Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Allah kasa yanda na fara lafiya in kare shi lafiya. Wannan labarin ya faru da gaske dan kusan Book dina da nake yi true life ne sai dai in yi masa kwaskwarima dan abun ya fi ba da citta.
Ku biyo ni ku sha labari.
Ku daure ku yi comment dan in ji ra'ayoyin ku a kan Littafin nan......
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
⚜️©J.A.W📚🖌️
Marubuciyar
* Amince Da Ni
* KAI KA JA WA KANKA
Yanzu kuma gani ɗauke da
ƘANWATA
Paid Book ne
Vip 300
Special 500
Acct No. 3115484026, First Bank, ko kuma Kati MTN (Ba na son VTU)
Idan kin biya ta bank kina iya turo shaidar biyar ki ta wannan 09069080725
🌟🌟 ƘANWATA Na Ikilima Adam [Kashi na 5]🌟🌟
7️⃣0️⃣
Yasa shi tashi
tsaye ya ce karta ga laifin Karima dan doka ne aka kindaya mata '' amma kuma
maganar cin zarafi zanji dalilin daya sa ta yi hakan...
Aminu ya ce OK
gara haka ai.
Ya za ai ta
shigo ne ta ce tanason ganin yayar ta..
Murmushi Samad
ya yi yana kallon Rahama dake kokarin rufe jikin ta da bargo '' ya ce uhmm
kudai ba ta hakuri nima ina nan fitowa ni kadai yanzu.
Mu hadu Sashin
Mamy.
Aminu ya ce
Tabe Tabe saika zo din Daga haka ya katse wayar..
Kallon sa yadawo
a kan Salma ya ce kindaiji abun da ya ce '' hakuri yake baki a kan ba za ki
samu ganin Rahama a yau ba.
Sai dai
gobe.....
Kallon sa
yamaida a kan Faruk ya ce kai kuma mene ne damuwar ka naga tun da akai maganar
Asiya ka canza Daga yanayin ka
Faruk ya ce Ah
Ah ba haka bane yanzu dai mu je Sashin Mamy din..
Barin Salma suka
yi awajen zaune..
Ganin lallai
suma sun raina mata wayau ya za ai tana kanwar matar gida za su taka ta..
Saida ta Share
minti goma zaune bayan tafiyar su Faruk.
Tashi ta yi jiki
asanyaye zata wuce masaukin su...
Jin karar
takun takalmi ya sata waigawa taga me zuwa...
Caraf Idanun
su ya tsarke cikin juna ita da Samad wani kallo yake bin ta da shi masu tarin
ma'anoni....harya iso gaban ta batasani ba dan ta shagala da kallon sa....
Tsintar muryan
sa ta yi yana Fadin Salma mekikeyi anan ke kadai..
Bama tasan
yana magana ba Sam hankalin ta baya kusa ta shagala da kallon sa..
Da Mamaki yake
kallon yanda ta kura masa idanu... Sunan ta data ji ya Ambata da karfi ya ce
Salmaaa firgit tadawo hayyacin ta.. Cikin Jin kunya tafara Murmushi yake.
Shiko kawar da
kan sa ya yi Daga kallon ta..
Ya ce mekike
yi anan maza ki wuce daki '' ba na son yawo fa..
Kin ce kina
son magana da yayar ki naga kusan wuni kukayi da ita a yau..
Dan haka
kibari gobe zata zo da inda kuke..
Wannan kallon
da kike yawan yimin na mene ne yafada tare da rungume hannayen sa a kirji.
Cikin Jin
kunyar kalaman sa da rikattatun Idanun sa daya zuba mata akaran farko na
rayuwar ta..
Cikin sanyin
murya ta ce meye A'ciki danna kalle ka kaifa mijin yaya ta ne..
Samad dake
nazartan kalaman ta ya yi shiru cen kamar ba zai magana ba..
Har ta cire
rai sai ta ji yana fadin eh lallai ni mijin yayar ki ce...
Wannan ba
hujja ba ce kiyi ta kallona har in tsargu da kaina.
Dan haka ina
son Daga yau ki daina inba da wata manufa kukeyi ba.....
Salma da bakin ta ya mutu ta ce ni dai ba da wata
manufa nake yi ba''
Saide kaine ba
ka yarda da kanka ba..
Cak yatsaya da
shirin tafiya da yake yi..
Waigowa ya yi yana
kallon ta tun daga kasa har Sama
Kamar ya ban
yarda da kaina ba''' Daga nace miki ki daina abun da beda amfani. Ke Ƙanwata ce inna sameki da kuskure to zan
hukuntaki daidai da abun da kika aikata koda khadija ce haka zan mata kisa ki
rubuta ina binki bashi daya karki bari yazama uku kinji Ko ya saki wani
shu'umin Murmushi tare da barin wajen cikin isa da izza...
Kallon sa take
harya ba ce mata da gani lallai ta yarda yarima duk yanda take tunanin sa ya
zarce ta..
Yana bin ta
bashi daya take ta maimaitawa tome yake nufi kenan rasa me ba ta amsa ya sa
Jiki babu
kwari ta yi hanyar dakin nasu...
Bakin ta dauke
da Sallama ta shiga dakin iske Asiya da Anty suna karatun Alkur'an tare..
Sallamar ta ya
sa suka katse karatun suna mata kallon ina ta fito..
Cikin inda
inda tasoma kame kame uhmm daman ina tare da su Faruk ne dan ciwon ciki na ya
tashi...
Anty ta ce
yanzu akwai wanda ya tambayeki inda kika fito.
Girgiza kai ta yi ta ce A'a..
Asiya dake
tabe baki ta ce to ai yawo beda amfani agareki kina matar aure kardai sashin
Rahama kika je dan Allah kibarta ta huta da mijin ta Karki kashe mata aure..
Salma da Ranta yagama baci ta ce au nice ma
zan kashe mata aure..
Innayi haka
meye riba ta..
Asiya ta ce
ribarki shi ne kiga kun rasa dukan ku.
Ma'ana ta rasa
Yarima kema kinrasa kinga babu wanda yake da shi cikin ku..
Salma zatayi
magana Anty ta yi mata hannun stop..
Ta ce ke me
kike tunani ne bamusan lagon ki ba..
Kin hana Adamu
auren Rahama yanzu zaki kashe mata auren ne...
Ni dai nasan
take taken ki bewuce kiga kin rabata da gidan Sarauta nan...
Wallahi kika
kuskura kika kashewa yata aure uhmm wlh ko ubanki be isa yarabani dake ba..
Tun da nake da
shi ba mu taba fada ba amma a kan haka zamuyi inhar ya ce ze daure miki gindi..
Salma sai hura hanci take yi cikin tsananin
bacin rai ta ce zato zunubi ne koda yazama gaskiya...
Banda zuciyar
ku babu Allah taya zaku yi mugun tunanina akaina...
Auren nata da
Adamu mugun halin ta ya sa ya fasa auren ta....
Bata karasa
fadin abun da zata ce ba ta ji anty ta wanke ta da gigitaccen mari wanda ya sa
nan da nan tafara ganin taurari..
Anty zata kara
mata marin Asiya tarike hannun ta ta ce kiyi hakuri InshAllah zata canza halin
ta....
Karmu biye
mata muzama irin ta..
Salma rushewa
da uban kuka ta yi hakan ya sa tadau wayar ta takira mama cikin sheshekar kuka
ta sanar mata da abun da anty da Asiya suka yi mata..
Daga can ɓangaren mama ta ce shegu
yan iska ɗangin
matsiyata sun je maula aidole su wulakantanki.
ita Rahama dan
uban ta tun da ta yi aure sau daya takirani kuma Koda zata tafi yakamata tazo
tamun sallama ki rabu dasu wallahi har Rahama sainayi maganin ta....
.
Salma cikin
Jin dadin kwantar mata da hankali da Mama ta yi ta ce mama.
Wai ina Abdul
jalil ne.
Mama Ta ce
shege baya wuni gida tun da yaga shegiyar uwar sa ba ta nan
a hanse free Salma tasa wayar yanda su Anty za
su ji abun da suke fade...
Ita Ko Anty banda
kukan zuci babu abun da take yi...
So take ta
sanarwa sheik gaskiya ya raba masu gida ita da Mama Ko kuma ita takoma gidan su
tazauna har asamu mafita hakanan takeji zuciyar ta be aminta da komawa gidan
nan ba..
Salma suna
gama wayar ta katse tana ta jijjiga jikin ta ta ce uhmm kalan dangi kawai..
Dukan ku babu
wanda ya hada jini da Rahama..
Anty ta ce
ninan na hada jini da Rahama Saboda inkika ga Abdul jalil to kamar kinga Rahama
ne suna mugun kama.
Jinina da nata
sun gwauraye wuri daya.
Asiya cikin bacin
rai tagama karanta sakon Faruk daya shigo wayar ta...
Dago kai ta yi
tana kallon Salma ta ce wawiyar banza watau sharri kika kulla mun wajen Faruk
meye ribarki algunguma...
Inkina son shi
kije ki kashe auren naki sai inhada ku aure....
Anty ta ce ke kuma
meya ha daki da Salma ne tana kallon Asiya da Ranta yake aba ce..
Asiya taba Anty
labarin abun da Faruk ya fada mata, ..
Cikin takaici Anty ta ce Asiya karki damu
matar mutum kabarin sa kalaman sa karsu ba ta miki rai kidai bashi hakuri.
Ke KUMA SALMA
kindai ba ni wlh halinki sai ke shasha......
Mamy zaune ita
da su Samad
Faruk na yar rubuce rubuce Samad ya dago kai
yana kallon Mamy ya ce wai Mamy ina Maryam take da Mamar ta..
Mamy ajiyar
zuciya ta yi ta ce uhmm ai sun tafi gida tun da taro ya tashi amma Maryam ta ce
zata dawo zuwa gobe.
Good ya furta ya
ce to ita bakuwar nan taki hassana Daga ina take ne.
Mamy wani
kallo take binsa da shi ta ce TO Sarkin tambaya ina ruwan ka ko a kan ka take
ne...
Haba Mamy Daga
tambaya sai kiji haushi na Allah yabaki hakuri..
Ameen ta furta
tana masa hararan wasa.....
Faruk yagama
rubuce rubucen yadago kai yana kallon Samad ya ce gaskiya awannan watan ba a
samu riba masu yawa ba...
Ribar ba ta wuce
millions 50 ba..
Mamy dake
sauraren su ta ce to garin ya haka ta faru ne..
Samad da ransa
yasoma baci ya ce duk laifin Marwan ne...
Yana zuwa
Samad air plan yana diban kudade na a banza da sunyi magana ce musu yake aina
dan uwan sa ne..
Saboda ke Mamy
nake kyale su yanzu lokaci ya yi fa ba zan kara barin takwana ba...
Mamy cikin
kwantar murya ta ce ni dai kar ka masa komai iyakar dai ka dakile hanyar da
yake bi wajen kwasan maka kudade shi ne kawai mafita...
Faruk ya ce
kwarai kuwa shi ne mafita dan manager ya ce yana sawa lissafi ya kunce masu
idan kullum zeje ya amsa bayan komai a rubuce yake a computer....
Yarima ya ce
babu matsala Mamy tun da kin ce haka nadau shawarki. InshAllah gobe zamu shiga
kotu kan wannan case din matar nan.
Daga goben
nakeson infara bin diddigi wannan baiwar nan da ake nema..
Mamy cikin jin
dadi ta ce Yarima Allah ya sa Adace yabada sa'a...
Ameen dukan su
suka amsa...
Wai ina
khadija take ne cewar Yarima yana tambayar Mamy..
Mamy ta ce
yawuce tana dakin ta kaje cen kaduba amma ka san babu inda take zuwa Ko...
OK ya furta ya
ce Aminu kujira ni bara in leka dakin khadija ina zuwa...
Da to suka
amsa masa suna cigaba da hada takardu waje daya....
Ahankali yake
tafiya ba bayason ta ji takun tafiyar sa...
Handle din
kofar ya bude hankali a sannu Ahankali ya tura kofar..
Jin muryan Khadija
tana waya ne ya sa shi kasa kunnen sa wajen Jin me take fade...
Ita Ko khadija
data shagala dayin waya sai fadi take haba Maryam ya zaki hadani kawance da yar
lesbien.. Kuma bayan.... Ganin Yarima gaban ta yana mata mugun kallo ya sa...........
Ta ku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
7️⃣1️⃣
Mugun kallo ya
sa hannun sa ya wabce wayar Daga hannun ta..
Kara wayar a
kunnen sa ya yi yana sauraren abun da ake fadi..
Daga cen ɓangaren ta ce haba khadija
meye dan na ha daki da Yar lesbien bafa harkan nan zaku yi ba..
Nima din da
mukayi da ita yanzu natuba nadaina dan haka ina rokon ki kiyi hakuri zumunci
zaku ringa yi tanada waye wa zata koya miki wasu abubuwan da bakisan dasu ba...
Hankalin
yarima ya yi mugun tashi jikin sa yadau rawa kamar mazari jijiyoyin hannun
saida suka tattashi Saboda tsananin bacin rai Idanun sa suka canza launi zuwa
ja...
Daga can ɓangaren Maryam sai Fadi
take khadija ya kikayi shiru sai magana nake yi.
Cilla wayar ya
yi a bango nan da nan ta fashe wargas akasa..
Ita Ko khadija
karshen gadon ta zauna tana baya baya ganin ya nufo inda take azuciye..
Kuka tasaki
tun kan ya isa gareta...
Kamar kura
haka yayo kanta bugun ta yake yi babu sassauci sai ihu take tana fadin wayyo
Mamy wayyo Mamy ze kashe ni..
Wani mugun
shaka ya yi mata wanda ya sa numfashin ta yin sama sama Idanun ta azare kamar
wacce rai yake gab da barin jikin ta....
Mamy aguje
sukayo ciki ita da su Faruk harda Hassana..
Har tuntube
Mamy keyi wajen rige rigen shiga dakin.
Innaliahi mamy
tashiga maimaitawa me zan gani haka Yarima za ka kashe ta ka saketa nace Ko..
Ina Ko Jin
Mamy baya yi yaci gaba da bugun ta..
Faruk cikin
zafin nama ya je ya rike hannun Samad da karfin tsiya Sannan ya sake khadija...
Ita Ko khadija
yana sakin ta faduwa ta yi kamar matatta tana numfashi sama sama...
Faruk da Aminu
cikin Fada suka ce haba Samad wannan aiba karfin ku daya ba..
Wani irin
abune ta yi mai girma da zakai mata wannan mugun hukunci ni dai gaskiya BANJI
dadi ba...
Duk abun da
suke ta fade be ce masu komai ba....
Mamy cikin
kuka ta ce ku duba mun khadija bede kashe ta ba Ko...
Hassana dake
yayyafa wa khadija ruwa ta ce mamy da Ranta karki damu ta jigata ne kawai amma
zata dawo normal...
Yarima Samad
tashi ya yi tsaye cikin bacin rai ya ce dakun barni da ita inga wanda ya ɗaure mata gindi agidan
nan...
Ahmad ne
yashigo bakin sa dauke da sallama ya ce nasan za ai haka ai tuntuni ina
gayamiki ki ki yaye kada Yaya Samad yadawo amma kika saura kina biyewa Maryam
Ko...
Yakarashe
zancen yana jifan ta da mugun kallo..
Mamy cikin kidima ta ce wai mêke faruwa ne
kunbarni cikin duhu..
Ganin su Faruk
da Hassana a dakin ya sa Samad da Ahmad kin fadin abun da ke faruwa...
Yarima cikin
isa ya ce Mamy maza ta hada kayan ta Daga yau sashina zata zauna wajen mata
ta.. Kuma wlh kada kice komi a kan ƙanwata...
Mamy dake
kallon sa yanda duk ya canza kamar bashi ba..
Ta ce nasan
yanzu jira kake ince wani abu ka dawo kaina...
Cikin sassaita
muryan sa ya ce A'h Ah taya zan dawo kanki Mamy kefa uwa ta ce itakuma ƙanwata
ce da banbanci ba zan yarda ba amun iko a kan ta ba...
Gabadaya dakin
hakuri suka Shiga bashi harda Ahmad..
Amma ya noke
dole abun da ya ce shi za ai Mamy babu yanda ta iya hakanan tanaji tana gani ta
hada kayan khadija tsaf..
Cikin kuka
khadija ke fadin Mamy yanzu har kina kallo ze wuce dani...
Mamy ta ce duk
da ban san laifin da kikayi ba.
Kin san ban
iya hana shi da kina jin magana ta da haka ba ta faru ba....
Faruk da Aminu
bayan sun Kammala komai suka yi Sallama da Mamy kusan tare suka fito Sashin
Mamy da Yarima...
Khadija na
biye dasu abaya da akwatin kayan ta...
Saida safe suka
yi da Su Faruk inda ya yi Sashin nasa '' tana bayan sa tafiya take kamar wata
kadangaruwa cikin tsoro ko bin takanta beyi ba kawai tafiya yake tana bin bayan
sa...
Faruk tsaida
Aminu ya yi suka je ɓangaren
su Asiya...
Kiran layin
Asiya ya rinƙa
yi tana ganin kiran amma taki Daga wa...
Anty ce ke
Lure da ita ta ce kamar wayar ki ce.
Ke ring baki
Daga ba..
Asiya cikin
tabe baki ta ce ai dan rainin wayau nan ne Faruk mana..
Anty ta ce
meye laifin Faruk abun da aka fada masa shi ze dauka haka ne dan Allah Daga
wayar ban san ki da fushi ba...
Cikin kunkuni
ta Daga wayar ta yi shiru taki magana...
Shiko Faruk
cewa ya yi gani a kofar dakin naku ki fito sauri muke..
Ganin anty ta
tsare ta da idanu ya sa ta fadin gani nan zuwa...
Murmushi Anty ta yi tasan ba hakan ta yi niyar
fada ba..
Allah ya sani
tana kaunar Rahama da Asiya har ita Salma din kawai de halin Salma ne bataso
amma tabbas batason mummunar abu ya faru da ita..
Cikin hanzari
Asiya ta saka hijab din ta tafita..
Iske Faruk ta
yi tsaye shida Aminu...
Sai kallon
agogon hannun sa yake Alamun ta dade ba ta fito ba...
Cike da
nutsuwar ta.
Ta iso wajen
su a ladabce ta gaishe su suka Amsa fuska sake...
Aminu ya ce
uhmm masoya sun hadu kun kasa magana Ko bara inkauce kun sake.
basu waje ya yi dan su tatttauna..
Murmushi
Farruk ya ce ya ce ka ga damar tafiya ne amma ai komai sai ayi agaban ka.
Aminu beko
tsaya sauraren Faruk ba yafice.
Faruk Murmushi
ya yi yana kallon yanda ta hada rai kamar an mata dole ne ta fito..
Ya ce haba
Asiya me laifina dan nayi miki fada a kan wayar ɗare..
Asiya ta ce
wayar ɗare kenan yar
iska ka daukeni wani irin waya ne
ba zanyi shi a
wuni ba sai cikin ɗare
nifa ba na son zargi duk abun da akace maka akaina ka tambayeni zan fada maka
gaskiya
ba kazo ka
yanke mun hukunci ba..ehee takarashe zancen cikin tsiwa..
Faruk cikin
yin kasa da murya ya ce Afuwan nayi laifi daman sonake inga kyakkyawa fuska ki shi
ya sa na leko dan Allah yimun Murmushi mana..
Yana kashe
mata idanu.
Shiru ta yi tarasa
tayanda ake murmushin..
Au baki huce
ba kenan...
Girgiza kai ta
yi ta ce komai yawuce.
Murmushi ta
sakar masa tana kokarin shiga Daga ciki..
Ya ce ba komai
wannan ma dakikai kin biyani zuwa dasafe zamuyi waya tun da kince bakya wayar ɗare..
Asiya dake
kokarin shiga daki kada kai ta yi tare da komawa cikin dakin nasu..
Shikuwa zuwa
ya yi ya ja Aminu suka wuce...
Yarima suna
shiga sashin nasa kai tsaye dakin Rahama ya je da khadija iske Rahama ta yi harta
rufe dakin nata...
Karar bubbuga
kofa ne.
Yatashe ta
Daga barci tasan shi ne cikin tsoro ta tashi batasan dame yazo ba..cikin kuka
zuci ta sauko Daga kan gadon ta.
Taku take yi
ahankali harta isa bakin kofar.
Ahankali tabude kofar tana murza Idanun ta..
Caraf Idanun
ta ya sauka a kan Yarima da Khadija dake tsaye da akwatin kayan ta tana
sheshekar kuka kanta aduke
Rahama
cikin.........
Taku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
7️⃣2️⃣
RAHAMA cikin
Rawar murya ta ce khadijat lafiya kuwa mêke damun ki.
Gayamin naga
kamar kuka kike nan da nan duk ta rikice tana me jawo hannun khadija zuwa dakin
nata...
Shiko Yarima
dake tsaye yana kallon su ya ce Hubby nan zata dawo da zama har muga Abun da
Allah zeyi...
Rahama cikin
damuwa ta ce na ji dadin hakan amma meye dalilin dayasa take kuka takura mata
kayi a kan saita zo nan sashin mu...
Yarima dake
kallon ta yanda duk ta rude tana sharewa khadija kwalla ya ce gâta nan ki
tambeye ta da kanta ta ce zata dawo gun anty ta kila wani abun ke mata ciwo..
Khadija da duk
jikin ta ciwo yake mata ta ce Anty Rahama ina son in shiga wanka..
Rahama cikin
hanzari zatayi bandakin da hada mata ruwan dumi na wanka
Yarima yarike
hannun ta ya ce ina zakije ne Sarki aiki Kibar ta da kanta zata hada ruwan
wanka..
Babu yanda ta
iya hakanan tasa idanu khadija ta shiga bandakin...
Dawo da.
Kallon ta yi a kan sa cikin kalan tausayi ta ce yanzu tun da ka ga khadija
tadawo nan sashina tare zanringa kwana da ita..
Wani kallo
yake binta da shi masu cike da baki isa ba..
Ya ce uhmm Rahamatullah
dauko hijab dinki mu. Tafi Saboda Sallah Asuba..
Rahama ta ce
ya zanbar khadija ita kadai..
Uhmm ni dai mu
je yafada yana kokarin Jan hannun ta...
Ganin zata ba
ta masa lokaci ya sa hannayen sa ya dauke ta..
Sai zazzare
idanu take ta ce Amjad meye haka ne idan khadija ta gan mu ahaka fa girma
yafadi...
Uhmm ya ce be
ba ta Amsa ba kai tsaye dakin nashi yakai tare da sauke ta a kan gadon sa..
Yana ajiye ta
yadawo tsakiyar dakin kokarin cire kayan jikin sa yake'ganin tana kallon sa ya
ce ba za ki tayani cirewa ba....
Kaida kasa
abunka kaine ka san yanda za ka cire su takarashe zancen tare da Jan bargo zata
lullube jikin ta...
Yarima beko tsaya sauraren ta ba..
Ya shiga ya yi wanka yana fitowa Daga shi sai
boxer gashin jikin sa luf suka kwanta Saboda damshin ruwa..
Bakin gadon nasa
yazauna tare da dauko wayar sa yana bin sakonni dake shigowa takan whsap din
sa...
Duk sakon
dayaga New number ne baya shiga ciki sai inhar yaga profile din wanda ya sani
ne...
Sakon ya shigo masa a kan hassana dake gidan
sarauta ba aiki yakaita ba....
Ta dalilin
Salihu Turaki tazo dan tasan sirrin sa...
Kuma son
Salihu Turaki take dan har haduwa suke yi...
Kallon number
data turo masa sakon ya yi yaga nomber Gabon ce...
Shiga cikin
message ɗin ya yi yana
kara karanta wannan sakon...
Maganar zuci
yake ya ce eh tabbas ta ce Gabon take inhar mutumin nan dayayi masa magana yana
da.masaniya a kan hassana Kenan ya san inda Shugaban Adalai..
Ba tare da ya
ba shi Amsa ba ya kashe datar sa..
Tagumi ya yi Daga
zaune yana nazarin yanda ze dauko lamarin da warware sa ganin babu mafita ya sashi
ajiye wayar gefen gadon nasa tare da jona ta a caji...
Kallon Rahama
yake ji ya san ba barci take ba amma ta lumshe Idanun ta...
Hawa gadon ya
yi yana kokarin jawo ta jikin sa tare da kai hannun sa saman boob din ta...
Zumbur ta
tashi tazauna cikin muryan wacce ke shirin kuka ta ce wayyo nace maka ban warke
ba..
Tun da baki
warke bara induba wajen ingani..
Ganin yana
kokarin cire mata pant tarike masa hannun cikin tsoro ta ce haba Amjad kayi
hakuri mana da wasa nake maka na warke..
Au kin warke
kikace
Gyada masa kai
ta yi cikin Kosawa da tambayar sa..
Ban yarda ba
saina gani da idona..
Duk yanda taki
yarda ta kasa kwatan kanta saida yakwantar da ita tare da duba wajen gani ya yi
kamar babu rauni tsabar raki ne ke damun ta.....
Dawo da kallon
ya yi a kan ta ganin tarufe fuskar ta da pillow ya sa shi murmusa.
Haba Amarya
meye na Jin kunya Daga ina duba wajen kada asamu matsala kuma naga babu wata
illa a wajen dan haka pls kidan ba ni inkara namiki Alkawari ba zan wuce awa
daya ba cikin marairaice fuska....
Rahama zazzare
idanu ta yi tasoma hawaye shar ta ce wayyo Allah Anty ki taimakeni dan Allah
kayi hakuri wallahi har yanzu ban koma daidai ba yanda take kukan iya gaskiyar
ta ya sa shi darawa ya ce ok kin amince Mala'ikun Rahama suyi ta tsine miki
Albarka..
Zazzare idanu
tasoma ta ce uhmm ni dai bazasu tsinemun ba dan ba da ganganci na hana ba...
Yanda take
zaro zancen sossai ya shagala da kallon ƙaramin bakin ta...
Hakan ya sa
shi lacuto bakin nata yana kokarin hade shi da nashi.
Ya ce uhmm
amma dai zaki barni in rage zafi Ko dan dai. Gaskiya ban iya kwana hakanan..
Babu yanda ta
iya duk yanda taso ta yi barci Yarima yaki ba ta damar haka...
Sossai ya raya
daren ba tare da ya kusance ta ba..
Tun tana
kaucewa har ta biye masa...
Kusan karfe
ukun ɗare Sannan barci
barawo ya yi awon gaba dasu dukan su......
Asuba tagari
Kasar
Gabon....
Karfe tara
daidai jirgin sheik da Aminin sa ze tashi zuwa garin kano...
Tun karfe
bakwai na safe yashirya tsaf komai nasu harda siyayyan da suka yi..
Sheik harda
kayan baby masu kyau ya siya a cewar sa ya yi kewar yan kananan baby yanzu
gashi zai samu....
Texte din Anty
ne yashigo wayar sa yana dubawa ya yi Murmushi ya ce madam kina raina..
Daga can ɓangaren ta ce ya Abban
Rahama dafatan kuna ta shirye shiryen koma.
To Allah
yakaiku lafiya.
Damar so nake
in rokeka wata Alfarma..
Jin ta ambaci
Alfarma ya sashi ba ta damar ta fadi abun da take bukata...
Anty ta ce tun
da muke da kai ban taɓa
kawo maka wani abu sabanin hankalin ka ba..
Sheik ya ce
Sa'adatu haka ne zancen naki ki fadi kai tsaye Alfarma InshAllah zan miki..
Cike da tsoro
da Fargaba ta ce ina son dan Allah ka raba mana gida nida Maman Salma..
Cikin tsananin
mamakin furucin ta ya ce to Saboda me Sa'adatu zan raba muku gida...
Anty tashiga
bashi labarin wayar da salma ta yi da Mama agaban ta...
Numfashi ya
fesar yana nazarin kalaman ta...
Ya ce yanzu
watan cikin ki nawa ?
Wata hudu ta
ba shi amsa tana mamakin meya kawo zancen ciki bayan ba maganar suke ba...
Sheik ya ce
Sa'adatu kiyi hakuri kibari watan haihuwar ki nakamawa zan canza muku gida..
Amma kowa da
part din sa..
Sai kunso zaku
ga juna hakan ya yi miki sabon gida sabon baby....
Sossai ta yi dariya
ta ce hakan ya yi nagode da Fahimta.
Suna gama fira
da Anty...
Yakira Mama
awaya cikin gadara ta ce harka iso ne...
Sheik ya ce
babu zancen gaisuwa Ko Allah yakawo mu lafiya wai ke Aysha yaushe zakiyi
hankali ne..
Bama wannan ba
ina Abdul jalil yake..
Hankalin mama
ya tashi Jin wannan tambayar inda inda tasoma ta ce yanzu yafita Daga gidan...
Sheik ya ce au
sammako ya yi kenan.
To ki aika
akirawo shi yadawo gida yanzu nan..
Banson na iso
ban same shi ba....
Mama rike da
baki ta ce uhmm nasan Algunguma ta fadamai ne shi ne ze fake da siyasa...
Ni yanzu ma
ina nasan yaron nan yakwana tashi ta yi tadau hijab din ta..
Tana ta shiga
makota cigiyar sa duk inda taje sai ace ba a gan shi ba..
Cike da
takaicin yaron ta ce amma dai wannan yaron mugun dan banzan yawo gare shi ace
yau kwanan sa biyu be kwana gida cike da damuwa take bin layi kwararo neman sa
duk inda taje sai a je ba a gan sa ba....
Wayar tazare
cikin jakar ta tashi ga kiran layin Abubakar.....
Har ta kusa
tsinkewa ya Daga..
Cike da damuwa
ta ce ABU wai ina Abdul Jalil tun shekaran jiya da safe bankara sashi a idanuna
ba..
Abubakar dake
tuki ya ce aikuwa gida yakwana jiya ma inaga sammako ya yi nasan sai ɗare kibari zan dubo shi
kila yana gidan su Asiya ne..
Mama kwata
kwata ta mance taje gidan su Asiya hakan ya sa ta yi hanyar gidan cikin
hanzarin ta isa gidan su Asiya....
Bakin ta dauke
da Sallama..
Maman Asiya
hajiya hussaina cikin washe baki har fararen hakoran ta dake dauke da hakorin
makkah suka bayyana...
Cikin sakin
Fuska ta ce Maman Salma yau kece agidan namu lale lale..
Mama cikin
tabe baki ta ce eh Nice dafatan dai kuna lafiya..
Lafiya lau
tabata amsa ta ce mu shiga Daga ciki mana...
Mama ta ce Ah
ah basai na shiga ba a kan hanya nake.
Abdul Jalil
nake nema Ko yazo gidan nan kuwa...
Maman Asiya ta
ce yana ciki kamar Abinci yake ci..
Maman Ranta
dubu yabaci cikin ɗAnne
fushin ta ta ce Ayya idan yagama yazo gida ya sameni yau baban su ze
dawo....takarashe zancen tare da juyawa...
Ita Ko Maman
Asiya da mamaki take kallon ta ta ce uhmm haryanzu dai Aishatu kinki canza
halin ki.
Mijin ki ma
beji dadin ki ba bare yaya bare makota uhmm Allah ya sa ki gane takarashe
zancen tana kar kada kai tare da shiga dakin ta iske Abdul Jalil harya gama cin
abinci duk hirar da suke yana jinsu...
Kallon Maman
Asiya ya yi ya ce nasan Abba yau zedawo bara inje inshirya indan gyara masa
daki...
Maman Asiya ta
ce to kadaiyi hakuri duk abun da zatayi maka.
KADA kai ya yi
ya ce babu damuwa.....
Wajen karfe
daya na Rana su sheik suka iso garin Kano...
Abubakar ne ya
je yadauko su ya sauke Aminin sheik agidan sa..
Shi kuma suka
yi nasu gidan kai tsaye.....
Sheik cike da
hamdala ya ce Allah ya yi mun dawo kasar tamu..
Abubakar dake
tuki ya ce Abba da bakanan kaida Anty gidan babu dadi...
Murmushi sheik
ya yi ya ce to ina maman taka take ba ta tayaka hira ne..
Tana yi ya ba
shi amsa atakaice yana cigaba da tukin nasa....
Kano
Tun da sassafe
Fulani tashirya tsaf cikin shigar ta na Alfarma hannun ta rike da wata bakar
leda mai cike da mugun sirri da bokan ta ya aiko mata
Cike da izza
da takama take taka kasa iya Firdausi tana bayan ta sai kirari take zuba
mata...
Barka da
Fitowa gimbiya Fulani takawan ki lafiya uwargida agun Sani Turaki.
Ba gaba da
gaba ba kota baya sai anshirya shuga ta...
Kasaitaccen
Murmushi ta yi tana cigaba da takun ta izuwa Sashin Yarima.
Har ta kusa
kai kofa ta ji muryan Karima na fadin..
Gimbiya Fulani
dakata !
Cak Fulani ta
tsaya cikin tsananin mamaki ta wai..................
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah7️⃣3️⃣
Cikin tsananin
mamaki ta wai ga tana kallon Karima..
Dake kokarin
isowa gareta kan aduke ta ce.
Gimbiya Fulani
Yarima ya sa doka hana kowa shiga Sashin nasa saida izinin sa....
Wani kallo mai
wuyar fassara Fulani ke jifan Karima da shi cikin tsananin bacin rai ta ce ke
shasha dabba karya mara hankali kaskantaciyyar baiwa har kin isa ki gayamin
doka bayan mune masu ba da doka da oder to bari kiji ingayamiki badai takamar
ki Yarima ba to zansa asauke ki Daga kan mukamin ki.
Zaki shigo cen
cikin bayi kina aiki..
Shasha dan
Allah matsa kiban hanya maza kisa key ki bude mun...
Karima dukar
da kanta kasa ta yi ta ce ina kara baki hakuri Gimbiya ba zan iya bude miki
kofar nan ba...
Iya Firdausi
dake bayan su cikin tsoron abun da zeje yadawo ta ce haba Karima Gimbiya Fulani
ce gaban ki......yakamata ki gyara kalaman ki..
Karima cikin
karfin hali ta ce mama nasani kawaide ba zan iya budewa bane...
Saukar Mari
Karima ta ji afuskar ta wanda ya gigita ta rike da kuncin ta da Idanun ta ɗa suka kada take kallon
Marwan sai huci Sama sama yake cikin tsawa ya ce ke har kin iya kihana Fulani
shiga Sashin Yarima to yanzu zaki ga hukunci da zansa ayi miki wanda ze koya
miki hankali....
Ihu ya fara
yana fadin ina bayin gidan nan suke nan da nan duk suka bayyana na daki ma
agurguje suke ta fitowa dan zuwa wajen nasa....
Koda suka jeru
kallon su yake kamar yaga kashin Awaki tare da yamutsa fuskar sa..
Cikin zafin
Rai ya ce cikin ku mutum daya ya je yakira mun..
Karfin Iko na
gidan Yari..
Babu ba ta lokaci
daya Daga cikin su ta tafi dan kiran sa..
Shikuwa Karfin
Iko yana zaune bakin kofar Gidan Yari sai hura hanci yake yana tauna asawaki ya
mimmike kafafun sa kan doguwar kujera ga redio kusa dashi...
Isowar wannan
Baiwar ya sashi sauke kafafun sa akasa yana kallon ta cikin zakuwa..da son Jin abun
da yakawo ta
Cikin Rawar
Murya ta ce Karfin Iko '' jikan Sarki Marwan ke son ganin ka ya ce mu taho tare..
Jin Marwan ya
sa babu ba ta lokaci ya tashi yabi bayan ta ya san aikin mugun ta ce zeyi..
Karima banda
innaliahi babu abun da take maimaitawa acikin zuciyar ta....
Iya firdausi
ta shiga tashin hankali ganin za a hada Karfin Iko da Karima sossai tsoro ya
bayyana A fuskar ta....
Murmushi
Fulani ta yi ganin Sarkin iko ya iso shida baiwar nan..
Cike da ladabi
ya gaishe da Marwa da fulani....
Marwan cikin
Daga Murya ya ce wannan baiwar Karima ina son ka kaita gidan Yari tare da horon
yunwa na kwana uku hade da bulala dari...
Idanun Karima
nan da nan suka kawo Ruwa cikin Rawar Murya ta ce Allahumma arjini fi
musibati...
Wayyo Allah
gani gareka za su cutar dani ba tare da da hakki ba.
Kan kace me
karfin Iko ya yi mata wata muguwar cafka
bayi maza masu tsaron sashin Yarima da suke
sanye cikin uniforme din su ''suka yo wajen aguje su uku kallon karfin Iko suke
yanda yake Jan Karima akasa.
Bayi mata
dasuka jeru awajen Ko wanne kansu akasa kwalla suke suna tuna irin wahalar da
Karima zata sha hannun Karfin iko..
Dan sun taba
dandana wannan azabar a hannun sa..
Fulani ganin
har sunkai bakin kofa da Karima cikin Daga Murya ta ce Karfin Iko ina son yanzu
kayi mata jina jina bakin nata dake rashin kunya ka murje mun su...
Karfin Iko
kallon Fulani ya yi cikin babban muryan tasa ya ce an gama Ranki yadade an gama
'' amma makullai na hannun ta yakamata akarba...
Marwan dake
karasowa inda suke ya ce amsa ka miko min '' Karfin iko wabce makulli ya yi hannun
Karima tare da bawa Marwan....
Kai tsaye ya
yi gaba da Karima cikin zafin nama....
Fulani cikin
Jin dadin wannan abun ta ce Marwan ba ni makullan nan '' 'mika mata ya yi ya ce
inaga sune makullan kofar dakunan Yarima da Matar sa...
Babu ba ta lokaci
ganin abun da akayiwa Karima ya sa bayin dake gadin kofar shiga suka ba Fulani
damar shiga ba tare da sunce uffan ba.....
Shiko Marwan
cikin kallon banza da yake bin bayin da shi ya ce Ko acikin ku akwai me magana
ne..
Kada kai suka
yi Alamun babu....
Cikin karaji ya
ce To mama Nina tafi in wani abu yataso ki sanar mun Daga haka yafice cikin isa
yana tafiya kamar wani bajimin sa...
Ita Ko Fulani
tafiya take a hankali tanayi tana waige waige sai adu'a neman sa'a take cikin
saurin ta..
Ta iso gab da
kofar dakin nasu....
Khadija Daga
cikin dakin tana moppin dan yarima ya ce babu wata baiwar da zatayi aikin sai
ita rashin aikinyi ne ya sa har suke shashanci awaya '' cikin gajiya da aikin
da ba ta Saba ba...
Ta iso daidai
kofar dakin zatayi moppin har tasa tsumma saita ga baya goguwa sossai..
Hakan ya sa
tasa hannun ta ta murda handle kofar ahankali zata bude...
Ita Ko Fulani
Jin ana kokarin bude kofar ya sa ta make da bangon lungu tare da toshe hancin
ta....dan kada ta ji numfashin ta...
Cigaba da
moppin dînta tashiga yi tana yi tana fadin wash Allah yau dai naga takaina
Yarima haka yake babu tausayi....
Rahama ce ta iso wajen nata cikin tsananin
mamakin uban aikin da take yi ta ce haba ƙanwata dakin barshi nayi.
kokarin amsar
moppan take hannun khadija...
Ita Ko khadija
sai Fadi take Ah Ah wallahi kibarshi zanyi da kaina kada yaya ya fito yagan
mu....
Yarima daya
fito Daga dakin nasa cikin shigar sa na lauyoyi tare da hulan lauya akansa
kallon time ya yi yana tafiya hakan ya sa ya leka dakin Rahama ganin ba ta nan ya
ce Hubby hubby hubby kina ina ne m'y Wife...
Jin babu
Alamun ta ita da khadija ya sa ya yi hanyar fita Daga dakin nasa..
Yaci karo da
Rahama da khadija suna moppin tare...
Kallon Rahama
yake babu Ko kiftawa soyake ya wuni da ita dan yanuna mata zallan so da kaunar
da yake mata...
Wuyar rigar sa
ya gyara tare da yin gyaran murya...
Hakan ya sa
khadija ta dukar da kanta akasa ta ce yaya ina kwana..
Lafiya lau
baby na yabata amsa atakaice...
Tare da maida
kallon sa a kan Rahama da Idanun su suka tsarke cikin juna wani kallo yake
binta da shi masu manufofi da dayawa..
Cikin yin kasa
da murya ya ce hubby zan tafi Kotu ki kulamun da kanki kinji Ko..
Kada masa kai
ta yi ganin Khadija ya sa duk tasa bashi wata Amsa...
Cike da ladabi
ta ce Amjad daman ina son inje gun mamy da Anty inkaban dama....
Kallon ta yake
ya ce Ah haba to kibari zan kira Karima ta yi miki j'agora har dakin su 'Fulani
har wajen Mama karama zaki je ki gaishe su idan na dawo zan sameki acen sashin
Mamy amma kada Khadija tabiki ta zauna daki..
Rahma cikin
yin kasa da murya Alamun roko ta ce pls Dan Allah ka barta mu je tare kafana
kafar ta ta mairairaice fuska...
OK ya furta
yana kokarin sa kai zefi ce..
Ita Ko Fulani
zazzare idanu tasoma Jin takun tafiyar Yarima...
Cike da
nutsuwa Rahama ta take masa baya..
Daidai saitin
da Fulani take nan Rahama ta tsaya hakan ya sashi waigowa ya ce hubby harkin
iya rakon miji Ko uhmm nasan Asiya ta koyamiki
Rau Rau da
idanu take kallon sa ta ce Asiya kuma wacce Ko auren ba ta dashi..
Murmushi ya yi
ya ce nasani mana amma ai tafiki wayewa
..hannayen sa
ya sa tare da tallafota suna Jin numfashin juna '' kiss dîn ta ya shiga yi yana
fadin uhmm kamar dai mu koma cikin daki my hubby...
Murmushi ta sakar
masa cikin cool voice din ta ta ce Amjad dîna Allah yakaika lafiya yatsare
hanyar ka '' ta tafiya da ta dawowa gida..
Allah yarabaka
da sharrin Karfe '' ameen ya furta tare da manna mata kiss a goshi...
Ita Ko Fulani
sai kallon su take tana zazzare idanu gashi ta toshe bakin ta da hancin ta...
Sakin hannun
Rahama ya yi ya ce wife zanturo miki Karima kedai ki shirya saina dawo yafada
yana kokarin barin wajen...
Ita Ko Rahama
juyawa ta yi dan komawa cikin dakin ta...
Cikin hanzarin
sa ya sakai zefi ce haryakai bakin kofar Fita yaga Bayi masu tsaron Sashin sa..
Cike da ladabi
suke gaishe shi Barka da fitowa ranka yadade Allah ya ja zamanin ka dan Sarki
jikan Sarki...
Yarima kallon
su yake yana kada kai ya ce nagan ku kamar bakwa cikin hayyacin ku...
Daya Daga
cikin su ya ce babu komai Ranka yadade '' gimbiya Fulani ciki zata zauna ne
harsai kadawo ne dan zamuje cin abinci yakarashe zancen cikin ladabi...
Yarima cikin
tsananin mamaki ya ce Fulani ba ta ciki ai waya ce muku ta shigo..
Ranka yadade
tana ciki kila tana sashin Gimbiya Rahama ne...
Yarima beko
tsaya bin takansu ba kai tsaye yajuya zuwa ciki sai dube dube yake yana tafiya
cikin hanzari da zafin nama.....
Ya shiga har
dakin Rahama ya duba Sam bega Fulani ba ya duba sashin nasa nan ma be ganta ba...
Rahama cikin
mamaki ta ce wai Amjad me kake nema ne..
Shiru ya yi yana
kallon ta ya ce Fulani ba ta shigo ba kada kai ta yi Alamun A'a...
**************************
Karfin iko
yana shigar da Karima gidan Yarin '' ya rinƙa dukan ta da bulala ba kakkautawa ''
wani razananne kara ta saki tana fadin wayyo Allah na Ya Allah ka cece ni ya
Allah ka kawo mun dauki..
Karfin Iko
dake tsaye a kan ta dako riga babu a jikin sa..
Duk kirjin sa
ya tattashi Saboda azabar wahalar da yake ba Karima....
Yana cigaba da
dukan ta har sai da kayan jikin nata suka yayyage dukan jikin ta jini tsiyaya
yake....
Cilla ta ya yi
da kafa ta fadi kasa wargas...
Wani kofi ya
je ya dauko mai dauke da ruwan gishiri..
Tana kallon sa
da Idanun ta da suka kafe babu digon hawaye ta ce InshAllah abun da kayi mun
sai Allah ya yi maka wanda ya Ninka nawa....
Dariya ya
bushe da shi ya ce shegiya bakin ki be mutu ba Ko..
To. Yanzu zan
murje bakin naki...
Ruwan gishiri
dake hannun sa yadauko tare da nufar ta cikin wannan Jinin dake tsiya a jikin
ta da raunuka ya zuba mata shi yana murzawa da karfin sa..
Wani razananne
kara ta saki wanda amon muryan ta saide ya je kunne iya firdausi da take dakin
nata tana kukan Abun da akewa Yar ta..
Jin bazata iya
jurewa ba ya sa ta fito cikin hanzarin ta zatayi sashin Yarima Samad...
Bayi masu
tsaron kofar suka ce bazata wuce ba '' saide tajira kamar fita zeyi yanzu zata
ganshi......
Shiko Yarima
fitowa ya yi Daga dakin nasa adu'oi yatsaya karantawa dan yama mance kwata
kwata beyi ba.
Ita Ko Fulani
gajiyar da ta yi awajen aboye ga zafi ya sata sakin tari me karfi..
Yayi daidai da
karasowan Yarima daidai wajen..
Wayar sa ya
kunna tochla din sa '' tare da haskawa dan ganin meye awajen..
Caraf Idanun
su suka tsarke cikin juna shida Fulani cikin.....
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah7️⃣4️⃣
09069080725
Shida Fulani
cikin tsananin Mamaki ya ce Mama Fulani mekike anan lungun ya tsura mata
dararan Idanun sa '' masu kwarjini..
Fulani gyara
Tsayuwar ta yi tana saki tarin dayazo mata lokaci daya '' cikin Rawar murya ta
ce daman nazo inma ka wasan April koka mance yau ne first....
Cike da kallon tuhuma da yake bin ta da shi ya
ce inaga nidake ba abokan wasa bane inma haka ne din ma '' 'meye zaki shigo
lungu acikin lungun nake ne Ko a daki acen zaki sameni Ko.
Gayamin me
kike nema a lungun nan' 'hannun ta yake kallo ganin makullai dakin nasu cikin
tsananin mamaki ya ce mama Fulani wayannan makullan fa ina kika same su..
Cikin Rawar
murya ta ce makullai kuma ban san ya'akayi sukazo hannuna ba..
Mika mata
hannun sa ya yi ya ce miko min ingani yana karba ya tsurawa makullan idanu
ganin SD a jikin makullan ya tabbatar masa nasa ne ba zargi bane..
Nan da nan annurin dake kwance saman fuskar sa
ya ba ce bat ya murtuke fuska cikin rashin mutunci irin nasa..
Ya ce Hajiya
Salamatu kike Ko Fulani ni Sam bana iya tuna ainihin sunan naki...
Cikin tsawa ya
ce zaki gayamin abun da makullan dakina suke yi a hannun ba tare da da izinina
ba...
Koko so kike
mu je gaban Sarki acen zakiyi min bayani...
Cikin Daga
murya yake mata magana wanda ya sata gigicewa cikin tsananin tsoron yanda ya
canza launin sa..
Ta ce pls dan
Allah katsaya zan maka bayani Karima taban makullan ta ce bazata samu damar
bude mun dakin naka ba...
Gashi ina son
naje naga surukata insan ya ta tashi..
Kasaitaccen
Murmushi ya sakar mata cike da takaici ya ce uhmm wasa farin girki yaushe kika
fara damuwa da iyalina ban sani ba...
Karki damu
lafiya lau ta '' ta tashi.
mu je Ko yana nuna mata hanyar fita Daga
sashin sa
..
Sum Sum ta
fito cike da kunya tana gaba yana bin ta abaya yana Girgiza kai cike da mamakin
me yakawo ta..
Cikin hanzari
da saurin ta tafita sashin Yarima '' kofar fita ta iske Iya Firdausi tsaye tana
kuka hawaye shar shar...
Cike da
tsananin mamakin meya kawo ta '' cikin zare idanu ta ce iya Firdausi mekike yi
anan gashi tana tsoron Yarima yaritsa da ita tsaye anan wajen hakan ya sa ba ta
jira amsar da iya firdausi zata ba ta ba.
Tasakai tawuce
cikin sauri sauri..
Daidai da
fitowar Yarima da mamaki yake kallon saurin da Fulani ke zubawa.
Dawo da kallon
ya yi a kan iya Firdausi dake kuka ya ce Mama cike da girmamawa me kikeyi anan
wajen ya tsareta da idanu gashi time na tafiya dan baya Jin zeje gun Mamy..
Tsagaita kukan
ta ta yi ganin Yarima na shirin tafiya dan yama manta ya ce a kira masa Karima
taje ta taho da Rahama cikin masarautar...
Tsintar Murya
Iya Firdausi ya yi tana fadin.
Dan Allah
Yarima katsaya Karima ce tana hannun Karfin iko dan Allah kataimaka kada ya yi mata
illa takarashe zancen cikin tsananin kuka mai tsuma rai..
Cak yatsaya tare
da waigowa Arazane ya ce Karima !! Karima !! take hannun Karfin Iko..
Be jira amsar
iya Firdausi ba kai tsaye ya yi ɓangaren
gidan Yarin zuciyar sa tana harbawa da karfi
idanuwan sa sun rufe baya ganin gaban sa sai
duhu...
Tun daga Nesa
Karfin Iko ya hango Yarima zuwa hakan ya sa ya yi maza ya sa Rigar sa tare da
barin inda Karima take ya dawo da zaman sa kan kujera kan sa aduke...
Yarima kamar
anjefo shi Daga Sama haka ya karaso wajen yana bin Karfin iko muguwar kallo ya
ce kai dan iska ina Karima take bakin sa na Rawa...
Karfin iko
cikin farga ya ce tana ciki ranka yadade...
Wani tsawa
Yarima ya daka masa ya ce shege dan iska shiga ka fito mun da ita za ka gayamin
uban daya daure maka gindi A'cikin masarautar nan..
Karfin Iko cike
azzama da tsoro ya je kiran Karima ganin kamar ba ta numfashi.
Yasa shi ruɗewa yasoma jijjiga ta cikin
tsananin mamaki ya ce Karima bude Idanun ki '' ga Yarima nan..
Takun tafiyar
Yarima yaji ya shigo ciki cike da mamaki yake kallon Karfin iko da Karima dake
kwance kamar sumammiya' '..
Karfin Iko
cikin tsoron Abun da zeje yadawo ya ce InshAllah Yarima zata farka bekarasa
fadin abun da zefada ba Yarima ya daka masa tsawar daya gigita shi..
Cikin gigita
yake kallon Yarima' ɗuk
yabi yagama tsoracewa hakan ya sa cikin hanzari ya samo ruwa tare da dawowa gun
Karima ya yayyafa mata...
Amma still dai
shiru ba ta motsa ba.......
Wayar Yarima
ce tasoma ring yana dubawa yaga Kiran Faruk ne..
Babu ba ta lokaci
yakara wayar a kunnen sa cike da damuwa kwance a kan fuskar sa amma Idanun sa
nakan Karima dake kwance..
Ya ce Faruk
dafatan dai lafiya kuwa..
Daga can ɓangaren ya ce kai kadai ake
jira kai ka san Alkali badan shar'iar ka ba ce wlh ba zai saurare ka ba..
Dan kawuce
time amma nace su fara gudanar da wani shari'an kafun naka..
Yarima cikin
gamsuwa da bayanan Faruk ya ce godiya nake yanzu babu ba ta lokaci InshAllah
zantaho nima wani uzurin ne ya rike dafatan kuna Tare da Aminu Ko..
Faruk ya ce eh
gashi cen zaune yana chat.
Daga haka suka
yi sallama...
Shiko Yarima
dawo da kallon sa ya yi a kan Karfin iko dake ta faman yayyafa wa Karima
ruwa...
Bangaje karfin
Iko ya yi sai gashi yafadi akasa wargas yana nishi kamar wanda ya yi wasan
tsere...
Yarima
durkushewa ya yi gaban Karima yana kallon fuska ta yanda take walwali Idanun ta
arufe gam...
Hannun ta ya ɗaga tare da soma dan buga a
hankali '' still dai shiru kake ji..
Hakan ya sa da kansa yadauki wannan Kofin
ruwan da karfin iko ya ajiye agefen nasa...
Ya dauka yana
kallon ruwan yanda duk datti yataru acikin sa...
Cikin Daga
murya ya ce kai Karfin iko kake Ko Iko nima Sam bana gane sunayen ku kaida wasu
agidan nan..
Banza dakiki
maza je ka dauko mun ruwan Swan afirij din yan yari...
Shiru Karfin
iko ya yi yana kif kif da idanu cikin Rawar murya ya ce Ranka ya dade ai jikan
Sarkin Marwan ya hana asa ruwa a firij din sai dai na rijiya.....
Wani mugun
kallo Yarima kebinsa da shi tare da tashi tsaye ya ce what waye ya isa ya canza
dokar da nasaka babu izinina...
Na fada maka
babu wanda ze shiga gidan Yarima sai inhar ankama shi da laifi da shaidu..
Inada labarin
baku daina azabtar da bayi ba bisa zalunci kai har ka manta ni ne silan zaman
ka anan da innaso sai inbar ka a cigaba da azabtar da kai... Ba wannan ba..
Miko min
wannan ruwan hakanan ya Amshi ruwan hannun sa tare da karanto bismillah ya
watsa mata a fuska sau uku...
Numfashi ta ja
da karfi hade da sheshekar kuka sai fadi take dan Allah Karfin Iko ka kyaleni
wayyo kar ka kashe ni..
Jin muryan
Yarima ta yi yana Fadin Karima..
Bude Idanun ki
Abdul Samad ne agaban ki...
Ahankali
tasoma bude Idanun nata tasauke su a kan shugaban ta...
Ganin sa ya sa
sabon kuka ya kwace mata...
Cikin kukan
sai Fadi take ya shugabana kayi hakuri na take dokar ka ba tare da na iya
hanawa an amshi makullan kofar naka ba..
Wallahi fin
karfina akayi....
Rau Rau da
idanu yake kallon ta cike da tausayawa cikin cool voice dinsa da Idanun sa da
suka kawo ruwa ya ce uhmm Karima suwaye suka amshi makullan da karfin tsiya a
hannun ki...
Dago kai ta yi
tana kallon Karfin iko shima kallon ta yake yana Girgiza mata kai Alamun karta
ce shi ne...
Kasa da kanta
ta yi ta ce Karfin Iko shi ne ya amshe a hannun na...
Kallon kallo
Yarima da Karfin iko sukewa juna ajiyar zuciya Samad ya sauke yana kallon
Karfin iko dayaga Alamun tsoro ya bayyana a fuskar sa...
Ya ce kai dan
uban ka waya ba ka izinin amsar makullan sirrina...
Karfin iko
dake markakata bakin sa na rawa ya ce Yarima umarni na samu Daga Gimbiya Fulani
da Jikan Sarki Marwan...yakarashe zancen yana dukar da kan sa Alamun neman afuwa...
Yarima Samad
kallon sa yake yana nazartan kalaman da yanayin sa''' kauda kai ya yi Daga
kallon sa yadawo da kallon sa a kan Karima dake kokarin tashi tazauna nauyin da
jikin ta ya yi mata ya sa ta kasa....
Cikin takaici ya
ce wannan mugun dukan da kayiwa Karima ka faffasa mata jiki duk jikin ta jini
ne..
Wallahi saina
fanshe shi kabari inje indawo amma kafun nan zanturo gangami ya kulle ka a dakin
yari lamba uku inda yake kusa da masai nan za ka zauna tsawon wata daya tare da
horo yunwa '' sau daya za ka ringa ci arana''' bulala kullum za ka ringa shan
guda hamsin har tsawon wata daya wannan hukunci yana Daga cikin Adalci na....
Nan da nan
Karfin iko yarikice ya san abun da Yarima Samad yafada babu me canzashi..
Karima Da ƙyar
tamike cikin kuka ta ce shugaba na Da ƙyar inzan iya tafiya cike da tausayawa ya
ce wai gayamin abun da ya faru mana....
Nan ta shiga
bashi labarin abun da ya faru..
Jikin Yarima
ya yi mugun daukan zafi tana kai karshen labarin...
Cikin yin kasa
da murya ya ce zauna nan zanturo iya firdausi tazo ta tafi dake cen sashin ta
zata kula dake har indawo InshAllah '' 'inada aiki a gabana yafada tare da
barin gidan Yarin cikin saurin sa...
Cin karo da
iya firdausi ya yi da take kuka cikin saurin da yake yi yana kallon agogon dake
daure a tsintsiyar hannun sa..
Ya ce yawwa
gwamma ɗana hadu dake
Iya firdausi ina son kije gidan Yari ki dauko Karima ki ciccibe ta dan Allah ba
ta iya tafiya..
Ki kira
likitan masarautar mu ɗuk
abun da yake yi yabari ya je yaduba karima kice injini
yakarashe zancen tare da barin wajen ba tare
da yajira amsar iya firdausi ba.....
Ita Ko Iya
Firdausi cikin hanzarin ta '' tawuce wajen Karima zuwa ta yi ta ciccibe ta ta
yi dakin nata da ita tare da kiran likitan masarauta dan yaduba ta....
Yarima daidai
fita Daga cikin masauratar ya yi Horn mai gadi yana kokarin bude masa gâte..
Ya hango
gangami cikin shigar su na masu kula da yan gidan Yari..
Ihu kiran
sunan sa yyi hakan ya sa Gangami yakaraso cikin hanzarin sa..
Yarima cikin
ba da umarni ya ce ina son kaje ka hukunta mun karfin Iko kaida yaran ka..
Sannan horo
har tsawo wata daya har da na yunwa.....
Maida glass
din motar sa ya yi ya rufe tare da ficewa cikin tsauri yabar masarautar cikin
hanzarin sa..
Sam ya mance
da batun Rahama tana son fitowa
Labarin abun
da ya faru ya je kunnen Mamy dan kuskus akaitayi acikin masarautar..
Cikin tashin
hankalin daya bayyana a fuskar mamy '' barin dakin ta ta yi tare da fitowa nan
falo '' ta iske Ahmad zaune yana kallon video a tiktok sai washe baki yake musamman
wata big baby da taketa tikan rawa cikin wakar turanci tana sanye cikin riga da
mini siket ga karin gashi cike a kan ta '' tazubo shi '' Ko' 'ina sassan jikin
ta motsawa yake..
Cibiyar ta
yatsurawa idanu' '' yana Murmushi ''
Sam hankalin
sa ya yi nisa besan da fitowar Mamy ba...
Sai ji ya yi ta
wabce wayar Daga hannun sa''cikin fada ta ce baba na yaushe ka zama hkne kai ba
za ka bar rayuwar yahudu da nasara ba da rayuwar Arna ba' 'meye ribar wannan
video da kake kallon' 'cikin Daga murya take fada sossai Ahmad ya tsorace yau
Mamy da kanta take hawar shi da fada haka.
Cilla masa
wayar sa ta yi a kan kafar sa..
Ta ce maza
kashe wayar nan biyo ni kaji abun da Ya faru da Karima baiwar Samad..
Cikin tsananin
Mamaki ya ce Ah Ah meya same ta cikin gigita yake magana dan Sam baya Jin ze
iya yafewa wanda ya taba Karima..
Tashi ya yi yakama
hannun mamy cikin damuwa ya ce mu je Ko Mamy..
Yayi daidai da
fitowar Hassana Daga kitchen Ahmad na ganin ta yadaure fuska cike da takaicin
Mamy na wajen ya ce mata ina kwana..
Lafiya lau ta
ba shi amsa.
Kallon Mamy
take ta ce na ji kuna maganar Karima Allah ya sa lafiya Ko...
Nan Mamy
tashiga ba ta labarin abun da ya faru '' '.
Ahmad bejira
yaji karshen labarin ba..
Cikin zafin
nama da saurin sa kai tsaye dakin iya firdausi ya tafi...
Hassana cikin
tausayawa Karima ta ce gaskiya ba a kyauta mata ba..
Cikin yin kasa
da murya ta ce yawwa mamy yau nakeson inje babban kasuwar kwatano Tokpa zanje
indan yi siyayya kin san gobe tafiya ta..
Mamy cikin
rashin son Rabuwa da hassana dan sun Saba ta ce haba hassana yanzu baki Daga
tafiyar ba...
Hassana
Murmushi ta sakar mata ta ce Mamy tun da nazo banga mijin naki ba '' daman ya
rasu ne '' ko baya zama garine...
Mamy cikin
tsananin mamaki take juya kalaman hassana Girgiza kai '' ta yi ta ce Ah Ah be
mutu ba..
Idanu ta
tsurawa hassana ta ce nayarda dake zanbaki labarina '' amma da sharadi...
Hassana cikin
Jin dadin saukin kan Mamy ta ce meye sharadin InshAllah zan yi...
Mamy gyara Tsayuwar ta yi tana fuskantar
Hassana ta ce saikin gayamin abun da yakawo ki '' masarautar mu''
Kina gayamin
gaskiya nima zakiji gaskiya abun da kika tambaya...
Hassana sossai
ta yi mamakin Jin furucin Mamy..
Cikin tsananin
kaduwa ta ce kibari mu je mu duba Karima' 'mu dawo Ko..
Ahmad koda ya
isa dakin iya Firdausi iske Karima ya yi tana barci ga bandeji fari duk an
nannade mata kai...
Hannun ta
dauke da kalula ana mata karin ruwa..
Iya firdausi
cikin kasa da murya ta ce Ah Yarima Ahmad kaine..
Eh nine yabata
Amsa atakaice ina zuwa kawai ya furta '' be tsaya ba ta lokaci ba kai tsaye ya
yi Sashin Fulani cikin azzama..
Yayi daidai da
fitowar Mamy da hassana cike da mamaki suke kallon inda Ahmad din yashiga...
Mamy cikin
gigita ta ce Yaron nan yanda yake tafiya ba lafiya bane '' mu take masa baya....
Ahmad da
kafafun ya bankada kofar Fulani ya bude '' maida kofar ya yi yarufe tare da
danna mata key...
Fulani zaune
take tana yagan cinyan kaza...
Bata Ankara ba
'' sai ji ta yi anbuga mata uban naushi abaki '' kashin kazar...........
Muje zuwa.
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah7️⃣5️⃣
09069080725
Kashin kazar
dake hannun ta faduwa ya yi ka san carfet '' cikin gigita ta dago kai take
kallon Ahmad dake shirin kai mata wani dukan '' kaucewa ta yi cikin neman
hanyar guduwa ta ce Ahmad haukar naka ya tashi ne daman ba ka samu lafiya ba..
Wani wawan
rikon da ya yi mata ya sa cikin zazzare idanu ta ce Ahmad ka mance Koni wacece
nifa matar kanin uban ka ce...
Me nayi maka
ne '' da har za ka saka hannun a jikina takarashe zancen cikin kukan da yazo mata...
Ahmad dake
huci sama sama cikin dagawa ya ce uban me Karima ta yi miki kika sabanta mata
rayuwa zan babbalaki nima duk hukunci da za a dauka akaina adauka na yarda
zanjure '' cigaba da bugun Fulani yake ta '' ta Ko ina sai ihu take tana neman
ceto..
Mamy da
Hassana suna ta bubbuga kofar cikin ihu take magana tana fadin Ahmad kabude
kofar nan bakajina ne..
Ina bemasan
tanayiba '' ihun Fulani ya karade dukan Masarautar.
Labari ya je kunnen
Mai Martaba da Abban Marwan ga Ahmad nan yanata bugun Fulani '' bugun bana wasa
ba.....
Hakan ya sa
Sarki ya tura waziri ya je a balla kofar koda suka je kokarin su na balla kofar
'' Mamy ta ce karku balla kamar ya tsai gaita da bugun nata '' 'cikin ihu ta ce
babana dan Allah bude kofar nan' 'cikin tashin hankali take magana dan sossai
Ranta yake aba ce...
Daga cikin
dakin yana Jin muryan Mamy yakara damkar Fulani tare da kai mata naushi a bakin
ta nan da nan bakin ya rinƙa tsiyaya da jini..
Razannannen
kara ta saki' Kuka mai cike da tsoro Idanun ta sun canza launi zuwa ja' ''
hannun tasa ta taba bakin nata taga jini yabi hannun ta cike da ruɗewa take kallon Jinin tana
kallon Ahmad dake tsaye yana kallon ta '' hannun ya yi mata alamu cikin Daga
Murya ya ce Inkika kuskura kikayi tari anan wajen saina taka ki..
Hannayen tasa
ta toshe bakin nata tana zazzare idanu..
Jin karar buga
kofar yaki karewa ya sa ya nufi inda kofar yake..
Cikin hanzarin
sa ya bude kofar caraf Idanun sa ya tsarke cikin juna shida Mamy cikin bacin
rai Mamy ta Daga hannun zata mare shi..
Hassana tarike
mata hannun cikin magiya ta ce dan Allah karki mare shi Mamy ''
Waziri da bayi
da hadimai da kuyangu harda Abban Marwan cikin hanzarin su suka Shiga dakin...
Ita Ko Mamy
kallon Ahmad take cikin tsawa ta ce dan rainin hankali kashige ciki kajira ni ina
zuwa make kafada ya yi Alamun oho Ko a jikin sa '' tun da ya yi abun da ran sa
yake so beki duk wani hukunci da za ai masa ba....
Ahmad nawuce
wa '' 'Mamy ta ja hannun Hassana suka yi cikin dakin Fulani koda suka Shiga
iske fulani suka yi ana ta jero mata Sannu..
Abban Marwan
rike da roban ruwan dumi yana gasa mata bakin nata...
Sai Wash take
fadi tana ciza labban ta..
Cikin kidima
Mamy ke kallon yanda Fulani takoma cike da rudani ta karaso gaban Fulani cikin
muryan ban hakuri ta ce dan Allah Mama Fulani kiyi hakuri '' wallahi tallahi ban
san ya akayi yaron nan Bejin magana ta ba...
Harara Fulani
take watsawa Mamy cikin dauriya ta ce uhmm daman kin turo shi ne ya karasa ni
ko''' bayan kinsa dan naki yana da mental problèm ba daidai yake ba..
Abban Marwan
dake cikin Jin haushin Mamy cikin Daga Murya ya ce kinzo kiga Ko mata ta ba ta karasa
bane Ko..
To wlh kujira
kiga abun da zebiyo baya inban da rashin hankali Mata ta ze buga '' yaro mara
Tarbiyya irin uban sa...
Ran Mamy yakai
kololuwa wajen baci ta ce uhmm Ai mijina shi kuwa keda Tarbiyya ka san ance
Albasa batayi halin ruwa ba..
Ahmad danka ne
duk zagin da zakayi masa a kan ku ze koma amma InshAllah shi Allah ze wanke
sa''bana goyon bayan sa dan kowa bewuce kuskure ba...
Takarashe zancen
tare da kama hannun hassana dake shirin magana ta katse ta ta hanyar Jan ta
suka fice...
Waziri cikin
tsananin mamaki ya ce Ah Ah Fulani kinga ikon Allah ashe haka Yarima Ahmad ya
yi miki mugun ta'asa...
Barin su ya yi
dan zuwa sanarwa Sarki yanda abun ya ka sance....
Sarki na zaune
cikin jama'ar sa yana sauraron dawowar Waziri...
Isowar Waziri
ya sa Fadawa suka bashi hanya ya iso gaban Sarki cike da za kuwa ya rinƙa
bashi labarin yanda sukaga Fulani...
Salati Sarki
ya yi cikin tsananin damuwa ya ce Amma dai Ahmad wuyan sa ya isa yanka tome
dalilin daya sa ya mata wannan dibar haukan...
Gangami ya
nemi ayi masa iso '' 'babu ba ta lokaci Sarki ya ce ashigo dashi....
Cike da
girmamawa ya shiga jerowa Sarki kirari..
Allah
yataimaki Sarki Yarima Samad yabada umarni ahukunta Karfin iko' Kuma harna
aiwatar Saboda sanin dokokin masarautar nan..
Bisa laifin
dukan Karima da ya yi cikin umarnin Fulani a kan ta hana ta makullan sashin
Yarima' 'shi ne Marwan ya ce ahukunta Karima yana kai karshen labarin.
Gabadaya wajen
suka dau Salati..
Sarki cikin
gyaran murya ya ce da dai ba Karima ba ce wata baiwar ce zan iya magana' '' iya
firdausi da Karima '' yarima ne ya Fanshe su Daga masarautar zaria Nigeria dan
haka banda ikon shiga wannan zancen...
Duk abun da
Ahmad ya yi wa Fulani abu daya zan iya shi ne in hana shi kada ya sake amma
adokar masarautar nan babu hukunci a kan wanda yadauki hukunci a kan antaba
baiwar sa.....
Iya Firdausi
itama baiwar Yarima Samad ce ban san yanda abun ya juye takoma sashin Fulani
ba....
Gangami ya ce
Allah yataimaki Sarki zankoma daman dukan zancen kenan daya kawoni Daga haka ya
fi ce...
.........................................
Yarima Samad
'' cikin murnan Nasaran daya samu a kotu kan wannan matar da Aka ɗAnnewa hakkin ta...
Takardun ta da
komai ya mika mata..
Cikin kuka mai
tsuma zuciya ta ce Yarima nagode Allah ya saka maka da Alkhairi yanda ka
taimakeni InshAllah zan taimaka maka...
Cike da mamaki
Faruk da Aminu suke kallon ta...
.
Yarima ya ce
bangane zaki taimaka mun ba..
Hajiya zulai
'' cikin ɗAnne kukan
dayazo mata '' ta ce ina masaniya a kan wannan baiwar da kake nema shekara da
shekaru ɗana...
Cikin zazzare
idanu Yarima ke kallon ta cike da nazartan kalaman ta ya ce wace baiwar kenan
kike magana a kan ta..
Hajiya zulai cikin
yarda da kan ta ta ce Saratu mana baiwar Mahaifiyar ka habiba ''...
Yarima Samad
cikin hada rai ya ce kin san inda Saratu take kika kasa gayamin '' to ya akayi
ma kika san ina neman ta
ina da ayar
tambaya a kan ki....
Faruk da Aminu
dake tsaye wajen suna sauraron su''suka ce kwarai kuwa zancen ka haka yake
Yarima....
Zatayi magana
wayar Yarima tasoma ring' 'yana duba wayar yaga Mamy ce hakanan yaji faduwar
gaba cikin dauriya ya Daga wayar ta...
Daga can ɓangaren ta ce inafatan ka
gama abun da kake ina son ganin ka yanzu gidan nan ba ta jira cewar shi ba ta
katse wayar...
Rike da kugun
sa yake kallon Su Faruk ya ce muna iya tafiya na so inje gidan Su Faruk ingaida
iyayen nasa kaima Aminu mu biya naku gidan '' Daga baya zankai Rahama ta gaishe
su...
Faruk ya ce Ah
kar ka damu wani uzurin yana gaban wani naga kamar Mamy ke neman ka mu je dukan
mu.
Ko zuwa gobe
saikaje gidajen namu aiba bakon waje bane a wajen ka...
Yarima ya ce
godiya nake Abokaina dawo.da kallon sa kan Hajiya zulai ya yi ya ce wannan sirrin
da kike da shi kina tabbaacin zaki sanar mun komai kowani zaki gayan ki boye
wani...
Hajiya zulai
cikin tsananin mamaki yanda yake zaro zance.
da ya yi magana
inyayi shiru za ka ce bashi bane ya yi kalamin ba...
Ta ce Yarima
wannan hakkin da Aka kwace mun ka karbo mun wlh hadda hakkin daure wa karya
gindi shi ne Allah ya nuna mun ishara ina nufin Nina boye Saratu agida na watan
uku Sannan ta bar kasar ''...
Cikin razana
suke kallon ta dukan su''yarima innaliahi kawai yake ta maimaitawa acikin
zuciyar sa..
Ya ce hajiya
zulai maganar mu dake mai tsawo ne...
Tun da nasan
gidan naki nan da kwana uku innagama uzurin gabana zamu zo nida Abokaina harda
Mata ta...
Sossai ta ji
dadin furucin sa Daga haka suka yi sallama...
Faruk motar
Samad ya shiga '' Shiko Aminu ya ja tasu motar da suka zo da ita kotun....
Ahanyar su
Yarima Samad ya ce ka ga yanda Allah yake ikon sa Ko...
Wannan matar
ta yi AlKawarin zata gayamana inda Saratu take InshAllah mun kusa kawo rabin
matsalar gidan mu...
Faruk ya ce
gaskiya kam haka ne.....
**************************
Kano
.
Mama ita da
Aminiyar ta zaune gaban wani tsohon malami yana jan carbi dago kai ya yi yana
kallon su..
Ya ce Aishatu
gaskiya wannan matar saita haihu kuma tagwaye ne acikin nata mace da namiji...
Abu daya zakiyi
shi ne kisa mata guba acikin abinci taci ta mutu..
Koko kisa mata
maganin daze barar mata da cikin nata cikin ruwan shan ta...
Amma asiri ba
zai kamata ba dan tanada kariya sossai tattare da ita ba ta wasa da karatun
Alkur'an..
Sannan adu'oi
koda yaushe cikin su take '' 'mijin naku shima ba a iya samun sa..
Maganar
gaskiya yafison wancen matar' Ke kuma yana tausayin ki ne a matsayin matar da
mahaifin sa ya yi masa zabi kuma ya haramta masa rabuwa dake....
Sai maganar
Diyar ki Salma kuna son akashe wannan auren' 'shi abune me sauki' '' saide
mijin nata yanzu da gaske yana son Salman ya tuba a kan laifin sa na baya...
Yakuka. Gani
dago kai. ya yi yana. Kallon su....
Aminiyar Mama
ajiyar zuciya ta sauke cikin yin kasa da murya ta ce ai kawai araba auren
nan...
Akwai wanda
zamu hadata da shi wani Alhaji Ibrahim bushasha...
Sossai Malam
ya yi mamaki ya ce Alhaji Ibrahim baya kasar nan fa...
Aminiyar Mama
ta kwace zancen hannun malam ta ce yana garin mana '' 'har waya muna yi
dashi...
Shiko shiru ya
yi yana Girgiza kai yaso ya yi magana amma Aminiyar mama ba ta bashi dama ba...
Mama ta ce
uhmm ni dai araba auren so muke yazo har gida yabata Takardan saki har uku...
Malam ya ce
babu matsala cikin da take dauke da shi ya zaku yi...
Mama ta kalli
kawar ta tana jiran amsar ta...
Kawar ta ce
kawai Malam a barar da cikin me zatayi da wani ciki Ana neman wani sabon miji........
Malam ya ce
uhmm gaskiya ba zan iya lalata cikin ba '' Amma zan iya raba auren Daga haka
dai suka yi abun da za su yi.
Ya sallame
su...
Ahanyar su ta
komawa gida Mama ta ce ni dai ina son Sa'adatu wannan cikin jikin nata ya bare
wallahi niban haifi tagwaye ba ita ce zata haifa...
Kawar mama ta
ce karki ɗamu kamar
jibi za su dawo Ko '' sha kurumin data dawo ki sanar mun...
Cike da Jin
dadi suka taba hannun ita da Mama.....
Sheik zaune
kofar gidan nasa yana kallon ta inda Mama zata taho dan tafita babu izinin
sossai ransa ya baci....
Zaune yake
yana nazarin ina take zuwa ne. Kullum tun da yadawo ba ta zauna ba...
Kukan zuci
yake ya ce Abbana mahaifina kaine ka hadani da Ayshatu nasan rabon yaya ne ya
koka tsakanina da ita...
Amma tun da na
aure ta banji dadi ba '' 'ya Allah kashirya min Aisha ta''' adua yake sossai
A'cikn zuciyar sa...
Hango ta Daga
nesa ita kadai tana tahowa ya sa shi maida kallon sa a kan ta...
Cikin. Tsoro
da fargaban ganin mijin nata a kofar gidan nasu...
Jiki babu
kwari ta karaso, wajen tana kokarin wuce shi...
Taji yana
fadin Aysha dakata dan Allah karki dauke ni sakarai mana...
Cak ta tsaya
cikin sanyin jiki ta juyo tana kallon sa ''...
Bakin sa na
rawa ya ce Daga ina kike kuma da izinin wa kika fita sossai ya hada ransa...
Cike da tsoro ta
ce magani naje siye...
Maganin me
kike je siye yana kallon ta cikin ido...
Cikin yin kasa
da murya ta ce maganin haihuwa mana''' naga tun a kan Salma bankara haihuwa
ba...
Saboda tsabar
mugun ta shi ne ka nemowa Sa'adatu maganin haihuwa nika kyaleni Saboda ba ka ya
yi na..
Cikin kukan
Borin kunya ta ce dan niba fara ba ce irin ka shi ya sa ba a sona...
Baka nemana a
shimfida sai inhar Nice na nema....
Sake da baki
Sheik yake kallon ta har dariya ta subuce masa besaniba.....
So yake ya yi dariya
amma ganin ta ya sa yadaure...
Uhmm Ayshatu
kenan ya furta cikin Jan sunan ta.
Ya ce me kike
so inmiki wanda ban miki ba...
Kinzo kina
kawo zancen shirme mara tushe...
Bana kwanciya
dake uhmm dukan zancen banza kike yi ayshatu...
Kishin naki ne
ya motsa Ko haihuwa ta Allah ce shike ba wanda yaso kuma ya hana wanda yaso...
Keda Allah
yaba arzikin yaya wasu suna nan basu haihu ba kuma sun zauna lafiya...
Bâri kiji
maganar gaskiya aure zankara kwanan nan InshAllah..
Mama jin
kalaman sa ta yi kamar anbuga mata guduma akai...
Cikin zazzare
idanu ta ce aure kace fa
..
Cikin yarda da
kai ya ce eh mana kona wuce yin aure ne..
Dan haka
maganar haihuwa kishirya Inkinada Rabo sai Allah yabaki..
Cike da
takaici yawuce ta ya shige cikin gidan nasa yana juya kalaman na baya kwanciya
da ita...
Zama. ya yi kan.
Kujera yana Girgiza kai. Ya ce oh Allah mata iyayen sharri duk abun da kake
musu wataran za su ce ba ka taba tsinana musu komai ba...
Barin wani
tunanin ya yi tare da dauko Alkur'an mai girma yasoma karantawa.......
*******************,
***
Kwatano...
Sossai Mamy
take ta yiwa Ahmad fada a kan abun da ya aikata '' '
Koda ya Yarima
ya shigo Jin labarin abun da Ahmad ya yi besa yaji haushi ba kuma be masa fada
ba...
Zaune yake
yana kallon yanda Mamy ta zage. Tana fada iya gaskiyar ta...
Saida yaga
tagama ta zauna ya ce Mamy hakuri zakiyi damu fa..
Dan na Ahmad
kadan ne a kan nwa yanzu ma dakin Fulanin da marwan zani...
Sallamar
Rahama da Khadija ne Asiya da Salma suna biye dasu ya sa kallon sa yakoma
kansu...
Ganin Rahama na
cikin su ya fara kokarin dawowa hayyacin sa amma ina yariga da yadau zafi hakan
ya sa bekara.kallon inda suke ba....
Cike da ladabi
Rahama da Asiya da salma suka gaishe da Mamy amsa musu ta yi cikin yin kasa
murya ta ce Rahama har kin iso '' 'nuna musu Kujera ta yi da su zauna hakan ya
sa suka zazaauna Ko wanne su ya yi shiru..
Ita Ko Rahama
satar kallon Yarima Samad take da sam hankalin sa baya kanta....
Mamy cikin son
dakatar da shi ta ce bangane na Ahmad kadan bane me kake nufi Abdul Samad ta
tsare da idanu...
Ganin ya tashi
tsaye hannun sa dauke da katuwar ɗorina
ya ce Mamy babu ruwan ki...
Cikin Daga
Murya duka waɗanda ke
falon saida suka tsorota ganin yanda jikin sa yadau rawa sossai kamar mazari..
Cikin zafin
nama yajuya a fusa ce ze wuce kokarin tare shi Mamy take yi..
Ita Rahama
cikin hanzarin tabi bayan sa ganin yanda yake zuba uban saurin sai fadi take
Amjad Amjad Amjad....
Tsaya dan
Allah dan Allah katsaya Nice Rahama..
Cikin.............
Ta ku har
kullum KYAUTA Daga Allah7️⃣6️⃣
09069080725
Nice Rahama
cikin hanzarin ta da zafin nama amma ina ya yi nisa sai buga sauri yake kafun
isowar sa labari ya isa wajen Fulani ga Samad shima zuwa '' Fulani cikin
hanzarin ta canza daki tare da kulle kanta ta cewa bayi karsu ga inda take...
Koda Samad ya
iso yana ta dube dube '' 'cikin tsawa yake kallon bayin ya ce ina Shugabar ku
take....
Bakin su na
rawa suka ce ba mu inda ta tafi ba' '' ya yi daidai da karasowan Rahama da
Mamy...
Rahama kama
hannun sa ta yi cikin takaicin ashe haka ya iya fada '' ta ce haba Amjad dan
Allah kayi hakuri duk da ban san mêke faruwa ba.
Ganin Mamy
zatayi magana ya fi ce Daga dakin direct dakin Marwan ya shiga..
Marwan kwance
yake yana Waya da Yarinyar da yake so ya aura...
Kamar Daga
Sama yaji antake masa hannun sa dake rike da wayar da karfi wanda yajawo
fashewar wayar a hannun sa''nan da nan hannun ya amsa Alamun gocewa...
Cikin gigita
yadago kai ganin Yarima' Samad ne a kan sa Idanun sa '' babu annuri..
Wannan dorinar
yake ta lafta masa ta Ko ina yana magana cikin ihu ya ce na rabaka da Karima da
ka san wacece ita Sam ba za kayi mugun tunani a kan ta ba...
Karima ba
baiwa ba ce '' tsagaita maganar sa '' ya yi yaci gaba da bugun Marwan yana ihu
iya karfin sa...
Mamy da Rahama
ne suka yi nasaran shigowa dakin '' 'cikin tsawa ta ce daman haka kuke kaida
Ahmad bakuda mutunci''' kuma inhar rashin mutunci naku ya motsa bakwajin bari..
Yanzu dan
Allah ni me kuka daukeni mara amfani kenan inhar ba ka daina bugun sa ba'''
wallahi zanbar muku gidan naku'''.
Cak Yarima ya
tsaya kamar an dasa shi '' cike da nadama ya juyo yana kallon yanda Mamy ke ''
kuka '' cikin rarrashi ya ce dan Allah Mamy karkiyi fushi damu '' fushin ki ''
'musiba ce a gare mu..
Ban san yanda akayi
nakasa iya contrôle din kaina ba....
Shiko Marwan
da Allah ya cece shi be jigata ba''' ya fara neman hanyar barin dakin...
Mamy dake
kallon sa cikin kalan tausayawa ta ce ɗana
Marwan dan Allah kayi hakuri'' Nice Mamy dinka ka san ba zan taba yarda Samad
ya zage ka ba..
Bare duka' ina
neman Afuwa....
Marwan dake
kallon ta''' cikin kuka dayazo masa '' ya ce Karki damu Mamy nasan ba za ki
aiko shi dan yabugeni ni sheda ne '' kece ma kika dakatar da abun da yake
aikatawa...
Kokarin fita
Daga dakin yake '' 'yaji Mamy ta kama hannun sa''' ta rungume sa cikin kuka ta
ce Marwan dan Allah kadawo a Marwan dinka na Asali dana sani' '' Nice nan na
raineka '' Saboda me za ka juya mun baya '' 'ina tarbiyyan ɗana ba ka sossai take
kuka...
Dukan ila irin
jikin kowa dake dakin saida ya yi sanyi har shi Samad din..
Sossai yake
nadaman daukar wannan dokar a hannun sa''' sai yanzu yake Jin dadin da Allah ya
sa bega Fulani ba ''' da ita ce yakama abun ba zaiyi kyau ba...
Marwan cikin
tsagaita kukan nasa ya ce Mamy InshAllah zanshigo sashin naki zuwa anjima yanzu
zanje aduba mun hannuna ne kamar na goce '' yafada yana kokarin sakin jikin
Mamy.....
Mamy Sam taki
bashi damar tafiya da kanta tasa Samad yakira wanzam ya duba shi '' Koda wanzam
yazo yana duba hannun ya ce gaskiya ya yi mugun gocewa zeji zafi inhar zan gyara'..
Mamy dake
kallon Marwan ta ce kabari ya yi maka dan kada abun ya fi haka..
Wanzam ya
shiga gyaran hannu Marwan yana ta ihu cikin Jin zafi da radadi da azabar ciwo
da yake masa..
Gabadaya dakin
kowa ya yi jugum yana kallon Marwan cike da tausayawa...
Sallamar Ahmad
ne ya sa hankalin kowa yakoma a kan sa.
Mamy taresa ta
yi tana ce shima yazo ya yi na rashin mutunci ne...
Ciki damuwa ta
ce kai baba na meya kawo ka...
Ahmad ya ce ah
ya ba zan zo ba nida dakin kanina marwan na ji abun da ya faru da shi ne '' shi
ne nazo in jajanta masa yakarashe zancen tare da shigowa cikin dakin...
Kallon Asiya
yake yanda ta yi shiru tana jinjina Al'amarin '' 'cike da isa ya ce keee baki
isa gaisuwa bane....
Kowa ya gaishe
ni acen bandake.
Asiya cikin
rashin son magana' Kyale shi ta yi ba ta tanka masa ba..
Ransa ba ƙaramin
baci ya yi ace kamar shi wai ze mata magana ta' '' amma ta kunya ta shi lallai
zata san koshi waye agidan nan....
Nan dai aka
gama komai
Mamy ta rinƙa kula
da Marwan ba ta bari ya nemi abu yarasa ba..
Yarima Samad
da Ahmad fadar Sarki suka nufa..
Inda suka iske
Sarki zaune bayi suna masa fifita '' 'shigowar su ya sa ya fadada Murmushin' tare
da fadin maraba lale da mazan fama...
Watau baku
tsoro ko..
Yarima Samad
cikin yin kasa da murya ya ce tsoho mai ran karfe...
Kayi hakuri a
kan abun da Ahmad Yayiwa Fulani zan masa fada nan gaba kada yakara..
Ni kuma dai
sai Adu'a abun da na yi wa marwan ina son komai yawuce duk wannan abun ya faru
ne a kan taba Karima..
Basu San
wacece Karima ba'' shi ya sa suke takata son ran su...
. Sarki dake
kokarin gyara rawanin sa' 'ya ce bangane basu San wacece Karima ba..
Naga baiwar ka
ce..
Yarima Samad ya
ce eh mana baiwa ta ce...
Katse firan ya
yi da fadin gobe in Allah yakaimu yan uwan Rahama za su wuce..
Sarki ya ce
MashaAllah har lokaci ya yi babu matsala kadai shirya masu tafiyar Ko..
Samad ya ce na
shirya komai '' rana kawai ake jira yazo..
Suna gama
tattauna suka bar fadar Sarki cike da mamaki Sarki ke kallon su yanda suke
tafiya komai nasu iri daya......
Anty cikin
shigar ta ta atamfa sossai dinki ya zauna mata ajiki tasaka hijab din ta..
Wayar ta na
ring cikin hanzari ta duba ganin yayar ta ce Daga can kanon cike da hanzari ta.
Ta Daga wayar Daga
can ɓangaren ta ce
Sa'adatu ance gobe zaki dawo in ji mijin naki...
Murmushi anty
ta yi ta ce amma dai Sheik yacika zumudi shida ya ce mun aure zekara yakamata
abawa Amarya hakkin ta Ko...
Daga can ɓangaren ta ce wai kina
nufin dagaske auren zeyi ina ya samu matar auren ne...
Anty ta ce a
Gabon ya samu kuma ya karba daman a jirace yake..
Amma Sa'adatu
kina ganin beyi tsauri ai sheik duka nawa yake dazeyi mata uku ''..
Anty cikin
jinjina kalaman ta ce yanzu sheik bekai 50 ba aduniya yaya ta kinga Ko haryanzu
da karfin namiji ne fa..
Wallahi ya yi auren
sa '' Allah yabamu tagari '' meye matsalar dazai sa kadamu kanka tun da mijin
ka yana kula da kai yana kula da cin ka da shan ka lafiyar ka....
Mata dayawa
wallahi rashin samun wayannan abubuwan ya sa suke gudun mazan su
Su kara aure
ni wlh har gudummuwa zan bashi in auren ya tashi...
Daga can ɓangaren rasa abun cewa ta
yi cikin kuka ta ce Sa'adatu ke anya kina da kashi a jikin ki kuwa...
Sossai Anty ta
jinjina kalaman ta '' ta ce ban san me kika gani ba ya sa kika fadi haka ba..
Amma sai ince
miki babu ɗan Adam dake
rayuwa babu kashi a jikin sa...
Nasan kina
magana a kan karin auren sheik..
Ba a aure ne
'' ni ya aure ni....
Karfa ki manta
yana da aure na aure shi..
Inhar nadauki
hakan amatsayin laifi ne auren dazeyi kenan nima kuskure na tafka wajen amincewa
da auren nasa..
Duk da Aminin
sa ne yahada auren...
Numfashi ta
fesar tana kokarin daukar jakar ta..
Ni dai Dan
Allah mubar zancen auren mijina...
Daga haka suka
yi sallama..
Ita Ko Anty
tsaf ta fito inda kai tsaye sashin Mamy ta nufa dan kiran Asiya ta rakata
kasuwar kwatano...
Tana isa
sashin Mamy ta iske su Rahama cike da jin dadi ta rungume Rahama ta ce daughter
kina nan..
Rahama ta ce
eh antina bark da fitowa..
Cike da
girmamawa anty ta gaishe da Mamy ɗasu
Samad da Ahmad...
Kallon ta ta
dawo da shi a kan Asiya ta ce yawwa Asiya zoki rakani kasuwar kwatano atamfofin
garin ance suna kyau sossai...
Ahmad dake
sauraren zancen nasu ya ce kwarai kuwa suna da kyau sunfi na Nigeria kyau da
kwaliti...
Kasuwar zakije
ne yajefo mata tambaya.
Anty ta ce eh
nan zamuje nida Asiya..
Jin da Asiya za
a je ya ce OK bari zan kaiku.
Salma ta ce
nima zanje.
Ahmad cikin
sakin fuska ya ce ai babu matsala..
Rahama tana
satar kallon Samad da Idanun sa ke kanta yana jiran yaji itama me zata ce.....
Cikin yin kasa
da murya ta ce nima......
Kema zaki je
Ko be bari takarasa fadin abun da zata ce '' 'uhmm babu inda zakije agidan in
gayamiki nima akwai inda zamuje nidake dan haka tashi Muje...
Mamy dake
kallon rashin idon Yarima Samad ta ce uhmm ni kadai za a bari agida ne...
Samad ya ce ga
khadija nan nabaki aron ta har indawo.
Sossai Khadija
ta ji haushin hanata fita da ya yi gashi babu waya '' 'cike da takaici ta kasa
boye fushin ta..
Ta ce haba
yaya Samaɗ 'bekamata
amun haka ba' kabari in raka su Asiya ka ga baki ne suna bukatar taimakon yar
gari..
Sossai ya
jinjina kalaman babu daman ya ce bazata je ba ganin yanda anty ta tsura masa
idanu cikin yarda da zancen khadija...
Kasa da muryan
ya yi ya ce to Allah yakaiku lafiya yadawo daku lafiya...
Mamy ta ce
ameen babu komai ai hassana tana nan maida kallon ta yi a kan hassana ta ce
yawwa taso mu je mu duba lafiyar Karima..
Bayan duk sun
watse masu tafiya kasuwa sun wuce '' 'Yarima ya ja Rahama a mota da batasan
inda za a kai ta ba........
Ko da Mamy ta
isa wajen Karima iske ta ta yi zaune iya firdausi na ba ta ruwan shayi Da ƙyar
take amsa...
Ganin Mamy ya
sa ta kakaro Murmushi cike da kaunar Mamy tai mata alamu da idanu na Barka
dazuwa..
Mamy ta
karanci abun da take son fadi ya sa ta nufe ta cike da tausayawa sannu kadai
take ta jerowa Karima '' 'iya firdausi na amsawa da yawwa.......
Hassana gyaran
murya ta yi tana kallon iya firdausi ta ce amma gaskiya ba ƙaramin
illa akayi mata ba' Koda yake ai yarima yadau mataki a kan wannan abun shida
Ahmad...
Iya firdausi
cike da Jin dadi ta ce wallahi banda abun da zan iya biyan Yarima Samad da
Ahmad wallahi sun mun dukan mutunci nida Karima.....
Juyowa ta yi tana
fuskantar Mamy ta ce dan Allah Mamy ki Amsheni Daga hannun Fulani akwai bayi
dayawa a masarautar nan kuma tanada wasu bayin bayan ni dan Allah ki maidani a
matsayina na yar wajen ki....
Sossai Mamy ta
tausaya mata ta ce InshAllah zan aikawa Sarki takardan na janye ki Daga hannun
Fulani '' 'itama Fulani zan aika mata saita nemi wata a madadin ki....
Saboda tsabar
Jin dadi iya firdausi durkushewa kasa ta yi tana jerowa mamy godiya da
adu'oi...
Yarima kiran
Mamy ya yi yana tambayar irin kayan abincin da ze siyo wa Karima wanda zata ji
dadin cin su...
Ganin tana
dakin ne ya sa ta yi musu sallama tabar hassana a dakin..
Cikin Jin dadi
ta zayyana masa duk abun da yadace da siya mata yakawo gida Daga haka suka yi
sallama....
Ahmad koda
suka isa kasuwar daidai parking space ya paka motar sa...
Habawa jama'ar
wajen suna Ganin jikin lambar motar An rubuta Yarima Ahmad no 6..
Gabadaya wajen
aka tattaru da masu son ganin sa basu taba haduwa da shi ba sai a hoto dan ana
maganar '' matashi ne me cike da izza da takama........
Ahankali ya
fara sauke kafafun sa Daga cikin motar wanda yajawo hankalin dumban jama'a
wajen jiran suga fuskar sa.....
Fitowa ya yi gabadaya
Daga cikin motar yana sanye cikin boyel fara ba ƙaramin kyau shigar ta yi masa dan ya samu
din ki Daga kwararren tela...
Ganin Idanun
mutane a kan sa ya sa ya hada rai sossai kamar be taba dariya ba..
Kokarin bude
musu kofar yake Albarkacin Anty ya yi daidai da Asiya tana cikiniyar budewa...
Ganin hakan ya
sa ya janye hannun sa yana hararan ta '' taka san idanu...
Tsaf tagane abun
da yake Ganin su Anty ya sa ta sakar masa Murmushi tare da fadin yaya Ahmad
basai ka bude mu ba..
Kawomu ma da
kayi shima wani karin girma na samu awajen ka..
Drever dan
Allah mu je ka kai mu shagon da zamuyi siyayya duk abun da take fade babu wanda
yake Jin abun da take fadi sai shi da yake kusa da ita....
Sossai ran sa
yabaci yana nanata kalmar drever''' a zuciyar sai fadi yake wlh saina gyara
miki zama Asiya kafun kibar garin nan........
Jama'ar wajen
sai kuskus suke ta yi. Suna fadin anya ba matar sa ba ce...
Wasu Daga
cikin su suka ce gaskiya beyi aure ba sai dai in ita ce ze aura duba da irin
kallon da suke wa juna yakawo cece kuce a kasuwar...
Wata mata
acikin shagon ta le kowa ta yi dan kallon su cike da tabe baki ta ce amma
wannan kamar matar sa baku ga yanda yake bin ta abaya ba '' yana Girgiza kai...
Ganin Khadija
ya sa su Fadin kai yau khadija Turaki nan wlh ba mu taba ganin ta acikin gari
ba...
Sai dai a
hoto...
Babu ba ta lokaci
suka cusa cikin kasuwar inda ya yi musu jagora wani babban shago dan yin
siyayya '' ɗuk abun da
suke hankalin sa nakan Asiya yana tabe baki aransa sai ayyana yanda ze hukunta
ta yake....
**************************
Yarima Samad
bayan sun gama siyayya kai tsaye wani babban wuri yakai su wanda sai wanda ya
amsa sunan sa yake zuwa wajen....
Isowar Yarima
Samad ba ƙaramin
matukar bazata ya yi wa mutanen wajen ba..
Karanta sunan
wajen nayi naga anrubuta SAMAD...
Cike da Mamaki
Rahama take bin wajen da kallo..
Ganin su ya sa
duk aka fara fitowa da duk waɗanda
ke wajen dan oga yazo ba asan ganin kowa harsai yafita....
Rike da hannun
Rahama suke.tafiya. Ma'aikata suna ta yi. Masa welcome
Hannun kawai
yake Daga musu '' 'cikin isa da izza yakara rike hannun Rahama gam yana satar
kallon ta ya ce kinga nan wajen.
KADA masa kai
ta yi ya ce nan wajen na danki ne da zaki haifa mun' Kuma sunan ubansa zeci
watau Abdul Samad kin san Saboda me zanyi haka....
Girgiza kai ta
yi ta ce A'a saika fada cikin zazzakar muryan ta....
Uhmm wannan
wajen...... 7️⃣7️⃣
Uhmm wannan
wajen yana Daga cikin wurin da nayi shekara da shekaru ina mafarkin ki...
Rau Rau da
idanu take kallon sa cike da tsananin mamaki ta ce bangane ba.
Fahimtar
dani..
Ciikin da
zakuwa ya ce Rahama yakamata kisan, wanene asalin mijin naki '' dan kisan yanda
rayuwar auren namu ze tafi...
Cike da
gamsuwa ta ce inajin ka Amjad dîna tare da maida kallon ta agareshi cike da
zakuwa son Jin labari abakin sa..
Numfashi ya
fesar ya ce Mahaifiya ta Asalin ta Yar garin bohicon ce cikin unguwar zongo...
Rahama cike da
rashin Fahimta ta ce inane bohicon Amjad.
Murmushi ya sakar
mata cikin sakin Fuska ya ce bohicon itama jaha ce me zaman kanta kamar kwatano
'' amma asalin garin kamar kauye ne '' zamani yazo da sauyi hakan ya sa ba za
ka taba iya kiran sa da kauye ba '' saide kwatano yana gaba da ita dan ita ce
Capital din kasar Benin Republique...
Sossai Rahama
ta jinjina uhmm Amjad cigaba da ba ni labari dan nima inba wasu anan gaba...
Murmushi ya yi
ya ce wasu kamar wa Kodai yayan da zaki haifa mun su zaki ba labari..
Cike da
Murmushi ta ce uhmm yaya kuma ina nagansu ni dai yanzu abar wannan zancen aci
gaba da ban labarin baya....
A garin
bohicon ne mahaifina Salihu Turaki ya yi karatu wajen mahaifin Mamy wanda ake
kira da malam Ahmad sossai wannan malamin ya yi suna awannan garin Daga nisa ɗana kusa ake kawo masa
dalibai karatu lokacin da Sarki Turaki ya tura yayan sa guda biyu Salihu da
SANI GARIN BOHICON SANI YAKI ZAMA YA CE WAHALA AKE BASU BASU CIN Abinci kan
lokaci...
Ya damu shidai
ba zai iya zama ba shi kwatano ze zauna har yasoma guduwa Daga Makaranta yana
yawon bin abokan banza wannan dalilin ya sa Sarki Turaki yadawo da shi gaban
sa..
Yabar Salihu
kadai a garin kwatano yanda ake ba mu labarin sa '' babu wanda yataba sanin Dan
Sarki ne saboda yana mu'amalar sa kaman dan dabeda gata duba da irin suturar da
yake sawa '' 'Malamin da yake koya masa Karatun Malam Ahmaɗ'' duk cikin daliban sa
babu me yi masa biyayya kaman Salihu Ko lokacin da Salihu ya je Saudiya ya yi karatun
sa ya yi degree acen Daga can ya samu wani babban aiki' '' mahaifin Sa ya ce
Sam be yarda ba yana bukatar sa akusa da shi dan yanzu girma yasoma kamashi...
Babu yanda ya
iya hakanan yadawo kwatano watan bakwai da dawowa malamin sa ya aika yazo garin
bohicon yana son ganin sa....
Koda ya je garin
yanata sake sake dalilin kiran gaggawan da ya yi masa bekawo komai aransa ba..
Yatafi garin
bohicon '' a lokacin cikin shigar sa na Alfarma yatafi '' ya bakar motar sa
jeep '' daidai kofar gidan Malam Ahmad ya paka motar tasa....
Bayan ya isa
gidan sun zauna sunyi firan yaushe gamo' '' Sannan Malam Ahmad yazo masa da
bukatar yanason ze ba sa daya Daga cikin yayan sa...
Sossai Salihu
ya shiga damuwa dan bekawo aure akusa ba...
Malam Ahmad
daya karanci damuwa a kan fuskar sa ya ce inhar kana ganin ba ka bukata ba zan
matsa maka ba na yi wa yayana sha'awan samun miji irin ka nagartacce...
Jin wannan
furucin nasa ya ce ya amince hakan ya sa a kira masa yayan sa mata guda uku ''
dan manyan yayan nasa ba sa kasar suna misra..
Koda suka iso.
Farida.
Habiba.
Firdausi...
Salihu yana.
Ganin su yarasa wacce ze zaba kawai lissafi ya kunce masa hakan ya sa ya yi amfani
da llimin sa '' wajen yi musu tambayoyin da ya shafi Addini Ko wanne su ya ba
shi amsa daidai gwargwado '' duk da basu son dalilin turo da akayi wajen Salihu
ba '' amma Farida lokaci daya ta ji ta yaba dan batasan hakan yakeda kyau ba
duk zaman da ya yi agidan nasu saida hutu yazauna jikin sa sossai...
Ganin yarasa
Mafita ya sa shi tunanin inda ze bullowa Al'amarin '' tun da suka shigo dakin
Sam Habiba taki Daga kai bare ta kalle sa '' sai dai yaji ta yi magana kanta
aduke...
Yana son mace
mai Alkunya '' kuma ya san habiba ciki da waje '' duk cikin su ba ta da
hayaniya hakan ya sa ya ce ya ce sauran su bashi waje ze gana da Habiba sossai
ran Farida yabaci ya za ai tana babba ze fadi haka....
Koda yagama
tattauna da Habiba ya nuna mata yanason ta da aure kuma bakowa ne yaturo sa ba
daman ya dade da wannan kullin aransa mahaifin ta ne ya ba shi damar yazo ya
duba wacce ta yi masa '' 'shikuma yana da muradin sa ita ce...
Sossai ta ji
dadin haka duk da ba ta nuna ba'''..
Koda sauran
yan uwan nata suka ji labarin aure za a kulla tsakanin habiba da Salihu afili'
'farida ta nuna zallan kiyayyan ta....
Da hassada da
bakin ciki ta yi magiya a kan mahaifin nasu ya janye auren da Habiba ayi da
ita...
Shikuma ya ce
besan da wannan zancen ba...
Amma zehada da
wani yaron wani dan kasuwa Alhaji kawu.....
Sossai ta ji
bakin cikin hakan duk da bashi taso ba ta amince ne dan shima akwatano za su zauna....
Masarautar
gheuzo suka nemi auren Habiba aka basu kamar yanda suka bukata..
Komai ya
kankama akayi auren Salihu da Habiba..
Farida da
bilyaminu wanda ake. Kira da kawu....
Koda aka kawo
Mamy masarautar babu kowa sai ita Abban Marwan beyi aure ''ba...
Sallamar me
kawo abinci da kayan drinks su lemuka ne ya sa Yarima yin shiru yana kallon
abinci cikin kasaitaccen murmushin sa ya ce Ramatullah ga abun tabawa muci
indan mun gama sai aci gaba da labarin Ko...
Hada rai ta yi
cikin wasa sossai labarin da yake ba ta ya yi mata dadi kamar wasan kwaikwayo
take kallo ganin yanda yake ba ta labari daki daki kamar a gaban sa kayi...
Cikin tsare sa
da idanun ta masu kashe masa garkuwan jiki '' ta ce uhmm daman lauyoyi akwai
iya ba da labari '' tun da kace sai naci wani abun Sannan zakaban sauran
labarin ''..
To kafara ci
dan ni wallahi hakanan na ji bana sha'awar wannan abincin tana turo baki gaba..
Kallon ta yake
cikin sakin Murmushi ya ce bakyaso Ko..
Gyada masa kai
ta yi eh banaso saide Insha lemu...
Waini dan
Allah ba ayin dan wake ne yau na tashi da bala'in kwadayin sa...
Kuma inhar
banci ba akwai matsala...
Rau rau da
idanu yake kallon ta tare da dauko kofi ya tsiyaya lemun yana kokarin kaiwa
bakin sa '' 'Ya ce dan wake kuma Hubby meye hadin mu da shi nifa tun da nake
sau daya aka taba cin sa agaba na..
Naga Mamy tana
yawan cin sa amma saide taban labari..
Pls hubby
karki ci ki fadi wani abun daban zan nema miki yana marairace mata fuska kamar ƙaramin
yaro...
Hada rai ta yi
sossai tasha kunu shi ne karo na farko arayuwar sa daya ganta cikin wannan
yanayin cikin sakin kukan shagwaba tana bubbuga kafafun ta akasa ta ce wallahi
ban yarda ba..
Ni dai inbanci
danwaken nan ba akwai matsala fa...
Ganin hankalin
ma'aikatan zedawo kansu ya ce to na ji zomu je cikin zongo na ji acen ake samun
masu saida kokuma inkira Ahmad ya nemo miki amma fa wallahi zaki zubar masa da
aji wajen siyan dan waken nan yana sakin dariya...
Uhmm babu komi
aiba kashi ya je siye ba kawai bawa na bukatan abu ace wai da kunya siyan sa...
Yaji kunya din
kila akwai yan matan sa ne a unguwar takarashe zancen tare da daukar wayar nasa
ta ba shi...
Kallon wayar
yake ya ce kash sarkin mayata wai Ahmad din ne zan kira yana kasuwa fa...
Ganin zata
fara bubbuga kafarta ya sa shi fadin yi hakuri gashi na danna masa kira....
Ahmad dake
kokarin saka kayan da anty ta yi siyayya yana zubawa a boots din motar sa...
Yaji karar
wayar sa yana dubawa yaga Samad cikin hanzari ya ɗaga...
Daga can ɓangaren yana Murmushi ya ce
uhmm kanina na kaina kana ina ne...
Ahmad najin
wannan kirarin ya san aike ne wanda ba zai masa dadin zuwa ba...
Turo baki ya
yi gaba ya ce yaya kenan fadi me zan maka...
Yarima cikin
ba da umarni ya ce yawwa mata ta ce take son dan wake duk inda ake saida shi
kaje yanzu ka nemo mata. Kamar a zongo ba a rasawa...
Ahmad cikin
razana ya ce what banji da kyau ba yaya danwake fa kace...
Daga can ɓangaren ya ce eh shinake
nufi yanzu nakeso fa '' 'mata ta ke bukata...
Cikin tsananin
bacin rai ya ce kamar...........
Ta ku har
kullum kyauta Daga Allah
Ta ku. Har
kullum kyauta Daga Allah7️⃣8️⃣
09069080725
Ya ce danwake
fa kanbuhu lallai '' cikin yin kasa da murya ya ce to yanzu de muna kasuwa sai na
koma gida nakoma nasiyo mata dutsen...
Samad dake
murmushin kalamin Ahmad ya ce na ji Ko Arfa ce ni dai kaje kuma ta ce asa yaji
sossai Ko kuma kabiya super market kasiyo mata haddaden yaji...
. Cikin Kosawa
da zancen Ahmad ya ce na ji bejira cewar Samad ba ya katse wayar maida kallon
sa ya yi a kan Asiya dake kokarin zuba kayan nasu cikin mota ba '' suna gama
zubawa yarufe..
Anty tashige
gidan baya '' ita da Salma da khadija '' 'Asiya zata shiga Ahmad ya ce' Kai
Asiya kunyi yawa abaya ke dan zo gabana mana ki zauna...
Cike da
takaicin kalaman sa tasan da wata manufa akasa...
Hakanan taje
kujerar gaba ta zauna ya juya ta dayan ɓangaren
motar ta sa tare da zama mazaunin drever' '' kokarin tada motar yake..
Ganin sansanin
yan kasuwa da yan shigo na fito '' duk suka jeru ana kallon sa wasu har selfie
suke daukan sa Daga nesa ganin haka ne ya sa shi tada motar tare da tada kura
awajen wanda ya yi sanadin wasu na fadin wai Allah ze kashe mana idanu..
Wata ta ce ba
gulma bane yakai ku ba aiyana sane wlh maganin sa'idawa yayi..
Tuki yake
yanata cin fada shikadai ya ce haba mutum beda ikon ya je wani wurin asirrince
sai dandazon mutane sun cika a kan sa wannan dalilin ya sa duk son yawo na Inde
ba ɗare bane to
bancika yin sa ba...
Asiya hararar
sa take ta gefen idanu' 'cikin yin kasa da murya ta ce in banda shirme irin na
mutane me za su kalla a tattare da kai nagadai ba kyau kafisu ba..
Ko wani
abu.ba..
Salma dake
kujerar baya tabe baki ta yi ta ce haba Asiya wallahi Yarima. AHMAD aikuwa abun
kallo dan yana kyau fiye da misali dan ya fi mijin Rahama ehee....
KADA kai Ahmad
ya yi cikin takaici ya ce Salma kedai barta '' banda lokacin ta.....
Khadija da Anty
dariya suke yi inda anty ta ce yi hakuri Ahmad '' Asiya haka take da wasa
take....
Asiya ta karbi
zancen ta ce haba anty wlh ba wasa nake ba..
Ke kuma Salma
da kike cewa ya fi Yarima Samad kyau lallai na yarda bakisan me ake kira
natural kyau ba wlh..
Habawa mijin
kawata' 'hadadden namiji ne' ga kyau ga iya taku''' ga respect ga ilimi duk
inda ake son namiji yakai kedai Salma bar zancen kawai Rahama ta dace.....
Ahmad sossai
kalaman ya doki zuciyar sa sai sake sake yake yi a kan yanda ze gyara mata
zama' '' murmushi ya yi ya ce Asiya bakiyi karya ba '' Ance yabon gwani yazama
dole...
Shiru ne ya
ratsa acikin motar '' babu wanda ke magana banda wakar dake tashi acikin motar
da anty duk ta takura bude volume din ya yi duk yacika motar da wakar Hamisu
break..
Wanda yake
fadin
Ashe da rai
nakeson sahiba ba da zuciya ta ba...
Komai ruwa da
iska a kan ba zana daina kewa...........
Sossai khadija
da Salma suke bin wakar.......
*****************
Rahama tana
gama shan lemun kwalin exotic dake gaban ta '' cike da zakuwa ta ce yawwa Amjad
ba ni labarin Da kake ba ni dazun nan..
Tsagaita abun
da yake yi ya yi ya ce uhmm labari yasha ruwa inhar kina son inbaki full labari
saide yau kimun AlKawari zakiban Zuman ki indan latsa...
Ta gane abun
da yake nufi sai ta wayance masa ta ce bangane Zuma na ba..
In Zuma kake
so akwai su anty tazo dasu roba nawa kake so...ehee
Kasaitaccen
murmushi ya sakar mata
cike da kaunar ta Ya ce uhmm Rahama idan munje
gidan zan nuna miki inda Zuman take sai kibani...
OK ta furta
tanajin faduwar gaba dan ya ambato mata abun da bataso '' 'cikin dauriya ta ce
wani irin mafarki kakeyi akaina dakace anan muke haduwa...ina sauraron ka...
Naki wayau
naki Rahama nafa gayamiki wal ba ni wal hanani wal keme me...
Yanda ya ja zancen
ba ƙaramin
dariya yabata ba...
Tsare shi da
idanu tayi.
Gira ya Daga
mata ya ce ya ce yes haka nake nufi gwanati ta hana aikin banza...
Tabe baki ta
yi ta ce na ji shi ne harda latsamin Zuma abaki Ko dan ka ga na matsu shi ne za
ka fake da abun da ban san mene ne shi ba da kake so...
Samad yin kasa
da muryan sa yayi. Ya ce kema ai Zuman kika latsamin kika hanani kara latsa
kinga munyi anko kenan...
Dan haka tashi
mu je super market zamuyi wa Karima shopping kinsa mara lafiya saida kulawa...
Da ƙyar ta
tashi Daga zaunen tana kokarin daukar jakar ta''' Ya ce Ah Ah bari nizan daukar
miki Hubby na...
Yana gaba tana
biye da shi abaya....
Ma'aikatan
ganin basu wani dade ba '' cikin hanzari suka nufo su '' Daya.daga cikin su ya
ce shugaba har za ka wuce ne...
Gyada masa kai
yayi. Ya ce eh zan tafi ne in akwai abun da kuke bukata manager ya nemi ni...
Dan waje ne na
shakatawa wajen wasan yara da manya sossai Park din yahadu hade da decoration
dake WAJEN Samad aka. Rubuta '' Komai samad...
Uniforme din
dake jikin ma'aikatan sa sanye suke da rigunan polo fari da Aka rubuta Samad
Park da manyan baki....
Rahama sake da
baki take kallon yanda jama'ar da suka zo shakatawa wasu da matan su' '' wasu
da yan matan su'Wasu da yaran su da dai sauran su...
Duk akayi waje
dasu Saboda zuwan su...
Ganin sun fito
ne Idanun mutane yana kansu suna fadin wannan ai me waje da kansa ne yazo amma
kunata fadin wani me kudi ne yasiye wajen...
Dan ya shakata
da matar sa...
Sossai suka
shagala da firan su' '' duk abun da suke fade Rahama tana Jin su..
Cikin su wata
ta tsurawa Samad idanu kamar zata cinye shi...
Ganin kallon
ya yi yawa ya sa Rahama kama hannun sa da yake kokarin bude motar sa...
Dawo da kallon
ya yi a kan ta Daga mata gira ya yi ya ce wife ya akayi ne Ko mu koma ciki ne
baki gaji ba.
Kada masa kai
ta yi ta ce A'a kawai naga wata mayya tanason ta cinye mun kai adu'a zanmaka
Allah ya kareka da sharrin idanu..
Ganin Rahama
tarike hannun Samad '' suna face din juna ita dashi...
Sossai wajen
suka dauki tabi harda masu daukan hoto da video suka dauke su ba tare da sun
sani ba...
Wacce ta
kurawa Samad idanu ganin Rahama na hararan ta taka san idanu ya sa tasha Jinin
jikin ta...
Tana gama masa
adu'a suka shige motar har suka bar wajen..
Maganar su ake
'' nan da nan aka ringa daura hotunan su kan Facebook '' WhatsApp '' Twitter ''
harda video da suka yi masu ba tare da da sanin su ba suka daura kan tik tok da
sauran su....
Sheik zaune
yana duba Facebook dan daura waazi yaci karo da wannan hoton Rahama da Samad
saide Rahama sanye take da hijab hakan ya sa bacin ran nasa beyi zafi ba....
Daukar wayar
ya yi yakira anty wacce yanzu ne suka isa gidan masarautar.
Tambayar
Rahama yake ta ce basanan sun fita da mijin nata...
Cikin hanzari
ya nemi ta turo masa nombar Rahama..
Anty ta ce
kash ai inaga ba ta da layin kasar nan tun da tazo '' amma bara innemi na mijin
nata tun da suna tare sai yahadaka da ita...
Babu ba ta lokaci
tasamo lambar Samad gun Ahmad ta turawa sheik...
Sheik yana
ganin sakon texte babu ba ta lokaci ya nemi Samad saida wayar takusa tsinkewa
ya Daga ka sancewa yaga suna ya fito da baya Daga bakuwar lamba....
Cike da
girmamawa ya ce Sheik imam bark da warhaka bayan sun gaisa Sheik ya ce haba
Samad ya za ka bari a dauki hoton matar aure ana yadashi a social media ''
wannan ba wayewa ba ce '' kamar kuna kyakwayon halin turawa ne....
Samad dake
tuki parking Daga gefen titi ya yi ya ce sheik nifa ban san a kan wani hoto
kake magana ba..
Ni banda taba
daura hoton Rahama a kan social media ba' nasan illah haka amma kayi hakuri ''
katura mun hoton da kake magana akai ban san an yi ba....
Sossai jikin
Sheik ya yi sanyi ya ce kar ka damu ɗana
dan naga kamar rungume kuke da juna da simple hoto ne ''na kamala ba zance komi
ba...
Ka san yanda
duniya tasan ni kuma tasan ka' Kuskure kadan ake jira afara cece ku ce....
Samad ya ce haka
ne Sheik Imam zan kiyaye Daga haka suka yi sallama...
Mika wa Rahama
wayar ya yi cike da shagwaba ta ce Abby kayi hakuri kaida Mama har yanzu
bankira ku ba' '' bansamu layi bane '' 'amma na ji ance yau za a samo min...
Sheik ya ce UHMM
RAHAMA INDE KINA LAFIYA NI BA DAMUWA TA BA CE SANNAN NA MANCE BAN GAYA MIKI
ZANCEN AURE NA BA...
cike da zare
idanu Rahama ta ce aure kuma Abby..
Eh aure mana
yabata amsa''' amma matar da zan aura din bazawara ce'' Inkin samu layi zan
miki bayani daughta Daga haka ya katse wayar...
Jikin ta ya yi
mugun sanyi sossai Jin batun auren nan.. Maida kallon ta ta yi a kan Samad
ta ce inajin abun da kuke fade kaida Abby uhmm
mutane sai Aslow' Jin karar message acikin wayar sa ya sa ya bude whsap dinsa
ganin hoton da video ba ƙaramin Girgiza shi ya yi ba...
Har yana
nunawa Rahama itama mamaki ta yi ta ce uhmm yaushe muka rungumi juna kai
wallahi wannan sharrin mutane ne.....
Murmushi
takaici ya yi ya ce dadin abun ba kamani suka yi da kwartuwa ba '' 'mata ta ce
dasauki ai....
Murmushi
Rahama ta yi
Ta ce uhmm
kaide Ko..
Ni dai me Ko
karya nayi ne wife..
Girgiza kai ta
yi Alamun a' a
Cigaba da
tukin nasa ya yi babu ba ta lokaci suka iso gida...
Koda ya iso
sun iske Ahmad baya gidan ya tafi neman danwaken jaraba...shida Asiya ya ce tun
da kawar ta ce wlh ita zata je siye bashi ba...
Ahmad sharara
uban gudu yaketa yi cike da tsoro Asiya ke kallon sa ta ce haba Yarima kar ka
jefa mu a rami irin wannan gudun haka...
Ko kallon inda
take beyi ba bare tasa ran ze tanka mata '' ganin abun nasa gaba yake yi duk
inda ya gifta da motar sa sai ya tada kura '' ganin lambar motar ya sa har
jami'an tsaro suka kasa tsaida su suna tsoron su tsaida shi su jawa kansu
Wahala....
Gabadaya Asiya
ta tsorace da lamarin sa babu damar ta yi fada gashi taga babu annuri a fuskar
sa cike yake da takaicin wannan danwaken daze ba ta time din sa wajen siyen
sa...
Koda suka iso
Daga cen nesa ya yi parking din motar inda babu idanun kowa...
Shiru ne
yaratsa acikin motar cikin ba da umarni ya cewa Asiya tabude motar tafita ''
taje neman inda ake saida danwake inta samu tasiyo tazo nan yana jiran ta....
Asiya cikin
tsoron ta yi magana ya huce haushin a kan ta '' tamika masa hannun Alamun
yabata kudi...
Drower gaban
motar ya bude tare da zaro jaka goma kudin kwatano yamika mata ya ce duk yanda
yakama kawai ayi...
Cikin sanyin
jiki tafita tana waige waige cike da tsoron unguwar daya kawo ta '' koda tasamu
inda wasu mata suke zuwa ta yi ta tambayesu...
Taci Sa'a aka
raka ta har gurin saida danwaken
Katuwar Wamer
dake hannun ta saida suka cika mata' ta biya su' '' cike da jin dadin ta yi musu
ciniki suka ce baiwar Allah amma wannan kular taki ta yi kyau sossai kamar ta
zinare..
Murmushi ta yi
ta ce nagode cikin azzama takoma inda tabar shi...
Cike da mamaki
take kallon wajen ganin ba ta ga motar sa ba...
Daidai saitin
inda motar ya tsaya.
Ta tsaya sai
waige waige take babu Ahmad babu labarin sa..
Gashi ba ta zo
da waya ba..
Daura hannun
ta yi a kan ta cikin tsananin fargaba ta ce wannan Ahmad din meyake nufi dani
ne...
Sake sake take
awajen ita kadai atsaye......
*****************************************
Rahama da
Samad kai tsaye dakin Karima suka nufa cike da godiya suke bin Yarima dashi...
Iya Firdausi ta
ce gaskiya nagode bisa kokarin da Mamy ta yi wajen janye ni Daga ɓangaren Fulani...
Yarima cike da
Jin dadin kalaman ta..
Ya ce babu
komai iya Firdausi..
Maida kallon
sa ya yi a kan Karima da ita shidin take kallo ganin ya tsura mata idanu ne ya
sa ya sa ta sauke nata a kasa...
Cike da ladabi
ta ce ya shugaba na nagode da wannan kulawar da kayayyakkin nan daka ba ni Allah
ya saka maka da Alkhairi...
Rahama cike da
tausayawa take kallon Karima ta ce inbabu damuwa zan so ingana dake
Karima.......
Iya Firdausi
najin haka ta ce Ah babu matsala bara in tashi inbaku waje...
Babu ba ta lokaci
tafita dakin tare da nufar sashin Mamy.....
Shiko Samad
kallon Rahama yake ganin yanda ta canza babu wasa a tattare da ita...
Cikin muryan
ta me kama da wacce take cikin takaici ta ce Karima...
Karima dago
kanta ta yi tana kallon Rahama cikin ido kasa jure kallon nata ta yi hakan ya
sa ta yi kasa da Idanun ta
Rahama tashi
tsaye ta yi ta rungume hannayen duka biyun a kirjin ta...
Ta ce Karima
kinada Amsar tambaya ta..
Ina son ki
gayamin meye tsakanin Fulani da Mamy '' da Maman Maryam '' da Maryam '' Abban
marwan '' da Sarki '' 'a karshe ina son ki gayamin ina uban mijina yake kuma
meye ya sa tun da nazo gidan ban ganshi ba....
Maida kallon
ta ta yi a kan Samad da ya yi shiru yana sauraren ta bayajin ze iya dakatar da
ita dan bega wasa a Idanun ta ba....
***********************
Asiya daura hannun akai ta yi tana salati tare
da ajiye Wamer din danwaken akasa....
Jin Horn a
bayan ta hakan ya sa tawaiga taga uban waye a kan ta....
Ganin Motar Ahmad
ne cike da takama ya fito Daga motar ya ce yar rainin hankali daura hannun da
kikayi akai mutuwa akai miki ne..
Bata kula shi
ba ta rinƙa
sauke ajiyar zuciya akai akai dan tagama tsoracewa...
Cikin hanzarin
ta tabude murfin motar tashiga hade da Wamer dake hannun ta....
Babu wanda ya
yi ma wani magana har ya tada motar yana tuki yana kira'a tare da bin karatun
Sudais......
Ita Ko kallon
sa take ganin yanda ya nuna kamar besan da zaman ta a motar ba...
Koda suka isa
masarautar '' yana parking din motar kai tsaye fadar Sarki ya nufa...
Ita Ko Asiya
ta yi cikin gida...
Bakin sa dauke
da Sallama ya shiga fadar Sarki....
Waziri da bayi
masu yiwa Sarki fifita ganin Yarima yashigo be nemi ayi masa iso ba....
Dukan su sun
sa babban magana ce tazo dashi...
Hakan ya sa
dukan su suka watse bisa Al'ada in haka tazo fita suke yi abar Sarki da jikan
sa....
Suna fita
Ahmad yazauna tare da nannade kafafun zuciyar sa na kuna....
Sarki ya ce
Ahmad Allah ya sa ba laifi akai maka ba..
Ko wani ne ya
taba ka...
Ko Ko kanada
wani bukata ne fadi Ko mene ne zan maka inma banda shi zan siya inbaka...
Kai nake
sauraro...
Cikin tsaita
nutsuwar sa ya dawo da kallon sa a kan Sarki cike da yarda da kai da shawaran
da abokan sa suka basa
Ya ce Allah ya
taimaki Sarki aure nakeso...
Sarki fadada
murmushin sa ya yi ya ce wacece wannan yarinyar mai sa'a da zata mallaki wanna
gwarzon na miji
Bakin sa na
rawa ya ce bakowa ba ce illa..........
Masu karatu
wakuke tunani Ahmad ze furta saina ji ra'ayoyin ku...
Ta ku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
LITTAFIN NAN
KUDI NE INKIN GANSHI A WAJEN GROUP DÎNA NA SATA NE
09069080725
7️⃣9️⃣
Bakowa ba ce
illah Asiya..
Sarki ya ce
wacece Asiya yar Gidan wacece agarin kwatanon nan....
Cikin yin kasa da murya ya ce tana cikin bakin
da suka rako matar yaya Samad kawa ce agun matar sa...
Murmushi mai
cike da daddatako Sarki ya yi ya ce MashaAllah Abu ya yi har kun daidai da
yarinyar Ko...
A'a ni basai
mun daidai ta ba '' Kawai de ina son a aura mun ita ta zauna kar kashin iko na..
Dariya sossai
Sarki ya yi ya ce ikon Allah duk ikon da kake yi a gidan nan da wajen gidan nan
be ishe ka ba...
To daman
inkana auren ta dole kayi iko da ita kar ka damu tun da kace a nema maka zance
yakare zanyi magana da Sheik Abdurrazak nasan ya san iyayen ta ba zai gagara
ba..
Cikin yin kasa
da murya ya ce Sarki nifa ba na son auren yadau lokaci a sati daya kacal..
Sarki cike da
izza ya ce Ah Ah haba Yarima Samad Ko kaza ce za ka dauko aika shirya bare ɗan Adam.
Auren Yayan
naka ai daga sama aka dauro shi '' babu yakawo zeyi aure awannan garin '' duba
da natsara Ko yana so Ko baya so Maryam ze aura awancen lokacin...
Kaga Allah ya
yi hikimar sa tun da na masa aure babu izinin sa...
Shi ya sa na
janye zancen Maryam din...
Kaikuma da
kanka kazo da bukatar ka ga ina bukatar shiri sossai '' dan tare zan aurar daku
kaida Marwan harda yar autar ku...
Gaskiya zuwa
nan da wata daya zan gama shirina Daga nan azo asanya ranar aure...
Babu yanda ya
iya cikin tabe baki da ba haka yaso ba ya ce uhmm ni dai baza a hada aure na ɗana kowa ba..
Maganar
gaskiya sonake asan babu wani daurin aure sai nawa...
Maganar Marwan
da Khadija saida kabar nasu bikin zuwa bayan an yi nawa '' ita khadija ta
tsaida mijin aure ne....
Murmushi mai
kayatarwa Sarki ya yi yana kallon Ahmad ya ce kwarai kuwa na dade da bayar da
khadija uwar ta tasani tun da kace haka '' 'naji korafi ya karbu....
Sossai Ahmed
yaji dadin Amincewar da Sarki ya yi hakan ya sa suka karasa fadin abun da yake
so ayi masa sannan yabar Fadar yanajin saukin damuwar sa ta ragu....
Anty tabude
kayayyakin da suka siya Mamy na dubawa daya bayan daya..
Cike da Jin
dadi ta ce amma fa kun iya zabe sossai murmushi anty ta yi ta ce Ahmad ne ya yi
mana zaben kin san ya san kan gari....
Asiya ta ce
aikuwa dai Mamy ya iya zaben kaya kamar mace..
Yayi daidai da
karasowar sa''falon caraf kalaman ta suka fada a kan kunnen sa...
Cike da isa ya
iso falon ya ce aini nafi karfin kiyi misali na da mace...
Mamy cike da
mamaki suke kallon sa ita da Anty da Salma da khadija yanda yake cika yana
basewa...
Murmushi Mamy
ta yi ta ce uhmm Babana maida wukan yabon ka take waika iya zaben kaya...
Cikin takaici ya
ce shi ne zatayi misali na da mace banaso fa kigayamata ta fita idanuna....
Asiya ganin
Mamy awajen ta ce Ayya yi hakuri bankarawa '' Wayar ta ce tafara ring tana
dubawa taga kiran mamar ta ce hakan ya sa ta ce ni zan fita Daga waje ana dan
Amsa waya.....
Ahmad bin ta
da kallo yake har tabar dakin yana Ayyana kardai ace Farruk ne ya lalata masa
shiri dan yaci Alwashin sai ya gyara mata zama duk da bawani abun zeyi da ita
ba Daga baya ya sakar wa Faruk ya aura.....
Cike da zargi
yabi bayan ta...
Mamy ta ce kai
Babana ina za ka je ne kazo ina son ganin ka...
Cak ya tsaya tare
da dawowa cikin dakin ya zauna....
Sallamar bayi
ne hannun su riki riki da kaya wanda ya fito Daga Fada...
Cike da
nutsuwa suka karaso falon tare da sauke kayan...
Daya Daga
cikin su kanta aduke tana fuskantar Mamy ta ce ya shugaba ta.
Wannan kayan
sako ne Daga Fadar Sarki..
Paper dake
hannun ta '' tamika wa Mamy tare da dawowa gefe tazauna...
Mamy bude
sakon ta yi tasoma karantawa kamar haka...
Kyautuka ne
Daga Sarki..
Mama Karama..
Sani
Fulani..
Munce abawa
bakin mu dazasu koma gobe dafatan Allah yakai su kasar su lafiya....
Sossai Mamy ta
ɗara dan farin ciki ta
ce ah basai na bude kayan nan ba..
Da kansu sun
bude abunsu..
Kuma da kuka
kawo sakon nan zan aiko khadija da tukwici ta kawo muku...
Cike da jin
dadin Albishir da Mamy ta musu suka koma bakin aikin su...
Mamy kallon
Ahmad ta yi dake zaune yana latsa wayar sa ta ce ka ga wannan kayan na bakin
nan ne Sarki da su Fulani da Abban Marwan suka bayar a basu..
Anty dake
sauraren ta ita da salma sossai ta ji dadin haka Itako Salma tsabar bakin ciki
kasa zama dakin ta yi hakan ya sa ta ce bara taje tadawo ta zura hijabin ta
tafita...
Anty godiya ta
rinƙayi
sossai tare da musu fatan Alkhairi...
Mamy shiga ta
yi ta fito da nata kyautan ɗana
Samad da kudin da ya bayar a basu...
Cike da Jin
dadi mamy ta ce wannan gatan ta yi yawa..
Mamy ta ce ina
gatan yake wanda kuka mana ya fi namu...
Kunbamu hasken
gidan nan watau Rahama kun gama mana komai wallahi saide mu biku da adu'a...
Sossai anty ta
yaba da hali irin na mutuntaka na Mamy...
Mamy ta ce
kash banji dadi ba akwai yar autar mu tana kasar misra acen suke zaune da mijin
nata ta ce jibi zata zo dan yi mana murna auren Samad ba ta samu zuwa a kan lokaci
ba na so ku hadu...
Anty ta ce
Ayya Allah Sarki karki damu wataran zamu hade ne InshAllah....
Mamy cike da
Jin dadi ta dauko wayar ta ta dannawa yayyen ta maza guda biyun da suke saudiya
kira babu ba ta lokaci suka Daga...
Daga can ɓangaren me suna Auwal ya ce
Habiba yau da kanki kika kirani...
Murmushi mamy
ta yi ta ce afuwan yaya Auwal ka san dai ina neman ka wani lokacin bana samun
ku ne...
Daga can ɓangaren ya ce karki damu
nasan da hakan yakike ya taro ya tashi kiyi hakuri nida Sani a satin nan zamu
zo InshAllah nasan Abban mu yana bukatar ganin mu '' ga dan namu ya yi aure
kinga yakamata muga surukar tamu....
Mamy ta ce eh
wallahi yakamata ku ganta shima Abban namu Nina hanashi zuwa bikin Samad shida
maman mu' to yanzu gida babu kowa Ka san masarautar nan ba zaune kalau ake ba..
Ba na son suzo
suga abun da be musu ba' '' ka san kuma har gobe basu San mijina baya garin ba
'' suna sani akwai matsala...
Auwal ya ce
kai Habiba kina nufin haryanzu Abban besan da zancen ba
Ta ce eh
besaniba...
Kaima dan
Allah karku gayamasa na rokeku kaida Sani...
Karki damu
Habiba ba zai ji ba InshAllah...
Tashi ta yi Daga
inda take zaune ta tabo kusa da anty ta ce ga Yayana Daga Saudiya zaku gaisa...
Mikawa anty
wayar ta yi cike da mutuntawa suka gaisa da Auwal din...
Auwal ya yi masu
godiya sossai a kan halarci da suka yi wajen bawa dansa Samad mata...
Sossai anty ta
ji dadin mutuntaka irin na yan uwan mamy Daga haka suka yi sallama...
Ita Ko Asiya
waya take da mamar ta sun shagala sossai suna hira '' ta ji an wabce wayar Daga
hannun ta da mamakin ta juyo dan ganin wanene ya yi mata wannan rashin
mutunci...
Ganin Ahmad a
kan ta hakan ya sa ta yi tsaki..
Kashe wayar ya
yi gabadaya yadawo da kallon ta a kan ta...
Cike da isa ya
ce nan fa ba gidan ku bane..
Zaki zo kiyi
ta fira da kattai babu aji babu girma..
Wai kina
kallon kanki a madubi kuwa...
Cike da mamaki
take juyawa kalaman sa tahada rai ta ce bangane wai ina kallon kaina a madubi
ba...
Eh mana idan
bakya yi tokiyi ke bakiga yanda matar yaya Samad take bane amma kike kiran
kanki da kawar ta...
Wallahi
tunwuri ki nemi daidai ke dan wannan matar yayar tamu tawuce ajin ki''..
Tafiki kyau ilimi
wayewa tafiki Asali ke intakaita miki babu wanda ze kalli Rahama ya kalleki ya
ce kun hada hanya......
Sossai Asiya
Ranta yabaci cike dajin haushin zagin nata da ya yi ta mika masa hannun ta ce
ba ni waya ta..
Idan ban baki
ba akwai abun da zakiyi ne..
Girgiza kai ta
yi ta ce A'a kawai kabani wayata banson fitina...
Kin ba ta wayar
ya yi hakan ya sa yawuce yabar ta atsaye...
Cike da mamaki
take kallon sa harya ba ce mata da gani..
Cikin hanzarin
ta tawuce masaukin su tare da fadawa kan gadon nasu...
Kuka take
sossai mai tsuma rai tana da na sanin zuwa kwatano...
Tana kukan
tana tuna Adamu da basu gama chat ba ta amsa kiran mamar ta....
Tashi ta yi taje
gaban madubi tana ta kallon kanta Daga kasa har sama ta ce yabon kai jahilci
dasai ince banga wani makusa afuska ta da jikina ba..
Cigaba da
kallon madubi take cike da takaicin kanta ta ce kila ma gaskiya yafada din
banida kyau......
Tana kallon
madubin hawaye shar a Idanun ta sossai suka canza launi zuwa ja.......
******, *************
Karima cikin
karfin hali take kallon Rahama ta ce matar shugaba na..
Kin cancanci
in gayamiki komai koda kuwa shugaban yahana dole in sanar miki da abun da
nasani...
Amma ina rokon
ki Alfarma kibari zuwa nan da gobe yanzu haka Da ƙyar nake iya magana....
Rahama dake
mata kallon tausayi ta ce karki damu Karima InshAllah zan saurare ki zuwa goben
tashi ta yi tsaye ta ce mu zamu wuce '' shima Samad tashi ya yi yarike hannun
Rahama ya ce Karima mun tafi Allah yabaki lafiya...
Sossai ta yi farin
cikin ganin yanda Rahama take manne wa Samad tasan karshen zaluncine yazo
karshe....
. Kai tsaye
sashin Mamy suka nufa...
Koda suka je
iske Anty suka yi tana shirin tafiya masaukin su...
Rahama cike da
shagwaaba ta ce Ah anty ina zakije ne kizo muci danwake nasan ankawo shi
nan....
Anty sake da
baki take kallon Rahama ta ce danwake kuma..
Ko shi ne
nagani a babban Wamer din da Asiya ta shigo dashi....
Mamy dake
fitowa Daga dakin ta hannun ta dauke da Wamer din ta ce ga danwaken nan Rahama
kwantar da hankalin....
Kan danwaken
nan baba na kamar zeyi kuka dazeja Asiya suje siyen sa...
Sossai Samad
yadara ya ce Amma Ahmad dan rainin hankali ne watau ba zaije siyen danwake
shikadai ba shi ne ya ja Asiya..
Mamy ta ce to
ka san dan gayu ne ya za ai agan shi riike da Wamer zuwa siyen danwake daka
gayamin da da kaina zan mata taci iya cin ta....
Rahama banda dariya
ba abun da take cike da Jin kunya ta ce Ah mamy gobe ma zanci InshAllah da kaina
zanyi dandai ina tunanin kafun ayi danwaken zan jigata shi ya sa nace ina son na
siyarwan....
Mamy ta ce
babu komai yanzu de zauna kici....
Kallon Anty ta
yi da take shirin fita ta ce Maman Rahama dawo kuci tare...
Anty ta ce Ah
Ah ankai mana Abinci taci kayan ta lafiya kasai ta yi tafi ce...
Yarima Samad
kallon Rahama yake yanda take cin danwake tanaci ba ta fuska...
Kallon ta yake
da mamaki ya ce yadai Ko akaro yaji ne...
Cike da ba ta rai
ta ce ni dai danwaken na ya isheni haka kada ya sani amai..
Samad danne
dariyar ya yi ya ce Mamy kinajin abun da take fade Ko...
Murmushi Mamy
ta yi ta ce inajin ta..kyaleta tahuta eheee banson takura..
Kallon Rahama
ta yi cike da so da kauna ta ce gayamin abun da kike so zansa Hassana ta dafa
miki....
Fitowar
hassana Daga kitchen waya hannun ta cike da mamaki take karanta sakon whsap din
ta...
Mahaifin ta ne
ya yi mata sako hakan tadawo hakanan duk da besan me taje yi a kwatanon ba....
Ya mata miji
har ansa rana auren nata nan da wata daya....
Sossai zufa ya
keto mata
Mamy da Samad
da Rahama kallon ta suke suka hada baki wajen fadin lafiya kuwa....
Muryan ta na
rawa ta ce mahaifina na ne ya ce indawo gida Sannan ya sama mun mijin aure har
ansa rana...
Mamy cike da
Jin dadi ta ce meye abun ba ta rai ke fa ba yarinya ba ce kiyi adua Allah ya sa
shi ne mafi Alkhairi...
Kasa magana
Hassana ta yi hakan ya sa tazauna shargab akasa tana maida numfashi...
Rahama barin
danwaken ta yi ita da Mamy suke nufi inda take zaune cike da jinjina Al'amarin
ace bazawara ce za a fitar mata da miji ai an yi son kai...
Mamy ta ce
karki damu kila ya hango Alkhairi ne shi ya sa yake son hada wannan auren.....
Salma tana
fita masarautar kai tsaye wani babban pharmacie ta nufa...
Ta ce su ba ta
maganin bera....
Ma'aikaciyar ta
ce nan babu maganin bera sai dai kije kasuwa...
Salma cike da sake
sake tana ciza labban ta '' ta ce uhmm to kuban poison
Ta ku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
LITTAFIN NAN
KUDI NE INKIN GANSHI A WAJEN GROUP DÎNA NA SATA NE
INKINA BUKATA
GA NOMBA
09069080725
8️⃣0️⃣
Tokuban poison
'' ma'aikaciyar ta ce me zakiyi da poison ne hajiya ya tsurawa Salma idanu...
Salma cikin
kasa da murya ta ce beraye ne suka takura mun babu daman in kwanta sai suzo
suyi ta cizo na dan Allah ki taimaka ki siyar mun very important nake bukata...
Jinjina kai
Ma'aikaciyar ta yi tare da danna computer dake gaban ta '' ta ce..hajiya kudin
ki jaka daya...
Salma ta ce
babu matsala zanbiya..
Ma'aikaciyar
nuna mata wajen da ake biyan kudin tayi' 'itako Salma cikin Rawar jiki taje
tabiya ta amshi poison din hannun ta''' na rawa cike da murna......babu ba ta lokaci
ta yi hanyar gidan Masarautar...
Mai gadi da securite
dake kofar gidan kallon ta suke yanda taketa kif kif da idanu Alamun rashin
gaskiya...
Securite stop ya
ce mata hakan ya sa ta wai go tana kallon sa...
Tsura mata
idanu ya yi '' yaga ta hada rai ta ce kakosan koni wacece kuwa..
Securite ya ce
ban san koke wacece ba''amma kabar bakuwa ce' yi hakuri kina iya shiga na dauka
bakuwar fuska ce...
Ajiyar zuciya
tasauke cike da murnan Allah ya taimake ta be caje ta ba....
Cikin hanzarinta
kai tsaye sashin Mamy ta nufa ta iske Rahama har tabar dakin...
Kallon Wamer
din danwaken da Asiya ta kawo take cike da rawar murya take kallon Mamy ta ce wai
Anty Rahama ta shigo nan ne...
Mamy ta ce eh
sunshigo mana ita da Samad yanzunnan suka wuce sashin nasu...
Cikin kunan
rai ta ce Ayya amma takoci danwaken nata kuwa...
Mamy ta ce
taci gashi nan tabar shi inkinaso ki tafi dashi...
Salma ta ce Ah
ah nakoshi nadai tambaya ne zankoma masaukin namu naga magrib ta karato...
Hartakai kofar
fita ta ji muryan Mamy na fadin Salma Inkin je ki turo mun Asiya '' da an yi Sallah
tazo takai Abinci sashin Samad...
Salma cike da
Jin dadi ta ce to meze hana ni inkai mata Mamy ai duk daya ne...
Mamy ta ce haka
ne '' to kije in an yi Sallah isha'i kinzo ki dauka '' dakin je kiwa securite
sashin nasa magana kice Nina turaki za su barki ki wuce..
Salma ta ce
babu Matsala Mamy saina dawo Daga haka ta fice tabar dakin...
Koda ta isa
dakin iske Anty ta yi ita da Asiya suna kokarin tada Sallah hakan ya sa itama
tafada bandaki domin yin Alwala..
Koda ta fito
Daga bandakin iske anty da Asiya harsun idar da Sallah..
Wayar Anty ne
ke ruri cikin hanzari ta duba taga bakuwar lamba ce..
Daga wayar ta
yi tare da yin shiru Daga can ɓangaren
ya ce anty ina wuni dafatan kina lafiya
Al'amin mijin
Salma ne...
Anty fadada
murmushin ta ta yi ta ce ah surukina sai yau za ka neme mu lallai m'a...
Daga can ɓangaren ya ce wlh anty
banzaune ne '' aiki nasamu saida naga komai ya daidai ta shi ne nasamu nutsuwa
dan Allah kihadani da Salma Ko kiban number ta inbakya tare....
Anty maida
kallon ga Salma dake sallah ta yi ta ce muna tare sai dai Sallah take yi ''
'Al'amin ya ce Tom anty zan sake kira ganin Salma ta sallame ya sa ta fadin
tsaya kamar ta idar da sallah...
Daga can ɓangaren dadi yaji sossai
hakan ya sa ya ce to anty kibata wayar....
Salma ganin.
Anty tamika mata wayar ta karba dan duk firan da suke tana Jin su....
Tashi kusa
dasu anty ta yi takoma cikin daki....
Cikin Isa da rashin
kunya ta ce Al'amin kenan wai meye dalili kira dan a ba ka ni....
Daga can ɓangaren murmushi ya yi ya
ce babu laifi miji dan ya nemi matar sa...
Salma kiyi
hakuri mu dawo da rayuwar mu irin ta da kafun muyi aure...
Salma ina son
ki a yanzu sona hakika nayi kuskure ɗana
dauki auren ki amatsayin wulakancin bayan na manta ke yar wacece kuma na mance
irin kawaicin da mahaifin ki ya nuna mun..
Yatsine fuska
Salma ta yi tabuga uban tsaki ta ce Al'amin kayi sake dan zaki ya girma yanzu
babu ni babu kai wallahi ka sake ni ba zan iya zaman aure da kai ba...
Kana matsiyaci
ana batun daula wake maganar gidan bukka...
Wallahi ni sai
dan Attajiri Ko attajirin Ko Jinin Sarauta kar kai tunanin zan zauna gidan masu
saida waina a kan titi ka makaro '' wallahi Ko Ada danake kula ka kuruciya ne
da dangin hauka ya sa na mance ni matar manyan mutane ce ba irin ka me tsaron
shago ba...
Sossai Al'amin
ya nutsu yana sauraren ta tare da juya kalaman ta yanajin kuna acikin zuciyar
sa...
Danne fushin
sa ya yi ya ce Salma ba zan iya sakin ki ba..
Yanzu haka na
kama muna gida mekyau plat babu kowa ciki dagani saike sai yayan da zamu haifa
har Allah ya horemun in yi gidan kaina.....
Sossai Ranta
ya ba ce ta ce ni Salma Abdurrazak Nice zan zauna gidan haya kam buhu lallai
kanka ya kwance Al'amin
Maza ka nemo
shi in saita maka shi.....
Nusarin namiji
kawai Alfarma daya zan maka '' tsinannen cikin ka dake jikina nakeson ɗana dawo ka kaini acire mun
shi dan wallahi ba zan haifi dan Masu saida waina ba.....
Al'amin cikin
takaici ya ce aikuwa tun da ba shege bane saikin haifi dan masu wainar..
Zankai kararki
wajen mahaifin ki danshi ba mutumin banza bane...
Salma Jin
zeyiwa sheik magana ya sa ta fadin kaima ba ka san wasa ba...
Ai gobe zan
dawo kabari inna dawo mun karasa ko
Cikin takaici
Al'amin ya katse wayar..
Sai safa da marwa
yake ta yi cikin dakin...
Mahaifiyar sa
me waina ce ta shigo bakin ta dauke da Sallama ta ce Al'amin matar nan taka ''
Nina rasa wani irin aure ne wannan duka kwanan ta uku agidan ka...
.
Kuma ace
haryanzu ba ta koma ba...
Al'amin cike
da takaicin Salma yake kallon mamarsa ya ce Inna Salma Albasa ce batayi halin
ruwa ba...
Duba kigani fa
ya za ai ta ce wai zata barar da cikin dake jikin ta '' kasa gayawa mamar sa abun
da Salma din tafada ya yi dan kar abun ya yi tsauri...
Mamar Al'amin
cike da mamaki ta ce ciki gare ta kuma takeson ta zubar dan uban ta mara
tarbiyya astagafirullah na mance iyayen ta mutanen Arziki ne dasai ince Daga
gida tadauko mugun hali...
Al'amin dake
kallon uwar tasa yana tabe baki ya ce ai Daga gidan ta dauko mana a nono tasha
uwar ta wlh ba yar arziki ba ce...
Maman Al'amin
cike da mamaki take kallon dan nata ta ce Ah Ah Al'amin karmuyi haka da kai
laifin wani baya shafar wani dan yarinya ta yi ma rashin Arziki kar ka hada da
uwar ta nasan Ayshatu ban san ta da mugun hali ba...
Kaima harda naka
laifin Ko gun auren yarinyar nan wani rashin mutunci ne ba ka shuka ba har
daurin auren Da ƙyar ka tafi aka ba ka yarinya kayi mata diban Albarka dan dai
uban ta sarkin hakuri baya nuna fushin a kan abu da wanine da kaine zakayi
jinyar ta.....
Kila wannan ta
duba shi ya sa take maka haka..
Takarashe
zancen tana kwance kudin wainar dake daure jikin Zanin jikin ta dan kirgawa....
Al'amin cike
da takaici yake kallon yanda take kirga kudin ya ce ni dai Daga yau banson ki
kara saida waina..
Dago kai ta yi
tana kallon sa ta ce Yau na ji iskanci inace da kudin wainar kabiya sa dakin
auren ka...
Oho dai ni dai
na gayamiki banaso wlh haba kina jamin zagi agari inna yakamata ki daina fa
ehee yana huci sama sama...
Sakaka da baki
take kallon sa ta ce to inbada abun ka da iskancin naka daya motsa wani sana'ar
zanyi ne ka ga dai mahaifin naku beda karfi yanzu da wannan sana'ar muka
dogara....
Ku barshi nace
Inna zandau nauyin komai agidan nan Daga yau Daga cinku har sha..
Duka abun da
kuke bukata ku sanar mun...
Inna dariya ta
yi ta ce ikon Allah Alhmdulilah ɗana
yasoma hankali Allah ya sa dagaske kake inhar haka ne nima wlh zan dena sai
innemi sana'ar gida Ko sare sare ne ina iringa taba kasuwanci...
Al'amin cike
da Jin dadin zehuta da gorin Salma yaciro bandir din kudi dubu dari ya mikawa
inna cike da isa ya ce wannan gashi kija jari kuma kiyi cefane duk abun da babu
agidan nan ki siye mugani kafun su kare zankaro miki wasu...
Cikin Jin dadi
ta girka kudi hade dayin guda sossai baki na rawa ta ce Alhmdulilah Al'amin
Allah ya sa kafi haka..
Ameen ya Amsa tare
da barin ta a dakin tana murnan samun da tayi....
Ita Ko Salma
suna gama wayar ajiye wayar gefe ta yi tafara tunanin yanda zata kai karshen
Rahama
Wata muguwar
Tsanarta takeji A'cikin Ranta..
Tun suna yara
kullum ita ce Asama duk abun da tasa agaba saide ya je kasa '' 'cikin jin
haushin ta take Ayyana yanda za ai jana'izzar Rahama a masarautar..
Kuma InshAllah
Nice zan maye gurbin ta awajen Samad inma ban aure shi ba...
To kowa yara
sa Amma tabbas Rahama barin duniyar zakiyi kin isa ki kwace komai ke kadai
waike ta Allah zamu gani ne...
Tashi Daga
kwance ta yi tare da nufar falon ta iske Asiya tafita Faruk ya aika a kira
ta....
Ganin Anty
kadaice zaune cike da murmushin dole ta ce Anty ga wayar taki mun gaisa da shi ya
ce yana gaishe da kowa da kowa..
Sossai anty ta
ji dadin hakan ta ce yauwa koke fa Salma ina son ki nutsu ki kama mijin naki
sossai wallahi yanzu maza wuya suke...
Kinmaci sa'a
ke kin san Al'amin kafun aure '' nida wlh ina kuka ina fadin ba na son auren da
za ai mun mahaifana suka yi ta rarrashina indau kaddara InshAllah ba zanyi ɗana sani ba...
Yanzu fa duba
kigani zamana da baban ki sai Sam Barka wallahi daidai da. Rana.daya be taba
yimun abu da. Gangan ba dan raina yabaci ba '' duk da Adam agizi ne....
Nima kuma bêta
kamani da nayi masa laifi ba..
Ina kikaye wa
duk da a lokacin bawai son shi nake ba...
Amma Daga baya
fa uhmm Kullum adua nakewa iyayena dan sun mun zabi nagari dan haka ina son ki
rike irin nawa Salma...
Ƙaramin
misali duba fa yayar ki Rahama aure aka daura mata batasan mijin ba shima besan
matar ba kuma suka rungumi kaddara...
Dan Allah
Salma ki nutsu ina son kizama wayayya InshAllah ba zakiyi da na sani ba inkika
dauki shawara ta ba....
Salma jikin
nata ya yi mugun sanyi kamar wacce tadau nasihan Anty amma azuciyar sai fadi
take uhmm ai baku isa ba Daga ke har Rahama zaku gane....
Afili cikin
sanyin murya ta ce Anty nagode da shwarar ki....
INSHALLAH
NADAUKA...
Asiya samun
wuri suka yi ita da Faruk suna fira cikin nishadi ''...
Cike da Jin
dadi ta ce ka ga Daga gobe shi ke nan zan bar kasar taku '' sai kuma mun dawo
suna in Allah ya sa ta haihu...
Faruk dake
Murmushi ya ce kina nufin cike gare ta ne Rahama...
A'a ba haka
nake nufi ba wai in Allah yakawo Ko '' dole inzo mata suna...
Kamar ita
Rahama na ji Samad na. Fadin nan da wata daya za su tafi kano...
Faruk ya ce
kwarai kuwa kanon za su je '' kamar akwai abun da yake nema a kanon har yanzu
Burin nasa be cika ba dole yakoma....
Uhmm Allah
yakaimu gwamma inringa ganin kawata wlh banson ina nesa da ita sai dole...
Wai in
tambayeka
Faruk ya ce
inajin ki fadi......
Dan Allah
gayamin gaskiya kar ka ga dan gaban idanuna ne...
Uhmm inajin ki
fadi mana....
Wai dan Allah
Faruk da. Gaske ni mummuna ce Ko kyakkyawa ba na son ka boye mun dan girman
Allah....
Dariya mai
sauti Faruk ya yi ya ce inhar mafarki kike TOKI FARKA
Babu wanda ze
kalleki ya kushe ki wallahi saide hassada..
Son kowa kike
kin wanda ya rasa..
Asiya ke
kyakkyawa ce ajin farko banson in cika ki da surutu ɗana bude miki file din kyaun surar da Allah ya
yi miki...
Wallahi kinada
kyau iya kyau gaki fara ga tsini hanci mai daukar hankali...
Asiya ke ta
musamman ce..
Gayamin waya
ce miki ba ki da kyau...
Cike da Jin
dadin kalaman sa ta ce uhmm babu wanda ya ce haka kawai na tambaya ne dan insan
yanda nake in daina Rawar kai...
Faruk cike da
yarda da kai ya ce Asiya ina son magana dake serios..
Inajin Faruk
din Samad...
Uhmm ba Faruk
din Asiya ba...
Taya kazama na
Asiya rufamin Asiri...
Ni dai inajin
ka...
Asiya ina son
ingaya miki kalmar da ban taɓa.
Furtawa wata ya mace ba
Asiya ina son
ki '' ina son ki ina sonnnnn kaiiii ya ja kalmar da wani irin voice me kashe
garkuwan jikin wanda ke sauraron sa....
Asiya dago kai
ta yi Idanun ta cike da hawaye ta ce Faruk kana sona kace uhmm mikewa tsaye
tayi...
Faruk shima
tashi ya yi ya ce haba Asiya ina zaki je muna magana..
Kasa Tsayuwa
ta yi ta ce Faruk ka makara kayi hakuri na yi wa Adamu AlKawarin zan aure shi
kuma har nayi shawara da Rahama..
Bankika ba
Faruk ka kai duk inda ake tunani kai gwarzon namiji ne tun farko kayi nauyin
baki...
Gashi Adamu
yazo da Gadan Gadan ba zan ki shi ba...
Cikin hanzarin
ta tabar wajen nasa tana sheshekar kuka...
Shiko Faruk
Mutuwar tsaye ya yi yakoma kamar wani matacce '' sossai jikin sa yadau
rawa.....
Kuka yake yana
fadin Asiya karkimun haka...
Yayi daidai da
fitowar Samad Daga Sashin nasa yana sauri zeje sallah insha'i....
Cike da mamaki
sukaci karo shida Faruk dake kuka...
Samad ya ce............
Ta ku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
LITTAFIN NAN
KUDI NE INKIN GANSHI A WAJEN GROUP DÎNA NA SATA NE
09069080725
Page biyu ne
nan na hada zaku ga ya yi tsawo '' na safe ɗana
ɗare ne..
Nagode masu
mun uzuri..
Love you All
my Fans...
Jinjina gareku
yan kungiya ta Jarumai writ associat..
8️⃣1️⃣ ___8️⃣2️⃣
SAMAD ya ce
kai lafiya kake kuka meya faru ne '' fuskar dauke da damuwa....
Faruk cikin
saita nutsuwar sa ya ce Ah babu komai mu je muyi sallah in mun fito zan maka
bayani.....
Kai tsaye
masallacin suka nufa...
Ita Ko Asiya
zama kusa da Anty ta yi tana ba ta labari Anty ta ce da bakiyi saurin dakatar
da shi ba....
Matar mutum
kabarin shima wanda kike takama a kan sa ba lallai bane inshi ne zaki aura ba.
Uhmmm haka ne
Anty banson ya sa ran zan aure shi inzo ban aure shi ba ya yi tunanin naci
Amanar shi...
Adamun danace
masa shi zan aura '' shima Adamun haryanzu ban bashi baki ba..
A tsakiya nake
Anty..
Cike da Jin
dadi anty ta yaba hikima irin ta Asiya ta ce kai Amma Asiya kina wayau da
hikima yanda ki ka san babba haka kike abun ki kina burgeni wallahi..
Sossai Asiya
ta ɗara ta ce uhmm
aidole anty na namiji kar ka nuna masa wai Daga shi babu wani kuma kar ka nuna
masa kana mugun son sa nan ze samu damar juyaka yanda yake so...
Sossai Anty ta
ɗara cike da Jin dadin
kalaman Asiya ''
tadauko Alkur'an zata karanta kenan Idanun ta
ya sauka a kan Salma dake shirin fita
Asiya ta ce
Salma ina zuwa ne babu magana...
Cikin takaici ta
ce dole inzan fita saina sanar miki ne '' zanje sashin Mamy ne abinci zankai
sashin Rahama..
Asiya ta ce Ah
kice zaki je gun yayar ki Allah yakai ki lafiya saikin dawo...
Anty dake
kallon Salma cikin yin kasa murya ta ce amma fa karki dade idan kinje..
Salma ta ce Ah
Ah inazuwa ba zan zauna ba Daga haka ta fice Daga dakin...
'' Yarima
Samad tare da Faruk suka fito Daga masallacin inda suka samu gefe daya suka
zauna...
Cike da
nutsuwa Faruk keyiwa Samad bayanin son da yakewa Asiya kuma ga Amsar data
bashi...
Samad cike da
jinjina Al'amarin ya ce kar ka damu abokina yanda kamin bayani ni naga son ka
A'cikin idon Asiya kawai tana ja maka aji ne irin nasu na mata...
InshAllah da
kaina zan mata magana '' zanji ta bakin nata'' kaidai sha kurumin ka zamu nema
maka auren Asiya InshAllah....
Faruk cike da
Jin dadi ya ce gaskiya na ji dadin wannan maganar taka Allah ya sa rabo na ce..
Samad ya ce
Ameen kawai mu nemi Zabin Allah...
Tashi mu je sashin
Mamy danni yau ba zan dade banshiga Daga ciki ba..
Faruk ya ce
Tabe Tabe za a je sana'ar ne...
Yarima hade
rai ya yi ya ce uhmm aina ga tabe taben kakeson yi yarinya tana ja maka Aji dan
iska katsaya a kan hanya kamar ƙaramin yaro zakai mana kuka da na sani nabar
ka saika kukan indau video wanda zansawa suna Tabe Taben iskancin da kuke
kirana kaida Aminu....
. Sossai Faruk
ya ɗara ya ce na ji koma
meye nawa dasauki kaida kake mafarki kana kuka kana ihu kana fadin karki tafi
kibarni ni ban ce maka ƙaramin yaro ba '' sai kaine za ka fada mun haka...
Kasaitaccen
murmushi Samad ya yi ya ce uhmm ai wannan mafarkin danake yi ka san ta bude
Idanun nata a karshe kuwa...
Faruk ya ce Au
haba dagaske..
Wallahi
dagaske nake maka kuma fuskar mata ta ce ta bayyana...
Cike da mamaki
Faruk ya ce ni dai tun lokacin nan na dade ina zargin kamar Rahama ce wannan
zanen nasan ba za ka fahimce mu ba..
Shi ya sa
mukayi shiru..
Alhmdulilah tun
da ka gano mafarkin ka saura Abban mu da Saratu...
Samad ya ce
uhmm sune kadai yanzu agabana Amma Allah zeyi jagora...
Faruk kallon
Agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa ya yi ya ce Ah ba zan shiga ba akwai
inda zanje saina biya gidan su Aminu...
OK.babu damuwa
cewar Samad sallama suka yi Daga haka Faruk yafice shikuwa Samad kai tsaye
sashin Mamy ya nufa...
Wayar sa ce
tasoma ring yana dubawa yaga number wannan matar daya taimakawa a kotu....
Kukan ta ya sashi
fadin subuhannalah bayan ya Daga wayar....
Cike da mamaki
ya ce lafiya kuwa mêke Faruwa...
Daga can ɓangaren ta ce yanzu haka
nagudu nabar gidan mu '' zan tafi kauye farautar rayuwa ta ake yi kuma Daga
cikin masarautar ku ne..
Ansamu labarin
kamar zan bayyana maka inda Saratu take..
Ita kanta
Saratu labari ya je mata a kan zan tona mata Asiri...
Yanzu haka
tana shirin barin kasar akace...
Ko ta jirgi Ko
ta mota..
Samad cikin
tashin hankali ya ce wani gari take ne..
Matar ta ce
kano sossai yaji zancen nata kamar saukan aradu..
Yanzu ya
tabbatar lallai ita ce wannan matar dayagani a super market....
Karki damu
yanzu kisan yanda zakiyi ki boye kanki ita din kibar ta tagudu '' ni Samad inna
tashi kamata wallahi a sati daya yamin kadan kawai wuyan ban san kaina Gadan
Gadan bane a neman ta...
Kibar ta duk
inda zata je a fadin duniyar nan zan iya sawa a kamo min ita tahanyar yada
hotunan ta kuma kin san kamar ni innace ina son abu anamun shi saide in mutuwa
ta yi shi ne kadai ze raba ta dani...
Sossai Matar
da yarda da zancen Samad ta ce Allah ya taimakeka yabaka Sa'a AMEEEN ya furta
Daga hakan suka yi sallama.......
Maida wayar nasa
ya yi a Aljihun sa kai tsaye yawuce yiwa Mamy sallama tare da kiran wata baiwa
cikin bayin sa..data biyo ta daukar musu abinci zuwa sashin nasa...
Cike da naam
take bin shugaban ta abaya...
Bakin sa dauke
da sallama ya shiga ya iske Mamy na. Zuba abinci cikin Wamer tashirya komai '' Kokarin
mikawa Salma take yi Samad ya kunno kai cikin hanzarin sa ya ce Mamy zanshige
barci nakeji na tara gajiya...
Abincin namu
tare nake da lantana abata abinci..
Salma cikin
takaici ta ce ni zan kai muku basai taje ba...
Samad kallon
ta yake ya ce ok to saita tayaki rikewa Ko...
Cikin. Jin
haushin haka ta ce babu matsala Muje...
Kai tsaye gaba
ya yi suna biye da shi abaya '' nan da nan securite suka buda musu hanya ganin
shugaba na gaba....
Koda suka yi
isa Samad nuna wa lanta dinner table ya yi ta jera abinci cike da nutsuwa har na
hannun Salma saida ta karba ta gyara komai tsaf..
Kan ta aduke ta
ce ya shugaba na nagama zankoma...
Gyada mata kai
ya yi hakan ya sa ta fice babu ba ta lokaci.....
Ita Ko Salma
tsaye ta yi tana kallon yanda ya zauna gindin abinci yaki tashi...
Sai chat yake
a wayar sa yana kallon ta.
Ta ka san
idanu tabe baki yake ya ce uhmm ban san meyasa wannan kanwar tamu Sam ba ta burgeni
ba...
Sake sake yake
ganin ta yi kikau a tsaye a sanyaye ya dago kai yana kallon ta..
Cikin voice
din sa mai daukar hankalin ta... Ya ce kina son ganin Rahama ne..??
Kada masa kai
ta yi ta ce uhmm ina son ganin ta mana ka san gobe zan wuce Ko...
Murmushi ya yi
mai nuna zallan kyawun sa ya ce ok bismillah Amma karki dade dan dawuri zan
kwanta...
Cike da
hanzarin ta tashige ciki iske Rahama ta yi da khadija zaune Rahama tana koya
mata karatun Alkur'an sossai khadija take ganewa cike da Jin dadi ta ce Anty
Rahama na iya nan Ko..
Gyada mata kai
ta yi ta ce eh kin iya saura hadda...
.
Shigowar Salma
ya sa suka katse karatun nasu '' 'cike da fara' a Rahama ta ce kai ƙanwata
kece adaren nan...
Uhmm Nice
abinci nazo da shi shi ya sa...
Zoki zauna mu
taba karatu cewar Rahama...
Tabe baki
Salma ta yi ta ce Ah ah mijin naki na ji yana fadin za a rufe sashin naku kinga
zama be kamani ba
Rahama ta ce
Ayya Amjad kenan shidai.becika son ana yawan zuwa nan sashin ba..
Barin wani
tunani ta yi taje tadauko wannan milyoyin da Samad yadaura a kan lefen nata...
Kama hannun
Salma ta yi ta ce wannan kudin gashi kiba Anty In kunje cen zata bawa Abby..
Wannan kudin
kowa na ba acikin yan gidan namu harda Asiya za a cire mata nata...
Khadija ta ce
gaskiya Anty Rahama kinyi kokari toke ina. Naki..
Kallon khadija
ta yi ta ce Ah ah ni bana bukata mezan dasu..
Nasan kila
wasu Daga cikin su suna da bukatan hakan.. Yan uwana ne banajin shayin basu
koda kuwa suna da shi ina son surike amatsayin kyauta Daga gareni...
Khadija cikin
fara'a take kallon Salma dake murmushin dole ta ce kai amma Salma kunji dadi ni
ina yaya Samad Ko yaya Ahmad suka taba ba ni kudi uhmm ai saide su siye abu subani
ba kudin ba...
Rahama
murmushin ta yi ta ce my khady mu ma agidan iyayen mu bama rike kudi to me
zakayi dasu bayan komai kace ana maka...
Tabe baki
khadija ta yi ta ce haka ne..
Salma dake
rike da kudin a hannun ta cikin gajiyawa ta ce uhmm nizan koma m'a sauki saide
mun hadu....
Rahama tashi
ta yi dan take mata baya....
Salma ta ce Ah
Ah kiyi zaman ki nagode antina...
Murmushi
Rahama ta yi ta ce kin tabbatar..
Salma ta ce eh
wlh babu komai..
Cike da Jin
dadi Rahama takoma ciki dan cigaba da karatun nasu....
Koda Salma ta
fito iske Samad harya tashi bayanan wajen hakan ya sa ta '' taho a hankali tana
kokarin bude Wamer din abinci dan yanzu sotake Daga Rahama har Samad din su
mutu......
Cikin hanzarin
ta tabude wamer din '' tana kokarin fiddo poison din '' ta tsinkayo muryan
Samad dake karasowa falon sanye cikin kayan barci...
. Ah Ah Salma
daman baki ci Abinci bane...
Cikin Rawar
baki da tsoro daya kamata ta ce uhmm ban koshi bane...
Juya kalaman
ta yake yana nazarin ta uhmm Salmatitinaaa ya ja sunan da wani irin husk
voice..
Dararan Idanun
sa ya sauke a kan ta cike da iya takun sa ya ce to bara in zuba miki kin san ke
kanwar mu ce....
Kokarin dauko
plate yake sai ga Rahama da khadija sun fito cike da mamaki suke kallon Salma ashe
ba ta wuce ba...
Rahama cikin
sakin Fuska ta ce my kanwaty kina nan keda yayan ki...
Murmushi Samad
ya yi ya ce eh muna nan nida Salmatiti na ya kika gan mu...
Murmushi
Rahama ta yi ta ce naganku normal Amjad...
Dauko wayar ya
yi ya ce yawwa Salmatitina zo nan mu ɗau
hoto mana..
Keda khadija..
Cikin hanzari
khadija ta isa kusa da shi Salma cikin sanyin jiki taje tana tunanin anya
wannan mutumin be gano ta ba...
Hotuna yadauke
su shida khadija da Salma yana tsakiyar su ya dafa su..
Kasaitaccen
murmushi ya yi tare da mikawa Rahama wayar ta dauke su...
Babu musu
cikin Jin dadi ta dauke su hotunan ba ƙaramin kyau suka yi ba...
Samad ya ce
yawwa tun da nayi daku kuban waje nida Amaryata mu dauka...
Khadija da
Salma gefe daya suka koma suna kallon yanda yake ta daukar su zafafan hotuna
masu zafi Ko wanne yana manne da ita....
Akarshe ya ce
to duk suzo ayi tare harda Rahama..
Hoto me kyau
yadauke su...
Murmushi ya yi
ya ce Salmatitinaaa yawwa zomuje in rakaki har wajen fita banson securite suna
miki wani kallo zan gaya musu ke din ta daban ce...
Sossai Rahama
ta ji dadin yanda yake kula da kanwar ta.....
Suna fita Daga
dakin '' ya ce kash na mance baki ci abinci ba...
Salma ta ce Ah
Ah abarshi akwai tsaura a dakin namu zanci...
OK to ya furta
yana kallon cikin ido cike da iya taku ya ce Salma dan ba ni maganin dake
hannun ki mana kin san na dade ina neman irin sa bansamu....
Wani magani
kenan tafurta tana zazzare idanu....
Gashi nan mana
tare da saka hannun sa cikin nata sossai taushin hannun sa ya saukar mata da
kasala hakan ya sa ta saki roban poison din akasa ba tare da ta Ankara ba...
Durkushewa ya
yi yadauka ya Daga robar sama yana duddubawa da kyau kada kai ya yi yana
jinjina Al'amarin...
Salma kallon
sa take bataga ya canza yanayin sa ba...
Cikin sassaita
murya ya ce aro nayi gobe inzaki wuce zan baki abun ki...
KADA kai ta yi
cike da tsoro da Fargaba da kuma Jin kunya...
Kai tsaye
barin sashin Nasu tayi....
Shima ciki yakoma
bayan sun gama cin abinci khadija ta ce Anty Rahama mubar karatun nan saida
Asuba barci nakeji tashi ta yi tabar Samad da Amaryar sa....
Ganin Khadija
tawuce ya sa yakama hannun ta tana ja cikin muryan shagwaba ta ce wai me zan
maka ne..
Wanka zamu yi
tare yabata Amsa ''
Haba Amjad
wani irin wanka zamuyi za ka fara halin naka Ko...
Uhmm mu je dai
banson musu....
.
Tanaji tana
gani ya ja ta har bandaki tana nokewa haka ya matsa a la dole wanka yake mata..
Sossai take ta
kare kirjin ta...
Shiko dariya ta
ba shi ya ce uhmm kiyi kigama kin san zakisiye labari na Ko..
Nace sai kin
biyani Sannan inbaki....
Oya tashi mu
je tun da munyi wankar......
Yana makale da
ita har suka fito Daga bandakin..
Daga nan wasa
ya canza salo Samad kara rikicewa ya yi ganin yanda komai nata ya cicciko cike
da kwarewa ya ringa sarrafa ta iya son ransa tun tana nokewa harta saki jikin
nata....
Kokarin
ratsata yake tuna abun da ya faru na farko ya sa tafara hawaye ta ce wayyo
Allah Amjad kar ka illatani na tuba....
Beko tsaya
sauraren ta tanaji tana gani ya ratsa ta ji zafin sossai amma bekai na ranar
farko ba..
. Hakanan ta
jure ta daure..
Yarima Samad ranar beze da wasa ba '' sai
kusan karfe hudu na Asuba ya tsarara mata....
Da ƙyar ta
tashi ta yi wanka tana jinjina jaraba irin na Samad....
Shima wankar
ya yi yadawo tare da makalkale ta kamar wacce zata gudu '' babu wuya barci ya
yi awon gaba dasu '' itako Rahama barci take tana mafarkan ban tsoro gameda
mijin nata firgit ta tashi ta zauna '' tana shafa kan sa tare da karanto wasu
adu'oi ya yi daidai da bokan jeji yana zaune tsakiyar dajin Allah yana ta
gurnani...
Ganin Guban
daya tura be isa jikin Samad ba..
Mamaki yakama
shi'' daya hango Rahama zaune a tsakiyar dakin hannun dauke da da carbi....
Razana ya yi sossai
cikin Jin takaici ya shegiya har kin wanke najasar jikin naki...
Shi ya sa kike
kokarin hana mu aikin mu...
Caraf kalamin
nasa ya doki dodon kunnen Rahama kamar Daga Sama take Jin muryan tasa......
Tabe baki ta yi da bushe da dariya ban san
kome ta karanta ba '' sai gani nayi gabadaya ba a ganin gadon da Samad ke
kwance akai......
Cikin Daga
Murya ta ce uhmm na wanke najasan '' saura kai ka wanke naka.....zunubin..
Kuma da dukan
Alamu Nice zan kawo karshen wannan ta'adancin naka...
Kallon gefen
ta ta yi taga bakin Aljanin da Aka turo....
Umarni aka
bashi a kan ya kashe Samad sannan yahada da Ahmad cikin wannan daren.....
Be Ankara ba
besan Rahama tana ganin sa ba...
Sai ji ya yi ta
watsa masa wannan ruwan adu'ar dake hannun ta...
Wani razananne
kara ya saki mai hade gurnani daya cika dakin gabadaya banda ita babu wanda
yakeji....
Doso ta ya yi cikin
zafin nama cike da bacin rai kan yakaraso '' takara wasa masa wannan ruwan ''
nan da nan ya fara ja da baya baya yana ihu ya ce wallahi Rahamatullah baki isa
ba...
Zan dawo
gareki..
Kokarin barin
dakin yake yaji Muryan Rahama tana fadin ina za ka ne..
Babu inda za
ka je ingayamaka anan wajen nida kai zamu gwada muga wanda zeyi nasara..
Ba a sanin
gwani sai angwada....
Kokarin barin
dakin yake yaga duk wata kofofin daze sa ya ba ce duk sun rufe....
Cike da tsoro
cikin gigita yake kallon Rahama ya ce kee me kike nufi ne....
Kika toshe mun
hanya ta....
Murmushi ta yi
cike da isa nan da nan ta daure fuska kamar ba ita ce ta yi murmushin ba...
Kace za ka dawo
ka nuna mun kokai wanene...
Ni kuma yanzu
nakeson in gwada maka matsayina yanda zakaba wasu labari n irin shirin da za su
yi su cini da yaki...
Doso shi take
cikin azzama Shiko ja da baya yake yana Girgiza kai cikin gajiyawa ya ce Rahama
dan Allah ki bari mu sasan ta....
Babu sasanci
tsakanina da kai saimun cire rainin....
Aljanin ganin
Rahama abun nata Azimun ne ya sa jikin sa yadau rawa...
. Duk abun da
suke boka yana cen yana kallon su '' Idanun sa sun kada jajir yana tambayar
kansa wannan wace irin yarinya ce dudu ba ta wuce 18 ba aduniya amma take
wannan iskanci....
Rahama nan da
nan tafara karanta suratul Ar Rahama '' tana gamawa ta dauko bakara tanayi tana
wasa masa ruwan adua..
Ihu yake kamar
ran sa zefi ta yana sosa jikin sa da hannayen sa...
Cikin tsananin
Azabar da yake fuskan ta....
Ya ce Rahama
dan zatin ubangiji ki kyaleni haka dan Allah narokeki wallahi ba zan kara ba
kuma zan hana wasu aikatawa saide insunyi taurin kai ne za su tunkare ki....
Rahama
tsagaita karatun nata ta yi cikin Daga murya ta ce suwaye suka turo ka...
Bokan jeji ne
yaturoni azo a kashe Samad da Ahmad a kan wulakancin da suka yiwa Fulani.....
Rahama cikin
dauriya zuciyar ta na harbawa ta ce kune kuka rayawa ? ?
Kune kuke
kashewa
Girgiza kai ya
yi ya ce A'a Allah shike rayawa yake kashewa....
Ka san da
hakan kazo shiga hurumin ubangiji...
Cikin Rawar
murya ya ce tuba nake....
Wallahi Fulani
ce da aiko mu da Farida.....
Rahama ta ce
wacece Farida kuma...
Cikin kasa da
murya Aljanin ya ce yayar Habiba ce matar gidan nan....
Kasaita cenn
murmushi ta yi ta ce in kamun karya wallahi saina wulakanta '' Rantsuwa ya
shiga yi ya ce wallahi da gaske nake Inkina tantama kije gidan Farida dakin
saman sif din' '' ki duba zaki ga laya....
Rahama cike da
daurin kai wannan Al'amarin ta ce layan na mene ne.
Layan shi ne
wanda muka daure bakin mai Martaba Sarki Turaki.....
Cikin zazzare
idanu '' Rahama ta ce kamar ya kun ɗaure
bakin nasa...
Eh mun ɗaure bakin nasa ne a kan dan
sa Salihu dan kada yaga Farin sa....
Akwai wani
kanin Nasa Sani shikuma layan da muka hada yana dakin Fulani na yanda ze tsani
da uwan nasa '' kuma duk abun da Fulani ta ce ba zai mata gardama ba...
Tun farkon
zuwan Fulani gidan ya nuna mata Inde tanason zaman ta dole tabi dan uwan sa
Salihu....
Da kuma Matar
sa...
Ita Ko Fulani
yar Asiri ce da Asirin ta yi nasaran auren Sanin duk a lokacin ba ita yake so
ba...
Mulkin da Salihu yake zaune akai sossai ya
dame ta hakan ya sa suka yi kokarin Rabawa shi da wannan kujerar harda taimakon
Sani amma ba cikin hayyacin sa ba...
Sarki ya Karbi
zancen ba cikin hayyacin sa ba...
Rahama cike da
Girgiza da labarin ta ce wani sharri ne akayiwa Sarki Salihu...
Aljani cikin
gajiyawa ya ce dan girman Allah ki kyaleni in tafi namiki AlKawari zan miki
takarda cike da sirrin komai da sani nan da kwana uku zan ajiye miki a gadon
naki yanzu wallahi bana cikin hayyacina....
Ajiyar zuciya
tasauke adua tafara yi nan da nan hanya tabude masa ya ba ce bat Daga
dakin.....
Shiko Boka
wani ihu ya yi harda Girgiza ya ce wannan tsinanniyar ta ji sirrin mu...
Kuma wannan
Aljanin inyayi AlKawari yana ci kawa harda cewa ze mata takardan komai...
Ina ba zaiyu
ba zansa yanda zanyi in dakatar da shi ze tona mana Asiri hanyar cin Abincina
ze rufe......
Ita Ko Rahama
ganin babu kowa a dakin hakan ya sa tafara adu'oi sossai kusan minti goma sai
ga gadon da Samad ke kwance akai ya bayyana a inda yake...
Bakin gadon ta
zauna '' tare da sauke ajiyar zuciya akai akai juyawa ta yi tana kallon Samad
yanda yake barcin sa hankali kwance rungume da pillow......
Agongo dake
makale jikin bango ta kalla taga karfe biyar na Asuba...
Hakan ya sa
tafada bandaki domin yin Alwala...
Bayan ta yi nafila
tadauko Alkur'an mai girma tasoma karantawa cike da nutsuwa..
Zazzakar
muryan ta ya doki dodon kunnen sa.....
Hakan ya sa ya
bude Idanun sa dake cike da barci tare da sauke su a kan ta....
Mika yasoma
ganin haka cikin sanyi murya take kallon sa ta ce kayi adu'a tashi Daga barci
Ko...
Girgiza kai ya
yi ya ce afuwan bara in yi koda ya yi kai tsaye bandaki yafada babu ba ta lokaci
ya yi fitowa sanye da jallabiyar sa maroon..
Farar hular sa
ta saka ya saka a kan sa''' '..
Kallon ta yake
tana kokarin tada Sallah' '' Ya ce hubby na...
Yanzu kika
tashi ne..
Murmushi ta yi
ta ce uhmm ni dai saika dawo....
Daga haka ta
fuskan ci Alkibla Shiko kai tsaye ya nufi massalaci babu ba ta lokaci aka tada
Sallah
Kusan Karfe
bakwai saida gari ya yi haske Sannan suka nufo cikin gida shida Ahmad dake
kokarin wucewa sashin sa...
Yarima Samad
kallon sa yake ya ce dakata nan Sarki ya aiko yana son ganin mu nida kai..
Cak Ahmad
yatsaya tare da waigowa cikin Idanun wanda ke Jin barci ya ce Amma tsohon nan sai
ya bari gari ya waye Ko...
Inmunje saika
fadamai shiga gaba muje..
Dan tsabar
rainin wayau dan waken daka siyo wa Rahma ba a sa mata ya ji yaji ba...
Uhmm aisai ta
yi yajin da kanta har danwaken nifa adaina mun zancen wani danwake raina baci
yake..
Samad dake
kallon sa ya ce Ah to yaya na gama min fada sannan Muje...
Kama kunnen
Ahmad ya yi ya murza da dan karfi saida ya saki kara..
Yana sosa
kunnen cikin ba ta fuska yaturo baki gaba wai Yaya menayi maka ne tun sanyin
safiyar nan...
Zaka wuce mu
je Ko sai....
Ganin zekara
cikin hanzari suka yi sashin Mai martaba...
Iske shi suka
yi zaune bayan sun gaisa...
Cike da fara'a
yana Jan carbi ya ce uhmm ku zauna yan Albarka...
Zama suka yi
suna sauraren abun da ze ce...
Daman nakira
ku ne a kan maganar auren Ahmad...
Yarima Samad
dake mamakin furucin Sarki ya ce aure kuma..
Yaushe ya samu
matar aure...
Ahmad yasoma
sosa keya ya ce uhmm damar Asiya ce nakeso kuma za a nema mun auren ta....
Yarima Samad
cikin tsananin damuwa ya ce wace Asiyar ?
Badai kawar
mata ta ba..
Ahmad ya ce
ita nake nufi mana...
ZUMBUR YA MIKE
TSAYE..
Me Martaba da
Ahmad da mamaki suke kallon sa Sarki ya ce lafiya kuwa yarima...
Goge Zufa
yasoma yi ya ce inafa lafiya yarinyar nan abokina Faruk yake son ta...
Ya za ai ya ce
a bashi wannan zancen banza ne...
Sarki ya ce
haba Samad kanin ka ne fa ya fi Faruk matsayi awajen ka...
Yarima Samad
zama ya yi cikin sanyin murya ya ce Sarki babu soyayya tsakanin Ahmad da
Asiya....
Sarki
numfasawa ya yi yana kallon yanda Samad yazubawa Idanun sa toka a kan lamarin..
Ya ce inaga
kaima da akai maka auren aiba soyayya ta hada ba amma kuma yanzu fa na ji labarin
yanda zaman ku yake.....
Turo baki gaba
Samad ya yi yana surutai kasa kasa ya ce shi ke nan nayi shiru an nuna mun ban
isa inhana laifi afkuwa ba...
Ahmad kallon
Samad yake ta gefen idanu ganin lallai da gaske yake beson lamarin....
Sarki gyaran
Murya ya yi ya ce ai aikin gama ya gama da ce gaban ka yazo da zancen ka hana
toya hanu '' 'nikam harna yi magana da Sheik Abdurrazak ya ce yau zeyi magana
da baban yarinya...
Yarima kayi
hakuri adua' zakayi kaba abokin naka hakuri...
Yarima tabe
baki ya yi tare da yin tsaki ya ce ninasan wallahi badan Allah yake son Asiya
ba da wata manufa akasa.... Yarinyar nan kwata kwata ba sa shiri shi ne dan
zalunci ze ce ze aure ta...
Naji na amince
ayi auren amma ya sani wallahi naga rashin daidai a kan Asiya ba zan duba
Alakar mu ba.... Zan gyara maka zama...
.Ahmad
murmushin dole ya yi ya ce na ji na amince..
Uhmm Allah ya
sa Alkhairi cewar Samad tare da tashi tsaye..
Ahmad shima
tashi ya yi mai martaba ya ce '' Samad ina son Daga yanzu afara gyara Sashin
Ahmad ayi masa komai yanda akayi maka...
Yarima ya ce
babu matsala zanje inda kwanta kafun mu je rakiyan baki.....
Kusan tare
suka fita shida Ahmad..
Kowa ya yi ɓangaren sa.....
******************
Kusan karfe
tara Rahama da Samad suka shirya tsaf a gaggauce suka yi break duba da lokaci na
tafiya za su je rakiya...
Sabon layi
daya siyo mata ya mika mata..
Ya ce miko
wayar insaka miki '' cike da Jin dadi ta ba shi ya saka mata...
Tana sanye
cikin doguwar riga Abaya mai adon Stone '' baki sossai kalan kayan yamata kyau
ka santuwa ita fara ce....
Shima Samad
cikin suite baki da wandon sa baki takalmin sa haf cover ya sanya sossai shigar
ta karbe su hakan ya sa ya musu selfie masu kyau yana rungume da ita....
Rada ya yi mata
a kunne ya ce Rahama anjima zaki ba ni Ko...
Bata fuska ta
yi ta ce uhmm wayyo Allah Abbana Amjad ze cinyeni...
Dariya sossai
ya yi ya ce Abby inyaji ban taba cen kwaceki zeyi Daga hannun abun da yakawo ki
kiyi kenan...
Uhmm ni dai
Abbana yakawo ni dan inringa dafa maka abinci ne....
Kuma in
gayamaka babu na ɗare
kama shafa wa kanka lafiya ni tunkiya ce zakai ta tumurmusa ta..
Sossai ya dara
harda rike ciki itako uhmm take fadi ni dai mu je ka ga khadija ta yi gaba mu
ake Jira....
Babu ba ta lokaci
suka fito suna kokarin rufe kofar yaga Karima cikin hanzarin ta ta durkusewa
kasa tana gaishe su....
Uhmm shugaba
ku tafi zan rufe sashin...
OK. Ya furta ya
ce ya jikin naki ta ce dasauki...
Rahama ta ce
Allah yakara lafiya Karima sai mun dawo...
Daga haka suka
sa kai..
Anty da Asiya ɗa Salma tsaf suka shirya
suma ɗuk sun fito
farfajiyar gidan.....
Mamy da
Fulani' 'Abban Marwan harda marwan da Ahmad duk sun hallara wajen rakiyan
baki....
Rahama da
Samad kadai ake jira ganin su ya sa babu ba ta lokaci' '..
Motoci suka Jeru
aka fara shirya kayan su a bayan boots...
Motoci hudu
suka fita Daga masarautar dan kai su filin airport...
Koda suka isa
airport din sun iske Faruk da Aminu...
Asiya tana
ganin Faruk murmushi ta sakar masa hakan ya sa suka koma gefe daya su biyu suna
tattaunawa...
Ahmad duk abun
da suke Idanun sa na. Kansu....
Mamy cike da
farin ciki ta rungumi Anty tare da musu godiya '' 'fulani ma godiya ta yi a kan
kawo musu mata...
Nan dai suka
yita fira na rabuwa da junan su....
Har lokacin da
matukin jirgin Samad personl ya fito ya ce su shiga ya shirya...
Babu ba ta lokaci
anty tafara shiga jirgin..
Salma cikin
kunan rai ta shiga..
Asiya zata
shiga ta wai go tana dagawa su Faruk hannun '' 'harara ta watsama Ahmad tare da
yin tsaki...
Sossai ran sa
yabaci..
Rahama dake
kukan rabuwa dasu ta ce bara tashiga zatayiwa anty magana...
Samad be hana
ta ba...
Tana shiga ta
iske anty tana adu'oi cikin kuka ta ce yanzu Anty zaki tafi kibarni...
Ita ma Anty
kuka take ta ce kiyi hakuri Rahama aikin ba mu lambar ki Ko kuma kin amshi namu
ba mu rabu ba banda abun ki ga waya....
Rahama ta ce Anty
keda Asiya. Banson tafiyar ku..
Kema salma
banson ki tafi...
Anty salma
tabaki kudi Ko..
Anty ta ce eh
tabani wannan kudin ne nagane su inna isa zamuyi magana...
Asiya rungume
Rahama ta yi tana kuka Rahama itama tana kuka..
Yarima Samad
ganin ta dade ba ta fito ba..
Hakan ya sa ya
shiga ciki Da ƙyar ya fito da ita tana kuka...
Zuwa tayi ta
rungumi Mamy...
Itako Mamy
rarrrashi tashiga yi...
Suna kallo
jirgin su Asiya ya keta azo a sararin samaniya.....
Farruk da kusa
da Ahmad ya ce uhmm zanyi miss din masoyiya ta.
Ahmed
fuskantar Faruk ya yi ya ce...........
Ina barar
adu'ar ku a kan mahaifiya ta yau tacika shekaru 13 da rasuwa 4 march...
Sannan
inajiran ruwan comment...
Taku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
Littafin nan
kudi ne Inkin ganshi a wajen group dîna na sata ne
Inkina bukata
ga nomba
09069080725
8️⃣3️⃣
Ahmad
fuskantar Faruk ya yi ya ce uhmm daman kuna soyayya ne...
Faruk cike da
mamaki yake juya kalaman Ahmad ya ce Ko kana so ne ?
Ahmad ya ce eh
mana nagani inaso harna yi wa mai martaba maganar a neman mun auren ta....
Wani irin
shock Faruk ya shiga nan da nan kansa ya sara yana ganin hajijiya...
Ahmad ganin
yana tangal tangal ya ce yadai yaya Faruk lafiya kake kuwa tare da dafa shi....
Faruk cikin
aro jarumta tare da saita nutsuwar sa da taki komawa daidai ya ce uhmm Ahmad ai
ko rana aka samun da Asiya kace kana sonta wallahi zan janye in barmaka kaifa
kanin mu ne..
Ahmad cikin
tausayin sa ya ce Ah Ah kabari ni zan janye kafini bukatar Asiya gashi naga
zahiri...
Faruk ya ce
kanina kenan kaidai na janye Allah ya sa hakan shiyafi zama Alkhairi..
Wallahi babu abun
da za ka so '' face nafika son abun kar ka damu kanina Allah yabar kauna...
Ameen Ahmad ya
furta Azuciyar sa sai fadi yake uhmm dan ba ka san dalilin daya sa zan aure ta
bane da ba ka barmin ba inna koya mata hankali zan sako ta ka aure ta...
Murmushi ya yi
yana yiwa Faruk godiya ganin su Samad da Rahama har sun shige mota ne ya sa
Yayiwa Faruk sallama '' '.
Faruk wajen
Aminu ya je ya zauna cike da damuwa ya ce Aminu shi ke nan na rasa Asiya ban
san haka so yake ba..
Soyayya Zuma
ce amma tafi madaci muni inka rasa abun sonka..
Shi ke nan
tawa ta sameni...
Aminu ya ce
tofah waiku bakuda aiki sai kuka a kan mata ne kaida Samad tsaki ya yi ya ce
yanzu wai me akayi maka ne...
Faruk cikin
tsagaita kukan nasa ya shiga bawa Aminu labari yanda suka yi da Ahmad...
Aminu jinjina
Al'amarin ya yi ya ce kar ka damu '' ka ga Rahama ta samu yar uwa akusa da ita
in Ahmad ya auro Asiya....
Ka san
shawaran da zanbaka kabawa zuciyar ka hakuri maganar mata..
Ka tattara su
gefe daya ka ajiye sai nan gaba...
Faruk ya ce
InshAllah na ji shawarar gashi kai kana zaune lafiya tun da ba ka harkan mata..
Aminu Murmushi
ya yi ya ce Ashe dai ka gane abun da nake nufi kaide ayi sha'ani kawai mata Ko
wahala...
**************************
Gabon 🇬🇦
Baba Salihu
cikin shigar sa ta Alfarma shida wasu a bokan nasu za su je kai goron sa ranar
auren sheik da hassana sossai yakejin kansa a nishadi hadin da ya yi kuma sheik
ya karba....
Zama ya yi bakin
gado yana tuna irin Alkhairan sheik gashi faran daya ya ba shi mata ya karba ba
tare da ya musa....
Dattijo ne ya
shigo bakin sa dauke da sallama yana sanye cikin farar shadda..
Kansa aduke ya
ce shugaban Adalai Barka da wannan lokacin..
Kai muke jira
mu tafi..
Baba Salihu
cike da farin ciki yake kallon dattijon ya ce uhmm ka ga wannan Aminin nawa
sheik Abdurrazak ban san da wani kalma zan gode masa ba...
Matar da
takeso taje har gidan mu tana bincike dan sanin sirrina shi ne naga gaskiya
taje tabinciko sirrin namu ba ta aure ni ba nasan yadawa zatayi duk da babu
rashin gaskiya a tattare da hakan...
Shi ya sa na
zabi in hada ta da sheik in kanta na rawa ne ze sata ahanya..
Kuma na ji mijin
nata marigayi mutum kirki ne...
Kuma itama an
shede ta shi ya sa banyi kasa a gwiwa ba..
Banson na yi
wa Habiba kishiya '' shima sheik dan ya tara biyu ne shi ya sa zankara masa da
daya ya iya rikon gida...
Niko fa Inde a
kan mamy ne ba zan iya yiwa wata matar Adalci ba...
Sossai Dattijo
ya jinjina bayanan baba salihu ya ce shugaba na maganar ka dutse....
Shi aure
anayin sa ne inhar mutum zeyi Adalci tun da ka nuna hada mata biyu anan za ka gaza
dole ne ka janye...
Uhmm yawwa ka
gane nufina tashi ya yi Daga zaunen babu ba ta lokaci suka fito Daga gidan....
Koda suka isa
aka kai goron baba Salihu ya ce uhmm Nine zankai Amarya garin kano '' bikin
nake jira sanna in tafi...
Sossai suka
yaba da halin mutuntaka irin na sarkin adalai.....
Baba Salihu
sanarwa sheik labarin yanda akayi komai ya yi sossai sheik yaji dadi tare da
masa Albishir tun da Amarya zata tare za su koma sabon gida...
Yanacen anata
gyare gyare Daga haka suka yi sallama....
Shiko Sheik
cikin hanzarin sa ya sa aka gyarawa anty dakin nata da ya yi kura komai aka
gyara mata tsaf har tukwane saida ya sa duk aka wanke mata su....
Mama dake
kallon shiga da fitar sa ta ce uhmm mijin ta ce anata hidima gimbiya zata
iso....
Cak sheik ya
tsaya yana jinjina kalaman ta...
Waigowa ya yi tare
da isowa kusa da ita ya ce...
Ai ban girma
ne kazama matar ka duk abun da ta ce shi zakayi wannan ba haramun bane dan ance
min mijin ta ce....
Dan bakiyi
karyaba sai abun da ta ce shinake yi nima sai abun da nace shi take yi kinga
ita matar nace take ni kuma mijin ta ce ya kike ganin sunan yada ce ɗamu Ko....
Yar uwar ki
zata zo amma kinkasa tsinana mata komai dan bakin hali..
Da kaina zan
shiga kitchen indaura masu girkin Ko inkira kanwar Asiya '' tazo ta dafa musu
koda taliya ce dadin abun harda yar ki acikin su.....
Kwabe baki
Mama ta yi ta ce uhmm yata tana ciki namata girki ita da Asiya wannan bakar
Aljanar ka ita ce bazata ci ba..
Alhmdulilah ya
furta tun da ita bakar Aljana ce ke kuma bakar zunubi Ko..
Ba girmana
bane in tsaya ina biye miki ba...
Amma kisani
wallahi Aisha na gaji da halin ki.....
Daga ji shi ya
sa nakosa wannan Amaryan da zanyi Sa'adatu tasamu abokiyar shawara da sauran su
wacce zasuyi taimakeni in taimakeki bawai zaman dutse irin naki ba....
Ran Mama ya yi
mugun baci waini yau Sheik yake fadawa bakaken maganganu...
Wuce ta ya yi domin
shirya dan jirgin su Anty na gab da karasowa..
Wayar Mama ce
ta soma. Ring tana dubawa taga bakuwar lamba ce kuma ta kwatano shi ya sa ba ta
ki dagawa ba.....
Daga can ɓangaren cike da murna harda
buga uban tsalle a daki bakin ta awashe ta ce wayyo Mama na '' Rahama ce....
Mama kallon
wayar taki da kyau Jin dai ba Mafarki take ba..
Ta ce Rahama
yau kece kike kirana dan kinga anty taki ta baro kasar Ko....
Nan da nan
jikin Rahama ya yi mugun sanyin cikin kasa da Murya ta ce mahaifiya ta kodaya karkiyi
fushi dani wallahi tun da nazo kasar banda layi sai yau nasamu...
Ki tambayi
Abby ran nan ma da yake son magana dani kiran Abdul Samad ya yi ya hadashi
dani...
Haba Mama kin
san in inada waya da layi ba zanki nemar ki ba....
Kece uwa ta
karki yi fushi dani dan Allah...
Mama cikin Jin
dadin kalaman Rahama ta ce uhmm na zata kin canza uwa ne...
A'a Mama banda
kamar ki aduk duniya dagake sai Abby sai Anty na...
Jin ta Ambaci Anty
nan da nan hannurin dake kwance kan fuskar mama ya ba ce bat...
Ta ce dan uban
ki meye na kawo zancen Sa'adatu agabana...
Rahma sossai
takejin haushin Rashin kaunar da mama ke nunawa Anty '' ba a canza uwa ne data
canza haka zuciyar ta ke raya mata....
Afili kuma
hakuri tashiga bawa Mama ta ce ina yaya Abubakar yake ne tasan inta ce ina
Abdul jalil yanzu zancen ze lalace...
Mama ta ce
yana lafiya lau nayi kewar ki yata tun ranar da kuka zo Asibiti duba Salma keda
mijin naki bankara sanyaki a idanuna ba...
Rahama cike da
bukatuwa ganin uwar ta ta ce InshAllah mun kusa zuwa zanzo gida in yi kwanaki
Mama na..
Sun taba hira
sossai Rahama taba Mama labarin su Mamy sossai Mama ta ji dadin karamci na Mamy
ta ce Rahama ta turo mata lambar Mamy ɗana
Samad '' 'babu ba ta lokaci Rahama ta tura mata Daga suka yi sallama....
Mama tabe baki
ta yi ta ce uhmm yata tana gidan daula' ɗaman
ba a son ka fito gidan dadi kaje gidan wahala ba irin na Salma ba dole yau zamu
rikita Al'amin......
*************************
Shiko Al'amin
zaune yake gaban malamin nasa..
Ya ce malam
inada mata ta amma nalura sotake ta rabu dani..
Ni kuma ban
gama latsar Zuman ta ba..
Malamin ya ce
uhmm ai hâr mijin dazata aura sun fitar mata...
Amma mijin dan
karya ne suka hada baki da Aminiyar uwar ta dan acuce ta yanda za su samo kudi
ta hannun su....
Al'amin
jinjina Al'amarin ya yi ya ce uhmm ni dai gaskiya ba zan sake ta...
Badai karyan
Arziki takeso ba uhmm kwanan nan zan Faso gari wallahi zatayi mamaki Ko yanzu na
fara samun kudi...
Malam ya ce
yawwa kayi kokari kabar gidan da kake ciki kasamu miliyan daya kaba uwar ta..
Ita kuma
yarinya basai na fada ba...
Kar kayi wasa
inhar ka san kana son ta...
Dan inhar ba
ka nuna mata kudi masu yawa ba na tashin hankali ba akwai matsala....
Al'amin cike
da yarda da shawaran da Aka bashi ya ce InshAllah zangwada
Sai kusan
karfe daya jirgin su Asiya ya sauka a babban filin airport na kano....
Sheik da kan
sa ya je dauko su Anty tare da drever ka sancewa Abubakar baya zama gida Ayyuka
sun masa yawa shike kula da komai na baban sa.....
Cike da jindadi
ya tarosu yana ganin sun sauka a jirgi...
Anty sai Washe
baki take taga mijin nata shima din murna agun sa baya misaltuwa yau gashi ga
sanyin zuciyar shi...
Basu ba ta lokaci
ba suka shige mota direct gida suka zarce...
Asiya cike da
gajiya ta ce nikam nayi gidan mu..
Sheik ya ce
A'a babu inda zakije kin dawo da zama agidan nan bakisan mun bayar da auren ki
ba...
Gab gab haka
zuciyar Asiya yashiga dukan uku uku....
Dago kai ta yi
tana kallon Sheik dake kokarin shigar da kayan su dakin Anty...
Ita Ko Salma
dakin mama ta tafi cike da takaicin wannan rashin nasara data samu.......
Ita Ko Asiya
Mutuwar tsaye ta yi tana kallon Sheik dake fira da Anty yana bude mata kulolin
abincin da Aka aiko Daga gidan Asiya....
Mama
nunawa ta yi batasan da zaman anty ba bare ta
yi mata barka da isowa
Anty tana gama
shirya kayan su ta tashi ta nufi dakin mama cike da ladabi ta ce Maman Salma
mun dawo...
Mama tabe baki
ta yi ta ce uhmm nasan kindawo to Barkan ki.....
Anty ta ce
yawwa godiya nake..
Tare da komawa
dakin nata.....
*************************
Bayan kwana
uku rayuwa nata tafiya yanda akeso...
Al'amin yazo
da niyar daukar Salma su tafi '' Mama ta ba ta wani kullin magani da zata shaka
miki inhar yazo...
Cike da
hanzarin taje ta tarbeshi har tana wani shafa shi '' lura da bayanin da malamin
ya yi masa ya sa ya fara ja da baya baya.
Ita Ko tana
kokarin ta kamo shi..
Yana zille
mata.....
Ganin akwai
abu a hannun ta hakan ya sa yakama hannun nata ya murda saida ta saki kara dan
Azaba ya ce uhmm wallahi baki isa yau dinnan zaki zo mu je sabon gidan mu...
Yarfe hannayen
ta take yi cike da Azaba ta ce ahaka zanbika..
Babu inda
zanje ka kama kanka...
Yayi daidai da
shigowar Abubakar daidai wajen nasu ya tsaya yana kallon yanda Salma ke rashin
kunya....
Cike da mamaki
ya daka mata tsawa tare da kai hannu ya wanke ta da mari.. Cikin fada ya ce
mijin ki yawuce raini Ko bakisan girman miji bane...
Wannan ba
tarbiyyan gidan mu bane..
Kallon sa ya
maida a kan Al'amin ya ce kayi hakuri kadawo anjima da an yi lasa'ar kadauki
matar ka.
Ku tafi..
Al'amin cike
da Jin dadi ya ce yaya Abu nagode Allah ya saka da Alkhairi....
Itako Salma
sossai marin da yayan ta ya yi mata ya yi mata zafi..
Yana shiga
cikin gidan ya iske Mama da sheik zaune a dakin nasa.
Da Alamun
korafi take masa a kan wannan auren da zeyi '' shikuma sai fadi yake mata sunyi
yawa dole ayi ta rage su...?
Mama ta ce wai
wannan matar a ina take ne..
Ya ce Gabon
Girgiza kai ta
yi ta ce wani munafuki ne yahada wannan auren '' dan nasan ba ka zuwa nema ''
saide abika dashi....
Kokarin ba ta Amsa
yake ganin Abubakar yashigo ya sa shi yin shiru '' dan yanzu soyake ya kora
mama makarfi '' tunanin mahaifin nasu yake '' yaki bashi daman ya koya mata
hankali ta hanyar tura ta makarfi ta yi koda shekara daya ne...
Abubakar da
ransa yake aba ce ya ce Abby wallahi Salma batasan darajan aure ba..
Kaga yanda
take zagin mijin ta Shiko yana tsaye yana kallon ta....
Ran sheik
yakai kololuwa wajen baci hakan ya sa miki tsaye cikin zafin nama yabar dakin..
Koda ya isa
zaunen be iske su Salma ba.....
Cikin gidan
yakoma tare da zuwa dakin su Salman iske ta ya yi zaune zata bude data....
Dago kai
azabure ta yi ganin yanda...........
Ta ku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
Littafin nan kudi
ne Inkin ganshi a wajen group dîna na sata ne
Inkina bukata
ga nomba
09069080725
8️⃣4️⃣
Dago kai
Azabure ta yi ganin yanda yake kokarin kai mata mari...
Cikin gigita ta
ce Abby lafiya kuwa...
Dan uwar ki
mijin naki kike wa rashin kunya abun da kika ga jatimar ki ta nayi shi ne zaki
masa to wallahi ba zan lamun ta ba...
Mama dake
karasowa ta ce A'a kar ka zage ni inzakayi mata fada kayi mata amma ai wannan
zagina kake yi Nice mara kunya Ko...
Sheik cikin
Jin haushin Mama ya ce Aishatu wallahi inhar Salma ba ta koma gidan mijin nata
a yau dinnan ba a bakin auren ki duka igoyiyon su tsinke....
Azabure Mama
da Salma suke kallon Sheik dake kokarin wucewa sashin nasa cikin bacin rai....
Bakin mama na
rawa ta ce '' Salma kinji abun da yafada kuma tun da muke betaba mun irin
wannan furucin ba....
Salma cikin
gigita ta ce mama ni gaskiya ba zan koma ba...
Tass kake ji
mama ta wanke ta da mari yau na tabbatar ke banza ce Salma a kan ki igiyar aure
na '' 'na neman tsinkewa shi ne zaki ce' '' ba za ki koma ba '' kenan inbar
gidan nan kike so...
To wallahi
baki isa ba...
Salma rike da
kuncinta hawaye shar a Idanun ta ce mama yau da kanki kika sa hannun ki kika
mare ni...
Yaya Abubakar
ya mareni..
Abby ya
mareni..
Kema kin
mareni..
Kusan lokaci
daya yau na tabbatar ba a kauna ta agidan nan..
Mahaifina na
korana ke kuma dan ya miki barazana tome A'ciki Dan ya sake ki din..
Mama batasan
sanda ta doki takalmanta ta rinƙa bugawa Salma ba '' tana ihu '' sossai
mama ke bugun ta '' ta ko' ina..
Sheik yazo
daidai fita yaji yanda take bugun Salma cak ya tsaya ganin Anty ta fito hakan
ya sa shi kallon anty cikin bacin rai ya ce Sa'adatu koma daki nace Ko..
Babu musu ta
koma tana Girgiza kai...
Shiko Sheik
karasowa wajen Mama ya yi cikin Daga Murya ya ce Aishatu ki sakar mun ya....
Dan ke ba ki
da hankali saiki buge ta..
Mama cikin
takaici ta ce yarinyar nan ta rainani waini take gayawa zancen banza...
Sheik ya ce
kwarai kuwa ta gayamiki ai Salma kawar ki ce...
Dan me bazata
fadi son Ranta ba ni tafadamun mana wargi waje ya samu...
Daga haka ya
sakai yafice Daga gidan yana Girgiza kai...
Ranar mama ba
ta bar Salma ba '' kiran Al'amin ta yi ta ce yazo daukan Salma cike da Jin dadi
Al'amin yaturo yayar sa Mariya...
Koda Mariya ta
iso gidan '' cike da girmamwa ta gaisa da mutan gidan...
Anty ta ce
badan ban nemi izini ba '' ɗana
raka ku har gidan ki..
InshAllah
innasamu dama zamu kawo miki ziyara nida Asiya...
Sossai Salma
ke kukan zuci wai yau mama ce ta hada mata kayan ta..
Babu rarrashi
babu magana me dadi neman kawai take tabar gidan....
'' 'Mariya'
tarar me napep ta yi tare da taimakon Abdul jalil aka saka kayan Salma cikin
napep din.....
Kwatance
mariya tayiwa me napep din unguwar da za a kai su...
Ita Ko Salma
zaune take zuciyar ta na tafasa..
Sam taki kula
Mariya data rakota banda hararan ta ba abun da take yi...
Suna isa gidan
'' Mamaki ne yakama Salma ganin wani shahararren gida na gani da na fada.
Kamar gidan
daya da gidan Samad sai dai nasu bekai nashi haduwa ba..
Mariya dake
kokarin kama hannun Salma domin shiga gidan..
Nan da nan
taga Annurin a fuskar Salma..
Waigowar da
Salma zatayi Al'amin ta hango cikin wata bakar mota Mercedes cike da zallan
Mamaki take kallon sa har ya yi parking A gaban su...
Bakin Salma na
rawa ta ce.........
Al'amin ina
kasamo mota ne...
Murmushi ya
sakar mata cike da jin dadin ganin ta '' ya ce Amarya mushiga Daga ciki wannan
motar ɗana tuko
mallakkin kine nawa yana cikin gidan..
Hannun ya yi musu
ya ce mu je Ko..
Ba musu suka
bi bayan sa ya yi musu jagora har cikin gidan.....
Mai gadin
Barka da zuwa yake ta fadi '' soya ke ya yi magana da Al'amin ya tambaye sa Ko
ita ce matar sa '' yana gudun kada ya kwabsa masa......
Hakan ya sa suka
yi cikin gidan...
Wani katoton
falo '' sossai mai girman gaske..
Anzuba daula a
falon '' kujeru yan waje forein '' komai special hatta carpet din dake malale
tsakiyar Falon shima abun kallo ne...
Salma tazama
kamar wata bakauya badan ba ta taba gani ba saidan mamaki ne yakamata wai nan
gidan mijin ta ne....
Ita kanta
Mariya cike da mamaki take dan a tunanin gidan haya ne..
Saita ga
sabanin haka so take ta zanta da kanin nata amma babu dama ganin Salma na
wajen.....
Salma dube
dube tafara acikin gidan tana leka lungu da sako na kowani gidan....
Ganin Salma
tabar falon ya sa Mariya fuskantar Al'amin ta ce kai ina kasamo wannan gidan ''
da kudi da kake ta fantamawa nifa abun ya fara ba ni tsoro.....
Al'amin tabe
baki ya yi ya ce kema zakiyi irin abun da baba ya yi ne nacewan ba zai ci kudin
ba '' sai yaji kwakwaran sana'a ta...
Toke ba zan
boye miki ba kuma dan Allah karki tona min Asirin nashiga kungiyar Asiri na
mafiya....
Mariya cikin
gigita take kallon sa ta ce haba Al'amin meya kaika ka san hadarin dake cikin
wannan kungiyar..
Uhmm Mariya
kenan nifa ba zan ba da Jinin kowa ba saina Salma...
Azabure Mariya
ke kallon sa ta ce bangane Jinin Salma za ka bayar ba...
Matar ka ce
fa...
Murmusawa ya
yi ya ce mata ta ce amma batasona dukiya takeso fiye da komai zanbata dukiya
taci a karshe inmika ta....
Innaliahi
wa'inna ilairajun Mariya take ta maimaitawa ta ce Al'amin kaji tsoron Allah dan
Allah kar ka cuce ta '' tana dauke da cikin ka...
Anty Mariya
saita haihu zanbada Jinin ta '' kinga tabar tarihi kenan.
Narokeki karki
tona mun Asiri yarda ce tasa nabude miki cikina..
Isowar Salma
ya sashi yin murmushi ya ce yadai Amarya gidan ya yi miki ko ''
Kada kai ta yi
ta ce gaskiya gidan ya yi kabari sai na haihu saika canza mana gida....
Kuma ina
bukatar yan aiki...
Mariya cikin
dauriya da tausayin da Salma tabata ta ce uhmm.zaki samu yan aiki har ki gaji dasu
yar uwa ta...
Nan dai ya
nunawa Salma dakin ta..
Da komai yanda
suke..
Sossai ta ji
dadin hakan...
Tana murna
sotake takira mama marin da ta yi mata da duka ya sa ta ce uhmm ba zan kirata
ba..
Sai dai ta ji
agari ina fantamawa da naira badai ni ta wulakanta ba..
Koda Mariya
zata wuce''' Al'amin duba dari yadauko yamika mata amma taki Amsa ta ce kabar
shi nagode...
Salma ta
yatsine fuska ta ce haba anti ana baki kina kin Amsa..
Murmushi ta yi
ta ce aiya ba ni kafun inzo sun isheni haka...
Al'amin ya ce haka
ne to anti mariya mu je in raka ki.....
Har bakin gate
ya rakata yana kara jaddada mata karfin AlKawari data dauka..
Cike da yarda da
kai ta ce Al'amin baza a ji shi a baki na ba..
Komawa ya yi cikin
gidan yabarta anan tsaye..
Itako tsaye
take tana lissafin anya zata iya barin akashe rai..
Taci Alwashin
inhar salma ta haihu zatasan dabarun dazatayi ta ganar da ita gaskiya ba tare
da ya sani ba..
Da wannan
tunanin tabar kofar gidan....
Kwatano
Fulani cikin
tashin hankali take kallon bokan jeji ta ce kana nufin bakin Aljani ya fallasa
sirrin mu..
Bokan jeji
cike da takaici ya ce baduka bane dan ya kwantar mata da hankali ya ce '' wace
ita data San sirrin namu sai dai ta ji na Farida...
Ajiyar zuciya
Fulani ta sauke cike da Jin saukin Asirin ta be tonu ba..
Ta ce bokan
jeji yakamata mijina a sake masa sabon jiko jiya naga kamar yana fadin '' ina
zega Salihu koda sau daya ne........
Bokan jeji ya
ce ina ba zai ga Salihu ba''' kuma kisan yanda zakiyi kibashi magunguna yasha
'' shikuma yaba baban shi...
.
Kasaitaccen
murmushi cike da takama ta ce '' watau abun naka aike aike ne...
Kwarai kuwa
cewar bokar jeji..
Sun dade suna
tattauna Daga karshe suka yi sallama..
Ta fito cikin
ciyayi nan tare da nufar motar ta......
Rahama zaune
take tana gyare gyaren dakin '' mijin nata..
Taji wani iska
me karfin gaske ya kada '' nan take tafara adu'oi....
Wannan iskan na
tsai gaitawa Idanun ta suka sauka akan.....
Takarda dake
kan gadon nata.
Cikin Azzama
hannun ta na rawa tadau takardan
Koda ta
warware takardan ganin rubutun ta yi dan Jan biro aka rubuta shi ta harshen
larabci '' hakan ya sa hankalin ta ya yi mugun tashi cike da aro jarumta take
son ganin meye A'ciki...
Sallamar Samad
ne ya sa ta kokarin boye takardan amma ina yariga da yagani '' kusanto inda
take ya yi cikin hanzari yana mata kallon tuhuma
Cikin tsaita
nutsuwar sa '' ya ce Hubby me kike boye mun ne bakyason ingani...
Bakin ta na
rawa ta ce uhmm kai me ka gani..
. Hannun ta ya
kamo ya hade da nashi yana kokarin amsar takardan...
Girgiza kai tasoma
ta ce A'a Amjad dan Allah kar ka amshi wannan takardan Idanun ta nan da nan
yakawo ruwa''Sam batason yakaranta abun da ze Girgiza shi...
Kallon ta yake
yana nazartan ta''' miko mun ya furta cikin kakkausar murya tare da hada rai
kamar bashi ba...
Ganin yanda ya
canza launin sa' 'yasa ta tsoro ta
Babu musu ta
mika masa
Zama ya yi bakin
gadon yasoma karantawa''' a fili.
Kamar haka....
Rahamatullah
hakika haduwa ta dake bemun dadi ba' 'nasan kinada sirrin adu'a da zaki iya
dawo dani cikin dakin ki inhar bancika AlKawari ba.....
Bokan jeji ya kar
kade ni kada in sanar miki da komai nace masa naji..
Amma ban dauka
ba...
Rahama nafara
baki labari to yanzu zanci gaba Daga inda natsaya aranar kin tambayeni laifin
mène uban mijin naki yayi...
Abun da ya faru
da sa hannuna ni Aljani Sultan..
Sarkin Adalai
Sarki ne mai gudanar da mulkin sa a kan ka'ida da dokokin musulunci '' babu
yanda Fulani da Farida basuyi ba dan asauke shi ba...
Ita Farida
tanason ya sauka ne dan tun farko be aure ta ya auri kanwar ta da Aka bashi
zabi '' wannan bakin cikin yana nan aranta...
Ita Ko Fulani
ta nemi da Sarkin Adalai da ya yi Alfasha da ita...
Ya nuna mata
Sam shi ba zai iya cin Amanar kanin sa ba..
Watarana
safiyar wata juma'a Sarkin Adalai ya fito Daga sashin nasa zanshi Fada ''
yahadu..........
Ta ku har
kullum kyauta Daga AllahƘANWATA
Littafin nan
kudi ne Inkin ganshi a wajen group dîna na sata ne
09069080725
8️⃣5️⃣
Yahadu da wata
baiwar Fulani mai suna Saratu '' cikin gigita tana ihu ta ce Shugaban Adalai
dan Allah ka taimaka mun kwarto ne acikin dakina....
Cikin gigita
yake kallon ta ya ce Saratu kwarto a dakin naki kuma...
KADA kai ta yi
cikin kuka ta ce wallahi da gaske nake ya shugaban Adalai nasan saukin kan ka
ba kamar tsauran sarakuna bane dan Allah kasa wani ya taimaka mun....
Kallon ta yake
yana nazartan ta ya ce yanzu na aiki waziri da fadawa wajen duba dabbobin da za
a yanka Sadaka..
Kin tabbatar
yana cikin dakin mu je ingani sai insa '' akamashi..
Gaba ta nayi
yabinta abaya ''hannun sa najan Carbi...
' 'Fulani da
maman Maryam suna labe suna kallon yanda Al'amarin ke faruwa' 'hakan ya sa
cikin sanda sanda suka ringa binsu abaya....
Dakin ta bude
ta shiga''' tsaye bakin kofar ya yi rike da wayar sa a hannun sa yana haska
cikin dakin....
Cikin fada ya
ce ina kwarton yake ne...
Be Ankara ba sai
dai yaji anbuga masa karfe' a kan sa wanda ya sa ya sa ki uban kara nan take
yafadi akasa tsumamme...
Fulani data
buga masa wannan karfe da taimakon Maman Maryam da saratun suka shigar da shi cikin
dakin...
Kaya suka fara
cire masa '' saida ya saura Daga sai boxer ''
Saratu itama
cire nata kayan ta yi takwanta kasa '' Fulani da Farida suka daura shi saman
Baiwa Saratu...
Nan da nan
Fulani ta fita taje tadauko wani kwarya mai dauke da Jinin kaza..
Ta shigo dakin
dashi...
Abakin Sarkin
Adalai ta zuba masa tare da shafe jikin nasa....
Soma bubbuga
kafafun sa ta yi tare da shafa masa ruwa a fuska '' ganin numfashin nasa na
kokarin dawowa ya sa ta diba aguje tana tsala ihu cikin masarautar.
Ita Ko Farida
nan da nan tabar dakin '' ta yi ɓangaren
Mamy tare da shiga dakin Khadija dan tsafta ce jikin nata.....
Nan da nan
dandazon bayin dake cikin masarautar da jama'ar Sarki da suka shigo da dabbobin
daya basu umarni za a yanka na sadaka..
Dukansu cikin
gidan masarautar suka nufa Gadan Gadan cikin zafin nama....
Tsohon Sarki
Turaki shida uwar gidan sa Mama karama har rige rige suke dan zuwa ganin abun
da ke faruwa...
Cikin gigita
suka nufo inda Fulani ke tsala ihu suka yi tare da Abban Marwan da shima dakin
nasa ya fito..
Cikin Rawar
murya suka ce Fulani meyake faruwa ne jibi yanda kika tara mutane amma kin ki
bayani sai ihu kike kina salati...
Cikin kuka
take kallon su ta ce Sarki Salihu na dade da gayamuku masafi ne baku yarda ba..
Gashi cen
yayiwa baiwata fyade hade da zukan Jinin jikinta nima ihun ta najiyo nazo naga abun
da yake faruwa...
Cikin gigita
tsohon Sarki. Ya ce mu je mugani.
Mamy da Samad
kusan a tare suka nufo wajen Ko wanne cikin hanzarin sa..
Koda aka nufi
dakin Saratun iske Sarki Salihu akayi yana kokarin tashi Daga kwance da yake ''
itakuwa Saratu zaune take gefe tana kuka mai tsuma rai '' tana fadin Sarkin
Adalai menayi maka da zakayi lalata dani' Wayyo jinina daka diba mezakai
dashi...
Cak Mamy da
Samaɗ ɗa Mama karama suka tsaya
kamar an buga musu kusa...
Mamy bakin ta
na rawa cikin kuka ta ce mezan gani Salihu kaine awannan yanayin tana nuna shi
da ya tsaya..
Bakin sa na
rawa cike da mamakin yanayin da yake ciki ya ce wallahi tallahi niban sa abun
da ake zargina akai ba...
Juyowa ya yi yana
kallon Saratu dake kuka ya ce ke Saratu kiyi musu bayanin abun da ya faru
mana....
Sauratu bakin
ta na rawa ta kasa hada idanu da shi cikin kuka ta ce fyade yamun...
Kuma harda
Jinin jiki na ya fara tsotsewa wai kada yarasa mulkin sa..
Samad rintse
Idanun sa ya yi Jin kalmar fyade..
Tsawa ya
dakawa Saratu yana kokarin shako ta '' keee wallahi karya kike.. Nace karya
kike bude mun gaban naki mugani inda ya yi inzali..
Tsohon Sarki
da shima duk yagama yarda da Al'amarin ya ce Kai Samad kanka daya kuwa ya kana
ganin gaskiya kana takewa.....
Yarima Samad
cikin ruwan bala'i dake cin yajuyo kan tsohon Sarki ya ce wallahi karya ne
sharri ne '' in gaskiya ta bude gaban nata mugani....
Mamy dasai
yanzu hankalin ta yadawo jikin nata ta ce '' wallahi nima ban yarda mijina ze
aika haka ba..
Cikin zafin
nama taje zata kamo hannun Saratu..
Mama karama
tarike ta ta ce Habiba dakata abi komai a hankali..
Baba Salihu da
yanzu ya fahimci ashe sharri ne akayi masa kuka ya fara ya ce Saratu '' menayi
miki '' wallahi karya take abu daya nasani shi ne ta ce in taimaka mata akwai
wani a dakin nata...
Koda nazo
banshiga dakin ba Daga waje natsaya daganan bankara sanin abun da ke wakana
ba...
Ni Aljani
Sultan ni ne na shiga jikin Tsohon Sarki da dan sa Sani.....
Tsohon Sarki
da dan sa nan da nan suka ji sauyin yanayi a tattare dasu...
Sani cikin
tafasar zuciya da maganin dake cinsa ya ce '' Wallahi Salihu kabani mamaki kana
sarkin Adalai.....
Shima Tsohon
Sarki ya ce Albasa batayi halin ruwa daman abun da ake fada a kan ka ina karyatawa
gaskiya ne...
Samad ya ce
A'a Sarki kar ka yarda da zancen nasu Sharri ne nace tabude gaban nata kunki
yarda...
Sarki Turaki
cikin jin Haushin Samad da Mamy da suka ki yarda da zancen sai Karima dake
bayan su''' itama kam taki yarda wannan abun gaskiya ne..
Tsawa ya
dakawa yarima da Mamy cikin Daga Murya ya ce inban da iskanci kuna ganin zahiri
kuce karya ne...
Maman Maryam
cikin shigar ta da ta yi na dogon riga karasowa wajen nasu ta yi '' cikin ɗamuwa take tambayar Mamy
wai mêke Faruwa ne..
Mamy shiru ta
yi banda kuka ba abun da take...
Maida kallon a
kan Fulani ta yi suna kashewa juna idanu ta ce Fulani dan Allah gayamin mêke
Faruwa ne..
Fulani cikin
tsananin Tashin hankali ta ce '' Sarkin Adalai ne aka kama yayiwa baiwa ta
Saratu Fyade....
Harda shan
Jinin jikin ta...
Salati Maman
Maryam tafara tana tafa hannu sake da baki take kallon Mamy dake kuka ta ce
Habiba hakan ya faru '' daman nasha gayamiki mijin ki dan kungiyar Asiri kinki
Yarda yau dai gashi gani da Idanun ki...
Marin da Samad
ya yi mata ya sa tafara ganin walkiya har tana neman faduwa '' ba ta Ankara ba
'' sai ji ta yi ya yi mata muguwar shaka '' wanda yajawo hankalin Mamy '' '
Cikin hanzari
taje kwatar yayar ta hannun Samad amma ta kasa...
Saida Abban
marwan ya je Da ƙyar ya banbare ta a jikin sa...
Fulani na
ganin Abun da akayiwa Farida kama bakin ta ta yi ba ta kara fadin komai
ba......
Shiko Sarki
Turaki gyaran murya ya yi cike da takaici ya ce '' Likitar masarautar yazo
yaduba Saratu '' ya bincika shin dagsk ne ya yi mata fyaden kuma ya duba inda
aka dibi Jinin nata....
Sossai
hankalin '' Fulani da maman Maryam dake numfashi sama sama '' dan ba ƙaramin
shaka Samad ya yi mata ba....
Likitan
masarautar yana zuwa ya fara bincike sossai cikin aikin nasa '' ya ce sai nan
da Awa biyu result ze fito...
Gabadaya Fadar
Sarki aka hallara dan jiran sakamakon wannan Abun da ya faru...
Mamy zaune
take ta yi uban tagumi tana jiran yanda za a kaya.....
Sarkin Adalai
dake gefe zaune kukan zuci yake yi sossai yana ayyana Abun da ze faru.....
Likitar
Masarautar koda yadawo da Result din wajen yi gwaji nine nan Aljani Sultan na
canza result din na maida shi positive....
Koda result ya
fito yaga Positif sossai hankalin sa ya tashi babu damar ya canza ya ce negatifs
ne a je wani Asibitin aka sabanin nashi....
Cikin Rashin
kuzari ya mikawa Sarki Turaki result din...
Sarki na
budewa yaga positive Salati yasoma ya ce Salihu Allah yatsine maka Albarka
Allah ya tarwatsa ka '' 'Allah yahana gaban ka yin kyau ya hadaka da tsautsayi
da hasara....
Sarkin Adalai
cikin kuka da yazo masa ya ce Nina San sharrine a kamun babu me yarda dani sai
mutum uku kacal' 'Mata ta sai ɗana'
'sai baiwar sa...
Ya Abbana ka
fahimce ni wallahi ban aikata ba.....
Mama karama
dake kuka ta ce nima nasan ba ka aikata ba.
Fulani da suka
ji dadin abun ita da mijin nata da maman maryam' 'murmushi suka yi....
Baba Salihu
tashi Daga zaunen ya yi ya ce ni Salihu Daga yau na sauka Daga kan karagan
mulkin nan..
Kuma na
damkashi a hannun Abbana'''..
Yau zan bar
Masarautar nan....
Sarki Turaki
dake masa kallon Azzalumi cikin Tsawa ya ce za ka iya tafiya amma babu inda za
ka je da Mamy dan bazata bika ba.
Yayan ka ma
babu wanda ze bika kai kadai za ka tafi kaje kaji da mugun Aikin ka
Mamy cikin
kuka zatayi magana Sarki Turaki ya dakatar da ita ya ce Habiba babu inda zakije
da wannan mushurikin....
Baba Salihu
cikin zafin nama ya yi hanyar dakin sa yana kuka duk wasu abu dayasani masu
muhimmanci ne a tattare da shi ɗuk
ya dauko su.....
Ta bayan gida
ya fi ce dan Sarki Turaki beyi tunanin shin dagaske yake ba a kan zebar gidan
ba...
Tura dogarai
ya yi a je aduba me yake yi ne a daki dan gidan kurku '' za a kai sa nan zeyi
shekaru uku..
Sannan ya fito
koda suka dudduba dakin wayam suka gani babu Sarkin Adalai aciki
Labari yajewa
Sarki a kan ya gudu Sarki ya ce dan iska ya san mugun aikin da ya aikata ba zai
iya hada idanu da Al'umma ba...
Wannan shi ya
tabbatar mana ya gujewa hukunci ne...
Labarin Ankama
Sarkin Adalai yana yi wa baiwar matar kanin sa Fyade yakara de duka duniyan
hausawa harda turawa dan Shugaban Kasa na saudiya saida ya yi magana a kan haka
ya ce cin Amana ne ''Sarki ya cutar da nakasa dashi....
Duk cikin
kwatanon duk inda ya je maganar sa ake yi gidan TV gidan redio kasa zama kasar
yayi' '' tare da tafiya kano gun neman Wani malami Ko ze samu mafaka agidan
nasa.........
Tun da Daga
wannan Ranar Saratu ta shiga tashin hankali sam ba ta da nutsuwa inta kwanta
barci abun tsoro da mugun mafarkai ke hanata barci...
Zuwa ta yi tasamu
Fulani ta ce wallahi nayi nadamar abun da na aikata tun daga ranar sainayi
Mafarkin Sarkin Adalai yana kuka yana fadin Saratu kin cuce ni...
Yana fadin
Saratu zaki girbi abun da kika shuka....
Fulani. Ta ce
karta damu zata daina '' amma shiru abun sai gaba yake yi sai tana barci sai ta
ji ana kama kafafun ta '' tana ihu tana fadin me nayi muku ne....
Akarshe ta
yanke shawaran zata fallasa sirrin su..
Fulani data
Samu labari ta aika a kashe Saratu '' labari yazo m'a Saratu a kan kisan da
akace ayi mata hakan ya sa tabar gidan taje gidan wata mata tabuya....
Tsawon wata
uku...
Rahamatullah
anan na kawo karshen labarin abun da nasani ina fatan ba za ki dauki mataki
akaina ba.
Bisalam Daga
Aljani Sultan....
Sossai wani
zufar wahala ya ketowa Samad da Rahama kusan a tare suke kallon juna suna
kallon takardan
Yarima Samad
tashi tsaye ya yi hannun sa rike da takardan ya ce uhmm Rahama ke Jaruma ce..
Kin jure
gwagwarmaya akaina ga wani yanzu kindakko wannan karan tare zamuyi meye mafita
Rahamatullah ke nake sauraro..
Tare da dafata
'' kallon sa take cikin kunan Rai ta ce Ancuci Sarkin Adalai bazamu kyale su
ba..
Dole mu ɗau Fansa..
Yarima ya ce haka
ne yanzu lokaci ya yi da za su gane kuren su ina case dayawa agaba na..
Amma case din
Saratu shi ne babba ita ce lomar farko...
Rahama ta ce
bayan Saratu waye agaban naka...
Bakin sa na
rawa ya ce..
Marwan da
Salma...
Cikin Rawar
Murya ta ce Salma kuma kardai kace ƘANWATA...
Kwarai kuwa
kanwar taki yanzu ba lokacin maganar ta bane '' yakatse zancen da neman mafita
a kan Saratu.....
Tunani
yashigayi sossai '' cikin tabe Baki ya ce nasan wani Soja A buja babban soja
ne. Mataimakin shugaban kasa ne...
Rahama ta ce
'' ya sunan shi Ko wannan sojan nan mai rikon gaskiya da Amana wanda ya yi fice
a kan harkan bincike da bin diddigi '' Yusuf Sani Yaro...
Yarima Samad ya
ce kwarai kuwa shi nake nufi '' zan masa magana a kan Saratu '' yana zaune a
abujar zeyi komai tun da tana nijeria tazo gidan sauki....
Rahama ta ce
gaskiya kasa shi agaba dan wanda yakama mahaifin sa '' a kan laifi to ka ga ba
zai yi shayin kamo mana Saratu ba..
Cike da
jinjina Al'amarin Ya rungume Rahama yana kuka ya ce Rahamatullah tun ranar
danayi tozali da mugun abu a kan mahaifina adaren ranar ne nafara mafarki a kan
ki Rahama....
Cike da zare
idanu ta ce Amjad kamarya kenan dan fahimtar dani yanda zangane......
Rahma a wannan
Ranar nafara ganin ki a mafarki na kina zuwa min fuskar ki dauke da nikabi'''
kullum abu daya kike faɗa
min shi ne in yi hakuri da jarabawa zanyi nasara...
Kullum faɗa min kike Amjad ina son ka
'' ina son ka amma akwai tazara a tsakanin mu...
Niko nace dan
Allah meye tazarar sai kika gayamin A mafarkina tazarar b kasa daya muke ba ''
idan zan iya inzo kano neman ki '' kuma mahaifina yana cikin garin kanon kusa
da wani shahararren malamin Addini..
Koda naje kano
duk inda nasan manyan malamai sainaje neman sa. Amma babu nasara...
Ajiyar zuciya
Rahama tasauke ta ce Amjad '' Iskar dake tare da kai ita ce take nuna maka
hanyoyi acikin mafarkin ki ita ce take zuwa maka da suffa ta dan tasan lallai
zamu hadu kuma zamu zama mata da miji tasan tare nida kai zamu kawo karshen duk
wani makirci shi ya sa ta yi amfani da wannan damar tun ranar data bude maka
idanu a mafarki da fuska ta ka kara ganin ta??
Girgiza kai ya
yi ya ce Ah Ah bankara ganin ta ba...
Uhmmm tun da
Daga Ranar Burin ta yacika shi ne tabar jikin ka tabar rayuwar ka tadau
Alwashin taimaka maka ne bisa zaluncin da taga anshuka muku ta turo ka gareni
ne dan mu taimaki Sarkin Adalai....
Yarima Samad
jinjina Al'amarin ya yi ya ce nayarda da bayananki hubby na wai ya akayi kike
ganin Aljani bayan mu bama gani...
Murmushi ta
sakar masa wanda yake sanya ya m'asa zuciya...
Amjad kakana
Sheik Kabeer Hizqeel Makarfi shi ne wanda yake ba ni sirrin abubuwa da makaman
su' ɗa kariyar su...
Duk sanda zamu
hadu sai ya koyae dani abun da mahaifina be koya mun ba...
Ita Salma Sam
taki maida hankali''' ka ga nida Abubakar da Abdul jalil mune muke daukan
darusan da yake koya mana...
Tun ina gida
ake kawo mun irin yaran mata da Aljanu suka aure su..
Da waɗanda iska ke damun su...
Ninan Rahama
ana kawo mun mara lafiya daga wata kasa dan neman magani a kan warware sihiri
Ko muguwar cuta.....
Ina ba da magani
da ayoyin Allah kuma Alhmdulilah ana dacewa dan abun ba dagani bane Daga Allah
ne '' kuma Nice sila..
Amjad tun da
nataso agidan namu bansamu shakuwa irin ta uwa ba..
Anty ita ce ta
zame min uwa ita ce ta zame tamkar uba na.. Duk da mahaifina yana kula dani...
Da karatun
mu..
Anty ta koyar
dani Addini da koyamin yanda zan mu'amallanci mutane..
Ta koya mun
yanda ake zama da miji tun ina karama...
Agidan mu
Salma ita ce babban matsalata ina son ta sossai kuma har gobe ina sonta...
Matsalar da
Aka samu mahaifiyar mu batason ganin laifin Salma a kan ta zata bugeni '' Salma
tana iya fadin abu wajen ma maman mu kuma maganar ta zauna kenan babu wanda ya
isa ya ce ba haka bane...
Salma ita ce
silan raba aurena da Adamu da za a daura '' wanda yakawo mai Martaba ya karbar
maka aurena...
Hakan na dauke
shi a matsayin kaddara sai gashi nasamu wanda nafi so game da komai sai yanzu na
tabbata Adamu kaunar sa nake a lokacin...
Kaine ainihin
wanda nakewa pur love Amjad......
Farkon
haduwata da kai tun daga ranar nakasa sukuni '' duk da bawai na gane ainihin me
nakeji a tare da kai bane......
Zagin da kai
mun na rashin kamun kai shi ne ya hanani barci...
Kayaita ceen
murmushi ya yi saida kuncin sa ya lotsa ya ce Rahamatullah '' ranar na ji bakin
ciki ganin ki da wannan Adamun hakanan na ji kamar in shake shi...
Nikaina na
dauka rashin kamun kai ne ya sa na ji haushin ganin ku...
Saida ga baya
nagane ashe kishi nake yi....
Sossai suka ɗara har lakuta mata hanci ya
ce Uhmmm shi ne nace mun a airport Ko...
Uhmmm na nace
maka koka nace mun harda wani ɗanne
fitananne kawai tana murguda baki....
Bawani Fitina
kice kinsha dadi '' dariya ta yi sossai saida fararen hakoran ta suka bayyana ta
ce uhmm kaida ka afkamun amma ka tashi kanata zuba ruwan masifa harda wani ka
fasa tafiya ka san a ranar bama ka isheni kallo ba....
Uhmm inban
isheki kallo ba aina ishe Salma Ko...
Tun da suka
dauki hoton mu sanda muke kwance a wayar Marwan.....
Cikin zazzare
idanu ta ce hoto kuma.........
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.