Ticker

6/recent/ticker-posts

Ƙanwata Na Ikilima Adam (Kashi na 2)

Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Allah kasa yanda na fara lafiya in kare shi lafiya. Wannan labarin ya faru da gaske dan kusan Book dina da nake yi true life ne sai dai in yi masa kwaskwarima dan abun ya fi ba da citta.

Ku biyo ni ku sha labari.

Ku daure ku yi comment dan in ji ra'ayoyin ku a kan Littafin nan......

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa}_

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

Marubuciyar

* Amince Da Ni
* KAI KA JA WA KANKA

Yanzu kuma gani ɗauke da

ƘANWATA

Paid Book ne

Vip 300
Special 500

Acct No. 3115484026, First Bank, ko kuma Kati MTN (Ba na son VTU)

Idan kin biya ta bank kina iya turo shaidar biyar ki ta wannan 09069080725

kanwata

🌟🌟 ƘANWATA Na Ikilima Adam [Kashi na 2]🌟🌟

Rahama zaune suke ita da asiya a dakin Mama.

Cikin damuwa Rahama ta dafa asiya ta ce kawata kin san Ko har yanzu baba salihu be dawo ba.

Cikin zazzare idanu Asiya ta ce whattt ban....

2️3️

Asiya ta ce What

 banganeba Rahama wai kina nufin har yanzu bedawo ba chabdi amma saina ke ganin da Adamsy akaba auren naki zefi kwanciyar hankali kinga yana mugun son ki.

Rahama kema kina son sa.

Ajiyar zuciya Rahama tasauke ta ce ni fa banda zabi wanda yawuce na iyayena komai sona da abu komai kin abu danake yi.

Amma wlh Asiya da so samu ne in auri Adamsy.

Zuciyata tafi aminta da shi dari bisa dari.

Abba dake tsaye kofar dakin mama duk abun da suke fade a kan kunnen sa.

Cike da tausayin Rahama yabar wajen.

Yana shiga dakin sa ya shiga nazarin yanda ze bullowa Al'amarin zuwa yanzu ya gama sarewa a kan dawowar baba salihu.

Anty yakira awaya ya cemata tazo dakin sa ta same shi 'babu ba ta lokaci sai gata tashi go sanye take da doguwar riga Atamfa takashe daurin dankwali sai kamshi take zubawa

Barka da warhaka baban Rahama.

Ta furta fuska a sake.

Fuskar sa babu walwala ya amsa mata.

Shigar ta ba ƙaramin daukar hankalin sa ya yi ba.

 ba ta izinin zama yayi.

Zama suka yi yana fuskantar ta ya ce nayi tunani a kan Rahama nalura baba salihu ba dawowa zeyi ba.

Allah kadai muka barwa sanin gaibu.

Kuma kinga yarinyar nan ta mana biyayya a kan amincewa zata auri dan baba salihu ba tare da ta san shi ba.

Nayanke shawarar bawa Adamsy auren Rahama koya kika gani ?

Anty cikin murna ta ce wallahi ni hakan ya yi min dadi sossai ka ga ka taimakawa masoya.

Wani hanzari ba gudu ba koda Baba salihu yadawo zan ba dansa diyar Hassan kanina.

Shi ne kawai kwanciyar hankali na kuma mutanen nan yanzu zankira su in sanar musu kawai su kawo sa daki na basu Rahama dan haka ki gaggayawa mutane makota araba alawa daurin aure ranar juma'a.

Itakuma salma nata me sauki ne dan saurayin da suke tanbadewa tare shi zan hadasu aure.

dan uban sa koyanaso Ko baya so sai ya aure ta.

Cike da farinci anty ta ce hakan ma ya yi bara in tafi in sanar cikin gida.

Cike da farin ciki anty taje tsakar gidan tana ta guda.

Kowa saida ya fito har bakin da suka fara zuwa Daga makarfi sun fito.

Mama ta ce wannan gudar fa na mene ne.

Salma ta ce uhmm tana murna ne Yar dakin ta zata auri dan me gadi.

Dariyan mugun ta ta yi tana me kallon anti.

Maganar tayiwa Rahama da Asiya zafi aransu..

Anty kara yin wani gudar ta yi ta ce MashaAllah MashaAllah tana dafa Rahama ta ce congratulations my daughter tare da rungume ta sassanyan kiss ta yi mata a goshi.

Ta ce yau Allah ya amshi rokona Rahama.

Mama da ranta yasoma baci ta ce to ai saiki fadi abun murnan muji.

Anty ta ce nasan mama zakifi kowa farin ciki gashi yau Abba yaba Adamu auren Rahama.

Kwabe fuska mama tayi.

 ta ce ba shakka abun farin ciki ne Allah ya sa ayi damu Daga haka ta kama gaban ta.

Wani farin cikine ya lullube kowa cikin gidan duk wanda ya san shakuwar Rahama da Adamsy ya san akwai tsantsar soyayya.

Rahama kasa boye farin cikin ta ta yi dukawa kasa ta yi tayiwa Allah sujjada.

Tare da dago kai gaban kowa ta ce Allah ina godiya agareka.

Rungumar anty ta yi tana murnan farin ciki.

Salma tun da ta ji maganar wai Adamsy ne ze auri Rahama hankalin ta ya yi mugun tashi.

Kasa tsayuwa ta yi cikin kuka tashige daki ta danne kanta da filo tana kuka mai taba zuciya.

Rahama ta lura da yanayin salma sai ta ji tausayin ta yakamata bin bayan ta tayi.

Ta iske ta tana ta rusa uban kuka jiki asanyaye ta Haye gadon jawota ta yi salma na turjewa.

Cikin yanayin damuwa Rahama ta ce salma ke kadai ce ƙanwata ya mace pls meyasa ba za ki soni ba koda kadan ne wlh salma ina son ki fiye da komai banda iyayena.

Banda kamarki.

Salma dago kai ta yi tana me Jin tsanar Rahama nakara ruruwa acikin zuciyar ta.

A fili murmushi mai kama da ciwo ta yi ta ce ayya kukan da nake kaina ke min ciwo karkiyi tunanin wani abu cen ka san ranta tana ayyana yanda zata tozarta Rahama a fili kuma murmushi yake ta yi mata wanda hakan ya sa Rahama Jin dadin sun fahimci juna ita da kanwar ta.

Rahama na fita.

Salma hijab dinta tasaka ta bayan gida tafita ba tare da kowa ya sani ba.

Direct gidan Amina taje ta iske ta awaje wani me mota ya sauke ta.

Tana masa bye bye.

Aguje taje ta rungumi Amina cikin kunan rai take ba ta labarin auren.

Amina ta ce zancen banza zancen wofi wai ina maganin da malam isa yabaki kinkoyi aiki da shi kuwa.

Salma Girgiza kai ta yi Alamun A'a

Amina cikin fushi ta ce meyasa salma kodan bakisan zafin kudi bane.

Insa kudi masu yawa in biya miki dan biyan bukatun ki

Amma kika ajiye bakiyi ba yanzu me kike son in yi miki tana kallon salma ranta a ba ce.

Salma hakuri tasoma ba ta ta ce wlh dan naga Abba ya ce dan me gadi zata aura shi ya sa banyi ba.

amma pls miye mafita karki manta yau saura kwana shidda na ji Abba na cewa wai Al'amin ze aura min kijifa.

Tana yatsine fuska.

Ina aiba zan iyaba dan ambassador zata aura fa ni kuma in kare da yaron dako sana'a bashida shi.

Amina ta ce yanzu inbaki komi mu je gun malam isa.

Haka suka kwashi juna suka je malam isa yaba salma maganin da zatayi tozali da adamsy inhar suka hada idanu tabbas zeso ta inkuma be sota ba alokaci to duk abun da tafadamai a kan Rahama ze yarda koda karya ne.

Murmushi kwance kan fuskar salma ta ce ai gwara mu rasa dukan mu wallahi itama anemi Ko me ga ruwa ne abata ta aura ehee tana hura hanci sama sama

Cike da Jin dadi suka baro wajen malam isa.

Tun da salma tadawo gida take ta safa da marwa yanda zata hadu da Adamsy kawai take tunani

Iyayen Al'amin sunzo sheik cikin mutuntawa ya karbesu dan mutanen arziki ne.

Gasu makotan arziki.

Sheik be fadama musu abun da yaron nasu yake aikatawa ba shida salma Saboda ya san rufa asiri ɗan Adam yana da cikin kyakkyawan dabi'un mutanen kwarai.

Al'amin dake tsunkuye da kai tsoro da fargaba ne yakamashi kada a tona masa asiri.

Sheik cikin gyaran murya ya sanaar da Iyayen Al'amin diyar shi salma ta ce babu wanda takeso sai Al'amin.

Gaban Al'amin saida ya yi mummunar faduwa azuciyar sa sai maimaita innaliahi wa'inna ilai rajun yake.

Me zanyi da salma wacce ba ta da kamun kai dadai yayar ta ce amma anhadani da alakakai.

Cike da farin ciki da Jin dadi Iyayen sa suka ce sun amince tun da ya ce beson komai sai sa daki suka nemi Alfarma koda andaura Salma tazauna na kwana biyu kafun su nemi inda za su tare da mijin nata.

Sheik ya ce babu matsala wannan ai munzama daya..

Al'amin gaza magana ya yi dan yana tsoron ya ce wani abu Abba ya tona masa asiri.

Daga haka suka yi sallama da Iyayen Al'amin jiki babu kwari Al'amin yakoma gida....

....

Kannen anty suka zo sunyo ayari dan tayata murna zata aurar da yarta Rahama.

Kanwar anty tazo da kayan gyaran amare masu kyau su turaren wuta humra dilka.

Sossai anti ta yi farin cikin gudumuwar da suka kawo.

Dakin baki aka sauke su.

Aranar Rahama saida tasha gyaran jiki gun kanwar anty

Salma Sam taki yarda ai mata gyaran jikin saima tarufe su da masifa.

Dole suka kyaleta.

*******

Adamsy labari ya je masa anbashi Rahama murna awajen sa baya misaltuwa.

Shago ya je yasiyo sabuwar wayar Samsung galaxy edge 7 yakawo mata hade da layi ranar sun sha hira ta waya.

Cikin farin ciki ya ce Rahama kinga ikon Allah Ko Allah ya ce ke matata ce gashi saura kwana shidda a adaura wayyo zan zama baban baby

Nakosa inzama Daddy nima.

Kunya yakamata

Hannayenta tasa tarufe fuskar ta kamar yana ganin ta

Cikin zazzakar muryan ta ta ce adamsy na.

Idanun ta a lumshe wani ni'ima da kwanciyar hankali suka ziyarci zuciyar ta lokaci daya.

Allah ya yi zan zauna kar kashin inuwar ka ina mai godiya ga mahallicina.

Wani hawayen farin ciki ne ya lullube fuskar ta.

Adamsy dake jinsa a sabuwar duniya ya ce kinga bara inkashe kin san tun da su Daddy suka samu labarin anbani ke zama be gansa ba.

Yanata gayyatar manyan mutane Daga kasashe.

Cikin su harda sarkin kwatano zezo daurin auren mu..

Rahama banda dariya babu abun da take ta ce aini ma nan Abba ya gayyato manyan malaman addini na kasashe ketare dana cikin gida Nigeria harda abokanan sa larabawa da suka yi zaman saudiya duk za su halarci taron.

MashaAllah Adamsy ya furta ya ce lallai ranar juma'a akwai kallo.

Daga haka suka yi ta firan su cikin nishadi.

Ta sanar masa gobe za su je makarfi amma kwana biyu kacal zasuyi ba haka yaso ba amma ya ce Allah yakaiku lafiya zamu ringa waya.

Kinga saida safe zan kira Daddy ne kan lefen auren ki Kin san babu jira lokaci yakure.

Daga haka suka yi sallama.

********kwatano

Mai martaba zaune shida mama karama ya sanar mata bikin da za su je ranar alhamis bikin dan Dr Abdullahi Auwal ne.

Mama karama cikin Jin dadi ta ce tome zehana in bika tun da nima ban taɓa zuwa kanon ba.

Kuma zanga maigidana yarima Samad.

Inga Ko akwai wacce zata iya ta kwace min shi.

Tana dariya mai martaba ya numfasa ya ce ki shirya mu je ranar Alhamis kinga tare da Samad zamu dawo dan yana da zama kotu ranar litinin anan garin namu.

Cikin gamsuwa da bayanan sa ta ce Allah yakaimu.

********

Yarima Samad zaune yake a falon sa.

Hannun sa dauke da remote.

 Faruk yashigo hannun sa dauke da leda ya ce kanada masaniya mai martaba zezo bikin dan Ambassador shida mama karama.

Waziri ze rakosu.

Samad da hankalin sa ke kan kwallo da ake bugawa A TV ba tare da ya kalle sa ba ya ce inada masaniya ai duk tare zamuje daurin auren.

Nuna masa kusa da shi ya yi ya ce ka ga wannan shaddunan anko zamuyi nida ku abawa telan nan dake mana dinki kai ka san wanda za amin tun da daurin aure zamu je.

Ka san dole muyi kara dan uban angon tun muna yara yake zuwa kwatano gidan mu yake sauka akwai shakuwa sossai tsakanin sa da mai martaba ka ga dole mu zage.

Aminu dake gefen sa kwance kan kujera 3str ya ce gaskiya ne yarima Samad Allah yakaimu

 Da Amin suka amsa dukan su banda marwan da ransa yake a ba ce.

********

Washe gari

Salma tana ta tunanin ya zatayi ta hadu da adamsy ne gashi yau za su je makarfi.

Wata dabara ce tafado mata gun Rahama taje cikin murmushi ta ce anti wai ina yaya Adamsy ne.

Rahama ta ce ai yanzu zezo Wayar ta yasoma ring murmushi ta yi ta ce kinga salma gashi cen yazo yana waje.

Aguje Salma tabar Dakin.

 Dariya Rahama ta yi dan a tunanin ta salma tasauko tana kaunar farin cikin ta.

Salma daidan wajen zauren gidan su ta tsaya tana.....

 

2️4️

Ta tsaya tana kokarin fiddo maganin Daga jakar ta.

Abubakar da buta ke hannun sa ya fito toilette sake da baki yake kallon abun da take shirin yi.

Tsayuwar sa ta ji a kan ta ba ƙaramin firgita ta yi ba har tana neman faduwa.

Azabure tana sakalo murmushin dole ta ce yaya kaine cikin muryan ta dake rawa.

Kallon yake yana nazartan yanayin ta ya ce au baki ganni ba tun dazu me kikeyi ne.

Me wannan a hannun ki

Cikin inda inda ta ce tozali nane nake dubawa Ko yana nan.

Sai anan zaki duba ya jefo mata tambaya.

Yana mai tsareta da idanu.

A'a yaya kawai de inadubawa ne.

OK to ina zakije ne ?

Yaya adamsy ne yakirani zanje mu gaisa yanzu zandawo ba tare da ta jira amsar shi ba tafita jiki na rawa.

Tana fitowa kofar gida ajiyar zuciya ta soma saukewa ta ce azuciyar ta.

Da wannan uban nacin yaga abun da zanyi shi ke nan daya tonamin asiri gashi ta dalilin shi bansamu nayi ba.

Oh my God ta furta ta dunkule hannayen ta tabugi iska.

Adamsy dake tsaye jikin motar sa yaci kananun kaya sanye yake da wando jeans riga teashot hash kala ba ƙaramin kyau ya yi ba sajen shi kwance lub a fuskar shi.

Da fara'a dauke a fuskar shi yake kallon salma ya ce ya na ganki a birkice haka.

Kaman wacce ta yi wasan gudu.

Haushin shi ta ji danma ya raina mata wayau ita ze fadawa haka.

Karasowa gaban shi ta yi ta ce yaya na ai antina ce muke rige rigen waze fara ganinka.

Dariya ya yi ya ce ai ita basai ta yi rige rigen ganina ba.

Dan zamu ka sance tare na har a bada.

Kekuma Al'amin zakiyiwa wannan tseren dan kiga fuskar abun ki.

Koba Al'amin na ji ance sunan shi ba.

Yana kashe mata idanu cikin tsokana..

Salma ranta yakai kololuwa wajen baci ta ce ayya haka ne kuma ai shima Al'amin din yanzu ze zo.

Jiki asanyaye ta ce ni zanshige Girgiza mata kai ya yi yana kallon ta harta shige.

Baza idanu ya yi yaga ta inda tauraruwar sa zata Bullo.

Yayin da iska take busowa yanajin shi cikin shauki da begen abun son sa.

Cike da nutsuwar ta da kasaitar ta ta fito kamshin turaren ta ya doki hancin sa.

Sai asannan yadago kai yake kallon ta babu Ko kiftawa.

Sarki ya tabbata ga ubangiji kyakaywa.

Murmushi ta yi cikin girmamawa ta gaishe shi.

Kasa cire idanu ya yi a kan ta saida ta soma tsarguwa da kallon da yake binta dashi.

Turo baki ta yi gaba ta ce wannan kallon fa.

Murmushi ya yi ya ce mene ne dan na kalli fuskar matata.

Uwar yaya na ?

Girgiza masa kai ta yi ta ce babu laifi amma ka rage.

Kallon shigar da ta yi yake yi.

ya ce gaskiya dole inbiya wankan nan.

Sanye take da abayas doguwar riga egyptien yasha stonne gaba da baya ta yi Rolling dankwalin a kan ta.

MashaAllah ya furta tare da dauko wayar sa ze masu selfie.

Yayi juyin duniya Rahama ta ce Sam baza ta yi hoton ba.

Beji dadi aransa ba amma ya dake ya ce idan kinzo gidana zanga tayanda zaki hana muyi hoto.

Dariya ta yi mai sauti ba zan dade ba ka san yau zamuje makarfi so muke mu je dawuri.

Adamsy ya ce Ko zaku bari ni inkaiku ne.

A'a kabarshi drever Abba ne zekaimu jibi ze koma yadauko mu.

Bandir din dubu daya yabata da ƙyar ta amsa tana mai masa godiya.

Sunkai mintina goma

Kafun suyi sallama Cike da begen juna.

**, ********

Salma tana shiga daki kuka tasaki mai cin rai ta ce yanzu shi ke nan burina ba zai cikaba wata zuciyar ta ce ai zecika tun da jibi zaku dawo ana saura kwana uku daurin aure.

Murmushi ta yi ta ce ai har yanzu ina nan a kan bakata wlh dan saina wulakanta ku.

Zan auri Al'amin InshAllah Rahama saide a daura auren naki da dan gamai ruwa na miki alkawari ni salma abdurrazak zansaki kuka ranar daurin auren ki.

Badainiba shibanda munafukine adamsy nifa ya fara gani ya biyo dan yahada ido da mai farar kafa ya ce ai ita ya biyo.

Cijje labban ta ta yi ta ce mu je zuwa wanda ya fasa badan halak bane.

Shegu taron matsiyata har ita anty.

Sallamar Rahama ne ya katse mata surutan da take yi..

Cikin Jin dadi Rahama ta ce salma kinga kudin da adamsy yabamu.

Murmushi dole salma ta yi ta ce kai amma wannan adamun yana mugun ji dake Rahama.

Eh wlh Rahama ta furta yi maza ki dauko mana jakar kayan mu.

Abba ya ce mufito mu ake jira bara inshiga ciki muyi sallama da su mama da anty tare da jama'ar gidan.

Tana fita.

Salma ta rinƙa watso mata harara Jiki asanyaye tadau jakar kayan nasu ta fito.

Rahama saida tayiwa kowa sallama suka bisu da Adu'ar Allah yatsare hanya.

Mama ta ja salma gefe ta ce karki damu yata ai Al'amin dinnan ya yi degree yana samun aiki zaki Faso gari yata karki damu shi Adamun beda halin kirki iyayen sa 'mutanen banza ne.

Banda bauta babu abun da Rahama za taje yi a gidan.

Murmushi salma ta yi azuciyar ta fadi take kema mama mai farar kafa tasiye ki..

To wlh koda yar aiki zata je yi giɗan Adamsy ba zan bari ta aureshi ba bare zaman aure.

Afili ta ce Ayya mama karki damu ni tun yaushe ma nacire tunanin adamsy araina.

Mama Cike da Jin dadi salma tasauko ta ce Allah ya yi maki Albarka da amin ta amsa.

Mama ta dan canja ne tun da mahaifiyar ta takira ta awaya ta zageta tsaf ta nuna yakamata ta jawo Rahama a jikin ta.

Kishi da anty zatayi tacire yarta aciki dan suna tarayya da anti.

Da wannan fadar da akayi mata tafara son yar ta har tana hira da ita.

Tana kokarin taga taraba anty da Rahama amma Sam anty taki ba ta dama intai maganar ai yar ta ce sai anty tabata amsa da ita ce ta raineta tun tana karama kuma anbata ita aure kadai ze rabasu da Rahama..

Rakiya suka yi masu har sheik shima baa barshi a baya ba 'suna kallon motar tasu ta tashi sai Daga masu hannu suke suna fadin Allah yatsare.

Gidan gabadaya Cike da kewa suke tafiyar Rahama dan ba ƙaramin sabo suka yi da ita ba.

........

Asiya hannunta dauke da din kuna Cike a leda tazo Cikin girmamawa tagaida jama'ar gidan.

Kallon mama da anty ta yi tarasa wa zataba din kunan acikin su..

Tana gudun ta yi laifi dan tasan zaman da suke yi..

Murya cen kasa ta ce anty gashi Rahama ta ce a baki ki ajiye mata..

Asiya na kokarin mikawa anti mama ta taso ta ta kwace kayan ta ce banda shishigi kayan Rahama ai ni zan ajiye mata..

Anty ta ce Asiya kindai kawo sako Ko kina iya tafiya mun gode.

Asiya ta juya tana ta girgiza kai.

***************

Kan hanyar su ta makarfi sunyi nisa sossai dan ma befi nan da mintuna a shirin ba suka sauka.

Cike da kwarewa drever ke tukin motar.

Rahama tuni barci ya yi awon gaba da ita 'banda kallon ta babu abun da salma take yi.

Tana tunanin yanda zatayi tunowa ta yi akwai kudin da adamu yaba Rahama dasu ta taho ahankali tajawo jakar a kan kafafun Rahama durkusawa ta yi acikin mota Saboda kada drever ya hango ta tacikin madubin mota.

Kirga kudin ta yi taga dubu hamsin ne sabine kudi ne Daga gani a banki ya ciro su.

25k ta zara cikin jakar tare da saka wa cikin brezia dinta.

Komawa kan kujerar mota ta yi tana kokarin maida jakar Rahama inda ta dauke su.

Rahama da batasan wainar da ake toyawa ba..

Har suka iso tana ta barci.

Cikin barci salma ta rinƙa bugun ta tashi anty mun Iso.

Idanun ta tasoma murzawa tana bude su ahankali mika tasoma hade da hamma.

Idanun ta sun nuna tasha barci a mota.

Suna shiga gida sunsha tarba mekyau wajen matar kakar su.

Gidan iyayen sheik suka fara sauka nan nan da su tai ta yi dasu matar kakar su.

Abinci me rai da lafiya ta girka musu.

Da yamma sheik kabeer yashigo Cike da fara'a ya ce yau wa nake gani kaman amare na.

Rahama ta ce aisune tun da kishi yahanaka zuwa kanon ganin mu.

Kallon salma yake ya ce uwar miskilan ci haryanzu kin saura da halin ki 'Allah yataimaka ba ni ne zan aure ki ba.

Danni kam nayafe mishi Al' amin din.

Dariya salma ta saki harda shewa ta ce na ji din dandai ka san ba samu zakai ba shi ya sa kace ka yafe.

Sunsha hira sossai da kakan su.

*******

Bayan sallah magrib Salma na idar da sallah ta cewa Rahama bara inje shago insai wani abu.

Da to Rahama tabita da shi taci gaba da azkar din ta.

Salma tana fita shagon siyar da waya taje.

Mai shagon cikin Jin dadin ganin salma dan sun San Juna washe baki yake ya ce yau kune a gari.

Murmushin salma ta yi ta ce ai yau ma dalili yakawo mu ka san mutumiyar ka ranar juma'a daurin auren ta.

MashaAllah MashaAllah amma Ko ina taya mijin daze aure ta murna dan wlh ya yi babban kamu yarinya so silence ga kyau ga ilimi ga tarbiyya.

Salma cikin dakiya ta ce haka ne dan walwalan ta yarage Jin yanda yaketa yabon Rahama.

Mai shagon ya ce bismillah zauna ke kuma yaushe zakiyi auren ne.

Sai ranar da Allah ya yi ta ba shi Amsa.

Allah yakawo lokaci yafurta mata.

Kallon wayoyin shagon tashiga yi ta nuna masa airtel touch yadauko mata.

Kallon wayar take tana tambayar sa Ko Android ce.

Ya ce kwarai kuwa ita ce ga kyau ga rikon caji...

Farashin sa 20k ne.

Bata nemi ragi ba tasai wayar tare da siyan layi mai rajista.

Saida ta tabbatar komai normal na wayar tasa yatura mata whsap..

Bata bar shagon dako kwandala ba.

Duka kudin ta kashe gun saka Kati.

Lalubo Katin marwan ta yi acikin brezia tare da daukan nombar sa.

 Tasa wayar ta.

Kira ta danna masa wayar tana ta ring ba a daga ba..

Kusan mis call shidda ta yi masa.

Be Daga ba

Tana kokarin shiga gida ta ji wayar ta soma vibrer.

Alamun kira yashigo.

Komawa da baya baya ta yi tashige wani lungun layin su.

Ta Daga Daga can ɓangaren ya ce dawa nake magana ne naga mis call..

Murmushi salma ta yi ta ce kako gane ni kuwa.

Nice wacce mu kazo airport nida yaya ta.

Har suka fadi ita da uban gidan ka.

Bakaine kadauke su hoto a wayar ka ba.

Oh oh oh nagane ki yabata Amsa tun lokacin naita tsumayen ki sai yau kika neme ni.

Ajiyar zuciya salma tasauke cikin sanyin murya ta ce dan Allah wannan hoton daka dauke su yana nan a wayar ka kuwa.

Marwan dariya ta subce mishi ya ce to ita wannan me za ta yi da hoto kuma dukan Alamu ya nuna wacce ya gan su tare yayar ta ce.

Akwai tsatsar kamanni da suke yi.

Amma tafita kyau sossai dan baza a hada ba.

Dawo da shi Daga duniyar tunanin daya fada ta yi ta ce kayi shiru koka goge ne ?

Ban goge ba turon lambar ki ta whsap inmiki send dinsa yanzu.

Wani tsalle salma ta yi ta ce ai da wannan nombar nake yi inajiran ka.

Babu ba ta lokaci ta bude data.

Farkon abun da ta yi tozali da shi kan whsap shi ne.......

 

2️5️

Shi ne hoton da marwan yadauka a filin airport wani kayataccen murmushi ne kwance a kan fuskar ta take kallon hoton waouh ta furta ta ayyana aranta yanda wasan ze ka sance inhar Adamsy yaga hoton nan.

Jin motsin mutum a lungun ya sa cikin hanzari ta yi hanyar gida daidai shiga gidan marwan yakara kiran ta awaya dan gefe ta matsa ta Daga wayar murya cen kasa ta ce naga hoto ya yi kyau sossai kabari gobe zamuyi waya kashe wayar zanyi.

Marwan dake kwance kan makeken gadon ya shafa gemun sa ya yi ya ce toni me zaki ba ni wannan kyautar danai miki.

Cikin kosawa salma ta ce pls kabari gobe zan kira ka fada min sunan ka.

Marwan sani turaki yabata masa.

Suna me kyau tafurta tare da katse wayar.

Kashe wayar ta yi gabadaya ta tura cikin brezia..

Kai tsaye ta cusa kanta cikin gidan hango Rahama ta yi da kishiyar kakar su 'suna hira Rahama na dariya.

Da dukan alamu labarai masu Jan hankali take bata.

Kallon Salma suka yi dake shigowa.

Kakar su ta ce haba salma baa San Amarya da yawo fa tun dazun ina kikaje ne ke bakya Jin gajiya ne.

Salma turo baki ta yi gaba ta ce gajiya kuma aita bi jiki yanzu banda ikon inje insai wani abu tana kokarin zama kusa da Rahama.

Rahama ta murmusa sai da kuncin ta ya lotsa ta ce uhmm yaudai naga fadan kishiyoyi 'maida kallon ta a kan salma ta yi ta ce my qanwaty wai ina kika tsaya ne Abba yakira waya yana son magana dake nace mai kina sallah banson yamiki fada.

Tafada cike da kulawa.

Gaban Salma saida yabuga rass.

Ta ce ikon Allah Ko me Abba ze cemun ne yake nema na.

Rahama ta ce nikam ina zansani tsakanin uba da ya ne.

Kaka ta ce ai gaskiya ne.

Rahama dauko wayar dake ring ta yi ganin nombar Abba ne ke yawo a kan screen din wayar.

Cikin hanzari tadaga.

Assalamu alaikum ya Abby.

Daga can ɓangaren amsa mata ya yi ya ce salma ta idar da sallah kuwa.

Duban salma take data kura mata idanu Alamun duk hiran da suke tanaji muryan na fita.

Eh Abba gatanan tare da mikawa salma wayar.

Cikin tsoro ta ce Abba inayini bayan sun gaisa ya ce yawwa maganar lefe ne kin san bana amsar lefe agidana da duk wani abun da yazama Al'ada dan haka na ware kudi dubu dari biyar keda yayar ki zaku siye duk wani abun da kuke da bukata.

Sa dakin ki yana hannuna.

Bayan daurin aure InshAllah zan damka miki a hannun ki.

Sannan jibi sammako zaku yi.

Cikin sanyin jiki ta ce Allah yakaimu.

........

Washe gari.

Bayan sun karya sunyi wanka tsaf suka shirya dan kaiwa mahaifiyar uwar su ziyara sheik kabeer da ya fito Daga dakin sa' yana sanye da farar jallabiya.

Kallon su yake yanda suke ta dokin fita.

Rahama cike da ladabi tagaishe shi ta ce my ango sai yanzu kafito tun asuba daka shige Ko sanyi ne ke ratsaka nasan ka da tsoron sanyi.

Kayataccen murmushi ya yi ya ce dadina dake Rahama akwai ganuwa.

Har kunshirya kenan zakuje gidan zubaida 'salma dake kallon sa ta ce cen muka nufa maza mu je kaimana rakiya.ta furta

An gama ranki yadade tun da umarni ne mu je to.

Yana gaba suna biye da shi abaya.

Matar kakar su rakiya ta yi musu ta ce aida goben zaku kai yamma da tare muka je danni ban amso din kuna na ba.

Sheik kabeer ya waigo yana kallon matar shi ya ce ai kuna iya tafiya tun da jibi zanzo kinga saina wuce miki dashi..

Ta ce takwana gidan sauki Allah ya sa telan nan karta kwafsa mun tamin dinki me kyau yan zamani.

Salma data kosa subar gidan ta ce to kaka wani irin dinki zamani kuma za' ai miki.

Yawuce tadinka miki tazarce.

Kaka rike da baki Ta maimaita tazarce to badani ba ehee kan mage yawaye..

Dukansu fita suka yi suna mata dariya.

Sheik kabeer dakansa yajasu a motar sa.

Yaita zarya da su gun yan uwansa akai ta samusu Albarka.

Gidan zubaida ya ajiye su.

Inda nan m'a suka samu tarba na mussaman aranar dai sunsha kyautuka naban mamaki dangin mama sunyi abun ayaba musu..

Rahama tadauko jakar ta tafara kirga kudin da tazo da shi ganin babu rabi hankalin ta yatashi ta ce to kudin nan daukar su akai taya za a dau rabi abar mata rabin su.

Kallon salma dake kokarin fita waje ta yi harta yafa gyale.

Cike da nutsuwar takaraso kusa da ita ido cikin ido take kallon salma ta ce.

Salma meyasa kika daukar mun kudi baki gayamin ba.

Rau Rau salma ke kallon ta ta yatsine fuska bangane nadaukar miki kudi ba.

Sharrin sata zaki daura min.

Rahama ta ce Ko shakka babu ke ce kika dauke shi dan babu wacce zata dauka saike kuma tare muka kwana.

Wallahi anty Rahama ki kiyaye ni daman kiyayyar da kikemin yakai haka ban saniba kuka ta saki wanda yajawo hankalin jama'ar gidan akansu.

Kowa sai tambayar abun da akai mata take ta zabga uban kuka haka.

Rahama ta ce karku damu wai dan ina tsokanan ta ne shi ne take kuka batasan wasa ba..

Mutanen gidan suka ce ke kuwa Rahama ba yayar ki ba ce kuma ta ce wasa take miki.

Da ga haka kowa ya watse yabar su.

Salma cikin huci sama sama tana hura hanci ta ce Wallahi Rahama saina saki kuka kuma saikin yi nadaman ka sancewa yayan mutum daya nidake.

Kalaman ta bakadan ya Girgiza ila'iriin jama'ar dake gidan ba.

Dawowa suka yi wajen kanwar mama ta wanke salma da mari ta ce ke wawiyar inace me ya yi zafi da har zaki ringa jifar yar uwar ki.

Da mugayen kalamai.

Rike da kuncin ta salma ta dago kai ta kalle ta Idanun ta cike da kwalla ta ce ni kika mara ?

Kanwar mama ta ce anmareki kozaki rama ne ?

Kanta gama rufe bakinta saiji ta yi tass salma ta wanke ta da mari.

Mamaki kwance kan fuskar Rahama.

Rahama da takai kololuwa wajen bacin rai.

Ta ce Wallahi salma kinyi asara wannan fa kanwar uwar ki ce.

Yanda kike kallon mama to ita ma haka take amma dan kina wawiya sha sha sha shi ne kika mare ta.

To bari kigani.

Maruka uku ta wanke salma da shi Ko kuwa na kokarin barkewa tsakanin su.

Dakyaar aka rabasu Rahama banda kuka babu abun da take ita bakin cikin ta marin da tayiwa kanwar uwar su.

Zuwa gun kanwar uwar su data zabga uban tagumi cikin rarrashi ta rinƙa ba ta hakuri kakar su zubaida ita Kanta ta Girgiza a kan wannan rashin idon salma.

Kowa wajen yanata Allah wadai da halin ta.

Salma ficewa Daga gidan ta yi tasamu wuri tazauna marin da Rahama ta yi mata ba ƙaramin sa mata ciwon kai ya yi ba.

Tana ta shafa fuskar ta.

Ciro wayar ta yi Daga cikin jakar ta ta yi tare da kunna ta.

Wayar na kawo haske ta danna nombar marwan.

Yanata ring ba a da gaba dan marwan yana zaune kusa da yarima Samad yarasa yanda zeyi ya Daga wayar gashi Idanun yarima Samad yadawo kan wayar sa dake ta ring amma yaki dagawa.

Banda bari babu abun da jikin marwan yake.

Kokarin daukar wayar yake 'Samad yarigashi dauka Daga wayar ya yi ya sa hansfree Jin muryan mace ya sa shi zare idanu..

Yaji tana fadin jiya na kashe wayar Ko' uhmm kaidai gidan mu ba asan ina rike waya ba.

Naji kace dame zanbiyaka kyautan dakamun.

Gayamin me kake so dan kabiyani komai a rayuwa wlh..

Jikin marwa yadau rawa Saboda wani mugun kallon da yarima Samad ke jifan shi dashi.

Idanu ya yi masa daya ɗau wayar 'cikin hanzari yadau wayar tare da cire hansfree din yabar falon.

Da Idanu yabishi da shi yana Girgiza kai ya ce lallai saina sa idanu a kan yaron nan kenan neman mata yasoma a garin nan.

Marwan wani corridor daze sadashi da babban falon gidan' na su yabi waya na kunnen sa.

Soma share Zufa da ya keto masa a fuska ya yi da hankicin.

Salma Jin shirun ya yi yawa Daga cen ɓangaren tana gyara zaman ta ta ce hello marwan bakajina ne.

Marwan bekuma bin takan wayar ba dan ya tsorata sossai da abun da yarima ya yi masa dan ma Allah yataimake sa.

Su faruk basu nan da sun gane lagon sa.

Numfashi ya fesar yana tunanin ta inda zefara.

Dan sun tsara shida Abban sa sai mai martaba yazo kanon za su kai hoton gidan jaridu 'amma kafun nan yana son ya san yar wacece me matsayin mahaifin ta.

Dariyar mugun ta ya yi ya ce kajira ranar juma''a

Wannan barazanar da kake mun zekare ne.

**************

Yau takama ranar talata su Rahama tun da asuba suka shirya tsaf tare da kyaututukan da a ka basu.

Drever Abba karfe takwas ya Iso makarfin.

Tare da matar kakar su.

Zasu juya kanon.

Adamsy sai kira yake yi ba arziki rahama ganin kaka ya sa takejin kunyar daga wayar dan suna gaf da juna zaune cikin motar.

Salma data lura Adamsy ne ke kira murmushi ta yi ta ce au naga angon naki nakira amma kinki dagawa lafiya kuwa.

Tana me tsareta da idanu.

Rahama ta ce babu komai

Tare da kame bakinta ta yi shiru.

Kakar tasu talura kunyar ta takeji murmushi ta yi tana jinjina alkunya irin ta rahama Sam Sam wayewar ta cike yake da hikima da hangen nesa.

Kafun ta furta zancen saita tauna shi ta fidda mekyau sannan ta isar dashi.

********

Kusan karfe daya suka Iso kanon dabo tumbin giwa 'salma banda murna babu abun da take yi cikin zumudi ta fito Daga motar tana kokarin shiga Daga ciki cin karo da Abba ta yi dake kokarin fita zuwa massalaci da fara'a fuskar shi ya tare su' Abubakar ya kwada kira shida hussain nan da nan suka fito kaya ya nuna musu da sushiga dashi.

Sannu ku da zuwa inna tare da durkusa ya gaisheta cikin ladabi.

Cike da farin cikin haduwa da shi ta amsa masa gaisuwan.

Hussain yana kallon innar tasu ya ce su Hassan yaushe za su zone ya jefo mata tambaya.

Ta ce ai inaga gobe sammako zasuyi harda abban naku.

Cike da farin ciki suka shiga gidan wanda tuni gidan hargitse yake da jama'a anata hada hadan kai kayan amare...

Anty da duk ta rude ba ta nutsuwa zuwa ta yi tasamu sheik a zaure tare da baki.

Ta ce tana son magna da shi ya taso ya sameta cike da kulawa yake kallon ta kuma da dukan alamu sauri yake yakoma wajen bakin nasa yaraba hankalin sa gida biyu.

A nitse tafara magana ta ce daman zancen kai kayan amare ne abari bayan daurin aure mu zamuje kai kaya.

Saboda ka ga har yanzu kujerun dakin su basu karaso ba.

.

Au to babu matsala ayi yanda kika ce din yabata amsa yakara da cewa wannan raguna guda shidda da saniya guda biyu gobe in Allah yakaimu za a yankan su.

Dan Allah masu kula da ɓangaren abincin suyi mana farfesu nama ya yi kyau kingan na taron daurin aure ne.

Yayi magana cike da nuna muhimman cin abun.

Ta ce babu matsala za a kula tare da juyawa cikin gida shima yakoma gun bakin nasa.

************

Dr Abdullahi shida matar sa banda zumudi babu abun da suke yi wai yau saura kwana uku kacal dan su ya angwance farin ciki a fuskar su baya misaltuwa.

Ɓangaren Adamsy sossai yake ta shirye shirye yahada mata akwatuna takwas harda akwatin zinari karama.

WAOUH MASHAALLAH MASU BUDE KAYAN LEFEN SUKA YI TA FADI SUNA GUDA.

DAN SOSSAI GIDAN YACIKA DA JAMA'A.

Adamsy ya shiga damuwa inya kira Rahama ba ta dagawa hakan ba ƙaramin Daga masa hankali yake ba.

Shiryawa ya yi cikin boye blue ya sa takalmi half cover ba ƙaramin kyau ya yi ba sai baza kamshi yake.

Abokin sa hamza yaimasa jagora zuwa gidan su Rahama..

Da ƙyar ta fito takasa hada idanu da shi 'ya ce yau rowar fuskar taki kike min ne Rahama yana me tsareta da idanu yana murmushi.

Hamza ya ce ka ga bara inbaku wuri kila batason magana a gabana ne.

Barin wajen ya yi hamza

Adamsy ya ce pls wannan kunyar taki tana bala'in cutar dani ki Daga kai Ko saudaya ne ki kalleni.

Dago kai ta yi takalle shi Idanun su suka tsarke cikin juna sauke Idanun ta ta yi ta ce Idanun mutane a kan mu pls kabari zamuyi waya..

OK ya ba ta amsa ya ce akwai abun da kike bukata ne na biki.

Girgiza kai ta yi Alamun babu...

Adam ya ce ai ranar juma'a gida na zaki kwana gado daya nidake zancire miki kunyar nan inhuta yana kallon yanayin ta.

Maganar sa ya sa takasa Tsayuwa domin faduwar gaba da kunya suka dirar mata lokaci daya.

cike da nutsuwa tajuya ta ce masa sai anjima..

Shiko Adamsy yana ganin tashige yakira hamza suka tafi.

*********

Yau takama Alhamis gobe daurin aure.

Kasar kwatano.

Me martaba shida iyalan sa a airport hade da waziri.

Mamy da Ahmad ɗa khadija..

Fulani ba ta biyo su ba.

Amma mijin ta da shi za a je.

Mai martaba ya ce lallai wannan bikin ya yi kai gashi mun taho da yawan mu..

Karfe daya jirginsu ya sauka a kano.

Yarima Samad cike da farin ciki yanata baza idanu yanda zehango kannen sa.

Da mahaifiyar sa.

Marwan ya ce haba Samad ka tare mana gaba kai kaidai ne kake zumudin ganin su kenan bandamu kenan.

Faruk ya ce kash marwan yanzu ina gaban daya tare maka.

Samad ya ce kyaleshi dan rainin wayau mana ba ka ga Ko kallo be isan ba.

Yana magana hankalin sa nakan masu fitowa Daga jirgin.

Aminu ya ce ammaa ba sa cikin jirgin nan fa.

Kamar ance Samad air plan personnel suka shiga.

Yarima Samad dake kallon sa ya ce gaskiya haka ne waigowar dazeyi suka hango su Daga cen nesa suna tunkaro su.

Cike da zakuwa Yarima kamar ƙaramin yaro ya je ya rungumi mamy.

Ta nata murna ta ce ɗana gashi yau Allah yakawoni kanon nima.

Ya ce eh wlh mamy kamar kin san nayi kewar ki yana magana cikin shagwaba kaman ƙaramin yaro.

Kallon khadija yake yabude hannayen sa.

Alamun tazo aguje taje ta rungume shi cike da farin ciki ya ce yau gani ga ƙanwata a kano uhmm.

Ahmed yabata fuska cikin wasa ya ce ni dai Ko !

Samad dake kallon yanayin sa ya ce kaide Ko me akai maka sarkin rigima.

Zumbura baki Ahmad ya yi ya ce bakai bane to.

Bani bane nayi me yana kokarin ya ja masa kunne a guje ya je bayan mamy yabuya yana ma Samad gwalo.

Mamy banda dariya babu abun da take ta ce au airport dinma sai kun nuna halin ku.

Khadija da Ahmad cike da Jin dadi suka gaisa da kowa.

Wani mayata cen kallo marwan ke jifan khadija da shi har yana cijje laban sa.

Yana tunanin yanda zeyi ya sameta cikin ruwan sanyi.

Motocin da aka kawo suka shige ciki kai tsaye gidan Samad suka nufa.

A hanyar su Ta zuwa masaukin su mai martaba yakira Dr Abdullahi ya sanar masa da zuwan sa da inda ya sauka cike da farin ciki ya ce yana nan zuwa duba su....

Washe gari babban rana kuma ranar farin ciki ahlin gidan sheik '

Da

Gidan Dr Abdullahi.

Gidan su Al' amin.

Kowannen su yana Alfahari da zuwan wannan ranar.

Ɓangaren Al'amin

Al'amin Sam baya son zuwa daurin auren nan.

Da ƙyar Abban sa ya lallaba sa suka tafi.

Gidan sheik yau da farin ciki aka tashi anata hada hada hada farfesun nama na yan daurin aure tuni aka fitar dasu ɗan karfe goma za a daura auran.

Rahama banda faduwar gaba babu abun da zuciyar take yi.

Anty data fito dakin ta sanye take da farin lace riga da zani hannayen ta sun sha zanen lallai ba ƙaramin kyau ta yi ba.

Dakin da rahama take ta nufa.

Sallama dauke a bakinta tashiga dakin.

Kallon Rahama take da kulawa ta ce yata wai har yanzu me makeup din nan ba ta zo bane.

Rahama cikin sanyin murya ta ce anty yau kwata kwata wallahi nakasa gane kaina gabakidaya.

Shi ya sa banma kira me makeup ba Ta fada cike da damuwa.

Anty samun wuri ta yi tazauna kusa da Rahama suna fuskantar juna ta ce haka kowa yake amma tun da naga har kinkasa boye damuwar ki gayamin ya kike ji.

Nan da nan Rahama tafara ba ta labarin yanda takejin zuciyar ta na mata matsifaffen harbawa

Jim anty ta yi har ta bude baki za ta yi magana wata kanwar ta tashi go ta ce anty sa'adatu neman ki ake yi kizo kibada inda za a zuba jallof din shinkafar ta fada cike da bukatuwa.

Anty ta ce mu je tare da yiwa Rahama maganar zata dawo.

Dan wajen daurin aure kowa ya hallara manyan abokan sheik ne da basu karaso ba su ake jira a daura.

Kamar anjefo salma Daga sama haka tafado dakin su' dube dube take cikin jakar ta tadauko wannan maganin da malam isa yabata sakawa ta yi cikin brezia tare da daukar wayar ta da kudi 'sauri sauri take tana kallon agogon hannun ta.

Dayasha zanen lalle.

Ganin time na tafiya uban sauri take ta zubawa ka sancewa duk mazan gidan babu kodaya duk sun tafi wajen daurin auren.

Ɓangaren Yarima Samad sun sha farar shadda harda babban rigar Dayasha aiki gun kwararren tela takalmin sa half cover sossai shigar ta yi mishi kyau dan yau shi ne rana ta farko a rayuwar sa dayayi shiga ta mussaman har yanzu dai faduwar gaba yakeji.

Faruk da Aminu da marwan suma kusan kayan iri daya suka sa.

Nan dai Faruk ya ringa daukarsu selfie da babbar wayar sa iPhone.

Sossai Samad yadara a hotunan wanda ya bayyana zallar kyawun sa.

Da cikar haibar sa.

Kokarin fita suke ya ce wa marwan kashiga ciki ka gayawa mamy ita da khadija su tafi gidan Dr Abdullahi inda ake taron.

Dan tuni mai martaba ya hallara wajen daurin auren inda wuri ya amsa gayyatan manyan manyan kasa harda larabawa motoci kuwa sun gama cika unguwar da shi kamar sallah idi haka jama'a suka yita hallara ana zaman jiran babban aminin sheik wanda shi ne waliyin Rahama.

Kafun nan su hussain Hassan 'Abubakar sunata rabon lemuka masu sanyi kowa wajen saida ya samu yajika makoshin sa' suna jiran adaura adawo ɓangaren ciye ciye.

Ɓangaren salma mai napep din daidai kofar giɗan Adamsy ya sauke ta sanye take da nikaf a fuskar ta 'sallamar mai napep tayi.

Daidai bangon gidan nasu ta tsaya.

Nan da nan tadauko wannan kwallin Daga cikin jakar ta.

Waige Waige take yi tana adua Allah ya sa Adamsy bewuce ba.

Aiko waigowan daza ta yi taganshi sunfito da abokan sa' sunci fararen shadda wai tsiya suke masa yana dariya.

Wani yaro ta hanga takira sa yazo ta ce ya je yakira mata angon cen..

Ba musu yatafi ya sanar masa.

Adamsy da mamaki kwance a kan fuskar sa ya ga wacce ke kiran shi sanye take da nikaf a fuskar ta.

Ce m'a abokan sa yana zuwa ya yi tare da tunkarar inda take.

Ganin ya doso inda take cikin azzama ta yi saurin shafa kwallin nan a Idanun ta.

Yana karasowa suka hada Idanu gabadaya

Ya fara ganin taurari dishi dishi yake ganin ta.

Idanun sa na juya masa.

Kallon ta yake cikin yanayin daya kasa tantancewa na mene ne.

Murmushi ka san zuciyar ta

 A fili kuma fuskar ta cike da damuwa ta ce yaya Adamsy hakika ni me kaunar ka ce ba zan bari acuce ka ba.

Na gayamaka Rahama yar iska ce amma ba ka yarda ba.

Yaudai ga sheda nan.

Badalar da ta yi a jiya. shi ya sa inka kira wayar ta ba ta dagawa sai taga dama..

Adamsy daya koma kamar tabbabe agabanta ya ce muga shedar dakike da shi yana kallon ta cikin idanu.

Kunna wayar ta yi tare da nuna masa hoton Rahama kwance a kan wani.

Kallon wayar yake cikin tashin hankali.

Gaban sa ya yi mummunan faduwa Azabure ya furta A'a Rahama ban sanki da haka 'ya zaki min haka yana kuka mai tsuma rai.

Salma ganin abokan sa hankalin su yadawo kan su ya sa tajuya tabarshi wajen tsaye.

zuciyar ta cike da farin ciki tabar wajen.

Nan da nan Idanun Adamsy suka kada jajir banda hoton wanda Rahama ke kwance kansa babu abun da yake gani a Idanun sa.

Wani uban kara ya saka wanda yajawo hankalin jama'a gidan bikin da abokan sa sukayo kansa suna tambayar lafiya kuwa cikin tsananin damuwa kwance a fuskar su.

Cikin tsawa ya ce wallahi billa'l'azim nafasa auren nan kuma babu uban daya iya sa ya daura shi Ko andaura saina kwance shi yana musu nuni da hannun yanda ze datse auren.

Abokan sa suka ce haba ai zancen banza kake ba ka tashi fasa aure ba sai ana sauran yan mintuna adaura kai ma ka san zancen banza ne wlh daya Daga cikin abokan ke magana ransa a ba ce.

Shiga motar Adamsy ya yi suma suka shiga dakansa ya ja motar aguje yanata sharara uban gudu kaman ze tashi sama..

Nan gidan su Adamsy jama'a sunata jujjuya kalaman wai yafasa auren labari yajewa mommy da take cen zaune cikin baki harda mamy zaune suna taya ta rabon abinci.

Firgita ta yi dajin mummunan labarin nan.

Lambar Adamsy take kira amma Sam baya dagawa..

Haka ya sa tasoma kiran na Daddy sa shima taron jama'a ya sa besan ana kira ba.

Cike da damuwa ta kalli mamy da mama karama ta ce wannan yaron tun haihuwar shi zuwa yanzu be taba konamun rai irin na yau ba.

Jibi yanda ya samu auren nan da ƙyar amma ya ce yafasa zama ta yi dirshan kan kujera tana goge Zufa nan da nan hawaye yacika Idanun ta ce ace ranar farin cikin ta shi ne ze zama bakar rana agareta.

Mamy suka yi ta rarrashin ta suna ba ta hakuri tare da ba ta karfin guiwar InshAllah Daddy sa bazasu saurare shi ba.

Ɓangaren Adamsy ikon Allah kadai yakaishi wajen daurin auren Ko daidaita parking motar beyi ba.

Ya fito a ujajan cikin uban sauri, yan jaridu sunata barka da zuwa ango inaa Ko kallon inda suke Sam beyi ba.

Yanata cusa kan sa cikin dumbin Al'umma.

Ka sancewa ansan shima angon ne ya sa akai ta bashi hanya.

Yana isowa aka gama daurin auren salma da Al'amin.

Sun gyara zaman tare da fadin yanzu za a daura auren Adamu da Rahama ina waliyin ta aminin sheik, ya bayyana kansa...

Ku dakata cikin tsawa wanda ya yi sanadiyan kallo yakoma kansa..

Cikin ihu yana huci sama sama ya ce karku daura auren nan nafasa banayi.

Dr Abdullahi zumbur ya Mike tsaye ya ce wannan wani irin zancen banza ne adamu kake fadi bainin nasi.

Cikin tashin hankali yake magana.

Adamu

Cikin kuka ya ce nace kada adaura wallahi idan kun daura anan wajen zanmata saki uku na rantse da Allah.

Yana haki muryan sa ya disashe.

Sheik wani Zufa ne ke keto masa ta Ko ina cikin rawan murya ya ce adakata daurin auren nan.

Kunji furucin sa dan haka ni uban Rahama na hakura.

Yana kokarin cewa kowa a tashi Daga wajen daurin auren tun da andaura auren salma da Al'amin.

Mai martaba ya dafa sheik da waliyan ango ya ce ku dakata.

Kowa wajen hankalin sa yadawo kansa zaro bandir din kudi ya yi Daga cikin aljihun sa naira dubu dari ya ce gashi sa daki ne.

Kallon sa sheik yake yi da Idanun sa suka kada.

Yana masa kallon kudin mene ne ?

Mai martaba ya ce adaura auren Rahama da jikansa Abdul Samad.

Yarima Samad duk abun da akeyi wajen daurin auren bedame sa ba Jin an ambaci sunan sa cikin tsananin tashin hankali ya..................

 

2️6️

Cikin tsananin tashin hankali yake kallon mai martaba muryan sa na rawa ya ce wani jikan naka kenan 'Sam yama mance cikin taro suke..

Mai martaba ya ce inaga kai kadai ne Abdul Samad a masarauta.

Mai martaba beko bi takan yarima samad ba ya tsaya yanata kokarin shawo kan sheik daya amince adaura kawai.

Aminin sheik Isa

yayi wa sheik magana yabari kawai adaura kodan su fita kunyar jama''a da aka tara.

Sheik ya ce wa Aminin sa banki zancen ka ba shin wane ne yaron kuma ya tarbiiyyar sa yake.

Nifa ba neman kai nake yi da yata ba.

Suna gama tattauna da sheik.

Aminin Abba ya tunkari mai martaba ya ce uban Amarya ya amince adaura.

Sheik mamaki ne kwance a kan fuskar sa ganin ba haka suka yi da Aminin sa ba.

Nan da nan yan daurin aure suka gyara zaman su 'Aminin Abba yamika sa dakin hannun Abba.

Dr Abdullahi banda kukan zuci babu abun da yake yi.

Jin za a daura da jikan sarki ya sa yadanjin saukin abun da ke damun sa.

Yarima samad da hankalin sa ya yi mugun tashi kokarin tashi yake ya ce wallahi badashi ba abokan sa suka rirrike shi suna kokarin barin wajen dashi.

Daidai fita filin daurin auren yaji ana sanarwa ta cikin lasifika.

Ana fadin Alhmdulilah andaura Auren Rahama da angon ta Abdul samad bisa sa daki dubu dari.

Wani ihu yakasa mai fidda sauti nan da nan Idanun sa suka kawo ruwa 'murya na rawa ya ce ni me martaba zeyiwa haka wallahi ze san yataboni da ƙyar faruk da Aminu suka jashi.

Tare da sakashi cikin mota suka yi hanyar gida dashi..

Adamsy kuwa yana gama fadin haka yabar wajen direct gida ya nufa shida abokan sa.

Andaura aure lafiya mutane sun fara halarta inda za ayi ciye ciye a kofar gidan sheik.

Mai martaba da Dr Abdullahi suka dakatar da sheik da suke shirin wuce wa.

Hakuri Dr Abdullahi yashiga bawa sheik a kan abun da dan sa ya aikata cikin kuka ya ce wallahi Adamu ya yi asaran nagartaciyyar mata.

Sheik cikin sanyi murya ya ce kada ku damu tun ran gini tun ran Zane dama Allah yakaddara Rahama ba matar sa ba ce.

Kaddara ce haka Allah ya aiko mudai bin ta kawai muke yi.

Ba ƙaramin dadi mai martaba suka ji ba furucin da sheik ya yi musu..

Suna kokarin sakai mai martaba yayiwa sheik hannun Alamun su tsaya cak haka sheik ya tsaya yana kallon sa.

Mai martaba gyara Tsayuwar ya yi ya ce ya batun daukan Amarya.

Dan gobe zamu je kwatano nida mijin nata.

Nan yashiga yiwa sheik bayanin aikin da Abdul samad yake yi.

MashaAllah sheik ya furta tare da sauke nauyayyen numfashi ya ce magana tana hannun ku ni yanzu Rahama ba ta kar kashin ikona.

Aminin sheik ya ce wannan zancen naka gaskiya ne.

Mu zamu tafi duk yanda ake ciki kun sanar mana.

Sheik suka yi gaba shida Aminin sa.

Mai martaba ya ce Dr Abdullahi wannan auren da aka daurawa samad Allah ya sa Alkhairi ce dan wallahi da kunya ace anzo daurin aure ace anfasa wallahi yana da karfin imani uban Amaryan nan.

Sun dade suna tattauna Daga nan suka kama hanyar gida Dr Abdullahi tare da mai martaba da waziri.

Sani baban marwan yana cikin su.

....

Cen gidan Amare kuwa tuni labari ya je musu anfasa auren Rahama da Adamsy andaura da wani.

Rahama najin wannan labarin saida ta suma aka cika a kan ta sunata yayyafa mata ruwa.

Mama cike da tausayawa take kallon Rahama cikin kuka ta ce wannan wani irin masifa ne.

Adamu yaci amanar ki Rahama Allah sai ya saka miki.

Salma ba ƙaramin dadi ta ji ba

Amma a zuciya ta sai maimaita sunan Abdul samad din da. Akace da shi aka daura mata auren..

Yana tunani to wanene Abdul Samad din wata zuciyar ta ce yanzu haka dan Almajiran unguwa ne.

Tana dariyan mugun ta.

Sheik na samun labarin abun da ya samu Rahama aguje yashigo koda ya Iso ya iske harta bude Idanun ta..

Sannu ya ringa jero mata

Tana Girgiza kai.

Kallon fuskar Rahama yake yanda ya yi fari kal.

Cike da tausasa murya ya fara rarrashin ta yana nuna mata yarda da kaddara me kyau Ko mara kyau yana Daga cikin imani dan haka yana ba ta hakuri daura mata aure da akayi da wani ba tare da shawarar ta ba.

Girgiza kai Rahama tasomayi cikin raunin murya tafara magana a nitse.

Abba banso in ji kalmar banhakuri agareni ba.

Duk yanda ka zabamin daidai ne ba tare da ka nemi shawara ta ba.

Kowa wajen sun kokawa Al'amarin nan sossai.

Anty kama hannun Rahama ta yi ta wuce da ita dakin ta.

Shiko Abba shiga sabgogin sa yayi.

Mama duk abun duniya ya isheta gashi tanason taje ta rarrashi Rahama

Girman kai yahanata zuwa Saboda taga sun tafi dakin anty.

Asiya kawar Rahama fita waje ta yi dannawa Adamsy kira ta yi tafara zagin sa.

Macuci maci Amana ashe son karya kakewa Rahama shi ne ka nemi ka wulakanta ta agaban dunbin jama'a

Adamsy da zuciya haryanzu ci gaba da tafasa take yi.

Cikin kunan rai ya ce ke dakata malama ke har kun san girman amana har dake ake hada baki dan acuce ni.

Kin san cewa Rahama yar iska ce maza take bi amma... bekarasa fadin zancen nasaba yaji saukan kyawawan mari Daga mommy abun da ba ta taba yi masa Arayuwar sa.

Sake wayar ya yi kasa ba tare da ya Katse ba.

Rike da kuncin sa ya ce mommy yau da hannayen ki kika mareni.

Cikin tsawa ta ce dan iska an mareka din ni ba zan maka baki ba amma ka sani ka cutar da zukata.

Amma Allah yashare mata hawaye yabata wanda yafika dakomai sai dai imani ne shi ne ban san wanda ya fi wani ba acikin ku.

Cikin zazzare idanu da maganin daya fara sakin jikin shi ya ce kina nufin andaura wa Rahama aure da wani daban.

Wani mahaukacin dariya yabushe da shi ya ce to mene ne ai tafi nono fari kal.

Lokaci daya ya hade fuska tamau kaman bashi bane ke dariya ha yanzu.

Baku tambayeni abun da tamin ba cikin kuka yake magana dan yaji zafi sossai aransa da mommy ke fadin andaura mata aure da wani.

Mommy ta ce gayamin abun da ta yi ranta aba ce take magana..

Cikin kuka ya ce mommy kanwar Rahama ita ce ta nuna min wani hoton Rahama da wani tana kwance a kan sa wallahi na firgita sossai inada kishi ban iya kallon wannan kazantar kuma inzauna da ita a matsayin mata.

Duk abun da suke fade a kan kunne Asiya da har yanzu ya mance be Katse wayar ba itakuma Asiya ta tsaya sauraron abun da suke fade.

Mommy ta ce kayi bincike a kan wannan lamarin kuwa Adamu 'no banyi bincike ba amma ai naga zahiri shi ya sa.

Kallon sa mommy take yanayin yanda yake zaro kalaman sa ta ce wannan yaron hanya lafiyar sa kalau kuwa.

Jikin asanyaye tabar dakin.

 ranar bugu ne kadai besha wajen Daddy ba domin harda hawaye Daddy ya yi na bakin ciki.

Yaita jifan Adamu da mugun kalamai mai martaba da Abban marwan ne suka yi ta tausasa shi.

Mommy adamu tashiga Daga ciki ta iske mammy da mamaki yacika ta wai andaura wa Samad aure yaron da Ko mace be taba gani ya ce yanaso ba.

Khadija da Ahamad murna awajen su ba a. Cewa komai.

Ahmed ya ce yanzu da matar yaya Samad zamu tafi kwatanon kenan yana kallon mamy da take kada kai Alamun tarin mamaki a kan auren nan.

Mamy ta dago kai ta kalle shi ta ce wannan tambayar ba ni zakaiwa ba mijin ta za ka tambaya.

Mama. Karama dake gefen mamy zaune ta ce nimadai auren da ban mamaki yake samun kishiya Daga sama.

************

Ɓangaren Asiya tana gama sauraren wayar Adamu taci karo da Abubakar duk abun da ke faruwa ta sanar masa.

Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba daya tuna dalili tarwasewan farin cikin yar uwar sa ita ce.

Sannan tajawo silan da za su kunyata a idon duniya wajen daurin aure.

Asiya ta ce ban san kiyayyar da salma takewa yar uwar ta na mene ne.

Harda mummunan ka zafi.

Abubakar ya ce wlh hassada ce ai Allah yafidda mu kunya tun da an daura dawani.

Cikin gidan ya nufa ya sanar wa mama da anty da duk wani wanda yake cikin gidan.

Ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba...

Mamaki suke to menee dalilin dayasa ta yi haka.

Anty ta ce mugun haline da bakin ciki irin na uwar ta shi ta koyo afusace take magana

 guda ta rangada cikin Daga murya cikin gidan ta ce Ai abun da Salma ta manta shi ne ai wani hanin ga Allah baiwa ce wallahi dan haka wlh ko yanzu bana bakin cikin mijin da rahama ta aura..

Cikin takama take magana yanda salma zata jiyo ta ta ce Ai Allah ya wanke yaba Yata nasara fiye da na baya wallahi.

Waye besan wane ne Yarima Samad kyakyawan matashi ajin farko ga ilimin adinnin da na zamani ga kudi ga izzar kai Allah yakashe yabamu..

Ta fada cikin shewa.

Kuma yan bakin ciki sai dai su mutu a binne su.

Mama kalaman anty Sam kodaya basu ba ta haushi abun da Salma ta yi ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba.

RAHAMA DA TA FITO DAGA DAKIN TA BAYAN ANGAYAMATA ABUN DA ya sa AKA FASA AUREN.

Tafiya take cikin sauri sauri takaraso tsakar gidan kama hannayen mama ta yi cikin kuka mai tsuma rai ta ce.

Mama kina ganin Abun da salma ta yi mun kuka take sossai harda shesheka.

Mama da Idanun ta suka kada kaman gauta lokaci daya da ƙyar Ta furta Rahama kiyi hakuri kanwar ki ce.

Rahama Daga hannayen ta sama ta yi ta ce ya Allah kana ganin abun da ƙanwata ta yi mun ya Allah ka.....

Cikin hanzari mama ta toshe mata baki tana Girgiza kai Alamun karta ka rasa fadin abun da takeda niya

Dan tasan adu'ar wannan aka zalunta karbabbiya ce agun Allah.

 

2️7️

Rahama cikin kuka ta ce mama karki damu nasan yanda kike son Salma dan haka na yafe mata duniya da lahira.

Tana gama fadin haka tashige dakin su aguje

Mama jikin ta ya yi mugun sanyi da furucin Rahama kukan kurciya jawabi ce mai hankali ne kadai zai gane.

Kannen mama da suke wajen suka ce gaskiya Sa'adatu bakiyiwa yarinyar nan Adalci kina ganin badan ke ce kika haife ta ba zataji maganar ki a kan cutar da akai mata.

Cikin bacin kai suke magana wani mataki kika dauka a kan Salma koko dai duk abun da ta yi daidai.

Mama nata Girgiza kai cikin kuka ta ce wallahi bahaka bane ina son Rahama fiye da Salma boye wa nake yi acikin zuciya ta.

Kuma......

za ta yi magana ta ji zubaida kakar su Rahama ta ce rufemin baki sakarya kawai.

Ki sameni a daki tafada cikin tsawa tare da yin gaba mama na biye da ita abaya cikin faduwar gaba.

Banda haushin mama babu abun da kowa keji a gidan.

Rahama nashiga daki ta yi tozali da Salma dake bakin gado zaune.

Kallon kallo sukewa juna ita da Salma wuce ta ta yi ta shiga toilette tare da cire kayan jikin ta a toilette din.

 Sakar wa kanta ruwan sanyi ta yi har cikin tsakiyar kanta takejin sanyi na ratsata.

Kaico na ni Rahama shi ke nan ta Rabani da Adamu wanda nake mafarkin zama tare da shi na har abada.

Banda hoton Adamsy babu abun da take gani a Idanun ta kuka take yi sossai Jin karar buga kofar toilette dinne ya sa ta yi sauri tagama abun da za ta yi tare da dauro Alwala ta fito jikin ta daure da tawul.

Asiya da Anty tare da yayar antyn su zaune suke sun zabga uban tagumi ganin ta fito ne 'yasa suka nufo ta kallon ta suke cike da damuwa da tausayawa.

Anty ta ce munga kin dade toilette baki fito ba shi ne hankalin mu ya tashi.

Murmushin yake ta yi ta ce wallahi wanka na tsaya na ba ta lokaci Ko ?

take tambayar anty muryan ta asanyaye.

Eh kinbata lokaci kin san yamma ta yi ya kamata ace mun shirya ki dan Abba ya ce za a zo daukan ki da an yi sallah isha'i.

Rahama saida gaban yafadi Jin za a zo daukan ta azuciyar ta sai fadi take nashiga uku Ko wane ne mijin nawa.

Kallon anty ta yi lokaci daya Idanun ta suka ciko da kwalla ta ce to anty bara nayi sallah sai inshirya.

Asiya dake mata kallon so da kauna da tausayin aminiyar ta cikin sanyi murya ta ce bara inje gida insanar zanbiki gidan mijin naki dan acen zan kwana da safe Ko zuwa yamma In Allah yakaimu sai indawo gida.

Cikin nutsuwa take maganar.

Cike da gamsuwa da bayanan ta anty ta ce hakan ma ya yi kinga kinsamu kidan tausasa mata zuciya kin san abu da zafi zafin yake yanzu azuciyar ta.

Asiya wucewa ta yi Rahama ta ce saikin dawo dan Allah karki dade.

Gyada mata kai ta yi cike da tausayawa.

Anty ta ce gaskiya Rahama kinyi dacen kawar arziki kinga yanda take kuka sossai dazun kuwa da akace anfasa daurin auren ki da Adamsy andaura da Abdul samad.

Rahama sunan Abdul samad taketa juyawa cikin zuciyar ta dan sai yanzu tasan sunan mijin da aka aura mata.

Yayar anty ta ce ai abun da Asiya ta yi Allah ne kadai zebiyata ance sai hali yazo daya ake abota.

Ita wancen me bakar kafa ai ba ta da kawayen arziki tana kallon salma data dukar da kanta kasa.

Rahama na idar da sallah nan da nan aka shiga shiryata me makeup Anty takira da ƙyar Rahama tayarda akai mata makeup din saida taga ran Anty yabaci Sannan ta amince.

Wani hadadden shadda gezner na kwatano wanda akalla kudin sa zekai kimanin dubu dari.

New design ne new fashion.

Riga da siket akai mata shaddar maroon color ne yasha ado da goldin color ba ƙaramin kyau ya yi mata sossai ajiki ba.

Da yake tanada tsayi ga ta farar mace mai cikar halitta bob.

Ga hip

Nan da nan wannan dinki yazauna mata dass a jikin ta tare da fitar dawani sirritancen kyawun Rahama wanda ya sa dakin suka yita ihu suna shewa hade da tafa hannayen su.

Suna ta fadin azo aga Amarya Rahama wallahi saide haushi saide a mutu.

Salma ba ƙaramin tashin hankali tashi ga ganin yayar ta yanda tasha kyau harta gaji gashi sai habaice habaice suke ta jifan ta dashi.

Cikin zafin nama takaraso inda suke ta ce wallahi kunji kunya bandaku sakar karu ne taya zaku yita habaice habaice inba tsoro ba kufito fili mana tana magana cikin bacin rai.

Kuma Rahama da kuke karewa kune bakusan wacece ba to wallahi karuwar gida ce bari ku gani.

Sake da baki kowa ke kallon ta cikin dakin. dauko wayar ta yi ta shiga whsap tare da nuna musu hoton da Rahama tana kwance kan wani.

Anty karban wayar ta yi tana kallo zoomin din hoton ta yi taga eh lallai maganar salma haka ne amma ahoton yanuna kamar faduwa suka yi.

Tsaki take ta jerowa tare da je fa mata wayar ta.

Ta ce wannan hoton yana Daga cikin mugayen halayen ki ke ce kika dauka dan ki ba ta mata suna.

Kuma Daga gani kindauka ne dan ki nuna zallan kiyayya ki agareta dadina da Abun kema dai andaura miki aure ki tafi mun gani Ko zaki iya zaman auren tafada cike da Jin haushin ta.

Mu wallahi yanzu muka fara ganin kimar ta da darajan ta.

Rahama da duk abun da ake tana jinsu banda kuka babu abun da take yi.

Azuciyar ta sai maimai ta kalmar karuwan gida da salma ta fada take.

Afili kuma kallon su anty ta yi ta ce ku barta da halin ta ni ba zan ce mata komai ba.

Tayi magana cikin raunin murya da tafasan zuciya.

......

Kasar Gabon.

Baba salihu zaune yake gaban talabin sa yana kallon tashar Arewa 24

Lumshe Idanun sa ya yi yana tunanin halin da sheik ya shiga na rashin dawowar sa.

TV nata aiki shikadai ba tare da ya maida hankalin akai ba Remote yadauko yana kokari kashe TV yaga wani.

Sanarwa.

Yaji ana gabatar da labari da dumin dumin sa.

Shahararen malamin Adinnin nan mai suna sheik Abdurrazak kabeer hizqeel makarfi.

A yau Ranar juma'a aka daura auren yayan sa ga kadan Daga ciki dafatan masu kallo suna biye damu.

Dan Jaridan ke fade alaman gabatarwa

Baba salihu daya shagala da kallon TV sakin remote ya yi Daga hannun sa tare da gyara zaman sa.

Ya tattara nutsuwar sa wajen kallo.

Hasko video daurin auren dayaga an yi yanata baza idanu koze hango sheik acikin su.

Ganin mai martaba acikin video ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba.

Afili ya ce Abba meya kaika kano 'ba tare da ya rufe bakin sa Yaji ana fadin andaura auren Rahama da angon ta Abdul samad.

Bisa sa daki dubu dari.

Salma tare da angon ta Al'amin zumbur ya Mike Daga zaune yanata safa da marwa cikin tsakiyar falon.

Banda wasi wasi babu abun da zuciyar sa take yi ya ce to ainaji Adamu zata aura ya akai aka fasa auren kuma wani Abdul samad ne me sa'a haka daya samu Rahama.

Kuka yake da iyakar zuciyar sa ya ce sheik ban kyauta maka ba.

Bancika Adali ba gashi bankawo ɗana ba Sannan Rahama ba ta auri wanda takeso ba.

Toshi wane ne wannan Abdul samad din yake tambayar kansa.

Cije labbansa ya yi ya ce shikuma Abbana waya gayya ce shi daurin aure.

Rasa me bashi Amsa ya sa ya danna kira gun me bashi labari.

Wayar nata ring ba a daga ba zama ya yi kan kujera tare da dafe kansa dake masa ciwo.

Ya ce shekara nawa rabon da inga fuskar mai martaba sai yau yau ma din a TV

Uhmm inama ace zan iya danaje gareka mai martaba ya fada cike da raunin murya.

 dattijon gidan sa yataho gaban sa tare da durkusawa ya ce ya shugaban Adalai mai tausayin talaka.

Naganka cikin matsanancin damuwa kozaka iya faɗa min damuwar ka.

 kansa adauke yake.

Cikin tausasa murya yake magana.

Baba salihu ya kalle sa. Ya ce haba malam Musa nace kadaina durkusa min Daga masa hannu ya yi Alamun ya tashi Daga durkeshen da yayi.

Kallon dattijon yake wanda zasuyi tsara ashekaru kokuma ya girme sa.

Ya ce bismallah zauna.

Zama dattijon ya yi suna fuskantar juna.

Baba salihu a jiyar zuciya ya sauke ya ce bari inbaka labarin wani butulcin ɗana aikata a kano.

Dattijon kallon sa yake yana jujjuya kalaman sa ya ce ranka yadade ina sauraren ka.

Tare da maida hankalin sa a kan sa.

Dan numfasawa baba salihu ya yi ya ba shi labarin sheik da auren daya amince zebashi dakuma dalili baro kasar.

Dattijon ya ce ya shugaban Adalai ai wannan ba butulci bane kaddara ce haka Allah yatsara wannan yarinyar bazata auri danka ba kuma bazata auri wanda take so ba.

Naka kawai kabisu da Adua.

Sossai baba salihu Yaji dadin kalamin wannan dattijon da kansa yadauko lemukan kwali Daga frij din falo tare da tsiyaya musu a cup ya mika masa.

Shima yana shan na hannun sa.

Dattijon mamakin saukin kai irin na baba salihu yake duk da ya san shi jinin sarauta ne amma saukin kan nasa ya yi masifar yawa.

...

Kano.

Yarima Samad da ƙyar aka shiga da shi cikin gida ya yi daidai da shigowan mai martaba da su mamy da khadija da Ahmed.

Mama karama tana gaba.

Sani baban marwan yanata buga uban sauri dan ji yake kamar ze mutu dan bakin ciki

Ya ce kashin shi yabushe tun da aka daurawa Abdul samad aure.

Cikin hanzari ya shiga gidan tare da kama hannun dan sa Marwan suka shige dakin sa.

Domin zantawa.

Faruk nan tsakiyar falo suka zaunar da Abdul samad.

Sunata buga masa baya Alamun rarrashi.

Aminu ya ce Kayi hakuri wallahi Alkhairi ze zame maka wannan auren.

Jajayen Idanun sa da suka kada ya dago yake kallon Aminu cikin rawan murya ya ce Alkhairi ne kace Ko yana me watsa masa mugun kallo.

meyasa ba ka bari andaura auren da kai ba sha sha kawai wallahi natsani wannan auran.

Bari kuji kaida Faruk kune ku rirrikeni da karfin tsiya dan na so inje na murje bakin waliyin Amaryan kuka hana to wallahi kuma kun ciyo bashi.

Kokarin tashi yake zeshige dakin sa.

Yaji muryan mamy ta buga masa uban tsawa saida kowa cikin gidan ya firgita dan basu taba ganin ta cikin wannan yanayin ba tun da suke.

Cikin Azzama takaraso falon cikin bacin rai ta ce kai uban wane ne da za ka ce sai abun da kake so shi za ka samu.

Tana me tsare shi da Idanun ta da suka kada Daga fari zuwa ja.

Cak Yarima Samad ya tsaya yana sauraren kalaman mamy da Sam basu sassauci a ciki.

Taci gaba da magana cikin bacin rai da Daga murya ta ce kai harka kai mai martaba ya zartan da hukunci a kan ka.

Kaja da maganar sa har kana kokarin zuwa kunyata shi gaban dunban jama'a dan kawai ya ce adaura maka aure.

Wai ma in tambayeka kai a zaton ka haka za ka kare rayuwar ka ba tare da aure ba.

Kayi kuskure Samad tun wuri ka canza tunanin ka.

Umarnin da zanbaka yanzu shi ne maza ku dau motoci guda goma kuje daukan Amarya kuma wallahi tallahi kaje har wajen uban Amaryar ka. ka gaishe su tare da nuna musu farin cikin ka.

Cikin zazzare idanu Samad......

 

2️8️

Cikin zazzare idanu Samad ke kallon Mamy kuka ne kawai beyi ba amma da duk Alamu yanuna soya ke ya yi kukan dan gani yake ba ƙaramin dauriya ya yi ba tun daga wajen daurin auren har zuwan sa gida.

Mamy gaba ta yi tana ta fada khadija nabiye da ita abaya.

Mai martaba da mama karama kallon Samad suke yanda yakoma ƙaramin yaro bilhakkin kuka yake da iyakar gaskiyar sa.

Dafashi mai martaba ya yi cikin Rarrashi ya ce Abdul Samad aure fa ba mugun abu bane yarinyar nan da aka aura maka ita wallahi tanada tarbiyya kar ka kayi bakin ciki da auren ta yakai jikana abun sona.

Yarima Samad tuno bacin ran dayaga kan fuskar Mamy game da shi karo na farko Arayuwar shi.

Fesar da numfashi ya yi yana kallon mai martaba ya ce cikin sanyin murya dan kada Mamy ta jiyo takara fitowa kallon mai Martaba yake zuciyar sa na suya ya ce banda Abun da zancemaka.

Domin zuwan ka shi ne silan rugujewan farin ciki na tsarina Abubuwan dake gabana sokake su ruguje lokaci daya yana kallon mai martaba cikin son nuna masa rashin kyautawan da ya yi mashi.

Mai martaba ya ce yanzu Abdul Samad me kake so in maka daze sa kaji na maka Adalci yana kallon sa soyake yaga iya gudun ruwan sa.

Sassaita muryan sa ya yi ya ce ni dai kawai kaban daman insake ta kawai yana turo baki gaba.

Abun da ya manta da belura ba tun firan su da mai Martaba Mamy tana jinsu dan ba ta karasa dakin ba ta tsaya.

Sai ji ya yi ta ce tabbata ce wallahi Abdul Samad kaban mamaki wallahi koda wasa ka saki yarinyar nan saina tsinemaka Albarka.

Arazane yake kallon ta yanzu yagama tabbatar wa komai Mamy tana iya yi masa a kan wannan auren.

Hakuri ya shiga ba ta harda durkushe gwuiwowin aka sa ya ce.

Ya ce dan girman Allah mamy ku yafe min hankalina da tunanina sun gushe ban san me nake aikatawa ba naroke ku yana mai dafa kafafun ta.

Mamy ta ce inace nace ku tafi dauko Amarya ne meka saura kake yi a gidan nan karfe tara saura.

Mai Martaba kama hannun Samad ya yi suka yi dakin su da shi tare da Mama karama.

Sunata bashi hakuri ya rungumi kaddara ita ma yarinyar da aka aura mashi ba a son ranta hakan ya faru ba.

Da ƙyar suka shawo kansa.

Yana fitowa falon kaida ka kalle shi ka san yasha kuka iya ransa dan Idanun sa sun kumbura.

Faruk yaba umarnin suje su gayyato abokan nasu.

Parking space yatafi yana duba motocin da za a dauka dan dauko amarya.

Faruk cikin tsokana yakaraso wajen yana murmushi ya ce ina nima me Martaba ze min irin wannan auren wallahi ɗana more.

Ko kallon inda Faruk yake beyi ba bare ya sa ran ze masa magana 'Kira ya kwada mai magadi yabada umarnin maza agoge motocin sa guda hudu duk sunyi kura.

Babu ba ta lokaci mai gadi yashiga aiwatar da abun da uban gidan sa ya sa shi.

Mamy Ko zaune take A falo duk takosa a kawo amarya waya take yi acen kwatano ta sanarwa yayar ta batun auren Abdul Samad.

Yayar ta taita fada ta ce ai wannan munafuncine daman tana sane da auren shiyakaita kanon.

Da ƙyar Mamy ta shawo kanta taita mata Rantsuwa, har ta ba ta labarin abun da ya faru.

Yayar ta ta ce yanzu kina nufin Maryam bazata auri Abdul Samad ba.

Cikin Rarrashi mamy ke nuna mata ita ma bayin kanta bane Amma suyi hakuri inhar matar shi ce ze aure ta koda a ta biyu ne.

Daga haka suka yi sallama.

***********

Cen garin kwatano.

Maman Maryam sai safa da marwa take ta ce wallahi zama be ganni ba.

Duk shirin danake yi a kan yaron nan duk yatafi abanza kenan.

Wallahi dani suke harshi da uwar tashi ya za ai taki nata taso na wani Saboda Allah.

Maryam data shigo da fara'ar ta ta ce mama yana ganki ahaka lafiya kuwa.

Tana kokarin ajiye jakar ta kan kujera.

Maman maryam datarasa taya zata sanar mata mummunan labarin nan ta ce ai Mamy ce wallahi ta batamin Rai.

Maryam da Sam batasan kwanan zancen ba ta ce to me tayimiki ne kifadamun ita da ba ta gari tafada cikin son Jin ba asi.

Maman maryam cikin rawar murya ta ce yata Abdul Samad ya daura Aure.

Maryam Sam kunnuwan ta toshewa ya yi gabadaya ta ji garin na juya mata kamar haka jikin ta yadau rawa kamar mazari Idanun ta lokaci daya yacika da kwalla.

Cikin kuka ta ce dan Allah mama kice min wannan labarin tatsuniya ce ba gaskiya bane ki gayamin in mafarki nake in farka.

Mama ta dafata tare da zama kusa da ita ta ce kalleni da kyau suka hada idanu ta ce maganar nan nima yanzu ƙanwata takirani take sanar min

Kuma ta sanar dani ba a son ransa akai auren nan ba..

Maryam ta ce shi ke nan mama tawa takare banda sauran amfani a duniya rayuwa ta a kan shi na tsarashi bana sauraron kowa a kan son da nake masa.

Mama ta ce karki damu wacce ya aura da kafafun ta zata bar gidan Ko ince miki saki uku zemata yanda babu gyara.

Maryam ta ce dagaske mama zaki iya yin haka tana kallon uwar ta cikin son tabbatar da hakan.

Ta ce kwarai kuwa kedai wuyan ba a kawota kwatano ba ke koda ba tazo ba wallahi ba zan barta ba.

Kisa Aranki Abdul Samad naki ne ke kadai.

Rugume maryam ta yi tana me tabbatar mata da niyyar ta ta yi hakuri...

Garin kano.

Tsaf aka shirya Rahama wani goldin mayafi anty ta yafa mata tare da feshe ta da turaruka masu kamshi.

Anty da kanta takai Rahama gun sheik da yan uwan sa.

Nan suka shiga yi mata nasiha tabi mijin ta.

Yi nayi bari na bari.

Karta yi wasa da riko da Addinin ta Azkhar ta rike su da muhimmanci Domin kariya ce Daga dukan masifu.

Kanin sheik hussain ke mata fada wajen saida kowa jikin shi ya yi sanyi maganganu masu ratsa zukata ya rinƙa fadi.

Suka ba sheik daman ya yi mata nasiha.

Sheik cikin kuka ya ce Rahama Allah ya yi maki Albarka ɗuk cikin yaya wallahi kincire tuta biyayyar ki da hakurin InshAllah zekai ki da nasara.

Duk Abun da zanfadi yan uwa na sun fada.

Allah yazaunar daku lafiya dake da mijin naki.

Da ameen kowa ya amsa awajen da ƙyar aka banbare Rahama Daga jikin sheik tana kuka shima yana kuka....

Jin Horn din motoci a kofar gidan ya tabbatar wa jama'ar gidan yan dukan Amarya sun iso.

Asiya rike da hannun Rahama suka shigar da ita gidan tare da kai ta dakin mama dan ta yi mata adua.

Mama kuka yahanata yin magana dan babu abun da take tunowa sai wuyar da Rahama tasha hannun ta da salma gashi yau za su rabu.

Da ƙyar tafurta Allah yazaunar daku lafiya.

Sossai gidan suke ta binta da fatan Alkhairi.

Abokan Abdul Samad sun kai su talatin suka zo

Kowanne su da mota yazo 'motoci talatin suka yi parking kofar gidan.

 hayaniya ya gauraye unguwar gabadaya

Banda busan Algaita na gidan sarakuna babu abun da ke tashi a kofar gidan.

Matan layin da mazan unguwar cika akayi gun kallon wasan sarakuna.

Kusan minti shabiyar suka dauka awajen sunata wasanni da busan Algaita masu daukan video da manyan wayoyin su.

Sunata yi.

Abdul Samad hayaniyar ba ƙaramin damun shi yake yi ba.

Sannun a hankali ya bude motar tare da zira kafafun sa kasa da yake shanye da takalmi haf cover ba ƙaramin haduwa ya yi ba dan sanye yake cikin shadda gezner goldin color.

Ya tako kafarsa wajen motar gabadaya kallo ya dawo kan sa.

Hannun ya yi masu Alamun ya isa haka.

Nan da nan suka bari.

Surutu ake ta yi cikin unguwar sai fadi suke kodai shi ne angon.

Wasu nacewa anya kuwa shi ne wannan kyakaywan balaraben dayar ta ce ai ita ma Rahama badaga baya ba.

Wallahi Ko ya'akai shi ne angon bakiga shigar shi bane suna nuna shi da hannun.

Abdull Samad tambayar gidan ya yi aka nuna masa kofar shiga kai tsaye ya cusa kansa gidan Abokan sa gabadaya suka take masa masa baya.

Cike da izzar da takama yake tafiya kallon yanayin gidan yake da tsaren tsaren ta yana Girgiza kai.

Hussain ya fara musu la le Barka da zuwa shida Abubakar jagora suka yi masu dakin sheik.

Hussain nagaba suna biye da shi abaya.

Komawa ya yi tsakiyan Abokan sa ya musu hannun da su fara shiga.

Sallama dauke abakin su.

Suka shiga dakin.

Neman waje suka yi duk suka zazzauna.

Cike da girmamawa suka gaida sheik da yan uwan sa.

Sheik daya kasa gane wane ne angon acikin su dan Abdul Samad tsakiyan su yazauna kansa aduke yake banda latsa waya babu abun da yake yi.

Sheik ya ce madallah kunzo daukan Amarya Ko.

Ina surukin nawa yake ?

Ya tambaya Cike da bukatuwa.

Faruk ya yi murmushi ya ce Sheik imam gashinan tsakiyar mu tare da dafashi.

Ya ce kai ango Dago kai baban Amarya na magana yafada Cike da kulawa.

Dago kai ya yi Daga latsa wayar da yake yi.

Caraf Idanun su suka tsarke cikin juna shida sheik.

Sheik y..

2️9️

Sheik ya ce MashaAllah maraba da ɗana ku dan matsa masa mana.

Nan da nan abokan sa suka masa Daga baya dan tasowa ya yi yana murmushin dole cike da ladabi ya gaida sheik da yan uwan sa.

Suka amsa masa cike da farin ciki sheik ba ƙaramin Jin dadi ya yi ba ganin wannan shi ne mijin Rahama godiya yakewa Allah acikin zuciyar sa.

Ya tabbatar da yaro ne nagartacce da nutsuwa kamar matar shi Rahama.

Sheik da yan uwan suka shiga yiwa Abdul Samad nasiha ayita hakuri intayi badaidai agyara mata.

Cikin aro jarumta ya ce sheik imam mun gode

Da wannan amanar da kabamu InshAllah zamu rike.

 dan yagane sheik shi ne ke basu sallar juma'a awannan masallacin.

Nan da nan suka tashi suka fito abokan da da shi kan sa waje suka koma suna jiran a kawo Amarya.

A ka'idar sa Yarima Samad baya wuce karfe goma na ɗare beyi barci ba.

Amma gashi yau Saboda wata an dagula masa lissafi tsaki yake ta jerowa shi kadai.

Abokan ango sai fadi suke ayi afito da Amarya ɗare nayi akwai masu iyali acikin mu.

Wani cikin abokan ya ce aini yau mata ta nashiga uku inna koma gida cewa za ta yi naga kawar Amarya ne shi ya sa na dade a waje.

Inama zan samu koda kanwar Amaryar ne.

Cikin su wani ya ce amma kai dan iska ne mata biyun suna caza maka kai shi ne za ka kara gafara cen dallah.

Duk hayaniyar da akeyi ɗuk Jin sa yake a takure.

Guda yaji yana tashi sossai Asiya rike da hannun Amaryar, matan gidan duk sun fito domin raka amarya dakin ta.

Kakar Amarya zubaida ta ce ku bude mana mota mu shiga ɗare nayi.

Cikin kosawa take magana.

Faruk ya ce kaka aiba mota daya zaku zauna keda amaryar ba.

Kinga angon ta cen nan zata shiga bayan mota tazauna drever ya jasu.

Asiya ta ce ikon Allah aini sonake mu zauna tare.

Duk juyin da zasuyi abokan ango suka ce wallahi saide Rahama tashiga motar da Abdul Samad yake.

Abdul Samad da duk abun da suke fade yana jinsu ba daman ya fito yaci uban abokan sa yaga yan uwan ta duk suna wajen hakan ya sa ya kame bakin sa.

Jin anbude mota ya sa ya dukar da kansa kasa Ransa a ba ce yake duk ya takura.

Muryan Asiya yaji tana cewa kishiga da kafar dama.

Tabe baki ya yi yana fadin iyayen iya yi wai kafar dama daman ance ɗana hagu zata shiga yana maganar zuci.

Shigar da ita motar suka yi tare da rufe musu.

Gabadayan su suka shishige motocin su tare da diban iyaye mata da kawayen Rahama.

Tafiya ake inda drever ya sa wakar Nura m inuwa.

Abdul samad da tun shigowan Rahama cikin motar ya matsa sossai yanda ka san su shida ne a motar.

Ita kuwa banda kuka babu abun da take yi kukan Rabuwa da Anty da Abba da mama.

Sheshekar kukan ta yacika masa kunne ya Salam ya furta a fili dago kai ya yi kamar zece wani abu sai ya fasa.

Yana cije labban sa...

Sun sha Tafiya kafun su Iso unguwar.

Horn motocin suka yi nan da nan aka bude musu gate babu ba ta lokaci suka shigo haraban gidan.

Abdul Samad da duk ya kosa su Iso nan da nan yafita a motar yanata zuba uban sauri zeshige dakin sa.

Ganin Mamy dasu khadija da Ahmed ga mai martaba da baban Marwan Waziri duk suna falo.

Ina za ka ne kake ta zuba uban sauri cikin sanyi murya ya ce Mamy wlh barci nake ji kinga shadaya saura.

Yana kallon agogon hannun sa.

Mamy dake kallon ikon Allah ta ce ka sallami abokan ka ne kuma Amaryar dawa za ka barta anan ta jefo masa tambaya.

Mai martaba yaji dadin zafi zafin da take masa dan shi ne yabata wannan shawaran inhar sun dawo tabude masa wuta.

Cikin kasa da murya ya ce Mamy duk dakunan gidan nan ace babu daki sai dakina pls dan girman Allah kubarni wallahi kaina ke ciwo.

Shiru suka yi duka falon Mamy ta ce na ji amma nayau ne gobe saika san yanda za ai dan bazata kara kwana wani dakin ba

Gyada mata kai ya yi Alamun yaji.

Jin guda masu shigowa ya sa mamy yin shiru.

Murna fal Aranta abun da ba ta kawo shi kusa ba.

Shi ne yau ya tabbata.

Nan da nan gidan ya hargitse kaka zubaida takama hannun Rahama ta yi mata jagora zuwa falon nan ta damka wa Mamy amanar ta da Mama karama.

Mama karama Saboda tsabar Jin dadi ta ce Ai kishiya ce kawai tazo mu gwada wane ne gwani awajen angon namu.

Nan da nan akadau shewa anata tafi ganin Mama karama takama Rahama ta rungume tana kukan farin ciki.

Shiko Abdul kamoshi akai Daga tsayen da yake suka kawo shi tsakiyan falo shiru kake ji bakin ya mutu.

Nan da nan aka shiga musu nasiha mai ratsa zukata danshi Abdul Samad duk abun da ake fade ba fahimta yake dan ya sa epeace a kunnen sa.

Yan kawo Amarya suka fara watse wa harda kaka zubaida duk sun wuce sunata yaba hankalin surukan Rahama da kuma gidan daulan data shiga dan ma basu shiga cikin gidan sunyi kallon daulan duniya ba...

Asiya zaune kusa da Rahama Khadija sai janta da hira take ta ce wai Anty Rahama bazata bude Idanun ta nakosa inga matar yayan mu.

Mamy ta ce sarkin zumudi keda zaku kwana gida daya da ita.

Sai Asannan Abdul Samad yatashi Daga zaunen da yake yana kallon Mamy cikin muryan me Jin barci ya ce.

Mamy zanje inkwanta kin san gobe zamu je kwatano inada case inaga tare zamu koma daku yafada yana me barin falon.

Kallon shi Mamy take ta ce ka je kaba Matar ka masauki ita da kawar ta.

Nan da nan yaji Ransa yakara baci da to ya amsa mata.

Kallon Asiya ya yi ya ce ku tashi mu je bejira cewar su ba ya yi gaba.

Asiya da Rahama tashi suka khadija nabiye dasu abaya dan takosa taga fuskan Rahama.

Dakin dake kusa da nashi ya nuna musu dan shikadai yarage wanda keda kayan bukata a ciki.

Yana bude dakin ya shiga suka take masa baya.

Asiya sai kallon yanayin tsaruwar dakin take komai na adon dakin ja ne hâtta zanin dake shimfide saman gadon ja ne.

Uhmm ta ce kudi na inda suke Ni dai fatana Allah yazaunar dasu lafiya tare da Rahama.

Shiko yana gama nuna wa Asiya abun da ze nuna mata yafice haryakai bakin kofar fita.

Asiya ta ce ji mana tsayawa ya yi yana sauraren ta ba tare da ya waigo ba.

Ta ce duk yunwa muke ji rabon mu da abinci tun na safe kafun daurin aure.

Uhmm ya ce a zuciyar shi baga irinta nan ba yau yau dinnan aka tare amma har za su fara ba ni aiki..

Afili ya ce kiyiwa khadija magana zata gayawa faruk nizanje inkwanta

Ya kara gaba.

Asiya ta ce uhmm Rahama wannan mijin naki badai izza ba.

Khadija ta ce wlh haka yake amma fa yana da saukin kai wanda besan halin shi ba haka zedauka.

Pls matar mu ki Daga gyalen nan inga fuskar ki.

Rahama Daga gyalen tayi.

Khadija tarude Ta ce Allah mai halitta wannan zankadediyar mata yaya na ya auro ta ware manyan Idanun ta.

Wallahi anty Rahama ke kyakyawa ce aji farko ina m'a insamu Rabin kyaun naki.

Sossai Rahama ta ɗara lokaci daya ta ji khadija ta kwanta mata arai.

Asiya ta ce aikinfi Rahama kyau khadija.

Mâke kafada khadija ta yi ta ce inafa saide in zagina kike.

Fita khadija ta yi dan ta sanarwa faruk bukatar Asiya.

Cen ɓangaren Yarima Samad kwance yake a kan gadon sa.

Duk yanda yaso barci yadauke sa yakasa..

Tashi Daga kwanciyar ya yi yazauna yana cijje labbansa ya ce to shi wannan auren me ake nufi da shi dan shi wlh bega abun da zeyi da yarinya ba.

* * ******

Adamsy yana ta safa da marwa cikin dakin sa.

Gabadaya hankalin yadawo jikin sa.

Kuka yake yana fadin wayyo kaicona yazanyi ina son Rahama ban san ya akayi na aikata haka ba..

Fita Daga dakin sa ya yi direct dakin su Daddy yatafi ya iske su zaune shida mommy.

Kallon shi suke yanda yabi ya rame na lokaci daya Mommy ta ce lafiya ina za ka je adaren nan.

Jikin a sanyaye yakaraso gaban su ya durkusa ya saki wani marayan kuka ya ce Daddy kayafemun na tafka babban kuskure dan Allah karku yi fushi dani wallahi ina son Rahama Daddy dan Allah ka taimaka min Adawo mun da Rahama ta.

Daddy cikin tashin hankalin furucin ya ce.....

3️0️

 Daddy cikin matuƙar kaɗuwa ya ke magana ya ce "ban san ba ka da hankali ba kuma kai daƙiƙi ba ne sai a yau.

 Tana matar wani za ka ce haka in shaye-shaye ka fara to maza kadaina tun wuri na faɗa maka wallahi lefen nan dana haɗa gobe in Allah yakaimu zamu kai gidan mijin nata.

 Mommy Idanun ta ya ciko da ƙwalla yanzu Adamu tausayi ya ke ba ta ɗan nata ta lura kamar iska ne ke damun shi.

Cikin sassauta murya ta ce Daddy Adamu dan Allah kayi haƙuri na lura yaron nan kamar bayin kan shi ba ne.

 Ta faɗa cike da damuwa.

Dr Abdullahi ya juyo kanta yana zazzaga masifa ya za ayi yaron nan ya wulaƙanta mu a idon duniya ya sa mun tara jama'a wajen ɗaurin aure tsabar hauka ya ce yafasa harda faɗin in an ɗaura zai yi mata saki uku a nan wajen Sannan ki buɗe baki ki ce bayin kan shi ba ne,

Laifina ne kenan yafaɗa ya ƙarashe maganar nan cikin fushi.

 Ficewa ya yi daga ɗakin y tare da barin gidan baki ɗaya cikin ƙunar rai dan da wuya ya yafewa Adamu wannan abun da ya yi masu.

 Mommy banda kuka babu abinda ta ke yi kama hannun ɗan nata ta yi ta ce "kayi haƙuri Rahama ta yi maka nisa,

Ka nemo wata matar sai a ɗaura maka aure da ita.

 kuka ne ya kwace mashi ya ce " ba na jin zan iya yin wani aure mommy na haƙura kawai ya ƙare furicin yana mai ficewa daga ɗakin.

 Kallon shi ta ke harya fice zama ta yi dirshen kan kujera tare da zabga uban tagumi.

*******

Kashe gari

 Tun da Asubar fari Rahama ta tashi ta shiga toilette ta yi wanka tare da ɗaure Alwala kallon Asiya take da ke ta sharara barci ba ta san ma inda kanta ya ke ba.

 Murmushi ta yi tare da ƙarasowa inda ta ken cike da so da ƙaunar Aminiyar ta tashafa fuskar ta da hannayen ta dake da damshin ruwa.

 Sanyin da Asiya ta ji ya sa ta bude Idanun ta ta sauke su a kan Rahama da ke ƙoƙarin ta da sallah.

Mika ta yi tare da karanto adu'a tashi Daga barci.

 Alhmdulilahi lazi Ahyana ba ada ma Amatana wa'ilaihin nushur.

 Cikin hanzari ta faɗa toilette ko da ta fito ta iske Rahama ta idar tana kan darduma.

 Asiya ta fito ita ma Daga toilette din bayan ta idar da sallah takoma gado takwanta.

 Rahama tunani ta keyi ina zata samu Alkur'ani mai girma hakan domin dabi'ar ta ce karatu bayan sallah asuba.

 Tana fitowa kofar ɗakin tunanin ta ke ina ne ɗakin khadija ganin ɗakin kusa da ɗakin ta ta yi zaton Ko nan khadija take.

Cike da nutsuwar ta ta doka sallama ganin shiru babu amsa banda sanyin AC da kamshin turare babu abun da ke tashi a dakin.

 Tana fita Daga ɗakin ta jawo ƙofar ta rufe,

Ƙoƙarin sauka ta ke Daga kan step domin tasa A ranta sai ta yi karatun nan.

 Faruk ya shigo sanye ya ke da farar jallabiya kallon ta ya ke ya na son ya tuno ina ya taɓa ganin fuskar nan.

 Kallon ta ya ke lokaci babu Ko kiftawa domin kyawun ba ƙaramin tafiya da imanin sa ya yi ba.

Sassaita nutsuwar sa ya yi ya ce "baiwar Allah kina cikin ƙawayen amaryar da suka kwana nan gidan kenan.

 Kasa ba shi amsa ta yi sai dai ta gyaɗa masa kai Alamun haka ne.

 Dan Allah kozan samu AlKur'ani taf faɗa Cike da buƙatuwa.

 Eh mana zaki samu ɗan jirani a falon yanzu inje in ɗauko miki dafatan amaryar Samad tana lafiya shiru ta yi ba ta bashi Amsa ba.

Cikin hanzari ya yi hanyar dakin nasa.

 Mamy ta fito dan hada wa Amarya da kawar ta break taga Rahama a falon itama mamy ba ta iya sheda ta fitowar khadija Daga dakin taga ta tafi aguje ta rinsina tana gaisheta anty Rahama antashy lafiya.

 Murmushin ta yi ta amsa da lafiya.

Mamy da take sake da Mamy daman wannan ita ce matar Da Samad ya aura amma sai lallabashi ake kamar wanda akaba kashi.

 Rahama har kasa ta durkusa cike da ladabi ta ce mama ina kwana.

Cikin Jin dadi Mamy ta ce lafiya lau diyata ya kwanan bakun ta cike da kunya ta yi shiru.

Faruk yakaraso falon tare da miƙa mata Alkur'ani.

Tana karba ta yi masa godiya tare da barin wajen.

 Gaishe da Mamy ya yi ya ce Mamy danna cikin kawayen Amaryan ne.

Mamy dake kallon yanayin sa ta ce yanzu kana nufin ba ka san Matar Abdul Samad ba.

To ita ce.

Mamaki yake ya ce daman akwai kyakyawan mata irin haka a duniya ni dai na dade bangani ba.

 Marwan tun safe yake ta kiran layin Salma yana ring ba a ɗagawa.

Tsaki yaketa jerowa ya ce ita wannan banzar ina ta ajiye wayar ta ina son ta turomin hotunan nan ban san waya dau wayata dana baba na ba.

Ya goge su koya akai akwai wanda yake bayan mu.

 Kara kiran layin Salma ya yi cikin sa'a ta Daga.

Bayan sun gaisa ya ce kwana biyu kona kira bana samun Ki inafatan dai lafiya Ko.

 Daga can ɓangaren ta ce lafiya lau ne.

Marwan ya numfasa tare da Tsayuwar sa ya sanar. Mata yana bukatan ta sake turo masa hotunan ɗaya tura mata.

 Salma cikin Jin haushin sa da bakin cikin dake cinta ta ce nifa tun Ranar na goge awaya ta naga bazasu mun Amfani ba tafada cikin bacin rai.

 Marwan ya ce " yanzu gayamin inda kike ina son inzo wajen ki zamu dan tattauna kin San mutumin ɗana dauka hoto da yayar ki wanda naga kin kyasa ya yi aure a jiya.

 Riƙe da baki Salma ta ce ya yi aure fa daman cen ansa masa 

rana ne ?

 Marwan ya ce "A'a ai ɗiyar wata malami ne da za a daura mata aure da wani mai suna adamu sai ya ce yafasa shi ne aka ba Abdul Samad. 

Banda innaliahi wa'inna il raj un 

Babu abun da Salma take furtawa cikin kukan da ya kwace mata ta ce yanzu kana nufin wannan balaraben shi ne ya Auri Rahama. 

Marwan da mamaki yacika shi ya ce eh sunan matar da 'aka bashi ce. 

Kin santa ne ya jefo mata tambaya cike da rudani. 

Kwarai kuwa niko nasan ta yaya ta ce uwa daya uba daya. 

 Kuma ita ce awannan hoton daka dauka. 

Sallamar sheik ne ya sa takasa cigaba da magana kallon ta yake yake yana kallon wayar hannun ta cikin tsawa ya ce dawa kike waya. 

Bakin ta na rawa ta ce wata kawata ce. 

 Ki je waje mijin na ki yazo Daga haka ya fi ce Daga dakin domin sun zanta da anty kan kai kayan Rahama. 

Salma banda kuka babu abun da take yi kaicona ni Salma ɗana sani keya ce. 

 Wallahi danasan wannan mijin zaki aura dako ba zan taba rabaki da Adamsy ba. 

Tana ajiye wayar ta tadau gyale ta yafa kai tsaye zauren na su taje ta same shi. 

Cikin faɗuwar gaba takaraso wajen shi. 

 Kallon shi take Daga sama har kasa tana Girgiza kai. 

 Al'amin shima ita yake kallo cike da tsana yana ayyana irin wahalan daze ba ta intaje gidan shi. 

 Mugun kallo yake binta da shi cikin zafin rai da tafarsa zuciya da takura mishi da a kayi dole sai ya je wajen ta. 

 Ranshi A ɓace ya ce ke Salma kidauka watan mutuwar ki ce takama. 

Karuwar gida. 

 Cikin zazzare idanu nan da nan suka ciko da kwalla ta ce "bangane karuwan gida ba. 

Dawa ka ga ina karuwan ci. 

 ba ta gama rufe bakin taba sai ji ta yi ya wanke ta da kyawawan maruka guda uku masu gigita kwakwalwa kokarin.... 

3️1️

Kokarin kara mata wanin marin yake saita kauce.

Nan da nan Idanun ta suka ciko da kwalla.

Al'amin duk kukan da take besa yaji zuciyar shi ya yi sanyi ba.

Cikin tsawar daya daka mata wanda ya sa hantar cikin ta kadawa.

 Keee Salma wallahi ba na son ki zan zauna dake dan tilasta mun da akai kwabe baki ya yi yana jifanta da mugun kallo ya ce nabaki dama kina iya tunkarar iyayen ki a kan zancena su nemar miki mafita inkuma kinki uhmmm da kanki zaki sai ruwan dafa kanki.

 Salma tagama fusa ta ba ta taba sanin Al'amin jaki bane sai yau.

Cikin zafin rai ta ce kai meya hana ka sake ni naga hannun ka sakin yake.

 Maganar iyayena in sanar musu su raba auren kaine zakayi ba ni ba kuma wallahi zan tabbatar maka ni karuwan gidan ce.

Kar ka dauka ka mari banza wallahi, inba jahili ba wake dukan mace.

 Tun da tafara magana bakinta kawai yake kallo yanda take zaro zance.

Girgiza kai ya yi ya ce haka kika ce Ko ?

 Ta ce eh haka nace saime takara zancen tare da koma gida.

Bayan ta yakebi da kallo kafun ya sakai cikin tafasar zuciya yabar gidan.

Tana shiga dakin su bakin gado tazauna kukan zuci take yanzu ita Al'amin zecewa karuwar gida, kalmar nan ba ƙaramin sosa mata zuciya yayi...

Sheik yakira Dr Abdullahi ya yi masa zancen kai kayan Amarya.

 Dr Abdullahi ya ce ku bar kayan kafun agama gyara mata wajen zama ka san an yi auren ne ba tare da anshirya ba kar ka damu yanzu ba ta da matsalar komi a gidan yafada masa cike da girmamawa.

 Sheik ya ce to babu matsala nagode Daga haka suka yi sallama.

Kallon anty ya yi ya ce saide ku kaimata kayayyakin sababbin din kuna.

Mama ta shigo dakin bakin ta dauke da sallama ganin sheik da Anty a dakin su biyu kadai wani katutun bakin ciki ne yarufe mata idanu lokaci daya.

Cikin Jin haushin su takaraso dakin..

Daman nazo ne in gayamaka yan uwana sunce yau za su tafi kuma suna son suje gidan Rahama tanabin anty da muguwar harara.

Sheik daya lura tsiya ce kecin ta ya ce Aishatu ai babu matsala a kan yana da kyau bara insa koda Abubakar ne yakaisu yakai karshen zancen tare da tashi yabar dakin danshi beson abun da ze Daga mai hankali.

 Sheik nabarin dakin Anty itama ta tashi zata fice mama tasha gabanta ta ce watau kundaukeni yar iska zuwana ya sa duk kuka watse.

 To bari kiji Asirin da kikaiwa wa mijina harya tsaneni wataran sai ya koma kanki tana huci sama _sama kayataccen murmushi Anty ta yi ta ce dadina da gobe saurin zuwa.. Tun da kin san inayin Asirine tokema ki je kiyi mana tafada tare da barin wajen cike da mamakin wai me laifin ta dan ta auri mijin ta.

*, ***********, *****

Yarima Samad kusan makara ya yi Daga barcin dayakoma bayan sallah Asuba.

A gaggauce yashirya cikin kananun kaya Jean bleu da hash din riga ba ƙaramin kyau ya yi da shigan turawa ba.

Gaban mirrow ya je ya taje sajen sa tare da fesa turaren sa one love shi ne asalin turaren da yake shafawa tun kuruciyar sa.

Cike da nutsuwa yagama shiryawa tsaf takalman sa ya zira a kafafun sa kokarin daukar wayoyin yake ya yi daidai da shigowar Faruk da Aminu suma duk sunshirya.

Aminu ya ce ranka yadade yau fa mun so mu makara fa.

Faruk ya ce ai harda gajiyan jiya wlh ka san mun dade ba mu tara gajiya irin haka ba.

Samad na daukar jakan kayan sa ya ce mu je Ko tare da yin gaba take masa baya suka take masa baya.

Cikin sauri sauri yake taka matakalan step.

A gaggauce ya sauko kasa iske su Mamy da khadija da Ahmed yayi.

Cike da ladabi yagaida Mamy ta amsa masa fuskan ta babu walwala..

Muje Ko ya furta yana me kallon yanayin ta.

Shiru ta yi taki bashi Amsa.

Faruk ya ce Mamy karmuyi latti fa dan mai martaba da Abban marwan da marwan da waziri sunyi gaba sunyi gaba sunce mun same su acen.

Still dai shiru ne ba ta basu Amsa ba.

Har sun cire rai da zata kulasu sai suka ji ta ce ita kuma Matar taka ya zakai da ita da kake ta shirin tafiya babu tunani tafada cike da bacin rai.

Ya Salam Yarima Samad yafurta shi Sam ya mance da ita cikin damuwa ya ce Mamy ai sai ta zauna har in dawo Ko yafada cike da gajiyawa da zancen.

 Mamy ta ce koda a gidan mahaukata ne ban taba ganin Amaryar data kwana daya gidan miji ba yatafi yabar yar mutane babu kwakwaran bayanin da ya yi mata.

Asiya ce ke saukowa Daga kan step hannun ta dauke da kwanunka da suka yi break zatakai kitchen sannun ku da warhaka ta furta tare da zuwa kitchen takai kwanunka tadawo.

Cikin nutsuwar ta da kamalar ta take kallon Abdul Samad ta ce mijin kawata zuwa dan anjima zantafi gidan mu.

Da zaran ankawo kayan Matar ka tafada cike da tabbatar masa da zancen nata.

 Kakalo murmushin dole ya yi ganin Mamy ta tsare shi da idanu.

 Cikin cool voice dinsa ahannu sa cikin aljihun wandon sa ya ce tun yanzu zaki tafi haba dakin kara mana kwana mana yafada cikin sakin fuskan dole.

 Asiya da ta ji dadin amsar da yabata dan tadauka har cikin ransa yake zaro kalaman bakin sa.

 Ta ce inna kara kwana gidan mu za ai mun fada tana kokarin hawa kan step hartakai karshen matakalan yabata amsa da OK zaki ga khadija da sako na yafada tare da kallon reaction din Mamy ganin tana murmushi ya sashi tabbatar wa eh lallai ta ji dadin abun da yayi...

 Asiya na wuce wa Mamy ta ce kokai fa haka ake son gwarzon namiji.

 Yanzu abun da nakeso da kai kai zaman ka kaci gaba da binciken daya kawo ka.

 Faruk zeja ragaman zaman kotun da zakai tafada cike da ba da umarni.

Innaliahi wa'inna il a rajun yafada a a bayyane gabadaya falon kallon sa suke cike da mamaki..

 Turo baki ya yi gaba ya ce yanzu Saboda Allah Mamy Alkawari fa nadauka zan taimaki bayin Allah nan kuma ke ce kikaban karfin gwiwa lokaci daya ki rushe ni dai aduba lamarin nan.

Yafada kamar me shirin yin kuka.

Faruk me ze iya yaron da Ko magana be iya ba.

Sake da baki Faruk ke kallon sa ya ce Ah lallai ban iya magana ba kace yanzu na tabbatar kayi aure duk Ada ba ka san haka ba sai Daga jiya zuwa yau..

Faruk ya ce Mamy wlh kada kibarshi ya je kuma Mamy kibari gobe ku tafi nida Aminu munyi gaba yau dan dole nine zan maye gurbin sa.

 Kallon Abdul Samad ya yi ya ce ai bazamu wuce sati daya ba mun dawo kaide kazauna ka kula da aikin ka da kuma Amaryar ka yafada cike da tsokana kama hannun Aminu suka yi tare da barin gidan zuwa airport.

 Gabadaya Abdul Samad yadauke wuta a tsaye wani katutun bakin cikin hanashi tafiya ke damun sa Kasa magana ya yi yana kokarin komawa dakin sa.

Mamy ta ce dakata ya tsaya tare da waigowa dan Idanun sa sun canja launi zuwa ja.

 Kaje dakin Rahama kataho mun da ita kuzo tare dan sonake inkara ma ku nasiha dan jiya ina Lure da kai ana muku fada eapace ne a kunnen ka kai ka ga tabbata ce Ko maza katafi inajiran ka tafada cikin tsawa.

 Ba musu ya yi hanyar dakin da Rahama take a hankali yadanna hadle din kofar Ko sallama beyi ba yashige dakin kai tsaye dan Idanun sa sun rufe bemasan inda yake jefa kafafun sa ba.

Asiya sake da baki take kallon yanda yashigo tsakiyar dakin

 Rahama ta ba shi baya tana karatun Alkur'an zazaakar muryan ta ya gauraye dakin.

Kallon ta bayan ta yake ya ce uhmm mun hadu da yayan malamai.

Bara ta nuna mana gidan jahilai tazo.

Asiya bakinta na rawa take kallon Rahama ta ce Inkin kai Aya ki dakatar ga mijin ki nan tun dazu a tsaye yakasa fadin koda kalma daya ce.

 Gab Gab Gab haka zuciyar Rahama ya shiga bugawa da karfin tsiya Ajiye Alkur'an ta yi tana kokarin saka hijab din ta.

Cikin sauri kallon ta yake babu Ko kiftawa soya ke yaga fuskar ta.

 Tana saka hijab din ta ta juyo a hankali zata cemishi ina kwana caraf Idanun su ya tsarke cikin juna.

Kusan A tare suka bude baki za su yi magana tare da fadin.........

3️2️

Kusan A tare suka bude baki zasuyi '' magana tare da fadin kaine '' shima ya ce ke ce bakin sa na rawa lokaci daya yaji wani katutun bakin ciki ya mamaye zuciyar shi karfin hali ya yi ya kalli Asiya ya ce dan Allah Ko zaki ba mu waje zan danyi magana da ita yafada fuskar babu yabo babu fallasa.

 Asiya ta ce ai babu matsala in kun gama ina kasa tare da farin dakin.

 Ta ja musu kofar

 yadawo da kallon sa a kan ta banda rawa babu abun da jikin ta keyi tsoro da fargaba dan tabbas ta gane shi ''

 Wani kallo yake bin da shi mai cike da ma'anoni da keda wuyan fassarawa ya ce uhmm.

 Sai yau na gane ke mayya ta ce au daman abun da kikai mun a airport be isa ba saida kika san hanyar dakikabi dan ki aureni ke wai ma in tambayeki inban manta ba kun taba zuwa ma'aikata na keda Adamu wanda yafasa auren naki aka lika min ke

 Tun ranar ɗana ganki kina yawo da Adamu na raina wayon ki da Ajin yakarashe zancen cikin bacin rai banda tafasa babu abun da zuciyar shi keyi.

 Rahama kanta aduke banda kuka babu abun da take cikin sanyi murya cike da ladabi ta ce Dan Allah kayi hakuri kabar zuciyata ta samu nutsuwa tashi Daga inda take ta yi tana kokarin fita Daga dakin cikin zafin nama ya jawo ta tare da dawo da ita dakin kallon ta yake ya ce sokike ki je kihadani da Mamy shi ya sa kike kokarin fita.

 Girgiza kai ta yi ta ce Alamun ba haka za ta yi ba.

 Wlh koda wasa kikai abun da ya sa Mamy ta fahimci wani abun zaki ga Abun da zanmiki a gidan nan.

 Dan haka shiga toilette ki je kiwanke fuskarki kaji min mata da Jan sharri daman mata haka kuke masu neman sanadi.

 Kallon yake yanata zuba ruwan masifan da shi kansa besan na mene ne ba '' ganin yacika mata kunne ya sa tafada toilettes tadauro Alwala hajabin ta tasaka tana kokarin daukar dadduma dan sallah kadai shike ba ta nutsuwa in ranta ya baci 'fisge dadduman ya yi Daga hannun ta yana huci cikin bacin rai ya ce kin daukeni dan iska Ko.

Nikadai ke ta magana shi ne kika shareni ga banza Ko yakarashe zancen yana bin da kallon haushin ganin ta da ya yi ranar farko ita da Adamsy.

A kamfanin sa.

 ALLAH YABAKA HAKURI SHI NE KALMAR DATA FURTA DAN Allah ba ni dadduma ta.

Ta fada cike da gajiya da takura mata da ya yi da masifa.

 Kibari inkin dawo kinyi sallah Mamy keson ganin ki kuma kada ki sake kinuna damuwa a kan fuskar kinji na gayamiki Ko.

 Gyada masa kai ta yi Alamun ta ji gaba ya yi tana biye da shi abaya har suka karaso falon.

 Cikin murmushin yake ya ce Mamy gamu mun iso tare da zama akasa dukan su

 Asiya ta ce uhmm kodai jarabar tashi ce ta motsa shi ya sa yakoroni oh Rahama zataga sabon Rayuwa da batasan shi ba tana murmushi.

 Sossai Mamy ta yi masu nasiha mai ratsa zukata ta ce Abdul Samad kanada ilimi banson yazama na banza kai ne me kare hakkin Al'umma ina son ka kare hakkin matar ka dan Allah badan ni ba.

 Jiki Asanyaye ya ce Mamy bakida matsala dani cikin sanyi murya ya ce Mamy Inkin gama dani ina iya tafiya Saboda Dr Abdullahi yakirani a waya ban san kiran mènene yafada tare da Mikewa tsaye.

 Ahmad ya ce yaya Samad zanbika pls OK mu je ya ba shi amsa cike da sauri yake tafiya yana gudun kada Mamy takara sa shi wani aikin yakosa yabar gidan gabadaya.

 Kusan lasa'ar Anty sukayo ayari tare da yan uwan Mama da yan uwanta da kawayen su 'harda makwaftan su.

 Abubakar tare da shi aka zo Abdul jalil ya biyo shi sossai waɗanda basu zo kawo Amarya ba suka saki baki suna kallon tsaruwar gidan.

 Mamy daman tasan dazuwan su kyakyawan tarba suka yi masu tare da mommy Adamu dan tazo ta taya su amsar baki.

 Girki me Rai da lafiya Mamy tasa akai musu cike da babban kula.

 Abubakar yana shigowa bayan sun gaisa da surukan kanwar shi ya nemi ayi masa jagora har dakin Rahama.

Asiya takaishi Rahama na ganin sa aguje taje ta rungume shi tana murna ta ce yaya dan Allah ka ringa zuwa ina ganin ka kwana daya bakaji yanda na ji ba.

 Murmushi yake harda hawaye ya ce Rahama ta kenan wayagayamiki haka akeyi aini yayan ki ne koda kanin ki ne.

Ba zaiyu kullum a rinƙa gani na a gidan ki ba hakan zubda mutunci ne kin gane Ko my kanwaty tare da shafa fuskar ta yana mejin son ta da kaunar ta 'ina kyakyawan mijin naki yake ya tambaya cike da kulawa.

 Shiru ta yi ta ce ban san inda yake ba tana turo baki cikin shagwaba' dariya ya yi ya ce uhmm shagwaban nan dai tana nan ba a daina ba.

 Uhmm ta ce yaya wai ina Salma take tafada cike da kewa shiru ya yi yana tunanin anya Rahama ba irin matan Aljanna ba ce kuwa yanzu ace duk wannan bakin cikin da ta shayar da ita a jiya amma yau tana tambayar ta.

 Murmushi ya yi a fili ya ce tana gida aikin San mijin nata sai ya kama haya Ko ince dangin sa za su kama mishi sai su tare ya sallam tafurta ta ce amma meze hana Abba yakama mashi daki su zauna nasan zaman kadaici ze dame ta.

 Abubakar kallon ta yake yanda duk ta damu ya ce kwantar da hankalin ki ai sun ma kama daki kaya kawai ake jira yafadi haka ne dan tabar zancen Salma dan haryanzu cike da Jin haushin ta yake

Sun dade suna hira kafun ya yi mata sallama ze tafi kuka tasoma tana fadin yanzu shi ke nan za ka tafi ka bar ni yaya na gayamin yaushe za ka dawo. Ya ce inaga saikin haihu Ko kuma kinzo gida.

 Kalmar haihuwa daya furta take ta juyawa ta ce uhmm wai haihuwa sai dai a gidan marayu zan samo yaya in rena dan wlh ina sha'awar reno.

 Tare suka sauko Daga kan matakalan step din ita da Abubakar sannu da zuwa tayima bakin ta da suka ba je suna cin abinci a falo kallon Anty ta yi da take waya tana fadin kalan labulayen da za a kawo wa Rahama wuce su ta yi tabi bayan Abubakar ta same shi jikin mota yana kokarin budewa Kallon shi take Idanun ta cike da kwalla ta ce inka je ka gaida Abba da Mama zuwa tai ta rungumeshi tana kuka sai Rarrashin ta yake' ya yi daidai da shigowar motar Yarima Samad tun Daga nesa yake hango Rahama rungume da wani da besan Ko waye ba.

 Parking din motar ya fito ta gefen idanu yake kallon su saida yazo daidai su yayiwa Abubakar hannun suka yi musabaha cike da Jin dadi Abubakar ya ce kanina dan Allah ga ƙanwata Amana.

 Yarima Samad cikin Jin haushin su ya ce bakada matsala yanzu kazo ne ya tambaya.

Abubakar ya ce eh bandade ba kuma yanzu zan tafi.

Abdul Samad ya ce dan Allah ka gaidamin surukina sheik imam

Yana kokarin shiga Daga cikin gidan kai tsaye yashige gidan yana tunanin hukuncin dazeyiwa Rahama a kan rungumar Abubakar da ta yi yarinya babu kamun kai kana magana tana kada kai kaman kadangariya mtssss ya ja tsakiii kasa karasawa falon ya yi ganin baki cike duk sunyiwa falon kaca_kaca da abinci kokarin barin falon yake anty ta hango shi kuma ta tabbata shi ne mijin Rahama dan yanda aka suffan ta ma ta shi.

 Anty ta ce haba Surikina ya ka tsaya bakin kofa ne

 Shigo mana duk nan iyayen ka ne fa 'cikin sanyin jiki yakaraso yana kallon yanda suka maida masa gida kamar gidan dambe a ladabce ya gaishe su' Mamy data fito Daga dakin ta ta ce ka ga wannan ita ce uwar rikon Rahama Ma'ana matar baban ta tana me nuna masa Anty cike da girmamawa ya sake gaishe ta yana kokarin barin falon.

 Sai bayan isha'i suka tattara za su tafi 'Abdul jalil be gaji da ganin Rahama ba dan tun da suka zo yana manne da ita a daki da ƙyar anty ta tsawata masa a kan yazo sutafi aizekara dawowa Asiya ta tattara inata inata tana kuka Rahama na kuka ta ce shi ke nan Asiya zaki tafi kibarni kaicona daman haka aure yakesa zukata kuka dan Allah karki tafi kuka suke sossai Aguje takama kafar Anty dake kokarin shiga mota tana kuka iya ranta ta ce anty kema tafiya zakiyi kibarni wayyo uwata shekara da shekaru a jikinki nake kwana ke ce fitila mai haska duhun dake cikin zuciyata shi ke nan Farin cikin na yakare anty.

Cikin kuka anty ta ce Rahama banso kika sani kuka ba tunjiya nake ta kokarin daurewa nakasa inaganin kamar yawuce a yau shi ne zaki kara sani kukan kiyi hakuri Abdul Samad shi ne rayuwan ki yanzu duk abun da ze je yadawo karki taba Daga murya a kan nasa zakiyi nasara InshAllah takarasa zancen tana kokarin shiga mota..

 Kuka take sossai har motar su yabar haraban gidan jiki asanyaye tadawo cikin gidan iske Mamy da mijin nata kadai ne a falo khadija da Ahmed duk sun tafi sun kwanta dan suma sun tara gajiya.

 Falon tadawo ta nemi waje kasa ta zauna tana watsa da yatsun hannun kewar khadija take da ba ta kwanta ba data taya ta kwana gashi batasan dakin nasu ba '' bare taje ta taso ta.

 Falon shiru banda karar message din WhatsApp babu abun da kake ji Kallon shi Mamy take yanda ya kar kata hankalin sa kan wayar hannun sa gaban sa ledan kaji ne da juice da Mamy ta sashi dole ya siyo su.

 Mamy da barci ya fara dibarta ta kalle shi ta ce ina kayan da ka amso Daga gidan Dr Abdullahi sunce lefe ne Ko' eh yabata amsa suna A mota mance su nayi yafada ba tare da ya dago kai ba.

 Katashi kuje ku kwanta ɗare ya yi Ko kallon Rahama take da duk tsananin tsoro yakamata me Mamy take nufi daki daya zata kwana da wannan mutumin uhmm wayyo Allah anty ze zalinceni maganar zuci take dawo da ita cikin tunanin ta ya yi ya ce tashi mu je Ko tare da yin gaba da ƙyar ta tashi dan ta lura Mamy kallon ta take cikin Jin kunya tabi bayan nashi ita Ko mamy daman jira take su tafi gaban Idanun ta dan tasan halin nashi shi ya sa takara kwana dan tagyara masa zama.

 Kashe wutar falon ta yi tare da wuce wa dakin nata cikin kasala.

 Abdul Samad tun da suka shiga dakin banda safa da marwa babu abun da yake yi kallon ta yake yanda ta rakube jikin bangon dakin

 Tunanin maganar da Mamy ta yi masa lokacin daze je siyo kaji.

Girgiza kai ya yi cikin zuciyar sa ya ce ina Mamy na ba zaiyu ba sai dai ki gafarceni Ko hadani kwana daki daya da ita ba ƙaramin kokari nayi ba.

 Barin wani tunani ya yi tare da shiga toilette ya yi wanka yashirya cikin kayan barci saida ya Haye gadon yakwanta yana kokarin rage hasken dakin ya hango ta inda yabar ta nan tsaye.

 Cikin bacin rai ya ce ga kaji nan Mamy tasa in siyo miki karma kiyi tunanin wani abu kin wani tsaya kaman an kafaki awajen yafada cike da fada to dan Allah karki cinye ni danye wannan kallon haba ya yi yawa mana.

 Ita dai Rahama kallon sa take tana son ta koma dayan dakin data kwana jiya dan batasan inda zata kwananta anan ba.

 Kokarin fita take har ta murda handle din kofar tana kokarin sa kai cikin zafin nama zata tona mai Asiri ya kamo hannayen ta masu taushi da tsansti wani yar yar haka yaji tsikar jikin sa na tashi sakin hannun ta yayi.

 Ya ce ki wuce ciki nace Ko dauki bargo gashi cen ki shinfida a kasa ki kwanta ''

Yafada cikin fushi.

cikin hanzari da tsoron sa ta hau gadon tana kokarin dauko bargon hannun yakai.....

 

3️3️

''' kokarin dauko bargon take hannun ta yakai kan wayar sa dake dake Ring kan screen din wayar anrubuta Maryam '' maimaita sunan take cikin zuciyar ta 'shiko ganin ta tsaya ne ya sa shi fadin me kike yi ne da ba za ki sauko ba Daga kan gadon ba.

Daga dauko bargo yakarashe zancen yana mata kallon tuhuma.

 Jin karar wayar ne ya sa shi zuwa daukar wayar ganin Maryam ce me kiran ya so ya katse Ganin Rahama ya sa ya Daga.....

 Daga cen ɓangaren ta rushe da kuka ta ce yanzu yaya Abdul Samad aure kayi me ye laifina dan nace ina son ka dan Allah kaduba lamarina wlh ina son ka''' soyake ya rufe ta da fada amma ganin Rahama ya sa ya ce haba baby na meye ze dameki dan nayi auren Sadaka kedai kinsha kurumin ki aini naki ne har Abada karki damu kanki kinji Ko amma pls kibari gobe zamu yi waya gobe

Ran maryam yabaci Jin yana shirin katse wayar ta ce pls yaya Abdul Samad kayimin Alkawari daya'' inajinki my baby yafada idon sa na kan Rahama duk abun da yake fade bama Jin sa take ba tun da ta ji ya ce auren Sadaka ta toshe kunnen ta ahankali take karanto suratul Ar rahman tana Jin nutsuwa na saukar mata dan ita ba bakuwar zafi ba ce Adamsy tafara tuno wa tana kukan zuci ta ce da kaine na aura da yanzu nasan nayi aure daman haka na tashi cikin wahala banda Anty da Abba da mutanen gari to bana samun sauki.

 Ina Ganin tsananin Mama ashe wannan ya fi ta uhmm batasan sanda barawo barci ya yi awon gaba da ita ba tana ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya a dunkule ta kwanta dan Sam ba ta saki jikin ta ba.

 Shiko yarima Samad ya ce inajin ki Maryam wani Alkawari kenan zan miki'''

 dan Yanzu ya lura duk abun da yake fadi Rahama batasan yanayi ba tuni ta yi barcin ta.

 Kalamin maryam ne yadawo da shi cikin hayyacin sa ya ce mene ?

 Maimaita banjin da kyau ba.

 Cikin tsoro yanda ya canja launin sa lokaci daya ta ce ina nufin dan Allah kada ka kusanci wannan matar taka.

 Tsawar daya daka mata ya sa wayar ta fadi Daga hannun ta cikin hanzari ta dauka takara a kunnen ta.

 Cijje labbansa ya yi ya ce ban san bakida hankali ba sai yau.

 Ni zakiyiwa maganar banza kada na kusance ta fa kika ce wai m'a meye ruwan ki da hakan innayi '' ba na son shishigi komai lalacewan naka naka ne inafatan kin fahimce ni.

A yanzu dai tana amsa sunan Mata ta ki kula da harshen ki.

 Maryam ta ce kaifa kace min sadaka aka ba ka ita tana turo baki gaba '' eh dan nace miki sadaka ne shi ne ze baki damar gayamin abun da k ranki yaso''Ke tsaya kiji kalmar da kikaji nace miki baby to badake nake ba.

 Da ita nake ya katse wayar yana maida ajiyar zuciya.

 Sai fadi yake watau ma barci take na so ta ji kalaman da za su kona mata zuciya Ko zata je gidan nasu ta ce batason aure insamu inhuta da wahala.

Itako Maryam kuka take ta ce wallahi mama asirin nan be kamashi ba dafarko wlh kamar yaci shi amma Daga baya wlh sai ya canja dan Allah mama kimin kokari wajen wannan malami

 dan Allah ayi masa aikin da kwata kwata ba zai ji shi a namiji ba '' Ko kuma ya tsane ta '' ina son ayi aikin da zai sa yazo nan kwatano da ita dan wlh masarauta zankoma da zama sai auren ya mutu inacen za a daura nawa auren da nashi tafada cikin kuka.

 Mamar ta na bugun bayan ta ta ce haba wane Yarima Samad Ko kin mance baban ki dan siyasa ne yana da mushurikan malamai wallahi duk wani mugun aiki babu wanda basu iya ba kedai kibari yadawo gida zan zauna da shi a kan haka.

 Ita kanta Mamy ba zan kyaleta ba so nawa muna jifan ta baya samun ta narasa dalili dole in canja hanya nima tafada cikin bawa Maryam tabbacin abun da za su aika ta.

 Kallon Maryam take ta ce Share hawayen ki mu je kitchen ki tayani aiki ba musu suka tafi tare....

**************************

Kashe gari.

Kasar kwatano🇧🇯

Masarautar gheuzo.

Jakadiya mai yiwa mutanen Iso wajen mai martaba ce durkushe a gaban mai martaba cike da girmamawa ta ce Gaisheka Adalin Sarki ya shugabana Barka da dawo Al'umma daukakacin masarautar nan suna Maka Barka da isowa kaida tawagarka.

 Kanta akasa tana ta zuba masa kirari.

 Mai martaba gyara zaman sa a kan kujerar mulki tare da gyara rawanin kan shi kana kallon ka san yana cikin farin ciki.

 Kallon Jakadiya ya yi ya ce ina son keda Waziri su sanar a masarautar nan lungu da sako ''

 A sanar masu labarin auren Yarima Samad a shekaran jiya a garin kwatano ita kanta Jakadiya maganar ta Girgiza ta matuka aure ta fada a zuciyar 'afili ta ce Ranka yadade yaushe za su Iso ne yariman shida Amaryar tasa.

Takarashe zancen cikin Jin dadi.

 Mai martaba ya ce in har na shirya hakan zan sanar ma ku sai ku fada''

Yakarashe zancen yana kallon waziri

cike da girmamawa suka bar fadan''

 'bayi masu yiwa sarki fifita suna bayan sa' kamar yanda suka saba aiwatar da aikin nasu.

 Labari ya karade masarauta wai Yarima Samad ya yi aure kuma yar Sahararren malamin Addinin nan da duniyar musulmi suka San da zaman sa.

Ita ya aura banda gulma babu abun da ke tashi a masarautar.

 Baiwar fulani Asabe tare da yar ta Karima zaune suke suna zancen auren Yarima '' Karima ta ce mama wai kin san meyake ban mamaki kuwa.

 Girgiza kai ta yi tana me cigaba da gugan kayan ta '' numfashi ta fesar ta ce wallahi ina ganin karshen zaluncin. Masarautar nan yakusa zuwa karshe tana me jinjina kanta.

 Asabe ta ce meyasa kikace haka Karima ba tare da ta kalle ta ba.

 Karima ta ce kin san ni ce baiwar dake kula da sashin Yarima Samad ce kuma yawancin halayen sa nasani '' Wlh wani lokacin innaje da niyar inmasa gyara a dakin sa sai in iskeshi shikadai yana ta fada yana dukan bangon dakin har jini yana fitowa nasha ganin haka wlh shi ya sa nasamu wani magani da baba yataba ba ni irin na masu shirin hauka nasamai a ruwan shan sa.

 Ni dai tun lokacin yadauki lokaci mai tsawo be tashi ba sai yana gab da tafiya Kano naga abun yadawo sabo.

 Asabe barin gugan ta yi rike da baki ta ce Amma Karima kinada karfin hali in wani yaganki sai ace mugun abune zaki masa dan Allah karki kara wannan gangancin kinji Ko ta gyada kanta alamun gamsuwa '

 Ni wlh mama nayi haka ne dan yana mugun ba ni tausayi kin san miskilan cin sa Ko na bashi ba amsa zeyi ba.

 Asabe ta ce da wannan KUMA YANZU DE TUN DA ya yi AURE Alhmdulilah karshen su yakusa zuwa karshe fashewa da kuka ta yi ta ce munyi Rashin Adalin sarki Alhaji Salihu turaki a mulkin sa babu girman kai shima mai matarba bashi da aibu kodaya be samu mataimaka adalai bane..

*************************

 Fulani sai safa da marwa take yi cikin daki '' a hasale ta kalli wani bawan nata mai suna Abdul gafar ta ce amma yau an yi dan iska ya kabari akayi auren Yarima Samad dawuri haka bayan nace banson kwata kwata ya yi aure dan yakusa mutuwa '' Marwan ɗana shi ne zeyi aure a masarautar nan yanzu inhar ya kusanci Matar sa ta yi ciki wlh kashin mu yabushe yanzu ma wlh auren nan dayayi ba ƙaramin kalubale zamu fuskan ta.

 Abdul gafar kansa a kasa cikin sassauta murya ya ce ya shugaba ta wallahi yanda kika sani aka ake aiwatar miki da aiki ban taɓa koda mistek daya ba tuba nake yakai karshen maganar kansa a kasa.

 Taku daya zuwa biyu ta yi ta Iso gaban nasa ta ce yanzu abun da nakeso da kai ka tashi ka koma wajen wannan malamin ka gayamai nace Duk abun da za ai ayi kada ya kusance ta asa masa son zuwa da ita masarautar nan hakanne kadai ze sa a cimma buri dan wallahi ba yar malamai take ba Ko a saudiya ta fito sai tabar Yarima Samad amma ba zan barta taci bulus ba wallahi auren sa da ta yi saina mata hukunci mafi muni Sannan a karshe in kashe shi taimasa takaba ka ga kenan ta yi zaman banza a tare dashi.

 Dole yarinya takoma inda ta fito.

Takarashe zancen cikin tafasar zuciya.

***************.

Maman Maryam ita Abban ta gaban wani malamin tsibbu banda tashin gurnani babu abun da kake ji awajen.

 Dago jajayen Idanun sa ya yi yana kallon su bayan ya gama buga kasa.

 Ya ce gaskiya wannan yarinyar ba mu iya jifan ta Daga nesa damun tura mata Aljani take kashe su kota raunata su mafita daya shi ne ayi Amfani da Yarima Samad wajen kawo ta kasar nan inbahakaba gaskiya babu abun da zan iya''.. diyar ku tasha kurumin ta saita aure shi inhar yadawo kasar nan.

 So muke abun da ya je yi acen yaji yafita aransa itakuma Matar tashi uhmm murna ze koma ciki dan uban ta '

 Amma karku bari Yarima Samad ya kusanci Matar sa muddin ya aikata tofah ya karya mana aikin mu dan yarinyar nan Ashirye take iyayen ta sun dafata.

Yakarashe zancen cikin tabbatar musu da bayanan sa.

 Abban Maryam ya numfasa yana kallon matar shi da ta yi tagumi ya ce to mallam zamuyi kokari ganin mun hana shi kusantar ta InshAllah.

 Mu zamu wuce.

Malam. Ya ce saikun dawo Daga haka suka fice zuciyar su babu dadi.

.................

Kasar Gabon.

BABA SALIHU yana wajen ginin gidan sa shida dattijon nan 'murmushi kwance a kan fuskar sa yake kallon yanayin yanda akai tsarin ginin acikin zuciyar sa sai fadi yake'' Mata ta kece keson irin wannan ginin gashi nayi ba tare da kin sani ba.

 Dattijon ya ce ya shugaban Adalai ya naga yanayin ka ya canza kodai ginin be maka bane musa arusa shi.

 Girgiza kai ya yi ya ce A' a Ko Kusa kar ka damu..

 Karar wayar ne ya sa shi saka hannun cikin Aljihun rigar sa.

 Kallon sacreen din wayar yake yana murmushi tare da barin inda dattijon yake yakara wayar a kunnen sa.

 Sallama ya yi ya ce ina kashiga ne kwana biyu inata kiran layin ka ba a Daga wa.

Daga cen ɓangaren ya ce yi hakuri mun shiga busy ne daman zan sanar da kai Yarima Samad ya yi aure '' cikin kaduwa baba Salihu ya ce aure kuma dawa..

 Yana kokarin bashi amsa sai Jin ya yi network ya dauke gabadaya sakamakon hadarin daya hadu sama sossai.

 Baba salihu sai hello yake ta fadi yanaga kayi shiru kallon wayar ya yi yaga ta katse.

Sake danna masa kira ya yi yaji wayar ba ta shiga busy.

 Fuskar sa cike da damuwa ya ce inhar Yarima ya yi aure da wacce bana so dole ne insan abun yi yafada cikin damuwa.

********************

 KANO.

 MAMY tsaf suka SHIRYA za su wuce khadija fuskar cike da damuwa za su tafi subar Rahama '' Ahmed ya ce Mamy muyi sauri kada mu makara fa.

 YARIMA Samad suka hango yana saukowa Daga kan matakalan step da sassarfa cikin shigar shi ta wani tsadaddan boyel ya saka hula ba ƙaramin kyau yayiwa Mamy ba harya tuna mata da mijin ta.

 Inakwana mamy yafada fuska a sake lafiya lau ta ba shi amsa Khadija da Ahmed suka gaishe cikin saikin fuska ya ce au duk kun Kosa ku tafi Ko.

 Nima din nakusa zuwa yafada yana lacakan bakin khadija.

 Khadija cikin shagwaba ta ce Mamy kina gani Ko.

 Mamy ta ce babu ruwana kullum yara kuke komawa shida ya yi aure yakamata ya fara hankali.

 Hade fuska ya yi yanajin haushin furucin Mamy.

 Mamy ta ce wai ina Rahama ne banji duriyar ta taci brek din da aka kai mata kuwa.

Eh Mamy tacinye duka harda side kwanun yafada cikin sanyin murya.

Mamay ta ce bara inje da kaina in sauko da ita ka san ina son ta saki jikinta tafada tare da bin hanyar matakalan step.

 Hankalin Yarima Samad ya yi mugun tashi dan ya san Rahama tana zaune kan wannan bargon da ta kwana jiya.

 Mamy na gani komai ze iya faruwa.

 Cikin sauri yabi bayan Mamy da hannun ta yakai kan handle din kofar zata bude tashiga.

 Kama hannun Mamy ya yi a hankali atashe ya.....

3️4️

Kama hannun Mamy ya yi hankali atashe.

Mamy kallon sa take da mamaki ta ce yadai lafiya kuwa tana mai kallon hannun ta daya rike..

 Murmushin ya yi yana sosa keya ya ce namance ban gayamiki ba tashiga wanka nasan yanzu tana kokarin shiryawa yakarashe zancen cikin tsoron kada ta bude.

 Murmushi Mamy ta yi ta ce kuma kafini gaskiya dole ne sai na nemi izini kafun nashiga bara na

 koma kasa in jira tagama dan Allah shiga ka gayamata ta yi sauri.

Juyawa ta yi tana kada kai mamakin Yarima take yi yanda taga tsoron ta a Idanun sa murmushi ta yi ta ce saida haka ake zama lafiya dasu.

 Shiko Yarima Samad dakin ya shiga babu sallama iske ta ya yi ba ta nan Jin karar ruwa ya sashi sanin tana toilette.

 Kwankwasa kofar toilette din yayi.

 Rahama gaban ta ne ya fadi Jin buga kofa da akai.

 Kayan data cire ta maida tare da fitowa Daga toilette din duk kayan jikin ta damshin ruwa ya sa sun dan jike.

 Kallon ta yake tun da ta fito yanda take raba gefen sa.

 Cikin ba da umarni ya ce. Keee kadangaruwa yi maza kishirya Mamy yau za su wuce '' tanason ganin ki yanzu'' gyada kai ta yi alamun gamsuwa.

 Ganin takasa aikata komai ya ce ba magana nake miki bane cikin Daga murya nace jiranki ake ki canja mu je Ko yakarasa zancen cikin Jin haushin ta.

 Cikin muryan ta mai dadin sauraro ta ce dan Allah ka fita zan canja kaya.

 Uhmm ya yi yana kallon ta hannayen sa cikin aljihun rigar sa yafice Daga dakin dan shi ya manta da yafita din saida ta tuna masa.

 Mamy ta ce yanaga kataho kai kadai ina take ne ba ta gama rufe baki ba ta hango Rahama na kokarin saukowa Daga kan matakalan Step sanye take da doguwar riga material mai Stone marron color ta yafa mayafin ta maroon kafar ta dauke da takalmi flat cike da nutsuwa takaraso falon gaishe da mamy ta yi a ladabce tare da gaida Ahmed da khadija cikin sakin fuska.

 Mamy cikin Jin dadi ganin Rahama ta ce diya ta yau zamu koma kasar mu sai Allah yakawo ki

 Rahama duk yanayin ta ya canja tadawo kalan tausayi Mamy ta lura Sam batason Tafiyar tasu hakan ya sa Ta kalli Abdul Samad ta ta ce to mudai zamu tafi kar ka manta in bana nan akwai Allah.

 Mamakin furucin Mamy ya yi cikin son kawar da zancen ya ce mu je Mamy kada mu latti.

 Khadija na kuka Rahama na kukan Rabasu da za ai.

 Shiko Yarima kallon ikon Allah yake yaushe suka San juna da har suke kuka.

 Cikin sauri sukabar gidan Rahama tana kallon motar su yatashi wanda mijin ta ne ke tukin.

 Kukan zuci take ta ce yau gidan nan zemin zafi cikin sanyin jiki takoma gidan tana tunanin abun da zatayi.

 Har airport yakaisu suna zuwa ya yi daidai da jirgi ze tashi babu ba ta lokaci suka shiga '' yarima na kallon su har jirgi nasu ya tashi.

 Komawa ya yi inda motar sa take 'cikin sauri yabar filin airport.

*******************

 Mama da kawar ta Talatu suna shawaran yanda za' akai kayan Salma.

Talatu ta ce mun je munga gidan gaskiya dakin ya yi kadan haba yarasa inda ze kama haya sai wajen gari gaskiya yaron nan beda Adalci.

 Mama tasauke nauyayyen ajiyar zuciya ta ce yazanyi talatu na gayawa uban ta yakama musu haya koda babban gida ne nasu sukadai ya ce Sam besan wannan zancen ba waishi hakkin Salma yafita a kan sa abun da yazama wajibi a kan sa yariga ya yi mata.

Uhmm talatu ta ce tana mai gyara zaman ta ta ce ina hankalin ki yake ne.

Mama ta ce bangane mekike nufi hankali yana kanki.

 Uhmm gaskiya baya kanki cewar talatu.

 Ke baki lura ba a gidan nan kece babba fa amma sheik duk abun da Sa'adatu ta fada wlh baya mu sa mata da ita ce ta ce a kamawa Salma haya wlh sai yayi shi koda kuwa beso.

 Da jimm Mama ta yi tayi tagumi ta ce aini tariga ta shanye shi ta wanke ta bashi yasha ai Allah yahadaka kishi da fulani wallahi kabani.

 Talatu hararar mama ta yi ta ce ke ba za ki tashi tsaye ba ki kwatar wa kanki yanci ba '' ba ina nufin kishiga malamai ba.

Yaki zakiyi acikin gidan ki. wallahi matarbarki da kimar ki yadawo Idanun Sheik.

 Sallamar Anty ne ya sa talatu yin shiru tana me sakarwa anty murmushin yake.

Maman Rahama ke ce ?.

 Eh Nice inna Talatu'' anty tabata amsa.

Tana me kallon Mama da ta juya musu baya.

 Cikin sanyin murya ta ce Maman Salma wajen ki nazo.

 Mama ta juyo ta ce inajin ki Ranta aba ce take magana hakan da take yi ita anty Ko a jikin ta.

 Dama batun kai kayan Salma ne waɗanda basu zama dole sai ta yi amfani dasu ba ajiye su zamuyi a store dan dakin nata bashida girma '' Sannan kibada kudin da za aje adauko mai makeup kamata ya yi akai Amarya tsaf tsaf da ita gwanin ban sha'awa tafada tana kallon talatu.

 Talatu ta ce kwarai kuwa maman Rahama maganar ki dutse.

 Mama ta waigo tana kallon anty ta ce babu matsala zan aiko da kudin abaki.

 Cikin Gamsuwa anty ta ce saina jiki tare da barin dakin.

Mama da talatu suka kalli juna a tare.

Talatu ta ce baga irin ta nan ba wlh babu asirin da matar nan take miki ''..

ta iya kissa da kisisina jifa yanzu tazo tana tambayar kudin makeup.

Uban Salman shima wani abun daban zata ce ana bukata ahaka zata siye miki miji ke kina zaune wai kishi Allah natuba wa ke ta kishi yanzu kishina sutura ta wlh ki daura dammara kawata.

 Shewa suka buga Mama da kawar ta '

Shi ya sa nake son ki talatu kanki yana ja InshAllah zan bi shawaran ki.

...

Salma suna zaune ita da Aminiyar ta Amina suna shawaran yanda za su yiwa Al'amin asiri dan ya sake ta.

 Amina ta ce kyalemu da shi ai yau zaki tare Ko nasan da wuya ki samu magani yau ki jira cikin satin da kaina zanje miki.

 Amma haryanzu kin tsaura kina son Adamsy kuwa tana kallon Salma.

 Salma ta numfasa ta ce kedai me zanyi da Adamsy ga Abdul Samad.

Cikin zazzare idanu Amina ta ce bangane ga Abdul Samad ba.

 Mijin yayar taki.

Salma ta ce kwarai kuwa shinake nufi.

Tashi ta yi Daga zaunen da take tare da jujjuyawa tana kada kugun ta ta ce kalleni Amina dan Allah banida diri ne Ko kyau ne bandashi.

 Tun Ranar ɗana fara ganin mijin Rahama na ji ya kwanta min.

 Amina cikin bacin Rai ta ce haba Salma meyasa ba za ki sassauta wa Rahama ba jibi abun da kikai mata a kan Adamu.

 Sai Allah yabata wanda yafishi ni kinga badani za a lalata aure ba dama ace be aure ta bane sai mu Rabasu '' cikin bacin rai Amina ta ɗau jakar ta zata fita '' a guje Salma tarike hannun ta ta ce haba Daga ina miki wasa saikiyi zuciya.

Tsaki Amina ta yi ta ce ai aure yawuce wasa.

Salma Da ƙyar ta rarrashi Amina ta hakura tazauna jiran lokacin daukar Amarya.

Abubakar zaune a kofar gidan nasu yana shan iska Alkur'an na hannun sa.

 Parking motar da akai ne ya sa hankalin sa yadawo kan wanda ke kokarin fitowa.

Adamsy yagani cikin farar jallabiya fuskan shi dauke da damuwa yakaraso wajen Abubakar yana mai bashi hannu Abubakar kin bashi hannu ya yi yana bin shi da kallon banza tashi ya yi yana kokarin shigewa Daga ciki yasha gaban sa 'ya ce dan girman Allah katsaya.

Cak Abubakar yatsaya yajuyo yana kallon sa ransa aba ce.

Cikin kuka Adamu ya ce nasan dole ku yi fushi dani wallahi shaidan ne ya kadamin gangan dan Allah ku yafe min natuba duk yabi ya marairaice fuska Abubakar jikin sa ya yi sanyi ya ce Allah m'a muna masa laifi ya yafe mana bare ɗan Adam kar ka damu yawuce.

 Adam ya ce ina son ganin sheik dan Allah kar ka hana.

Shiru ya yi yana nazarin ina sheik yaje.

 Cen ya ce kaduba massalacin juma'a ne ba ka ganshi ba.

 Adam ya ce ban je ba nan nafara zuwa.

 To kaje cen za ka same shi yana tafsir.

 Daga haka ya juya a motar sa dan zuwa massalaci.

 Abubakar cike da tausayin Adamu yashige gida.

 Adam zuwa ya yi ya iske sheik na kokarin fita Daga massalacin kafafun sa yarike yana kuka sheik Sam bega fuskar wanda ya kama shi ba sai jiyayi yana fadin dan girman Allah ka kayafemun hakkin ku ba zai barni inzauna lafiya ba.

 Jin muryan Adamu ya sa sheik sa hannayen sa ya dago ka yana kallon yanda hawaye ya wanke masa fuska.

Cike da tausayin sa ya ce kai ma bayin kanka bane Allah ne ya kaddara hakan saita faru daman rubutacce ne '' irin haka inta faru sai ka ga ansamu matsala Daga dangin amaya da Ango mutane ba sa daukar kalmar kaddara.

 Ya kalli sama ya ce nayi imani da Allah shi ne ke bayarwa shike hanawa.

 Allah yahanaka yaba Abdul Samad dan haka kar ka damu na yafe maka Rahama ma ta yafe dan ba ta da riko adua za ka bita da shi na zaman lfy da a gidan auren ta.

Godiya adamu ya shiga yiwa sheik ya sanar masa gobe za su tafi england shida iyayen sa.

 Sheik ya yi masu Adua Allah yakai lafiya ai zumunci be kare ba za a ringa gaisawa.

.................

Bayan isha'i dangin Al'amin su kazo da mota daya dan daukar Amarya anty kadai ce tabisu da amina dan babu kowa duk sun watse.

 Sunsha zaman mota 'Amina ta ce wai gidan Salma saikace zamu bar gari''' anty ta ce ai mun kusa ahaka dai har suka iso unguwar'' dangin Al'amin sai wani kallon banza suke wa dakin yanda ka san ba dan uwan su bane yakama ba

 Suna kaita suka juyo Salma ta yi tayi amina takwana ta ce ina

 Ba zan kwana a jejin nan gashi babu wuta badaniba..

 Tanaji tana gani suka tafi suka bar ta.

Tasha kuka har ta gode wa Allah.

 Tashi ta yi ta leka cikin dakin taga babu toilette sai a tsakar gida.

 Wayyo Allah na ni salma yazanyi in yi rayuwa nan wajen.

 Sallamar Al'amin ne yadawo da ita cikin hayyacin ta.

 Hannun shi dauke da leda kallon ta yake ya ce kee karuwar gida

Tsawar daya daka mata ya sa ta rikice bakin ta na rawa ta ce naam.

 ba ni kwanu in juye mana farar nan bakiga yanda yake ta zuba kam shi ba yana murmushi '' ga kunun Aya ya fiddo shi Daga ledan me dankaren sanyi.

 Cikin razana ta ce fara kace fa ina kazar take ''

 Dariya ta ba shi ya ce Keko ai sandar dake hannun ka da shi zakai duka.

 Maza dauko kwanun kinga da dumi dumin ta umma na ta soya mana.

Cikin kuka ta ce wallahi ba zanci ba kaji shege dan iska.

 Al'amin yazare idanu ya ce ni kike cewa shege.

 Ta ce angayamaka tana murguda baki.

 Kaman jira yake yacire belt din wandon sa 'bugun ta yake ta Ko ina inda ya samu saida ya yi mata likis har ba ta iya motsin kirki' banda sautin kukan ta babu abun da kake ji.

Makotar su babu wanda ya leko sai fadi suke yanzu haka kukan jima' i take yi ne.

......

.********************

Abdul sai kusan karfe tara yadawo gidan agajiye iske ta zaune a falo sanye da hijab tana kallon tashar Afrika tv3.

 Hankalin ta da tunanin ta yakoma a kan kallon bama ta ji shigowar sa ba.

Sai ganin mutum ta yi tsaye a kanta wani razananne kara tasaki tana neman hanyar guduwa hannu ya sa ya damko ta jikin ta nata kyarma wanda tuni tafada jikin sa ba tare da tasani ba.

Ashhh yafada yayin da....

3️5️

Ashhh yafada yayin da yaga ta sake masa nauyi.

Tsawar daya daka mata yadawo da ita cikin hayyacin ganin a jikin sa tafada ya sa cikin Jin kunya ta sake shi kokarin haurawa sama take yi ''

Taji kakkausar muryar sa wanda babu komai cikin sai bakin ciki da bacin Rai.

 Kee daka ta!! Yafada cikin Daga murya

Watau kin Saba kwanciya jikin maza shi ya sa kika danne ki Ko uhmm ke bara in gayamiki Ko a airport da gangan kikai fada kaina tare da tara min gajiya '' yanzu haka wannan wanda yafasa auren naki aka likamin ke '' yasha gugar jikin ki yafada cikin takaicin tuno wannan ranar.

Rahama kamar wacce aka sokawa mashi haka ta ji kalaman nasa sun ba ta mata rai matuka.

Juyowa ta yi ta dawo falon tafiya take kamar ba ta so '' zararan Idanun sa ya sauke su akanta yayin da take kusan to falon haka yaji bugawar zuciyar sa yana tsanantawa ganin ta a adurkushe gaban sa '' cikin nutsuwa tafara magana Dan Allah kayi hakuri abun da ya faru a airport akasi aka samu '' maganar Adamu kuma da ka ganni da da shi a wannan campagny babu wata mummunar alaka tsakanina da shi narokeka dan girman zatin Allah kar ka kara taso da wannan zancen '' cikin kuka ta ce kana danganta ni da halayen da ba nawa bane '' tashi ta yi cikin sauri ta haura sama.

Direct dakin da tafara sauka ranar farko nan ta nufa '' toilettes ta fada ta dauro Alwala'' tazo tada sallah nafila a raka'ar ta karshe ta dade a sujjada tana fadin ya Allah ga baiwar ka nan kaikace muyi wa iyaye biyayya inhar ba ni da rabon Jin dadi a duniya Allah kabani Jin dadi a lahira' kuka take sossai abun da ya faru tun daga ranar daurin auren ta ya fara dawo mata sabo.

Tana idar da sallah tazauna ta zabga uban tagumi tuno wayar ta ta yi taje tabude jakar ta tadauko shi '' tun da aka kawo ta ba ta waiwaye shi ba sai yau.

 Kunnar wayar tayi..

Tare da kunna data sakonnin suka fara shigowa na masu mata fatan Alkhairi da masu tambayar shin dagsk Yarima Samad ta aura.

 Group whsap din tashiga nan firan auren nasu taga anayi wasu na fadin ai kyau ne ya hadu da kyau irin su in suka haihu kyawawan yara za su haifa.

 Uhmm wai yara gidan marayu zan je InshAllah anba yaro Ko yarinya in rena da kaina.

Niko ikilima Adam nace Rahama bakisan kan dawan garin bane mu je zuwa dai..

Fita group ta yi ta rinƙa bin sakonni message sakon Asiya tagani ta ce oh Rahama sai yanzu ake ganin ki online da Alama jarababben mijin naki yahanaki sakat ne.

Bata ba ta amsa ba sai dai rubuta mata uhmm tayi.

Kawar da zancen ta yi ta ce yakika koma gida sannun ku da kokari Allah ya saka da Alkhairi yar uwa rabin jiki.

Sossai Asiya ta ji dadin kalaman kawar ta.

Sakon Adamu ne yashigo wayar ta hakan ya sa ta ji hankalin ta ya yi mugun tashi ganin ya rubuta.

Rahama nasan kila dawuya ki kara amfani da layin ki ina me baki hakuri nasan na cutar dake amma wlh ban san ya akayi na aika ta miki haka ba..

Shaidan ne ya rudeni.

Kallon sakon take tana kuka har sauti na fita ya yi daidai da Abdul Samad ze shiga dakin sa yajiyo sautin kukan nasa har yaso yaba banza ajiyar ta tuno da kalamin Mamy na karshe kafun tabar garin ya sa yatafi dakin kai tsaye '' bude dakin ya yi babu sallama a bakin sa.

Kallon ta yake yi yanda take zaune kan darduma ga waya gaban ta.

 Ta ku daya ya yi zuwa biyu sai ganin shi ta yi ya sa hannun ya wabce wayar '' cikin tsananin tashin hankali yake karanta sakon Adamu wanda ba ta fita a kan sakon nasa ba.

 Dubawa ya yi yaga eh lallai Adamu nakan online sticket mai dauke da hoton zuciya ya tura mata..

Yarima Samad cikin tafasar zuciya ya ce kan uban cen yarinyar nan watau ba ta da Tarbiyya da auren nawa a kan ta take chattin da wani kato..

Tsawar daya daka mata ya sa ta firgice tana mai kallon yanda yakara sauya kamanni sa zuwa mugu '' keee ya ma sunan ki ?

Ya tambaya cikin Tsawa.

Bakin ta na rawa ta ce Rahama tasan ya sani tsabar rainin wayau ne.

In banda ke wawiya ce wayake chattin da tsohon saurayi da auren wani a kan sa '' taku daya zuwa uku ya yi ya Iso tsakiyar dakin cikin haushin ta da tsanar ta da yakeji acikin Ransa '' ya ce kibari idan na sake ki saiki je kuci gaba da tambadewa keda shi.

Ze fita Daga dakin ta dago kai a hankali ta ce ba ka ban wayar ba.

Babu abun da yabata masa rai illah ba ta nuna nadamar ta a kan laifin fira da kwartaye ba '' wayar ne yadame ta.

 Sa kai ya yi yawuce dakin nasa sai huci huci yake sama sama ya ce ai laifin mai Martaba ne nakaranta a AlKur'ani wanda baya kishin matar sa ba zai shiga Aljanna ba ''

Toshi kishin basai kana son matar bane koko dai Ko ba ka son yazakai kenan '' Wlh Mamy banda haramta mun saikin ta dakikai ba da babu auren nan ze je.

Wayar sa yazaro kirar iPhone 13 plus wani Malamin su me basuda Hadda yakira yake tambayar sa fatawa.

Malam ya ce Allah ya sa nasani Yarima.

 Cikin sanyi murya ya ce malam kamar ace mutum ayi masa auren dole Kuma matar daya aura' tana fira da wani samarin awaje dan Allah yazakai mata yakarashe tambayar cikin jiran amsa.

Malam ya numfasa ya ce Abdul Samad inhar mijin auren dole akai masa ya wajaba a kan sa ya yi wa iyayen sa biyayya wajen sauke nauyin da Allah yadaura masa ''

indai yakula da hakkin ta kuma take kula maza ya yi kokarin ya sa ta ahanya ta hanyar yi mata waazi sai in hakan ya gagara ne zai sako manya a ciki.

Kuma InshAllah za a samu maslaha.

Abdul Samad ya ce godiya nake Malam Daga haka suka yi sallama.

Zama ya yi bakin gado yana nazarin kalaman malam toshi ya zeyi da rayuwan sa ne yarinyar nan shifa ba sonta yake ba zeyi ta zama da ita ne ahaka.

Faruk ne yakirashi a waya Daga wayar ya yi yaki magana '' Daga can ɓangaren ya ce Angon Rahama yakake ne tun da ba ka nema na ni kam na ne me ka.

Wai in tambayeka mana sau nawa kayi ne adaren jiya yana me rufe bakin sa dan dariya na cin sa.

Halin duniyan ci Yarima ya yi masa ya ce Daman ba ka san sau nawa nake cin abinci a wuni bane dan iska sai yau.

Faruk cikin tsokana ya ce wlh yarinyar nan karama ce kabita ahankali.

Kalaman Faruk ba ƙaramin kona masa rai ya yi ba '' cikin son kawar da zancen ya ce gobe zaku yi zaman kotu Ko ?

Faruk ya ce daman dalilin kiran ka kenan ina son kaban duk wasu bayanan daka. Tattara dan gobe shari'ar mu ita ce za ai na farko.

Yarima Samad ya ce zantura maka ta WhatsApp ina Mamy take ba mu yi waya da fatan sun isa lafiya.

Lafiya lau suka isa ya ba shi amsa...

Kadai rike amana yar mutane.

Tare da katse wayar yana dariya.

********************

Rahama yana fita Daga dakin ta ce yau dai na ba ni yazanyi da rayuwa ta Da Abdul Samad da Salma wayafi iya mugun ta ne take tambayar kanta.

Nima dai nace bara in tambayeku ku ba ni Amsar dazan ba Rahama

.....................................................................................

Al'amin ya yi wa Salma bugun dayasa Ko kwakwaran motsi ba ta yi banda sautin kukan ta dake fita ahakali babu abun da kake ji.

Kallon ta yake yanda dukiyar fulanin ta ya bayyana nan take yaji sha'awar sa ta motsa.

Kofar dakin nasa ya murza wa key tare da dawowa ciki yana kallo yanda take nishi.

Hannun ya sa yana kokarin cire mata rigata 'cikin kuka ta ce Dan Allah kar kamin komi wallahi banaso.

Bakyaso kikace Ko ta Girgiza kai Alamun eh.

Fincikota ya yi kayan jikin nata saida suka yage danyasha Alwashin sai yayi koda ta karfi ne.

Duk yanda taso ta kwace Al'amin ya fi karfin Nata.

Ba tare da wani wasannin motsa sha'awa ba '' hakanan ya Afka mata wani razannen ihu ta saiki wanda ya sa makotar na gidan fitowa dan su abun ya fara basu tsoro kardai yakashe yar mutane.

Al'amin ba ƙaramin illah ya yi mata ba '' gadon kaca kaca da jini '' ita Ko Salma ta dade da sumewa.

Cikin tsananin tashin hankalin ganin ba ta numfashi ya sashi bude kofar neman agaji.

Mutane nashigowa ihu suka saka dansu basu taba ganin mugun aiki irin wannan '' ciccibar Salma suka yi sai Asibiti.

Al'amin da duk yabi ya rikice haka yabi bayan su.

***********************

Abdul Samad daure da towel a jikin sa lafaffen cikin sa yasha ya ce oh ni yunwa nake ji wancen yarinyar tun da ta shigo rayuwa ta shi ke nan komai nawa ya tsaya cak.

Komawa da baya ya yi tare da dan kwanciya a gadon waya na Hannun sa.

Sakon Fulani ne ya shigo wayar sa ta ce ɗana munji auren ka Allah ya sa Alkhairi.

Ameen yabata amsa atakaice ya san gulma ne ke cin ta.

Kokarin kashe data yake yaga ta turo.

Amma ka san Al'adan masarauta Ko a kan jinin sarauta insuka yi aure.

Maida mata amsa ya yi da A'a saikin fada.

Cikin Jin dadin yabata hankalin sa ta ce duk rintsi duk wuya kar ka kusanci matar ka harsai kunzo. Kwatano Saboda akwai farin kyalle da ake nunawa a masarauta dan a tabbatar da matar tazo da budurcin ta a gidan miji.

Yarima Samad zumbur yamike tsaye yana mai cije labbansa ya ce budurcin.....

3️6️

'''' Ya ce budurci kuma nana ta zancen ya shiga yi cikin zuciyar yana mamakin rashin kunyar Fulani a fili cikin takaicin furucin ta yadau wayar yarubuta mata.... Ai lokacin da aka daura auren wace irin gudummuwa kika bada'''

Zancen budurci kuma ku je da banzar Al'adar ku '' angayamuku ni mai kazamin kwakwalwa ne da tunanin dabbobi irin naki '' Mata ta kuma tun yaushe na buge boss ba mamaki ma tasamu shigen ciki yakarasa zancen cikin muguwar tsanan ta yana tura mata sakon ya kashe data kai tsaye toilettes yafada domin yin wanka '' yana wanka kalaman Fulani na masa yawo cikin kwanyar kansa ''...

Tuno kalamin Mamy ya yi cikin kuka ya ce Mamy ki yafemun zuwan wannan yarinyar cikin Rayuwa ta ya sa nazama mara biyayya a gareki..

Kokarin fita Daga bayin yake bayan ya tsane jikin sa da tawul '''' wani walkiya yagani mai tsoratarwa nan take Idanun sa suka fara kada wa ihu yake muryan sa na fita Azabure yazo dakin ya zauna bakin gado wadrobe din sa yabude ya sauka jallabiya bleu tare da zira takalmin sa dan ba ƙaramin yunwa yake ji ba.

Hakan ya sa cikin hanzari ya zira takalmin kafar sa.

Kokarin fita yake Daga dakin yakara ganin wannan walkiyan adu'oi ya fara karantowa dan dazun yaji Rahama tana karanto su sai ya haddace dan ya tabbata adua kariya ce '' a hankali yaji nutsuwa na saukar masa.

 Ita ma Rahama yunwa takeji hakan ya sa ta fito Daga dakin zata je kitchen iske shi ta yi a falo yana kokarin fita Daga gidan motsin ta ya sashi waiwayo wa yana kallon ta yanda take kokarin shiga kitchen ba tare da yabi ta kanta ba ya fi ce Daga gidan '' motar sa yashiga kai tsaye babban restaurant yatafi ya yi order abinci fruit salad dan shi mayen wannan abincin ne '' har ya baro restaurant sai ya tuna da Rahama a kan ya sa ya sauko yakoma tare da kara yin wata order koda ya dawo gida iske Rahama ya yi zaune ta cire hijabin kanta.

Kamshin indomi ya baibaye duka gidan..

Kallon Abincin nata yake yana kallon yanda ta daura kafafun ta daya a kan tebur din tsakiyar falon kwabe baki ya yi yana me mamaki hartakai tazauna masa kan kujerar mulkin sa Ko su Faruk ba sa zama akai.

Ganin yashigo ya sa ta sauke kafafun ta murya a sanyaye ta ce Sannu da dawowa Amjad.

Maimaita sunan ya yi da Amjad kuma dawowa falon ya yi yazauna one Sister kan kujerar hannun sa dauke da ledoji tashi ta yi cikin sauri dan yanzu ta lura da leda hannun sa tana karba ta ajiye su gefe shiko kallon ta yake yana tuna kalamin Fulani.

Direct kitchen ta nufa tadauko plate me dan girma tadawo falon cike da nutsuwa fruit salad din ta juye masa tare da kai masa a gaban sa.

Cike da girmawa ta ce anzuba kadauka...

Ganin be ba ta amsa ba ya sa takara maimata kaci abincin ka.

Cigaba da danna wayar sa yake yi hakan ya sa ta dau indomi ta zata koma daki takusa kai karshen matakalan step din ta jiyo muryan sa yana fadin.

Wa kika barwa dayan abinci ba tare da ya kalle ta hankalin sa nakan wayar sa.

Kallon shi ta yi nawasu dakiku kafun ta juyo ta dauka.

Tana kokarin komawa. Dakin nata ya ce ke wannan dakin dakike tunanin naki ne to ba dakin ki bane oho kwanan bargo ne baki so ko ? Girgiza kai ta yi Alamun A'a bahaka bane.

Tun da ba haka bane a dakina zaki kwana kina gama cin abinci kidauko bargon nan ki kwanta akai kafun nashiga dakin.

Tana barin dakin ya tabbatar tawuce Sannan ya fara cin abincin beci wani abinci me yawa ba hakanan ya ajiye sauran anan.

 Kiran wani abokin sa ya yi da suka rako shi dauko Amarya.

Bayan sun gaisa Yarima Samad ya ce ya gajiyar ku dan Allah ka mikawa sauran abokan sakon godiya bisa karar da suka min gun dauko diyar sheik imam.

Kokarin tashi yake yaga kiran Mamy a wayar saida yaji faduwar gaba amma ya dake yana Daga wayar ya gyara zaman sa kan kujera sallama ya yi mata Daga can ɓangaren ta amsa masa.

Abdul Samad dafatan duk kuna lafiya Ko tafada cike da kulawa ina Rahama yata take..

Abdul Samad inafatan kana kula da hakkin ta.

Dan Mamy tasamu labarin Abun da Fulani ta gaya masa, cikin hikima da dabarun ta '' ta fara sheshekar kuka '' hankalin Yarima Samad ya yi mugun tashi ya ce Mamy kukan ki babban hatsari ne a rayuwa ta inhar Saboda ni kike yin sa..

Mamy ta numfasa ta ce Yarima Samad Mahaifin ka beda buri a duniya daya wuce yaga kayi aure har ka hayyafa.

Allah ya sa cika masa dayan burin inada yakinin duk halin da muke ciki yana sane damu.

Duk ranar da matar ka ta haihu ranar Mahaifin ka ze taka kafafun sa cikin masarautar nan inada yakini.

 Yarima Samad tashi Daga zaunen ya yi yanata safa da marwa '' yakasa bawa Mamy amsa da ya fahimci abun da takeson ya yi duk da ba ta fito a fili.

Cikin dauriya ya ce Mamy yakamata ayiwa Ahmad aure fa.

Ran Mamy yabaci tasan soyake ya kawar da zancen ''

ganin ta yi tsaki ya sa jikin sa ya yi sanyi sossai.

Murya cent ka san makoshi ya ce Allah ya azurtamu da Mata nagari da zuri'a nagari.

Mamy ta ce bangane ya azurtaku da mata nagari

Cikin bacin rai ta ce sai wani lallabaka nake kana kaucewa to wallahi indai ka tauye hakkin yar mutane Allah ba zai Barka ba.

Batajira cewar sa ta katse wayar

Shiko dafe da kai ya yi hanzar dakin sa.

***********************

Wani docto ne mai suna Hamza wanda shi ne yana Daga cikin Malaman su Salma a skul kallon ta yake bayan yagama mata dinki uhmm wai wannan yarinyar uwar Rashin kunya ita ce yau miji ya yi wa diban Albarka.

Kallon Al'amin ya yi cikin bacin rai ya ce Amma kai jaki ne Ko a dabbobi ba sa haka duka Salma nawa take yarinyar da ba ta kai 16 yrs '' Al'amin a stage din da ake Ko wani irin zagi za ai masa ba zai ba ta masa rai burin bewuce ta samu lfy ba.

. Makotar su suka ce wa Al'amin ka kira dangin ta mana inaga hakan zefi.

Cikin tsoro ya ce ai wannan matsala ta ce ba tasu komai ake so zan ba da kudi koda kuwa nawa ne inada kudi.

Duk wani taimako anba Salma inda yadauke suka koma gida.

Restaurant yatafi yasiyo mata manyan gasassun kaji '' ya ce zakici tun da kema kin bayar da wannan tunanin yakoma gida '' iske ta ya yi lumshe da idanu '' ya yi juyin duniya taki cin Abincin nan.

Kyaleta ya yi yazauna yaci kajin shi ya ce a wannan garabasar ɗana kwasa dole saida irin wannan Kazan zan maida abun da na rasa a jikina.

.

Salma tana kwance Rahama ce tafado mata arai ta ce yanzu nasan tanacen cikin daula tare da wannan balaraben.

Taya zaki aure shi Rahama bayan Nice na cancanci haka dole wataran zan je inga daulan da kike ci ''

Wai shi Abban mu da be kaunata yaushe ze mutu ne dan wlh yana da dukiya masu yawa fidda kudin ne bayason yi Saboda zalunci.

Ji mijin da ya aura mun

Tare da fashewa da sabon kuka.

*************************

Zaune zaune shida yayan sa Abubakar Abdul jalil kallon su yake cike da so da kaunar yana musu nasiha mai ratsa zukata a kan Jin tsoron Allah..

Gabadaya dakin yadauki shiru sheik ya ce Abubakar kaine babba duk gidan nan Dan Allah koda bayan Raina ka rike kannen ka da Amana.

Abubakar ya ce InshAllah Abba zamu rayu da kai kaine za ka binne ni da hannun ka yana magana cikin raunin murya.

Sheik ya ce A'a ai duk iyaye sun fi son yayan su.

Su binne su.

Abdul jalil ya ce Abba in Allah ya yarda muna tare da da kai.

Mama ce ta shigo bakinta dauke da sallama.

Sheik ya ce Ah sannu da zuwa uwargida rangida.

Murmushi ta yi Jin wannan kirarin da mijin ta yake mata.

Bismillah ga waje ya nuna mata kujera.

Zama ta yi tana kallon Abdul jalil ta ji Ranta yasoma baci watau shima ga shi dan sheik Ko shegiyar mata saida ta yi har ta haihu gidan nan.

Murmushin yake ta yi ta ce Abdul jalil ɗana ku ne anan.

Cikin fara'ar sa ya ce uwata Nice ya gida ya aiki ta amsa masa da lfylau ne.

Abubakar ya ce mama kinga yau ban shigo sashin ki ba.

Yanzu nake shirin zuwa inna fita nan

Ganin Mama ya sa sheik katse nasihar da yake musu ya ce su tashi su tafi.

Duk suka tafi ba ƙaramin dadi Mama ta ji ba ganin sheik ya fara dawo da hankalin sa a kan ta.

Cikin sanyin murya ya ce Aishatu ta ce naam tare da kallon sa.

Numfashi ya fesar ya ce Amma kin san Sa'adatu cikine da ita Ko duk yau bakiga ba ta fito ba zazzabi ne yarufe ta yafada yana kallon ta da murmushi kwance kan fuskar ta..

Innaliahi wa'inna take m'aimaitawa a cikin zuciyar ta waini Aishatu kullum sai an kunsamin bakin ciki ne.

Banda tsanar Sa'adatu babu abun da takeji cikin ɗAnne kishin ta ta ce Ayya MashaAllah tabarakallah Ashe dai Allah ya yi da rabon zata kara haihuwa a gidan nan.

Tun da. Yanzu ka aurar da yayan ka yakamata ace ka saida haihuwa gudun abun fade.

Sheik ya yi murmushi ya ce kuma haka ne fa.

Kin san me ta ce A'a saika fada mijin Rahama yana mun kama da wanda nasani amma har yanzu nakasa tuno ainihi inda nasan me kama da shi din.

Zan je insayo fura ki dama mun yakarashe zancen tare da fita dakin.

Mama ta ce kam bala'in nan aiko ba zan bari ki haifi cikin nan ba InshAllah zankira kawata a waya asan abun yi....

*************************

Abdul Samad kwance yake a kan makeken gadon sa Ac na ratsashi wayar hannun sa yake kokarin ajiye wa dan yakwanta sai ganin Rahama ta fito Daga toillete ta manta yana dakin tana tafiya Ko 'ina na jikin ta na Girgiza..

Idanun sa yakai a kan kirjin ta da ba ta gama rufe su ba.

Cijje labbansa ya yi ya tashi Daga kwance ya zauna' Kallon ta yake itako harga Allah tama mance yana dakin dan Ko a gida ta Saba fitowa Daga bayi haka.

Kallon ta yake babu Ko kiftawa yana tunanin anya wannan yarinyar lafiya ta kalau kuwa tana daki daya da namiji take wannan.

Rahama ci gaba da abun da take yi '' dauko brezia Daga jakar kayan ta tana kokarin sawa hakan ya sa Idanun sa suka sauka kan manya manya dukiyar fulanin ta.

YARIMA Samad banda salati babu abun da yake yi.

Wani uban tsalle ya yi ya diro a kasa..

Hankalin Rahama sai yanzu yadawo kansa cikin tsoro tana kokarin dauko hijabin ta.

Taji ya rike mata hannun ta gam banda rawa babu abun da jikin sa yake yi Idanun sa suka kankance baki na rawa ya ce.......

3️7️

Baki na rawa ya ce bakisan hakan da kike yi ba '' babu kyau fa kidaina dan Allah narokeki '' kasa sauke Idanun sa ya yi Daga kan dukiyar fulanin ta shikuma be saki hannun ta ba '' kiciniyar kwace hannun ta take yi dan a shafin Rayuwar babu wanda ya taba ganin a ahaka sai Anty itama din sai ba ta da lafiya ne.

Malam na ji ka sake min hannuna tana kallon inda Idanun sa suke kallo a jikin ta '' kuka ta fara ta ce ka cikani dan Allah dan ta tsorata da lamarin sa.

Shikuma banda kafe ta da idanu babu abun da yake yi yana jiran ta gama fisge fisgen ta Sannan ya saki hannun nata.

 Kallon ƙaramin bakin ta yake yanda take motsa su alamun magana take amma muryan ba ta fita.

Sake mata hannu ya yi tare da komawa gadon nasa yakwanta yana mejin haushin kansa '' sai tsaki yaketa jerowa cikin Daga murya ya ce inbanda rashin kamun kai

Mace ta rinƙa yawo tsirara a dakin ka kuma ba zakai mata fada ba saita turo baki gaba karki dauka kina da abun da ze burgeni harda wani isa kike nuna mun dan ina miki fada.

Itako fasa saka brezia ta yi haka nan ta saka hijabin ta tacure waje daya takwanta adu'oi take ta jerowa ahaka barci ya yi awon gaba da ita.

Yarima Samad yana kallon duk motsin ta ya ce yakamata yafita harkan yarinyar nan gashi tana neman raina shi laifin mai Martaba ne daya hadashi da ita Ko uban me zeci da ita yakare surutan sa yakwanta da niyar gobe ze je kamfanin sa ɗa kuma cigaba da Ayyukan nasa..

**************************

Kashe gari

Yana farkawa Daga barci ya fara mika kallon sa take ta ce Barka da tashi yana da kyau inka tashi kafara da adua..

Tsaki yajero tare da sauka Daga kan gadon nasa kai tsaye yazarce toilet kai tsaye wanka ya yi tare da dauro Alwala ganin ana dab da tada Sallah ya sa cikin sauri sauri ya zira jallabiyar sa tare da dukan casbaha Ko sake kallon inda take beyi ba.

Ci gaba da karatun nata ta yi tana yi tana kallon agogo dan batason lokacin Sallah yawuce batayi ba...

Lokacin Sallah nayi ta yi Sallah tadawo tazauna tana azkarai saida Alfijir ya fito Sannan ta nade Daddumar ta tare da tattara kayan shimfidar ta.

Gadon nashi take kallo yanda duk yabi ya yamutsa shi kaikace ƙaramin yaro ne ya tashi akai.

Canza masa zanin gado ta yi nan da nan ta gyara dakin tsaf tare da fesa room freshna.

Cikin hanzari ta fada toilette ta wanke shi anan take ta tsaya ta yi wankan ta da ruwa mai dumi.

Da kayan da zata canza tashiga toilettes din.

Tana canzasu ta fito gaban mirrow dinsa ta nufa ganin babu wani tarkace awajen hakan sai turaruka guda shida.

Barin dakin ta yi tare da saukowa kasa nan ma ta gyara ko'ina tare da kunna turaren wutan da yar kwatano market ta saidawa Anty.

Duk. Daga waje ya dinga Jin kamshi na tashi karasowa falon ya yi yana kallon yanda aka gyara Ko ina dan shi ma'abocin safta ne.

Be tsaya wata wata ba ya yi dakin nasa nanma ya iske yanda ta canza masa tsarin dakin sai yaga ashe duk iyawar sa akwai wacce tafishi..

Ka santuwa yau akwai aiki dazeyi ya sa yakara shiga bayi ya yi wanka ya sanya

Suite riga da wando'' ba ƙaramin kyau ya yi da shigar ba takalmin da haf cover ya sanya turaren sa one love yadauko ya feshe jikin sa cikin dan sauri sauri yake saukowa Daga kan matakalan step din '' yana kallon time dake tafiya.

. Zazzakar muryan ta me dadin saurara yaji tana fadin inakwana Amjad.

Be ba ta Amsa ba ta gefen idanu yake kallon ta '' cikin isa da ba da umarni ya ce acikin kitchen dame dame babu.

Shiru ta yi tana nazari cen saita ce inaga akwai komai mai ne kadai yakare ''.

Barin ta ya yi nan durkushe tare da zuwa kitchen din yabude frij din yaga naman yakusa karewa haka ma kayan tea yaga duk sunyi kasa.

Cikin sauri yabaro kitchen din sallamar drever dinsa ya sa yamaida hankalin sa a kan sa dauke yake da biredin kwakwa cike a leda dan shi Yarima Samad yake ci..

Drever kallon Rahama yake ya ce inakwana Madame fuska a sake ta ce lafiya lau dan gaisawan da suka yi da drever ba ƙaramin haushi suka bashi ba.

Daidai ta nutsuwar sa ya yi ya ce kaje market kayo cefane tare da bashi Atm card dinsa.

Ya amsa cike da girmama wa yajuya tare da barin falon.

Shima yarima take masa baya ya yi zefi ce har yakai bakin kofar fita yaji tana fadin bakayi break ba '' Ko kallon inda take beyi ba'' sa kai ya yi ze fice yaji tana fadin Allah ya kareka da sharin hanya yabaka Sa'a yadawo da kai gida lafiya.

Ameen yafada cen ka san makoshin sa tare da fita cikin sauri saurin sa..

Rahama zama ta yi tana tunanin bara takoma takwanta daki '' tunowa ta yi taga wayar ta ya ajiye kan mirrow har ta yi tunanin taje tadauka saita fasa tsoro take ya ce ta take umarnin sa.

 Gashi duk ta damu so take ta yi waya da Abba wanda tun da tabar gida ba ta karajin muryan sa ba har ita mama.

Tunanin Salma take ta ce anya ba ta tare gidan mijin nata ba ita gaskiya tanason taga yar kanwar ta batasan ya za ta yi ba.

************************

Kwatano.

Baban Maryam ne tare da Mamy yakawo mata ziyara '' tarba mekyau ya samu Daga gareta.

Cikin sakin fuska ta ce ina anty na yasu maryam suke ya ce lafiya kalau Alhmdulilah.

Baban Maryam ya ce daman nazo wuce wa nace bara inbiyo ta wajen ku dan agaisa.

Mamy ta ce wlh muna godiya da ziyara kaci abinci mana cewar Mamy

Uhmm na koshi ya ce tare da tashi cikin kasa da murya ya ce wai yaushe Yarima Samad zedawo ne Mamy '' kallon sa take kaman mai nazarin sa.

Ta ce nikaina ba zance ga rana ba.

Dariya ya yi ya ce aiko yakamata yazo da Amaryar sa Ko dan dangi su ganta kin san Amarya farin jini gareta.

Mamy ta ce haka ne gaskiya amma InshAllah zezo da ita.

Sa kai ya yi tare da barin gidan kai tsaye gidan malamin sa yatafi.

Cikin bacin rai yake magana ya ce haba Malam kullum kana min aiki inajin dadi a kan siyasa ta da komai m'a ya za ai wannan ta gagareka.

Malam yabuga kasa ya ce kayi hakuri wallahi wannan matar da yake aure Rahama hatsabibiya ce bawai tana bin bokaye da malamai bane '' A'a ita kullum cikin ambaton Allah take koda kuwa a zaune take bakin ta baya shiru '' hanya daya ce kawai shi ne '' asamu tazo garin nan '' mun San yanda zamuyi asamu wanda ze shagaltan da ita har ta saki layi wlh muna yin haka ba ta kara koda kwana daya da auren Samad a kan ta korar wulakancin ze mata.

Kuma ka san me ze faru.

Abban Maryam ya ce A'a.

 Malam ya ce Mamy zata tsine masa Mai martaba zeyi Allah wadai da shi harya kore sa a masarauta ka ga kuna samun sa ze karbi tayin ku na auren Maryam.

Amma dole saita zauna masarautar ita kanta Maryam din.

Baban Maryam ya ce yanzu na ji bugu '' cike da farin ciki yabar wajen malamin sa.

.........................................

Abdul Samad yana isowa Ma'aikatan gabadaya suka fito ana masa Barka da zuwa rabon sa da yazo tun ranar da aka daura masa aure...

Cikin nutsuwa ya fara magana dafatan babu wata matsala daya kunno kai a kamfanin nan dukan su suka ce babu matsalar komai..

Chief accounta ne yakaraso gaban sa kan sa adurkushe ya ce Ranka yadade ranar juma'a anfita da motar shinkafa ba tare da sa hannuna ba.

Mamakin kalaman sa Samad ya yi ya ce kai kana ina hakan tafaru.

Chief accounta ya ce ina office babu inda naje ranka yadade.

Yarima Samad ya ce duk ku sameni a office dîna kai tsaye yafice.

Cike da kasaita yake tafiya wanda duk wanda ze ga yanayin tafiyar sa za su yi zaton takama ne basusan kwarjini ne na gidan sarauta ba.

Nan surutu ya barke sakanin Ma'aikatan MD ya ce taya za a ce anfita da motar shinkafa babu sa hannun Chief accounta.

Manager ya ce gaskiya hakan da ake yi shi ne zekara sawa ya canza mu be dade da canza ma'aikata ba Saboda yakamasu da laifin sata.

PA ya ce gaskiya aduba lamarin nan kada ya yi mana kudin goro.

Yarima Samad yana shiga office dinsa cctv camera ya kunna yana kallon abun da ya faru na sati daya da suka wuce.

Wannan motar da ake complain din fitar ta babu sa hannun chief accounta yake kallon yanda yasha lodin buhunan shinkafa dari biyar acikin sa harda dauri.

Sallamar chief accounta da manager da PA ne ya sa shi maida hankalin sa a kan su kallon suke yake amma su a zaton su hankalin sa baya kan su.

Chief accounta ya ajiye file din gaban sa '' dauka ya yi ya shiga duba ranakun watan da time din ya yi daidai da wanda yake a cikin camera din.

Karshen file din sa hannun Marwan yagani cikin tsananin mamaki ya ce Marwan kuma a zuciyar sa.

Kallon su yake ya ce akira masa mai gadi babu ba ta lokaci PA yatafi suka taho tare da cike da girmamawa mai gadi ya ce Ranka yadade gani kansa aduke.

Lokacin da za a fita da shinkafa ranar juma'a ba a nuna maka file bane.

Mai gadi ya ce Ranka yadade an nuna min da zanyi magana ince kada motar tafita shi ne wannan kanin naka yazo ya ce ai tun da shi ya sa hannu ana iya fita da shi kaji dalilin bude masu gate.

Kallon sa yake yana kallon su chief accounta hannun ya yi musu Alamun su koma bakin aikin su.

Dukan su fita suka yi.

Chief accounta ya ce Allah yataimakeni wallahi yanda nakejin dadin masana'arta nan ai ba zan so in rasa mukami na zancigaba da rike gaskiya kana ganin ba a kai Ko'ina ba harna fara ginin gida na PA ya ce gsk muna Jin dadin kamfanin sa kuma baya tauye hakkin kowa amma fa kashiga hakkin sa baya nuna ma ya sanka bare kayi tunanin sassauci Daga gareshi.

Hakadai suka yi ta firan su kowanne cike da farin ciki ya yi office din sa..

Shiko Samad kiran Marwan ya yi Awaya ya ce watau kai Dan iska ne Ko.

Taya za ka fitar da dukiyata ba tare da sanina ba.

Marwan ya ce ai inaga na isa da kayan ka shi ya sa nayi haka kuma kudin bukatu nayi dasu.

SAMAD ganin ze ba ta masa lokaci a banza yafita harkan sa tare da katse wayar..

Yana murmushin da shi ya baiwa kan sa sani.

Kiran Faruk ya yi yana tambayar ya suka kare a case din.

Daga can ɓangaren ya ce abun ba sauki fa wallahi dan kaina ya kulle Yarima ashe haka ka keda na mijin kokari ban sani ba.

Atakaice dai andaga shari'ar sai nan da sati biyu wlh kazo da kanka dan matar harta fara sarewa da lamarin.

Yarima Samad cike da damuwa ya ce ni dai ba zan bar zaluncin ina gani ban dakatar ba.

InshAllah zanzo kafun lokacin.

Ina son duk abun da kake gobe kataho kaida Aminu kada ku kuskura kuzo da Marwan cikin gamsuwa da bayanan sa Yarima Samad ya ce kar ka damu.

Anjima kadan zan je filin airport dinka induba maka abubuwa dake tafiya kamar yanda ka tambaya.

Nasan kanada bayanan komai a kan système dinka.

Yarima Samad ya ce kwarai kuwa inada bayanin abun da ke wakana inka je kamun magana zanyi magana da secretaria har za su yi sallama Faruk ya ce wai ina matar taka take ne amma tare zaku taho Ko.

Cikin Jin haushin sa ya ce kodai in sake ta ka aura ne.

 Bejira amsar Faruk ba ya katse wayar.

Yana Girgiza kansa.

Ran sa nakara baci cikin fada ya ce yarinya saikace Aljana nifa shi ya sa mata masu kyau ba sa burgeni.

.........

Faruk yana ganin ya katse wayar ya ce ikon Allah shi wannan wai meye matsalar shi da matar shi.

*************************

Baba Salihu zaune a dakin nasa yana kallon wani film din larabawa a tashar saudiyya sossai film din ya ja hankalin sa.

Wayar sa ce tafara ring bugu biyu zuwa uku ya ɗaga ba tare da ya yi magana ba.

Daga can ɓangaren ya ce ya shugaba wlh Abdul Samad ya yi aure ya a garin kano '' baba Salihu ya ce ka gayamin rannan daman yana neman aure ne ba ka taba gayamin ba.

No wlh Daga wajen daurin auren ne aka maida auren a kan sa.

Baba Salihu tashi Daga zaune ya yi ya ce bangane aka maida auren kansa ba yimin bayani yanda zangane yakarashe zancen cikin kwadaituwa da son Jin labarin.

Wanda ke ma sa bayani numfashi ya fesar yana waige waige kada wani yana bayan sa besani ba.

Ganin babu kowa ya sa.

Ya fara masa bayanin yanda abun yaka sance tun daga farko har zuwa daurin auren.

Baba Salihu cikin tsananin Mamaki ya ce kana nufin Rahamata Abdul Samad dîna ya........

3️8️

'' '' Rahama ta da Abdul Samad dina ya aura.

Ya ce kwarai kuwa ita ya Aura ya shugaba NA !!

Baba salihu dan tsananin farin ciki mantawa ya yi be katse wayar ba..

Sujjada yayiwa Allah nagodiya a kan ni'imar da Allah ya yi masa na azurta dan shi da matar Arziki.

Ihun kiran dattijon yashiga sai gashi yazo aguje ganin shugaban na dariya shima yasoma murmushi ya ce ya shugabana ba ni labarin ni'imar daka samu tare da zama kan kujera.

Baba salihu ya ce Allah ya Amshi rokona tashin daren da nake yi Allah ya amsa wallahi Abdul Samad Rahama ya aura.

Dattijon baki yaki rufuwa dan Murna ya ce ya shugabana ka ga yanda Allah ke ikon sa Ko daman inkarokeshi zebaka inkuma yahanaka kila babu Alkhairi ne tattare da hakan..

Kayataccen Murmushi baba salihu ya yi tare da sake daukar wayar sa yakira wannan me ba sa labarai.

Baba salihu ya ce dan Allah ina son kabincika mun yaya zamar Abdul Samad yake da Rahama narokeka Daga can ɓangaren ya ce Ranka ya dade kaban nan da zuwa gobe duk wani motsin sa InshAllah yana kan idanu na kuma zan hada maka cctv a falon nasa ba tare da da ya sani ba.

Cikin gamsuwa da hakan Baba salihu ya ce hakan ya yi wallahi na dade ina mafarkin wai Dana ya auri diyar shahararren Malamin Addinin zuwan ta gidan haske ya bayyana duhu ya yaye...

Daga haka suka yi sallama.

Baba salihu fita ya yi tare da tara jama'a ya rinƙa musu sadaka da kudade masu tsoka wasu har mashina ya sai musu wasu jari yabasu mata kuma keken dinki yaraba musu yasha Adu'oi bakin mutane sossai.

*************************

Kwatano

Baiwar Yarima Samad mai suna Karima cikin kwarewa da sanin aikin ta take moppin din dakin koda baya kwana ciki kullum sai angyara shi tsaf ''

Mamar ta Asabe ta shigo dakin fuskar ta dauke da damuwa ta ce Karima.

Yarinyar ta dago kai ta suna kallon juna.

Asabe numfashi ta fesar ta ce Fulani nason tasani harkan halaka kuma wlh ina tsoro duba fa baiwar nan Saratu yanda masarautar ghuezo ke neman ta ruwa a jallo shima Yarima Samad neman ta yake har gobe be same ta kuma bai daina neman ta ba..

.

Karima ta ce wai me ke faruwa ne kifaɗa min dan Allah..

Fulani ce taban wani laya insa a kar kashin gadon Yarima Samad inhar akai haka mazakutar sa zata mutu har abada babu shi babu kara sha'awar wata diya mace..

Innaliahi wa'inna ilai rajun

Karima take ta furtawa.

Cikin damuwa ta ce wallahi mama baza a saka ba kuma saina fadawa Mamy kinji na rantse ai ke baiwar Fulani ce bakida ikon shiga dakin nasa saida izinina duk wani mugun abun da za a gani a dakin sa cewa za ai da sa hannuna dan haka kikoma kice mata kinyi kinyi baki samu damar shiga dakin ba.

Ko kuma kice mata kawai kin san Mama dan Allah kifita da layan nan aikin ma dazanyi wallahi nafasa.

Asabe kallon yar ta take ta ce anya ba son Yarima Samad kike ba Karima.

Uhmm ta dan numfasa ta ce Daga na fadi gaskiya saiki zargeni '' yo ni Ko ina son Yarima Samad ba zan taba samun shi ba..

Sawun giwa ya take na rakumi wallahi.

Abun da ba za ka taba samu ba kar ka sashi aranka '' ya yi aure da Amaryar sa mahaddaciyar Alkur'an mai girma '..

Fatana su zauna Lafiya takarashe zancen tana mai nuna wa Asabe hanyar fita' '.

Asabe tafita itama ta take mata baya tare da rufo sashin Yarima Samad.

Kai tsaye dakin Mamy ta nufa bakin ta dauke da sallama''' iske Mamy ta yi zaune khadija namata tsifa cike da girmamawa ta rusuna tana mata kirari.

Uwa goya marayu Matar sarki uwar sarki Allah ja da ranka yake shugaban Adalai.

Mamy tun da ta ji Karima na mata kirari tasan Akwai magana a bakin nata hakan ya sa ta ce wa khadija ta tashi tabasu waje..

Khadija ta ce haba Mamy wai dan Allah mene ne dan an yi maganar gabana tana turo baki gaba cikin shagwaba.

Mamy ta ce ki tashi nace Ko ba na son taurin kai.

Badan taso ba ta tashi tana buga kafa kasa..

Karima taba Mamy labarin abun da ke faruwa cikin tsananin tashin hankali Mamy ta ce wai mutanen nan me suke nufi ne sun samu gaba so suke su ga bayan mu..

Karima ta ce Mamy wallahi ba na son abun da ze cutar da Yarima Samad koda na second daya..

Dan Allah kiyi wani abu akai Mamy ta numfasa ta ce karki damu Karima nagode Allah ya shige mana gaba..

Cike da nutsuwa Karima ta koma inda take kwana..

Mamy nazarin kalaman kArima take na fadin ta yi wani abu akai...

*************************

KANO...

''' Yarima Samad a gajiye yadawo gida be tsaya wata wata ba ka santuwa lokacin magrib yakusa.

Hakan ya sa cikin hanzari ya dauro Alwala..

Cikin sauri sauri yake ze tafi masallaci kallon Rahama yake a falon zaune so yake ya ce mata baza ta yi Sallah bane sai yafasa ya sa kai.

Ta gefen idanu take kallon yanda yake ta zuba uban sauri sanye yake da Farar jallabiya a jikin sa..

Har yafice Daga gidan tana kallon hanyar dayabi..

Uhmm waishi wannan mutumin me yake nufi ne ba zai ban wayata bane.

Ina son inkira Abba wayyo Allah ya sa yadawo da wuri tafada cike da damuwa...

Shiko yana shiga massalaci aka tada Sallah..

Be baro massalacin ba saida akai sallah isha'i.

Shafa cikin sa ya yi ya ce tun shayin ɗana sha office ban kara cin komi ba.

Sauri yake yazo gida ya yi wanka yashirya zuwa restaurant..

Yana shigowa falon '' Rahama ta tashi Daga inda take zaune kusa da shi ta matso murya cen kasa ta ce dan Allah kaban waya ta ina son nayi waya da Abba na.

Kallon bakin nata yake yanda take zaro zancen.

Cikin nuna isa ya ce Abban ki ai ya saidake tun da ya miki aure.

Turo baki ta yi gaba ta ce ni wallahi ba saidani ya yi ba Atoh takarashe zancen tana turo baki gaba.

Kallon ta yake ya ce ba saidaki ya yi ba to mekike yi a gidana.

Yarfe hannayen ta ta yi ta ce ina zansani.

Oho. Ina zaki sani kikace Ko ?

Eh haka nace ni dai kataimaka wlh ina son nayi waya..

Muje daki ya ce mata..

Ganin ta tsaya ya ce nace mu je Ko inbaki wayar..

Rahama ta ce sai dai kai kafara yin gaba.

OK yafada tare da yin gaba.

Tana binsa a baya '' suna shiga dakin yaga tabar kofar a bude.

Zuwa ya yi dan yarufe '' yaga tazo tana kokarin fita da mamaki yake kallon ta ya ce harkin ɗau wayar ne..

Girgiza kai ta yi ta ce A'a nafasa dauka.

Ki koma daki Ko nace ganin ta noke ya sa ya daka mata tsawa cikin tsoro takoma dakin kallon shi take yarufe dakin tare da murza mata key yacire makullin jikin kofar...

Bude wadrobe din sa ya yi yadauko wata sabuwar waya kirar iPhone 13 plus irin tashi ya ce amshi da wannan wayar zaki ringa amfani yanzu akwai layi a ciki.

Hannun ta na rawa ta karba.

Nagode ta furta cike da Jin dadi ta ce Allah ya saka maka da Alkhairi.

Ameen yafada yana kokarin cire kayan jikin sa.

Wayar tashi tafara ring..

Duba screen din wayar ya yi yaga sunan Mamy.

Daukar wayar ya yi tare da karawa akunne.

Ya ce Mamy inada niyar inkiraki sai ga Kiran naki.

Dafatan duk kuna lafiya.

Daga can ɓangaren ta ce kalau muke Samad..

Ina Rahama take.

Kallon Rahama yake ya ce gata nan Ko inbaki ita ne.

Mamy ta ce ba ni ita..

Mika mata wayar ya yi cike da ladabi harda rusuna kamar Mamy na gaban ta ta ce Mamy ina wuni da lafiya lau ta amsa mata..

Rahama ta ce ina ƙanwata khadija '' da Ahmad cikin Jin dadi Mamy ta ce kalau suke diyata..

Shiru ne ya ratsa tsakanin su..

Mamy ta ce Rahama ina son kibi mijin ki yi nayi bari na bari nasan kin sani

Tunatar dake nake.

Cike da Jin dadi ta ce InshAllah Mamy nagode

Mikawa Abdul Samad wayar tayi.

Mamy ta ce Tsakanin ka da Allah wani abu yashiga tsakanin ka Da Rahama ko beshiga ba.

Shiru ya yi ya gaza ba da amsa '' hakan ya tabbatar mata haryanzu be kusance ta ba..

Cikin ba da umarni ta ce Yarima kacire girman kai ka rungumi kaddara '' duk wanda yabi maganar iyayen sa ba zai taba tabewa ba..

Yaushe kazama haka ne Yarima ina yabon ka sallah za ka gaza Alwala..

Dan Allah kataimakeni wallahi jika nake so kuma a jikin Rahama koda bakason ta kature kiyayyar dan wataran ze iya zama so.

Hakkin daya rataya akanka shi za ka duba kar ka bari shaidan yamaka huduba..

Gabadaya jikin sa ya yi sanyi ya ce Mamy kiyi hakuri wallahi ban san ya akai na rinƙa ba ta miki rai ba kiringa tayani da Adua yake mahaifiyata..

Cikin Jin dadi ta ce InshAllah ɗana Daga haka suka yi sallama..

Kallon Rahama yake da sai murna take ta kunna wayar takawo haske.

Tunanin kalamin Mamy yake ya ce ni yazanyi da yarinyar nan...

Cikin cool voice ya ce Rahama zo nan..

Dago kai ta yi ta kalle sa.

Bata kawo komai aranta ba..

Ta tashi ta nufi inda yake.

Nuna mata kusa da shi ya yi data zauna..

Ba musu tazauna tana sauraren abun da ze fada.

Hannun sa ya sa yana kokarin yaye mata hijabin ta.

Ta rike hajibin tana Girgiza kai dan Allah karbani da abuna kokarin tashi take ya sa hannayen sa ya jawo ta ta fada jikin sa..

Cikin tsananin tsoro da firgici ta ce Dan Allah kabari '' ganin Idanun sa sun rufe cikin zafin nama ya cire mata hijab.

Hannun sa na.........

 

3️9️

Hannun sa ya sa kan boob dinta yana kiciniyar cire mata brezia '' kama hannayen sa ta yi da karfin ta tana kokarin tashi '' takasa koda kwakwaran motsine ba ƙaramin riko ya yi mata ba.

 Cikin kuka ta ce dan Allah kabari wallahi banaso meye haka ne wayyo anty ki taimakeni.

Yana rabata da brezian ta rikicewa ya yi ganin manyan manyan boob a tsaye cak..

 Murya cen kasa ya ce ki nutsu kiban hadin kai koda sau daya ne kacal ba zan cutar dake ba..

Tare da mata rada a kunne...

Jin hannun sa kan boob din ta yana shafa su ba ƙaramin rikicewa ya yi ba dan ji ya yi bêta taba abu dadin shafawa ba irin sa.

Rahama cikin kuka yanda yake murzasu ta ce wlh da zafi dan Allah kabari kar ka keta min haddi taya za ka kusance ni bayan bana sonka.

Wayyo Anty ki taimakeni.

Cigaba dayin abun da yake yi ya yi Sam baya fahimtar abun da take fadi dan ya Lula wata sabuwar duniyar yana yawo sararin samaniya.

Yawo yake da hannun tun Daga ƙaramin bakin zuwa kan hudan cibiyar ta gabadaya ta rikice kalaman sa daya ce sadaka aka bashi ita suke mata yawo cikin kan ta..

Yarima Samad dake kokarin kai hannun sa kan privet pad dinta gam tarike hannun sa '' hankalin sa yadawo jikin sa ya ce yanzu da kika rike mun hannu me hakan ke nufi ba za kiban hakkina ba kenan..

Eh ba zan ba ka ba '' tafada murya a tausashe kaida Kace auren Sadaka aka ba ka ni kar ka manta bana sonka kar kayi gigin tabani domin ba ni da Sallah ina Al'ada.

Iyaye sun hada auren nan nayi biyayya ne duk mai son dace to zebi iyayen nan..

Kallon ta yake da fitannanun Idanun sa banda wutar sha'awar ta babu abun da ke yawo cikin sa...

Murya cen kasa ya ce mu gani in baki da sallah..

Kokarin kwantar da ita yake takara fashewa da sabon kuka ta ce wai meye haka ne dan Allah kabari.. Ba na sonka Ba na sonka zata kara maimaita wa yarufe mata baki tare da sakin hannayen ta..

Jikin sa yahau rawa kamar mazari dafe da kai yake kalaman ta kadai suke masa yawo akai.

Ganin ya matsa kusa da ita.

Cikin sauri sauri tafada toilette tana maida numfashi ga boob dinta da suke mata zugi dan murzan da yasha.

Ruwan dumi ta hadawa kanta wai ita dole boob dinta zata gasa...

Maganar zuci take ta ce wannan mutumin daman haka yake beda kunya jibi fa yanda yake neman zubar da girman sa a idanu na.

Kuma yake son yagane min sirrina uhmm Allah ka ceci Daga hannun sa..

Tana fitowa Daga bayin ta iske baya dakin yafita hakan ya sa cikin hanzari ta canza kayan jikin ta.

Tare da baro dakin nasa kai tsayye dakin dake kusa da nashi tashiga hade da kayan ta..

Tana shiga dakin

Key ta murzawa kofar..

 Shiko yarima Samad tuki yake amma hankalin sa baya jikin sa surar Rahama kadai yake gani a Idanun sa...

Ji ya yi daman ya ka sance kullum yana manne da ita..

 Kalmar Ba na sonka Ba na sonka shiyafi tsaya masa a rai mtss tsaki yaketa jerowa ya ce wannan Kalmar taki tafi guba daci tun tasowa na Daga kan kuruciya ta babu wanda yataba gayamin haka..

Yan mata suna bina suna kuka in sosu amma banda lokacin sauraren su.. Sai mata ta ta sunnah zata furta ba ta sona..

Har ya je restaurant yadawo hannun dauke da kwanun abincin falo yazauna domin cin abinci sakalar abincin yake da ƙyar yaci kadan a ciki.

Banda tafasa babu abun da zuciyar shi yake yi.

Kiran Faruk ne yashigo wayar shi '' da ƙyar ya ɗaga wayar muryan sa ba ta fita sossai.

Faruk ya ce Yarima meyake damun ka ne naga yanayin ka akwai damuwa a tattare da kai.

Yarima Samad ya ce kaide gajiyar aiki ce kar ka damu '' Faruk tun suna yara ya san halin Samad dan haka ya san karya ce kawai yake masa..

Dan Allah Yarima gayamin meyake damun ka kar ka sa inkasa barci '' kai ma ka san haka..

Ajiyar zuciya Yarima Samad ya sauke ya ce wannan yarinyar Rahama wai ni take gayawa ba ta sona batasona..

Faruk ya yi Murmushi ya ce karfa kamanta kacemin ba ka son ta..

Kodai yanzu kafara son ta ne..

Tsakiii ya yi ya ce a kan me zanso maso wani duk abun da wani yarigani shiga to hakura nake dashi.

Faruk ya ce bangane wani yarigaka shiga ba.

Eh ina nufin zuciyar ta akwai soyayyar wani ka ga zaman namu beda amfani kai min Alfarma daya '' Faruk ya ce inajin ka '' ya ce ina son gobe kataho da wuri Aminu kadai ze biyo ka Sannan Baiwa ta Karima nake son ka sai mata waya asirince kabata nombar wayata '.

Cikin gamsuwa Faruk ya ce InshAllah tun da safe zan je wajen nasu zan yi yanda kace..

Daga haka suka yi Sallama lemu yasha tare da tashi yabar falon.

Bakin sa dauke da Sallama yashiga Jin shiru ba a amsa ba ya sa shi shiga dakin dube dube yake yi a dakin ganin ba ta ciki ya leka toilettes din nanma shiru rike da kugun sa ya ce yarinyar nan ina taje ne.

Wata zuciyar ta ce yo ina ruwan ka da ita wacce ta dubi tsabar Idanun ka ta ce ba ta sonka.

Wanka yashiga ya fito ya canza kaya zuwa na barci..

Rage haske dakin ya yi yana lumshe Idanun sa kalaman sa kadai suke masa yawo akai..

Ahaka har barci ya yi awon gaba dashi..

Ita Ko Rahama tuni barci ya yi awon gaba da ita '' cen cikin barcin ta taga wani rikitaccen Aljani yana bin Yarima Samad shikuma yana gudu iya karfin sa..

Wani mahaukacin dariya Aljanin ya yi ganin Rahama ta bayyana gaban sa '' ta ce kai me mijina ya yi maka ne kake bibiyar rayuwar sa cikin kaduwa take magana.

Ya ce mijin ku dai Ko kuma ince tsohon mijin ki dan kishirya zaman takaba nan kusa.

Firgit. Ta farka ta fara karantowa adu'oi kala kala ta dade zaune tana tunanin me wannan mafarkin yake nufi wata zuciyar ta sharrin shaidan ne da wannan tunanin takara komawa ta kwanta...

**************************

Kashe gari

Anty tashirya tsaf dan zuwa dauko Salma dan kwance take babu lafiya tun da wannan abun ya faru..

Zuwa ta iske Salma duk ta rame ta lalace saika ce ba Amarya ba cike da tausayin ta tadauko ta tare da dibar kayan ta..

Makotan su suka ce wallahi mijin ta beda kirki kabar mace kwance cikin wannan halin ace tun jiya da yafita besake dawowa ba haba ai wannan zalunci ne..

Salma tana ta cije bakin ta Alamun zafi takeji sossai acen kasar ta..

Anty ta ce ai kubarshi ze san ya iya wulakancin ya mance Ko waye uban ta.

Makotar suka ce wane uban ta dan Allah.

Anty ta ce sheik Abdurrazak kabeer hizqeel makarfi ni kuma amaryar sa ce..

Salati suka fara suna mamaki diyar sheik imam ce muke zaune gida daya da ita amma wannan dan iskan yake wulakanta wa.

Ta ce kwarai kuwa ran anty ya yi mugun baci dan tasani rainin wayau.

Da ƙyar ta tashiga motar da taimakon anty..

Suna isa gida kofar gida suka iske Sheik yana sallamar wasu baki.

Da suka kawo maka wata Wasika amma be bude taba ganin su Salma ne ya sa yake kallon yanda Salma ta fito yanda take tafiya yake bin ta da kallo ba ƙaramin tashin hankali yashiga ba.

Cikin hanzari yakaraso gaban Salma yana jero mata sannu tare da taimaka mata wajen shigar da ita gida.

Mama cikin tashin hankali ta ce amma Al'amin dan iska ne jibi abun da yayiwa Salma..

Kwantar da ita anty ta yi saman gadon su..

Ta ce taware kafafun ta ba musu ta ware dan azaba wajen tagani kamar danyen nama jajir har wani jini jini yabushe awajen..

Cikin ihu ta ce ya Sheik dan Allah zoka gani..

Sheik aguje yayo dakin Girgiza kai ya yi ya ce A'a sa'adatu ban iya kallon.

Mama ce ta shigo cikin rudani ta leka salati ta saka tana kuka iya karfin ta ta ce wallahi sai yasan ya mana wulakancin zamu rama ne...

Sheik da duk yafita hayyacin sa hakan ya sa yakira babban Aminin sa ya sanar masa abun da yake waka na.

Aminin nasa ya ce subuhannalah gani nan zuwa wannan ba maganar shiru bane Daga haka suka yi Sallama..

*************************

Kwatano..

Masarautar gheuzo.

Mama karama ce ta aika baiwar ta gayawa jakadiya tana son ganawa da mai martaba.

Cike da girmamawa taje ta sanarwa jakadiya bukatar Mama karama.

Da sallama jakadiya ta isa fada cikin risina hannun ta asama ta ce Barka da hutawa ya shugaban Adalai mama karama tana neman ayi mata Iso...

Waziri ya ce anbaki dama jakadiya Sarki ya amsa.

Cike da girmamawa ta koma da sanar da baiwar Mama karama..

Sarki zaune ya kalle bayin da ke cikin dakin da waziri da su liman ya ce duk su tafi dan a tsarin sa inzeyi magana da Mama karama Ko Yarima Samad baya yinta gaban kowa....

Mama karama ta Iso fada cikin tsananin damuwa ta ce Allah taimaki Sarki gaskiya wallahi daga ji da rashin ɗana haba shekara nawa yanzu yana raye Ko ya mutu ban sani ba '' kullum cemin kake InshAllah ze bayyana yaushe ne kuma a wani lokaci saina mutu kenan bangana da ɗana ba..

Duk abun da ya faru a masarautar nan kanada masaniya amma ka take sani ni dai daga ji daga ji tana yarfe hannayen ta..

Kallon yake ya ce meye hujjar ki a kan Salihu dazakice bashi ya aikata laifin nan ba.

Mama Karama ta ce nikuwa keda hujja ita ce baiwa Saratu.

Kallon ta yake cikin dan bacin rai ya Daga mata hannun tsaya kiji wlh duk son da nakewa salihu bazai sa inki gaskiya ba.

Mene ne abun damun kai tun da ga dan sa nan..

Duk son da nake mishi namaidashi a kan dan sa bana kaunar sake hada idanu da shi ya ce cikin tsawa har tari yasoma dan bacin rai..

Mama karama tashi ta yi Daga zaune ta ce banzo da asamu matsala ba nida kai.

Amma tun da abun yazama haka InshAllah saikayi nadama karubuta ka ajiye Daga haka tabar sashin sa cikin bacin rai..

Shiko Sarki dafe da kai nan take ya fara tuno abun da suka wuce shekaru biyar tashi Daga zaune ya yi ya ce Allah ya isa tsakanin da kai Salihu hawaye nabin kuncin sa..

**************************

Kano

Kusan karfe goma na safe Faruk ya Iso kanon shida Aminu kai tsaye gidan su nufa.

Da sallama bakin su.

Abun da sugani ya sa suka tsaya cak.

Ganin Rahama kwance a kan kujera 3str hannun Yarima Samad acikin rigar ta..

Kallon juna suke Faruk da Aminu...

 

4️0️

Hannun Yarima Samad acikin rigar Rahama yana shafa boob din ta

ita Ko barci take batasan abun da ke faruwa ba Daga ta gama aikin ta tadan kwanta ta huta shi ne yatsaya lalabe.

Jin kamar inuwa Daga waje ya sa ya sa yai maza yacire hannun sa yana kallon hanyar waje.

Faruk da Aminu labewa suka yi gefe dan kada ya gan su..

Fitowa suka yi Daga inda suka labe suka yi kaman yanzu suka shigo bakin su dauke da sallama.

Yarima Samad cikin Farin ciki ya tarbe su ya ce sannun ku dazuwa mu je dîner table ku zauna..

Binsa suka yi Abaya suna dariya dan shi beson Idanun su ya sauka a kan Rahama da rabin boob din ta ke waje.

Jin hayaniya a cikin gidan ya sa ta farka tana mika agogo ta kalla taga lokaci harya tafi.

Tana saka hijabin ta tahau kan matakalan step Faruk ya ce Amarya babu magana ne.

Juyowa ta yi ta tsaya Daga gefen nasu cike da girmamawa ta ce sannun ku da zuwa ya gajiyar hanya yasu Mamy da su Ahmad

'' lafiya lau suka ba ta amsa cike da Jin dadin sakin fuskan ta.

Shiko Yarima Samad kauda kan sa ya yi gefe shi ala dole fushi yake yi da ita..

Wuce su ta yi takoma dakin nata dan tashirya zuwa kitchen yau ga baki babu cin indomi dan Ko ta yi girkin ma baci yake ba..

Faruk ya ce uhmm kaide Allah yabaka duka.

SAMAD ya ce kamar ya kenan ?

Ina nufin Matar ka kyakyawa kaima kyakyawa yanda ka san ku ne kuka zabi kanku a ma'auratan.

Aminu ya ce maganar ka dutse Faruk gâta da nutsuwa, wallahi.

Yarima Samad cikin son kawar da zancen ya ce nasan kun kwaso yunwa Ko.

Bara inkira ta tadafa muku Abincin.

Tashi ya yi ya nufi dakin nata.

Cikin sauri sauri yake taka matalan step din.

Faruk da Aminu kallon juna suka yi suna dariya kasa kasa..

Aminu ya ce kana ganin Yarima katon jarababben boye ne tun kan ya yi aure nasha fada maka zeyi ruwan fitina inyayi aure kace ba ka tunanin haka dan baya harkan mata..

Faruk ya ce uhmm ai yau ganau muke amma ji yanda ya canza kamar bashi muka gani ba maciji sari ka noke kawai.

Dariya suka kyalekyale da shi suna tafa hannayen su..

Shiko Yarima Samad cike da takama ya shiga dakin iske ta ya yi zaune tana wasa da yatsun kafar ta.

Bakin sa dauke da Sallama kallon ta yake cikin yin kasa da Murya ya ce ya ma sunan ki ne ?

Tayi shiru ba ta bashi Amsa ba '' karasowa gaban ta ya yi yana son yaga boob din ta amma durkushen da ta yi ya sa be ganin komai..

Ganin ta kasa take kallon shi ya sa shi gyara Tsayuwar shi cikin ba ta fuska ya ce nasan kin san munyi baki amma da yake bakisan girman baki ba.

Shi ne kika zo daki kika zauna

'' Ko dan abinci sai sun roka.

Bata dago kai ba bare ya sa ran zata amsa masa sai gani ya yi Daga zaunen tana laluben gadon dan dauko hijabin nata tasanya.

Cikin sauri yadauke hijabin yana zuba ruwan masifa beda Burin daya wuce yaga ta tashi amma ya lura kamar ta gano shi.

Ki tashi nace Ko ina magana kinyi shiru kina diyar Imam amma bakisan darajan aure ba.

Tashi Daga zaunen ta yi kallon da yake bin ta da shi ya sa ta sauke Idanun ta kasa '' cikin sanyi murya ta ce kayi hakuri maganar taka ce ban san Amsar da zan ba ka ba shi ya sa na yi shiru.

Kallon hijabin ta dake hannun sa ta yi ta ce dan ba ni hijabina daman ina shirin inje indaura masu girki kayi hakuri ba zan kara ba..

Hannun ta mika masa Alamun yabata hijabin ta..

Uhmm zoki amsa yafada 'Wayyo Allah na nashiga uku..batasan maganar ta fito fili ba.

Kin shiga uku dame yatsare ta da zararan idanun sa..

Bakomai ta ba shi amsa tare da zuwa wajen akwatin kayan ta zata dauko wani hijabin.

Ta ku daya zuwa uku ya yi sai gashi a gaban ta dagowa ta yi '' nan da nan yanayin ta ya canja ta ce mayye na dan Allah ka kyaleni banaso Jin hannun sa saman boob din ta yana kokarin Jan ta zuwa gadon nata ta turje wajen cikin kuka ta ce kamatsa mun wallahi saina yi ihu Abokan ka susan cewa fyade za ka min tana mai turo bakin ta waje..

Kan uban cen au fyade kikace mamaki yake wai wannan karamar yarinyar ashe tanada baki sossai haka..

Jin ta wabce hijabin ta Daga hannun sa tabude dakin ta yi gaba cikin sauri ta saka hijab dinta..

Faruk ya ce ka ga Yarima Daga ya je yakira ta dan iska in ance maka ɗAnne ta ya yi kar kayi mamaki.

Aminu ya ce wannan ma da muka gani kadan ne.

Hango Rahama suka yi tana saukowa Daga kan matakalan Step.

Kallon ta suke suka ɗara to ina yake shi sarkin tabe tabe..

Ganin saukowan shi

Yasa suka maida kallon su a kan sa.

cikin sauri yakaraso wajen su cikin Jin kunya ya ce ka ganta wai cikin ta ke ciwo shi ne natsaya ba ta magani.

Faruk ya Girgiza kai ya ce gaskiya ne danma maganin yana nisa ne shi ya sa ka dade ba ka gani ba..

SAMAD YA CE KWARAI KUWA TARE DA ZAMA KUSA DASU YANA KALLON Rahama yanda take tafiya duk da hijabi ne a kan ta..

Aminu cikin danne dariyar sa ya ce tabe tabe.

Samad ya ce me ma'anar tabe tabe dawa kake ne ?

Faruk ya ce dani yake tabe tabe ka san Aminu akwai iya sa suna.

Uhmm ya ce Kunga zan je in shirya zuwa aiki karfe biyu zandawo zaku rakani gidan surukai na.

Abban Adamsy ne yakirani a kan naje dan haka ku shirya zaku rankani..

Faruk ya ce uhmm masu surakai Allah yakai mu.

Uhmm suka ce suna kwabe baki dukan su biyun '' kallon su yake ya ce nalura akwai munafuncin a tattare daku...

Rahama cike da nutsuwa tafara aikin ta fried rice ta daura musu cikin kankani lokaci tahada girki kitchen din gabadaya yadau kamshin girkin nata har cikin falo..

Faruk ya ce da Alama yar malam ba a barta a baya ba wajen girki ba.

Hakadai suka wuni fira har Rahama ta gama girkin tazo ta jera masu kan dinner table..

Zubawa Samad nashi daban ta yi duk da tasan baci zeyi ba..

Cikin zalama dukan su suka je dinner table dan cin abinci.

Faruk nakai loma daya a bakin sa ya ce Amarya wannan abincin restaurant ne kai inaga Restaurant ba sa dafa irin wannan delicieux girki.

Aminu sai Girgiza kai yake yi ya ce uhmm abun ba a cewa komi anya Samad yana cin abincin gidan nan kuwa dan gaskiya anbarshi a baya.

Rahama dariya take masu tare da jera musu lemun kwali hade da kofuna anutse tabar falon dan komawa kitchen ta yi wanke _ wanke Allah Allah take tagama taje tadau wayar ta takira Abban ta..

Tana gamawa ta fito dakin nata ta nufa wayar nata tadauko tare da kunna shi yakawo haske..

Uhmm tsalle take yau zataji muryan Abba..

Danna masa kira ta yi cikin sa'a bugu daya ya ɗaga Assalam alaikum ya Abby na cikin murna..

Abba da yake yana cikin case din Salma ya sa be dago muryan ta ba.

Cikin uzuri ya ce wacece ne kibari anjima saiki sake kira..

Rahama kwabe baki ta yi cikin shagwaba ta ce Abby kana nufin ba ka gane Rahama ba.

Murmushi ya yi ya ce MashaAllah diyar Albarka ashe ke ce yar uwar kice ba lafiya muna Asibiti.

Cikin tsananin damuwa ta ce Abba Salma meya same ta ne nan da nan Idanun ta suka kawo ruwa..

Abba ya ce kedai rashin lafiya ne ya mijin naki dafatan kuna zaune lafiya Ko.

Shiru ta yi yakara maimai ta tambayar sa ganin ta ce uhmm yagane kunyar sa take kawar da zancen ya yi wajen fadin nayi kewarki sossai kirike martaban aurenki.

Zuwan docto gaban sa ya sa ya ce Rahama kibari zamuyi waya anjima.

Cikin kuka ta ce Abba zanzo duba ta.

Saurin katseta ya yi da A'a karki takura mijin naki banson yawo kinji Ko '

Ta ce na ji Abba.

Daga haka yakatse wayar..

Itako zama ta yi ta zabga uban tagumi tana tunanin meke samun Salma ne.

Yanzu ya za ai ta tafi dubata shi ne kawai take lissafi karta yahana ta..

*************************

Gabon 🇬🇦

Baba salihu ne zaune tare da wata mata mai suna hassana tana magiya ta ce kar kamun haka wallahi dagaske ina son ka koda kuwa matan ka uku..

Hajiya hassana babbar yar kasuwa ce tana yawan tafiye tafiye har kwatano take zuwa sare saren Atamfofi da shadda.

Tun ranar da suka hadu da baba Salihu yana rabon kayan Masarufi ta ji yakwanta mata duk da dattijo ne amma ta lura a dattijan ma daban yake dan Ko wani saurayin ba zai nuna masa kwarjini da kamala ba..

Kallon ta yake cikin dan hade Rai ya ce inada Mata ta kuma Daga ita babu kari dan haka kicireni a ranki dan zuciya ta nata ne ba zan mata kishiya ba a gidan duniya sai cikin Aljanna..

Ba ƙaramin haushin kalaman sa ta yi amma ta nuna babu komai tana son suci gaba da zumun ci..

Baba salihu ya ce to hassana nagode.

Daga haka tabar wajen tare da Jan motar ta yana kallon ta har ta bar inguwar tunawa ya yi da ya ce ahada masa CCTV a gidan Samad ya sa ya nufi cikin gida dan ance masa zuwa karfe biyu yakan dawo gida..

Gaban système dinsa ya nufa tare da kunna ta '' ya rubuta passport gaban système din ya matso sossai dan yaga abun da yake wakana..

Hango Abdul Samad ya yi Daga gani Daga wajen aiki yake a gajiye besan me suke fadi yaga faruk ya tashi yana dariya.

Shima dariyan ya yi harda kwalla..

Kallon su yake yanda suka shagala sossai..

Alamun cikin nishadi suke...

Rahama ya hango sanye cikin hijab doguwa har kasa fuskar ta yake kallo da kyau ganin ita ce.

Lallai kam gatanan.

Sam ya mance ba ta Jin abun da yake fade ya fara fadin Rahamtullah ta sai ganin Abdul Samad ya yi yahada rai ganin Rahama.

Be gama firgita sai ganin ta ya yi Alamun kamar magiya take masa..

Daga can ita Rahama magiya take masa a kan yabarta taje tadubo yar uwarta ganin su faruk sun bar falon dan shiryawa ya sa ya ce bazata je ba.

Amma inta matsa a kan haka suje daki sau daya ze matsa boob din ta..

Rahama har ta ce bazata amince ba.

Sai ji ta yi cikin tsawa ya ce ki tashi kiban waje.

Baba salihu dake kallon ikon Allah duk da bejin abun da suke fade ya san ruwan bala'i yake sauke mata ita kuwa kan ta aduke tana durkushe gaban sa

Daga can ɓangaren Rahama ta fara kuka ta ce mu je na'amince amma dan Allah kar ka wuce daya ya ce na ji kina iya yin gaba ina zuwa yafada fuskar sa ahade.

Baba Salihu dake kallon su ganin sunbar falon bekara ganin komai ba dan camera iya falo kadai aka sa.

Jikin sa na rawa yadau waya Domin kiran me ba sa labarai..

Yana kira yaci sa''a ya ɗaga amma shiru kake ji yaki magana.

Baba Salihu ya ce yadai kaki magana.

Shiru kake ji.

Cen ɓangaren suna shiga dakin yarufe kofar.

Idanun ta cike da kwalla ta ce meyasa karufe kofar.

Cikin fada ya ce dakin nan abokaina suna iya shigowa shi shi ya sa narufe kofar.

Dan matso mana kadangaruwa yafada yana me nufota ita kuwa tafara ja da baya baya...

Post a Comment

0 Comments