Ƙanwata Na Ikilima Adam (Kashi na 7)

    Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Allah kasa yanda na fara lafiya in kare shi lafiya. Wannan labarin ya faru da gaske dan kusan Book dina da nake yi true life ne sai dai in yi masa kwaskwarima dan abun ya fi ba da citta.

    Ku biyo ni ku sha labari.

    Ku daure ku yi comment dan in ji ra'ayoyin ku a kan Littafin nan......

    *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

    _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa}_

    https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

    ⚜️©J.A.W📚🖌️

    Marubuciyar

    * Amince Da Ni
    * KAI KA JA WA KANKA

    Yanzu kuma gani ɗauke da

    ƘANWATA

    Paid Book ne

    Vip 300
    Special 500

    Acct No. 3115484026, First Bank, ko kuma Kati MTN (Ba na son VTU)

    Idan kin biya ta bank kina iya turo shaidar biyar ki ta wannan 09069080725

    kanwata

    🌟🌟 ƘANWATA Na Ikilima Adam [Kashi na 7]🌟🌟

    9️6️

    Cikin Rawar hannu ya bude hoton 'Murmushi ya yi Aminin Sheik dake zaune kusa da shi ya ce dan lubaiya nima' ka koya mun wannan soyayya haka...

    Dago kai Sheik ya yi yana Kallon sa 'ya ce in soyayya ne kaine malami koka mance nan kake zubawa da Uwargidan ka Sa'adiya....

    Malam Isa ya ce uhmm ai yanzu tarage kula dani' Wai yaya' hidimar gida....

    Uhmm saika lallaba ta ahaka ka san ba ta son kishiya Ko.....

    Malam Isa ya ce anya nima ba karawa zanyi ba..

    Sheik ya ce Gaskiya kar ka kara kasata ahanya kana da rauni bana tunanin za ka iya contrôle din mata fiye da daya..

    Su Mata da kake gani in mutum ya yi wasa sai suka yi shi ga halaka...

    Adalci shi ne babban abun dubawa ɗayawa maza cikin sai su ringa fadin ai zanyi Adalci inada kudi' inada kaza ɗuk aikin banza ne' indai kaiba Adali bane ɗukiyar ka bazata kare ka ranar gobe Alkiyama ba.....

    Kai ka san cewar na kara aure ne saboda matsalolin uwargida ta..

    Da kuma inada yakinin zanyi Adalci.

    Har kwanan gobe ban yarda Sa'adatu ta raina ta Ko babu komai ita ce farkon shafi na rayuwa ta.

    Iyayen ta nake dubawa sun mun halarci koda mukayi aure' mahaifin ta saida yaban dubu dari biyar kyauta ya ce in jari...

    Ya ce wlh ba yabani bane dan ina auren yar sa.

    Yabani ne dan mutunci iyayena dani kaina kada in duba dan yamun kyauta Aisha tamun laifi Inkin hukuntata...

    Alhmdulilah wannan kudin tazamo silar Arziki duk da Allah ke azurtawa 'amma wannan kudin sun mun rana kafun in zama wani abu saida silar su...

    Kwanaki ma har tafara goran ta mun a kan tsohon gidan' wai ita ce sila ɗariya tabani ka san mata ba a biye musu.

    Bare in kishi ya motsa....

    Shin za ka iya rike mata biyu kuwa ka zauna kayi nazari' babu ruwan ka da wane ya yi 'nikaina danayi taimakon Allah nake nema..

    Sossai jikin Malam isa ya yi Sanyi ya ce zankara aure Sheik amma sai nan da shekara biyu haka lokacin' mun sake gida.....

    Sheik maida kallon sa ya yi a kan wayar sa '' ganin stick da hassana ta turo na tagumi Alamun Ana jira ya ba da Amsa..

    Rubutu 'yayi ya ce MashaAllah tabarakallah kitso ya wanku' wanka tabi jiki....

     Maza kema ki goge wann hoton awayar ki kada a dauka ayi ta turawa....

    Me kitso abata dubu hamsin ta turo Acct nomba yana gama fadin haka ya sauka online din.....

    Kai tsaye tashi suka yi dan zuwa Tarbo su Rahama ance sun taho... Abubakar ya hango shida Abdul jalil suna sanye cikin jallabiya hash color..

    Dadin ganin su ya yi ganin sun tunkaro inda suke.....

    Abdul jalil ya ce Abby zamuje mu nuna wa masu kawo shanaye gidan nan sunce basu gane Kwatance ba..

    Sheik ya ce to maza katafi kaji Ko...

    Dawo da kallon ya yi a kan Abubakar ya ce ya angyara masaukin baki Ko.....

    Abubakar ya ce an yi komai Abby sai dai fatan ayi taro lafiya a watse lafiya.

    Iyayen yarinyar da nake nema sunce zuwa monday suke son aturo...

    MashaAllah Sheik ya furta to Allah yakaimu...

    Koda Abubakar din yawuce ya ce uhmm yaron nan duka shekaru 22 gare shi amma aure yake '' koda yake nima shekara 21 gareni aka mun aure ina wata kasa...

    Barin wani tunanin ya yi ya shiga tsabgogin gaban sa......

    Koda su Rahama suka iso ta yi harba da Sheik rungume shi ta yi sossai.....

    Cike da Farin ciki ya ce haske na harkin iso..

    Murmushi ta yi ta ce Abby ka ga yanda kayi kyau kuwa.... na ji dadin ganin ka '' bara in shiga ciki nakosa inga Mama....

    Aguje ta fada gidan tana dube duben inda zata ga Mama hangota ta yi zaune Daga can gefe ita kadai Alamun ta fada duniyar tunani...

    Rungumar da Rahama ta yi mata ne yadawo da ita cikin hayyacin ta...

     Ta ce la la Rahama ta yaushe a gari wayyo Allah dadi yata Idanun ki kenan zauna mana.....

    Rahama cike da Jin dadi ta ce mama nayi kewar ki sossai '' uhmm muna tare da baki '' mama firdausi kanwar mahaifiyar Abdul Samad ɗa yan uwan sa mata....

     Mama ta ce Ah sushigo mana..

     Lala Mama karki damu Abby yakai su masaukin baki farkon gida baki wajen ba yanda ya tsaru har abinci komai ankai...

     Mama sake da baki ta ce to waye ya yi girkin Ko daman abincin sune na ji jiya yana cemin in dafa na baki ne na zata na bakin sa ne da suka fito Daga wata uwa duniya nace ya nemo me dafawa...

     Rahama ba ta rai ta yi ta ce Mamaaaaa ta ja sunan wai yaushe zaki gane abun da nakeson kina ganewa ne...

    Abby fa mijin ki ne kinfini sanin hakkin mata a kan mijin ta biyayya dasai ki dafa masa ki jefa masa aniyar sa kinga anzauna lafiya 'mama ba na son kowace mace tazo gidan nan ya fi ki matsayi ina son matsayin ku yazo daya Ko ma ki ɗara su...

     Mama ki duba anty mana ba ta damu ba..

    Sau nawa Abby ze mata abun da ba ta so a kan ki kuma ina gani amma wallahi ba ta taba nuna masa kaza da ya yi mata be mata dadi.

    Sai dai ta cemin tamasa uzuri amatsayin ɗan Adam agizi ne tasan da ganganci ba zai mata haka ba...

     Irin haka shike karasawa miji ya yarda da kai dari bisa dari...

     Ni dai sonake ki hada kai da Anty sossai wallahi matar nan tana kaunar ki sau nawa Abby ze yunkuro ya ce ze sake ki 'Inkin takura masa tare da kawar ki Suwaiba Anty take tausasa tana gayamasa in har yabiyewa zuciya ze kaisa ya baro da yake yana Jin shawarar ta data fadi yake dauka kuma ya gode...

    Ina son yardan da Abby zeyi dake ya fi na kowa cikin gidan nan..

     Dan Allah mama ta kinji Ko...

     Tabe baki Mama ta yi ta ce uhmm na ji zanduba mu je in kaiki daki Ko..

     Ah ah mama ba dakin ki zan sauka ba.

    Wajen uwar dakina zan kwana haka kurum ga inda zansha lele....

     Mama ba ta rai ta yi ta ce haba Rahama nice ba za ki sha lele ba wajena ni fa mahaifiyar ki ce...

     Nasani Mama anty ita ce ta raineni haihuwa ta kawaii kika yi kin fita matsayi amma ba zan juya mata baya ba.

    Ki duba yanda tasha wahala dani agidan nan Keko Salma kadai kika sani..

     Mama ni kinga tafiya ta Abby ya aika kaya sama..

    Zan fito anjima bayan na huta da Asiya tazo kice mata ina sama ta sameni Daga haka tasakai cikin hanzarin ta....

    Mama rike da baki ta ce kam buhu amma yarinyar nan ta mugun gamawa dani Rahamatullah chab....

    Sallamar Yarima Samad suda Faruk Da Aminu yajawo hankalin ta a kan su.....

     Cike da fara'a ta ce lale lale ga waje ku zauna ta nuna musu kujerun suka zazzauna.....

    Babu ba ta lokaci tasa yan aikin gidan suka kawo musu lemu da ruwan Swan...

    Da ƙyar suka sha...

    Yarima Samad kallon Maman Rahama yake ta ka san idanu ya ce Ah lallai dole mata ta ta yi kyau watau kyau ne da kyau suka hadu ita da Sheik Imam..

     Bayan sun dan gaisa ne suka nemi ayi musu jagora zuwa gidan su Asiya kai lefe dan Marwan da Ahmad suna waje basu shigo...

    Mama ta ce me saukine drever.....

    Basu ba ta lokaci ba suka tafi kai lefe harda Rahama da mama firdausi ɗa Ahmad din dasu Faruk da Aminu' marwan......

     Sun Samu tarba mekyau Daga gidan su Asiya '' cike da farin ciki ake bubbude lefen harda busan Algaita akayi musu na sarakuna...

    Ahmad ne kadai be fito Daga Motar ba kallon gidan su Asiya yake babu laifi suma gidan nasu babu raini hadadde ne sai dai bekai nasu Rahama ba.

    Ya ce oh Ko me ruwana da zancen gida iyakata in koya mata hankali.....

    Yaso ya ganta a yau haka ba zaiyu bane ya sa ya kyale.... Gobe suna tare tun da tare za a juya zuwa kwatanon........

     Asiya sai kukan farin ciki take irin mutuntawa da dangin Ahmad suka yi wa iyayen nata.....

     Sossai aka hada su da kayan ciye ciye a motar tasu....

    Ita Ko Rahama da za su wuce ta cewa Asiya matar kanina '' Daga yanzu respect zaki ringa ba ni ehee...

    Darawa Asiya ta yi ta ce to anti babba...

     Sossai suke suka yi kamar kada su Rabu a ranar Rahama tabi dangin mijin nata suka juya....

    Marwan tsiya yakewa Ahmad ya ce dan Iska ka damu ka ga Asiya Ko....

    Tabe baki ya yi ya ce toni me zangani anan wajen chab

    Marwan ya ce ban gane chab ba banson gulma fa..

    Uhmm kaidai yi shiru kawai ba za ka bane..

    Uhmm na ji tun da haka kace

    ..

    Kwatano...

    Ambassador Abdullahi shida tawagar da matar sa da yan uwa da a bokan arziki suka isa garin kwatano

    Kai tsaye sashin Mai martaba suka je shida uban nasa..

    Sauran bakin aka tafi dasu masaukin su dan suna tare da gajiya...

    Mai martaba cike da Jin dadi ya ce ka ga Ambassador yanda Allah ke ikon sa Ko..

    Ka ba mu 'mun baka..

    Ambassador ya murmusa ya ce to ya za ayi da hukunci Allah...

    Sossai suka shagala da hiran yaushe gamo..

    Shiko Adamsy cire kunya ya yi ya ce a nuna masa sashin Mamy zeje yaga khadija...

    Mai martaba ya ce gaskiya kam gara kaje ka ga sarauniya dukar da kansa ya yi kasa ya ce uhmm zanje a rakani Daga haka ya fice Daga dakin cikin hanzarin.

    Ambassador da mai martaba kallon sa suke suna Girgiza kai..

    Shiko kai tsaye Kwatance sashin Mamy bayi suka yi masa dan sunsan Ko ya akayi shi ne angon....

    Allah Allah yake ya isa sashin Mamy gani yake kamar baya sauri....

    Koda ya isa sashin Mamy.

    Bakin sa dauke da Sallama ya shiga dakin...

    Iske Mamy ya yi da khadija suna hira '' Mamy lale lale Barka da zuwan Adamu har kun iso...

    Jin haka ya sa khadija Dago kanta.

    Caraf Idanun su suka tsarke cikin juna.....

    Saurin dukar da kanta kasa tayi..

    Shiko cikin hanzarin sa yakaraso falon tare da nan waje ya zauna yana kallon Mamy cike da ladabi ya gaishe ta Amsa masa ta yi cikin Sakin fuska ta ce ina mamar taka uhmm suna cen masauki sunce sun tara gajiya sai anjima za su leko...

    Ah Ah bara intashi ni zanje da kaina irin wannan bakin haka...

    Ihun kiran wata baiwa tasoma ta ce maza adauko abincin baki akai masu masaukin su da duk wani abun da da yakamata..

     Cike da ladabi baiwar ta ce an gama Shugaba ta...

    Mamy ganin Adamu ya kurawa Khadija idanu hakan ya sa ta ce yawwa ina zuwa bara inje in ji da bakin dake cikin daki....

    Mamy na ficewa yasoma mata magana ya ce please dijat dan Dago kanki in ganki mana wannan lalle da akayi miki ba ƙaramin kyau ya yi da fatar jikin ki ba..

    Duk da ban taɓa ganin ki ba sai yau dasai ince ke ta mussaman ce...

    Dijat Dago kan ki inga kyakkyawa fuskar da ake min rowa....

    Dago kanta ta yi '' sake da baki ya ce waow MashaAllah Allah mai halitta..

    Cike da zakewa ya ce bara in rera miki waka.....

    Kamar haka....

    Dama dake nafara haduwa danayi aure tuntuni '' wayyo soyayya na dadi '..

    Batasan sanda ta murmusa ba ta ce uhmm ni dai banson Zuga fa..

    Haba Dijat dîna kinfi karfin Zuga duk abun da nake fada Daga cen kasar zuciya ta ne...

    Banki inwuni ina kallon kyakkyawa fuskar ki ba...

    Dijat uhmm wani Abu sai jibi nasan goben ba barina za su yi inkare miki kallo ba..

    Amma jibi InshAllah ina tare da ke dan barin kasar zamuyi ɗomin zuwa honeymoon cike da Jin dadi da son yawo ta ce dan Allah da gaske kake..

    Nan da nan yaga farin ciki a kan haka...

    InshAllah dagaske baby na ranar Lahadi zamu wuce banson a takura mana..

    Uhmm Allah yakaimu ta furta..

    Kashe gari

    Ta kama yau Juma'a gabadaya masarautar ta cike da dumbun jama'a ka sancewa sai an yi sallah juma'a za a daura auren.....

    Cen ma Kanon sai bayan juma'a za a daura.....

    Sossai Khadija tasha makeup gun kwararriyar ma'akaciya...

    Maman Adamsy ita da yan uwan nata zuwa suka yi wajen dijat domin daukar zafafan hotuna da ita..

    Sossai ta saki jiki suka dauki hoto da Ita.

    Shima Adamsy zuwa ya yi akayi hoton dashi......

    Lokaci na karatowa....

    Ana idar da Sallah juma'a.

    Jama'a suka cika domin sheda wannan daurin auren.....

    Sossai aka cika wajen inda na ji Ana fadin andaura auren Khadija Salihu da Angon ta Adamu Abdullahi a kan sa daki dubu dari biyar.....

    Sossai wajen aka fara busan sarewa da Algaita..

    Nan dan nan aka fara wasan dokuna.

    Na yayan sarauta yan jaridu sun samu aiki dauka suke babu kakkautawa....

    Adamsy cike da murna abokan sa da suka zo ranar daurin auren suka yi ta masa congrat har hawaye ya yi beyi zaton za a daura wannan auren bece yafasa.....

    Nan da nan aka shirin taron Walima bayan lasa'ar..

    Adamsy kai tsaye wajen su Mamy da yan uwan ya nuna sabar cikan da akayi da ƙyar mutum ke tura kafar sa...

    Ganin babu hanya ya fara neman yanda zeyi suga dijat domin daukar hotuna da ita....

    Wata baiwar ta ce anty dijat tana Sashin yayan ta Yarima Samad cen take sittin da kawayen ta...

    Haka ya sa ya ce a nuna masa kai tsaye suka nufa...koda suka isa sashin bayi basu hana su ka sancewa in ana sha'ani manyan mutane ba a hanasu shige da fice da anbaza camera ta Ko ina shi ya sa Sarki be hana ba....

    Bakin su dauke da Sallama suka isa sashin inda suka iske Dijat atsakiyan kawayen ta ana selfie...

    Tun da ya tsura mata idanu kasa sauke su yayi...

    . Cikin hanzarin su suka Shiga dakin '' babu ba ta lokaci akasha hotuna zafafa harda rungume ta tana ta kaucewa ganin bashida kunya gaban mutane.......

    Kano......

    Kusan karfe uku aka daura auren Ahmad da Asiya..

    Ka sancewa ranar an yi daure daure aure dayawa....

    Nan da nan aka ɗau shela andaura auren Ahmad salihu da Amaryar sa Asiya Muhammad....

    Bisa sa daki dubu dari biyar...

    Sossai Yarima Samad da Ahmad suka ringa hotuna na tarih.

    Su Faruk da Marwan da Aminu ba a bar su abaya ba..

    Sheik sossai yake cike da farin ciki...

    Shima wajen suna ta masa Allah ya sanya Alkhairi ka sancewa andaura auren nasa acen gabon tun misali karfe biyu......

    YARIMA Ahmad Jan Marwan ya yi bayan sun bar wajen daurin auren..

    Kai tsaye gidan su Asiya suka nufa...

    Iske Rahama suka yi awajen sun sa kaya iri daya sunsha makeup.

    Salma na zaune gefen su sai tabe baki take tana taunan cingam....

    Ganin Ahmed tafara lale lale da zuwan Angon Asiya...

    Sossai ya fadada murmushin sa ya ce pls antina dan Allah kibamu waje zan danyi magana da ita.....

    Rahama ta ce Salma tashi mu je mudawo ango ze gana da Amaryar sa....

    Suna fita Ahmad yadawo da kallon sa a kan Asiya dake chattin data nuna bama tasan da shi ba..

    Tabe baki ya yi ya ce ke Asiya kike Ko mene ne sunan naki ni sam bana haddace sunan ki....

    Dago kai ta yi tana kallon da Idanun ta da suka kada jajir da kuka...

    Suna hada idanu jiyayi ta sauya masa ta yi bala'in kyau '' kawai de daka kalle ta za ka san ba ta cikin walwala...

    Tabe baki ya yi ya ce uhmm ke kowace Amarya tana kyau ranar daurin auren nata amma. Bandake...

    Shiru ta yi tare da maida hankalin ta a kan wayar ta..

    Hakan ba ƙaramin ba ta masa rai yayi...

    Hannun ya sa ya Dago ta... Cikin zafin nama...

    Saida yakai ta bangon dakin..

    Zazzare idanu tasoma tana son ta ce lafiya kuwa....

    Gani ta yi ya sa hannun sa yana...................

    Ta ku har kullum kyauta Daga AllahƘANWATA

    09069080725

    https://youtube.com/channel/UCCb-59DLAXr2BDMl3XJQvIA

    Dan Allah channel dîna KYAUTA TV nan a sama kushiga ku danna mun subcribe 👆🏻

    Saina jiku Masoya na...

    Akwai Sabon Littafina wanda ze zomu ku da Zafi zafin sa..

    Mai Suna *RUDANI* kai Daga jin sunan kun san akwai akwai abubuwan masu ruda kwakwalwa ɗakuma ban Al'ajabi..

    Wannan littafin tsaf na shirya wajen baje basira ta..

    Kun san Alkamila baya rubuta shirme.

    KYAUTA DAGA Allah.

    Shalelen Jarumai writ associat...

    9️7️

    Yasa hannun sa daidai wuyar ta yana shafawa..

    Uhmm kinji tsoro ko kinyi tunanin wani abu zanmiki.

    Ba abun da zan miki Asiya..

    Yawwa maza ki fito mu ɗau hoto kin san zuwa gobe kina hannuna Ko dafatan kin shirya karawa dani dan ninan ba kanwar lasa bane.......

     Murmushi ta yi tana ganin zallan yarinyar da ke dibansa cikin sassaita muryan sa ta ce uhmm aini ban isa inkara da mijina ba '' wake wasa da wuta.

    Fada da Aljani aiba dadi 'babu nasara...

     Cike da mamaki yake nazarin kalaman ta ya ce duk kiyi kigama me kamata kiyi laushi ba...

     Cikin ɗAnne fushin ta ta ce dole ne in yi laushi in ina gaban ka' 'sanin danayi maka Ada daban yanzu kai mutum mafi daraja ne awajena kar ka damu duk abun da zakayi zan jure lada nake nema agun ubangiji na...

    Wanda ya ce duk wanda ya zalunce dan uwan sa InshAllah ba zai kyaleshi ba..

    Dan baya yafe hakkin wani a kan wani...

    Sossai maganar ta yashige shi cike da mamakin ta betaba sanin tanada hankali ba sai yau to jiji da kan da take nuna masa agida na mene ne rasa me ba sa amsa ya sashi Fadin Allah yakyauta yanzu mu je muyi hotuna so yake ya watsar da kudurin sa saboda kalaman da ta ce Allah baya yafe hakkin wani...

     Wata zuciyar ta ce kai harka saurare ta wacce take ce maka drever...

     Barin wani tunanin ya yi ya ja hannun ta suka nufo cikin jama'a..

    Sossai jama'ar wajen suka ringa Fadin waouh Amma fa Amarya da angon na sun mugun dacewa 'jibi fa..

    Wayannan kawaye biyu Rahama da Asiya' sunada Farin jini Samun attajirai.

    Haka akayi ta fira sossai agidan bikin a kan su......

    Yana sunsha hotuna sossai ya yi daidai dazuwan su mama Firdausi da Yarima da su Faruk harda Abban marwan da sauran a bokan tafiya sunzo da motoci guda Ashirin na daukar Amarya....

    Sossai unguwar ta cika makil...

    Yarima Samad karasowa ya yi ciki ganin Ahamd da marwan ya ce ya Salam yan iska daman kuna nan nake ta neman ku...

    Ahmad ya ce haba Yaya nifa angon Asiya ne kake zagina...

    Yarima Da Faruk rike baki suka yi suna kallon juna suka ce ah ah to gayamana tun da ba mu sani ba...

    Baza idanu yake ina ze hango Rahama...

    Hango ta ya yi tana kokarin shiga dakin Asiya ya dakatar da ita tahanyar kiran sunan ta..

    Ya ce kai mata ta kizo mana tunjiya kinmun wuyar gani..

    Uhmm zomu dauki hotuna dasu Mama firdausi amma je ki fitowa mana da Amarya....

     Murmushi ta sakar masa ta ce yawwa to ina zuwa yanzu zamu taho tare da ita.....

     Suna fitowa aka fara daukan zafafan hotuna masu daukar ido...

    Asiya sossai ta sake a kasha hotuna..

    Harda Ahmad suka ɗau hotunan....

     Basu wani ba ta lokaci ba suka ce za su tafi da Amarya gidan Sheik zata kwana har zuwa goben...

     Sossai kakkanin Amarya da iyayen ta suka mata Rakiya....

     Hakan ya sa aka bude motoci kowa ya shiga ba a zarce Ko ina ba..

    Sai gidan Sheik Abdurrazak..

    Koda suka isa nan da nan aka shiga yiwa Amarya da ango fada a kan tsoron Allah harda mahaifin Asiya yana gidan sheik sunzo tayashi murna karin auren sa...

    Hakan ya sa yazaunar da Ahmad da Asiya ya yi masu fada sossai mai ratsa zukata.

    Ahamd ɗuk wani mugun tunanin sa ya fara canzawa beyi tunanin akwai abun da ze hana shi yiwa Asiya wulakanci ba...

    Tasha kuka sossai harda shesheka sossai Ahamd yaji ta ba shi tausayi harna zargin kansa anya badan ya kwacewa Faruk bane take kuka ba..

    Sai yanzu yakejin haushin abun da yayi...

    Itako Asiya tana kukan rabuwa da iyaye ɗa kuma tunanin wani irin rayuwa zatayi a hannun Ahmad...

    Abban Asiya yana gama masu nasiha sheik da abokansa suka daura da nasu' ɗan ba ƙaramin Aya sheik ya jawo ya fassara ba......

    Yakara kashe musu jiki..

    Haka dai akayi cikin gidan da Asiya da taimakon yan uwan nata...

    Cikin gidan ba a barta abaya ba nasiha akayi mata sossai harda mama da Anty.

    Salma tana gefe tana cika tana batsewa wai ita a la dole abby ya mata wulakanci...

    Rahama bayan kowa yawatse takai Asiya dakin nata...

     Salma take masu baya ta yi ta ce yawwa anty Rahama ina son ganin ki....

    Hakan ya sa Rahama fadin gani Salma ya akayi ne naga tare muke tun dazun....

     Eh mana ina son Inkin fito nan kizo sashin Mama maganar sirri ce....

     Rahama cikin rashin kawo komai aranta ta ce to zanzo InshAllah dana gama......

     

    Sheik waya yake yi da baba Salihu a kan suna airport yanzu Jirgin nasu ze wuce amma suna tare da Yar ta Hauwa wacce zata wuce kano....

     Dan ta kuma shidawo Gabon tare da yayar mamar sa da zata rako su..

    Sossai Sheik yaji dadin bayanan shugaban Adalai.....

    Hassana cike da mamaki take ta ce Sheik tun dazu be nemeta ba tun da yaji andaura aure...

     Danna masa kira ta yi hakan ya sa ya Daga wayar tana hannun sa..

     Cike da Jin dadi Ya ce Amarya ce dakanta.

    Ta ce eh nice Wai ace tun dazun ba ka kirani ba..

    Haba honey..

     Murmushi ya yi ya ce kedai hassana dan yana cikin mutane be iya kiran ta da wani sunan...

     Taron jama'a sai a hankali kinji dalili na yi hakuri....

     Jin kamar anfara kiraye kirayen sunan masu tafiya kano...

     Ta ce to gashi zamu taso yanzu InshAllah...

     Sheik ya ce Allah yatsare ya kuma kawo min ke lafiya dake da yan rakiya ameen ta furta cike da jin dadi.......

     Babu ba ta lokaci duk suka Shiga a jirgi daya tashi dasu sararin Samaniya....

     

     Kano

    Yarima Samad zaune a dakin da suka sauka yana chat da Yusuf Sani yaro a kan gobe ya sa a kawo Saratu airport..

    Yusuf ya ce ah ah da kaina zan kawo ta kuma zanzo da mata ta zamu raka ku kwatano in yi muku Allah ya sanya Alkhairi tun da bansamu zuwa daurin aure ba..

    Sossai Yarima Samad yaji dadin haka..

    Ya ce da so samune da katsaya ayi shari'a da kai Yusuf...

    Yusuf ya ce ni ba lauya ba wannan ai aikin naku ne.....

    Yarima Samad ya ce yawwa akwai wata kanwar mata ta nan yashiga bashi labarin duk abun da ya faru ya kuma tura masa wannan video da Cctv camera dinsa ya dauka ya ce....

     Wallahi ina tsoron kada ta cutar mun da ita bare yanzu suna waje daya..

     Yusuf na kallon video ya ce subuhannalah wannan ai makira ce saita kashe mutum...

     Har video biyu wani tana Barbade wani kuma abinci zata zuba magani...

     Hoton roban poisson din daya amsa hannun ta ya tura masa...

     Yusuf ya ce yanzu ya kake so ayi kabada damar a kamata ne...

     Yarima Samad ya ce uhmm ba na son mahaifin ta yaji haushina zan sanar masa da komai inhar ya amince a kamata a hukuntata koda na sati daya ne....

    To zanma waya anjima.....

    Yusuf ya ce gaskiya koya ce baza a hukuntata ba.

    Ni sainayi kwana uku kadai ya isheta ladabi da hankali da nutsuwa....

    Yarima Samad Murmushi ya yi ya ce nasan ka bakada wasa nawan sai kajini Daga haka suka yi sallama...

    Kwatano....

    Shugabar Kasar Niger yazo shida matar Amarya...

    Gaban su akayi daurin auren...

    Cewar su jibi za su juya ɗan gobe su Karima za su dawo..

    Sossai yaji dadi sossai ganin matar sa Firdausi ta warke tsab kamar ba ita ba...

    Ganin ta ya sa ya mance wannan Amarya ya tare a dakin nata.....

    Cewar shi taree za su kwana' 'Sam taki aminta ta ce haba' 'nan fa ba gidan ka bane..

     Kabari saimun koma Niger din...

    Cike da Jin dadi ya ce Ah mu je mu kama hôtel Alkur'an baki isa ba.... Tanaji tana gani ya fito da ita Daga dakin....

    Kai tsaya fadar Sarki ya nufa nan ya zayyana masa cewar matar sa ce..... Cike da mamaki Sarki ya ce wannan baiwar Mamy ce da Salihu yakawo...

    Murmushi ya yi ya ce ba baiwa ba ce Nina turo su dan amusu maganin hauka kuma Alhmdulilah sun samu waraka na so ace nayi tozali da sarkin Adalai....

    Mai Martaba fashewa da kuka ya yi ya ce yanzu kana nufin matar ka ce muka ringa mata kallon baiwa....

    Iya Firdausi ta ce eh mai Martaba mijina ne kuma Yarima Samad da Abban shi sun ce kada mu taba bari asan Asalin mu..

    Hakan zeja mana magauta...

    Sarki Share hawayen sa ya yi ya ce kuma gaskiya ne hakan '' kubari zuwa jibi kuntafi gobe Yarima Samad za su dawo harda kariman kenan dasu za ka koma...

    Shugaban kasa ya murmusa ya ce kwarai kuwa..

    Nakama. Hôtel dîna iyalai na acen zamu kwana...

     Sossai mai Martaba ya yi mamakin wannan Al'amarin....

    Iya Fidausi koda suka fito ta ce masa su jira ta zata je ta sanarwa Mamy zanje kwana hôtel din..

    Dole yabar ta tafi yana tsaye yana kallon takun tafiyar ta cike da nutsuwa hakan yakeji babu kamar acikin mata...

    Koda ya fito iske su bodygar dinsa ya yi Alamun shi suke Jira..

    Sossai maganar ya karade masarautar harda wajen gari cewar Karima diyar Shugaban kasar Niger ce uwar ta matar sa ne...

    Anata kuskus labari ya je gun yan jaridu nan da nan suka fara wallafa bayanan da Aka basu agidan redio...

    Iya firdausi tana shiga sashin Mamy iske ta ta yi zaune kusa da khadija..

    Cike da ladabi ta sanar mata mijin nata ya ce a hôtel za su kwana...

    Sossai Mamy ta ji dadin hakan ta ce wayyo iya Firdausi yana kewar ki dole yaso ya zauna dake...

    Saita ji ina ace taga mijin nata...

    Iya Firdausi cike da Jin kunya ta ce mata saida safe kallon khadija ta yi ta ce Na Adamu saina dawo...

    Murmushi dijat ta yi mata ta ce yawwa iya Fiddo saikin dawo...........

    ***********************

     Kano...

    Kusan magrib Jirgin su sarkin Adalai ya sauka a garin kanon...

    Motoci na Alfarma guda uku sheik yatura dan dauko su...

    Sossai labari ya je cikin gidan amaryar Sheik ta iso...

    Hakan ya sa kowa yadawo farfajiyar gidan ana jiran isowar su...

    Yarima Samad dasu Faruk duk suna zazaaune awajen.... Hakanan su kaji gaban su na tsananta bugawa da karfi......

     

    Cen Filin airport nan da nan Motocin suka kwaso bakin zuwa masaukin su........

    Ahmad ne zaune kofar gidan shida Marwan suna tattauna walimar da za ayi a masarautar........

    Jin Horn din mota ya sa hankalin su yadawo akai....

    Faruk ya ce mu je muga Amaryan sheik mana....

    Tashi suka yi dukan su sukayo cikin gidan....

    Sheik bakin sa dauke da murmushi da kansa ya je budewa Baba salihu mota...

    Baba Salihu ganin Abun da yake shirin yi ya sa yaki fitowa harsai da Amarya ta fita ita da yan uwan ta akayi cikin gidan da ita.

    Sashin Mama Aka soma ajiye ta ana jiran su Sheik su shigo.....

    Sheik ganin Baba Salihu yaki fitowa ya ce..

    Haba shugaban Adalai ka fito mana....

    Caraf kalmar da ya furta ya fada a kan kunne su Ahmad harda Samad dake shirin dauro Alwala..

    Azabure dukan su sukayo wajen motar dan tabbatar da abun da suka ji....

    Zuwan ya yi daidai da lokacin da Baba Salihu yasoma sauke kafafun sa...

    Yarima Samad kafar yake bi da kallo yana nazarin ya san wannan kafar....

    Cikin zafin nama ya karaso ɗab da motar shida kannen sa.......

    Baba Salihu na karasa fita Daga Motar Caraf Idanun su ya tsarke cikin juna shida yayan nasa cikin............

    Ta ku har Kullum kyauta Daga AllahƘANWATA

    09069080725

    https://youtube.com/channel/UCCb-59DLAXr2BDMl3XJQvIA

    Dan Allah channel dîna KYAUTA TV nan a sama kushiga ku danna mun subcribe 👆🏻

    Saina jiku Masoya na...

    Akwai Sabon Littafina wanda ze zomu ku da Zafi zafin sa..

    Mai Suna *RUDANI* kai Daga jin sunan kun san akwai akwai abubuwan masu ruda kwakwalwa ɗakuma ban Al'ajabi..

    Wannan littafin tsaf na shirya wajen baje basira ta..

    Kun san Alkamila baya rubuta shirme.

    KYAUTA DAGA Allah.

    Shalelen Jarumai writ associat...

    9️8️

    Cikin zafin Nama Yarima Samad ya ce babaaaa..... Bakin sa narawa rungume shi ya yi shima Ahamad runguma yakai masa suka kankame sa kamar za a kwace shi...

    Shiko kukan zuci yake da farin cikin ganin su cikin koshin Lafiya...

    Gabadaya wajen yacika makil dan zuwa kallon sa.....

    Bakin Samad na rawa ya ce Abba 'meyasa ka guje mu bayan ka san inda muke wayyo Abba kazo mu tafi kwatano yanzu nan...

    Sheik da kallon su yana hawayen Farin ciki ya ce Ah Ah ɗana a bari zuwa gobe saiku tafi tare na muku AlKawari duk da nima ina son zama da shi zanbiyo ku nan da sati daya InshAllah.......

    Ahamad ya ce Abban mu kaki magana tun dazu sai Girgiza shi suke....

    Kallon sheik ya yi ya ce baya magana ne...

    Murmushi sheik ya maida masa ya ce yana Jin ka bakin sa ne ya yi nauyi...

    Faruk da isowar wajen cike da mamaki ya ce sarkin Adalai Kai nake gani Ko idanu na ne kemun gizo 'sai murza Idanun sa yake...

    Yarima Samad kara Girgiza Abban nasu ya yi ya ce Abba kayi magana magana wayyo Allah ku duba mun shi koya samu matsala a kunnen sa ne..

    Cikin Rawar murya Baba Salihu ya ce yarima Samad dina bansamu matsala ba a kunne na ba.

    Ganin ku nake kamar a mafarki..

    Cike da Jin dadi Ahmad yakara rungumar sa Ya ce Abba yau kafana kafar wlh duk inda kasa kafar ka 'nan nima zan saka..

    Yarima Samad ya ce ashe ma duk inda kasa kafa duk inda ya sa kafa zamu bisa za ka ce aiba zan yarda amaimai ta ya ce mana yana zuwa mu rasa shi ina ba zaiyuba mun azbartu..

    Baba Salihu kallon su yake cike da so da kauna da kewar su Ya ce karki damu ba zan kara guje muku ba.

    Amma ba zan biku kasar taku ba..

    Aminu da Marwan Mutuwar tsaye suka yi 'cikin zare idanu' suka ce kai kai anya daidai muke gani kuwa...

    Malam Isa ya ce daidai ne basai kun wanke Idanun ku ba..

    Kama hannun Baba Salihu ya yi ya ce Sarkin Adalai mu shiga kayiwa Amare nasiha harda surukar ka...

    Sheik da Aminin sa tsakiya suka sakashi.

    Aikuwa Su Yarima aguje suka take masu baya...

    Koda suka isa Farfajiyar gidan..

    Gabadaya gidan ya hargitse da hayaniya ka sancewar labari ya je musu Sarkin Adalai na kwatano wanda dansa ke yawo nema shekara da shekaru ya bayyana.....

    Hatta Rahama dake dakin nata cikin Azzama suka sauko ita da Asiya data mance ita Amarya ce...

    Kan kace me Anty ta sauko kasa ita da yan uwan ta dasuka zo tayasu murna Auren sheik.....

    Maman Salma da Salma kowa ya yi tsaye cirko yana son ganin shugaban Adalai....

     Cike da mamaki da ya wanzu a fuskokin su..

     Suke kallon takun baba salihu har ya iso cikin gidan..

    Ita Ko Rahama bakin ta na rawa ta iso gaban sa tare da durkushewa kasa '' Barka da Isowa Shugaban Adalai ''baba na mai kauna taaaa ta ja zancen cikin tsarkewa murya

    Anty da Mama da kowa wajen da suka sanshi sanda yake gadin.

    Suka ce Shugaban Adalai kuma Rahama Ko bakya ganine wannan Baba Salihu ne mai gadin gidan naku cewar wata makociyar su...

     Ahmad hannu ya yi mata Alamun karta kara wannan mummunar furucin a kan uban sa...

    Salma ta ce baba Salihu kaine daman Shugaban Adalai cike da kaduwa take kallon sa takara masa kallo masu cike da Al'ajabi....

    Shiko tsaye ya yi ya gaza fadin koda kalma daya ne tak..

    Anty dake sake da baki ta ce tabbas nayarda kaine shugaban Adalai dubi tsantsar kamanni da kakeyi da Abdul Samad...

    Yarima Samad 'baki ya kasa rufuwa ya ce Abba kayi magana yau ranar farin ciki ne...

    Kuka yasoma wanda ya sa gabadaya dakin jikin kowa ya yi sanyi ya ce nabi rana' iska Ruwa' zafi '' dan neman ka Abba.

    Naje kasashe.. Dan neman ka.

    Nadawo kano dan tunanin zan ganka..

    Amma Abba yau na ganka ɗakyar kake iya fadin kalma daya a bakin naka.....

    Ahmad ya ce wallahi yaya muyi masa uzuri tsabar farin ciki ne yahana shi magana yanda yakamata...

    Sheik Abdurrazak ya yi gyaran murya ya ce kowa ya nemi waje ya zauna...

    Samun wuri akayi duk suka zazzauna..

    Shugaban Adalai na kokarin zama 'Ahmad da Samad Ko wanne su yana rike da dayan hannun sa...

    Hakan ba ƙaramin dariya suka ba mutanen wajen ba..

    Sheik yabude taron da adu'a.

    Ya fara da cewa dayawa sun San Salihu' dayawa sun sanshi da Baba Salihu a garin kanon nan..

    Kaddara ce takawo sa ya badda kamannin sa..

    Wannan da kuke gani shi ne Shugaban Adalai ɗa dumbun sarakuna suke koyi dashi....

    Sarkin kwatano Alhaji Salihu Turaki..

    Gabadaya dakin ya ɗauka da ALLAHU Akbar.

    Masu waya suna ta daukar video a wayoyin su..

     Kowa ya yi tsit banda karar fanka da ajiyar zuciyoyi ba abun da kake ji a falon....

     Sheik ya ce wannan shi ne uban Abdul Samad miji ga yata Rahama...

    Mama Salma cike da nadamar wulakanta shi da take yi abaya ta ce Allah mai iko.

    Sannu da dawowa shugaban Adalai..

    Kada mata kai ya yi beyi magana ba..

    Dawo da kallon ya yi a kan Rahama ya ce Yata zo nan.

    Cikin hanzari takaraso.

    Kallon sa ya maida a kan Asiya ya ce kema zo nan..

    Jiki na rawa Asiya ta tafi wajen nasa..

    Dafa kan Rahama ya yi ya ce Rahamtullah ke haske ce agareni dani da Ahlina kin kankaro abun da yake aboye kin fidda duhu kin kawo haske....

    Sheik ya ce maganar ka kanayin sa a nannade ne yakamata ka fayya ce mana...

    Baba Salihu nan yashiga basu labarin abun da Rahama ta yi a masarautar '' duk da baya wajen Faruk duk ya zayyana masa komai..

    Sheik sake da baki yake kallon Rahama besan ta iya wannan jarumtar ba..

    Ya ce Rahama kincika yar halak wallahi ina Alfahari dake Ko ina ne zan iya buga kirji dake duniya tasan ke yata ce..

    Kamar yanda kika gyara gidan wasu ya Allah ya gyara gidan ki ya sa ki gama da duniya lafiya...

    Da ameen kowa ya amsa harda mama dake kuka...

    Baba Salihu dafa kan Asiya ya yi ya fara masu adu'ar zaman lafiya ita da Ahmad...

    A gaggauce aka fito da Hassana Amarya...

    Nan ma aka shiga yi masu nasiha da fatan zaman lafiya ita da sauran matan....

    Anty ta ce Amarya kidan bude muga fuskar yar kanwar tamu.... Dago kanta ta yi hakan ya sa Idanun su tsarkewa cikin juna ita da Anty...

    . Zumbur anty ta Mike hakama Rahama da Asiya 'har da Samaɗ da Ahmad 'ɗasu Faruk kallo yakoma kan hassana....

    Anty ta ce hassana kece..

    Dukar da kai ta yi ta ce Nice Anty Sa'adatu sossai anty ta yi mamaki dan taga a kwatano ta bar ta...

    Rahama ta ce wai daman kece Amarya babana..

    Sheik ya yi caraf ya amshe zancen hannu ta ya ce eh ita ce mamar taki....

    Mama sake da baki take kallon hassana Daga kasa har sama ta ce Ah lallai Allah yabada zaman lafiya.

    Kowa ya amsa da amen.

    Anty ta ce Ai hassana ke mace ce ta gari dan zaman danayi dake acen na gane hakan InshAllah lafiya lau zamu zauna...

    Sossai ta burge kowa da kyawawan kalaman ta...

    Kowa ya amsa da Ameen...

    Yarima Samad ya ce MashaAllah Allah ya sanya Alkhairi kowa ya amsa da ameen...

    Akarshe Ahmad da Samad sunce Sam daki daya za su kwana da baba salihu kuma goben tare da shi za su tafi kwatano.....

    Yarima Samad kiran mai martaba ya yi ya ce akwai wani babban bako da za su kawo na ban mamaki dan Allah adakatar da tafiya da digat agoben a bari sai jibi...

    Sarki ya ce InshAllah hakan za ayi na kagu naga wani bakon ne wannan shima Amarya yake son gani ne...

    Yarima Samad kasautaccen murmushi ya yi yana kallon baba salihu dashima murmushi yake..

    Ya ce eh bakon nason ganin khadija...

    Ita ma Mamy kiran ta ya yi ya ce sunada babban bako..

    Cike da za kuwa ta ce wanene dan Allah...

    Yarima ya ce kedai saimun zo..

    Amma kada a tafi da dijat harsai mun iso garin....

    Nan Mamy ta basu labarin Abban Karima tsohon shugaban kasar Niger Muhammed yusufu.

    Yazo daurin aure...

    Cike da murna Samad ya ce kai kai Dole mu dawo gobe nasan yazo daukar iyalin sa kuma karima ta nan.

    Mamy ta ce kai bakaga zuwan sa yanda garin gabadaya ya karade da firan zuwan sa..

    Duk firan da suke Baba salihu yana jinsu sossai muryan Mamy yake ratsashi ji yake kamar ya yi tsuntsuwa ya ganshi a gaban ta...

    Ga kuma murna zuwan shugaban kasar Niger dinnan hakan ba ƙaramin dadi ya yi masa ba..

    Yarima na gama waya da Mamy yadawo da kallon sa a kan Abban su dake Jan carbi yana tasbihi..

    Ahmad cike da kosawa ya ajiye carbin ya ce Abba yanzu yakamata kadan ba mu lokacin naka ''.

     Kallon sa yake yana murmushi yana cigaba da Jan carbin nasa...

     Ganin Yarima shima yataho ze daura Daga magiyan da Ahmad ke masa 'yasa shi ajiye carbin..

     Kallon su yake cike da kauna ya ce karkuga naki magana tun da na iso gidan..

     Hakan danayi yana Daga cikin Adalci mutum ya iya bakin sa acikin dunban jama'a inda ba zai rasa masoya da makiya ba...

     Ina son kuje Ku yi Alwala kuzo muyi sallah tare..

    Gobe sonake ku koma ku kadai kwatano...

     Cikin zazzare idanu Yarima Samad ya ce ina wallahi ba zaiyuba Allah ba zanyi kaffara ba...

     Ganin yanda launin dan nasa ya canza lokaci daya '' ya tabbatar masa babu wasa a tare dashi..

     Shiru ya yi ya ce to Aje Ayi Alwala...

     Cen Gidan Sheik kuwa bayan kowa ya watse..

    Kara hada kan matan nasa ya yi yamusu Nasiha...

     Mai ratsa zukata..

     Maman Salma ta ce uhmm duk wannan surutun ita karama ce ya isheni da ji haka..

     Ai ƙaramin abu baya zuwa gidan miji.

     Bare wanda ya taba aure abu Shiba sabo ba....

     Hassana kada kai ta yi tana jinjina kalaman mama...

     Anty shiru ta yi ba ta ce uffan ba..

     Sheik cikin son kawar da zancen ya ce..

     Yawwa Amarya tashi Sa'adatu ta miki jagora...

     Ita hauwa da bakin naki ambasu masauki..

     Cikin hanzari hassana ta tashi dan takosa tabar falon '' bin bayan anty ta yi suka haura kan matakalan step..

     

     Yana ganin wucewar du anty yadawo da kallon sa a kan Mama.

    Ya ce ke yanzu wace irin mace ce ke kina zubar da girman ki a Idanun kowa..

     Wannan matar nifa na auro ta..

     ba da ita zakiyi ba dani zakiyi babu dalilin daze sa kina jifanta da kalamai marasa dadi....

     Ko kin manta manzon Allah tsira da Amincin Allah da bazawara ya fara..

     Mama ta ce ai shi tashi bazawarar saida aka sabun ta masa ita..

     Kai kuma fa...

     

     Sake da baki yake kallon ta ya ce Eh lallai kin iya ba da Amsa....

     To zanshiga ga ledan nan kazar ki ce A'ciki..

     Iyeh me zanyi da kaza naga Ko adaren farko na da kai balangu ka kawo..

     Murmushi ya yi ya ce uhmm Kodai amaimaita daren Farkon ne.

    Ita hassana tahakura da mijin a yau.....

     Juya masa keya ta yi Shiko ya ajiye ledar ya ce uwar gida natafi saida Safe ki kula da kanki da adu'oi kariya....

     Kai tsaye ya nufi dakin hassana iske su ya yi zaune Anty na mata hira..

     Isowar sa ya sa shi fadin iye har fada aka bude yau a dakina....

     Anty ta ce daman kai nake jira intafi...

     Kallon hassana ta yi ta ce to Amarya na tafi saida safe..

    Hassana ta ce Ah Ah tun yanzu zaki tafi dan Allah ki tsaya...

     Sheik ya ce mu je Sa'adatu in raka ki daki nasan kina tare da gajiya....

     Anty ta ce yi hakuri Amarya wallahi Agajiye nake zanshigo da safe InshAllah...

     Sheik ajiye kazar hassana ya yi da wasu abun tabawa...

     Yarike na Anty a hannun sa suka yi ɓangaren nata....

     Koda suka isa dakin nata..

    Ya ce Sa'adatu nagode da kulawa Allah ya saka da Alkhairi...

     Sa'adatu ina Alfahari dake cikin iyalina Kin taka Rawar gani..

     Azuciyar sa sai fadi yake Sa'adatu nafi son ki a kan Ko wace mace aduniya banda mahaifiya ta...

     Afili kallon ta ya yi ya ce ga ledar ki' hannu bibbiyu tasa ta karba tana godiya ta ce uhmm. Wannan kazar har ka tunamun baya...

    Cikin tsigar wasa ya ce Ko inzo a maimaita ne..

     Ta ce A'a baniso akaiwa Amarya..

    Daga haka suka yi Sallama ya fi ce kai tsaye dakin Hassana..

    Ita Ko bandaki ta shiga domin yin wanka......

     

    Sheik koda ya isa dakin iske Hassana ya yi har ta canza kaya tasaka na barci...

     Nan da nan ya umarce taje ta dauro Alwala suyi nafila...

     Babu musu taje ta dauro koda ta dawo iske shi ta yi yana Jan carbi...

     Yana ganin ta basu ba ta lokaci ba wajen tada Sallah ba....

     Bayan sun idar suka yi ciye ciye abaki ya rinƙa bata...

    Daga nan salon ya canza..

    Aranar dai hassana ta jinjina wa Sheik ta Daga masa hannu.

    Bayan ya samu kansa ne Daga duniyar Daya tafi ya ce Hassana ta ce naam..

    Ya ce ke ta musamman ce...

     

    Asiya zaune ita da Rahama.

    Suna hira tunawa ta yi Salma ta ce tana neman ta..

    Hakan ya sa ta kira Samad ta sanar masa..

    Dan ya ce mata duk abun da Salma zatayi ta sanar masa..

     Cikin tsoro ya ce Ah Ah Rahama karki je zanmiki bayani gobe da safe inna shigo...

    Jin haka jikin ta ya yi sanyi sossai...

     Dawowa ta yi takwanta kusa da Asiya dake shirin barci....

    Wayar Rahama ne yasoma ring tana dubawa taga Ahmad ne...

    Babu ba ta lokaci ta Daga

    Ta ce kanina ya gajiyar taro...

    Alhmdulilah yabata Amsa..

    Ina kawar taki take ne yana mai lumshe Idanun sa sai yanzu ya tabbatar wa kansa abaya cen bawai kiyayya ba ce yake mata soyayya ce...

     Dan ba ta wayar zan mata magana kin san gobe da wuri zamu koma...

    Rahama ta ce Ayya Amma ni dai abarni in yi Sati daya...

    Inafa bazamu yarda ba wallahi... Kafarmu kafar ki...

    Dariya ta yi ta ce Ah abun yakai haka..

     Ta ce yama wuce haka bakada labari ne....

     

    Mikawa Asiya wayar ta yi ta ce amshi angon naki yana son magana dake...

    Jin haka Asiya ta tashi Daga kwance cike da ladabi ta ce yaya Ahmad inawuni...

    Murmushi ya yi ya ce lafiya lau ƙanwata...

     Rasa me ze ce mata ya yi Saboda artabun da suka sha da ita.

    Wani kunyar ta ne ya lullube shi ya ce daman na kira in ji Ko kina lafiya ne..

     Lafiya lau nake ta ba shi amsa atakaice.. Ta ce to zan dan kwanta saida safe kenan...

     Babu yanda ya iya hakanan suka yi sallama shida ita.......

     Kashe Gari....

    Bayan Sallah Asuba Sheik da Hassana ya yi karin kumallo '' hassana ta ce uhmm m'y love bakada dama fa...

    Murmushi ya yi ya ce to ke din ce cakwala dadi...

     Daga haka suka yi ta zuba love a dakin kamar bazasu fito ba...

    Mama tana kasa tana kallon agogo ganin har goma be fito ba...

    Tana jijjiga tana cika.

    Shigowar Salma ne ya sa ta maida hankalin ta a kan ta....

     Mama ta ce subuhannalah Salma meyake damun ki ne...

     Cikin Rawar murya ta ce Mama wallahi guba nasawa Rahama a cikin abinci '' jiya..

    Naita jiran ta tazo taci ba ta zoba..

     Hannun nawa ya taba robar 'cike da mantuwa nasa hannu abaki na..

    Shi ne tunjiya nake fama da matsanancin ciwon ciki ga Al'amin a dakin sirrin nasa ya kwana....

     Caraf kalaman ta a kan kunne Sheik..

     Cikin zabura ya karaso falon ya ce Salma guba kika sawa yata Rahama cikin abinci..

    Ina Abinci yake yafada a matukar razane...

     Bakin ta narawa ta ce wallahi Abba na ba.

     Karen gidan nan..

    Aguje suka yi farfajiyar gidan ganin Karen suka yi kwance a mace bakin sa duk kumfa...

    Innaliahi wa'inna il rajun ya shiga maimaitawa ya ce yanzu Salma rashin Imanin ki yakai ki kashe rai...

    Bari kuji yadawo da kallon sa a kan Mama ya ce koda Salma ta yi Asiri ɗan Adamu kada ya auri Rahama inada masaniya ɗan inda take zuwa makotan su ne sukazo sukaban labarin anga yata wajen...

     Ta aikata babban kuskure ta ruguza farin cikin dunban mutane tasa yayar ta cikin damuwa Daga baya Allah ya wanke ta...

     Shirun da nayi a wancen lokacin bawai yana nufin ba zan iya daukar mataki bane...

    Sai dai kawai nayi shiru ne saboda anason ka rinƙa yiwa mutum uzuri...

     Ance hali Zane ne..

    Tabbas Salma wajen uwar ki kikayi gado...

     Kallon Mama ya yi rai aba ce ya ce a yau dinnan nakeson ki barmin gidana...

     ya yi daidai da karasowar Baba salihu da Yayan nasa harda su Faruk da Abban Marwan... Su mama Firdausi da sauran su...

     Sunzo daukan Asiya...

    Ganin Mama tarike kafar sheik tana magiya da kuka ya sa cikin hanzarin su suka karaso wajen...

    Ita Ko Salma sai ihu take tana fadin cikina 'cikina cikina.....

    Ihun nata caraf ya sauka a kan kunne Rahama da Asiya harda Anty a ujajan suka fito ganin Abun da ke faruwa...

    Abubakar da yaji abun da ya faru salati suka fara tare da mutan gidan gabadaya......

    Rahamaa kuka tasoma mai tsuma rai ta ce Salma menayi miki ne.

    Salma mena tare miki kike son kiga bayana...

    Cikin dauriya Salma ta ce Rahama ni baki taba mun laifin komai ba..

    Mama ta nuna min duk abun da nakeso shi zanyi babu me hanani..

    Mama ta nuna mun kada in yarda ki fini da komai dan kina yar Gidan Anty...

    Ni kuma nasa wannan araina tun ina yarinya nasha Alwashin ba zan taba yarda ki wuce ni ba...

    Saima ki dawo kasa ta..

    Inada bakar zuciya da banson in bude idanuna inganki Rahama...

    Gabadaya kowa wajen yadau Salati 'yarima Samad da Al'amarin ya ba shi tsoro..

    Kama hannun sheik ya yi suka koma gefe ya ce dan Allah yabari akaita Asibiti....

    Sannan ya ba shi labarin ɗuk abun da ya faru acen kasar su...

    Sossai Sheik ya Girgiza ya ce Ah Ah yarima Samad ba zan kai SALMA Asibiti ba..

    Abubakar ya ce wallahi baza a kaita ba saide ta mutu anan wajen....

     

    Ganin da gaske suke ya sa YARIMA Samad shida Rahamaa suka ciccibe ta zuwa Asibiti..

    Koda suka isa umergency aka tafi da ita...

     Likitoci suka yi ca a kanta.

    Babban likita ya ce wannan yarinyar wanna iskan guban ya kashe abun da ke cikin nata..

    Dole cs za a mata..

    Yarima Samad ya ce a mata tare da sa hannu...

    Rahama kuka take tana adu'a Allah ya sa ayi nasara...

    Samad rungume da ita ya ce InshAllah za ayi nasara hubby na...

    Cen gidan kuwa...

    Kowa gidan antaru anata ba sheik hakuri a kan ya kyale Mama ta zauna ya ce Sam ba wanna zancen.

    Shidai be saketa ba.

    Ci da shan ta ze ringa aika mata..

     Amma fa saitaje makarfi ta zauna sai ya nemeta...

     Kuka take sossai Anty ganin ba abun da zata iya ne ya sata yin shiru tun da ya rantse tasan ba zaiyi kaffara ba....

    Mai hakuri inyayi Fushi to babu kyau.....

    Baba Salihu shima sossai abun da ya faru ya taba zuciyar sa....

    Yarima kallon agogo ya yi ganin lokaci na tafiya ya ce Rahama kizo mu tafi zanje tarban Saratu ne da za a kaita airport...

    Wa zaki samu daze zauna wajen nata....

     Rahama cike da damuwa ta ce Amjad kawanta ce jinina ce....

    Nafison inzauna da ita...

    Dan Allah ka bar ni...

    Hada rai ya yi ya ce ba za ki zauna ba..

    Tare zamu bar Asibitin nan...

    Kiran Abubakar ya yi wanda yake cen yana kuka ya ce Dan Allah yaya Habu ka taimaka kazo Asibitin nan badan Halin ta ba dan Allah zakayi....

     Da ƙyar Abubakar ya yarda yazo Asibiti koda ya Iso har ankaita dakin hutu..

    Kannen Sheik hassan da hussaini ne suka rako sa Asibitin..

    Suma kam cike da damuwa suke jinjina Al'amarin nan...

    Yarima Samad barin Asibiti ya yi da Rahama kai tsaye suka fara shirin barin kasar..

    Ita Ko Salma tanacen kwance batasan inda kanta yake ba...

    Hussaini da Hassan da Abubakar sai safa da marwa suke yi ganin shirun ya yi yawa..

    Fitowar babban docto ne ya sa dukan su suka nufo sa....

     Hussain ya ce likita dan Allah ku mana bayani ya zancen yarinyar da akayiwa cs....

     Akasalance likitan ya kalle su ya ce ku biyo ni office dîna....

     

     Kai tsaye suka take masa baya....

    Koda ya isa dakin zama ya yi kan kujerar sa tare da sanya medicale glas yana yan rubuce rubuce a kan file me dauke da Sunan Salma Abdurrazak....

     Yana kai karshen rubutun nasa ya yi sign a karshe tare da dankwala wannan penti bleu dake gaban sa a kan pepper.

     Bakajin komai sai ajiyar zuciyoyi..

     Dago kai ya yi yana kallon su ya ce Kune yan uwan Salma watau abun da yake Faruwa shi ne.

    Wannan gubar data shaka ya yi afectin din mahaifarta 'ya kone ɗuk wasu kwayayan halittar ta... Dan binciken mu ya nuna bazata sake samun haihuwa ba..

     Kuma cikin dake jikin ta' 'shima numfashin sa ya tsaya daman cikin dudu wata hudu zuwa biyar ne..

    Munyi nasarar cire mata cikin Daga jikin...

    Kuma Allah yataimake ta da matsalar ta tsaya iya nan da ace tasha guban ne babu abun da ze hana ta mutuwa....

    Gabadaya dakin sai Zufa ke keto musu kamar waɗanda suke cikin rana duk karfin Ac dake dakin....

    Abubakar bakin sa na rawa ya ce docto babu abun da za'iya yimata ta haihu zuwa nan gaba....

     Kada kai likita ya yi ya ce Ko ina za a je bazata haihu ba''amma ka san hikima ta ubangiji yana iya canza komai fatan ɗai Allah yabata lafiya....

    Mika musu takardan ya yi ya ce duk magunguna da za a siya mata suna nan...

    Yanzu tana dakin hutu..

     Zuwa la'asar zata iya farfadowa....

     Ruwan lipton da suga zaku tanadar mata..

     

    Jiki Asanyaye Abubakar suka yi musabaha da docto tare da masa godiya tare suka bar dakin da su Hussaini...

    Koda suka fito sun iske Anty da yayar ta..

     Ganin su ya sa suke nufe su hankali tashe.

    Kuka anty take ta ce Salma bakyajin magana kash da wannan bakar rana....

     Abubakar ba ta labarin duk abun da docto ya ce yayi...

     Salati suka dauka suna taba hannu ita da yayar ta ta...

    Wayar Abubakar ne yake ring yana dubawa yaga mama ce...

     Cikin hanzari ya Daga tare da barin wajen da suke..

     Mama ta ce Abubakar Salma ta kashe ni '' tasa mijina ya koreni Daga gidan sa...

    Shegiya tsinanniya yau ta sani zubda hawaye...

     Abubakar ya ce Mama ina rabaki da mugayen kalamai..

     ba ta labarin abun da ke Faruwa ya yi nan da nan tafara kuka tadaura hannu akai ta ce '' shi ke nan yanzu Salma bazata sake samun ciki ba....

     Wayyo Allah nashiga uku Dan Allah ka kula da Salma '' taya zanyi magana da Rahama ne....

     Na cutar da ita 'yarinyar nan ba ta taba nuna fushin ta akaina...

    Wayyo ni Aishatu na cutar da wanda ya fi kowa kaunata aduniya Abdurrazak.

    Abubakar cikin kwantar da murya ya ce Mama tun lokacin da muke son ganar dake gaskiya nida Abby a kan Yanda kike daukan Alakar Rahama da Salma kwata kwata kinki ba mu dama...

     Abby tun da kika ga yaki bari kizauna tura ne yakai shi bango shekara da Shekaru ake abu daya..

     Cikin kuka ta ce Dana Dan Allah kaci gaba da tausar mun zuciyar baban ka narokeka..

    Daga hk suka yi Sallama....

     Yana gama wayar da ita sai ga Shugaban Adalai da Sheik sunzo Asibitin harda Hassana....

     

     Abubakar tarban su ya yi tare da yi musu jagora zuwa cikin Asibitin..

     Koda suka isa 'Sheik da Shugaban Adalai gun likita suka nufa..

    Bayanin da yayiwa su Abubakar shiyakara yiwa su Sheik..

    Salati suka fara dukan su...

    Sheik na Girgiza kai yana kuka ya ce Salihu'' Aisha ta cutar dani kuka yake sossai...

    Wanda hakan ya daga hankalin docto din ganin babban malami yana kuka to abun azimun ne....

     Rarrashin sa suka farayi...

     Sheik ya ce' badan nayi AlKawari ba zan saki Aisha duk rintsi to da babu abun da ze hana ni yin haka nasan girman AlKawari..

    Kallon Shugaban Adalai ya yi ya ce taso mu je dakin da Aka kwantar da ita muganta...

     Koda suka isa dakin iske ta suka yi tana kwance fuskar nan nata ya yi fayau '' numfashin ta sama sama yake fita.....

    Adua suka yi mata sossai kafun subar dakin.

    Wayar Sheik ne ya fara ring yana dubawa yaga Samad ne.

    Dagawa ya yi ɗagacen ɓangaren Yarima Samad ya ce Sheik Imam agayawa Abba shikadai ake jira anan Filin airport din......

     Sheik ya ce gamu nan zuwa yanzu' Kace anzo da Saratu Ko..

    Samad ya ce eh gatanan da ankwa zaune kusa da Yusuf Sani Yaro dayazo shida Matar sa...

     OK gamunan zuwa ya furta tare da katse kiran...

    Suna Fitowa Sheik ya kalli hassana ya ce Hauwa yar ki tabi su Rahama airport ta ce da ita za a je..

    Hassana ta ce eh da ita za a je wai gun Mamy zata zauna ta ce...

    MashaAllah ya furta babu ba ta lokaci ba suka bar Asibitin tare da barin Anty da hassana ɗa su Abubakar da hussain da suke masu Adua Allah yakaisu airport lafiya....

    Cen Filin jirgin Shugaban Adalai na isowa gabadaya wajen kowa ya tashi hatta masu wucewa da waɗanda ke zaune'

    Sake da baki suke fadin wannan kamar shugaban Adalai ne sarkin da ba a samu irin sa acikin zamanin da muke ciki ba..

    Surutu ya barke a filin airport din....

    Basu ba ta lokaci ba kai tsaye suka Shiga Jirgin Samad Personnel...

    Koda suka tashi Daga garin kano...

    Awa uku suka yi jirgin nasu ya sauka a babban filin airport....

    Daman Yarima Samad ya cewa Mamy duk abun da take tabari ita da mai martaba duk suzo tarban su....

    Mai Martaba ya yi matukar mamakin Jin haka amma ya ce bara ya je yagani me yake son nuna masa.....

    Ka santuwa mai Martaba yazo Filin airport din..

    Gabadaya wajen ya hargitse da jama'a hatta yan Jaridu ba a bar su abaya ba..

    Dan daukar bayanai ba.....

     Duk inda Sarki ke jefa kafarsa '' waziri da fadawa da bodygar suna biye dasu abaya...

    Ita kuma Mamy bayi da jakadiya duk suna biye da ita...

    Daukar su Video ake har suka isa bakin jirgin suna jiran fitowar su Samad din.....

    Yayi daidai da yan Jaridu duk sunyi layi suma sun kafa camera din su dan daukar waɗanda za su fito ajirgin duk da basu sani ba.....

    Daga Cikin jirgin Shugaban Adalai suka ce ya fara fitowa....

    Hakan ya sa Cike da nutsuwa yake tafiyar sa mai daukan hankali tafiya mai nuna izza da Mulki tattare dashi...

    Yana cire kafafun nasa kamar baya so takawa...

    Kafafun sa ya fara fitowa sannan gangar jikin sa....

    Cike da Zallan Mamaki babban Dan Jarida yake kallon sa yana taka step din jirgin ya ce wannan ai Shugaban Adalai ne....

    Jin Furucin nasa ya sa Mai martaba da Mamy Dago kansu Arazane cikin gigita suke kallon sa yana saukowa..

    Mamy...........

    Taku har kullum kyauta Daga AllahƘANWATA

    09069080725

    https://youtube.com/channel/UCCb-59DLAXr2BDMl3XJQvIA

    Dan Allah channel dîna KYAUTA TV nan a sama kushiga ku danna mun subcribe 👆🏻

    Saina jiku Masoya na...

    Akwai Sabon Littafina wanda ze zomu ku da Zafi zafin sa..

    Mai Suna *RUDANI* kai Daga jin sunan kun san akwai akwai abubuwan masu ruda kwakwalwa ɗakuma ban Al'ajabi..

    Wannan littafin tsaf na shirya wajen baje basira ta..

    Kun san Alkamila baya rubuta shirme.

    KYAUTA DAGA Allah.

    Shalelen Jarumai writ associat...

    Masu bukatar tallah hajar su suna iya tuntuba ta wannan nombar dake sama..

    9️9️

    Mamy zazzare idanu tasoma cikin kidime take murza Idanun ta '' ta ce Ah Ah ku dubani kada Aljanu ne suka kama ni....

     Jakadiya ta ce shugaba ta ba Aljanu bane 'uban yayan naki ne da kansa kike hangowa..

    Mai Martaba cikin hanzarin yana gudu har yana tuntube kadan yarage yafadi..

    Baba Salihu yataho aguje ya tareshi yafada jikin sa....

    Kuka ya saki yana Fadin ɗana Ashe kaine babban bakon da akace nazo na gani..

    Kuka yake sossai yakara rungume dan nasa...

    Koda Yarima suka iso wajen kallon su suke bakin su dauke da murmushi.

    Yarima ya ce Mai Martaba ka sake shi mana har mu isa gida nan duk motsin mu a social media yake yawo...

    Sassauta rikon da Yayiwa Salihu ya yi yana goge kwallan da suka gangaro Daga Idanun sa....

    Mamy Mutuwar tsaye ta yi tana hawayen Farin ciki kallon sa take kamar sabon abu da ba ta taba gani ba..

     Cikin takun sa mai cike da izza da tsantsar mulki yakarasa gaban ta...

    Ya ce Habiba ta Salihu..

    Ba mafarki kike ba nine nan mata ta.

    sossai wajen ya ɗauki shewa gun yan kallo da yan jaridu da yan gani da idanu dansu karar...

     

    Mamy wani wawan runguma ta yi masa Sam ba ta damu da waɗanda ke wajen ba..

    Ta kara kankame shi '' tana fadin ya Allah Ya Allah kai kace mu rokeka mun roka ka Amsa mana Allah nayi AlKawarin zanyi Azumin sati daya bisa godiya a kan ni'imar da kamin ka dawo min da mijina cikin koshin lafiya...

     Kukan nata sossai yake shiga jikin sa 'Jin kukan yake kamar irin wacce aka taso mata cutar data dade da kwanciya..

     Shafa fuskar ta ya yi yana goge mata hawaye.

     Ya ce Habiba yau gaki ga Salihu' 'nima yau gani ga Habiba..

     Ganin sun kasa barin junan su Yarima yazo wajen yana fadin to yakamata mu wuce gida..

     Mai Martaba ya ce Salihu kazo mu zauna mota daya...

     Abban Marwan da ya yi Mutuwar tsaye yana kallon yayan nasa' 'shima aguje ya rungume sa..

     Yarima Samad ya ce Ah Ah mai Martaba mota daya Abban mu da Mamy za su zauna kajira mu je masarautar sai kayi yanda kake so dashi...

     Mai Martaba murmushi ya yi ya ce an yi mai wuyan ai mu je kawai...

     Babu ba ta lokaci suka fara kokarin barin filin airport din..

     Securite nan da nan suka budewa Mamy da Shugaban Adalai mota suka Shiga.

     Mai martaba shima yashiga tashi motar tare da mataimakan sa.....

     Yarima da tawagarsa motoci duk suka kwashe su...

    Inda Asiya da Rahama da Karima da hauwa 'mama firdausi kusan motocin su nabin juna..

     Saratu kuwa tana cikin motar Yusuf Sani yaro.

    Tare da matar sa.

    Babu ba ta lokaci motocin nasu suka baro airport din direct Masarautar gheuzo ta nufa...

     Baba Salihu rike da hannun Mamy wacce suke sauke ajiyan zuciyoyi kusan a tare..

    Kan su isa Masarautar labari ya isa gabadaya jahar Sarkin Adalai ya bayyana.

    Dayawa barin Ayyukan su suka yi dan zuwa ganin tabbacin maganar da ake yayatawa a gari.

     Wasu har garin da suke suka baro suna hanya gani suke motar tasu baya gudu yanda yakamata....

     Babban Al'ajabi hatta gwanoni na kasar duk sun turo mataimakan su dan su tabbatar da gaskiyar lamarin....

    Mataimakin shugaban kasar kwatano duk sun hallara Saboda suna ta wasi wasi anya za a sake ganin wannan shugaba Adalin.

    Ministoci kuwa Kam ba a cewa komai sunce sai sun ganewa Idanun su abun da ke wakana...

    Koda motocin nasu ya kunno kai Alayin tare da ba ta kara piiiii da karfi alamun abasu hanya..

    Saboda cinkoso kai kace ranar Sallah Idi ce.

     Motocin nasu gabadaya sukaja birki ka santuwa babu hanya..

     Yusuf Sani Yaro sai kallo yake anata fama dasu a kan su ba da hanya sun tsaya suna yan surutai wai su kanun labari suke nema.....

     Ransa amatukar ba ce ya fito bakin sa na rawa cikin kakkausar Murya ya ce inna kirga daya biyu zuwa biyar baku bude mana hanya ba....

     Uhmm dukan ku saina ankwashe ku..

    Bekarasa fadin abun da ze fada ba kowa wajen ya matsa Daga gefen titi kallo daya suka yi masa suka gane koshi waye basai sun bari ya tabbatar musu da ainihin sa ba.....

     Ganin anabasu hanya nan da nan suka karasa shiga layin cikin kalilan lokaci suka isa Masarautar dake cike makil da jama'a hatta bayi duk sun jeru kamar an saka su...

     Koda suka fiffito Daga motocin nasu..

    Gabadaya wajen suka fara kabbara suna Fadin ALLAHU Akbar.

     Shugaban Adalai karasowa cikin jama'ar sa ya yi yana Daga musu hannu alamun Jin dadin ganin su..

     Bakin su narawa suka fara fadin Barka da zuwa Shugaban Adalai Sarki mai Adalci.

    Sarki mai tausayin talaka.

    Daga musu hannu yake yi yana mai cigaba da tafiya tuni tawagar sa suka take masa baya...

    Koda Mataimakan gwanoni suka karaso cikin masarautar.

     Anan farfajiyar aka dakatar dasu..

     Mai shigar da sako ya ce nasan Daga gwanati kuke shugaban Adalai ba daya yake da sauran sarakuna ba..

    Yau yadawo yana bukatar hutu..

    Kuna iya ajiye ranar da kuke son ganawa da shi asa sunan ku saman list..

     Mataimakan suka ce babu komai dan mu tabbatar ne kuma mun gansa da Idanun mu....

    Kasa mana munason zantawa da shi tare da gwanoni nan da Sati daya kenan InshAllah...

    Mai shigar da sako yan rubuce rubuce ya yi ya ce InshAllah bakuda matsala..

    Yan jaridu suka zo kan layi suma suna neman Alfarma a saka musu ranar da za su gana da shi dan wannan sojan ya hana su rawan gaban hantsi...

    Mai shigar da sako ya ce wannan kam sai shi da kansa inya yarda ze gana daku kun san aikin tambayoyi ku dawo nan da kwana uku duk yanda ya ce zakuji....

    Cen cikin Masarautar kai tsaye Fadar Sarki aka nufa duk suka zazzauna masu mamaki nayi 'masu murna bakin su yaki rufuwa..

    Sarkin Adalai samun kujera ya yi kusa dana baban sa..

    Ya zauna' cike da nuna zallan farin cikin sa ya fara yiwa Allah godiya daya kawo shi cikin Ahlin sa..

    Kowa wajen sai Fadi suke Barka dazuwa shugaban Adalai Sarki me koyi da sunnah manzon Allah Saw.

    Shigowar shugaban kasar niger ne ya sashi fadada murmushin sa..

    Koda ya shigo runguma yakaiwa baba Salihu harda guntun hawayen sa ya ce Ashe rai kan ga rai..

    Shugaban Adalai ya ce kwarai kuwa gashi Allah ya sa ke hadamu anan InshAllah har gidan Aljanna zamu ringa haduwa....

    Cikin farin ya ce nagode sossai daka halarci bikin khadija..

    Kar ka damu Shugaban Adalai Khadija yata ce 'naji dadin ɗana zo daukar iyalina kana garin' zuwa karfe bakwai zamu bar kasar nan na yamma....

    Baba Salihu ya ce haba wani irin a yau dinnan za ka tafi nida nakeson ka kai jibi..

    Kayi hakuri shugabana ina uzuriruka ne'.

    Baba Salihu shiru ya yi yana nazartan kalaman sa ya ce Amma ba da Karima za ka je ba...

    Kasaitaccen Murmushi ya yi ya ce ai Karima yar ka ce inkace karta kara zuwa niger din ma na amince...

    Ah Ah bama zan hana ta zuwa niger ba..

    Nama ta miji anan garin kuma InshAllah nan ba da jimawa ba za ayi auren....

     Sarki ya ce MashaAllah Salihu wani mai sa'a ne wannan ze auri Karima..

    Faruk shi ne mijin ɗana zaba mata.

    Shikuma Aminu zan bashi hauwa..

    Marwan daman yana da wacce yake so na samu labari komai na tsara yanda ze tafi...

    MashaAllah MashaAllah kowa ya rinƙa Fadi awajen...

    Cike da murnan dawowar 'Mamy dake gefe suna sauraren abun da yake fade cikin cire kunya ta ce Shugaban Adalai yakamata kaje daga ciki kasamu Ko wanka kayi....

    Gabadaya kowa dawo da kallon a kanta suka yi..

    Mama Karama data rungumi Baba Salihu tana kukan farin ciki ta ce ɗana tashi kaje kaji abun da matar ka ta ce..

    Sossai wajen sun Fahimci Mamy tanason kadaita da mijin nata.

    Kuma sunsan tanada gaskiya shekara da shekaru Kowa keda bukatar haka amma suka ɗAnne sun San nata dalilin ya fi nasu karfi.....

    Faruk cike dajin dadi anbashi Karima ya fara godiya awajen shida Aminu...

    Marwan ya ce wayyo Ashe nakusa zama ango nima..

    Kusan kowa dariya ya sa..

    Ita Ko Karima cike da Jin kunya taje ta rike hannun Abban ta 'ta ce baba na Allah ya yi zamu gana dan Allah kabari zuwa gobe da safe saiku tafi tun da badani za a je ba....

    Cike da gamsuwa ya ce na ji daman na janye tun da naga shugaba na bayaso..

    Sossai suka ɗara Jin furucin sa.

    Sarki ne ya yi gyaran Murya ya ce tun da Dana yadawo ni Daga yau zan ajiye mulkin..

    Azabure baba Salihu ya kalle sa ya ce Ah Ah banaso tun Farko ma tursasani akayi na hau karagan mulkin nan yanzu kuma ataimaka a barni inzauna normal kamar kowa....

    Wajen gabadaya suka cika da tashin hankalin Furucin nasa a kan bayason Mulkin...

    Gabadaya wajen kuka suka soma suka ce Ranka ya dade muna murna mun ganka kuma za ka yanke mana kauna da irin mulkin ka mai cike da abin burgewa...

    Dan Allah kataimaka kacigaba da Mulkin nan mun rokeka...

    Idanun Baba Salihu kadawa ya yi jajir ya ce inhar kuka cigaba da takura mun a kan wannan Mulkin zan bar kasar nan..

    Sai dai Aba Yarima Samad duk abun da zan iya shima ze iya nasani ne...

    ZUMBUR Yarima ya tashi yana haki cikin zallan tsoro da Fargaba ya ce Ah Ah wallahi banaso banaso '' daukar takalman sa ya yi a hannun sa yabar Fadar cikin hanzari..

    Da mamaki ake kallon yanda uba da dansa suke gudun Mulkin nan.....

    Sarki ya ce karku damu zamuyi zama na mussaman a kan haka..

    Sannan Aje araba abinci ciki da waje dan murna dawowar ɗana kafun ranar da za ayi bikin dawowar sa...

    Mama Firdausi ta ce Sarki me Ran karfe ga Amaryan Ahmad nan munzo da ita..

    Hakan ya sa yadawo da kallon sa a kan Asiya da kanta ke a duke ya ce MashaAllah MashaAllah..

    Aje afiddo Khadija.

    Kuma a kira mijin nata Adamu....

    Akira mahaifan sa...

    Kai kuma Ahmad saika zauna anan za ayi komai agama asamu akai Amarya dakin nata tahuta..

    Ahmad ya ce kwarai kuwa ɗan kowa ya tara gajiya Tsoho..

    Mamy ta ce uhmm nizan shige ciki.

    Mama Firdausi ta ce haba ki tsaya inace tare keda Shugaban Adalai zaku shiga ciki..

    Babu ba ta lokaci a kazo da khadija 'Adamu da iyayen sa cikin hanzari suka karaso falon..

     Aguje khadija taje ta rungumi Abban ta tana kuka cikin Rawar murya ta ce Abba na kai nake gani koko idanu na ne ke min gizo....

     Murmushi ya yi tare da ɗago ta yana kallon fuskar ta data sha makeup sumbata yakai mata a goshi ya ce yar auta ta.

    Ni dinne kike gani nayi kewar ki sossai '.

    Baki yaki rufuwa gun dijat dan murna hakan ya sa tafara kukan farin ciki ta ce nagode Allah da ban bar kasar nan ba Sannan ka bayyana ba...

     Baba Salihu ya ce yata kin kara girma sossai hankali yazo MashaAllah....

    Zaunar dasu ya yi ya rinƙa musu Adua zaman lafiya tare yake da gajiya tattare da shi hakan ya sa ya Mike dan tafiya sashin nasa....

     

    Ambassador ya ce MashaAllah Sarki ina tayaka murnan bayyanar wannan babban Arzikin.

    Sossai suka zauna tare da Abban Karima suka yi lifaya da ciye ciye dan murnan babban rana...

    Mamy kusan tare suka bar Fadar ita da mijin nata..

    Mama firdausi da yan uwa da Abokan Arziki suka zaga da Asiya cikin masarautar ''...

     Kowa nata sa mata Albarka da yaba kyawun ta.....

     Ahmad ya ce Ah yakamata taje tagaishe da Mama Fulani...

    Kai tsaye sashin gidan yari suka nufa...

    Koda suka iso 'sun iske Fulani zaune tana Aman jini..

    Cikin tashin hankali suka ce lafiya kuwa..

    Ba ki da lafiya ne...

    Cikin tsarkewan Murya ta ce eh yau kwana uku nake Aman jini...

    Ahmed ya ce subuhannalah zanturo likitan masarautar ya duba ki...

    Amma nasan kinada labarin Salihu Turaki ya bayyana Ko....

     Cikin rinannu Idanun ta da suka kada jajir dan wutar azabar cutar dake cin ta...

     Ta ce na ji ana maganar yadawo da kafafun sa '' kuka tasoma ta ce Ahmad ba zan iya hada idanu da Sarkin Adalci ba...

     Ahmad tabe baki ya yi ya ce kuma fa da kunya fa...

     Daman nazo in nuna miki mata ta Asiya ance kece ake fara kaiwa suruka ki gani..

    Ni kuma kece ta karshe da zan gabatar mata...

     Bakin ta na rawa ta ce Ahmad Allah ya sa Alkhairi wannan kawar Rahama ce...

     Eh kawar Rahama ce ko haramunne auren nata kiban Aya da fassara yana jujjuya hannun sa..

     Shiru ta yi sai huci take sama sama Alamun tana jin jiki sossai...

     OK nalura baki lafiya zanbarki yanzu zaki ga docto...

     Daga haka suka fice shida magoya bayan sa..

    Mama Firdausi rike take da hannun Asiya har sashin nata...

    Koda suka isa sun iske Rahama nacen tasa labulaye ta feshe Ko ina air frechner....

     Kamshin turaren har waje ake Jin sa...

    Guda sossai Iya Firdausi take yi yayin da suka iso dakin Karima bakin ta dauke da murmushi ta ce yau dai gamu dakin ango Ahmad..

    Shigar da Asiya suka yi da kafar dama..

    Sossai mama firdausi da iya Firdausi suka ringa yiwa Asiya fada da nasiha mai ratsa zukata....

    Koda suka kammala abun da za su yi barin dakin suka yi Rahama kadai ce ta tsaya wajen Asiya Amma hankalin ta yakasu gida biyu tun da suka zo.

    Tunanin halin da Salma take ciki take yi tanason taje daki ta kira su.....

    Rahama ta ce to Asiya ni kinga tafiya ta basai najira Ahmed ba kanwar mamar ki data rako mu ta ce gobe zata juya...

     Dan haka bara zanyi waya gida....

    Asiya cikin kuka ta ce Ah Ah Rahama karkimun haka dan Allah mu tafi tare..

    Sake da baki Rahama ke kallon Asiya wani guntun murmushi ta yi ta ce eh lallai ma matar nan..

    Ni da Aka kaini gidan miji kin tayani kwana ne koda yake kwananki daya agidan..

    Kema kin san mijina ba zai bari ba..

    Ahmad kuwa nama na ɗânye ze cinye innace zankwana....

    Ah Ah ni dai Dan Allah tsoron dakin nakeji...

    Sallamar Ahmad ne shida Yarima Samad yajawo hankalin su a kan su...

    Yarima samun wuri ya yi ya zauna yana karewa haduwar dakin kallo 'ya ce nine na rako Ahmad dakin Amarya dafatan zaki rike mana shi Amana....

    Rahama ta ce kace ɗai yarike mun ita Amana ai wannan son kai ne..

    Murmushi Ahmad ya yi yana kallon yanda Samad ke jifan Rahama da wani kallo masu cike da tarin Ma'anoni....

    Ganin haka ya sashi fadin yaya Samad zanje gun Abba indawo..

    Yarima ya ce ina ba za ka je ba kun hade gobe yana cen yana hutawa za a dame shi...

     Kaikuma nasihar da zan maka kaji tsoron Allah Ka sani aure ibada ne ba shashanci bane...

     Rike da baki Ahmed ke kallon Samad yana yarfe hannayen sa ya ce ikon Allah nibanta ganin an rako ango ba kuma ana zagin sa gaban iyalin sa..

    Rahama cikin Jin dadi wasan nasu ta ce to ai rakiya yamaka gun Amarya duk abun da yafada dole ka shanye...

    Kada kai Samad ya yi ya ce Atoh kedai gayamai.

    Kama hannun Rahama ya yi ya ce to Ango mu mun tafi saida safe...

    Allah yabamu Alkhairi Ahmed yafada yana gyara malun malun rigar sa....

    Yarima yana fitowa Sashin Ahmad shida Rahama kai tsaye wajen Yusuf Sani yaro suka nufa tare da musu ban gajiya shida matar sa....

    Sumayya cike da Jin dadi take yaba kyawun halayyar Rahama da kyawun fuska...

    Yusuf ya ce Allah yabata duka 'ilimi' kyaun hali'' kyaun halitta.

     Sumayya ta ce ai mijin nata ba Daga baya ba shima haka ɗai suka yi ta firan su shida matar sa.....

    Baba Salihu kwance a gadon Mamy agajiye' Daga shi sai boxer Mamy hannun ta na bin jikin sa tana masa massage..

    Sai wash yake fadi yana narke Fuska...

    Gabadaya jiyake wani yarr yarr a jikin sa....

     Ganin kamar massage din ya ishe shi ya tashi yazauna 'yana karewa Mamy kallo da take sunne kai kasa dan kunya....

    Ya ce Habiba dan matso mugani..

    Kaga me tafada tana kokarin barin dakin batayi aune ba ta ji ya......

    Taku har kullum kyauta Daga AllahƘANWATA

    09069080725

    https://youtube.com/channel/UCCb-59DLAXr2BDMl3XJQvIA

    Dan Allah channel dîna KYAUTA TV nan a sama kushiga ku danna mun subcribe 👆🏻

    Saina jiku Masoya na...

    Akwai Sabon Littafina wanda ze zomu ku da Zafi zafin sa..

    Mai Suna *RUDANI* kai Daga jin sunan kun san akwai akwai abubuwan masu ruda kwakwalwa ɗakuma ban Al'ajabi..

    Wannan littafin tsaf na shirya wajen baje basira ta..

    Kun san Alkamila baya rubuta shirme.

    KYAUTA DAGA Allah.

    Shalelen Jarumai writ associat...

    1️0️0️

    FINAL FINAL FINAL.

    YA ALLAH INA GODIYA A GARE KA DAKA NUNA MUN KARSHEN LITTAFIN NAN.

    ALLAH KABANI LADAN DAKE CIKIN SA..

    KUSKUREN SA YA Allah kayafemun zunubai na.......

    Masu fitar mun da novel da masu siyar wa da masu karantawa Allah kafini sanin su.

    Ya Allah kai mana maganin su...

    Duk wanda na yi wa ba daidai ba a kan wannan Littafin ina rokon sa daya yafemin kurakuraina da waɗanda suke mun magana ta private kila wasu abubuwan sun rike ban bashi Amsa da wuri ba ya ɗauki abun kamar wulakanci to amun afuwa agizanci ne na ɗan Adam..

    Godiya gareku masoyana duk inda kuke.

     Ina mika godiya ta ga yan kungiya ta Jarumai writ associat.

     Maman shkura.

    Maman Nusaiba bestie.

    Maman haneef.

    Khadijat M Abdullahi.

    Fadila Sani Bakori.

    Maman Amatullah.

    Ya Mu'allim.

    Basira..

    Ummi Iman..

    Dasaraun waɗanda ban Ambata ba amun afuwa....

    Ba zan manta dake ba

    Zahra bukar Allah ya saka da Alkhairi..

    Mujaheeda Matar Malam jinjina ga yabon girma....

    Hassana da hussaina yayyena kuna kan gaba...

    Babban Aminiyata hajiya umma Funtua duk ina jinjina a gare ku..

    Anty Bashira Buraima ina yaba kokarin ku a kan jajircewar da ba ni karfin guiwa a kan book Din..

    Allah ya saka muku da Alkhairi gabadaya har da fans dîna...

    Mu Hadu A sabon Littafina mai suna RUDANI....

    ƘANWATA complet din sa zaku same shi a Arewa Book duk wanda beda App din to ya sauke shi awayar shi Ko wani littafi zaku same shi acen...

    Last Page

    1️0️0️

    Mamy ta ce Ah meye haka kuma tana rufe Idanun ta...

    Kizo ingayamiki abun da nake nufi tare da jawo ta takoma cikin dakin..

    Niko Rufe musu kofa nayi nace bara inje dakin Ahmad inga me yake aikatawa.....

    Ahmad ya ce haba Asiya tun dazu sai fama nake dake kinki cin Abincin nan me haka yake nufi ne..

    Yatsare ta da zararan Idanun sa masu rikita wanda ake kallon sa....

    Haba Asiya kici naman nan Ko kadan ne please...

    Kallon sa take taka san idanu a hankali ta furta na koshiiiiii.

    Uhmm kin san ɗai dole kici jawo plate din ya yi gabanta yana tsakalo naman tare da yankan ta da ƙaramin wukar dake hannun sa...

     Kokarin jawo ta yake itako cike da fargaba tafara ja da baya tana Girgiza kai nan da nan Idanun ta suka kawo ruwa...

    Haba Asiya yau ina jarumtar ki ina tsiwar taki take ne kice duka yabi iska..

    Shiru yakeji banda faduwar gabanta babu abun da kunnan sa ke jiyo masa...

     Sossai ya takure ta tare da rirrike mata hannu cikin hada rai yake turo mata naman dan dole ta ringa ci kamar tana tauna magani haka take hadiye naman '' suna gama cin abinci yakai ta bandaki wai ta yi brosh da wanka..

    Kikau ta tsaya bandakin tana zazzare idanu Alamun yafita ganin haka ya sa yafita ya ja mata kofar...

     Dawowa dakin ya yi ya zauna yana Murmushi Kayan ciye ciyen su yakwashe yakai kitchen.

    Din ta..

    Dakin da yake mallakin ta bandakin ya shiga ya yi wanka shikadai yana murmushi.

    Nace oh AHMAD KO ME YAKE YIWA MURMUSHI..

    Fitowar ta ya yi daidai da isowar sa dakin cikin kayan barci sossai yake kare mata kallo ganin ta maida kayan data cire..

    Cike da kunya tafara kokarin zuwa sashin nata..

    Jin ya damko hannun yarike cike da zare idanu ya ce Asiya ina zaki je ne ?

     Barci nakeji zanje nakwanta na tara gajiya ta marairaice fuska Alamun hutu take bukata..

    Bata Ankara ba ta ji ya dagata cak sama..

     Wayyo Allah mama ina za ka kaini ne..

     Kimun shiru nan ba dakin mama bane dakin mijin ki ne kuma in kikayi wasa uhmm ba za ki ji da dadi ba..

     

    Furucin sa ya sa ta yi gum da baki tana kallon sa ya dire ta a kan gadon nasa..

     Cike da nutsuwa ya fara kai hannu jikin ta hakan ya sa ta ji wani yarrrr tsigar jikin ta na tashi karo daya a rayuwar ta data taba tsintar kanta awannan yanayin..

     Ahmad ganin kamar bazata samu ta dadi ba dole sai ya murzawa idanun sa ruwan rashin mutunci Sannan za su daidai ta....

     Duk yanda Asiya taso takwace hannun sa ina takasa iyawa domin ya nuna mata sawun giwa ya take na rakumi..

     Cike da kwarewa yake sarrafa ta son ran sa 'itako kuka take sossai iya gaskiyar ta' ganin yana neman ya rabata da kayan jikin ta..

    Hakan ya sa tarike hannun sa gam cikin kwallan daya taru idanun ta ta ce yaya Ahmad ka tausayamun wallahi ban iyawa...

     Wani kasaitaccen Murmushi ya sakar mata yana juya kalaman ta..

     Ya ce inhar ke ba za ki iyaba ni ance miki ba zan iya bane.

    Daman ba iyawar ki nake nema ba yakarashe zancen tare da hade bakin nasu waje daya sossai yake ba ta kiss masu zafi masu daukar hankali Wanda shi kansa besan ya iya ba...

     Atakaice dai Ahmad sossai ya samu ya ratsa Asiya wacce tun tana iya kiran sunan Rahama harta fara kiran sunan mahaifiyar ta dan neman ceto...

     Ahmad yana cikin Jin dadin duniyar sa da Asiya data koma kamar tsumamma ya ce wayyo Asiya Ashe haka kike da dadin gaske wayyo kinfi zuma..

    Wayyo daman haka aure ke dadi na saura ina bin abokai rakiya dakin amaren su..

    Wayyo Mai Martaba Allah ya saka maka da Alkhairi daka kaini gidan Dadi.

    Wayyo Rahama Allah yabiya ki ta dalilin na samu koramar dadi...

    Sossai yake ta zuba sambatu mara iyaka..

    Har Burin nasa ya cika..

    Sannan ya fara dawowa hayyacin sa..

    Yana goge gumin daya keto masa.

    Nan da nan yaji bayan sa yarike dan ba ƙaramin diba Yayiwa Asiya ba..

     Itako kwance take banda hawaye babu abun da Idanun ke fitarwa sai sheshekar kuka..

     Hakan ne yajawo hankalin sa a kanta cikin hanzari ya saka boxer din sa yana kare mata kallo tun daga boob din ta har zuwa kasa..

     Ganin aika aikan da ya yi mata hakan ya sa shi ruɗewa ya ce Asiya yi hakuri dan Allah ba da gangan nayi ba sossai ya rikice bakin sa na rawa ya ce wani taimako zan baki ne..

     

    Da ƙyar ta iya bude bakin nata ta ce Kataimaka kaban ruwa insha Sannan ka hadamun ruwan dumi wayyo kasa ne ze tsage cikin gigita take magana tana taune lip dinta...

     Beyi kasa agwuiwa ba cikin hanzarin sa ya je yadebo ruwan yabata tasha '..

    Kokarin tashin ta yake' Tafasa uban kara sakamakon Jin wani radadi da azaba cen ka san ta..

    Cikin lallaba ya dauke ta cak yakai ta bandakin tare da hada ruwan wankan......

    Sossai ta ji dadin wannan ruwan tun tana jin zafi har takoma tana jin dadin ruwan......

     Daren ranar ɗai barci sama sama Asiya ta yi sakamakon wannan radadin datake ji a kasar ta........

    Asuba Ta Gari.....

    Kashe Gari...

    Rahama cikin hanzarin ta ta kammala Ayyukan ta.

    Ta hada break din su.

    Sannan ta hada wa Asiya nasu ita da Ahmad...

    Isowar Karima n'e ya sa ta fadada murmushin ta..

    Ta ce Karima Yawwa gwamma da kika zo dauki wannan trey din kikai sashin Asiya kice mata ina nan zuwa ɗana gama break...

    Cike da ladabi Karima ta ce ya Shugaba ta daman Mamy ta ce tanason ganin ku keda Yarima Samad...

    Rahama ta ce babu matsala muna gama break yanzu zamu zo cen.

    Maza kije ki kaiwa Asiya in tana bukatar wani taimako dan Allah ki taimaka mata kinga zamuje wajen Mamy kafun na leko ta...

    Fuska dauke da murmushi Karima ta ce an gama ranki yadade shugaba ta takarashe zancen tare da barin dakin cikin Azzama hannun ta dauke da trey din break din su Asiya....

    Itako Rahama koma cikin dakin ta yi ta iske Yarima Samad yana waya a kan maman Maryam dake wajen sojoji ya ce ku tsaremin ita dakyau..

    Dan muna wani hidima ne agidan namu ina son duk wani abun da kake kaje ka samu rajistra agaya masa jibi nakeson a shirya mana Zaman kotu da Alkali Muhammad Haruna...

    Kuma Asanar aduk social media wannan taron shari'a da za ayi yanda wannan maganar ta bazu a duniya a kan ubana...

    Haka nakeson yanzu ma ta bazu kotu ta wanke sa.

    Waɗanda ke zargin sa Ko kokonto a kan sa za su tabbatar sharri ne aka masa...

    Yana gama wayar yajuyo système gaban sa..

    Cike da zallan so da kauna yake kallon Rahama ya ce hubby kece a tsaye amma zaki Katon ciki fa yafada yana mai tsare ta da idanu....

    Zare idanu ta yi tana kallon cikin nata daya fara tasawa ta ce wani irin Katon ciki ni dai banga wani cikin daya turo ba...

    Oh baki gani ba Ko.

    Gyada kai ta yi Alamun eh bangani ba....

    Batayi aune ba sai ji ta yi ya zura hannayen sa cikin rigar ta yana shafa cikin ahankali Wanda ya sa baby cikin nata suka fara wutsil wutsil suna matsa acikin cikin nata...

    Dariya ya yi ya ce kinga Baby ma sun San kamshin uban nasu...

    Kunne sa ya sa daidai saitin hudar cibiyar ta wai so yake yaji motsin su...

    Sake da Baki take kallon sa ta ce Amma fa Amjad yau na tabbatar kai yaro ne...

    Dan ba ta fuska ya yi ban gane ni yaro bane daga ina duba ajiya ta..

    Yaro ai baya iya yiwa mace ciki...

    Rufe masa baki ta yi ta ce oh kaide bakin ka akwai sakin zance..

    Kekuma naki akwai baro zance ya maida mata martani tare da kashe mata idanu...

    Kasaitaccen murmushi ta sakar masa ta ce nayi shiru uhmm damar Mamy ke son ganin mu nida kai..

    Taso mu je muyi break Daga nan sai mu je Ko...

    Yawwa mata ta kice komai ya kammala sai ci..

    Kama hannun ya yi tare da matse ta a jikin sa ahaka har suka iso falon yana makale da ita...

    Suna gama break basu tsaya ba ta lokaci ba kai tsaye suka yi Sashin Mamy....

    Inda suka Iske Har Mai Martaba da kan sa yana dakin.

    Kowa ya tattaru harda su Adamu da Abban Karima dasu iya firdausi..

    Harda Yusuf Sani Yaro....

    Mamy zaune take taci ado cikin manyan kaya na sarakuna sossai take baza kamshi...

    Shugaban Adalai yana zaune gefen ta....

    Sallamar Karima yajawo hankalin mutane a kan ta cike da ladabi ta nemi waje ta zauna....

    Khadija zaune take akasa..

    Haka ma Adamu.

    Manya kadai ne suka zazzauna...

    Abban Marwan ya bude taron da Adua' ya ce mun taru ne anan da abubuwa da yawa...

    Na Farko dai Ansaka auren Faruk da Karima '' Aminu da Hauwa''' sai Marwan da Halimatu..

    Nan da sati biyu masu zuwa InshAllah....

    Abu na gaba shi ne Mai Martaba zeyi sauka Daga kan karagan Mulkin ze baiwa Salihu babban yayana wanda Ada shi ne Sarkin.....

    Abu na gaba shi ne Ayau dinnan Za a wuce da khadijat garin katsina cen inda mijin ta yake da dangin sa..

    Iya Firdausi kece zaki mata jagora Daga can saiki tafi kasar taku lokacin biki nayi zaku zo keda yan uwan naki.....

    Sai abu na gaba Maganar zama kotu nan da zuwa jibi inshAllah an sanar agidajen redio da TV har da kafafun sadarwa ta yanar gizo.....

    Sannan wannan jami'in da kuke zaune ya nuna Yusuf Sani yaro da hannu ya ce shi ne wanda yakamo Saratu Ko muce ya yi silan kamata Kuma ya yi mana AlKawarin zama zuwa lokacin Shari'a da yabada nasa shidun.

    Sannan Abdul Samad shi ne lauyan me kara..

    Fulani da maman maryam da Saratu sunce bazasu ɗau lauya ba...

    Yana gama jawabin sa ya ce inda me magana acikin ku yana iya yi....

    Shugaban Adalai ya yi gyaran Murya ya ce maganar Mulkin nan banaso banaso...

    Abaiwa Sani kanina Ko mai Martaba yaci gaba da rikon Abun sa...

     Jin anrike kafar sa.

    Cikin tashin hankali yake kallon mahaifin nasa yana kokarin durkushewa agaban sa...

     Cikin hanzari ya tare sa ya ce Ah Ah Abba na ya za ka durkushe mun nifa danka ne dan Allah kar ka sa nayi aikin sabo.....

     Dago sa ya yi tare da zaunar da shi kan kujerar sa ya ce Abba me kakeso in maka dayakai saika durkushe agaba na yafada cike da damuwa a fuskar sa...

    Mai Martaba ya ce Ina son ka Amshi mulkin nan Salihu...

    Jiki Asanyaye ya ce na karba inhar shi ne muradin ka dan Allah kayafemun ba ta maka rai danayi dahar ya sa kake ganin ba zan maka biyayya ba..

    Ina kin mulkin nan ne saboda tanada hadari tanada Alkhairi...

    Hadarin shi ne banson Allah yakamani a ranar gobe Alkiyama da hakkin wani akaina...

    Amma tun da yazama saina rike din Allah ya tayani riko yafada cike da raunin muryan dake nuna ba haka yaso ba...

     Gabadaya wajen jikin su ya yi sanyi ganin launin sa ya canza..

    Mamy duk da waje daya suka kwana hakan be hana ta satar kallon sa ba ji take kamar akara basu lokaci ba ta gaji da ganin mijin nata ba...

    Abban marwan kuka yake sossai yana Rokan yayan sa gafara...

    Shugaban Adalai ya ce Sani ba ka min komai duk abun da ya faru sharrin matar ka ne...

    Kusan karfe daya suka tashi taron inda Su Adamu suka fara shirye shiryen tafiya da dijat shida dangin sa da iyayen sa...

    Tare da iya Firdausi da jakadiya...

    Sossai khadijat ke kukan rabuwa da mamy..

    Baba Salihu sossai Yayiwa Khadija nasiha a kan biyayya Sannan Mamy ta daura da nata tana kuka sossai mai tsuma rai a kan yar autan ta...

    Mama karama itama nasihar ta yi mata...

    Koda za su bar gidan da khadijat sossai Rahama da khadija suka rungume juna suna kuka sossai..

    Adamu tsaye yake yana kallon Rahama yanda ta murje ta yi mugun haske fatar ta tana wani sheki.....

    Yarima Samad yana lura da kallon da Adamu kewa Rahama hakan ya sa shi zuwa Jan Rahama Daga jikin Dijat ya ce yi shiru my wife yana rungume ta gaban Adamu ya ce karki damu kinji ai zaku ringa waya....

    Maza kije wajen Asiya an barta ita kadai.....

    Dawo da kallon sa a kan dijat dake kuka ya yi ya rungume ta cikin muryan lallashi ya ce dijat dîna kiyi hakuri kinji aure ke kawo rabuwa amma ai ba mu rabu ba..kina tare damu kuma zamu kawo miki ziyara InshAllah nida Rahama da zaran ta haihu..

    Da gayya ya fada ɗan Adamu yaji...

    Shiko Adamu ɗabe kawo komai aransa ba ya ce MashaAllah Allah yaraba lafiya...

    Ahmad ne ya fito cikin shigar sa na Alfarma sanye da Alkyabba ya ce har kun shirya ne mu je rakiyan nata Ko iyakar mu Airport...

    Rungume dijat ya yi yana kuka yana mata nasiha.

    Azuciyar sai fadi yake uhmm kema zumar zaki bayar kamar yanda na kwasa.

    Afili kuma sai fadi yake yi hakuri Sister...

    Shugaban kasar Niger tsaf shima ya shirya ze koma kasar sa..

    Hakan ya sa su waziri da hadimai za su masu rakiya har filin airport din Samad Plan....

    Kusan a tare motocin nasu suka bar gidan tare da Su Khadijat.....

    Koda suka isa filin jirgin shugaban kasa shida Amarya sa Samad personnell suka Shiga...

    Su Adamu kuwa sukabi Samad air plan wanda ake diban passgen A'ciki...

    ************************

    MAKARFI

    mama sossai ta rame ba ta da kwanciyar hankali..

    Dakin da take kwana Sam ba ta sake wa..

    Saboda dakin tun ginin da ne kuma haryanzu ba a gyara ba..

     Ga Azaban Zafi ga tsauro..

    Mahaifiyar ta zubaida ta ce Sam bazata kwana mata a daki ba...

    Dan me yara basu kashe auren nasu ba..

    Sai ita ce za a koro Daga gidan miji kuma a kan taurin kai..

     Duk wasu nau'i na aikin gidan Mama ce take yi babu sauki...

     Motar ta data bâri ta tuna ta kira Abubakar ta ce dan Allah mota ta kasiyar mun ka aiko mini da kudin koda ƙaramin gida ne insiya wallahi wahala nake ga zafi ga tsauro..

    Abubakar cike da tausayawa Ya ce Mama wallahi na yi wa Abby Maganar Motar nan ya ce wai Yarsa Rahama ce tabaki kudin..

    Da dai da kudin Salma ne ze ba da Asiyar..

    Ni kuma banda isashen kudi sai an yi Albashi kudin dake hannuna aka tura wajen kai gaisuwa...

    Mama ta ce subuhannalah yanzu Abubakar nawa zan samu hannun ka wallahi tun safe banci wani abun kirki ba sai koko kuma wallahi dari biyar gareni gaba da baya inada kudi dubu dari takwas a dakina amma mahaifin ka hanani shiga dakin ya yi yazanyi da rayuwa ta...

    Abubakar cike da sassaita nutsuwar sa ya ce karki damu inada dubu goma zanturo miki.... Yanzu nawa Abby yake turo miki ɗuk Sati...

    Cikin kasa da murya ta ce dubu biyar..

    Kai kai Mama dubu biyar shi ne yake karewa a sati kauye ne ra..

    Mama cikin bacin rai ta ce banson shashan ci dubu biyar arana sai incinye shi ni dai inajiran ka....

    Suna sallama ya zauna yana murmushi ya ce oh Mama ba a Saba da wahala ba..

    Salma sai a yau ta farfado Idanun ta ɗuk sun kumbure '' fatar jikin ta ya yi duhu sossai...

    Ahankali ta bude Idanun ta tana kallon waɗanda ke dakin Daga Abby sai Hassana dan cikin Anty ya tsufa Sheik ya hanata yawo....

    Hassana cikin hanzari taje tana shafa kan Salma ta ce ɗaughter sannu Ko...

    Gyada mata kai ta yi tana Daga kwance...

    Abby ya ce sannu kinji Salma ya jikin naki nan ma gyada masa kai tayi...

    Shiko gyara zaman nasa ya yi kan kujera ya zauna ya ce yawwa Salma yau za a ba mu Sallama.

    Zankira Al'amin yazo ya ɗauke ki yakaiki gidan nasa..

    Tun safe nake kiran layin sa baya shiga kuma ya ce yau dawuri zezo daukar ki....

    Zuru Zuru take kallon mahaifin ta..

    Hassana ta ce Abban Rahama kamar yanda ta ji anty tana fadi please kabar ta mu koma gida tare inta warke saita koma gidan nata....

    Sheik ya ce haba kina ganin yadace inkai wacce babu digon Imani agidana..

    Sam ba zaiyu ba yata ce ba zan iya canza ta ba..

    Saide ina iya yimata iyaka da gidana....

    Cikin rarrashi hassana ta ce dan girman Allah kayi hakuri wallahi yarinya ce tana iya canzawa duk da ance hali zanen dutse ne.

    Amma inada yakiniin zata canza kodan ishara data gani....

    Sheik ya ce Amarya tun da kince Allah an gama amma tasani ba ta kara Jin dadi na...

    Hassana ta ce na ji na amince wataran za ka wuce ne uba da ya sai Allah tafada tana murmushi yawwa dafatan su Imran da kannen mahaifiyata sun isa lafiya Ko..

    Dan nabar wayata gida..

    Sheik cike da kallon so yake binta da shi ya ce eh sun isa lafiya Amarya ta...

    Zanje indawo sai bayan Magrib sannu da kokari innadawo sai tattaara mu wuce gida Ko....

    Hassana ta ce babu matsala habibi byee byee shima byee yake mata tare da barin Asibitin....

    Al'amin zaune yake gaban shugaban tsafin nasu yana fada sossai..

    Ya ce garin ya kabari Matar ka tara sa cikin jikin ta..

    Kaida muka ce maka muna son Jinin ta ɗana jariri..

    Tun da babu dan yanzu muke bukatar kurwan ta....

    Al'amin cike da damuwa ya ce tana Asibiti fa Ko farfadowa batayi ba...

    Shugaban kallon banza yake binsa da shi ya dauko wani Katon kwarya ya zuba ruwa acikin sa...

    Nan da nan sai ga Salma ta bayyana tana kwance gadon Asibiti idanun ta abude ya ce kai shasha leko ka gani tun da kace ba ta farkaba..

    Kuma duk Alamu mahaifin ta gidan sa zekai ta jinya inhar tana cen bazamu iya daukan kurwan ta ba..

    Yanzu da duhu ya yi zamuje Asitin tare dukan mu ka kai mu har dakin da take ciki...

    Cikin Rawar Murya ya ce babu matsala.....

    Hassana bayan ta idar da Sallah zama ta yi tana lazimi barci ya fara daukan ta ka santuwa tana tattare da gajiya.....

    Hakan ya sa bataji karar bude kofa ba.....

    Ahankali yaturo kofar nasa...

    Ya leka sossai yaga barci Hassana take itama Salma Alamun barci take...

    Hakan ya sa shi komawa agurguje ya shigo da matsafan da suke sanye cikin jajayen kaya hannun shugaban su dauke da kwaryan jini......

    Ahankali suke taku har suka karaso dakin..

    Dube dube suke yi ganin babu kowa a bandakin....

    Ogan nasu sai zazzare Idanu yake yana kallon mabiya bayan sa...

    Da kowannen su Idanun sa zagaye yake da bakin abu....

    Ahankali suka tura kofar kokarin dannawa dakin key suke ya yi daidai da murda handle din kofar da Sheik ya yi shida Aminin nasa....

    Cike da tsoro Ogan Tsafin ke kallon waɗanda ke shigowan ganin Sheik hankalin su ya yi mugun tashi ba kadan ba musamman Al'amin da shima yake sanye cikin irin shigar su....

    Cikin tsoro da gigita Sheik ke kallon kwaryan hannun su tunanin sa Ko sun kashe masa yar sa ne...

    Arazane ya ce Isa maza ka kira mana securite..

    Da likitoci harda yan sanda...

    Ogan nasu uban dariya ya saka ya ce me za su mana yanzu zamu ba ce agaban ka...

    Sheik najin haka. Ya fara adu'a ba kakkauta wa wanda ya sa suka kasa ba cewa a dakin nasu........

    Shigowar jami'an tsaro da Securite ya Daga hankalin Al'amin ita kanta Salma cike da tsoro take kallon matsafan...

    Hassana firgit ta tashi tana salati ta ce innaliahi nashiga uku me zangani...

    Kankace me jami'an tsaro sun saka musu ankwa a hannayen su..

    Sheik cike da ban Mamaki yake kallon Al'amin shida Aminin sa..

    Suka hada baki wajen Fadi kai Azzalumi maza ka sakar mana yar mu kafun kabar dakin nan...

    Shiru ya yi yana kuka ya ce sheik ba laifi na bane Salma ce ta jefani cikin wannan halin ta ce innemo kudi kota halin kaka ne da bazata iya zama da talaka ba.

    Sheik tabi ya shiga yi ya ce Amma an yi Sakarai Salma ba ta da wuta ba ta da Aljanna.

    Dan haka wannan ba hujja ba ce illa son zuciya da kwadayi...

    Wani gigitaccen Mari Sheik ya sakar masa ya ce za ka sakar mun yata Ko sai nasa jami'an tsaron nan sun gyara mun kai....

    Bakin sa narawa ya ce nasake ta Saki daya..

    Sheik ya ce saki uku za ka mata mata..

    Dole yacike sauran...

    Jami'an tsaron figan su suka yi cikin zafin nama suka jefa su a motar su..

    Wanda haka yajawo hankalin dumbun jama'a a kan su.......

    Salma kuka take sossai iya karfin ta Jin abun da ya faru tana jin rayuwar ta beda Amfani musamman da hassana ta gayamata bazata kara haihuwa ba..

    Duk saitaji ta tsani mahaifiyar ta..

    Kuka take iya karfin ta tana fadin wayyo Ni Salma haka rayuwa ta juya dani..

    Yaya ta Rahama baki da hakki akaina shi ya sa Allah yake kareki Allah kaban lafiya inroketa yafiya kafun nabar duniya tun da akace ciwo ya taba mahaifata dawuya in rayu....

    Hassana ta ce Ah Ah InshAllah Salma zaki rayu kada ki karaya...

    Katsina...

    Bayan isha'i a bokan Adamu suka yi tsantsani wajen rako sa wajen Amaryar sa dijat........

    Koda Abokan suka siye baki..

    Iya Firdausi da Jakadiya masaukin su aka kaisu....

    Adamu sossai ya sa dijat suka yi nafila Sannan Da ƙyar ta yi ciye ciye duk da tana jin yunwa.....

    Aranar dai Dijat tasha kuka sossai ɗan Adamu be je da wasa ka sancewa ya dade yana jiran wannan ranar....

    Iya Firdausi tana masaukin nasu suna ta zuba soyayya ita da Abban Karima yana fadin gobe yake so tazo Niger din..

    Ta ce babu matsala megida duk hutawan da mukayi a hôtel be isheka ba..

    Ya ce inafa ya isheni kece kawai nake gani yanzu agabana ban ganin kowa.........

    **************************

    Bayan kwana biyu...

    Kwatano...

    Ayau ne takama za ayi zaman kotu..

    Tun da sassafe kowa yashirya cikin gidan harda Asiya da Rahama...

    Asiya Sam ba ta son hada idanu da Ahmad tun da abunnan ya faru Shiko hakan Ko a jikin sa dan fadi yake hutun kwana hudu nabaki babu ruwana a fili kuma sai janta da hira yake....

    Baki Daga Bohicon duk sun hallara zuwa kotu....

    Shugaban Adalai cike da izza ya fito Daga cikin masarautar magoya bayan sa..

    Duk suna biye da shi a baya...

    Basu ba ta lokaci ba dukansu wajen tafiya kotu ba..

    Ko kan su isa cen..

    Fulani da Maman Maryam da saratu duk suna cen......

    Kowa yana kotun hatta Alkalin yana zaune kawai shugaban Adalai ake jiran karasowan sa..

    Abban Maryam shida Amaryar sa suka iso kotun...

    Liman Bohicon mahaifin mamy da Firdausi da Yaya Auwal da Sani duk kowa ya kama waje yazauna..

    Koda shugaban Adalai ya shigo hakan ya sa gabadaya kowa wajen y tashi tsaye hatta Alkalin saida ya tashi..

    Kujerar da shugaban Adalai ze zauna akai baya cikin jerin waɗanda kowa yazauna tashi daban take tasha ado sossai irin na yan sarauta......

    Yana zama kan kujerar kowa yazauna hadda Alkali muhɗ Haruna....

    Mamy kallon mijin nata take kamar wani bakon mutum sossai ya yi mata kwarjini a idanu musamman dataga yazauna ya ja girman sa.....

    Me bayani dake zaune tashi ya yi yasoma magana yayin da yan jaridu suna daukar bayanan sa da camera da lasifika.....

    Kamar yanda kuka sani taron shari'a ne za ayi tsakanin shugaban Adalai da wasu mata guda uku....

    Wanda suka hada baki wajen cutar dashi..

    Cikin su akwai yar matar sa..

    Akwai matar kanin sa..

    Sannan da baiwa.

    Alkali gyaran murya ya yi ya ce Ko akwai lauyan wanda yake kara...

    Yarima Samad tashi tsaye ya yi ya ce ya mai girma mai shari'a gani nan..

    Sunana Abdul Samad Salihu Turaki...

    Nine lauyan mai kara..

    Alkali ya ce akwai lauyan masu kare wanda ake kara...

    Me ba da bayanai ya ce babu yamai girma mai shari'a...

    Alkali rubuce rubuce ya yi Sannan ya Dago kai yana kallon Samad ya ce lauyan mai kara muna sauraren ka...

    Yarima Samad cike da takama ya fara bayanin duk abun da ya faru zuwa abun da suka bugawa mahaifin sa...

    Sossai kotun ta yi tsit babu abun da kake ji sai karar fanka...

     

     Alkali sossai ya jinjina Al'amarin ya ce lauyan me kara Ko akwai tambayoyin da zakayi waɗanda ake zargi

    Yarima Samad gaban nasu ya isa yana kallon Maman Maryam ya ce kotu tanason tasan sunan ki..

    MAMAN MARYAM.. Ta ce sunana Farida Ahmad.

    Mata ce awajen Garba..

     Yarima ya ce Ko zaki iya fadawa kotu dalilin daya sa kuka kulla wa shugaban Adalai sharri..

    Maman Maryam ajiyar zuciya tasauke tana kallon mijin nata dake zaune kusa da Amarya sa...

    Ta ce nayi haka ne da ina son mijin ƙanwata...

    Gabadaya kotun zazzare idanu suka yi hatta Abban maryam din..

     Yarima Samad ya ce shi ne kika zabi ku kulla masa sharri..

    Ta ce A'a nayi nayi ya rabu da habiba ya aureni yaki amincewa '' shi ne nayi masa haka dan in tozarta shi yaji bakin cikin danake ji inna bude idanuna ina ganin sa da ƙanwata alhalin Nice nakeson sa tun farko shi ne ya zabe ta yabarni...

    Mamy fashewa da kuka ta yi sossai a wajen....

    YARIMA Samad ya ce mungode malama Farida...

    Gaban Fulani yakoma ita ma ya bukaci ta gayawa kotu sunan ta......

    Fulani ta ce Sunana Salamatu bashir...

    Yarima gyara Tsayuwar sa ya yi yana kallon agogon hannun sa ya ce...

    Ko zaki gayamana dalilin dayasa kuka kulla wa shugaban Adalai sharri..

    KUKA ta saka sossai ta ce.. Ta ce wallahi hassada ce Saboda banaso yaci gaba da mulkin nafison ta dawo hannun mijina da ɗana...

    Yarima Samad murmushi ya ce mungode Farida....

    Gaban Saratu ya nufa ya ce Sarki yawo yau dai Allah yakawo ki nan zaki iya gayawa kotu sunan ki...

    Saratu Muhd tafada ataikaice...

    Saratu kina iya gayawa kotu meyasa kika aikata mugun aiki..

    Bakin ta narawa ta ce Wallahi Fulani da Farida suka sani sunce inhar ban aikata ba za su kulla min sharri sata kuma nasan hukunci sa a masarautar...

    Akarshe da na nemi intona Asiri sai sukasa akasheni shi ne dalilin guduwa nabar masarautar......

    Alkali dake saurarann nasu ya ce kotu ta gamsu cewar Anyiwa Shugaban Adalai sharri ne dan haka kotu ya wanke sa...

    Fulani anyanke miki zama gidan Yaro tsawon shekaru 15..

    Kema Farida haka..

    Ita kuma Saratu bisa turasasa ta da suka yi shekara goma zatayi..

    Gabadaya kotun tadauka da ALLAHU Akbar...

    Mamy zuwa WAJEN farida ta yi kafun awuce dasu ta ce yar uwa na yafe miki duniya da lahira kuka take. Sossai ta rungume Farida.....

    Kallon ta tamaida kan Fulani ta ce kema na yafe miki..

    Hakama Saratu.....

    Sossai kotun ya tashi da hayaniya sai cece kuce ake yi...

    Abban Maryam zuwa ya yi gaban Farida ya ce yanzu gidan Yari zaki je koda zaki fito wallahi kin tsufa baki moriya dan haka na sake ki...

    Kuka ta fashe da shi tana fadin wayyo kaicona...

    Nan da nan aka fara bawa shugaban Adalai hanya ta bisa jagoran jami'an tsaro.....

    Kusan kowa Agajiye suka dawo gida..

    Liman Bohicon sossai ya yi kuka kuma Yayiwa Yarsa Farida fatan Allah ya kaddara saduwar su...

    Kuma Yayiwa Shugaban Adalai murna da samun yanci..........

    Bayan Sati biyu bikin Su Faruk ya gabato inda su Rahama da Samad da Asiya sune kirjin biki..

    Sossai suka gyara Karima ta koma kamar ba ita ba....tasha gyara sossai wajen mamy ita da hauwa...

    Hauwa zaune kusa da Mamy cikin zazzakar muryan ta ta ce uhmm Mamy ni dai da za a bar nawa bikin saina kara girma...

    Mamy tunstsirewa da dariya ta yi ta ce to Saboda me hauwa'u na...

    Uhmm ni dai wallahi ba na son rabuwa dake Alkur'an tana kwabe fuska cikin shagwaba..

    Murmusawa Mamy ta yi tana shafa kanta ta ce karki damu ai mijin daze aure ki da mijin Karima duk anan masarautar zaku zauna '' Shugaban Adalai ya ce Sam ba zai iya nisa dasu ba dan abokan arziki ne wanda suke wa Samad so na tsakani da Allah...

    Wayyo Mamy dadi kashe ni cewar hauwa

     Cike da ni nishadi suke firan su.....

    Wannan karan sossai masarautar takara amsar gayyatar baki Daga nesa dana kusa...

    Yan uwan hassana duk sun hallara Daga Gabon...

    Hassana ita da Sheik suka zo bikin ka sancewa cikin anty ya tsufa shi ya sa aka barta agida..

    Mahaifin Karima da mahaifiyar ta Iya Firdausi sossai suka yi tsantsani da jama'ar su zuwa wajen daurin auren yar su...

    Faruk da Aminu da Marwan wannan ranar babu kamar su dan kaya kala daya suka saka anko farar shadda harda Samad da Ahmad

    Sa dakin daurin auren nasu Samad ne yabiya kowani ango millions daya...

    Sheik sossai ya samu tarba mekyau musamman wajen shugaban Adalai nan nan yake ta yi da sheik..

    Sheik shi ne yayiwa Faruk wakilin ango....

    Sossai wajen daurin auren nan yatara dunban jama'a harda manyan manyan kasar irinsu Shugaban Kasar kwatano patrice Talon duk da Arne ne saida ya halacci wannan gagaramin taron..

    Faruk zoga murna awajen sa shida Aminu mussaman ɗa suka ji ance nan masarautar za su zauna murna fal acikin su bazasuyi nisa da Samad ba...

    Sai kusan karfe shidda na yamma aka kai Amare kowacce dakin mijin nata..

    Hauwa ta yi kuka sossai dan batayi zaton aure nan kusa ba...

    Hassana ta ce haba yata keda zakiyi murna koba komai kina kusa da Mamy..da kalamai masu taushi suka rarrashe ta....

    Bayan kwana biyu da bikin iya Firdausi suka koma kasar tasu cike da kewar Mamy da Karima..

    Dan Karima ta yi kuka sossai Faruk ya ce mata karta damu za su je tare ziyara dan wannan rarrashin ta dan samu sukuni...

    Kowa ya watse Alhmdulilah har Sheik yakoma tare da hassana Amarya..

    Koda suka isa sun iske anty babu lafiya jikin nata radau yadau mugun zafi....

    Yayar ta ce kusa da ita tana shirin kaita Asibiti dan Salma dake kwance haryanzu babu lafiya dan wannan kuban ya yi nasarar taba zuciyar ta...

    Kwance take tana kallon yanda su Sheik suka rikice dan kai Anty Asibiti......

    A gaggauce suka isa..

    Likitoci suka yi ca a kanta inda kai tsaye suka nufi blok da ita....

     

    Koda babban likitan ya fito samun sheik ya yi da zancen dole sai dai ayi mata CS sheik ganin halin da take ciki cike da ruɗewa kada ya rasa matar sa ya ce Ayi mata aikin su gaggauta...

    Sossai likitoci suka rufa a kan ta suna kokarin yi mata aiki... Sai ga nakuda tazo da karfin ta wanda ya sa tana nishi ta jefo yar ta '' katuwa Wani sabon nakudan yakara tashi kankace me ta sake haifo ya mace' likitocin cike da Al'ajabi ganin wannan ƙaramin cikin nata ta haifo yan biyu mata masu kama da Rahama sak komai nasu iri daya...

    Kuka suke tsala wanda hakan ya tabbatar wa sheik har an gama operation din.

    Babban Burin sa ya jikin sa'adatu yake.....

    Koda likitar ya fito cike da Zufa da kuma gajiyar wahala da suka sha a kan ta..

    Bakin sa dauke da Murmushi ya ce Sheik matar ka da kanta ta haihu ta haifo tagwaye mata...

    Sheik bakin sa dauke da Murmushi ya ce MashaAllah MashaAllah tagwaye nasamu.

    Agurguje ya nufi wajen hassana da yayar anty ya sanar musu da batun haihuwa yaya biyu..

    Cike da Farin ciki hassana ta ce wayyo abun dadi tagwaye ta haifa MashaAllah.

    Sheik zumudi ya sa shi kiran Shugaban Adalai ya sanar masa haihuwa har Rahama saida yakira ya sanar mata...

    Cike da Jin dadi ta ce Abby zanzo suna...

    Ah Ah Rahama kiyi zaman ki na ji ance kema kina hanya Allah yaraba lafiya '' Rahama cike dajin haushin hanata zuwa ta ce Abby na ji ance ranar suna za a daura auren yaya Abubakar..

    Sheik ya ce kwarai kuwa haka muka tsara.....

    Dan Jim ta yi ya ce lafiya kuwa Rahamatullah..

    Bakin ta dauke da damuwa ta ce dan Allah dan zatin ubangiji Abby kadawo da Mama sossai take kuka.....

    Jikin sa a mace ya ce Rahama tun da nake dake baki taba rokona wani abu ba ka sancewa na mahaifin inna ce Ah Ah ban miki Adalci ba '' daman inada niyar dawo da ita nabar ta ne ta dan sha iskan gida..

    Nan yakwashi abun da ya faru da Salma yafada mata..

    Sossai take kuka ta ce yanzu Abby Salma bazata sake samun ciki ba.

    Innaliahi wa'inna il ai rajun take ta maimaitawa...

    Sheik ya ce wannan Aya ce agare ta da duk mai irin halin ta...

    Karki damu ana gobe suna zan dawo da mahaifiyar ki...

    Daga hk suka yi Sallama...

    Kwanan su daya a Asibiti aka sallame su..

    Sossai Anty ta yi murna da samun yaya mata..

    Ranar suna yara sukaci sunan Hassana da hussaina...

    Hassana kam ba acewa komai Saboda tsabar murna an mata takwara aranar sai fadi take yaran hannun ta za su ringa wuni da anyaye su sunzama nata..

    Anty ta ce InshAllah nabaki yan biyun nan sossai sheik Kejin dadin mu'amalar hassana da Sa'adatu..

    Misalin karfe hudu aka daura auren Abubakar Sadik tare da Amarya sa Zahra sossai gidan yacika da murna haihuwa data aure..

    Salma tana kwance duk abun da ake sai dai ta yi Murmushi ba ta iya tabuka komai karfe shida na yamma Mama tadawo gidan tare da da yan rakiyan ta..

    Sheik yana ganin ta kamar bashi ne yakore ta ba..

    Ya fara fadin uwargida ran gida tun yaushe nake magiyan kidawo hakanan na gaji da jiran sai yau...

    Saka ka sake da baki take kallon sa ta ce lallai Sheik ya iya bariki ita da Ko wayar ta baya dagawa...

    Ganin ta zuba masa idanu ne yakama hannun ta beson Anty da Hassana su fahimci cewar ba da son ran sa tadawo yanzu ba yaso ta yi wata shidda agida...

    Karaso da ita falon ya yi yana nuna mata jariran ya ce kinga yayan naki kisa musu Albarka tare da dauko yayan ya mika mata..

    Karba ta yi tana murmushi ta ce Allah yaraya ya dayyaba '' sossai hankalin ta ya tashi ganin yanda Anty da hassana suka zama kamar kawaye agidan...

    Hassana ta ce Barka da zuwa anti babba ya hanya ya mutan gida..

    Lafiya lau ne ta amsa masu cike da sakon fuska...

    Kai tsaye dakin Da Salma take ta nufa ta iske Salma kwance Alamun tana jin jiki sossai...

    Sheik ya biyo ta a dakin tare da rike hannun ta yazaunar da ita..

    Ya ce Aisha kinga halin da yar mu Salma take ciki tana bukatar adu'ar mu..

    . Sonake nan da wata biyu inna gama harhada takarduna zan fitar da ita waje dan duk wata magani na auna mata amma abun babu cigaba....

    Mama kuka take sossai cike da damuwa take kallon Sheik ta ce Abdurrazak kayafemun kurakuraina wallahi ba ka taba cutar dani ba Kana min Adalci a zaman takewa kishi ne ya sa na ringa cutar da yar cikina..

    Hannun sheik ya sa yana goge mata hawaye..

    Tare da janyo ta rungume ta suna kuka dukansu a tare ya ce Aisha ina son ki mara misali wannan shi ne dalilin daya sa duk abun da kike nakasa iya sakin ki...

    Amma na tabbatar da wata macen ce bayan anty tabbas zan iya cire ta acikin Ahlina......

    Tsagaita kukan ya yi ya ce karki damu Aisha tun da kin canza zan Daga darajarki fiye da kowace mace agidan nan...

    Murmushi Salma ta yi tana kallon su..

    Cikin muryan ta da baya fita sossai ta ce Abby Allah ya saka maka da Alkhairi...

    Sakin juna suka yi suka koma wajen ta tare da sha kan ta cike da so da kauna suka hada baki wajen Fadi InshAllah Salma zaki samu lafiya.

    Sheik ya ce karki damu yata zaki warke InshAllah kuma ina son ki dauka Rahama babbar masoyiyar ki ce keda uwar taki Dan haka ba ki da kamar ta..

    Gyada kai ta yi ta ce Abby InshAllah nagane gaskiya...

     Aranar Amarya Abubakar ta tare agidan..

    Cike da Jin dadi yan gidan suke tarbi dangi Amarya....

    Katsina...

    Adamu yana makale da khadija dake ta fama da Amai Alamun shigar ciki gareta cike da shagwaba ta ce yaya ni dai ka kaini wajen mamy wayyo cikina..

    Sossai ya rude hakan ya sa ya kaita Asibiti koda aka mata gwaji aka tabbatar ciki ne da ita.

    Murna awajen shida iyayen sa...

    Kwatano...

    Ahmad sossai yake mannewa Asiya koda yaushe cikin ba ta aiki yake..

    Cike da gajiya ta ce wai kai yaya Ahmad meyasa bakajin kunya ta ne kullum ayi ta abu daya haba nikam na gaji...

    Kasaitaccen murmushi ya yi ya ce haba Amarya aikin lada kike bakiga yanda kikayi kiba ba..

    Ninasan kina dauke da cikina Asiya...

    Tabe baki ta yi ta ce au daman haka ake ciki uhmm na ji tun da kafada tare da kokarin tashi yajawo ta tafada jikin sa....

    Karima zaune makale jikin Faruk yana ba ta labarai masu dadi sai lumshe idanu take ta ce Maigida na nifa cikina ciwo yake kwana biyun nan...

    Subuhannalah ya furta mu je Asibiti aduba ki yafada yana me shafa cikin nata....

    Aminu kuwa Hauwa tasa shi agaba tana zuba masa shagwaba a la dole sai ya goya tun da yake ɗAnne ta..

    Sossai ya ɗara ya ce ga bayan nan zoki hau. Itakuwa tashi ta yi taje ta ɗâne a bayan nasa suna dariya sossai....

    Cike dajin dadi..

    Marwan kuwa soyayya ba a cewa komai shida Amaryar tasa sossai yake ba ta kulawa yanda yakamata..

    Bayan kwana biyu...

    Abban Marwan ya yi aure ya auro yar bafullatana yar bohicon dangin su Mamy sossai aka sha biki Amarya ta tare dakin miji nata cike da Jin dadi yake murna ya samu budurwa..

    Mamy Farin ciki baya misaltuwa awajen ta..

    Musamman da suka je dukan su har bohicon wajen daurin auren Maryam da Mijin ta mai suna Malam musa wanda yake da mata ita ce tabiyu...

    Yarima Samad sossai yakashe kudi a kan maryam yasiya wa mijin nata gida da za su zauna..

    Maryam kuka take sossai cike da nadama taje ta roki Rahama gafara data yafe mata..

    Rahama ta ce nayafe miki duniya da lahira Allah...

    Sossai hankalin kowa ya kwanta cikin ahlin...

    Bayan sati daya Rahama ta tashi da nakuda sossai kan kace me duk ta fita hayyacin ta...

    Yarima Samad ruɗewa ya yi Jin Matar sa tana buga Salati...

    Koda suka isa Asibiti nan da nan tafara sako yayan ta inda ta haifo kyakkyawan dan ta sak me kama da Yarima Samad..

    Takuma sake haifo yar ta mace me kama da Samad.. Cike da Jin dadi kowa Ahlin ke murna..

    Yarima Samad tsabar farin ciki har a bokan sa na Egypte ya gayyata wajen taron sunan yayan sa...

    Mamy da yan uwan ta murna awajen su baya misaltuwa..

    Shugaban Adalai cike da farin ciki ya ce ya dauki yayan yana musu huduba a kunne..

    Ya ce Samad nasawa yaran nan suna...

    Yarima Samad dake cike da Farin ciki ya ce wani suna kasa musu Abba...

    Ya ce wannan yaron nasa masa suna Abdurrazak...

    Kowa wajen ALLAHU Akbar ya furta harda mamy dake hawayen farin ciki...

    Itakuma wannan yarinyar sunan ta Sa'adatu...

    Rahama da Samad cike da farin ciki suka ce watau ansa sunan uban ta.....

    Sheik ya ce nasa sunan ne saboda sune suka gina rayuwar Rahama har muka samu moriyar ta....

    Cike da kukan Farin ciki Rahama tafara godiya ta ce hakika na ji dadin wannnan sunan da Aka sanyawa masu..

    Ranar suna yara sunci suna sossai akayi taro na gani na fada..

    Abubakar da matar sa zahra saida su kazo suna..

    Sheik da Anty cike dajin dadin wannan karar da akayi masu suka aiko da tasu gudummuwa..

    Mama da Salma sossai suka yi farin ciki duk da Salma tana kwance jikin nata na kara yin zafi...

    Amma be hana ta kiran yayar ta awaya ta yi mata murna cike da Jin dadi....

    Al'amin kuwa anyanke musu hukunci Gidan Yaro na shekara goma..

    Mahaifiyarsa sossai suka yi bakin ciki da kuka...

    Har gida suka zo duba Salma ganin yanayin da take ciki cike da tausayawa.....

    Rahama koda ta yi wata biyu da haihu sossai yaran nata suka dan yi wayau cike da Jin dadi zata je kano gun iyayen ta..

    Asiya ta ce sai dai su tafi tare Babu yanda Ahmad ya iya dole yabar Asiya suka tafi tare da dasu Rahama....

    Kwanan su daya Agarin Rahama tana dakin Salma rike da hannun ta.

    Ta ce ƙanwata.

    GA yayan ki nan masu sunan anty da abby inhar na yaye me sunan Anty zan baki ita halak malak da zaran kinyi aure....

    Cike da Jin dadi ta ce Salma ta ce antina nagode da wannan kyautar da kikamin Allah yabani lafiya..

    Ameen suka furta a tare..

    Bayan wata shida komai yana tafiya daidai harda fitar da Salma kasar waje Alhmdulilah ta ji sauki tadawo gida amma dai gatanan dai sai Aslow dan mahaifar ta mugun samun matsala...

    Acikin Sati daya Asiya da da Karima da Khadija suka haihuwa harda hauwa...

    Inda ita hauwa ita bakwaini ta Haifa..

    Asiya ta haifi dan ta namiji...

    Inda yaci sunan Abdul Samad..

    Ita Ko hauwa yar ta mace sossai aka sanya mata suna Aisha..

    Sai matar marwan ta haifo ya mace.

    Inda aka sanya masa suna Salamatu sunan mahaifiyar sa.....

    Dangi kowa da kowa ya hankalin kowa yakwanta...

    Yau takanas Mamy tashirya tsaf zata je kaiwa yar uwar ta Farida ziyara..

    Sossai maman Maryam ke kuka ita da Fulani ganin Mamy tazo musu da abinci da kayan abinci...

    Cike da Jin kunyar ta suke kuka suna rokon ta gafara....

    Bokan Jeji yau da wani Azababben ciwo ya tashi sakamakon Aljanun sa sun saka shi agaba ya daina kawo musu jini...

    Yana ta musu musu akwance yana zazzare idanu har rai yafita gangar jikin sa....

    Kwanan sa uku anan gawar tasa har tafara wari tana tsutsosi.....

    KANO...

    Tun da Samad suka je Kanon kai tsaye gidan sa suka zauna shida Rahama dan suna bukatar hutu shida matar sa da yayan sa...

    Asiya tuni Ahmad yazo ya dauke ta suka koma kwatanon abun burgewa...

    Rahama tana makale da Samad yana ba ta labarin yanda ya rinƙa mafarkin ta da irin zallan soyayya daya nuna mata......

    .zaune suke wayar ta ya fara ring cike da ruɗewa take sauraron muryan Anty da take fadin maza Rahama kizo gidan yanzu..

    Rahama cike da tashin hankali take kallon Samad ta ce Amjad tashi ka kaini gidan mu..

    Cikin dimauce ya dauko key ya ce yaran a barwa yar aiki ta duba su...

    Basu ba ta lokaci ba suka isa gidan cikin hanzarin su....

    Rahama gudu take ba ta Ko sanin inda take jefa kafar ta...

    Koda ta isa cikin gidan..

    Iske kowa ta yi cike a dakin Azabure takaraso dakin tana kallon Salma yanda ka san ta wajen mahaifar ta yana zubda jini...

    Cikin gigicewa ta ture waɗanda ke wajen ta isa gaban Salma ta ce my Kanwaty meyake damun wayyo Allah meye wannan cikin Idanun ta da suka kada jajir take kallon Jinin da fita jikin Salma tare da sa hannun ta taba tana ihu sossai ta ce Abby me ake jira ba a kaita Asibiti ba....

    Sheik ya ce Rahama ambulance 🚑 muke jira yazo ya ɗauke mu kai tsaye Asibitin SHIKA ZARIA..

    ZAMU JE...

    SALMA CIKIN tashin hankali da azabar dake dibar ta ta ce Rahama dan Allah kiyafemu.

    Rahama ta ce salma kiyi shiru ban taɓa kwana dake araina ba nayafe miki duniya da lahira InshAllah zaki samu lafiya Salma ta karki damu....

    Salma hannu ta mikawa Rahama ta ce ba ni taki hannu...

    Mika mata hannu ta yi hannun nasu suka tsarke cikin juna..

    Salma cikin kuka ta ce Yaya ta zanbar duniya dan Allah karki gaji da mun adu'a da nema min gafara wajen ubangiji...

    Rahama cike da ruɗewa take kallon ta tana Girgiza kai..

    Ganin Idanun Salma yana yin sama... Sheik cikin ruɗewa yake fada mata kalmar shahada...

    Nan da nan rai ya yi halin ta Salma ta ce ga garin ku nan...

    Wani uban Kara Rahama ta yi ta tsalle tana Girgiza salma wacce Idanun ta suke akafe..

    .sheik na hawaye ya sa hannun sa yarufe mata idanu yana kuka...

    Nan da nan yadau wayar sa yakira ambulance din ya ce musu su koma dan tarigamu gidan gaskiya........

    Anty kuka take sossai Mama duk tabi tarikice..

    Koda labari ya isa wajen Shugaban Adalai basu ba ta lokaci ba wajen bin jirgi ba shida mamy...

    Wayyo Rahama kuka take ana rirriketa Yarima Samad da shima kuka yake ya ja ta rike ta yana kokarin dauke ta a kan gawar Salma....

    Babu ba ta lokaci mata suka dauki Salma suka yi mata wanka..

    Mama kuka take sossai ganin gawar yar ta abun soyuwar ta kuka take sossai take ta ce yata na cuce ki na cuci rayuwar ki.

    Rahama kam sumewa ta yi hakan ya sa aka kwantar da ita Asibiti ana sanya mata ruwa.....

    Wajen Karfe biyar aka sallaci gawar Salma inda aka samu cinkoson mutane..

    Sossai anty take kuka ita da Mama da hassana....

    Bayan kwana uku da rasuwar Salma.

    Rahama ta farfado ta koma silence magana daya za ka mata zata fashe da kuka..

    Mamy da shugaban Adalai rarrashin ta suka dinga yi suka nuna mata babu soyayyar data wuce ta rinƙa binta da adu'a.....

    Rayuwa ta sauya abubuwa sun canja..

    Haka ake ta gudanar da rayuwa cike dajin Dadi.

    Har Allah yakara bawa Rahama haihuwa inda suka haihu lokaci daya da hassana...

    Rahama ta haifo ya mace wacce ta sanyawa Suna Salma tana kuka sossai rungume da hoton su na kuruciya ita da kanwar ta....

    Hassana ta haifo dan ta Namiji wanda suka sanyawa suna Salihu sossai ake murna...

    Mama zuwa ta yi tarungume Anty cikin kuka ta ce Sa'adatu ƙanwata dan Allah kiyafemu na cutar dake tun da aka kawo gidan na.

    Anty ta ce na yafe miki nima kiyafemin zaman tare.......

     Sheik sossai yaji dadin ganin duk sun hada kai.. Cike da kewa Salma duk yaji gidan ya rage masa dadi be kasawa dayi mata adu'a....

    Har yana nadaman korar daya taba yimata sanda tazo gidan sa da gyale...

    Rahama da Samad komawa suka yi kwatano inda sukaci gaba da rayuwar su cike da Jin dadi.

    Yarima Samad samun aiki ya yi inda yake shirin barin kasar shida Rahama za su koma egyte da zama...

    Shugaban Adalai sossai yake gudanar da mulkin sa bisa Adalci da tausayin talaka..

    Mamy sossai ta yi wani haske ta yi fresh ita da mijin nata....

    Mama karama da kanta taraka Karima har kasar su Niger ziyara....

    Asiya da Ahmed tamkar tagwaye haka suka koma...

    Bayan Sati daya Samad tafiyar tasu ya tashi shi da Rahama....

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.