da nan
yaji zuciyar sa na harbawa babu wacce yake so da gani kamar Mamy.
Cikin dauriya ya
ce MashaAllah Allah yakaimu babu tabbas mu hadu har yanzu kaci gaba da rike mun
sirrina...
InshAllah
shugaba na bakada matsala Daga haka suka yi sallama...
Kashe
Mai martaba Tun
da sassafe Abban Marwan ya je mishi da labarin komai sossai ya Girgiza ya fara
jerowa Salamatu
Allah ya isa ''
Yana fadin
gaskiya matar nan azzaluma ce..
Mama karama
dake gefen sa ta ce jinjina Al'amarin ta ce shi ya sa ban taɓa ji ta burgeni ba..
Kuma Sani ban
taɓa yarda halin sa
bane..
Na dauki abun
amatsayin beyi dace da matar arziki bane
Ashe ba banza
tabar shi ba..
Mai martaba
tashi ya yi tsaye yana kallon Abban Marwan ya ce '' yau dawuri zanje fada
asanar wa waziri
Zanshiga ciki
inda shirya '' tashi ya yi cike da juyayin Al'amarin..
Ita Ko Mama
karama maida kallon ta yi a kan dan nata ta ce Sani Allah ya sa isar muku ta raba
Ahlina tasa zukata cikin kunci '' kuka ta fashe da shi Abba Marwan ganin
yanayin da take ciki ya sa shi Sakin kuka shima ya ce da wani idanu zan kalli
Salihu '' bayan inacikin waɗanda
suka tozarta shi...
Mama Karama ta
ce kar ka damu Sani Allah ze shige mana gaba '' Amma wannan matar Samad din nan
kash ba mu da abun da zamu iya biyan ta '' domin ta yi jarumta...
Kusan karfe
tara '' Hassana tagama shiryawa zaune take kusa da Mamy cikin kukan rabuwa ta
ce Mamy ke mace ce ta gari harna ji ba na son rabuwa dake...
Mamy cikin
kewar da zatayi ta ce '' Hassana da wallahi mijina yana gari dana bashi umarnin
ya aure shi dabi'un ki da halayyar ki sun mun sossai wallahi...
Wayar Hassana tafara
ring tana dubawa taga Hauwa ce...
Cike da Farin
ciki ta ce Daughter dankinji ina nan tafe yau shi ne kika nemeni dawuri ko
Daga can ɓangaren ta ce mommy na kuma
Amaryar Abdurrazak '' ace zaki daura aure sai yau muke samun labari uhmm ni dai
Ko dani za a kanon na..
Sossai Hassana
ta dara tana kallon Mamy ta ce yawwa ga diyarki hauwa ku gaisa mikawa Mamy
wayar tayi..
Cikin hanzari
Mamy ta mika hannun ta takarbi wayar '' tare da karawa a kunnen ta...
Inawuni
daughter yanda ta ji hassana ta fada cike da fara'a
Daga can ɓangaren ta amsa da lafiya
lau Mamy daman mama ta tana ba ni labarin ki '' zanso wataran inganki '' kinyi
a rayuwa kun rike uwa ta tamkar yar gida '' Allah ya saka muku da Alkhairi
Mamy...
Cike da Jin
dadi Mamy ta ce Ameen ni dai daughter '' wajena zaki dawo nan da zama in Allah
yakawo miji sai kiyi aure Ko..
Sossai Hauwa
ta dara hadda rufe Idanun ta '' ta ce mezehana ni zuwa Mamy '' InshAllah in
Mama ta tawuce kanon to ni kwatanon zanzo....
Nan da nan
fira ta barke tsakanin Mamy da Hauwa..
Ita Ko Hassana
kallon su take tana dariya cike da farin ciki...
Suna gama
wayar tamika wa hassana wayar ta...
Ƙaramin
akwati Mamy ta cika da kaya ta ce hassana wannan kayan nida Rahama ne muka baki
dan Allah ba yawa ayi hakuri..
Cikin farin
ciki take kallon akwatin ta ce kai MashaAllah '' kaya sunyi kyau fa...
Cike da Jin
dadi ta ce Allah ya saka muku da Alkhairi....
Yarima Samad
'' kallon Rahama yake cike da mamaki tun safe ba ta ci komai ba..
Amma amai take
ta zuba duk ta galabaita......
Da ƙyar ya
lallabata yabata ruwan lipton shima saida yasha lemun tsami da kanunfari ''
Sannan ta kurba....
Kallon Samad
take cikin ciwon cikin daya taso mata tana dafa marar ta..
Ta ce wayyo
Amjad Mutuwa zanyi '' '..
Cikin gigita ya
ce Ah Ah Rahama ki daina Ambatan mutuwa please na rokeki...
Cikin hanzari
yadau wayar sa yakira likitar masarauta...
Koda likitan
ya iso..
Khadija ce ta
yi masa jagora har dakin Samad..
Ita Ko Khadija
cikin hanzari ta nufi sashin Mamy domin sanar musu abun da yake faruwa...
Cin karo ta yi
da Su Mamy da hassana harda Ahmad '' za su tafi parking space..
Ganin khadija
kamar ba cikin hayyacin ta take ba..
Mamy ta ce
lafiya kuwa Auta '' meyake faruwa ne
Ina Samad da
Rahama ana jiran su gashi har Hassana zata wuce ita kadai ake jira a filin
jirgin....
Hassana itama
kallon Khadija take cike da zakuwa ta ce lafiya kuwa yar nan kinyi shiru...
Bakin ta Na
rawa ta ce wallahi Mamy matar Samad bâtayi barci ba '' wai ciwon ciki...
Gata cen
likita na duba ta
..
Subuhannalah
Mamy ta Furta cikin hanzari ita da hassana da Ahmad suka yi Sashin Samad dan
ganin abun da ke faruwa...
Koda suka isa
iske Rahama suka yi...........
Wata yar uwa
acikin members dîna ta ce kusata a adu'ar ku a kan wata damuwa..
Sannan nikaina
ina barar adua a kan nawa lalurar ta rashin lafiya '' da kuma yar antina da
tasha guba jiya a rashin sani ''
Allah yabata
lafiya ya sa ta warware normal...
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah...8️⃣9️⃣
Koda suka isa
iske Rahama suka yi tana Amai''cikin tashi hankali mamy ke magana ta ce yata
jibi yanda kika fada Daga jiya zuwa yau...
Kama hannun
Rahama ta yi tana jero mata sannu.
Maida kallon
ta a kan likita daya gama auna fitsarin Rahama ta ce likita meya damun ta
kardai ace maleria ce...
Takarashe
zancen tana kallon Samad dake yarfe hannayen sa...
Cikin nutsuwa
likata ya fara magana ya ce ''
Ya ce uhmm ba
maleria ba ce..
Samad da Mamy
suka hada baki wajen fadi to mene ne...
Tana dauke da
ciki ne '' shi ne yake ba ta wahala cewar likita..
Cikin tsananin
Farin ciki Samad ke kallon Likita Sam ya mance Mamy na dakin ya ce likita kana
nufin Hubby tana dauke da ciki...
Kwarai kuwa
dukan alamu sabon ciki ne...
Bakin Samad
Yaki rufuwa zuwa ya yi ya rungumi Mamy ya ce kinji ance tanada ciki wayyo
dadi...
Cikin tsananin
farin ciki yake magana...
Mamy cike da farin
ciki ta ce kai Amma yaushe kazama mara kunya haka.
Furucin Mamy
ne yadawo da shi cikin hayyacin sa..
Cike da kunya
ya fara sosa keyar kansa.
Kallon Ahmad
yake shida Khadija yanda bakin su yaki Rufuwa dan Farin ciki..
Ahmad ya ce
congrat Yaya Samad wayyo dadi zan zama uba cewar Ahmad..
Hassana dake
dariya ta ce kwarai kuwa za ka zama uba kwanan nan..
Cike da Jin
dadi ya ce Mama hassana '' mu je mu rakaki airport din kada mu rasa jirgi...
Yarima Samad
da farin cikin da yake ciki ya ce Ah Ah Ahmad kayiwa drever na '' na Samad air
plan personnel '' kace ya yi maza ya shirya shi ne ze kaita kasar Gabon..
Ba ƙaramin
dadi Mamy da hassana suka ji ba'' hassana ta ce godiya nake Yarima Allah ya
inganta cikin dake jikin Rahama Allah ya sa ta haifo mana yan hudu..
Ameen ya Allah
ya furta kai tsaye ba tare da ya yi shayin komai ba...
Rahama duk
kunya ya lullube ta takasa hada idanu dasu Mamy...
Ganin haka
Mamy ta ce Rahama kikula da cin abinci kinji ko'Kuma ki daina girki' ɗuk kalan abinci da kike so
ki gayamin zan dafa miki..
Gyada kai
Rahama tayi' 'cikin muryan Mara lafiya ta ce Mama hassana Allah ubangiji
yakaiki lafiya yatsare hanya.
Da ameen suka
Amsa dukan su...
Likita cike da
Jin dadi ya ce toni zan tafi wannan takardan magunguna ne kuma Daga watan gobe
zata fara zuwa awo hakan yana da matukar muhimmanci..
Samad ya ce Ah
Ah harsai ankai watan gobe ni yanzu ma tafara zuwa..
Harara Mamy ta
watsama Samad ganin haka ya sa ja bakin sa ya yi shiru...
Mamy ta ce
likita sannu da kokari inda wani abun zamu nemeka...
Samad ganin
likitan ze wuce ya ce likita nabaka kujerar makkah..
MashaAllah
MashaAllah kowa dakin ya furta cike da Jin dadi likita ya fara kukan Dadi ya ce
watau Allah ya yi kira..
To Allah ya
inganta cikin Amarya da Ameen kowa ya Amsa dakin..
Babu ba ta lokaci
Hassana suka bar dakin da Mamy da Ahmed '' khadija kadai aka bari dan Samad
shima yafita rakiya..
Rahama kallon
Yanda Khadija ke kokarin gyara daki take '' tahana ta yin wani abu...
Nan da nan
tashare daki ta goge ta kunna turaren wuta..
Ruwan dumi ta
hadawa Rahama tadawo dakin tare da kama hannun ta '' ta ce anty tashi mu je Ko..
Babu musu
Rahama ta tashi dan ita kanta tasan tana bukatar wankan....
Har Filin
Airport Mamy suka Raka hassana..
Suna kallon ta
har ta shige jirgin tana ta Daga musu Hannun cike da kewar su...
Koda jirgin ya
Daga Samad cike da Jin dadi shida Ahmad suke fadin gaskiya wannan matar tanada
kirki ba ta da damuwa....
Mamy ta ce
gaskiya ba ta da damuwa jibi yanda Babana ya dame ta Ko ince kuka dame ta amma
ba ta taba nunawa ba tadauki hakan ne amatsayin dan bakusan ita wacece ba ''.
Sossai Ahmad
ke nadaman rashin kunyar da yake zuba mata inyayi tozali da ita agidan.
Cike da kewa
suka bar airport din....
KANO
Sossai sheik
ke shirye shirye sabon gidan su.
Da za su tare..
Mama kam cike
da Farin ciki ta ce uhmm zanfaso gari fa..
Samun sheik ta
yi azaune a dakin nasa ta ce gaskiya yakamata kasai mun mota mana...
Murmushi Sheik
ya yi ya ce Aishatu kedai baki rabo da abun dariya..
Akwai kudade
da Rahama diyar makiyar ki tabada zanbaki millions 10 '' itama Sa'adatu
millions 10..
Abubakar
millions 5
Asiya millions
5
Salma 5
Kinga Millions
15 ne nawa.
Inkinga dama
ki sai mota da kudin Ki '' duk yanda kika so daidai ne....
Mama cike da
takaici ta ce kambuhu nida haihuwar ya wasu da raba kudi..
Sheik ya ce
kwarai kuwa ɗanma
bansa Abdul jalil ba..
Cikin nawa
kudin zanba uwar shi ta ajiye masa millions biyu Ko shima ya san yayar shi
Rahama ta mana kyauta...
Aisha yanzu
dai nagama bayani '' kudi kuma anjima zanfiddo in baki naki..
Mama sake da
baki ta ce uhmm Abdurrazak kenan wai kai wani irin jarabben mutum ne '' duka
nawa kake za ka hada mata uku..
Kasaitaccen
Murmushi Sheik ya yi ya ce uhmm Indo tawa nikadai '' inbanda abun ki..
Mata suna yawa
ne ai bakwa yawa Inde kanada lafiya meye matsalar..
Mama rike da
baki ta ce ikon Allah '' yau na gida ya koshi har kake kiran kanka me lafiya..
Sheik kallon
ta yake yana nazarin kalamanta ya ce tun da baki koshi '' kibari zuwa ɗare '' sai agani Ko..
Zare idanu
Mama ta yi ta ce wallahi bana bukata '' haka kawai '' ina fama da kai ka sakar
mun da kasala da ciwon jiki '' inkasa samu abu ba ka san Ana ajiyewa ba.....
Sheik dariya
ya yi ya ce Aysha ke fa kikace banda lafiya nayi tunanin kin manta ne ashe kina
tune Kinga kenan kun mun kadan keda Sa'adatu saina auri Hassana inje innemo
sadakar yalla in hada da ita kinga na cika sunnah kenan
Sossai Ran
Mama ya ba ce ta ce aiga yayan ka nan gidan miji kana son ayi masu abun da
kamun..
Kwarai kuwa
indai karin aure ne ni zanba mijin nasu gudummuwa '' abun farin ciki ne fa ''
kuma karuwar su ce...
Mama sake da
baki take kallon sa ta ce kam buhu lallai kace wani Abu..
Ni zan tafi sai
dai anjima. 'tashi ta yi tafita tana tunanin tayanda zata Koma gidan Malam' ɗan kam bazata bari anty ta
haihu ba...
Tana fida
Sa'adatu ta shigo ya ce mata ze basu kudin nan..
Da Rahama ta
bayar..
Anty ta ce Ah
Ah kabar shi a hannun ka' Kaida kake dawainiya damu ba ka taba gajiyawa ba'' bama
siyen komai da kudin hannun mu. Kaine kake mana ba mu nema mun rasa ba..
Dan haka kabar
shi Nina yafe wallahi...
Sossai Sheik
yaji a zuciyar shi kaunar ta na dada ruruwa dan beda kamar acikin matan sa...
Ta cire tuta ita
ce mace daya tilo data sace bargon zuciyar sa' 'in babu Sa'adatu bayajin
rayuwar sa ze tafi daidai..
Dawo da
hankalin sa kusa ya yi ya ce Ah Ah Sa'adatu wannan kudin yar ki tabaki kisiye
koda gida ne da shi kisa haya..
Wannan kudin
hayar kiringa badashi sadakatul jariya' in canji sun rage ki gina massalaci
wanda Ko bayan ranki zaki amfana..
Sossai ta yi naam
da shwarar sheik ta ce Allah ya saka maka da Alkhairi...
Ameen ya amsa
yana murmushi ya ce gobe ina dakin ki 'nakosa gobe yazo..
Murmushi ta yi
cike dajin dadi ta ce InshAllah zata zone..
Daman kan
zancen inda Amaryar ka zata zauna nazo' 'yakamata dakin nata y azauna kusa da
nawa..
Kaga Mama ita
ce shugaban gida.
Sashin nata
zefi namu dan girma..
Sheik ya ce
kuma haka ne' 'nata zefi girma amma nayi girman irin nata guda uku kinga
inkinaso kizauna saman bene mana....
Ita Amarya ta
zauna saman bene na uku...
Anty ta ce
hakan ya yi ka ga Ko Mama kasar nan ya ishe ta ga dakuna barkatai..
Eh ya isheta
kinga har dan nata Abubakar ya samu dakin daze ajiye matar sa kafun yagama nasa
tun da ya ce mun aure yake so....
MashaAllah
Anty ta furta ta ce wayyo Dadi ɗana
zeyi aure '' kar abata lokaci wajen nema masa auren..
***************
Asiya tana
zaune a dakin mamar ta baban ta ya shigo ya ce '' yawwa kuna zaune ana kenan ''
Asiya cike da
ladabi ta gaishe shi ya amsa da yawwa yata...
Daman magana
ne a kan auren ki Asiya..
Saida gaban
Asiya ya fara dukan uku uku cike da razani ta ce Abba inajin ka tare da yin
kasa da kanta zuciyar ta na bugawa da karfi gab gab......
Kallon Maman
Asiya ya yi ya ce yau aka turo kudin auren Asiya harna basu sunce nan da Sati
biyu za a daura auren..
Kuma na'amince
duba ga irin gidan da mutuntaka irin na gidan da suke neman auren ta.....
Kuma Sheik
Abdurrazak ya jagorance su ba zan iya hanawa ba...
Dib Dib haka
Asiya ta ji jinta da ganin ta na kokarin daukewa..
Maman Asiya ta
ce MashaAllah Abu ya yi Allah ya sa Alkhairi...
Kenan rana
daya za ayi bikin ɗana
Asiya da Sheik kenan..
Kwarai kuwa
cewar Abba.
Ke Asiya ya
furta da kakkausar murya hakan ya sa ta Dago jajayen idanun ta da suka kada..
Ta ce na'am
Abba '' kindaiji abun da nace dake aure zanmiki duk wani Samari Daga yau ki
ajiye su gefe ki fadi abun da kike bukata a sai miki dan lokaci yakusa..
Sannan mijin
da zaki Aura ya ce bayason kina chattin..
Maman Asiya ta
ce wai yasunan mijin da ze auri Asiyar..
Abban Asiya ya
ce kamar Ko Ahamdu ne sunan nashi na manta zankara tambayar Sheik..
Abba na Fita
Asiya ta fashe da kuka ta ce shi ke nan anrabani da Faruk mama '' Ko wannan
dalilin ne ya sa kwata kwata ya daina nema na...
Kuma shi wanda
akace ze aureni ban san shi ban san Daga inda yake ba...
Maman Asiya ta
ce kiyi hakuri zaki sanshi ne '' Nina ai aurena da baban ki ban san shi ba''
Aka hada auren
gashi yanzu muna zaune kalau.
InshAllah
zakiyi Farin ciki' 'bubbuga bayan Asiya ta rinƙa yi Alamun rarrashi.
**********************
Salma zaune
take a falon nata ta mimmike kafa kan 3tsr remote na hannun tana canza tasha..
Al'amin ne
yashigo ya iske ta zaunen ya ce Amarya kina hutawa fa.
Eh ina hutawa ta
ba shi amsa tana yatsine fuska....
Ihun kiran yar
aikin take cikin izza da takama.
Nan da nan me
aikin nata tazo ta durkushe gaban su..
Wani kallon
banza take bin ta da shi ta ce ke je ki kawowa me gidan abinci da lemu..
Al'amin zama
ya yi yana kada kai cikin zuciyar sa sai fadi yake wannan yarinyar ta iya
rainin wayo fa......
Cike da jin
haushi ya ce kewai salma meyasa ba ki da Tarbiyya ne....
Tarbo ne
banida shi ba Tarbiyya ba cewar Salma tana huci sama sama banda wulakanci ni
baiwar me waina ce....
Dazan dauko
maka Abinci cikin Daga Murya take magana...
Al'amin cikin
fushi ya tashi ya ce wallahi kedai an yi asarar haihuwar ki..
Kuma zaki ga abun
da zanmiki agidan nan.. Shasha kawai fuuuuu ya tashi yawuce tare da barin
abincin beci ba yahaura sama..
Dakin sirrin
nasa ya shiga kai tsaye kayan jikin sa yacire ya dauko jajayen kaya ya saka...
Zama ya yi tare
da nannade kafafun sa ya takkwashe su waje daya fuskakantar kwaryan dake dauke
da jini yayi..
Yana wasu
kirari '' yana wasu maganganu nan da nan hoton wasu mutane ya bayyana..
Wanda ke nuna
sune shugaban yan mafiyan '' 'babban ya ce kai Al'amin tun da matar ka nada
ciki basai ka ba mu uwar ba....
Tana haihuwa
da wata biyu zamu ashe su dukan su..
Al'amin cikin
zazzare idanu ya ce what ban gane harda abun da zata Haifa..
Nifa...........
9️⃣0️⃣
Nifa ba zan ba
da ɗana ba ita dai
nakeson inbaku..
Shugaban yan
mafiyan cikin Idanun sa dake cike da bakin abu kamar kwalli yana zazzare su
kamar kwai ya ce kai Al'amin abun da dodon tsafi ya nema kenan saikace baza a
bashi ba.
Zancen banza
kake mu nan da muka ba da matan mu da yayan meya same mu bakaga muna ci gaba
ba..
Al'amin cikin
Idanun sa da suka kawo ruwa ya ce dan girman Allah kubari dai inbaku Mata ta
ita kadai abun da zata haifa mun ina son yazauna ina ganin abuna...
Shugaban ya ce
Al'amin zamuyi shawara sai dai kaji mu..
Suna kai
karshen magana.
Ya ajiye
kwaryan tare lakato Jinin kadan ya latsa a bakin sa....
Barin dakin
tsafin nasa ya yi kai tsaye yatafi dakin sa..
Yayi wanka
yashirya tsaf cikin kananan kaya..
Shigowar Salma
ne ya sa hankalin sa yadawo kanta sanye take cikin doguwar riga '' cikin nata
harya dan fara turowa..
Neman wurin
zama take tana turo baki gaba '' wayar ta ce tafara ring tana dubawa taga Mama ''
kamar bazata Daga ba.
Amma saita
daure ta daga cikin kasa da murya take magana..
Mama ta ce
haba Salma yau dan nace ki koma gidan mijin ki shi ne kika shareni bakya nemana
haba yata '' Nice fa uwar taki..
Salma yatsine
Fuska ta yi ta ce mama kenan tun da kika koreni gidan naki harda mun duka..
Keda Abby da
Abu saida nasha mari taya zan tuna ki..
Uhmm dadin
abun nima mijina ya samu wadata muna cikin daula Ko Rahama bazata nuna mun Jin
dadi ba saida ta nuna mun Sarauta...
Mama ta ce
MashaAllah yata kice Allah ya ɗauka
ki '' kenan basai ankashe auren naki ba..
Salma ganin
Al'amin na dakin ta ce Ah Ah kedai kawai zan nemeki..
Naji batun
auren Abby wai saura sati biyu..
Yanzu Abby
banda tsabar jaraba meze da wata bazawara '' mama ta ce kedai bari Salma kin
san halin uban naku '' da shegen naci kamar kurma..
Ya ce zekara
sonake insan hanyar dazanbi wajen dakile wannan auren '' har ita Sa'adatu bana
tunanin zan barta '' saita bar gidan nan kuma cikin jikin ta '' sai dai
abinne..
Wannan gidan
da zamu koma ni kadai zan tare Daga ni sai ɗana
Abubakar.
InshAllah sai
dai ta koma kauyen su ruggar Fulani '' makirar mata kawai...
Salma tabe
baki ta yi ta ce mama zan kira zuwa dan anjima ganin Al'amin ba ta iya fadin
komai...
Tana ajiye
wayar ya nufo soma ja da baya ta yi ta ce haba meye haka me zan maka ne....
Cikin Fada ya
ce hakkina zaki ba ni '' taya zaki hana ni '' tun da ki kazo Alkur'an baki isa
ba....
Cikin zafin
nama ya cakumo ta kasa kwacewa kuka take ta ce wayyo Al'amin zan daina zagin
ka..
Cikina ke min
ciwo pls kar ka tabani..
Beko saurare
ta..
Hakanan
yakamata '' ya yi mata dadddaya tare da rabata da kayan jikin ta...
Salma dai
tasha wuya hannun sa dan beje mata da wasa ba.....
Cikin Jin zafi
da radadi ta rinƙa fadi Allah ya isa mugu Azzalumi kawai..
Wayyo marata
'' wayyo cikina hakanan tafara ihu tana fadin innaliahi wa'inna il rajun.
Ganin da
gaskiya take salatin ya sa shi ruɗewa
tare da daukar ta...
Yakaita
bandaki ya yi mata wankan tsarki.... Kaya ya canza mata tare kaita Asibiti babu
ba ta lokaci....
Koda likitoci
suka rufo cikin hanzari suka kaita umergency '' taimakon gaggawa suka ba ta tare
da tsaida Jinin dake mata zuba....
Suna Asibitin
har babban su yazo ya yi mata scanin dan ganin lafiyar abun da ke cikin
nata.........
Yana dubawa
yaga komai normal kawai cikin na barazanar barin jikin ta
Magunguna
yabasu tare da yiwa Al'amin gargadi kada yakara kusantar ta harsai cikin nata
ya tsufa.........
Al'amin cike
da damuwa ya ce InshAllah zekiyaye..
Kashe Gari
Kwatano
Yarima Samad
cikin shigar sa ta zuwa aiki '' yana gaban mirror yadau hular sa'ta lauyoyi ya
saka' 'yana kokarin tashi dan feshe jikin sa da turaren sa one love..
Wayar sa''
tafara ruri.
Yana dubawa
yaga Ansa Yusuf Sani Yaro 'cikin hanzari ya daga' '
Daga can ɓangaren bayan gaisuwa ya
fara masa bayanin dalilin kiran nasa...
Ya ce Yarima
Ahmad matar nan mun gano inda take tana gwammaja' tagwayen gida nan cikin garin
Kano''' daidai lungun yan darika...
Gida mai lamba
111 ansa Garba shehu jikin gidan..
Dan haka zansa
wakilai na''suje gobe su dauko ta... In ankamo ta a ina kake so mu ajiye maka
ita...
Yarima Samad
cike da Farin ciki ya ce Namijin zaki' Kayi kokari sossai banyi tunanin lokacin
daka diba za a samu abun da ake so ba...
Wannan Shari'a
a kwatano za ayi Shi' Kuma sai Mahaifina ya bayyana...
Yusuf ya ce kana
son in zakulo maka inda baban ka yake ne
SAMAD ya ce abun
da na shekara da shekaru ina yi kenan babu nasara...
Kasaitaccen
Murmushi Yusuf ya yi ya ce' ɗa
tuni ka gâyamun dana dade da nemo maka shi' 'amma yanzu ba ta baci ba..
Katuromun
hoton mahaifin naka' 'nashi binciken sirri zanyi dan nasan beson asan inda
yake..
Samad ya ce haka
ne yana mai canza wayar zuwa dayan kunnen sa..
OK Yarima
turon hoton sa shi kwana uku zakaban dan akwai tarin Ayyuka gabana dasai ince
maka yau sai inbaka informations a kan sa.....
Yarima Samad ya
ce meze hana kaduba mun a yau haba Yusuf dîna..
Yusuf cikin
gajiya da wayar gashi ana jiran sa '' ya ce Samad inaga nagama da kai infira
kake ji mun hade online zuwa ɗare
'' matar bakace inda zan ajiye maka ita ba...
Yarima cikin
dan nazari ya ce ka ajiye ta a kanon amma in zamu tafi kwatano da kai zamuje Ko
zanzo bikin surukina kanina ze daura aure nan da mako biyu..
Yusuf ya ce
babu matsala zan gayyato shalelen gidan namu Zahradeen amma shi iyakar sa Kano
'' wajen daurin auren nan..
Yarima Samad ya
ce kai kai Deen yana gari shi ne Ko Daga hannun babu..
Yusuf ganin
firan bekarewa ya ce dakata malam firan ya isheni sai anjima
Bejira cewar
Samad ba ya katse kiran.....
Yarima Samad
maida kallon a kan Rahama ya yi ya ce kinga ikon Allah '' ya gano inda Saratu
take maman nusaiba..
Rahama ta ce
MashaAllah abun dadi Amjad gaskiya ya yi kokari amma yusuf dinnan kamar ba
jinine a jikin sa ba'
Be gajiya da
aiki '' Samad ya ce uhmm haka yake shi besan hutu ba' 'yanzu ma kina ganin
yakatse wayar ne dan anajiran sa....
Zanje wajen
aiki inna dawo zantura masa hoton abbana
Rahama cikin
da ba ta fuska ta ce ayya ni dai ban taɓa
ganin sa a hoto ba...
Yarima cikin
hanzari da lokaci yatafi ya ce haba hubby na kibari indawo mana '' zaki ganshi
''..
Har wajen
sashin nasu ta yi masa rakiya tare da adu'oi Allah yakare ka mijina..
Allah yakare
da mugun ido na yan mata..
Shiru yayi.
Ta ce ba za ka
ce ameen ba..
Murmushi ya yi
to inna ce ameen kina nufin ba zan kara aure ba...
Murmushi ta
sakar masa ta ce za ka kara mana amma ba yanzu ba..
Uhmm to Ameen
my Rahama bayan ke babu wata zolayar ki nake gimbiya ta nasan ke baki cikin
mata masu kishi kawai kina son kare ni Daga fadawa sharrin mata ne..
Kwarai kuwa My
Amjad ka gane ka ga inzaka dawo kabiya kasiyo mun agwaluma..
Zazzare idanu
ya yi ya ce Agwaluma kuma my hubby..
Eh mana inba
sokake in maka kuka ba '' ta marairece fuska...
Cikin
shagwaba..
Kallon kansa
yake ya ce kin kalli shiga ta kuwa zaki aikeni wajen masu saida agwaluma
'lallai na yarda wayannan yayan sun tasoni gaba Daga na taimaka musu zankawo su
duniya sai su takura mana nida kanina..
Hangon Ahmad
ya yi cikin shiga ta Alfarma sanye yake cikin babbar shadda gezner' 'sai kamshi
yake zubawa
Yarima Samad ya
ce yawwa kanina ina za ka je ne kake ta buga uban sauri haka..
Cak Ahmad ya
tsaya yana kallon su dan bema lura dasu..
Cikin sakin
Murmushi ya ce zanje daurin auren abokina dake sabon zongo' Shamsu ka tuna shi
Ko..
Yarima Samad
Alamar nazari ya ce eh eh nagane shi Ayya yaune daurin auren nasa to Allah ya
sanya Alkhairi ba ka fada min da wuri ba da munyi maka kara..
Yaushe za ka dawo
ne..
Ahmad ya ce da
an yi la'asar..
OK Good ni
inna fita zankai bayan magrib
Anty taka yake
son agwaluma kaje kasiyo mata a hanyar ka ta dawowa gida..
Nan da nan
Annurin dake kwance saman fuska Ahmad ya ba ce bat kamar bashi ba..
Ya ce kam buhu
ran nan danwake muka je nema yau agwaluma duk gidan nan babu me zuwa saini ''
haba yaya wai meye haka ne a kalle ni da wannan shigar tawa inje gun masu siyar
da kayan tsami...
Sossai Rahama
ta dara saida fararen hakoran ta suka bayyana '' cikin cool voice din ta Ta ce
My Ahmad dîna kar ka damu '' zan aiki Karima zata je ta zabomun masu zaki..
Shi yayan naka
yana Jin kunyar zuwa siye bare kai dan gayu..
Kada kai ya yi
ya ce Atoh anty kedai gayamasa ba ajina bane kinga tafiya ta kada ya ce wani
abun bayan wannan Bejira cewar Samad ba yakara gaba yana buga uban sauri...
Yarima Samad
murmushi ya yi ya ce kinga kanin nan nawa '' matar sa zata sha aiki...
Wai m'a kin
san cewar kawar ki Asiya ze aura nan da Sati biyu kuwa..
Zazzare idanu
Rahma ta yi ta ce Asiya kuma yaushe hakan ya faru ba ta gayamin ba..
Yarima ya ce
kinga tafiya ta karki kira Asiya a kan maganar auren nan inaga ita kanta
batasan Waye mijin ba '' cewar Mamy..
Kibari inna
dawo zamuyi magana saimu kirata Ko..
Kada kai
Rahama ta yi cike da Jin dadi ta ce woww yanzu Asiya zata zauna kusa dani ''
cikin masarauta '' Allah na gode maka daka Amshi adua ta a kan kahadamu zama
waje daya nida Asiya..
Neman Karima
tashiga yi '' cike da girmama Karima tazo ta ce ya shugaba ta gani kiban
umarni..
Cike da Jin
dadi '' Rahama ta ce yawwa Agwaluma zaki siyo mun'' biyo ni ciki in baki
kudin..
Koma ciki ta
yi Karima ta take mata baya....
**************************
Gabon 🇬🇦
Dakin hassana
cike yake Makil da jama'a dan gaishe ta da masu mata adua Allah ya sanya
Alkhairi na auren da zatayi.....
Hauwa cike da
murna ita da kanin ta Imran suke zaune kusa da uwar tasu...
Mama kinga
yanda kikayi kyau da kiba kuwa cewar Imran..
Hauwa ta ce
wallahi nima haka zance gaskiya kwatano zan tafi nima dakin wuce Ai Mamy ta ce
inzo..
Hassana kallon
su take tana murmushi ta ce uhmm kudai Ko...
Yanzu ku
kwashe kwanonin abincin nan nakoshi..
Kuma zanje
dakin mahafina ina zuwa ta ce musu tare da mikewa tsaye..
Kai tsaye
dakin nasa ta nufa '' koda ta isa iske shi ta yi yana waya..
Cikin Jin dadi
tazauna tana jiran yagama wayar..
Yana gamawa
yadawo da hankalin sa a kan ta ya ce Hassana ya gajiyar tafiya .
Alhmdulilah
yabiki jiki ta amsa cike da Jin dadi..
Imran ya ce
kana kirana shi ne nazo takarashe zancen tana sanda kanta kasa...
Yawwa ya furta
yana kallon ta ya ce wakilin angon naki yana waje yana jiran ki..
Yazo ganin ki
kuma ze baki wayar da zaku ringa gaisawa da wanda zaki aura.
Sannan ya aiko
da akwati guda biyu na lefe Makil da kaya..
Gaskiya
mutanen nan sunyi kokari bazawara harda lefe cewar baba..
Hassana cikin
ladabi ta ce Allah ya sa Alkhairi Abba zanje ingansa kamar yanda kace nasan ba
za kamun zaben tumun ɗare
ba..
Cike da
Fargaban waye wannan wakilin Angon nata' tazura hijab din ta..
Tafita kanta
akasa take tafiya cikin fargaba' '
Shiko tsaye
yake jikin bakar motar sa mercendez' ganin isowar ta..
Yasa shi Fadin
yar kwatano har kin dawo ne yana murmushi gashi nasa kindawo babu shiri...
Dago kai ta yi
dan ganin me maganar caraf Idanun su' suka tsarke cikin juna..
Cikin...............
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah akwai bonus inhar kunyi comment9️⃣1️⃣
Cikin mamaki
'' ta ce shugaban Adalai me kakeyi anan wajen..
Wani kake nema
ne dan a zaton ta Ko yazo ne ya ce ya amince ze aure ta..
Murmushi ya yi
cikin kasaitar sa ya ce '' Nine bakon da Aka turo ki wajen sa...
Kada kiyi
mamaki '' Nine nan na nemawa uban gidana auren ki..
Tun da nasamu
labari kina garin kwatano '' nasan kaunar da kike mun ya yi zurfi kada inbar ki
haka cikin Adalci na '' shi ne na ha daki da Uban gidana kuma malami 'surukina
sheik Abdurrazak kabeer hizqeel makarfi..
Cikin matukar
Mamaki ta ce uban Rahama shi ne mijin dazan aura wannan shahararren Malamin
Addinin da duniya tasan da zaman sa Yayiwa Addini hidima' 'mijin Sa'adatu
baiwar Allah da muka hadu a masarauta' 'hawaye tafara dan kukan Farin ciki ta
ce nagode shugaban Adalai niyau sheda ce' 'sunan ka yabika taimakon ka'
'yabika' Kyawun halin ka yabika' Wallahi kai adali ne kuma mai tausayi na kasa
da shi jibi irin wannan babban Alkhairin daka hadani dashi..
Durkushewa
kasa ta yi tana kukan Farin ciki' ta ce ta ce nagode sossai jazakallahu
khairan..
Murmushi ya
sakar mata ya ce amshi wannan wayar akwai layi A'ciki na kasar Nigeria' Wanda
Inkin je da shi zaki ringa amfani' 'Sannan layin ki na nan zaki ringa siyen
data da shi kina hawa online har kibar kasar nan....
Wayar iPhone
12plus yabata cike da girmamawa ta karba tana godiya..
Inkin je gida
kisa caji zuwa ɗare zaku
yi waya ke dashi..
Ina son ki
nuna masa kauna da soyayya mutum ne me saukin kai inka iya zama da shi ''
Sannan yana da Adalci '' dan na zauna da shi zakiyi Alfahari..
Hassana cike
da Jin dadi ta ce wannan mutumin kowa ya san adaline koda ba ka zauna gidan sa
ba wanda yake gina masallatai kowani reshe na kasa '' kuma ya gina gidan marayu
yana tallafa musu '' 'yana gidaje sama da hamsin akace amma ance duk haya ya
saka' Kuma kudaden gidan marayu ake kaisu.
Kai ka ga
yanda mutane ke yaba kokarin sa duk yana boye beson ana fadi hatta gidan sa
baya fada musu sirrin Alkhairin sa saboda neman dacewa awajen ubangiji..
Wallahi
kabiyani indai Abdurrazak ne' Kaikuma Allah yakawo karshen wata fitina ya
hadaka da matar ka Habiba lafiya..
Cike da Jin
dadi ya ce Ameen ya Allah godiya nake.
Kinga tafiya
ta' 'saide mun hade yar Albarka
Babu ba ta lokaci
yabar nan cike da Jin dadi
Ita Ko cike da
farin ciki ta shiga gidan tana ba hauwa da Imran labarin yanda suka yi' 'sossai
suka yi farin ciki' 'Imran tabe baki ya yi ya ce watau ni kadai za a bari a
gabon
Hassana ta ce
haba Imran kade san bazamu bar Abba shikadai ba'' tare da zaku zauna da
inna....
..
Bayan Isha'i
bayan takwanta dan tanada tarin gajiya tare da ita..
Tuno da wayar
da Aka kawo mata ta yi hakan ya sa tadauko ta kunna wayar' tana kawo haske babu
ba ta lokaci ta yi siye data' Koda ta shiga whsap dînta..
Ganin Nombar
sa ansa Sheik Abdurrazak cike da farin ciki tarubuta Salam
Shiko yana
online ganin salam din yashigo..
Ya fara shafa
gemun sa yana Murmushi..
Maida mata
reply ya yi da waalaiki Salam' Amarya Barka da warhaka...
Ganin reply
din sa sossai ya yi mata dadi hakan ya sa fira ta barke tsakanin su Kamar sun
taba sanin juna a karshe dai harda video call..
. Yana kallon
ta yana Murmushi MashaAllah ya furta' ganin ta da ya yi sanye da hijab kuma
gata Black beauty' 'bama ka sanin ta haihu Saboda yanayin jikin ta...
Ita ma tana
ganin sa wai washe baki take' ta ce yasu anty na...
Suna lafiya
lau yabata amsa '' hakadai suka sha firar su '' ta love zuwan mama a dakin ne
ya sa ya katse wayar dan kwanan ta ne kuma ya san hali....
Ita Ko Hassana
wani shauki takejin kanta harta Kosa ranar yazo....
***********************
Kwatano
Ka sancewa ɗare ya tsala hakan ya sa
baban Maryam barin dakin nasa sum sum ya fito Daga dakin matar sa '' 'yabar ta
kwance rungume da pillow..
Kai tsaye
dakin yar aikin nasu yatafi wacce ba ta wuce shekaru 16 ba matashiya ce' Kuma
da aikin suka dogara....
Yana shiga
dakin iske ta ya yi ta kwanta a wahalce irin ta sha aiki ta gaji' 'barci take
harda munsharri bakin ta' na bude..
Kare mata
kallo ya yi Idanun sa nakan cinyoyin ta''nan da nan yaji wani wutar sha'awa
takara dibar sa...
Cikin zafin
nama yahaye gadon...
Azabure cikin
barcin ta tashi tana mutsaka fuskar ta..
Ganin baban
Maryam ne tafara zazzare idanu tana kallon yanda yake wasa da boob din ta da
daman suna tsokale masa idanu...
Sarrafa ta yake
yi cikin kwarewa itako tana neman hanyar guduwa ganin zata ba ta masa lokaci ya
sa beyi wata wata ba '' ya fara kokarin isar da sakon shi...
Uban kara ta
saki lokacin daya ratsata ihun ta..
Ya zaburar da
Maman Maryam da Maryam din..
Cikin hanzarin
su suka fito kai tsaye dakin nata suka nufa..
Maman Maryam
sai dube dube take yi a dakin tana neman mijin nata yazo suje dakin yar aikin..
Ganin babu shi
babu labarin sa '' hakan ya sa kai tsaye suka yi dakin nasa.
Koda suka isa
dakin cikin razani take kallon Abban Maryam yanda yake ta sukuwa a kan yar
aikin gidan nasa da batasan inda kanta yake ba..
Wani razananne
Kara ta saki ta ce Gar.. b.... a ta ja sunan bakin ta na rawa..
Maryam daura
hannun ta yi akai tana ihu hade da salati duk abun da suke bemasan sunayi ba ''
dan ya yi nisa 'sossai yanata caccakar yar aiki....
Ganin haka ya
sa aguje Maman Maryam ta dubo ruwa ta kwara musu akai..
Firgit yadawo
hayyacin sa''' cikin tsananin tsoro da fargaba yake kallon ta..
Ya ce ke Maman
Maryam meya kawoki dakin nan...
Bakin ta na
rawa ta ce uban ka ne yakawoni '' Shege Azzalumi maci Amana...
Tashi ya yi Daga
kan yarinyar yadawo yana fuskantar cikin zafin rai da kuma karasa Jin dadin da
beyi ba...
Ya ce Amma dai
yau nalura ke sa karya ce ya zaki biyo ni har dakin Mata ta ina sunnah
Cak Mama
maryam take kallon sa Idanun ta cike da hawaye ta ce dakin Matar ka Ko
kwartuwar ka ankawo yar aiki Amana Kaci Amanar iyayen ta wallahi kotu ce zata
rabamu da kai...
Maryam dake
kuka sossai ta ce Abba meye haka zangani yau wani irin mugun gani ne nayi wa'
iyazubullahi na shiga uku ni Maryam tare da daura hannun ta akai....
Kallon banza
yabi Maryam din da shi ya ce dan uwar ki da kikeyi lesbien da kawayen ki 'na
taba hanaki Ko tona miki Asiri' 'cemiki nake yi ki daina babu kyau' Wannan kuma
auro ta nayi a kauyen nasu.
Tun da uwar ki
nada bakin kishi ya sa nakasa fada mata na ajiye ta amatsayin yar Aiki..
Ita uwar naki
me nake ci da ita na Jin dadi babu' '' bayan zuciyar ta ba ni take so '' mijin
kanwar ta takeso '' kawai ina binta ne kamar wani wawa bawai ban san me nake
bane..
Nashiga
lamarin ne '' dan naga Kina son Abdul Samad bawai dan intayata yaki ba a kan mugun
nufin ta.....
Kallon sa ya
maida a kan Farida da hawayen ta suka kafe ya ce.
Bana cin
haramun wannan mata ta kishiyar ki...
Nasan zakiyi
mamaki ne Ko..
Uhmm nayi haka
ne dan in inbarki kema ki auri muradin naki wanda kika kasa hakuri da rashin sa
'' tun kuruciya da aure na kina bayan sa...
Na Sake ki
saki daya dan Allah kifice mun Daga daki.....
Cikin razani
Maman Maryam ta ce wallahi Garba ba ka isa ba.
Nice za ka saka
acikin daren nan..
Nakama ka kana
cin Amana ta..
Cikin fushi
Yayiwa Maryam tsawa a kan tafita dakin..
Cikin Rawar
jiki tabar dakin tana salati da kuka.....
Ita Ko Maman
Maryam take mata baya tayi.
Suna fita
yarufe kofar gam.
Tare da komawa
kan yar aikin '' yana yayyafa mata ruwa '' cikin kuka ta farka '' tana fadin
wayyo Alhaji zafi zan mutu....
Ba za ki mutu
ba ya furta yana kokarin kaita bandaki.
Nan da nan ya
gasata da ruwan dumi.....
KUKA take yi
iya gaskiyar tana '' tana jin tsanar sa duk da tasan auro ta yayi..
Su Maman
Maryam da Maryam dakin yakoma kamar gidan mutuwa '' kuka suke sossai babu me
rarrashin wani..
Daukar wayar
ta yi dan kiran Fulani ta sanar mata abun da ke faruwa ji ta yi wayar Fulani a
rufe ''
Cikin tsananin
tashin hankali ta dannawa bokar jeji kira '' yana ganin kiran Da ƙyar ya
Daga sakamakon wasu kuraje da suka fiffito masa ajiki '' kuma Aljanun sa ''
sunce sai dai ya je ya roki duk wanda ya zalunta shi ne wannan kurajen za su bar
jikin sa...
Muryan sa cen
kasa ya ce Farida yadai karki zomin da sabuwar aiki yana magana yana sosa jikin
sa..
Ta ce kamarya
kada inzo da sabon aiki bokan jeji ''
Mijina yaci
Amana ta da yar aikina ''
Duk da Azabar
da yake ciki be hanashi dariya ba..
Ya ce uhmm ke
yanzu dan yaci Amanar ki meye abun jin haushi bayan sana'ar ki ce '' shima ya
iya..
Kinga naki
matsalar da sauki dan haka sai anjima..
Ɗif ya
kashe wayar tare da cigaba da tsine mata ya ce da ina aikina lafiya saida in
hana aure '' in kashe aure '' in hana samun haihuwa da sauran su..
Amma tun da nafarayiwa
Salamatu da Farida '' komai ya rinƙa lalacewa..
Kuma harda
zuwan wannan fitsararriyar Matar Samad....
Ita Ko Maman
Maryam kuka takara fashewa da shi hakan ya sa tafara kiran layin yar autar su
Firdausi..
Bugu daya ta
Daga Daga can ɓangaren
ta ce Uwar cin Amana kece yau kika kirani maciya Amana
To bari kiji
jiya na iso gari kuma gobe Yaya auwal da Sani za su zo..
Kadan ya rage
Abban mu be tsine miki dan ma Habiba ta hana shi da yake tanada hakuri..
Wallahi kin
cuce mu kin cuci kanki kijira hukinci daze biyo baya ɗif itama ta kashe wayar '' maman Maryam sake
da baki take kallon Wayar
Wani sabon
kuka takara fashewa da shi me cin rai..
Maryam rungume
ta ta yi suka cigaba da rera kukan tare...
Yarima Samad
yau ya yi ɗare sossai
cikin gari Agajiye yadawo gida '' Ko sashin Mamy beje ba..
Yana zuwa iske
Rahama ya yi ta yi uban tagumi ita kadai tana jiran sa sai kallon agogo take...
Ganin isowar
sa ya sa ta fadada murmushin ta cike da ladabi ta ce welcom Amjad wai Allah ka
gaji Ko tare da karasowa kusa da shi yana kokarin zama..
Eh wallahi
hubby daga ji yau Ayyuka sun mun ca badan nagama ba' 'nadai dawo ne dan inga
maman baby na..
Murmushi ta
sakar masa tare da tashi takawo masa abinci da abun sha..
Ayya Baby na
lemun kadai zansha banajin yunwa yakarashe zancen yana shafa cikin sa..
Bata fuska
Rahama ta yi ta ce uhmm kodai wata tabaka abinci awaje ne'Wunin yau ba ka gida
amma kace ba za ka ci ba..
Murmushi ya yi
yana me jawo ta tafada jikin sa cikin cool voice ya ce wacece zata ba ni abinci
inci inbanda Mamy saike '' uhmm kishirya zuwa jibi zamuje garin iyayen Mamy ''
autar su Mamy tazo '' gobe yayyen ta dasuke saudiya za su iso.
Cike da Farin
ciki Rahama ta ce Allah yakaimu rai da lafiya.
Ameen ya
Allah....
Kako turawa
Yusuf hoton Abban namu kuwa'Kuma nima ina son naga hoton nasa...
OK bantura ba
gwamma da kika tuna mun' ɗauko
wayar ya yi Daga Aljihu ya shiga gallery yana sashin hoton Abban nasu...
Idanun Rahama
nakan wayar sa..
Hoton na
fitowa ya danna a kan hoton' 'ya ce amshi kiga hoton mahaifina yau zanhuta da
tambaya...
. Hannun ta na
rawa ta karbi wayar' '
Zumbur tamike
tsaye cikin Rawar Murya ta ce Baba........
Ta ku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
09069080725
9️⃣2️⃣
Cikin Rawar
murya ta ce Baba salihu '' ina kasamo hoton sa tana zazzare idanu ''
Maida kallon
ta ta yi a kan Samad dake sake da baki yana kallon ta ''
Ya ce ina kika
sanshi wannan shi ne mahaifina wanda kike da buri da sha'awar ganin hoton sa..
Rahama cikin
kidima 'nan da nan tunanin ta ya hargitse ta ce wannan bawan Allah nasan shi' Wallahi
shi ne inma bashi bane suna mugun kama..
Shi ne wanda ya
ce yana nemawa dan sa aurena da yatafi dauko dan nasa bedawo ba' 'sai Abby ya
ce Adamu yaturo tun da da shi nake tsayawa.....
Yarima Samad
da gabadaya yagama gigicewa ya ce Rahamatullah ki nutsu kiban labarin wannan
baba salihu da kikace 'sanin kanki ne Mahaifina sunan sa Salihu' Wannan yana
nufin shi ne dai wanda kike magana akai my Hubby....
Dafata ya yi suna
fuskantar juna ya ce Rahama' Kinkosan shekaru nawa' 'nadauka ina neman wannan
bawan Allah' Kigayamin yana ina yanzu dan Allah rokeki' '
Rahama cikin
tsananin damuwa ta ce gadi fa yake yi agidan namu tsawon shekaru biyar da suka
wuce inaga yazo gidan ina yar karamata..
Ban san inda
suka hadu da Abby ba' 'amma Ada a massalaci yake kwana' ɗaga baya yadawo gadi gidan namu...
Sai dai inajin
Abby na yawan ce masa yakamata yakama sana'a amma ya Noke ya ce beson kowace
aiki sai na gadi....
Nice nan nasa
masa baba salihu ka sancewa naga yara da manya kowa salihu yake ce masa babu
girma...
Yanda suka ji
ina ambatar sunan sa da baba salihu sai kowa ya ɗauka..
Baba Salihu
yana daya Daga cikin mutane da nake kauna Ko Ada cen '' sau da dama Salma zata
min Sharri shi ne yake kare ni ya ce bahaka zancen yake ba...
Badan Shiba
dukan tsiya zansha a hannun mama..
Amjad kana
nufin wannan shi ne mahaifin naka '' kana nufin shugaban Adalai ya yi basaja ya
zauna agidan namu...
. ba mu kara
ganin sa tun da bikin namu ya saura sati biyu....
Yarima Samad
ya shiga shock sossai cike da mamaki da Al'ajabi ya ce kenan wannan mutumin ɗana gani A massalacin
unguwar ku '' bayan mun idar da sallah yanata zuba uban gudu harna bi bayan sa
ashe shi ne..
Kuka yake
sossai ya ce haba Abba na ya zakamin haka '' bayan ka san duk duniya insun
yarda ka aika ta ni ba zan taba yarda ka aikata ba.....
Kana gudun mu
hada idanu nida kai Abba why ya zakayi haka..
Rahama soma
rarrashin sa ta yi ta ce '' katuna mama ta ce kamar ta taba ganin hoton ka a
dakin nasa '' dukan mu 'mun dauka kila kama ce bakai bane..
Wannan ke
tabbatar mana da hoton ku yake yawo yana matukar son ku da kaunar ku...
Wannan abun daya
faru da kunya wallahi ashe amsa sharri kuma kowa ya ɗauka koni ce ba zan so mu hadu da kai adaidai
wannan lokacin ba....
Yanzu meye
Mafita Amjad '' maza katurawa Yusuf dan Sani Yaro hoton nasa ze maka binciken
inda yake....
Kuma InshAllah
Daga yau zanfara Tsayuwar ɗare
a kan sa '' ina adua duk inda yake zeji beda nutsuwa inba yazo gare ku ba kar
ka damu Amjad dîna..
Rungumeta ya
yi sossai yana kiss dinta a goshi ya ce Rahama ke Rahma ce agareni nagode da
kulawa my life.
Tare zamu
ringa Tsayuwar daren nan....
Yanzu bara
kiga inturawa Yusuf hoton..
Babu ba ta lokaci
ya tura hoton iske Yusuf ya yi baya online '' hakan ya sa ya yi masa sakon voice
tare da fada masa yana son binciken nan umergency..
Sossai Rahama
ta rinƙa
kawo fira masu Jan hankali wanda ya sa ya dan rage damuwar da yake ciki
Kashe Gari..
Mai Martaba kiran
Mamy ya yi ita da Ahmad da Samad da Marwan da Abban sa..
Harda mama karama..
Saida ya fara
da bawa Mamy hakuri a kan abun da ya faru a baya '' ya ce dan Allah su yafe
masa..
Mamy ta ce
Sarki bakayi komai ba illa a rashin sani..
Cewa ya yi yatara
su ne a kan yanda za ayi adawo da Salihu gida..
Samad ya ce
Sarki me ran karfe nayi magana da wani shahararren sojan nan mataimakin
shugaban kasa a harkan tsaro..
Ya ce inba nan
zuwa gobe InshAllah ze gaya mana inda yake...
MashaAllah
MashaAllah Sarki ya furta cike da Jin dadi ya ce Allah ya bayyana shi ''
wallahi nakosa inga ɗana
'' ban san da wani idanu zan kalle sa ba...
Sannan ina son
wannan matar nan Farida '' a je akamo ta akaita station ba na son tasamu labari
ta gudu...
Habiba kiyi
hakuri nasan ba za ki ji dadi ba tun da yar uwar ki ce..
Amma dole ta
fuskanci hukuncin cin Amana har cikin masarauta ba Daga waje ba..
Da ba da shawara
a kan buga masa makami akai wanda da rai yana kusa yana iya zama ajalin sa...
Mamy cikin
sanyin Murya ta ce A'a Sarki kar ka damu koni ce nayi laifi akamani.....
Mama karama ta
ce gaskiya Habiba ke ya ce kuma ta gari '' wace mata ce za a hana ta bin mijin
ta kuma ta zauna babu ita awannan zamanin.
Shima Salihu
ya yi kokari da ya yi biyayya yabar ta.... Allah ya yi muku Albarka..
Da ameen kowa
ya amsa...
Abban Marwan ya
ce aini nafi kowa laifi nida sai abun da Fulani ta ce shinake yi '' tana juyani
gashi tasa na yi wa dan uwana rashin mutunci...
Ahmad cikin
kwantar da murya ya ce Abban Marwan ance rana dubu ta barawo rana daya tame
kaya...
Yarima Samad ya
ce haka ne kanina..
Marwan cikin
kuka ya ce Samad ka yafemun yanda na ringa diban kudaden ka''ina bawa Fulani
duk a zatona daidai nake aikatawa duk da wani lokacin inajin ba dadi araina...
Yarima ya ce kar
ka damu Marwan kaima ba yin kanka bane' ''
Sarki ne ya yi
gyaran Murya ya ce sai magana ta gaba..
Zancen auren
Ahmad yataso nan da kwana 12.
Dan haka na
gama hada lefe '' komai sashin nasa duk angyara shi...
Sannan ina son
ahada auren ɗana
khadija..
Samad cikin
zazzare idanu ya ce Khadija kuma Ah Ah nifa bayanzu zamu aurar da ita ba..
Sarki ya ce to
uban me zatayi maka agida ne...
. Ahmad ya ce
kaide Sarki kacika rigima inbanda abunka duka nawa Khadija take kuma wai waye
za ka ba ta muji inbe mana ba Alkur'an ba za a daura auren yanzu ba sai nan
gaba intayi hankali......
Abban Marwan
saida ya murmusa ya ce kam buhu lallai ma...
.
Sarki dake
sauraren su ya ce kungama Ko...
Suka eh..
Ya ce uhmm
daman Adamu dan Ambassador libya Abdullahi shi ne nabawa khadija..
Kun san meyasa
nayi haka..
Dukan su suka
Girgiza kai da A'a suna sauraren shi...
Kunga dai abun
da ya faru wajen auren Adamu yaro ya birkice kaman mai Aljanu kuma nayi Imani
baya cikin hayyacin sa ya yi haka..
Shi ya sa
bayan biki da Mahaifin sa ya sauko Daga dokin fushi nace masa kawai abashi
khadija kanwar Samad din '' tun da shi ya Auri muradin sa...
Hakan zekara
mana karfin zumunci..
Yarima Samad ya
ce ALLAHU Akbar kabiran.
Sarki sake da
baki ya ce ka ga Yarima banson iya Shege me kake nufi ne...
Mamy da Mama
karama dariya suke ta kasa kasa..
Yarima gyaran
Murya ya yi ya ce tome laifina kayi abun da Alkhairi na jinjina maka...
Cewa kayi
zumunci za ka hada '' naga aiga Marwan nan shi ne inka hada kayi auren zumunci
wancen kam ba auren zumunci bane auren hadi ne irin wanda kamun...
Abban Marwan
sossai ya ɗara ya ce yau
dai naga Sarki da Yarima a fili mun ganku a rana..
Ahmad ya ce
Abban marwan kabar shi ya ba shi Amsa muji me ze ce....
Sarki sake da
baki ya ce Ahmad kaci uban naka kaida Samad din yan rainin hankali '' to na ji auren
hadi zanyi '' kai Samad ɗanayi
maka auren hadi ai kafi kowa samun Albarka..
Yarima Samad ya
ce OK na ji tun da bakada amsa ta..
Badai kaba
Adamu ba to Allah ya sa Alkhairi.
Tabe baki ya
yi ya ce inafatan ka gama jawabin naka ni zan tafi...
Mamy cikin
fada ta ce haba Yarima ya ana magana za ka tashi..
Komawa ya yi ya
zauna ya ce yi hakuri Mamy wallahi barci nakeji shi ya sa bana fahimta bayanin
sa sossai...
Sarki ya ce na
ji dai Yarima auren kuma ya badu '' kace kishi kake da Adamu.
Yarima Samad
Dago kai ya yi yana kallon Sarki tare da nazartan kalaman sa ya yi murmushi ya
ce ikon Allah indai haka zakabi da zancena tona amince dari bisa dari ya auri
khadija kaika san Inde banson auren nan bame yuwa bane kuma d kake cewa kishi a
kan me zanyi kishi da shi bayan '' be kasa ni ba a soyayya....
Sarki ya ce
wayasani to..
Sossai suka yi
tsare tsare yanda za a gudanar da shagalin bikin.
Nan take Sarki
yakira Ambassador Abdullahi ya sanar masa '' ga lokacin da ake bukatar a kawo
lefe..
Sossai
Ambassador ya yi murna ya ce InshAllah muma jibi zamu dawo dukan mu Daga
england..
Amma yakamata
ahada Adamu da yarinyar daze aura tun kafun ranar auren sudan Saba...
Sarki ya ce
InshAllah za ayi haka yau za a ba ta waya kuma za a bashi lambar ta...
Daga haka suka
yi sallama..
Hatta ankon za
su yi ranar bikin da wanda za a raba wa bayi kyauta da jama'ar cikin gari duka
an tsara komai..
Sarki ya ce ni
dai kam ba zani daurin aure Kano ba... Zan tsaya anan ayi na khadija gaba na...
Kema Mamy ba
za ki je ba..
Mama Karama ce
zata je ta wakilci Ahmad ita da Abban Marwan ga yarima Samaɗ' kuma nasan yan uwan
mahaifiyar ku duk za su tafi kanon gara araba biyu..
Kinga Mamy
zaki zauna ku amshi suruka..
Kuma kibada
Yar ki..
Mamy ta ce haka
ne Allah ya sanya Alkhairi ya nuna mana lokacin lafiya da ameen kowa ya
amsa....
Wuni Ranar Yusuf
Sani yaro
bincike ya
wuni sossai a kan Sarkin Adalai '' amma ɗuk
kasar daya duba babu shi babu me kama dashi...
Hakan ya sa ya
shiga nauyin kasashen french dan yagani Ko ze dace..
Yabarshi a kan
gobe tun da Asuba zefara gudanar da binciken sa kafun lokacin daya diba
yacika....
Kusan Karfe
biyar na yamma Dakarun sojoji suka ce gidan Maman Maryam..
Iske Abban
maryam suka yi waje yana waya..
Cike da mamaki
yake kallon motar sojoji ya yi parking kofar gidan nasa...
Kashe wayar da
yake yi ya yi yadawo da hankalin sa a kan su dasuke durowa Daga motar sa..
Babban cikin
su ne ya karaso gaban sa tareda cire madubin glas dake Idanun sa '' ya ce
sunana Sulaiman gaba tare da nuna masa ID Card dinsa..
Munzo ne mu
tafi da Hajiya Farida a kan zargin ta
Da ake yi
tanada sa hannu wajen yiwa Shugaban Adalai sharri in kuna neman karin bayani
kuzo office din mu..
Yanzu ina take
ne...
Abban Maryam
bakin sa na rawa ya ce tana cikin gidan ni Mijin ta ne..
Dan Allah
kubari mu sasanta '' babban nasu ya ce zancen banza ka ga wasa a tattare damu
ne..
Maza kayi mana
jagora mu je ciki...
Babu musu ya
bude gidan jikin sa na rawa yashigar dasu har cikin gidan...
Koda suka isa
Falon iske Maman Maryam suka yi tana dukan Yar aiki kishiyar ta..
Yarinya tana
ihu tana fadin wallahi hajiya zan bar miki gidan in koma kauyen mu...
Sake da baki
sojojin suke kallon junan su suna kada kai...
Ganin ba ta gansu
ba.
Babban cikin
su ya ce hajiya ayi mata rai hakanan Ko..
Cak ta Dago
kai cikin gigita take kallon sojojin da suka kewaye dakin nata...
Sakin yar
aikin ta yi bakin ta na rawa ta ce ku kuma Daga ina haka....
Babban cikin
su ya ce ina fatan kece hajiya Farida..
Kada kai ta yi
Alamun ita ce......
Hajiya munzo
mu tafi dake Umarni ne Daga Sarkin kwatano...
.
Cikin Rawar
murya ta ce what.............
Taku Har
kullum Kyauta Daga Allah9️⃣3️⃣
Ta ce what
laifin me nayi muku..
Angwa suka
nuna mata cikin tsawa ya ce wannan ma dukar da kike wa yar aikin naki shima ya
shiga laifi duk da bamusan me ta yi ba amma hakan ya nuna duk cikin zalunci ne
wannan dukar da ake mata....
KUKA tasoma
tana kallon mijin nata ta ce Abban maryam dan Allah kace wani abu mana za su tafi
dani..
Abban maryam ya
ce Farida mezan yi musu bayan sunce sai sun tafi dake kije kawai zan zo gashi
Maryam ba ta gida inta dawo zamu zo tare....
Hijab din ta
ya shiga daki ya dauko mata tareda mika mata '' tasaka tana kuka ta ce na ba ni
wayyo ni Farida Nice za a tafi dani gidan Maza...
Basu ba ta lokaci
ba wajen sa mata ankwa ba hakan ya sa nan da nan suka jata har cikin motar
su....
....
Fulani tana
zaune cikin dakin nata gangami yazo mata da abinci' 'hade da ruwa bakin ta na
rawa ta ce nagode gangami saura lemu....
Tsawa ya daka
mata ya ce shegiya munafuka ai ana ba ni lemu inbaki shanyewa nake' ''
Badan ba a ba
ni dokar zaneki ba dayau kinsha bulala..
Sossai take
kuka ta ce waini yar kwalisa Nice ke kwana awannan dakin...
Gangami ya
bushe da dariya harda rike ciki.
Ya ce sannu
yar kwalisa '' bari ayi shari'a kigani inhar kotu ta daure ki..
Alkur'an saikin
gwammance da nan fiye da cen shasha kawai yafice yabar ta yana wake waken sa
hade da fito..
Yarima Samad
mikawa Khadija wayar ta daya kwace ya yi tana ta murna ya ce uhmm yarinya
bakisan aure zakiyi bane shi ya sa kike kaudi...
Afili kuwa
fadi yake yawwa khadija ta '' zauna muyi magana....
Zama ta yi tana
fuskantar shi ta ce yaya inajin ka.....
Ya ce khadija
nasan kin san kaddara mekyau Ko mara kyau..
Khadija cikin
sanyin murya ta ce nasani yaya tun da malamin mu '' yana gaya mana...
Jawo ta ya yi jikin
sa ya ce yawwa yar ƙanwata..
Kin san yayan
ki Ahmed zeyi aure kuma Asiya kawar Rahama ze aura..
Kekuma Adamu
zaki aura dan abokin Sarki ambassador libya....
Arazane ta
Dago kai tana kallon sa ta maimaita aure a fili.
Make kafada ta
yi cikin kuka ta ce wayyo ni khadija yaushe nakai aure '' yaya kubari nakara
girma wayyo Mamy banaso..
Kallon ta yake
yana Murmushi da shikadai ya san ma'anar sa '' ya ce uhmm dijat dîna auren babu
fashi banine na hadaba tsoho me ran karfe ne '' Inkinada ja je ki same shi.
Kawo wayar
insaka miki lambar Adamun '' zan kira shi ince kinbude waya 'yakira ki' Wallahi
inkika masa rashin kunya zaki sani..
. Khadija
sossai take kuka wai ita ce za a ma aure kuma auren dole' 'mijin maci Amana'
'maganar zuci take ita kadai..
Ganin haka
Yarima Samad tashi ya ce kinga zanshiga ciki ina Antyn ki..
Tana ciki ta
ba shi Amsa atakaice koda ya shiga dakin iske ta ya yi zaune tana karatun
Alkur'an ahankali muryan ta ke fita..
Samun wuri ya
yi ya zauna kusa da ita...
Ganin zuwan sa
ya sa tana kai karshen aya '' tayanke karatun '' Murmushi ta sakar masa mai
sanya shi a gajimare...
Ya ce hubby
karatu ake '' nazo bita..
Dariya ta yi saida
fararen hakoranta suka bayyana '' habawa '' ai sai dai ka koya mun shugabana
takarashe zancen tana kokarin tashi tsaye..
Kusan tare
suka tashi '' cikin kallon da yake binta da shi 'mai wuyar fassara ya ce za a
ba ni Ko..
Uhmm Amjad wai
kai ba za ka barni in huta bane' 'ina fama da danka A'ciki na' kaikuma uba ka
hanani sakat..
Uhmm Rahama ta
ai duba lafiyar dan namu zanyi kema kin sani..
A'a ban sani
be cewar dan haka ka kyaleni barci nakeji kace gobe zamu garin su Mamy sokake
in tashi da gajiya ne.....
Uhmm Hubby duk
wayon naki saifa nayi haka kurum yau kwana uku kenan ana jamin rai....
Dariya take ta
ce wayyo Mamy zoki dauke ni a dakin Amjad 'sai ya cinyeni tass ya ajiye
kashi....
Dariya ta ba
shi harda rike ciki ya ce uhmm watau Mata ta ta yi baki' 'har kin iya fadin
cinye wa...
Hakadai yajata
suka yita hira be mata komai ba. amma tasha murza' ɗan yana kiyaye abun da likita ya ce a kan barin
ta' tahuta har cikin jikin ta ya yi kwari....
Kashe Gari....
Tun da sassafe
bayan yadawo Daga Sallah Asuba kiran Yusuf ya shigo wayar sa...
Yana ganin
Yusuf ne cikin hanzari ya Daga...
Daga can ɓangaren ya ce' '' Yarima
Samad na samo inda mahaifin ka yake yana kasar Gabon..
Cikin ruɗewa Samad yake maimaita
Gabon '' ya ce tome yakai sa wannan kasar kuma a Gabon din wani unguwa
yake.....
Nan da nan
Yusuf ya tura masa duk wani bayanai na gidan da yake ciki.....
Ya ce masa a
yau dinna za su je daukar Saratu amma Yaran sa '' ze tura ''
Yarima Samad
cike dajin dadi ya ce ina son a ajiye mun ita a kano innazo bikin Surukina da
Kanina zan tare da ita zamu tafi kwatanon ka ga shari'a ze tafi daidai
Yusuf ya ce kar
ka damu yau InshAllah za a je a dauko ta kuma zamu ajiye maka ita a kano..
Godiya Yarima
Samad ya shiga yiwa yusuf tare da masa Adua Allah yajikan baban sa da wan sa da
magabata '' yusuf ameen ameen ya furta Daga haka suka yi sallama..
************************
Kano
Dakarun sojoji
mota daya suka tafi unguwar rijiyar lemu '' gidan wani Alhaji mai naira '' nan
gidan Saratu take zaune basu ba ta lokaci ba..
Kai tsaye suka
nufi gidan '' bindigogi da suka nunawa yan cikin gidan ba ƙaramin
razana suka yi ba..
Babban su
cikin zazzare idanu ya ce Ina Saratu take..
Baki narawa
matar megidan ta ce tana kwance daki tana barci......
Cikin tsawa ya
ce ina dakin yake ?
Nuna masa
dakin ta yi da yatsa hakan ya sa su uku suka nufi dakin '' hankada kofar suka
yi da kafafun su '' koda suka Shiga dakin sai dube dube suke suka hangota
kwance tana buga uban munsharri bakin nata abude tama mance inda kanta yake...
Da bindiga
suka tashe ta Arazane ta tashi tana salati ganin sojoji har uku a kanta kokarin
ta yi magana take..
Babban ya ce
kitashi mu je inmunje cen kin karasa barcin naki...
Cikin Rawar
murya ta sauko Daga kan gadon tana neman hijab din ta..
Ta ce dan
Allah menayi muku ne..
Anturo mu ne
Daga shugaban sojoji Yusuf Sani Yaro...
Jin anbanci
yusuf hankalin ya yi mugun tashi tasan case din baƙarami bane Sam ta mance
da batun Masarauta na neman ta '' shi ya sa batakawo Ko su bane...
Sata gaba suka
yi 'cikin izza suke suna mata hanyar da zatabi..
Matar megidan
baki na rawa ta ce ranka ya dade inane zaku kaita in mun tashi..
Babban cikin
su ya ce kika zo sunan ki sorry zamu hada dake mu rufe..
Jin hakan ya
sa ta ja bakin ta ta yi shiru suna kallo suka tafi da Saratu 'cike da izza da
takama......
Unguwar makil
yake da jama'a ganin yanda suka jefa saratu cikin mota..
Gulma ya barke
a unguwar' Wasu na fadin wannan matar Kodai yar damfara ce kullum dai sai dai
muka tana fita asirrince'' kuma sai ɗare.
Na kusa dasu ya
ce Falyakul khairan auliyas mut.
Mudai bamusan
dalili kamata ba Koma daidai mene ne Allah yakyauta da Ameen kowa ya amsa..
Suna kallo
motar tabar unguwar.
Ayau ne su
Mama da anty suka tare sabon gidan nasu.
Sabon
fourniture sheik ya yi masu..
Yan uwan da a
bokan arziki kowa yazo yana ta kallon gidan' 'sake da baki ake ta yaba kyau da tsaruwan
gidan...
Mama ta cewa
Aminiyar ta kinga Sheik yanzu ya fara sakar mana mara muyi fitsari' 'ai wannan
gidan shi ne gidan sa na farko daya fara siya a' kano..
Amma ya ajiye
mu acen gidan Duk da cen din ma babu laifi....
Aminiyar mama ta
ce kedai Aisha kibar zancen wani gida'' ki dawo da hankalin ki kusa' auren
sheik befi saura sati daya ba za a ce me kika shirya koko kin zuba idanune wata
takara zuwa ta kwace miki miji...
Daga Sama ta
jiyo muryan Sheik na Fadi ba idanu ta zuba ba har kafa..
Ahankali yake
taku har ya iso gaban nasu..
Cikin hada
Fuska ya ce uhmm ke Suwaiba kike Ko Sharifa nakasa haddace sunan ki...
To bari kiji
duk abun da kuke ina sane gidan yan bori da gidan malamai duk ina sane Kallon
ku nake ita Aysha da yake sakarya ce bagidajiya takasa gane me son ta..
Yo mai son ta
mana.
Taya kullum
kike barin gidan ki kina zuwa tarwatsa mun nawa...
Sossai Suwaiba
ta tsoro ta ganin yanda Sheik yakoma kamar wanda ze buge ta..
Wallahi Daga
yau na rabaki da Aysha mata ta kuma inna kara ganin kafafun Ki nan gidan uhmm
basai na fada ba..
Kekuma Aysha
wallahi kika kara zuwa gidan ta koda satar hanya ne inhar nasani nidake har
Abada mun rabu inbanda jahilci da biye biye ake samun kan miji '' kiyi biyayya
kigani in baki rabauta ba..
Kullum kina
yawo da zani daban riga daban '' babu kitson kirki bare burgewa '' kullum babu
gyara ahaka kike son maganin bokan naku ya yi aiki...
Sannan kina
maganar cikin mata ta Sa'adatu zaku zubar Ko uhmm tun da kune kuka busa musu
rai to sai ku kashe su kar nake kallon ku..
. Aysha ina
hakuri dake bakya ganewa wannan auren Saboda ke nayarda zanyi shi da inajin
dadin zama dake tabbas babu auren da zan kara '' itako Anty ba ta iyawa ita
kadai kekuma kinyi sake dan Allah gyara kanki nace ki gyara kanki...
Sassaita nutsuwar
sa ya yi yana kallon Suwaiba ya ce yanzu kina iya tafiya Ko na sallame ki babu
ke babu indo....
Cike da Jin
kunya Suwaiba ta rinƙa rabawa ta gefe gefen gidan tafita tana fadin amma mutumin nan
ya shammace ni..
Millions daya
kacal na samu hannu aisha na so insamu suka yi goman..
Amma bakomai
dankoli yaci riba tafada cike da takaicin rabasu da sheik yayi...
Tana Fita
yadawo da kallon sa a kan Mama da ta yi kasa da kai ya ce ke indo ina rabaki da
kawayen banza bakyaji Ko uhmm ta yaro kyau take ba ta karko..
Yana fita
gidan kai tsaye kofar gida ya je ya samu waje yazauna tare da bude WhatsApp
dinsa..
Ganin Sakon
hassana ya shigo..
Ta rubuta..
Haba Masoyina
uban yaya na muna hira najika shiru uhmm my love kaifa nake jira kayi shiru
kafa San auren namu yau saura sati uhmm...
Murmushi ya yi
yana karanta sakon ta...
Voice ya yi mata
ya ce habibity na yi hakuri na dan je gun uwargida ne.
Kin san ku
Mata '' saida kulawa...
Tabe baki ta
yi tare da rubuta kace kana gun Babban antin tamu yaushe za ka hadani da ita...
Sheik ya
rubuta kibari dai kizo yanzu kanta yadau zafi anata hada hadan tarbon Ki
gimbiya ta..
Sossai ta dara
Daga kwancen da take '' ta ce masoyina ya ce naam habibity inajin ki...
Nifa in ankawo
ni gidan naka ka san me..
Ya ce A'a
saikin fada habibity na..
Ni dai ranar
dazan tare dakin angona uhmm sujjada zanyiwa Allah dan godiya ingayamaka sati
daya za ka dauka ba ka je aiki ba...
Shafa gemun sa
ya yi yana murmushi ya ce habibity na inban je aiki ba sokike su Sa'adatu suce
dadin angon ci ne yahana...
To mene ne da
sun fada babu komai fa ka san wata bazawarar tafi budurwar wallahi...
Sossai ya dara
ya ce kash habibty lokacin Sallah ya yi zanje ba da Sallah saide zuwa ɗare bayan isha'i kafun na
kwanta zamu hade yau fa dakin Uwargida nake dakin nata ba a waya fa..
Sossai ta dara
ta ce ayya nima nakusa mallakar ka ka ga babu me hana Jin ka ranar kwana na...
Sheik ya ce haka
ne habibty bye sai anjima inmun hadu...
Mama Sheik na
fita tarusa uban kuka ta ce shi ke nan yarabani da suwaiba kuma ya san sirrina
yazanyi ne...
Uhmm Wallahi
zanfara adu'a ina hana idanuna barci a kan Allah ya tarwatsa wannan auren
itakuma Sa'adatu Allah ya sa kada ta haihu lafiya........
Anty ce suke
saukowa Daga sama ita da yan uwan ta cike da farin ciki ta ce Kunga ga Maman
salma cen ku gaisa..
Cike da farin
ciki suka taho gun mama '' yayar anty da kanwar ta suka ce Maman salma inawuni
dafatan kuntare lafiya to Allah ya sa kundawo Asa'a..
Mama dariyan
dole ta yi ta ce Ameen ameen har zaku wuce ne..
Suka ce eh
zamu tafi munga gida ya yi kyau sossai musamman sashin naki ya fi daukar
idanu..
Mama ta ce kai
haba wai dagaske kike hindatu..
Kwarai kuwa
wllh dagsk muke suka karashe zancen tare da fita...
Mama bakinta
awashe sun yabi sashin nata ta ce Allah yakaiku gida lafiya...
Cike da mamaki
Anty ta yi Jin furucin Mama duk zaman da suka yi ba ta tabajin ta yi adua
mekyau a kanta Ko yan uwan ta ba...
AMEEEN dukan
su suka amsa.......
*************************
Salma zaune
take tana shirin zataje gidan iyayen ta..
Kai tsaye
motar da Al'amin yasiye mata ta bude ta shiga.
Mai gadi bude
mata get ya yi cike da takama take tuki tare da hawa kan titi... Tuki take tana
kada kai cike dajin dadi wai yau ita ce da motar kanta uhmm nasan Matar Samad ba
ta da mota... Uhmm innaje ma zanje gun Abby in karbi kudin da shegiyar ta ce
abani Ko mai na rinƙa sawa mota ta....
Asiya tsaf
tashirya itama dan zuwa sabon gidan su Mama' ita da mahaifiyar ta zuwan su ya
yi daidai da isowar Salma sake da baki suke kallon wacece wannan tazo a bakar
mota '' duk da ba sa gani sossai amma sun tabbatar wannan tukin mace ce..
Asiya sake da
baki take kallon Salma dake kokarin fitowa cikin motar tana sanye cikin doguwar
shadda gezner ta yafa farin gyale hannun rike da ash din jaka da takalmi hash
mai tsini' simple makeup ta yi hakan ya sa ta yi kyau ta yi fresh.
Asiya fuskar
ta dauke da mamaki ta ce Kai Salma kece
Rufe motar
nata ta yi tare da karasowa kusa dasu '' ta ce Uhmm anty Asiya kenan ke bakisan
nayi nisa bane nawuce raini ba..
Asiya ta ce
uhmm Salma ba ni labari arziki mijin naki yayi..
Salma tabe
baki ta yi Anty Asiya ai nima dawowa nayi na iske Al'amin ya yi Arziki..
Asiya ta ce
Kai salma wani irin aiki Al'amin ya samu ne...
Salma ta ce
inaruwana da aikin da yake yi ni dai kawai daula muka samu '' kudai yan bakin
ciki bakwa ganin mutum yaci gaba saiku ringa neman mugun suna suka daura
masa...
Asiya ta ce
haba Salma meye abun bakin ciki dannace meye sana'ar Al'amin '' kina matar sa
bakisan aikin sa ba mekenan akai..
Allah yabaki
hakuri Salma Allah yakara arziki da daukaka..
Ameen ta furta
inda gaske kike dan keda Rahama mugun hali gare ku..
Asiya barin
Salma ta yi tana tabe baki tare da yin cikin gidan tabi sahun maman ta...
Salma na
kokarin shiga cikin gidan...
Sheik ya dakatar
da ita tahanyar ihun kiran ta..
Cak ta tsaya
tana kallon sa harya karaso..
Ya ce yanzu
Salma gyale kika koma yafawa ina hijab dinki Ko ba ki da sune kar inkara ganin
ki cikin wannan shigar ta gyale..
Naji labari
acikin gari wai mijin naki ya sai gida da mota surutu ake mun ba a San sana'ar
sa ba..
Ba za ki shiga
mun gida ba harsai kin fadamun meye sana'ar da mijin naki yake...
Maza juya ki
wuce inajin Asiya tana miki magana harda zagin ta dan ta gayamiki gaskiya to
badaniba ba.....
Cikin kunan
rai da tafasar zuciya salma ta juya tana kuka ahaka ta ja motar tata tawuce
gidan nata..
******************
England
Adamu ne zaune
yana chattin da khadija wacce Da ƙyar take maido masa reply..
Ya ce Amarya
ta yakike ygida ya antyn ki Rahama da yayan ki Samad...
Lafiya lau
suke ta ba shi Amsa atakaice...
Adamsy cike da
Jin dadi tamasa reply ya ce yawwa Amarya nan da kwana uku zamu zo kwatanon nida
Abba na...
Lefe kuma jibi
yan uwana za su kai sai su jira sai andaura sai su koma...
Shiru ta yi tarasa
mezata ce masa...
Khadija ya
furta hakan ya sa ta kara maida hankali a kan wayar ta ce naam...
Wai naga kin
kasa sakin jikin ki dani kona miki laifine dan Allah ki gayamin...
Cikin yin kasa
da murya ta ce to bakai bane wanda ya fasa auren.........
Taku har kullum
kyauta Daga Allah9️⃣4️⃣
09069080725
Toba kai bane
wanda yafasa auren anty Rahama ba '' sokake in saki jiki da kai nima kazo kace
kafasa Ko.
Sake da baki
Adamu yake sauraron ta ikon Allah ya furta afili sannan ya ce haba khadija waye
besan kaddara ba..
Haka Allah
yatsara tun farko niba mijin ta ne bane '' ki fahimceni kuskure ne yariga ya
faru 'badaman ayi tariya bare a gyara shi..
Shiru khadijat
ta yi tana sauraren sa' 'cikin takaita zancen ta ce Allah yakyauta..
Ameen ya Amsa
mata kokarin yajawo hankalin nata yake dan ta sake da shi sossai..
Haka dai ya
lallabata suna hira.......
Yarima Samad
makale da Rahama a la dole shi ne ze saka mata kayan ta kala biyu da zata saka
a jakar ta..
Uhmm Amjad
dîna kabari na saka mana '' ka ga kwana zamuyi Ko..
Haba hubby na
ni ne nadace da in zaba miki kayan da zaki saka.
Cike da mamaki
take kallon sa ya fiddo mata tare da shirya su tsaf a jakar ta..
Cikin
marairaice fuska ya ce baby na adan taimakamin na kwana biyu ban taba ba...
Rike da baki
take kallon yanda yakoma kaman ƙaramin yaro yana kokarin cire mata riga..
Kasa hanashi
ta yi '' ganin haka ya sa yakara azzama wajen isar da sakon shi..
Awannan ranar
dai ahankali ya gudanar da komai wai kada babyn shi ya wahala..
Rahama kam
'sossai hakan da ya yi ya mata dadi' kusan a tare suka yi wanka.
Bayan sun fito
'suka sake yin sabon shiri' inda Rahama ta sanya babban leshi na malaysia har
wani shaining yake.
Dinki riga da
zani sossai ya karbe ta ka sancewa Milk color..
Shima Yarima
Samad irin wannan less din ya sa an yi masa aiki da Milk din zare rigar iya
gwuiwar sa ta tsaya sossai shigar ta masa kyau ga hular sa yadaura Milƙ'
cikin hanzari ya sako takalmin sa haf cover tare saka farin glass..
Sake da baki
Rahama ke kallon sa ta ce wannan kwaliyar fa '' yau shirin yarbawa kayi..
Mukayi dai
zaki ce yabata amsa a atakaice.
To na ji mukayi
amma dai nasan harda yan mata za ka nunawa wannan adon naka...
Uhmm Keko
Hubby yan mata me za su yi da mijin naki '' wanda Sam ya makance a kan son ki.
Ko sun shigo
wahala za su sha ɗan
kwalliya bazata biya kudin sabulu ba.
Tabe baki ta
yi tana dariya uhmm Amjad anya kuwa' kana samun sabuwa cewa zakayi ai aure
kaddara ce waya mutu Waya dawo..
Hubby na kenan
tun da Abbana beyiwa Mamy kishiya ba' Kema haka ba zan miki ba...
Kai kai ni dai
Amjad banson daukan AlKawari da ba za ka iya cikawaba..
Nifa inma
auren za ka kara kasamo mai hankali wacce zamu zauna lafiya' ɗan ma dai Ahmad ya yi mana
shigo ba zurfi Asiya na so inbaka ka aura' yanda zamu hade nida Aminiyata Ko
bayan raina inada tabbaacin Asiya zata rike mun yayana bisa Amana...
Dariya ya
sakar mata tare da lakacar mata hanci 'uhmm hubby na Keko'' mubar zancen Allah
babu ke babu kishiya tun da na ji m'a kinaso..
Dariya ta
fashe da shi ta ce au kana nufin daman mata dan suna nuna basu son kishiya shi
ya sa ake musu..
Eh mana dan
muga iya gudun ruwan su'' da kuma mu ragewa kan mu wahala..
Sossai ta dara
hakan ya sa ya yi Murmushi ya ce wife naci gari fa kin san kalmar da kike min
rowa kuwa..
Girgiza kai ta yi ta ce A'a maigida na saika
fada..
Baki taba furta mun kalmar je taime 💜
Ma'ana ilove you..
Rufe fuskar ta
ta yi da tafukan hannayen ta ta ce uhmm kaima ai ba ka taba gayamin ba' saini
ce mara aji..
Haba Hubby me abun rashin aji anan bayan
'nasan komai tattare dake ina kwanciya dake..
Sake da baki
Rahama take kallon sa ta ce uhmm nifa haryanzu ban yarda kana sona ba..
Kaga mu je inmun
dawo mun karasa zancen' '
Please hubby matso kusa dani ki gayamin kalma
me tsada tare da rufe idanun sa' 'hannayen sa ya bude Alamun tazo' ganin haka
ya sa tafi ce zuwa falo.
Koda ta fito
falon iske khadija batanan Faruk da Aminu ta tarar zaune suna jiran sa....
Faruk bakin sa dauke da Murmushi ya ce Amarya
bakya laifi ina Yarima yake ne..
Murmushi ta sakar musu tare da gaishe dasu.
Uhmm yana ciki
tafada atakaice tare da zuwa sashin nata..
Ganin tafita
zuwa ɓangaren ta ya sa
Faruk fadin kai Aminu bara inleka wannan dan Iska shi kadai ake jira yana ba ta
mana lokaci...
Koda ya shiga dakin iske Samad ya yi Idanun sa
arufe yana fadin haba My Rahama kizo ki rungume ni 'mana nace miki wannan
kalmar zaki fada min in samu sukuni...
Rike da baki Faruk ke kallon sa yana Murmushi ya
ce a zuciyar sa wannan yaron an yi jarababbe wallahi..
Ganin Samad na kara bude hannun yana wani
karya murya oya matso nan hubby' tun da ba za ki zo ba' 'bari ni inje'..
Aguje yakaraso
wajen Faruk yarungume shi..
Jin kamar ya
rungimi kato beji dukiyar Fulani ba '' ya sa shi bude Idanun cikin Sauri...
Caraf Idanun
su ya tsarke cikin juna shida Faruk....
Zazzare idanu ya yi ya ce wai Allah dan iska
me kakeyi anan wannan ai daukan Alhaki ne...
Faruk dake dan gyara rigar sa da Samad yajawo
dan runguma ya ce akwai dan Iskan daya kaika ka kwana daki daya da mace amma
kuma ba muda sukuni Kodai za ka fasa tafiyar ne Malam Tabe Tabe...
Tsaki Samad keta jerowa ya ce kash wannan game
over na buga.
Amma bakomai
zan rama ne na ji din ni Tabe Tabe nake kaikuma fa..
Kai bara kaji ingaya maka nidin nan uhmm.
Fadi mana
cewar Faruk yana kallon kwayar Idanun sa..
Kawai abar
zancen da na so in maka Rashin M.
Faruk ya ce ni
yanzu akwai rashin mutunci da ban sanka da shi ba..
Ni dai maza ka
fito mu je tabe tabe..
Kuma na ji Karima
ta ce da ita za a..
Yarima Samad ya
ce eh da Karima Za a je tama kusa barin Masarautar nan ita da Iya Firdausi...
Faruk ya ce
Saboda me zatabar masarautar nan yarinya mai hankali.
Ka yantata ne
?
Shiru Yarima
Samad ya yi ya ce Karima ba baiwa ba ce ''
Zazzare idanu
Faruk ya yi ya ce kamarya kenan fahimtar dani...
Samun wuri suka
yi bakin gadon nasa suka zauna suna face din juna..
Kamar yanda
kaji nace maka haka zancen yake Karima ba baiwa ba ce...
Diya ce ga
shugaban Kasar Niger.
Mahaifiyar ta
Mata ce ga
shugaban kasa...
Faruk cikin
Razana ya ce Samad kai za ka warware mun wannan maganar ta matukar daure mun
kai...
Wayar Yarima
Samad ne ya fara ring yana dubawa yaga Mamy ce...
Yasan fada
zatayi a kan su kadai ake jira..
Uhmm Faruk
kabari inmunje bohicon zanbaka tarihin Karima yanzu ga Mamy na kira babu lokaci
tashi muje...
Tashi suka yi suka fito iske Aminu suka yi
hankalin sa ya kar kata a kan TV..
Ganin fitowar su ya sa ya Mike ya ce kai Faruk
meya rikeka daga za ka kirashi..
Jikin Faruk a
mace yake Jin wannan zancen a kan Karima..
Babu komai
Aminu mu je Ko yafada asanyaye...
Samad ihun
Kiran Rahama ya shiga yi..
Aminu ya ce
yanzun nan tafita da jakar ta dan haka mu tafi kawai...
Koda suka iso
Rarfajiyar Mamy na ganin Samad tasoma Fada..
Ta ce haba kai
kullum in za a je inguwa da kai sai rai yabaci tun dazu ka shanyamu har Rahama
ta gaji da jiran ka... Ta fito ta barka ciki.
Kwantar da kai
ya yi Alamun ban hakuri ya ce natuba Mamy.
Babu ba ta lokaci
suka ɗau hanyar zuwa
bohikon dukan su harda su Faruk da Aminu da Karima 'su Khadija ana Murna za a je
gun kaka ziyara..
Samad Sam beso
Rahama ta shiga motar su Mamy ba..
Ba haka yaso
ba..
Faruk duk
jikin sa a mace tun lokacin da Samad yasoma bashi labarin Karima..
So yake ya kalle
ta dakyau'' cike da mamaki..
Aminu Da Samad
kadai ne ke fira a motar su biyu ke bayan kujerar mota..
Faruk na Tuki
Ahmad nakusa da shi a gaba..
Shi Ahmad
murmushi yake a kan Asiya Sam haryanzu Ko waya betaba hadasu ba..
Yana lissafin
yanda zeci gidan ta badai shi ta zaga
Wata zuciyar ta
ce Anya Ahmad yin haka ba kuskure bane 'inka sake ta za ka samu matsala da
iyayen ka kuma ka basu' kunya..
Tabe baki
shiyakadai yana maganar zuci ya ce uhmm to koda na saketa din Ko sunyi fushi na
kwana biyu ne za su huce...
Samad dake
kallon keyar Faruk Ya ce kai kabi damu a hankali fa kar ka jefamu cikin rami kajawa
mata ta asara...
Darawa Dukansu
motar suka yi harda Ahmad.
Aminu ya ce
kai Tabe Tabe tun da kayi aure shi ke nan ba mu da ta kan mu ka ishe mu ka
gallabe mu..
Nima dai auren
nan zanyi inhuta haba dan Allah..
Faruk dake
murmushi yana Tuki ya ce meye dan mun mutu iyaka dai ta yi maka takaba da
ankwana biyu ta samu wani mijin ta aura...
Sossai Yarima
Samad ya Girgiza Jin wai zata samu wani mijin ta aura.
Ya ce dan
bakin cikine kai Faruk ta Allah ba takaba ga Kabari na ga na Rahama InshAllah
tare zamu mutu..
Sossai suka ɗara
haka suka yi ta fira har suka isa garin bohikon....
Kai tsaye
gidan Liman Ahmad suka nufa..
Iske shi suka yi waje yana koyar da dalibai.
Ganin motocin su yaga tambarin gidan Sarauta
ya san eh lallai bakin kwatano ne suka iso.....
Nan da nan ya
sallami dalibai tare da koma ciki..
Koda suka iso.
Parkin space
suka paka motocin su...
Lale Lale Lale
cewar *Iya Gari* kakar su Samad wannan sunan ake kiran ta agarin Asalin sunanta
Amina....
Samad bakin sa
dauke da murmushi ya ce Iya Gari lallai matar nan bakya tsufa..
Tabe baki ta yi ta ce taya zan tsufa kuna ta
dankaromin kishiyoyi harda maigida na Ahmad shima kishiyar zemin..
Dariya suke nan da nan suka nufi masaukin su..
Firdausi Autar su Mamy ce ta fito Daga dakin
ta aguje tanufo Mamy ta rungume ta '' ta ce anty Habiba kin zama me iyali.
Kallon Rahama
take wacce suke gaisawa da Iya Gari tana mata tsiya a kan ta kwace mata
miji....
Firdausi ta ce kai kai wannan ce Matar Samad
kamar nasan fuskar nan..
Rahama juyawa
ta yi tana kallon Firdausi ta ce '' la la anty fiddo kece..
Sossai
Firdausi ta rungume ta '' ta ce Rahamatullah wai dan Allah dagsk kece matar ɗana '' shiru ta yi tana
murmushi..
Yarima Samad ya
ce Mama firdausi kin santa ne..
Kwarai kuwa
nasan Rahama Abdurrazak.
Mun hadu da ita Asaudiyya ita tana karatu ne''ni
kuma munje umra' sossai ta ringa koyamin karatu Katuna wataran muna waya da kai
lokacin inacen' 'har nacemaka wallahi wata yar karamar yarinya ta burge ni
sossai ga tarin ilimi a kan ta har daurani take a kan karatuna' nace maka 'nima
da Allah zai sa yata Aisha zata zama kamar ta danaji dadi.
Kacemin ai
abun rabone da dagewan iyaye...
Yarima Samad
cike da Jin dadi ya ce kwarai kuwa natuna ashe ita ce uhmm Allah ya yi kunsake
hadewa' a matsayin yar ki..
Mamy cike da
Jin dadi ta ce MashaAllah abu yayi..
Wai ina yaya
Auwal ne.
Da Sani..
Bata gama rufe
baki ba sai gasu '' sun taho harda baban nasu...
Cike da. Jin
dadi suka kara gaisawa da mamy.
Abban su
sossai yaji dadin ganin su.
Ya ce yau dai
Samad yazo mun da Amarya kuma babu wanda ya isa yatafi da ita..
Yarima Samad
sossai ya ɗara ya ce
uhmm banga kana aiken kudin cefane ba..
Liman Ahmed
kallon Rahama ya yi ya ce ke Rahama kullum bakina Jin alert awayar ki ba..
Cikin zazzakar Muryan ta ce Ko yanzu ma sun
shigo kudin.....
Gabadaya dakin dariya suka sa...
Bayan sunyi ciye ciye dukan su..
Rahama tabi
Firdausi zuwa dakin nata..
Sossai Samad
ya takura..
Sai bayan
Ish'ai Liman Ahmad yakira dukan yayan sa harda Su Faruk da Aminu Samad da
Ahmed.
Cike da nutsuwa kowa ya zazzauna kasa.
Ya ce yawwa
game da maganar Farida ne..
Gaskiya
yarinyar nan ta cuceni ta cuci kanta nabata tarbiyya Allah ne shedata' kuka
yake sossai ya ce shi ne zata janyo abun da ze ba ta martaban gida ni Liman.
Duk hukunci da
Aka zartan a kan ta babu ruwana wlh ita tajawa kanta..
Sannan zancen
Maryam zata dawo nan hannuna tun da mahaifiyar ta ba ta gida Kuma na ji ance
uban nata ya yi aure..
Auwal ya ce haka
ne gaskiya gwamma ta dawo hannun ka.
Zatafi samun
kulawa kuma zata nutsu..
Sannan maganar
mijin Habiba da baya kasar nan shekara shidda.
Anya wannan
zaman me billewa ce ba na son abun da ze kawo mace ta fada halaka..
Dan haka asan
abun yi...
Yarima Samad ya
ce Liman mun gano inda yake..
Nan ya shiga
bawa liman labarin abun da ya faru a masarautar da dalilin barin gidan nasa
dakuma inda yazauna ɗakuma
inda yake ayanzu..
Sossai Mamy ta
Girgiza Jin wai aikin gadi ya yi agidan su Rahama....
Kuma yana da
masaniya a kan inda yake amma be sanar mata ba..
Tabe baki tana
kallon shi
Ta ce kai
Samad ka san inda yake shi ne ka bar ni a duhu.
Kuma har gidan
su Rahama yazauna Daga kai har ita babu wanda yataba faɗa min..
Yarima ya ce ita kanta Rahama batasan shi ne
ubana ba saida taga hoton sa..
Kuma kin san ba
ta da surutu ba ta fiye magana ba..
Inhar ba
annemeta da zancen bane..
Firdausi ta ce
haka ne Tome zata ce miki kina uwar mijin ta..
Faruk ya ce
gaskiya ne kam bazata ce komai ba Inde Rahama ce..
Nan. Dai. Fira
ya bârke tsakanin su
Liman ya ce
maryam gobe yake so ta taho bohikon din in bikin khadija ya tashi taje
tadawo....
Sun zauna suna
ta tsara yanda za su yi shagalln bikin Ahmad da Khadija..
Kwanan su uku agarin
duk dangi saida aka zazzaga da Rahama '' masu zuwa ganin ta kuwa makil ka
sancewar ta diyar sheik Abdurrazak....
Karima kuwa
sossai ta rinƙa bin Rahama duk inda zata sa kafa a garin.
Duk yanda
Faruk yaso Samad ya ba shi labarin Karima abin yaci tura yabar shi sai sun koma
kafun su tafi Kanon ze matsa masa dan yaji labarin komai..
Koda Maryam ta
iso bohikon Liman Ahmad '' cikin Almajiran masu daukar karatu wajen sa ya yi masa
AlKawarin bashi auren Maryam 'sa daki da iyayen sa kawai yake bukata..
Maryam ta yi kuka
harta godewa Allah yanzu ita ce aka ba da auren ta kamar mara yanci' uhmm.
IYA GARI NAN
NAN TA RINƘAYI
DA Mamy da Rahama '' ita da yayan ta firdausi da Auwal da sani..
Suma sunce za
su je biki.
Amma iyakar
kwatano.
Rahama tasamu
kyautuka agun yan uwa da a bokan arziki....
Karfe biyu
suka baro garin cike da kewa....
Sai bayan
la'asar suka isa kwatano da yake babu nisa sossai.....
Suna isa gida.
Kai tsaye kowa
ya yi sashin nasa...
Faruk hango
Karima ya yi tana ta buga uban sauri zata wuce dakin nasu..
Muryar sa ta
sinkayo yana fadin dakata dan Allah....
Cak ta tsaya gaban
sa cike da ladabi ta ce naam yaya Faruk gani...
Kallon ta yake
cikin idanu yakura mata idanu 'sossai ganin mugun kyawun ta dabe taba lura ba
saida ya firgita shi yau ne karo na farko da ya yi mata kallon tsafta...
Kallon da yake
bin ta da shi ya yi yawa hakan ya sa ta ce uhmm yaya Faruk inajin ka kayi shiru
sonake inje in yi sallah...
Dawo da
nutsuwar ya yi ya ce yawwa Karima.
Daman ke yar
Shugaban Kasar Niger ce..
Cikin zazzare
idanu take...........
Taku har
kullum kyauta Daga Allah9️⃣5️⃣
09069080725
Cikin zazzare
idanu ta ce ina kaji wannan zancen..
Sake da baki
take kallon sa zuciyar ta na tsananta bugawa..
Murmushi ya yi
ya ce yanaga duk kin rude Daga tambaya..
Daga bakin
dabe mun karya na ji kema kin sani..
Shiru ne ya
ratsa na wasu dakiku ta ce kabari shugaba na inyabani izini zan gayamaka..
Tabe baki ya
yi ya ce nima ai shugaban naki ne nida shi duk daya ne Karima...
Haka ne yaya
Faruk '' to kabari zuwa dare na nutsu inka dawo zanbaka labari...
OK to Allah
yakaimu ya furta tare da barin wajen itakuwa tawuce cike da mamaki ya akayi
Yarima Samad yagaya masa.
Bayan Isha'i
kuwa sai ga Faruk yakara dawowa wannan karan Gun Samad yatafi direct.
Koda ya isa
sashin Yarima ya iske shi zaune a falon sa shikadai système na gaban Idanun sa
sanye yake da medical glass.
Yayi zurfi
acikin aikin da yake yi hakan ya sa beyi saurin Jin Sallamar Faruk..
Dafashi ya yi
ya ce kai Tabe Tabe wai aikine yatashi haka..
Dago kai ya yi
yana kallon Faruk ya ce kai yada zuwa gidan masu aure awannan time din..
Faruk darawa
ya yi ya ce na ji dai dan iska gunka nazo.
Bismillah
Samad ya ce yana nuna masa wajen zama..
Hakan ya sa
Faruk y azauna yana fuskantar Samad dake kokarin rufe système din sa..
Uhmm inajin ka
kazo ne a kan tafiyar mu Kano ne..
Faruk ya ce
Duka dai amma abu na farko shi ne kaban labarin Karima daka fara ba ni munje
bohicon kaki karasa mun sauran bayanai....
Yarima Samad
cike da mamaki yake kallon sa ya ce kai kai yanzu kan wannan zancen kasa harna
rufe système dîna ban gama aiki ba..
To meye dan
karufe système din kai din ma ai gulma ce bawai aikin zakayi ba...
Ni dai gayamin
kaine saurare..
Idan naki
gayamaka meze faru ne ya tsare sa da idanu..
Uhmm Aikuwa
inkaki gayamin babu inda zanje kuma wallahi ba ka isa ka tashi Daga nan ba.
Zanga ta inda
Rahama zata ganka..
Jin haka
Yarima Samad ya ce uhmm tun da kace haka zauna inbaka labari nasan ba mutunci
ne da kai ba saika aikata abun da ka fada din yanzu ni nayi hankali banson
banje naga sahibata ba...
Kamar yanda
nagayamaka Karima ba baiwa ce diyar shugaban kasar Niger 🇳🇪
ce..
Shugaban
Adalai ya ce kasar niger wajen wani taro da Aka gudanar na sarakuna..
Bayan anwatse
taron gidan Shugaban kasar ya sauka maimakon Hôtel.
Cewar shugaban
kasar Alh Salihu yawuce zama hôtel Saboda irin Adalcin sa.....
Bayan ya isa fadar shugaban kasa ya samu
masauki me kyau cike da kulawa...
Koda shugaban
kasa yazo dan zantawa da shugaban Adalai..
Zama suka yi ya
rinƙa
tsara masa yanda ze tafiyar da mulkin sa ba tare da hakkin kowa ba..
Sossai shugaban kasar Niger yaji dadin jawabin
sa kuma ya gamsu da duk hujjojin daya bashi...
Suna zaune
suna tattauna suka ji ihun Iya Firdausi ita da Karima ɗaman Shugaban kasar ya saba Jin haka...
Shugaban
Adalai ya ce suwaye ne suke wannan ihun kamar mata..
Shugaban kasar
ya zabga tagumi ya ce wallahi tun da wata Kanwar ta tazo gidan sabani yashiga
tsakanin su a kan ba ta sakar mata kudi' amatsayin ta na matar shugaban Kasa
ita Firdausi nuna mata take saina ba ta sanna itama tabata amma kanwar Sam taki
fahimta ta ce Ko motar hawa ba ta da shi amma yayar ta tana hawan na million
dari.
Aranar dai da suka
yi wannan fadan ina falon.
Karshen zancen
ta gayamata InshAllah saita zama abun gudu Kuma daulan sai ya gagareta indai
sunan ta Asma'u zata gani..
In gayamaka
adaren ranar ihu suke ta ita da yar ta Karima.
Har suna neman
hanyar guduwa subar gidan dan akwai securite hakan ya sa basu samu dama ba...
Yanzu shekara
daya kenan suna cikin wannan yanayin har yanzu *Kanwar ta* ba ta tako gidan
ba...
Iyayen ta duk
sun rasu daman su biyu suka rage sai dangi da abokan arziki.
Amma rufe
matsalar nan nayi kan duniya ta dauka shi ya sa ban shiga nemar musu magani a
kasar nan ba...
Sossai
Shugaban Adalai ya jinjina wannan Al'amarin ya ce bakomai ba ce illa cutar
hauka ne yake son ya kama su..
Inka amince
zan tafi dasu kwatano acen zan musu magani har su warke '' kuma zankaisu ne
amatsayin bayi amma zanwa mata ta da yayana bayani sunsan ba bayi bane..
Yin haka
zecire Idanun mutane a kan su.
Sossai
shugaban kasar Niger ya yi naam da zancen nasa..
Kuma ya ba shi
shawara yakara aure dan wannan za a dade Ana nema musu magani....
Wannan shi ne dalilin daya shugaban kasar
Niger yakara aure..
Akayi ta cece
kuce kanwar ta ta.
Tayita farin
ciki an saki yayar ta tashi ga duniya.
Wannan shi ne
takaita cen tarihin Karima da iya Firdausi.
Ni Samad ni ne
nan yasha dawainiya dasu wajen nema musu magani har bohicon nakai su gun liman
bohicon shima ya yi iya nashi kokarin har suka samu waraka...
Yau befi Sati
daya da mukayi waya nida shugabar kasar a kan maganar yana son iyalin nasa su
dawo '' saina ce masa yabari ayi bikin khadija..
To ya amince
da magana ta dan haka zezo daurin aurenn khadija kwana uku kacal zeyi tare za
su koma wanda hakan ze Girgiza makiyan su...
Duk da ba sa waya
amma kullum yana bibiyar lafiyar su kuma yana adua Allah ya bayyana Sarkin
Adalai..
Kafun nayi
aure har cemin ya yi wai in inaso na auri Karima mana..
Ni kuma nace
masa Kanwace na dauke ta inada wacce nakeso..
Ya ce babu
Matsala halarci da mukayi masa besan da me zai saka mana ba..
Karima yar
halak ce ka ga akaina tasha gwagwarmaya '' koda Uwar ta take hannu Fulani '' ba
ta yarda uwar ta tashi ga sashina tasan Fulani na iya juya uwar ta da magani..
Nine nabawa
Fulani iya Firdausi amatsayin baiwa Saboda naga hankalin na ba ta anya kuwa
bayi ne..
Yin hakan
danayi ya sa nacire mata shakku...
Ajiyar zuciya
Faruk ya sauke ya ce dankale lallai Labarin Karima da uwar ta akwai ban
tausayi..
Tun da kaban
labarin nata da ba ka karasa ba nakasa sukuni 'maganar gaskiya ina son Karima
sona hakika ina son in uban ta yazo ka sanar masa amma kuma ka dakata tukunna
an yi mun AlKawari ba ni Mata acikin masarautar nan indai ita ce zanyi farin
ciki inkuma ba ita ba ce zanshiga damuwa dan ina mata mugun so abaya na so Asiya
amma ban san radadin so ba sai a kan Karima duk yanda na so nayi hira da ita
dazun taki ba ni dama.....
Yarima Samad
Murmusa ya yi ya ce aibazata taba kulaka ba harsai na ba ta dama wannan ka'ida
ne...
Maganar ance za
abaka mata wanene ya yi maka AlKawari mai martaba ne..
Girgiza kai ya
yi ya ce uhmm kadai zamuyi magana zanje gida saida safe Kar ka ce mata komai
harsai na tabbatar da wacce za a ban..
Yarima Samad ya
ce basai inba Aminu ba..
Zare idanu ya
yi ya ce haba Tabe Tabe ya da haka..
Wallahi ina
mugun sonta inhar ba ita ba ce wacce za a ban zan hada biyu in aura' Kayi mata
magana a shirye nake...
Yarima Samad ya
ce na ji na mince zan duba lamarin ka..
. Tashi ya yi
ya ce yawwa mu je gidan kurku zanje induba Fulani...
Tare suka tafi koda suka je sun iske ta zaune
ta zabga uban tagumi.
Ganin su ya sa hankalin ta yadawo kansu..
Tafashe da kuka ta ce dan Allah Yarima Samad
ka taimakeni in bar nan wajen...
Faruk ya ce
inkinbar nan ina zakije kibari kawai ayi zaman kotu inhar kotu ta yi belin
dinki shi ke nan kin rabauta..
In hukunci
suka yanke miki duka daidai ne yakarashe zancen yana duba wayar sa....
Yarima Samad
dake kallon duk yanda ta rame ta yi baki duk ta zube ya ce kai Mama Fulani
kenan 'nida kike neman sabautawa a yau kike neman taimako na...
Na mugun taimaka miki ɗanasa ake baki abincin da kike bukata.
Sannan ina mai
shaida miki a kan Mahaifina angano inda yake atakaice bayan bikin Ahmad da
kwana daya zanje indauko sa.....
Fulani zazzare
idanu ta yi cike da mamaki ta ce kana nufin ansa inda Salihu yake..
Kuka ta fashe
da shi ta ce nayarda Allah keyi jibi irin abun da mukayi amma kuma zekara
dawowa masarautar nan..
Wayyo dan
Allah kuyafemun na tuba
Yarima Samad
kallon ta yake ya ce uhmm Abban Marwan aure ze daura bayan Auren Khadija da
Sati daya aranar indai ba a je kotu ba zansa a kawo miki abinci biki..
Daga haka
yakama hannun Faruk suka bar gidan kurku.
Gangami da
gidan Iko sai kirari suke masu...
Khadija kwance
a dakin Rahama tana waya da Adamsy da dukan Alamu tanajin dadin wayar duk da ba
magana take ba amma tana murmusawa...
Suna cikin
wayar ne Rahama ta shigo dakin....
Adamsy najin
muryan Rahama tana fadin ke dijat zantafi saida safe yayan ki nakirana.
Kada mata kai
ta yi Alamun ba matsala...
Shiko Adamu ya
ce kiba Rahama wayar mu gaisa mana..
Ihun kiran Anty
Rahama ta soma wance ta waigo ta ce yadai dijat kina bukatan wani abu ne....
Khadija ta ce ga Adamu ya ce zaku gaisa.
Kada kai
Rahama ta yi ta ce A'a dijat ba zan amsa wayar nan ba har mijina yaban dama
''..
Daga haka
tasakai tawuce tasan halin Yarima inyaji labari tofah ze ce da wani abu....
Dijat ta ce ka ga anty tamu har ta wuce kabari
zuwa gobe kun gaisa...
Haka dai su kaci gaba da hirar su.....
Kashe Gari..
Ayaune yan
uwan Adamu su kazo Daga katsina kawo lefe na gani na fada..
Akwatuna goma sha
biyu har fadar Sarki aka kai kaya......
Sarki ya yi Murna
ya sa Albarka '' nan ma aka kai kayan sashin mama karama itama har da taka
rawa..
Ana kai kayan
sashin Mamy yan uwanta da suka zo bikin tun wuri suka fara bubbude kayan suna
sa Albarka....
Sossai yan
kawo lefe suka samu tarba me kyau tare da babban masauki hôtel da Aka sauke su
inda Sarki ke ajiye baki yan biki...
Rahama da Samad da Ahmad suna ta shirye shirye
suma gobe Alhamis za su wuce kano kai lefe.
Ranar juma'a
daurin aure....
Sossai Ahmad
ke murna zeje dauko fitsaratu yakawo gidan sa...
Dan cewa ya yi da ba zai zauna masarautar da
ita ba saida cikin gidajen baban sa..
Mai martaba ya
ce tun da Samad ya zauna shima yazama dole yazauna anan da matar sa.....
Asiya da Rahama suke waya tana ba Rahama
labarin daulan da Salma take ciki kuma ba asan sana'ar mijin ta ba...
Rahama ta ce
subuhannalah kiban lambar Salma koma kawai ki barta ai dani za a kanon
InshAllah zanje in same ta in mata fada ta farga tun wuri banson abun da ze
taba min yar ƙanwata....
Ke kuma banda
munafunci Ashe Ahmad zaki aura shi ne kike boye mun 'sossai ta ɗAnne dariyar ta..
Asiya da ba ta
gane kan zancen ba ta ce wane Ahmad kike magana dan sunan mijin da zan aura
ne...
Rahama ta ce
angon naki mana' kin san gobe zamu kai l'efen naki...
ZUMBUR Asiya
ta tashi zaune ta kam bala'i kina nufin wannan yaron mara kunya nan shi zan
aura...
Fashewa da
kuka ta yi ta ce wallahi Rahama soya ke ya gana mun badan Allah ze aureni ba
tuntuni danasan shi ne 'aida nayi ta magiya a kan a fasa auren nan...
Rahama ta ce
Ko kukan jini zakiyi baza a fasa ba nida aka auramun Samad mutuwa nayi....
Asiya ta ce
haba Rahama karki hada auren ki da nawa.
Shifa akwai
mugun nufi azuciyar sa..
Uhmm kanin mijina beda mugun nufi kece baki
fahimce shi ba Asiya..
Dan Allah
karki biye masa koda anzo daurin auren
Koda ankawo ki
nan gidan sa dan Allah ki kwantar da kanki duk iskanci sa ze bari inma da
mugunta ne zekasa aikata abun da yakeda niya....
. Cikin
sheshekar kuka Asiya ta ce Rahama na ji zancen ki kuma InshAllah nadauka baki
taba ba ni shawara nabi na tabe ba..
Sossai Rahama
ta ji dadi ta ce shima Abby jibi ne daurin auren nasa '' amma ance nasa a 🇬🇦
za a daura Amarya kawai za a kawo masa Daga can...
Uhmm haka na
ji nima Rahama ai baban naki yana ta zumudi har sun tare sabon gida '' ya gyara
musu Ko ina..
Rahama ta ce
anty da mama sun gayamin..
Kice zumudi
yake uhmm Abby kenan Allah dai ya sanya Alkhairi....
Daga haka suka
yi sallama.
Kai tsaye
sheik ta danna kira.
Babu ba ta lokaci
ya Daga.
Bayan sun
gaisa ta ce Abby jibi ne daurin auren namu to Allah ya sanya Alkhairi
.
Ameen ya Allah
ya furta ya ce Rahamatullah dafatan kina lafiya na ji Aisha ta ce gobe zaku zo
Ko..
Nasan ɗai sashin Sa'adatu zaki
sauka nasa an gyara miki daki daughter..
Sossai ta ji
dadi ta ce eh sashin anty zan sauka dole ne wannan Abby.
Yakamata ka
hadani da Amaryar tamu Abby..
. Dariya ya yi
yana shafa gemu ta tsotsa masa inda ke masa kai kayi ya ce karki damu yanzu
zantura miki nombar kuma ai zaku hadu da ranar juma'a da yamma jirgin su ze
sauka....kano.
Rahama cike da
Jin dadi ta ce Abby uhmm da'ace ka nemi shawara ta dazance kada ka kara
aure....
Murmushi ya yi ya ce Ko kina taya Sa'adatu
kishi ne..
Zazzare idanu ta yi kamar yana ganin ta ta ce
A'a Nina San Anty babu ruwan ta...
Kuma kin san
da haka ne kike son ki hana '' gayamin Ko matar batayi miki bane...
Tun Farko da
kin nuna mun bakyaso inna gamsu da hujjojin ki zan iya hakura innemi Zabin
Allah.....
Kin san banda kamar ki Rahama duk acikin yaya
na.
a kan ki zan iya yin komai 'nasan kinada
tarbiyya ba za ki so muyi abun da mutuncin gidan mu ze zube ba..
Rahama ta ce haka
ne Abby na kar ka Adamu' itama wannan din Allah yakawo ta da Alkhairi..
Ameen ya Allah ya furta yana mejin kaunar
yarsa na kara ruruwa acikin zuciyar sa...
Daga haka suka
yi Sallama...
Shiko Sheik
Hassana ya dannawa kira..
Ya ce Amarya
bakya laifi koda kin kashe karen gida na..
Murmushi ta yi
Daga zaune ta ce my husband ai cewa ake koda na kashe dan masu gida..
Darawa ya yi
ya ce Ah Ah dan baki kashe bane dakin ni awajena kinyi laifi my love.
Uhmm yanzu de
jibi daurin auren mu karfa kisa aranki Daga ke babu kari ɗuk lokacin ɗana samu dama zan cike'
inkuma banyi ba to haka Allah yatsara...
Tabe baki ta yi Daga zaune ta ce haba angon
hassana Kai Adali ne Ko goma ake yi nasan zakayi adalci uhmm kaide wani abu sai
jibi ranar daurin aure na ji bakin cikin da ba za ka zo ba..
Kiyi hakuri Amarsu ta angon ta' akwai wata
diya ta Asiya ɗa kanin
mijin yata Rahama ze aura' kuma Nine na jagoranci komai na auren nasu..
Am sorry kinji baby na yakashe murya.
Hakan ya sa ta Jin kanta a nishadi ta ce uhmm
yawuce tun da ka kawo uzuri..
Amma fa nazo
zamu ɗau hotuna zafafa
nida kai.
Sossai ma zamu dauka yabata amsa.
Amma ki tabbatar da hijab jikin ki kafun muyi
hoton kin san irin wannan hoton yawo suke a social media' Kuma ni gida na ba' a
yafa mayafi hubby kizo da hijabai in sun miki karanci zan ha daki da Sa'adatu
zata dinko miki..
Uhmm na ji my love dîna uban yaya na sirrin
zuciyata 'mai gyara tunani na me sani farin ciki...
Sheik cire hular kansa ya yi yana dan shafa
kansa' Wani kayataccen Murmushi ya yi yana ayyanawa aransa uhmm shima yazama ƙaramin
yaro yau....
Amarya ta ina godiya sossai zan shiga Daga
ciki..
Uhmm yanzu har ka gaji da hira dani..
Ah ah banki mu kwana chat ba' yau ina dakin
Sa'adatu Kuma ita ba ta son jira' gara in je kin san yau da gobe duk wajen ta
nake jibi kuma ina tare da sweety na..
Sossai ta dara katse firan ya yi da Fadi ki
tabbatar kinyi mafarki na.
Da haka suka
yi sallama.
Kai tsaye
dakin Anty ya nufa iske ya yi zaune ta ce Abban Rahama Kaga yanda kayi kyau
kuwa...
Allah Ko
Sa'adatu tun da muke ban taba miki kyau ba sai yanzu..
Kai ka san kullum ina gaba wajen yaba kyawun
halittar ka..
Shi ya sa nake adua Allah ya sa in haifo mai
kama da kai kamar Rahama...
Sossai ya dara ya ce yawwa dan matso zanwa
baby na adua kin san jiya ina dakin Maman Salma 'babu damar ayi adu'ar..
Haka ne ta furta tare da matsowa yana tofa
adua tana lumshe idanu..
Nikam nace
bara inbaro dakin nan kada Sheik ya hango yaci ni tara.....
Asuba ta
gari......
Kashe Gari.
Kwatano.
Tun da sassafe
masarautar gheuzo ta tashi da Ayyuka tare da baki ta Ko ina daga garuruka harda
gyare gyare ake yi inda sarakuna za su sauka cikin su harda Sarkin kano.....
Yarima Samad
dasu Ahmad ɗa Rahama'
tsab suka shirya '' su Faruk da Aminu sammako suka yi dan zuwa jidan akwatunan
lefen suka yi airport.....
Mama Firdausi wanda da ita za a tafi tsaf suka
shirya tare da wasu yan uwan nasu Daga bohicon..
Karima ta ce
baza a abarta abaya ba duk suna cikin matafiya...
Khadija harda
kuka wai ba da ita za a je ba..
Yarima Samad ya
ce kije ina gobe daurin auren ki' muma jibi zamu dawo InshAllah da Amarya.
Mamy da Mai
Martaba Adua suka yi masu ɗa
fatan Allah ubangiji yakai su lafiya..
Abban Marwan
tuni yawuce aiport dan dole yakamata ace ga kanin uban Ahmad a wajen daurin
auren.....
Basu ba ta lokaci
ba Samad Personnel air plan.
Jirgin nasu ya
Daga sararin Samaniya.......
Sai Kano...
🇬🇦
Gabon
Hassana tasha
lalle hadadde ta yi wani fresh tasha gyara tsaf harda maganin tsaida Brest
tasha dan haka boob din ta yakoma kamar sabuwa
Magungunan
gyara ba a cewa komai gidan nasu ancika tun a ranar aka fara daura tukunya ana
sauke wa...
Me kitson dakewa Hassana kitso ta ce 'sai dai
aturawa sheik hoto yagani yabiya ta....
Daukan hoton suka
yi' 'shi kuwa Sheik yana cen yanata hada hada tarban bakin sa da suka zo Daga
nesa irin su saudiya' Soudan...
Ganin sakon
nata ta whsap ya shiga cikin hanzari..
Cin karo ya yi
da wannan tsalelen kitson nan..
Cikin.
Muje zuwa
Ta ku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
09069080725
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.