Ticker

6/recent/ticker-posts

Kanwata Na Ikilima Adam (Kashi na 3)

Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Allah kasa yanda na fara lafiya in kare shi lafiya. Wannan labarin ya faru da gaske dan kusan Book dina da nake yi true life ne sai dai in yi masa kwaskwarima dan abun ya fi ba da citta.

Ku biyo ni ku sha labari.

Ku daure ku yi comment dan in ji ra'ayoyin ku a kan Littafin nan......

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa}_

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

Marubuciyar

* Amince Da Ni
* KAI KA JA WA KANKA

Yanzu kuma gani ɗauke da

ƘANWATA

Paid Book ne

Vip 300
Special 500

Acct No. 3115484026, First Bank, ko kuma Kati MTN (Ba na son VTU)

Idan kin biya ta bank kina iya turo shaidar biyar ki ta wannan 09069080725

kanwata

🌟🌟 ƘANWATA Na Ikilima Adam [Kashi na 3]🌟🌟

4️1️

'' Ta fara ja da baya baya'

 Kallon ta yake banda haushin ta ba abun da yakeji danma tasamu har yana neman tabata shi ne take raina masa wayau cijje labban sa ya yi yana kara kusanto ta saida takai bangon daki Sannan tafara kokarin rufe Idanun ta da hannayen ta kasa tsayuwar ta yi tana kokarin durkushewa kasa.

Hannayen sa ya sa ya ɗago ta tare da Jan ta zuwa gadon '' cikin sanyi murya ya ce kwanta ina fatan kin samu Sallah yanzu Ko ?

Girgiza kai ta yi ta ce A'a nifa sai in yi wata ina jini be tsaya ba..

Dan jimm ya yi yana nazarin kalaman ta shi a iya sanin sa besan hukunce hukunce da suka shafi mata ba amma mamaki yake ya ce daman mata suna kai wata suna jini maganar zuci yake yana ciza labbansa.

Ci gaba da kallon ta yake sai fadi yake a zuciyar sa InshAllah saina cika Burin Mamy '' gashi rannan nataba boob din ta a rashin sani gashi yazame mun kamar jaraba kamata ya yi infita harkan yarinyar nan kada rainin ya yi yawa 'amma zan taba koda na karshe yakarashe zancen yana me kokarin bude zip din rigar ta..

Saurin zare hannun sa ya yi lokacin dayaga Rahma takoma masa kamar kunama wani ihu mai karfi ya saki jikin sa na rawa.

 tashi ta yi cikin razana ta ce Amjad me yake damun ka ''..

Baya baya yake ta yi yana fadin karki kusanto ni neman hanyar fita waje yake cikin sauri sauri...

Rahama tsaye ta yi tana mamakin ikon Allah ba ta kawo komai aranta.

Waigowar da zeyi sai yaga Rahama ta koma masa normal ''.

Ajiyaar zuciya yasoma sauke wa akai akai.

Kallon ta yake ya ce mu je Ko tare da yin gaba dan yanzu ya fara tsoron ta..

Kiyi sauri ki shirya mu je na ji kince suna Asibiti Ko ? ta gyada kai Alamun haka ne.

Good yafada tare da yin gaba yana tafiya cikin tsananin damuwa a kan abun da yagani........

Yana saukowa kasa ya iske su sun shirya cikin manyan kaya shadda ba ƙaramin kyau suka yi da shigan ba da huluna duk a kan su babban rigar dake jikin su yasha aiki wajen kwararren tela.

Kallon Yarima suke sake da baki Faruk ya ce banga kashirya ba kasauko.

Uhmm kun san na manta kuwa kallon yanayin shi suke ganin muryan sa ta canza sossai.

Faruk ya ce to maza ka koma kashirya kai zamu raka..

 OK ku dan jirani ya ce tare da komawa cikin dakin sa..

 Yana shiga ya iske Rahama har ta shirya tsaf tana sanye cikin shadda lace mai dankaren tsada yasha adon Stone sossai dinki ya zauna mata ajiki ka santuwa riga da siket ne ya fito mata da shap din boob din ta kuwa cas cas suke a jikin rigar da yakamata a jikin ta sossai..

 Kallon ta yake yanda ta yi masa kyau sossai kamar ba ita ba simple makeup da ta yi ba ƙaramin tafiya da tunanin sa ya yi ba..

 Azuciyar sa sai fadi yake wannan Yarinyar ta yi min kama da wacce nake gani a mafarkina wata zuciyar ta ce ba ita ba ce kada kai ya yi yana fatan yaci gaba dayin mafarkin nan nasa da tabbas wacce yake mafarkin ta ita ce matar da yake da Burin aure bayan neman mahaifin sa zanen hoton kamannin ta da ya yi da shi yake yawo.

Rahma ta juyo ta kalle shi a tsaye jingine jikin Kofa.

Muryan cen kasa ta ce dan matsa zan fita.

Kallon ta yake kamar me tunanin wani abu hannun ta yake kallo ganin ta dauko babban gyale a hannun ta.

Da mamaki yake kallon ta yana kallon abun da ke hannun ta..

Cikin Daga murya ya ce ina zakije ne ??

 Ta ce bakace inshirya mu je ba..

 Wani kallo yake bin ta da shi m'asu tsorata wanda ake kallon sa..

 Murya na rawa kaman za ta yi kuka ta ce kaine kace inshirya mu je Asibiti..

 Harara ya watsa mata ya ce eh kinyi abun da nasaki ne ba kunama kika zama ba dan ki harbeni yakai karshen zancen cikin takaicin abun da yagani ya san iska ne batasan an yi ba yanason yaga reactions din ta..

 Cikin rawar baki ta ce kunama kuma ya Allah kaimana tsari da kunama..

 Tsoro ne yabayyana a kan fuskar ta tana nanata kunama sai Girgiza kai take yi.

Alamun tarin damuwa a tattare da ita.

 Inhar ki nason kije ki ajiye gyalen ki saka hijab.

 Komawa cikin dakin ta yi tabude akwatin nata tare da dauko hijabin nata..

 Tasaka hartakai bakin kofa ya ce daka ta.

 Cak tatsaya ta ce wai Allah wannan mutumin ya fi Salma matsala tafada a zuciyar ta....

 Naam ta furta tare da waigowa..

 Ki dawo ki saka nikaf da safa yafada cikin bacin rai kinfison kina tafiya ahanya ki taraman jama'a ko

Ki bari inkinbar kar kashin inuwar aure na.

 Zakiyi abun da kika ga dama.

 Rahama ta ji zafin kalaman nasa amma ta nuna masa bakomai jiki asanyaye ta koma ta yi yanda ya ce din sannan tafita dakin..

 Saukowa kasa ta yi ganin Su Faruk suna selfie suna kyalyalewa da dariya.

Faruk yahau kan matakalan step yaba Aminu wayar sa dan ya yi masa hoto.

 Daukar shi hotuna Aminu ya yi tayi.

Rahama ta raba gefen nasu ta ce sannun ku.

 Yawwa Amarya sai yanzu cewar Faruk.

 Wai ina mijin naki ne.

 Tun dazu ya shanya mu.

 Shiru ta yi ba ta basu Amsa ba ba ta fiya son surutu Ko magana mara amfani ba.

 Samun wuri ta yi ta zauna zaman j'ira..

 Saida yakai minti Ashirin kafun ya fito Daga dakin.

 Aminu ya taba kafadar Faruk da hankalin sa yake kan waya yana chatin ya ce kalli mutumin ka.

 Wow suka Furta yayin da yake Saukowa cike da takama da izza.

 Yaci shadda geznar da babban riga kamar nasu '' takalmin sa haf cover suke kallon yanda take walwali tana sheki..

 Sanye yake da hula daidai da kalan shaddar nasa hash kala..

 Kallon shi suke ba ƙaramin kyau ya yi ba daya shanya gilashi a Idanun sa.

 Jajayen bakin sa Rahama take kallo dan tun fitowar sa itama takasa sauke Idanun ta a kan sa.

 Yana Saukowa ka san ya kalli Abokan sa ya ce sai fa nadan ci abinci restaurant zanje yana kwabe baki.

 Faruk ya ce Restaurant kuma abinci da matar ka ta Dafa fa.

 Dan Allah kaci koda kadan ne..

 OK dan kun hadani da Allah ne kun san Ko a gida bana cin Abincin yara yakarashe zancen yana kallon Rahama da ta dukar da kanta kasa.

 Tana maimaita kalmar yara daya fada Azuciyar ta sai fadi take kada Allah ya sa kaci din cikina Ko naka.

 Shiko dîner table yazauna ya bude food flask din tare da zubo abinci a plate.

 Kallon abinci yake yana kwabe fuska yanata Jero adu'oi harda rufe fuskar sa dan ze zuba abinci a bakin sa.

 Duk abun da yake ciki Rahama na kallon sa ta gefen idanu.

 Uhmm. Ta ce daman ina iya zuwa gaban sa dauke abincina zanyi ya je restaurant din dayasaba sai kace yaga kashi.

 

Bismillah yakaranto tare da saka loma daya a bakin sa wani dadi da gardi ne yaziryarci harshen sa'' ware Idanun ya yi kodai be gani sossai ne.

 Ganin eh lallai Abinci nata ne.

 Ciki yake yana yana lumshe Idanun sa saida yacinye abincin nan tas.

 Ya ajiye kwanun badan ya ishe shi ba saidan beson yaci abinci ya koshi sossai hakan yana Haifar masa da wani laluran...

Faruk ya ce mu je to tun da ka gama wai da Madam za ka je ne yana kallon Rahma.

 Samad ya ce eh yana iya ta ce wai yar uwar ta tana Asibiti cen zamuje ma gaisa acen ya wadatar kallon Rahama yake ya ce tashi mu je Ko.

 Tashi ta yi tadau jakar ta tana gaba yana bayan ta kallon ta yake yanda hijab dinta ya sauka har kasa.

Babu ba ta lokaci duk suka shiga motar.

'' Samad bayan motar yashiga itama Rahama nan tazauna..

Faruk ke drever din su yana tambayar inda Asibitin yake.

SAMAD ya yi masa kwatance da Asibitin da aka taba kwantar da shi ne.

 *********************

KA SANCEWA lasa'ar ta gabato sheik na kokarin fita dan yakoma ba da Sallah unguwar tasu.

 Limamin Asibitin yasha gaban sa cike da girmamawa da magiya ya ce Sheik Imam dan Allah ka taimaka kabamu Sallah hade da dan tafsir.

 Sheik kallon dattijon yake ya ce Baba Nike ba da Sallah a babban masallaci.

 Dattijon ya ce dan Allah kasa wani naka ya wakilceka nayau kadai zakai mana pls.

 Sheik ya ce to bara mugani kiran Abubakar yashiga yi wanda Alwala yagama ya ce kaje cen kabasu Sallah la'asar ni anan zanyi.

 Abubakar cike da girmamawa yatafi dan cika umarnin mahaifin nasa..

 

 Nan da nan unguwar yadauka Sheik Abdurrazak kabeer hizqeel makarfi ne zebada Sallah a wannan Masallaci dandazon mutane Daga nesa da na kusa kankace me Asibitin yacika da dunbun jama'a.

 Wasu unguwanni Daga nesa suka ringa tahowa Daga an yi shela maganar ta bazu.

 Cike da mamaki likitoci Asibitin suke kallon cikar da akayi danyin Sallah a massalacin..

 Dan za su iya rantsewa massalacin be taba cika ba''

ba a taba wuce sahu biyu ba bayan liman sai gashi Saboda sheik duk Asibitin babu hanyar wuce wa...

Tun daga nesa Samad yake hango cinkoson mutane a kofar massalacin.

 Daga nesa suka faka motar dan babu hanya..

 Kafun su fito saida suka yi Alwala hakan ya sa basu yi wata wata ba sukabi Sahu...

 Rahama dake zaune cikin mota Jin muryan mahaifin ta ya sa ta ware Idanun ta tare da sauke nikaf din dake kanta.

 Abba ta furta a fili waishi ke ba da Sallah uhmm Allah ya saka wa Abba da Alkhairi.

 Bayan An idar da sallah saida yadauki minti talatin yana waazi

' kuma waazi yake a kan Maza masu tauye hakkin matar su' da suji tsoron Allah ya yi Jan kunne ne a kan Abun da akaiwa Salma.

 SAMAD JIyake kamar dan shi sheik yake wa'azin nan.

Jiki babu kwari ya tashi bayan anfara watsewa ana ta tafiya

 Masu daukar wa'azi a wayoyin su sun dauka..

 Shiga suka yi a motar shida Shi da abokan sa kai tsaye Asibitin suka nufa...

 Suna parking motar a harabar Asibitin ya yi daidai da fitowar sheik Daga massalacin..

 Kallon su yake dan yanason yaga ne kamar mijin Rahama ne.

 Ganin Rahama ta fito Daga motar ta nufo inda yake ya sashi sakin Murmushi yana musu sannu da zuwa..

 SAMAD CIKE DA FARIN CIKI YADUKA YA GAISHE DA SHEIK.

 Suma Faruk gaishe shi suka yi nuna musu hanyar dakin da Salma suke yayi.

 Cike da fara'ar su suka shiga..

 Rahama ganin anty aguje taje ta rungume ta gam a jikin ta tana kukan farin ciki.

 Mama cikin farin ciki ta ce yata baki ganni bane.

 Tashi Daga jikin Anty ta yi taje gaban Mama tana gaishe ta cike da ladabi.

 Su Abdul Samad kallon ta suke yanda duk tarude ganin iyayen ta..

 Karasowa dakin suka yi dukan su harda sheik.

 Sheik ya nuna masu waje da su zauna.

 Cike da ladabi suka gaida Mama da Anty

 Mama sai kallon Abdul Samad take tana son tuno inda ta taba ganin fuskar shi..

Zumbur ta Mike tsaye kallon ta kowa yake a dakin.

Baki na rawa ta ce wannan na taba ganin hoton sa a dakin Baba Salihu.

 😳😳

Sheik ya ce Baba Salihu kuma '' ta ce kwarai kuwa lokacin da za ai gyaran gidan namu.

 Mukaje ajiye wasu kayayyakin mu anan naga hoton me kama da wannan.

SAMAD AZABURE YAMIKE TSAYE... YA CE WHAT...

 

4️2️

Ya ce What mai kama dani a hoto a dakin Baba Salihu waye Baba Salihu ya tambaya cikin kidima...

 Mama ta ce yana iya zama kamanni ne amma tabbas naga hoton nan.

Kuna yanayi sossai.

 Sheik ya ce hoton yana dakin nasa ne.

 Mama ta ce kwarai kuwa.

 Abdul Samad cikin kaduwa ya ce zanso naga hoton nan mama.

 Cikin kasa da murya ta ce babu matsala.

 Rahama zuwa ta yi gaban Salma dake kallon su cikin Mamakin ganin Yarima Samad din ganin shi take kamar cikin larabawa ya fito yanda fatar jikin sa ke fresh '

Bakin sa take kallon yanda leben sa yake jajir. '.

 Rahama ta dawo da ita Daga tunanin ta tahanyar shafa fuskar ta ta ce kanwaty ya jikin naki.

Salma ta ce na ji sauki amma Idanun ta nakan Samad.

 Rahama Kallon Anty take ta ce waimeke damun Salma ne.

 Ganin su Samad na wajen ya sa Abba fadin inaga Maleria ce da taifot sai dai result ya fito zamu ji..

 Sannu Rahama ke jero mata ta ce wai ina mijin Salma ne.

 Mama ta yi Jim ta ce ya je yadawo.

 Cike da tausayawa Rahama ke kallon yanda Salma ta rame sossai..

 Samad ya ce Abba daman munzo da niyar zuwa wajen naka sai mukaji kuna Asibiti..

 Cikin Jin Dadi sheik ya ce au to nagane nanma ya isa ya muka iya da kaddarar cuta sai hakuri..

 Samad ahannun ya sa cikin Aljihun sa yazaro bandir din dubu dari ya ajiye gaban Anty ya ce gashi babu yawa ayi hakuri..

Sheik ya ce an yi haka kuwa ɗana yana Murmushi ya ce amma kudin sunyi yawa ka rage su..

 Fauk ya ce kar ka damu ya sheik imam '' kudin Asibiti har ku gama zama yadauki nauyin sa.

 Adu'arku yake nema dan shima yazama dan Ku.

 Sossai Samad yaji Dadin bayanin Faruk.

 Tashi suka yi da niyar za su fita.

 Samad ya kalli Mama ya ce uwata zamu tafi Ko zan iya zuwa gobe gidan naku dan inga hoton.

 Sheik ya ce kar ka damu zanturo Abdul j'alil yakawo maka.

 Samad kallon Rahama yake yaga Alamun ba son tafiya take ba.

 Sheik na Lure da kallon Rahama da yake yi.

Haka ya sa ya yi gyaran murya ya ce Rahama tashi kuje Ko tun da an yi ziyar hankali yakwanta.

Samad ya karbi zancen da A'a ka barta akwai inda zamu je inmun dawo zamu biyo mu dauke ta yakarashe zancen tare da fita dakin.

 Abokan sa suka take masa baya.

 Sheik godiya yashiga yi musu bisa kokarin sa da kyautatawan su.

 Sheik dawowa cikin dakin ya yi yazauna yana kallon Rahama Sam bega Rama tattare da ita ba.

Yaga tadanyi haske.

 Cikin damuwa yake ba Rahama labarin abun da ya samun Salma.

 Salati ta fara tana kallon Salma ta ce Amma Abba mijin ta beda imani yanzu yana ina haka.

 Sheik ya ce inazan sani.

Sai dai Allah yakyauta ya tsare gaba.

 Salma cikin kuka ta ce ni dai ba zan koma gidan shi dukana yake yi tare da nuna musu shaidan dukan.

Ganin jikin ta da zanen bulala.

 Mama ta ce subuhannalah harda duka ta ce kwarai kuwa.

Sheik ya ce ai ba zan raba auren ba koda zaki koma ba yanzu ba Salma sai kinyi watanni agida InshAllah.

 Salma ta ji dadin furucin Sheik har ta murmusa Rahama ta ce Abba Ko zata dawo gidana da zama ne.

 Dasauri anty ta katseta ta hanyar fadin A''a bazata je ba a kan me zata zaune miki gidan miji..

 Ran Mama da Salma ya yi mugun baci hakanan su ka shanye abun da ta yi musu..

Sheik ya ce Sa'adatu ai gaskiya kika fada da auren wani ba za ki je gidan wasu ba ki zaune musu ba sai dai ziyara.

 Rahama ta yi shiru tana sauraren su.

 Sheik tashi ya yi ya ce to zanje sai bayan isha'i zandawo Daga haka yabar dakin.

 Sheik nafita Mama ta rinƙa jifan Anty da kallon banza.

 Ita Ko anty hakan bedamun ta inhar a kan gaskiyar ta ne.

*************************

🇧🇯 Kwatano.

Karima ce tasamu wani sirrintance waje tare da zama ta kunna wayar ta.

Nombar Samad ta danna wa kira.

Tayi ring kamar baza a Daga ba.

Jin an Daga ya sa ta sakin ajiyar zuciya.

 Cikin kasa da muryan ta ta ce ya shugaba na Yarimar Gheuzo baiwar ka Karima ce..

 Daga can ɓangaren ya ce Karima sai yanzu kika samu damar kirana ta ce kayimun Afuwa tare da risinawa kamar tana gaban sa.

 Abdul Samad ya ce ina son ki samun idanu sossai a kan Marwan.

 Da shige da fitan sa.

 Idan drever na yana nan ki masa sakon nan shi ne zeringa bin sahun Marwan har fulani ɗa Abba Marwan.

 Ina fatan kin fahimta ta ce naam ya shugaba.

 Ya ce ke cikin gida ne zaki min aiki taimako ki shi ne zekai ni da nasarar gano baiwar nan data gudu Saratu.

Cike da gamsuwa Karima ta ce InshAllah zanyi yanda kace.

 Har ze katse sai jiya yi ta ce ya shugaba na.

Ya matar taka take.

 Shiru ya yi na wani lokaci kafun ya ce tana lafiya Karima..

 Karima ta ce Ranka ya dade kar ka zo garin nan da ita harsai Allah ya azurtaku da haihuwa.

 Cike da Mamaki yake nazarin kalaman ta ya ce Karima banfahimce ki ba

Ki dan ban haske.

 Har ta yi tunanin bazata gaya masa ba sai ta tuna irin kaunar da take masa.

 Cikin raunin murya ta ba shi labarin abun da ya faru a yan kwanakin nan..

 Ya Girgiza matuka da Jin zancen nata.

 Cikin dauriya ya ce kada ki damu Karima ni wannan be dameni ba.

 Matata kuma zanzo kwanan nan wajen wani shari'a ba zan zo da ita ba.

 Sossai Karima ta ji dadin bayanan sa.

Daga haka suka yi Sallama.

************ ****** *******

🇬🇦 Gabon

Hajiya Assana ce zaune kan sallaya bayan ta idar da Sallah Daga hannayen ta sama ta yi tana rokon Allah ya mallaka mata zuciyar baba Salihu kuka take iya karfin ta..

Diyar ta mai suna hauwa ce ta shigo cike da mamaki take kallon uwar ta tana kuka ta durkushe gaban ta ta ce Mama haryanzu baki daina kukan mutuwar baba bane.

Adua'a yake bukata.

Girgiza kai ta yi ta ce hauwa Ba wannan kukan nake ba yata.

 Cikin tsananin damuwa hauwa ta tallabo fuskar uwar ta tana goge mata hawaye jiki asanyaye ta ce mama Ko baki yarda dani bane.

 Hajiya hassana dago jajayen Idanun ta ta yi tana kallon yar ta ta ce niko nayarda dake hauwa ta'''...

 Hauwa ta numfasa ta ce to dan Allah gayamin damuwar ki inbada maganin ta intayaki da adua

 Zaunar da hauwa ta yi ta ce akwai wani bawan Allah mai suna Alh Salihu turaki wlh nakamu da son sa banajin zan iya rayuwa babu shi.

 Hauwa ta ce Alhaji Salihu turaki daya dai ɗana sani dan gidan Sarauta ne fa tafada cike da zare idanu.

 Mamar ta ta ce ya'akai kika san haka daughter tare da share hawayen ta.

 Numfashi hauwa ta fesar ta ce mama nasan shi kiyarda wani dattijon yana gidan sa.

 Agun jikokin sa nake samun labarin sa ance Sarki ne a garin kwatano.

 Amma wasu dalilai ya sa ya sauka kan karagan mulki.

 Hajiya Hassana tashi ta yi Daga zaune tana ciza yatsar ta ta ce yanzu nagane dalilin dayasa yaki Amsar ta yi na.

. Hauwa ta ce mene ne dalilin mama ''

ta tsareta da manyan idanuwan ta.

 Hajiya hassana ta ce inhar Salihu turaki ne uhmmmmmmmm

 

4️3️

Hajiya Hassana ta ce inhar Salihu Turaki ne uhmmmmm nasan sunan sa tun da dadewa '' Saboda mummunar labarin daya karade a duniya a kan sa.

 Hauwa ta zare Idanun ta ta ce mummunar labari kuma wannan Salihin mutumin.

 Hassana taku ta yi taje wajen Windows dakin nata maida kallon ta ta yi a wajen ta ce ke ba zan iya gayamiki wannan labarin ba harsai na binciko gaskiyar Al'amarin.

 Hauwa kallon bayan uwar take fuskar ta dauke da damuwa ta ce taya zaki gano abun da ke boye bayan kina nan shikuma garin su kwatano ne.

 Dariya mai sauti hassana ta yi tana buga kafafun ta kasa tare da waigowa tadawo kusa da yar ido cikin ido take kallon ta ta ce kwatanon zanje InshAllah indai bashida hannun a kan abun da na ji to wallahi zan sama masa mafita.

 Hauwa ta ce la'ila rike da baki ta ce mama ki rufa mana asiri '' ki hakura da Salihun nan banjin dadin damuwa da wanda be damu dake ba da kike yi akarshe yazo be aure ki ba.

 Murmushi mama ta yi ta ce baby na zanyi ne Dan Allah dakuma kaunar da nake masa '' kimun adua dan Allah karki fitar da sirrina Ko kanin ki kada ki gayamasa ga inda zanje.

 Kinji Ko !!

Gyada kai ta yi Alamun gamsuwa Idanun ta cike da kwalla ta rungumi uwar ta cikin sanyin murya ta ce Mama Allah ya sa kada kiyi zuwan banza nasan ke uwa tagari ce dan Allah ki kara rike mana martabarki da mutunci ki ina Alfahari dake uwata.

 Kuka ya kwace mata tana shafa kan hauwa ta ce nagode daugheter tare da manna mata kiss 💋 a goshin ta..

*************************

Baba Salihu zaune a dakin kamar yanda ya saba ya kunna wannan cctv camera yana kallon abun da akai uhmm Samad yafada a zuciyar sa nasan ka bakada sauki fa tunanin mafita yake y' hakan ya sa ya dauko babbar wayar dake gefen nasa ya danna kira gun mai bashi labarin Samad..

 Cikin damuwa ya ce dafatan kowa lfy.

 Ya ba shi amsa da lafiya lau ne.

 Dan numfasawa baba salihu ya yi yana taune lip din shi.

 Ya ce nalura kamar Rahama ba ta Jin dadin zama da Samad '' Daga can ɓangaren ya ce shima yaso ya fahimci haka amma zekara sa idanu yaga ne gaskiyar Al'amarin.

 Baba Salihu cikin damuwa ya ce bana son mahaifina yabar duniya banyi tozali da shi ba..

 Idanun sa cike da kwalla.

 Kasa jure wayar da suke yi ya yi tare da katse wayar y azauna yana kuka iya karfin sa.

 Tuno abun da yasuka wuce shekara da shekaru yake cikin kunan rai ya ce waze wanke ni a idon duniya..

 Ya zanyi mahaifina yaga haske na..

 Daga HANNAYEN SA SAMA ya yi cikin kuka yana rokon sassauci a rayuwar sa....

Ita Ko hajiya Hassana ta shirya tsaf har airpor yayan ta suka rako ta zata tafi kwatano.

Suna Airport har jirgin nasu ya tashi sararin samaniya.

Hauwa da kanin ta jiki asanyaye suka koma gida

.

🇳🇬 KANO

Sai bayan isha'i suka koma asibitin dan dauko Rahama daidai da dawowar Abubakar da Abdul jalil 'cikin Jin dadin ganin Samad suka yi musabaha dashi'

Abubakar ya ce mijin Rahama Ko ?

Murmushi ya yi ya ce eh nine.

 Ah yanzu kuka zone mu shiga Daga ciki mana.

 Aminu ya ce Ranka ya dade ai munzo daukan Rahama mu kazo yi yafada tare da yin gaba.

 Abubakar ya ce bismillah mu je cike da dokin son ganin Rahama yashiga dakin.

 Yana shiga ya iske ta tana karatun Alkur'an.

 Kallon ta yake yanda take karatu a natse ya ce inkinkai Aya ki dakatar ga mijin ki yashigo...

 Samad da suke bakin kofar shida a bokan sa kallon ta suke hartakai Aya..

 Rahama ta ce la la Yaya ABU ashe dai zamu hadu daman ina takaicin tafiya ban ganka ba.

 Abubakar cikin Jin dadi yakama hannun ta cikin nashi yana matsama tare da dafata suna Face din juna.

SAMAD RANKA IN ya yi DUBU YABACI ya saN YAYAN TANE UWA DAYA UBA DAYA..

 Faruk ya lura ransa yabaci murya a tausashe ya ce yaya ABU sauri muke yi dan Allah..

 Abubakar ya ce babu matsala.

 KE RAHAMA TASHI KU TAFI KINJI KO..

 Kallon Anty take dake barcin Gajiya gashi Mama taje gida ta dawo..

 Rike hannun Salma ta yi ta ce my kanwaty mun tafi Allah yakara lafiya.

 Nikaf dinta ta sanya tare da nufar hanyar fita.

 Shiko Samad tuni suka bar dakin suna cikin Mota suna jiran ta.

 Sai cika yake yana batsewa wannan yarinyar yar rainin hankali ce.

 A rainin wayau ne tashanya mu 'mu yaran Tane tana cen tana murza hannun namiji.

 Kallon takun ta tana tahowa ya sa kallon sa yakoma akanta.

 Karasowa ta yi tare da bude murfin motar..

 Ta shiga ta inda yake zaune.

 Matsawa ya yi Daga gefe yana bubbuga kafa Alamun zamu je gida zaki sani.

 Faruk drever ɗinsu ya yi har gidan nasu.

************************

England.

Adamsy ne yake Chattin da Asiya ta whsap.

 Cikin tsananin damuwa yayiwa Asiya voice ya ce wallahi Asiya har gobe ina son Rahama da Yarima ze sakar min ita danafi kowa farin ciki wallahi nakasa sukuni.

 Asiya cike da nutsuwa ta ba shi Amsa ta ce babu abun da ya fi karfin adua..

 Ka yaki shaidan acikin zuciyar ka Rahama yanzu Matar wani ce kasa m'a ranka hakuri.

 Zan ba ka adu'oi da za su taimakeka...

 

 Adu'oi dayawa ta yi masa audio tare da tura masa.

 Adamsy dake kwance saman gadon sa mai laushi ya ce Asiya na ji bayananki InshAllah zan aiki dashi.

 Asiya ta ce to yaushe za ka dawo ne munyi miss dinka.

 Murmushi ya yi ya ce ai garin babu dadi babu Rahama daman Saboda ita nashiga koyarwa a wannan makarantar taku

 Uhmm Asiya ta ce kenan mu ba mutane bane.

 Yi hakuri Asiya ai kodan son da kike ma Rahama zanzo

Wai ina bakar munafukar kanwar Rahma take.

 Asiya ta ce indakwai sunan da ya fi wannan kana iya kiranta da shi Algunguma aitayi aure a ranar na tsani me bakar zuciya ace yayar ki uwa daya uba daya.

 Uhmm in'nice Rahma nida ita har Abada wlh saide ita Rahama zuciyar yafiya gareta yanzu za a mata abu anjima zata ce ta yafe.

 Adamsy ya ce dabi'un ta da hankalin ta suna Daga cikin abun da yajawo hankalina akanta Ko banza nasan yaya na za su samu tarbiyya.

 Asiya ta ce haka ne wlh tamasu raino Daga uba nagari uwar dakin ta mutumiyar Arziki da tawakali.

Ahakadai suka cigaba da hira ita da Adamsy sun shagala sossai..

**************************

Yarima Samad a gajiye suka karaso falon nasu.

Faruk ya fada kan 3tsr ya ce Wash munsha yawo kuma babu nasara.

 Aminu ya ce wlh babu nasara fa amma wataran zamuyi nasara.

 Yarima Samad kallon su yake yana kwabe baki ya ce kudai an yi ragwaye wlh jibi yanda kuka baje kan kujera yakarashe zancen yana hawa kan matakalan step.

 Tuni Rahama ta shige dakin nasa.

Sauri sauri take ta cire kayan jikin ta.

 Turo kofar da akayi ne ya sa cikin hanzari tamaida hijabin ta a jikin ta.

 Zama ta yi akasa tana latsa wayar ta.

 Da sallama bakin sa yakaraso falon kallon ta yake yanda ta na de kafafun cikin hijab.

 Wuce ta ya yi ya fara rage kayan jikin sa.

 Haka kawai yaji kamar tana kallon sa.

Ya waiga yaga hankalin ta nakan waya.

 Uhmm ya ce wannan Yarinyar zan gyara mata zama mu tasa Yawon da ba mu shirya ba.

 Gyaran murya ya yi wanda yajawo hankalin ta a kan sa.

 Ke taso ki je ki hadamun ruwan wanka gaki kin fito babban gida.

Amma Sam bakida wayau.

 Kallon shi take shima itake yake kallo yanajin bugawar zuciyar sa yana tsananta duk sanda ya yi tozali da ita.

Ko karya nayi miki ne ?

Banda son a taba ki babu abun da ke burgeki.

 Hararan ta yake tana tsaki.

 Tashi ta yi Daga zaune tana ciza labbansa ta suka bushe.

Azuciyar ta sai fadi take uhmm shi kullum laifi ake masa babu rana ta banza da ba zai ce ga wani abu ba.

 Kai tsaye toilette din ta fada tana kokarin hada masa ruwan wanka.

Taji taku a bayan ta.

Bata kawo komai aranta ba taci gaba da hada ruwan.

 Dagowar da za ta yi taga abu gabanta tsaye cikin bakaken kaya.

 Idanun sa kwala kwala kamar kwai.

 Soma ja da baya ta yi yana kusanto ta.

 Ta kai karshen....

 

4️4️

Ta kai karshen bangon dakin tafara adu'oi tana tofa masa tana adu'oi cikin aro jarumta ta ce me kake nema dani ne ?

 Nufo shi ta yi ta cire tsoro nan da nan ya fara ja da baya batt ya ba ce Daga bandakin.

 Ganin yaba ce be sa ta daina aduar da ke bakin ta ba ta nayi cikin Daga murya.

 Yarima Samad mamaki ne yacika shi Jin muryan ta ita kadai a bandakin.

 Daga shi sai dan gajeran wando jikin sa cikin hanzarin sa ya shiga bandakin ganin gabadaya hankalin ta baya kansa adu'oi take ta zubawa tana magana ta ce yakai mummunar halittar nan dawo nan ban gama da kai ba yaka gudu.

 Sai gashi ya bayyana gaban yanata susa jikin sa na masa kaikayi.

 Murya cen sama take jiyo wani murya mai amo hakan ya sa ta Daga kanta sama.

 Keee Rahama wlh inkika cutar da dan aikena namiki Alkawarin nadama a rayuwar ki.

 Samad dake tsaye yana kallon ikon Allah rike take da kugun ta Idanun ta sun kada sunyi jajir 'bejin komai sai tashin muryan ta.

 Jin muryan ta ya yi tana Wani buga uban kara hade da dariya ta ce bakuda abun da zaku yi maganina Ko mu gwada yanzu ne suratul bakara tafara karantowa da karfin ta wannan Aljanin dake gaban barin wajen yayi' '' Shiko me magana Daga Sama yana ihu fadi yake Rahama ki dakata Ko kin hanani wucewa hanyar dazanbi nawuce wuta nake gani.

 Rahama bako ta saurare shi ba cigaba da karatun take tana kara sautin muryan nata.

 Wani irin kara ya yi Daga cen Sama ya ce Inkina yiwa darajar Manzon Allah SAW ki bar karatun nan wlh natuba najanye kalamai na.

 Tsai gaita karatun ta yi cikin fushi ta ce gayamin me nayi muku kuke neman takura mun.

 Daga can ɓangaren ya ce wallahi turomu akai.

 Rahama cikin zafin rai da batasan tanadashi ba ta ce za ka gayamin gaskiya Ko sai nayi kasa kasa da kai.

 Wani huci Sama Sama yake yi yana nishi ya ce anturomu ne Daga baban Maryam.

 Yana fadin haka yabar wajen cikin tsananin wahala.

 Nanata kalamin nasa take yi ta ce baban Maryam kuma.

 TA MANCE A BANDA KI TAKE.

 JIN MURYAN ABDUL SAMAD YANA FADIN KE LFY KIKE..tare da tsareta da idanu cikin damuwa.

 Ajiyar zuciya tafara suke wa tana kallon sa.

 Kamo hannun ta ya yi sukaje daki tare da zaunar da ita bakin gado ya ce Rahama wai meke damun ki gayamin.

 Kallon shi take ta ce anya gidan nan bana Aljanu bane.

 Kallon ta yake ya ce kamar ya fa gidan Aljanu.

 Uhmm abubuwa ban tsoro nagani harda cemin wai baban Maryam yaturo su.

 Abdul Samad cikin tsananin tashin hankali yashiga Jin zancen nata..

 Ya Salam ya furta cikin Jin tausayin ta yakama hannayen ta ya ce Rahama ba gidan Aljanu bane.

 Shaidanun mutane ne da shaidanun Aljanu sune suke takura mana.

 Tunani yake cikin zuciyar shi ya ce karfa Yarinyar mutane tasamu matsala Saboda ni.

 A'a Rahama ba zan bari acutar mun dake ba.

 Maganar zuci yake yana kallon yanda take ta ajiyar zuciya.

 Besan sanda ya jawo ta ya rungume ba.

 Itako kasa fita Daga jikin nasa ta yi dan wani dumi ta ji yana ratsata kamshin jikin sa take shaka hade da lumshe Idanun ta.

 Tana tunanin to wannan abun shi mene ne shi taya akai suka shigo rayuwar ta, tunani take tasan duk a ɗangin nata babu baban Maryam.

 Kara shigewa jikin sa ta yi wanda hakan ya sakar masa da kasala.

Cikin dauriya ya ce bara inje in yi wankar Ko ?

 Sam tama mance shi ta runguma harda make kafada za ta yi kukan shagwaba.

Kallon bakin nata yake nan take Yaji wani yarrr.

A jikin sa.

Jin ya hade bakin sa nata ya fara tsotso kamar ya samun lollipop firgit ta dawo hayyacin ta tana kokarin kwacewa Yarima Samad yaki ba ta koda kofar kwacewa '' kuka tafara tana tana kokarin kwacewa.

 Hannun sa yana kan na shanun ta kokarin cire mata brezia yake yaji karar buga kofa da karfi.

 Jin muryan Faruk ya yi yana fadin zoka bude mana kofa.

Ransa ya yi matukar baci yaso ya samu sa'ar ta adaren nan duk yaga ta tsiya.

''

 Sakin Rahama ya yi cikin Daga murya ya ce ina zuwa.

 Jallabiyar sa yazura cikin hanzari.

Itako Rahama toilet ta koma dan yin wanka dan Allah ne ya cece ta hannun sa

 inhar ya yi mata mugun kamu tofa sai dai Allah shike kwatar ta.

 Tuno abun da ya faru da Salma ta yi ta dalilin jima'i hakan ya sa hankalin ta ya yi mugun tashi.

 Ta ce ina wallahi nafi Salma son jikina banson abun da ze taba lafiya ta.

 Kuka take ta ce ya zanyi Rahama banson wannan jima'in harda shesheka kuka haka kawai ya je ya sabatamun rayuwa ta.

 Tuno kawar su da ta yi aure ta yi irin wahalar datasha a hannun mijin nata...

 Uhmm ni dai Allah ya sa yakyaleni inhuta tana turo bakin ta gaba.

''

Shiko Yarima Samad bude kofar ya yi yana kallon Faruk da yanayin sa ya sauya.

 Cikin damuwa ya ce Yarima Samad muryan Rahama mukai ta ji tana surutai hankalin mu ya tashi sossai ''

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce bafa wani abu bane ta tsorata ne a bandakin kar ka damu.

 Ka san mata basuda hakuri insukaga abun tsoro.

 Aminu ne yakaraso wajen ya ce amma duk da haka akwai Ayar tambaya anan wajen kamata ya yi ka tambayeta abun da tagani asan mafita fa.

Yakarashe zancen yana yarfe hannayen sa.

 Faruk ya ce wannan gaskiya ne.

 Yarima Samad kallon su yake ya ce to yanzu ya kuke so nayi da ita ka san ba gayamin komi za ta yi ba.

 Faruk ya ce ai wannan ma zancen banza kake yi yaza ai kaida matar ka kace bazata saurareka ba.

 Su fa mata ba a musu sarauta agida dan sune keda linzamin juyawa Ko wani da namiji dan haka muna rokon ka.

 Kaje kabincika da kyau yanda Yarinyar nan ke kara gsk ruwa baya tsami banza.

 SAMAD shiru ya yi kamar yana tunanin wani abu ya ce to zan duba mugani yana kokarin komawa dakin..

Yaji muryan ta tana fadin dan matsa zan fita.

 ba ta hanya ya yi hakan ya sa ta yi tozali dasu Faruk dasuke jero mata sannu.

 Kallon su take cikin siririyar muryan ta wanda ke kashe garkuwan jikin Samad ta ce wani abu ya faru ne tana kokarin sauka Daga kan matakalan step din.

Aminu ya ce ihun ki mukaji shi ya sa muka zo.

 Cak ta tsaya Daga kan matakalan step din.

Taso waigowa saita fasa.

Ta ce nima ban san hakan tafaru ba tana mai cigaba da tafiyar ta.

 Yarima Samad da su Faruk kallon juna suka yi.

***********************

🇧🇯 Kwatano

Bokan baban Maryam ne duk Zufa ya keto masa ta Ko ina sakamakon Aljanun da ya tura sun dawo suka yi masa bulala hamsin shima Yaji kadan Daga cikin azabar da suka sha.

 Da ƙyar yasha a hannun su

 

Daukar wayar sa ya yi yakira baban Maryam ciki fada ya ce ni wannan aikin da kaban bankara tura Aljanuna ku hakura kawai tazo garin zefi yakin da ya kamata kayi kenan.

 

 Daga can ɓangaren ya ce haba boka hakuri zakai amma na maka Alkawari zamu sa tazo garin kwatano dan cika Burin mu baza a wuce sati ba InshAllah.

 Boka ya ce kar ka kara fadin kalmarka ta karshe ya daka masa tsawa tare da katse wayar.....

Dan Yaji haushin InshAllah daya furta.

 Baban maryam zaune a dakin sa Maryam tana zaune kusa da shi duk abun da ake fade a gaban ta ne.

 Kuka ta saki ta ce yanzu baba wannan matar ta yi nasara kenan.

 A'a batayi nasara ba cewar baban Maryam..

 Maman Maryam ta shigo falon hannun ta dauke da flask din abinci.

 Kallon Maryam da baban ta ta yi ta ce ya ake cikine naga kunyi jugum..

 Neman wuri ta yi tazauna suna face din juna da maryam..

 Baban Maryam ya ce wannan karan aikin naki ne tun da kin isa da Yarima Samad kibashi umarni yazo da matar shi inhar zezo shari'a da ze kawo shi...... Yazo da ita kawai shi ne magana.

Maman Maryam ta ce zankirashi yanzu ɗana shiga daki na.

************************

Hajiya Hassana cikin unguwar zongo Cotonou ta sauka hôtel royal wani kayataccen hôtel royal nan ta sauka.

 A garin batasan kowa ba tana ta tunanin ta inda zata fara tambayar Masarautar Gheuzo.

 Ta fito wajen hôtel din tana sanye cikin habaya bleu ba ƙaramin kyau ta yi da shigar ba..

 Kallon titunan take masu mashina dake ta wuce wa..

 Suna sanye da uniforme din su.

 Gefen ta ta hango wani babban restaurant ana gashin kaji awajen.

Ka santuwa ba ta ganin kaza tabari.

 ya sa ta nufi wajen cikin nutsuwa take tafiya Idanun dauke de glass..

Daidai wajen mai gashin naman ta tsaya.

 Barka dazuwa hajiya na nawa za a sako miki cewar me saida naman.

Yawwa barkadai ta ba shi amsa cikin fara'ar ta har hakoran makkah suka bayyana.

 Kallon kajin take ta ce aban guda biyu.

 

 OK to ya shiga yin abun da tasashi.

.

 Wani kyakywan matashi tagani ya paka motar sa.

Awajen tare da nufar wani babban super market dake wajen.

 Me naman rike da baki ya ce Wata Sabon gani.

 Yariman Gheuzo ne a unguwar tamu.

 Hassana cikin mamaki ta ce dan Allah ka san shi ne ?

 Wani Yariman ne ta jefo m'asa tambaya.

 Mai saida nama ya ce aikuwa nasan shi dan Sarki jikan Sarki ne.

 Ahmad salihu Turaki.

 Zare idanu ta yi cikin kidima ta ce me kace.......

 

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

.4️5️

Ta ce me kace bawan Allah sake da baki '' cikin sakin fuska ya ce amma hajiya ke bakuwa ce Ko ?

 Gyada masa kai ta yi alamun haka ne.

 Mai saida nama yana cigaba da yanka naman ya ce uhmm ai hajiya wannan a yanzu jikin Sarki ne.

 Hajiya Hassana ta ce shin zan iya ganin Ahmad din.

 Kallon ta yake yana kokarin zuba mata naman cikin teakaway ya ce hajiya beda girman kai amma inbukatar Kudi Ko taimako yayan sa zaki nema dan wannan ƙaramin zaki ne.

 Hajiya Hassana ta Murmusa ta ce kaiko inbanda abunka ai ƙaramin zakin sai ya zama babba.

 Mika mata naman ya yi ta amsa.

 Ganin Ahmad ya fito mutane sun biyo shi harda yan mata.

 Sai yauki suke sunga handsome gay jinin sarauta.

 ka ga ajiye mun naman nan ina zuwa tana Mika masa ta nufo wajen motar tashi.

 Kwankwas glass din motar ta yi dan yana kokarin tada motar.

 

Da mamaki yake kallon ta tare da sauke glass motar kallon take tare da hada fuska ya ce hajiya lafiya kuwa yana mata nuni da hannu.

 Murmushi ta yi tare da gyara Tsayuwar ta ta ce.

 Ta ce ina son ka kai ni masarautar gheuzo dan girman Allah Saboda...

Dakatar da ita ya yi da hannu ya ce Saboda kiyi maula Ko me tsaki ya yi tare da rufe glashin motar sa yabar wajen tare da tada mata kura.

 Waɗanda suka zo rakiyan Nasa kallon ta suke suka ce Keko hajiya Daga ganinki baki cikin wahala meye na damun kanki a kan gidan sarauta in taimako kike nema ki masarautar ki nemi aha daki da jakadiya in Allah ya sa kinada rabo zata saurare ki.

 Hajiya Hassana uhmm ta ce taya za a rakani masarautar gheuzo dan ina bukatar taimako ta marairace fuska.

 Kallon ta yake ya ce duk mai mashin din da kika tara kikace masa masarautar gheuzo za a kaiki ba boyayyen waje ba ne...

 Godiya tayiwa mai naman tare da komawa hôtel din.

Reception ta nufa ta nuna tanason layi na kasar.

 Zabi suka ba ta akwai.

 Layin MTN da MOOV.

 Batayi wata wata ba ta ce ita MTN za a bata.

 Tare da ba dan aiken kudi takoma dakin nata tana jiran akawo layin.

 Wani tafasassen daki na gani gado da kujeru mai taushi da laushi ga TV plasma a jikin bangon.

 Banda sanyi Ac babu abun da ke kadawa a dakin.

 Zuwa ta yi ta dan kwanta tana tunanin mafita '' ciza labban ta ta yi ta ce uhmm wannan Salihu na dauko wa kaina babban Aiki mamakin kanta take da har ta damu da lamarin sa....

***********************

Ahmad Horn ya yi mai gadi ya bude masa gate.

 Yana shigowa parking space cikin hanzari ya nufi cikin gida kai tsaye sashin fulani ya nufa dan ya yi mata wani magana Ko me yatuna sai ya dawo baya Jin murya na tashi Daga cikin dakin kamar muryan Maman Maryam yake ji abun ya yi matukar daure masa kai.

 Kasa wuce wa ya yi yana kokarin bude dakin yaci karo da Abban Marwan dake kallon sa azabure.

 Dariyar yake yake masa cikin muryan sa dake nuna fargaba ya ce Au Ahmadu kaine yana mai sutsa keyar kansa.

 Ahmad ya ce eh ni ne Mama fulani na ciki kuwa.

Saurin katse shi ya yi ta hanyar fadin ai babu kowa ciki.

 Ahmad ya ce kamar muryan Maman Maryam na ji a dakin nan.

 Zare idanu baban Marwan ya yi ya ce Maman Maryam kuma to meze kawo ta gidan nan.

 Ahmad ya yi shiru kamar me nazari ya ce haka ne kuma ainasan da tazo dakin Mamy zan ganta.

 Barin wajen ya yi yana tafiya yana tunanin anya kuwa ga kunnen sa beji masa daidai ba...

 Da Sallama bakin sa yashigo sashin Mamy iske Khadija kwance kanta nakan kafafun Mamy rike da waya tana chattin da kawayen ta.

 

 Mamy kallon sa take yanda duk yanayin sa ya canza lokaci daya.

 Zama ya yi kusa da ita yana kallon yanda Mamy ke shafa kan Khadija ita Ko lumshe idanu take abun da Mamy ke mata ba ƙaramin dadi yake mata ba.

 Gyaran murya ya yi ya ce Mamy Maman Maryam tazo gidan nan ne ?

 Kallon shi take cikin mamaki take kallon sa ta ce aida tazo da ka ganta ahmadu ya akai ne tana mai tsareshi da idanu.

 Numfashi ya fesar ya ce kawai de nazo wucewa ta wajen dakin Mama fulani na ji murya kamar nata.

 Mama fulani kuma Mamy ta maimaita ta ce A'a badai Maman maryam ba to me ze kawo ta gidan nan ba ta shigo sashi na in banda abunka tafada cike da rudani.

 Ahmad ya ce uhmm yana iya zama banji daidai ba '' Mamy wai yaushe Samad zezo da Amarya tasa ne.

 Khadija ta yi caraf ta karbi zancen ta ce wlh Haba Mamy ace ya yi aure amma haryanzu ba zai dawo kasar shi ba yo me yake yi acen din tafada tana me turo baki gaba.

 Mamy ta ce to iyayena kun gama mun fada rike kunnen ta ta yi ta ce korafi be karbu ba.

 Naga dai duk kunada lambar wayar sa amma kun tasani agaba da magana inba tsoro ba kirashi mana kai Ahmad.

 Dariya ya yi saida kuncin sa ya lotsa ya ce Mamy kin san zan iya gayamai kawai dai amsar daze ba ni shi nake tsoro.

 Oho ni kuka raina kenan cewar Mamy tana kokarin tashi dan shiga kitchen.

Khadija ta ce Mamy wlh banson ki tashi inhar kina mun tausa...

 Mamy Murmushi ta yi ta ce uhmm yar auta ai tashi zaki yi mu shiga kitchen tare..

 Ahmad ya ce Mamy mu je in tayaki mana tun da ita ta kasa tashi gaba ya yi Mamy na dariya ita Ko sai zumbure zumbure take yi.

.

 Ahmad ne ke feran doya dan yau Mamy ta ce doya da miya zasuci da miyar kaza....

 Yanka doyan har doyan yankewa yake hade da bawon.

 Mamy dake juya naman ta a kan wuta ta juyo tana kallon yanda Ahmad ke ta dawaniya da doya.

 Rike da baki ta ce yau naga ikon Allah aka ake feran doya.

 Da Yarima ne habawa tuni anwuce wajen..

 Khadija da yanzu ta shigo kitchen din banda dariya babu abun da take '' dago kai ya yi suka hada Idanu.

 ta yi masa gwalo sossai ya ciza bakin sa ya ce dani kike ta ce eh din kai fa.

 Aiko bin ta ya yi aguje.

Mamy rike da baki ta ce yau naga shashanci kullum ba sa girma ne.

Shiko Ahmad har daki yaki bita tana kokarin shiga bandaki ya j'awo daman be wanke hannun sa ba aikuwa ya shafa mata kaikayi wani uban tsalle khadija ta doka aguje tafada bandaki tsutsa jikin ta tashiga yi..

Banda dariya babu abun da yake yi harda rike ciki yabar dakin.

 Abunka da farar mace nan da nan fatar ta ya yi jajir ruwa take ta sakar wa kanta tana ayyana aranta wlh saita rama...

************************

Drever Samad ne ke ta zarya a compound din gidan Karima yake jira.

Jin takun ta ya sa yakoma da baya baya suka koma parking space..

 Cikin kasa da murya ta ce Ali drever yaya kasamu wani labari a kan su Abban Marwan kuwa.

 

 Gaskiya bansamu ba yabata Amsa cikin yanayin damuwa amma sainake ganin kamar sun fi mu wayau fa.

 Karima ta ce kamar ya..

Numfasawa ya yi ya ce duk sanda zanbi bayan su wuri daya kullum suke zuwa su dawo.

 Cikin yanayin damuwa Karima ta ce to amma inda suke tsayawa ka san inane.

 Kada kai ya yi Alamun A'a.

 Karima ta ce nex time ka tafi dani akwai abun da zan duba.

 OK karki damu yabata amsa cikin yin kasa da murya ya ce ke ga Marwan cen zuwa maza kibi ta baya..

 Babu ba ta lokaci tabar wajen cikin hanzarin ta kallon ta yake Harta ba ce masa da gani.

 Marwan ne yakaraso wajen yana kallon sa cikin tuhuma ya ce Ali me kake yi anan kai kadai.

Murmushin dole ya yi ya ce au daman aikena Mamy ta yi shi ne natsaya duba motar da zan fita dashi.

Wani kallo Sama sama yake jifan Ali da shi yana yatsine fuska.

 Ya ce kai ai Mamy bakowa ba ce a gidan nan ba ce matar barawo..

 Firgit ya yajuyo yana nanata kalaman sa.

Bangane Matar barawo ba ya ba shi amsa.

 Marwan ya ce za ka gane ne inhar aka kore su Daga masarautar nan kujira kuga abun da zebiyo baya.

Wuce shi ya yi yana huci.

 Ali cikin tsananin damuwa ya ce za su bar Masarautar to su koma ina kenan wa'iyazubillah..

Dole ya san abun yi.

 Yafada tare da neman layin Samad be same shi ba...

🇬🇦 Gabon

Baba Salihu zaune shikadai a dakin sa yana tunanin yanda ze gana da yarima Samad.

 Wata zuciyar ta ce inkai haka aika tonawa kanka asiri kazauna dai matsayin da kake ciki shize fiye maka..

 Karar wayar sa yadawo da shi cikin hayyacin sa.

 Yana Daga wayar ya yi sallama.

 Daga can ɓangaren ya ce ya shugaba gaskiya abubuwa suna tabarbarewa fa.

 Cikin kaduwa ya ce banfahimta cikin tsoro da fargaba yake magana Daga can ɓangaren ya ce gaskiyar magana dole ne.

Yarima Samad yakoma kwatano da zama.

Yawon da yake yi dan neman ka ya isa haka.

Sannan akwai wani zanen hoton wata Yarinya daya zana suna yanayi da Rahama har yanzu ya kasa gane cewar wannan zanen ita ce matar da yake aure..

Idanun sa sun rufe ya shugaba NA.

 Baba Salihu cikin damuwa ya ce wai haryanzu Yarima na yana bibiyan wannan hoton mafarki nasan shi ne yahanashi aure.

 Daga can ɓangaren ya ce aibe hakura ba rannan matar shi muka bar asibiti muka shiga gari da wannan zanen hoton ka kadai ne beda shi shima dan Mamy tahana ne.

Baba salihu ya numfasa ya ce turomin hoton zanen ingani.

Sannan dole yakoma gida aikin sa na kano Ko babu shi komai ze tafi daidai InshAllah..

Daga haka suka yi Salama..

Baba Salihu cikin yanayin damuwa yake tuno Mamy ya ce baiwar Allah na cutar dake shekara biyar.

Kuka yake sossai tare da durkushe a kasa.

************************

🇳🇬

Kano.

Salma sossai ta ji sauki har aka basu Sallama.

Bayan sun dawo gida akai ta shigowa gaishe ta da jiki harda iyayen Al'amin.

Shiko Al'amin Ko gezau bezo ba.

Sheik zaune kusa da Salma ya ce mata sannu ta gyada m'asa kai.

Kallon ta yake ya ce MashaAllah yanzu tun da kin dawo gida banda yawo kin san aure na kanki..

 Wayar sa ce tafara ring yana dubawa yaga nombar Rahama ne.

 Cikin Jin dadi ta ce Abba ygida ya jikin Salma.

Amsa mata ya yi ta ji sauki.

Shiru ne ya ratsa tsakanin su.

 Sheik ya ce Rahama ta

Ta ce naam Abby.

Yana ga kinyi shiru gayamin mêke faruwa ne.

Salma Jin furucin Abba dadi ta ji tana tunanin Ko itama duka tasha gun mijin nata.

 

Jin sheik na salati ya ce Rahama garin yaya kika bari iska ke damun ki agidan auren ki.

Ke ce fa kikewa mata ruƙiya yau shi ne ƙaramin abu ze gagareki maza ki farka in barci kike ki yaki da kanki.

 Daga jin labarin nan shaidanun Aljanune...

Sossai Rahama ke Zufa ta ce Abby ka kara turomin wasu adu'oi masu karfi..

Abba ya ce yanzu kuwa aikina WhatsApp da layin nan ta ce eh inayi Abba..

Daga haka suka yi Sallama.

Ran Salma inyayi dubu ya tashi ta ce chab ashe ma baduka tasha ba....

********

*************************

 Yarima Samad Daga shi sai Rahama kadai ne agidan.

 Kallon ta yake ta gefen idanu yanda taketa kai kawo a kitchen...

Uhmm taita yawo da katon hijabi acikin gida saikace matar mamaci.

Ita Ko Rahama a Nutse tagama girkin nata.

Ta gyara kitchen tsaf..

Abinci ta jera kan dinner table kamshin Abinci ba ƙaramin tadawa Yarima Samad hankali ya yi ba

Yana son ya yi magana ya kasa.

Kallon ta yake da mamaki bayan zumbulelen hijab dake sharan kasa da tasa.

Har nikaf taje dakin nata ta dauko tasa ta ce azuciyar ta za ka ga karyan, wulakanci dani kake zancen..

 Kokarin daukan remote yake yi dan canza tasha yaga tadawo falon ta zauna banda bakin kwayar Idanun ta babu abun da yake gani.

Cikin kidima ya ce keee ina zaki je?

Kallon shi take tacikin nikaf din ta ce hanyar waje ka ga nayi ?

Maida kallon ta a kan TV tayi.

 Sake da baki ya ce bayan katuwar hijab din nikaf kika sako.

Ta ce kwarai kuwa kaine ka koyamin in akwai namiji awaje in suturce jikina.

Kaman ce rannan a daki cemin kayi indai na yawo tsirara inda namiji a daki yo meye laifina takarashe zancen tare da maida kallon ta kan TV.

 Tashi Daga zaune ya yi yana cijje labban sa cikin tsawa ya ce ciremin hijabin nan tare da nufota ta gadan gadan cikin zafin....

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah4️6️

Gadan Gadan cikin zafin nama zafin nama yake kokarin cire mata hijab itakuwa gam tarike tana fadin please ka sake hijab din wuya wayyo anty zecire mun wuya..

Jin karar knocking Daga waje ya sa ya cika ta tare da komawa kan kujerar sa ya ce waye ne cikin bacin rai.

 Aminu ya ce dan iska to mune harda kulle mu a waje.

 

 Tashi ya yi yana tafiya yana tsaki murda handle din kofar ya yi ya bude kofar.

 Faruk da Aminu kallon shi suke yanda yake ta cika yana batsewa shikadai.

 Kusan a tare suka shigo falon '' Faruk ya ce Madam ke ce anan kallo kike ne ya jefo mata tambaya yana kokarin hawa kan matakalan step shida Aminu.

 

 Zazzakar muryan ta yaji tana fadin eh kallo nake sannun ku da zuwa ya gajiya tana magana hankalin ta nakan TV.

 Aminu ya ce kalau muka dawo Madam Samad.

 Yarima Samad tsaye yake kasa zaune danna wayar sa yake yi.

 Wayar sa ya fara ring ganin Maman Maryam ya sa ya ɗaga babu ba ta lokaci.

 Cike da nutsuwa yake yake gaishe ta ya ce ummy kina araina ya kike ya mutan gida ina Abban maryam yake da makawfta duk ya jero mata tambaya.

Daga can ɓangaren Murmushi ta yi tana zaune kan kujerar mulki ta ce kowa na lafiya lau Abdul Samad amma ba ka tambayi Maryam ba.

 Ransa ne yabaci sai ya dake ya ce kash narigaki a zuci kin rigani abaki.

 Aidole in tambayi yar ƙanwata mana.

Dafatan tana lafiya Ko tare da neman guri yazauna kan kujera 1str hankalin sa nakan TV.

 Maman Maryam ta ce tana lafiya lau saide ba ta gida taje unguwa inta dawo zan hadaku waya.

 OK toh yabata amsa dan abar zancen.

 Maman Maryam ta ce Ɗana.

 Naam ya ba ta Amsa tare da maida hankalin sa kan wayar dasuke yi.

 Maman Maryam cikin iya bariki ta ce daman sonake ince maka ina Matar taka take ka hadani da ita mugaisa mana wai ita ba ta tambayar ɗangin mijin ta ne koko feleke ta iya.

 Murmushi ya yi saida kucin sa ya lotsa ya ce kiyi hakuri zata San ku ne wataran.

 Daga can ɓangaren maman maryam ta ce Samad bangane zata san mu wataran ba ina matsayin uwar mijin ta.

 Shi ya sa auren yayan Malamai wallahi matsala ne kardai ta shanye maka kurwa.

 Samad Murmushi kwance a kan fuskar shi ya ce babu kodaya ummy na InshAllah zan gyara kokarin katse hiran yake dan shi kwata kwata beson korafi.

 Uhmmm Ummy na inba za ki damu ba anjima zankiraki yanzu fita zanyi ne yana kallon agogon hannun sa.

 Maman Maryam ta hada rai sossai kamar yana gaban ta ta yi tsaki amma beji ba.

 Ta ce daman sonake kazo da Matar taka mu ganta tun da rowar ta kake mana Ko hoton ta bamudashi.

 SAMAD YA CE Ummy na ina me baki hakuri ba zan zo da ita kwatano ba.

 Saboda auren nan dai Auren biyayya ne ''.

Kallon Rahama yake wanda shi take kallo itama tana jinjina kalaman auren biyayya daya furta...

.

Cigaba da magana ya yi kinga ba zan kawo ta cen kasar mu ba..

 Harsai ta Mallaki hankalin kan ta.

 Maman Maryam cikin fushi ta ce wani mallakan hankalin kai daya wuce auren ka da tayi.

 Ai tasan komai kaine kake mata kallon yarinya.

 Ni dai ka taimaka inzaka zo shari'ar da za ai nan da kwana shidda kuzo tare tun da ance befi kayi sati ba ka juya saiku juya tare dan Allah narokeka.

 Tagama kashe masa jiki cikin Sanyi murya ya ce InshAllah zanzo da ita.

 Sai dai ba zan barta a kasar ba.

 Cikin Jin dadi Maman Maryam ta ce eh kan ya yi ka ga zamu kulla zumunci.

 Daga haka suka yi Sallama.

 Ita Ko Maman Maryam suna gama waya da Samad rawan murna take ta yi yar aikin ta ta fito tana dariya ta ce maman mu abun farin ciki ne ya samu.

 Cikin Jin Dadi ta ce eh wallahi kedai ɗana ne ze zo da Matar sa kinga dole in taka.

 Yar aikin ta ce mama nima ina tayaki murna Daga hk tashige daki dan goge goge da mopin.

*************************

Yarima Samad yana gama wayar da Maman Maryam dakin sa ya nufa kai tsaye dan shiryawa za su je yawon neman baban sa dakuma hoton Mafarkin sa.

 Wanka ya fito yana daure da towel iya kugun sa....

 Gaban miroir yatafi yana kallon kansa a madubi tare da daukan mayukan sa masu dankaren kamshi ahankali yake shafawa a jikin sa.

 Kallon jikin sa yake yanda Ko ina da gashi ne kwance luf luf gwanin ban sha'awa.

 Sumar kansa yake kokarin tajewa dan yana dan tara su kadan.

 Kallon kansa yake ta cikin madubi ya ce Uhmmm..

 Bara in yi sauri na fita Ko Allah ya sa mudace a yau dinnan.

 Kayan da zai saka suna a gefen sa..

 Wando Jean ne da riga maroon.

 Saka kayan ya yi ba ƙaramin kyau ya yi ba.

 Shi kansa ya san ya yi kyau hakan ya sa ya yi wa kansa selfie.

 Yana daukar hoto yaji sallamar Rahama ta shigo dakin.

 Ko kallon inda take beyi ba yaci gaba da daukar hoton sa.

 Cikin hanzari ya zura takalmin sa komboss tafiya yake cike da izza da takama.

 Haryakai bakin kofa yaji muryan ta.

Tana fadin Abba na ya ce in gayamaka ba a ga hoton nan ba amma ya ce da zaran angani za a turo Abdul Jalil da sako.

 Jimm ya yi kamar me nazarin wani Abu..

 Be ba ta Amsa ba ya sakai ya fi ce Daga dakin.

 Itakuwa hakan be dame ta ganin yanda ya ba ta dakin dan shigowan da ya yi ta ce ikon Allah badai ba ta waje ba.

Jibi yanda ya hargitsa dakin nan kayan da yacire yanda ya watsar dasu a dakin take kallo da mamaki.

 Cikin hanzarin ta tashi ta gyara tare da maida komai a muhallin sa...

Nan da nan tagyara dakin har bandakin tashiga ta wanke shi tass..

 Jin karar wayar ta ya sa ta fito cikin sauri domin Dagawa.

 Tana amsa kiran ta ce wacece ne.

 Daga can ɓangaren ta ce eh lallai na yarda kin aure Rahama murya ta kika mance..

 Murmushi ta yi saida kuncin ta ya lotsa hijab din dake jikin ta ta cire tare da nikaf din..

 Ta ce Haba Asiya wace ni inmace dake kawar Arziki.

 Asiya ta ce ainagani kin canza layi baki nemeni ba amma nida na damu dake har gida naje gun anty tabani takarashen zancen cikin Jin dadi..

 Rahama ta ce kiyi hakuri inada niyar in kiraki natuba kawata..

 Asiya ta ce yawuce ya mijin naki yake ne ?

 Rahama ta ce kalau yake yafita ma.

 Wai yaushe zaki zone nayi miss dinki.

 Asiya ajiyar zuciya tasauke tana Lure da Rahama duk sanda ta yi mata maganar mijin ta basar da zancen take tahanyar dauko wani firan.

 InshAllah Zanzo cikin Satin nan aikina WhatsApp da layin nan Ko ?

 Rahama ta ce eh da shi nake yi mu koma kan whsap kawai Daga haka suka yi Sallama.

 Itako Rahama kayan ta take hadawa zata koma dasu dayan dakin dan tagaji da kwana kasa babu kwakwaran dalili bawai rasa wajen kwanan akayi ba mulki dai ake nuna mata..

************************

Yarima Samad yana saukowa kasa samun su Faruk ya yi har sun shirya.

Kallon Faruk ya yi ya ce inafatan ka fito da wannan zanen hoton.

Faruk ya ce ya za ai in manta da ranka yana Murmushi..

 Aminu ya ce ina fatan yau bazamu dade ba Ko.

 Kan wannan hoton wlh saikaita ba mu bakar wahala kai wallahi mafarkin ka munafuki ne taya ze nuna maka mace a kano be nuna maka gidan su ba..

 Faruk ya ce kuma fa haka ne wlh sai dai ya yi ta ba mu dan banzar wahala haba.

 Samad da duk suka cika mai kunne da hayaniya sunsan abun da yatsana kenan surutu.

 Dakatar dasu ya yi da hannun cikin halin Ko in kula da zancen nasu.

Ya ce akwai wanda na daure acikin ku ne.

 Duk wanda yaga be iya zuwa ya koma dakin sa yazauna.

Mikawa Faruk hannun ya yi Alamun ya ba shi zanen.

 Faruk ya ce dan Allah malam mu tafi in mun barka ka tafi kai kadai ba cewa zakai arasa gane inda kashiga..

Gaba suka yi Faruk da Aminu.

 Kallon su yake yana ciza yatsa lallai suncika yan rainin wayau...

Binsu ya yi abaya cike da dan saurin sa

************************

Rahama tana kai kayan ta dayan dakin Idanun ta ya sauka a kan lefen da Samad yadauko Daga gidan su Adamsy wanda tun da ya ajiye mata su.

 ba ta bi takan su ba..

 Kallon akwatunan take tsadaddu akwatina ne wanda Daga ganin su za su kai a kalla dubu dari biyar...

 Bude babban akwatin ta yi taga uban kaya turame guda dari na Atamfofi ikon Allah tafada yayin da taga wasu a ciki an dinkasu daidai size din ta.

Saita tuna lokacin da Adamsy yazo yadauke ta yakai ta gun tela da su auna size dinta.

 Murmushi ta yi me kama da ciwo ta ce Uhmmm haryanzu Adamu bandaina sonka ba..

 Bakin cikin rabuwa da Adamu take ta ce wayyo ni Rahama Allah kai ka san daidaii ina rokon ka a kan falalar ka kasama zuciyata hakuri da dangana..

 Jiki Asanyaye tabude sauran akwatunan.

Su lesss da materiel.

Hartakai kan ƙaramin akwati da gold ne zalla a cikin su.

 Mamaki ne yacika ta ta ce me zanyi da uban kayan nan harda kayan darirukan milyoyi.

Wayar tadauka tare da dannawa Anty kira.

Daga can ɓangaren ta ce my Rahama dafatan kina lfy.

Rahama ta ce kalau nake uwata ta kaina..

 Murmushi anti ta yi duk sanda ta ji Rahama ta ce mata haka to akwai magana mai muhimmanci da za ta yi mata.

 Rahama ta ce antina akwatuna lefe ne aka ajiye mun a dakina wanda Adamsy ya hada ne shi ne Abban Adamsy ya ba shi yakawo nan gidan da sunan nawa.

Anty ta ce wa 'akaba.

Rahama ta yi shiru batasan yanda zata fadi sunan sa ba..

 Anty ta ce haba yata yimun bayani wa' aka ba nace.

 Cikin yin kasa da Murya ta ce me nan gidan.

Murmushi Anty ta yi ta ce Haba Rahama ki maida hankalin ki waje daya nasan kinada tarbiyya kokarin da kikai na zama gidan miji bakowa bane ze iya ace Daga wajen daurin aure a canza a ba ka wani daban kinyi namijin kokari Rahama ta.

Abun da nakeso dake ki dauki komai ba komai bane kamar yanda naga mijin naki yana da saukin kai ga girmama na gaba da shi ki kalle shi da kyau Rahama duk inda ake son namiji yakai kyakywa mai Addini ga nutsuwa.

Hamdala zakiyiwa ubangiji ki..

Kema kam duk abun da na lissafa a kan sa Allah yabaki '' cancantar kune ya sa Allah ya hada auren naku '' uhmm Rahama ki kama mijin ki dakyau ni uwa ce ba ni ce zan koyar dake yanda ake kama miji ba.

Amma InshAllah zanturo da Asiya suna dan saki ahanya koda ta whsap ne inyakama suje gidan ki za su je.

Kinga Asiya kawar ki ce ina tabbacin bazata ci Amanar ki ba itama Ƙanwata haka.

Cike da nutsuwa ta rinƙa Jan hankalin Rahama...

Ta ce su wayannan kayan da suke a dakin naki wanda Adamu ya hada zan gayawa baban ki.

Muji abun da ze ce akai..

Rahama ta ce Anty nagode sossai samun uwa irinki sai Antona.

Cikin Jin dadi da Begen juna suka yi Sallama....

 Rahama maida kayan gefe daya ta yi tare da gyara dakin dan ya yi kura ka santuwa ba a kwana ciki..

***********************

Yarima Samad wani unguwa sukaje rijiyar lemu daidai wani babban Massalacin yan Darika ya paka motar sa..

 Faruk bude murfin motar ya yi yana kallon yanayin unguwar.

 Aminu shima fitowa ya yi ya ce ka ga la'asar takusa.

 Kallon Samad suka yi da Alamun jira yake su bude masa kofa.

Faruk y abude masa ya ce maza kafito inrufe motar.

Ka san yanzu za a tada Sallah.

 Samad ya ce to l'imam munji tare da yin gaba dan ɗauro Alwala.

 Ciki sauri sauri suka yi Alwala suna shiga Massalacin aka tada Sallah.

 Bayan sun idar ne suka dan zauna yin Azkarai..

Aminu duk yarigasu fitowa Daga Masallacin..

Suna fitowa suka same shi atsaye yana jiran su...

Samad kokarin bude murfin motar yake yaji sautin muryan mace Daga bayan sa.

 Firgita ya yi dan Jin muryan ya yi Daga sama.

 Nan da nan ya tsuke fuskar sa babu digon Mutunci ya fuskance ta..

Ya ce keee...

Wai meyasa ku yaran matan yanzu Sam bakuda kamun kai ne..

Kin tsaya mun a ka.

Fadawa zaki yi a jikina ne

Kallon banza yabita da shi tare da bude murfin motar yashiga.

Su Faruk da Mamaki suke kallon Yarinyar dan sunga ba ta da makusa amma matar shi tafita kyau.

Kwabe baki suka yi ganin yanda boss ke ta zuba ruwan masifa.

Wata matashiyar yarinya ce wacce ta dade tana kallon hoton Samad a labaran duniya kuma ta dade da fadawa kogin son sa har gidan su kallon zautaciyya ake mata fadi suke yi duk arzikin uban ki bekai na yarima Samad ba.

Yan uwan ta da iyayen ba ta shawara suka yi data hakura da shi dan ba Ganin shi za ta yi ba har Abada ba....

 Hawaye sun cika Idanun ta dan ko tun da ya tsare ta da ruwan masifa bakin ta mutuwa ya yi Daga ta ce Assalam alaikum shi ke nan cibi yazama kari..

Ganin har sun shige mota ne suna kokarin barin unguwar.

 ta yi saurin tarar me napep ta ce dan Allah bi bayan bakar motar cen mercendez...

Tayi mai nuni da hannun ta.

Inna ce zan tsaya daukar mota ta za su ba ce mun da gani tafada cike da damuwa a kan fuskar ta.

 cikin Jin tsoron kada tarasashi lokaci daya..

Me nepep juya akalar keken nasa ya yi yabi bayan su.

 Bama nisa suka yi ba daidai gidan Alh umar mai salula suka yi parking din motar tasu..

 Cikin sauri Faruk yabude wa Samad kofa.

 Kokarin dauko zanen Daga cikin motar yake Idanun sa ya yi har ba da yarinyar tana kokarin fitowa Daga napep din..

😳😳

Tana kokarin fitowa Daga napep din...

Tsaki ya yi yana maganar zuci.

Dauko zanen ya yi suka nufi jama'ar dake wajen bakin su dauke da sallama Farruk ya ce dan Allah tambaya nake.

 Cikin su wani ya ce Allah ya sa mun sani.

 Dan Allah muna neman Alhaji Salihu Turaki.

 Cikin mutanen da suka iske zaune ya ce gaskiya bana tunanin a wannan unguwar yake.

 Yarinya da ta biyo karasowa ta yi tana fuskantar Faruk ta ce wa kuke nema ?

 Farruk ya ce ke yar unguwar nan ce ?.

Ta ce eh mana tana me kallon Samad daya juya mata baya yana magana da wasu.

 Faruk ya ce Alhaji Salihu Turaki muke nema.

 Yarinyar mai suna Samira ta ce ayya ban san wannan sunan a unguwar nan ba.

Amma sunan yamin kama da sunan wani Sarki a kwatano.

Muna gani a jaridu.

Faruk ya ce eh to bashi bane.

Zanen hoton ya nuna mata kota San me kama da wannan..

 Samira ta ce eh tabbas nasan nataba ganin fuskar nan a rijiyar zaki.

 Makarantar ɗana bari ne..

Sunan yarinyar nan na mance gaskiya.

 Faruk ya ce dagaske kike dan Allah bamusan wasa fa.

Ta ce wlh dagaske nake maka yar uwar ku ce.

 Cikin zumudi Faruk ya samu Yarima Samad da yaketa tambayar sunan mahaifin sa da zanen hannun sa.

 Ya ce kai dan Sarki Albishirin ka yau burinka daya ze cika saura daya.

 Da sauri Samad yabar wajen da yake ya ce musu ya gode.

 Dawowa ya yi wajen Faruk ya ce ba ni insha mana.

 Faruk ya nuna Samira ya ce ka ga wannan yarinyar ta ce tasan zanen nan a rijiyar zaki....

 Samad kallon rashin yarda yake mata yana kallon zancen ta amatsayin karya ne dan tasamu suyi magana ne ta yi hakan..

Kallon ta yake yana nazartan ta cikin yin kasa da murya ya ce kin tabbatar da kintaba ganin wannan zanen..

 Eh nataba gani nasan ta munyi makaranta daya.

Aminu ya ce tana nan batayi aure bane Ko ta yi ?

 

Samira ta ce gaskiya ban san wannan ba saide naje na bincika..

 Numfashi Samad ya fesar yana kallon ta ya ce wlh inkikai wasa da hankalina zaki sani kalleni da kyau banson araina mun wayau.

Fuskar sa a murtuke.

 Faruk ya ce haba Samad tun da ta ce ta santa ai baza ta yi karya ba...

 Samira tagama lura yanzu duk abun da ta ce ze mata dan yana son yaga wacce yake nema da Jan ido.

 Cikin Jan aji itama ta ce na tafi naga sai bin ku nake kuna dizgani gaban mutane.

 Aminu ne yasha gabanta ya ce haba wane mu '' yanzu ki ba mu nombar wayar ki.

Tare da mika masa wayar cikin Jin dadi ta karba tasa masa nombar wayar ta.

Samad be bar abun da yakawo su ba yacigaba da tambayar Salihu Turaki kowa sai ya ce besan shi ba.

 Dawowa ya yi wajen su Aminu ganin yarinyar ta tafi ajiyar zuciya ya sauke.

Ya ce yww Faruk wancen yarinyar ka ga tafiyar ta Ko ?

Dan kada ta sake biyo mu.

Farruk ya ce eh ta tafi amma na karbi nombar ta nabata nawa tun da ta ce tasan ta.

 Make kafada Samad ya yi ya ce oh wannan matsalar kuce wlh kar ka sakoni koda wasa kar ka nuna mata gidana wlh.

Maganar zanen hoton.

 Inka shirya ta raka ka inta kaika kai kuma saika kaini inaga haka ze fi.

 Aminu ya ce kwarai kuwa hakan ya yi Yarima.

Maganar neman baban ka Samad Ko zamu canza kasa ce.

 Samad kallon sa yake ya ce meyasa kace haka Aminu.

 Numfashi ya fesar ya ce jikina yana ba ni yana raye kuma baya cikin Nigeria.

Wahalar da kanmu a banza muke nifa a ganina.

 Faruk ya ce gaskiya ne wlh adai duba lamarin nan.

Kokuma musa rokon Allah a kan a duk inda yake Allah ya bayyana shi.

 Samad ya ce na fahimce ku hakan ma mafita ce babba.

 Aminu gyara Tsayuwar sa ya yi ya ce to me ze hana kasa matar ka Rahama ta rinƙa tashin ɗare tana rokon ubangiji ya yi gaggawa bayyana inda yake a tunanina.

 Kuma surukin ka mahaifin ta babban malamin ne koshi mu nema ya sa mu a adua mana duniya fa da fadi cewar Faruk taya zamu gansa cikin dumbu jama'a bayan ba mu San inda yake ba..

 Sossai Samad ya yi Amanna da bayanan su.

Ya ce to mu je kai tsaye gidan sheik imam basai ankoma gida ba..

Cikin gamsuwa da bayanan sa suka bude masa murfin motar baya..

Shiga ya yi

Suma suka shige motar. suna Dagawa jama'ar wajen hannu Alamun godiya da kulawar da suka basu.

*************************

Al'amin tun da Salma tabar gidan sa sai yau ya samu yazo gidan nasu.

Sheik ya yi masa fada sossai da waazi da illan cin Amanar iyaye hakuri ya ba shi ya ce yarufa masa Asiri kar jama'a gari suji.

 Sheik ya ce uhmm Al'amin kenan kai kana tunanin ban san halin da kake ciki bane ka san Allah gafurum rahim ne ba a shiga tsakanin bawa da mahallincin sa.

Zancen Salma ta koma bema taso ba.

 Duk yanda Al'amin ya yi sheik ya ce babu wannan zancen fur yakiya akarshe ya ce to kana iya zuwa kasamu Salma inta amince saiku koma inkuma taki sai dai kabarta zuwa nan gaba.

Jiki babu kwari Al'amin ya shiga Daga ciki.

Dan ganawa da Salma.

Mama na ganin sa habawa tarufe sa da masifa dan iska shege la'ananne yanda ka cutar mun da yata InshAllah kaima za ka wulakanta.

Sossai Al'amin yaji haushin mugayen duar da take tamasa cikin rashin kunyar sa ya ce Mama karki sake zagina fa dan kina tunanin kinban jakar yar ki aini wallahi diyar kishiyar ki Rahama na so abani dan ba ta samu tarbiyya ba..

 Anty cikin sauri takaraso wajen tana kallon yanda Al'amin ke zazzaga wa Mama ruwan jaraba.

 Anty ta ce habawa Al'amin rashin kunyar ka haryakai ka zagi uwar matar ka.

 Sunne kai ya yi ya ce kiyi hakuri maman Rahama wlh matar nan ba ta da mutunci ne.

Kuka Mama ta saka iya karfin wiwi ta ce Abubakar kana ina ne.

Yau ga dan iskan surikin zamani.

Abdul jalil dake shigowa cikin gidan ya ce ai bayanan yafita lafiya kuwa ganin Al'amin yanda yake cika yana batsewa..

Mama ta ce wannan dan rainin wayon ne mana yazo waishi ze tafi da Salma.

 Abdul jalil ya mikawa Al'amin hannu suka yi musabaha kallon Al'amin yake ya ce kayi hakuri antina bazataba koma yanzu ba.

 Salma ce ta fito Daga dakin ta sanye take cikin doguwar hijab har kasa..

Karasowa wajen nasa ta yi tana masa kallon tara saura kwata..

Bismillah ta ce masa suka yi zauren gidan nasu.

Gyara Tsayuwarta ta yi tana kallon sa Daga kasa har sama.

Tana kar kada kafa.

 Amma wlh kacika dan rainin wayau Al'amin harkai kana tunanin zankoma wannan kazamin gidan naka kurkuku wanda a agidan namu Ko me gadi yafishi mukami..

Wlh ka yanka mun takardan Saki wawa lusarin namiji.

Al'amin banda tsuma babu abun da jikin sa yake yi ya ce nine lusarin lallai zan tabbatar miki da hakan.

Zancen saki kuma ai babu shi tsakanin mu dansai na wulakanta ki kamar yanda kika mun..

Murmushi ya yi me kama da ciwo ya ce eh daman nasan ke jarabbabiya ce shi ne nazo indaukeki mu je in rage zafi karuwar gida kawai..

 Salma zata Daga hannu ta mare sa Abdul jalil ya rike mata hannu'.

Girgiza kai yake yi ya ce antina kada kiyi haka komai lalacewar sa mijin ki ne iname baki hakuri ki shanye koma mene ne ya yi miki.

Kallon sa yamaida kan Al'amin ya ce kaikuma kaine shugaban ta intayi kuskure ka gyara mata ta hanyar nasiha yakarashe zancen tare da fita Daga gidan yabar su nan..

Kallon shi suke har ya ba ce musu da gani.

Salma ta ce ni zanshige wataran zamu hade ai.

Tana hararan sa tabar wajen sai wani yauki take yau gâta isassa.

Kallon takun tafiyar yake ya ce ai Salma ban dandani zumar ki ba har yanzu sonake ki shigo hannun na.

Zan canza miki gida fita Daga gidan ya yi yana tunanin yanda wasan ze kaya tsakanin su..

Salma na komawa gida Anty ta tareta ta ce karki damu da Abun da ya yi tashin balaga ne ke kuma kisan matsayin sa.

Ki girmama shi.

Mijin ki ne Aljannar ki na tafin kafar sa.

Hannun tayiwa Anty Alamun ya isa haka tana kunkuni ta ce ainasan da haka Rahama ce ba ta sani ba tana cen gidan da ba a son ta..

Fuuuuu tawuce cikin dakin su..

Anty da mamaki take kallon ta ta ce wai ita wannan yaushe za ta yi hankali ne.

Uhmm Allah yashirye ki tafurta tare da barin wajen...

**********************

Sheik zaune kofar gidan sa shida Aminin sa Isa.

Suna tattauna tafiyar da zasuyi zuwa kasar Gabon.

Gwanati ta gayya ce shi zuwa taron walimar daurin auren diyar shugaban kasar Gabon.

 

Parkin din motar da akai daidai kofar gidan nasa..

Murmushi Sheik ya yi ganin anrubuta Samad a jikin motar.

Aminin sa ya ce kamar surukin ka kobashi bane yana kallon Samad dake kokarin fitowa Daga motar.

 Sheik ya ce eh shi ne ashe ka gane shi.

Eh mana dole in gane shi ka san wajen daurin auren nan jinai yana fadiwa mai martaba wani Samad din za a daura wa aure..

Sheik ya yi Murmushi ya ce au Ko ni ne hakan zancen daga zuwa daurin aure sai ta juye dani..

Fuskar su dauke da Murmushi suna kallon Samad dake tunkaro su

Shida abokan sa..

Cike da nutsuwa suka karaso kan su akasa suka durkuse kasa cikin ladabi suka gaida sheik da Aminin sa.

Sossai suka amsa musu cike da fara'a.

Sheik. Ya ce kace munada manyan baki.

Muje Daga ciki Ko.

Tashi suka yi tare da Aminin sa.

Suka yi ciki Samad da abokan sa suna bayan su.

Direct dakin baki yakaisu tare da ajiye musu ruwa da lemu a gaban su..

.

Yarima Samad ya ce sheik imam mungode sossai da karramawa..

Sheik. Ya ce anzama daya ya Rahama take ?.

Cikin Jin kunya ya ce tana lafiya lau.

 Aminu ne ya yi gyaran murya yasoma yiwa sheik bayanin dalilin zuwan nasu...

Sossai sheik da Aminin sa suka jinjina Al'amarin

Sheik ya ce yanzu kimanin wata nawa baku ganshi ba.

 Yarima Samad cikin yin kasa da murya ya ce shekaru biyar kenan har muna neman na shidda..

Kada kai sheik ya yi ya ce eh lallai andade Allah ya bayyana shi.

Dukan su da Ameen suka amsa.

Kallon Samad ya yi ya ce kar ka damu zamu tayaka da adua.

Kaima ka dage har tashin ɗare kar kayi wasa dashi.

Samad ya ce InshAllah.

Adu'oi yarubuta masa masu muhimmancin

Jikin wata farar paper.

Masu karatu in kuna bukata zan turo muku very important wlh..

Mika masa ya yi ya ce sadaka kada kayi wasa da shi ɗana za ka ga haske.

Sannan kasa Rahama ta tayaka nasan ba ta da sanya wajen sallah ɗare.

 InshAllah za a mata magana Daga haka suka tashi har wajen mota suka yi masu rakiya shida Aminin sa.

saida motar tasu tabar unguwar Sannan suka juya shida Aminin sa..

Suna yaba hankali da nutsuwa irin ta jinin saurata basusan dawan garin ba.. *************************

🇧🇯

Hajiya Hassana daidai kofar masarautar mai mashin ya ajiye ta....

Ta sallame shi tare da nufo kofar masarautar gheuzo.

Kallon yanayin tsarin gine ginen su take yi yanda aka kawata wajen sossai..

Gwanin ban sha'awa.

Kwankwasa kofar ta yi ya yi daidai da ana kokarin budewa Yarima Ahmad kofa zefi ta yana cikin motar sa.

Sauke glashin motar ya yi yana zare idanu ganin hajiya hassana da ya yi cikin hanzari ya fara......

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah4️8️

Cikin hanzari ya fara kiciniyar bude kofar motar sa '' cikin azama yataho gaban ta kallon ta yake tare da sauke fask mask dake fuskar sa.

 Baiwar Allah me kike nema ne wai dan Allah.

 Meyasa ku mutane bakwa gane maula ba sana'a ba ce yakarashe zancen yana nuna mata hanya data wuce Daga nan..

 

Hajiya Hassana cikin dan ba ta rai yaro ƙarami na gayamata kalamai daya zo bakin sa, ta ce uhmm kai Ahmad ashe haka kake maganar mutane gaskiya ne kenan..

 Kallon rashin fahimtar inda zancen nata ya dosa ya fara ya ce bangane zancen mutane ba wani abu akace miki nayi..

Gyara Tsayuwar ta yi ta ce, kwarai Kuwa an gayamin kana da girman kai sabanin yayan naka.

 Kuma ni ba maula nazo yi kai kanka ka san nafi karfin haka..

 Kallon ta yake yanda ta hada rai take gayamai maganganu.

 Daga kasar Ghana nake.......

Aiki nake nema kuma a gidan sarauta nakeso dagaske nake maka ba maula nazo ba ka yarda dani

Wani kallo yake bin ta da shi masu tarin ma'anoni ''

Kinga dan Allah ba na son shishigi

Bama bukatar ma'aikata a masarautar.

Tun da angaya miki inada girman kai meye na tsaida ni yakarashe zancen tare da komawa wajen motar sa.

Kallon banza yake ta bin ta dashi.

 yana shiga motar yakara gaba

 kallon sa take harya fita layin.

Karasawa wajen kofar shiga masarautar ta yi taci Sa'a khadija ta fito yiwa kawar ta rakiya.

 Inawuni ta ce musu kallon ta suke suke..

 suka amsa mata da lafiya lau ne.

Tare da wuce ta.

Kawar khadija ta ce wannan matar kuma Daga ina tana kwabe baki.

Khadija ta ce ina zan sani nima hk nagan ta..

Ciki gaba da tafiyar suka yi inda suka tsaida me napep.

Kawar khadija na hawa napep

Khadija ta juyo da nufin komawa ciki.

Hajiya Hassana ta tareta cikin damuwa kwance a fuskar ta ta ce dan Allah baiwar Allah ki taimaka mun inshiga masarauta aiki nake nema kudina ne suka kare Daga nazo neman mahaifina gashi ina son komawa kasar mu Gabon kudin jirgin da gindin sa yazauna hôtel din ɗana sauka yau kudina zekare ban san ya zanyi ba insuka koreni ba..

Khadija ta ce subuhannalah wayyo baiwar Allah kinban tausayi.

Kin buga gidan ne ba a bude miki ba ?

A'a ina dai kokarin bugawa naga wani matashin saurayi ya fito a mota kin saurarena ya yi inaga sauri yake.

Khadija ta ce Ayya haka yake kiyi hakuri nasan yaya Ahmed ne, zan taimaka miki InshAllah bara inshiga ingayawa Mamy intaban izini zanshigo dake takarashe zancen tare da barin wajen...

Hajiya Hassana ta ce uhmm Allah ya sa ta amince dan wannan bukata ta shi ne farkon nasara ta InshAllah..

Khadija na isa sashin Mamy ta iske ta ta yi uban tagumi batayi wata, wata ta ce Mamy na wai haryanzu ba za ki rage damuwa ba.

Kinga wata bakuwa awaje ta ba ta labarin yanda suka yi ta ce kuma fa Ahmad kin sauraren ta ya yi yawuce.

Mamy ta ce gaskiya be kyauta ba ki je ki shigo da ita muji me tazo dashi.

Cikin Jin dadi ta tafita wajen

Dan ta shigo da hajiya hassana.

*************************

Fulani da Abban Marwan zaune suke fuskokin su dauke da damuwa.

Marwan cikin bacin rai ya ce wlh Mamy kashe Yarima ya kamata muyi da matar sa.

 Kokuma a raba su.

Idan anje miki ya kusance ta karkiyi Gardama wallahi.

Cikin takaici Abban Marwan ke ta huci SAMA YA CE AI INSHALLAH ba zai kusance ta ba dan haryanzu beda karfin sha'awa a jikin sa.

Fulani ta ce injiwa ya gayamaka haka bakada labari ne.

Bokan daji cewa ya yi wallahi rannan kadan yarage be kusance ta saida suka sauya mata halittar ta zuwa na kunama shi ne dalilin dayasa be aikata abun da ya yi niya ba.

Dankali Abban Marwan ya furta nan take wani Zufa ya keto masa duk sassar jikin sa..

 

Kiyi hakuri Fulani in Allah in Allah ya yarda da matar tasa zezo..

Ai kinga kwanaki da Samad zeje kano Mai martaba ya yi na'am da tafiyar sa yanzu kuma ya fara Jin haushin haka har yana mummunar furuci a kan Yaya Salihu..

Wlh koda mai Martaba kadai da ita shegiyar matar Samad zamu iya rusa su gabadaya.

Nifa har Mamys sonake tabar masarautar nan to zaman me take yi ne yafada cikin Daga murya...

Fulani ta ɗara ta ce kai ai Mamy da kake gani muguwar icce ce bakar munafuka ce ai yanda mijin ta yabar Masarautar nan InshAllah itama tana ji tana gani zata barshi bari har surukarta tazo ni Fulani wlh saina nasa sun zama abun tausayi acikin masarautar nan....

Dariya Marwan ya yi ya ce nima dai yanzu na ji bugu.

Har labari yazo mun wai Mai martaba yana son ya Nada Yarima Samad a matsayin Sarki kiji fa.

Yana kallon uwar sa.

Dafashi suka yi shida Fulani suna bubbuga bayan sa Alamun rarrashi.

Kwantar da hankalin ka Marwan InshAllah Burin su ba zai cika ba...

**********************

Da sallama bakin su suka shigo Sashin Mamy khadija na gaba Hajiya Hassana nabiye da ita abaya....

Mamy dake zaune tana canza channel ajiye remote din hannun ta ta yi fuskar ta dauke da Murmushi ta yi sannun ki da zuwa ga waje nan ki zauna.

Hajiya Hassana neman waje ta yi a kasa ta zauna cike da ladabi take gaishe da Mamy..

Mamy ta ce dan Allah tashi ki koma kan kujera.

 dan Allah kiyi hakuri a kan abun da Yarima Ahmad ya yi miki..

Hajiya Hassana Murmushi ta yi ta ce haba ai yaro da nakowa ne wlh bakomai bane '' Inkika duba wani ɓangaren yana da gaskiya yanzu mutum ba abun yarda bane..

Kuma zama ka san ya yi min dadi kada ki damu nagode da kulawa.

Mamy ta ce haka ne kuma Amma kasa kyakyawan niya InshAllah baza a ci galaba a kan ka ba...

**************************

Gabon 🇬🇦

Cikin tashin hankali baba Salihu yake kallon computer dakin nasa..

Ganin hassana hankalin sa ya yi mugun tashi ya ce wannan matar me take nufi ne wai haukar taje tafadawa mata ta Ko sotake ta tona mun asiri asan inda nake..

Wata zuciyar ta ce tome abun damuwa kawai kabar kasar..

Ya ce A'a kozan ban kasar nan sai nayi yanda za a yi wannan matar ta dawo Gabon InshAllah

Ransa a matukar ba ce yakira me bashi labari.

Bugu daya ya Daga..

Daga can ɓangaren ya ce ya shugaba na ji muryan ka sai a hankali..

Baba Salihu ya yi masa bayanin matsalar daya kunno kai

.

Jinjina Al'amarin ya yi ya ce ka san dai ina kano Ko amma akwai wanda nayarda da shi anan kwatano kuma amintaccen yarima Ahmad ne zansashi ya sa idanu a kan ta.

Ba tare da ya san dalilin yin haka ba.

Cikin. Gamsuwa da bayanan sa baba Salihu ya ce pls ka taimaka mun dan banson duk shirina yatashi a banza ta dalilin ta..

Daga haka. Suka yi sallama.

Kasa zaune ya yi yanata safa da marwa a dakin nasa..

*************************

🇳🇬 KANO

Horn suka yi mai gadi ya wangale masu gate....

Parking space suka ajiye motar..

Faruk ya zagayo dan budewa Samad mota

Sai gani ya yi ya bude amma be fito ba.

Ya saura acikin motar be fito ba

Aminu ya ce, wannan lafiya kuwa shibe fito ba.

Faruk ya ce ka kyaleshi Sarauta ce ta motsa naga dai yanzu yagama waya.

Zomu shige ciki inya gama ya fito dan kansa.

Barin sa wajen suka yi..

Tare da shiga cikin gidan.

Rahma zaune take duk hankalin ta yatashi sossai Saboda mummunar mafarkin da tayi.

Ganin su Faruk sun shigo Daga cikin gidan '' cikin sauri sauri ta nufo su.

Fuskar ta babu walwala ta ce sannu ku da dawowa

Yawwa suka amsa mata.

 baza idanu take yi inda zata ga Yarima Samad ya bullo sai gani ta yi shiru ne..

Kallon ta tamaida a kan su Faruk dasuke kokarin hawa kan matakalan step..

Da kakkausar murya ta ce ku daka ta nace Ko ?

Da mamaki suka juyo suke kallon yanda Idanun ta suka kada lokaci daya.

Faruk ya ce Madam Samad lfy kuwa ?

Ta ce ina fa lafiya kunshigo gida babu bayanin da kuka mun.

Ina Mijina yake kuka dawo ku kadai bayan tare kuka fita kallon agogo ta yi ta ce karfe goma ɗa rabi na ɗare..

Ina magana kunyi shiru.

Aminu ya ce yana cikin mota zaune muka barshi.

Be gama rufe bakin sa.

Tayi hanyar wajen aguje..

Har buge kafar ta ta yi dan sauri.

Wajen motar tasa ta nufa mutuwar tsaye ta yi ganin..

Taku har kullum kyauta Daga Allah4️9️

Mutuwar tsaye ta yi ganin Yarima Samad hancin shi na fitar da jini ya jingina kansa jikin kujerar mota numfashin sa nata fisga sama_sama harya fara fita hayyacin sa.

Sossai hankalin ta ya tashi batasan lokacin data shiga taba jikin sa ba, jikin ta na rawa aguje takoma gidan gudu take ba ta ganin inda take jefa kafafun ta.

Faruk takira sunan sa da karfi har gidan ya amsa da sautin muryan ta.

 Faruk dake kokarin canza kayan jikin sa.

Jin muryan Rahama ya sa suka fito cikin hanzari shida Aminu.

Da sauri sauri suke saukowa Daga kan matakalan Step.

Rahama na ganin sunfito.

Cikin fita hayyacin ta datayi ta ce Dan Allah kuzo mu je bakin ta na rawa '' ku taimaka mun mijina ba ta jira cewar su ba ta yi wajen a guje.

Cikin hanzari suka take mata baya kokan su Iso

Har tana kokarin fiddo shi Daga motar da iya karfin ta.

Faruk a razane ya ce Abdul Samad cikin tsananin tashin hankali suka tara hannu shida Aminu wajen ciccibar sa zuwa daki...

Daga shi suka yi cikin tashin hankali Rahama ta ce ina zaku kaishi ne.

Ku dawo da shi mu je asibiti ta fada cikin raunin murya.

Faruk ya ce kibari a dai fara du bashi mugani suna cigaba da shiga ciki dashi.

Kan kujerar 3str din falon suka ajiye shi..

Aminu ya ce yanzu wani likita ne zamu kira ya duba shi.

Rahama dake arude shafa fuskar Samad ta yi ta ce akwai docto family house din mu zan kira Abbana ya turo mana shi..

Cikin hanzari tadauko wayar ta tare da dannawa sheik kira.

Wayar sa ta yi ring har ta katse ba a Daga ba.

Tallafo kansa ta yi tana ta masa fifita.

Ganin Zufa yake ta yi duk karfin Ac dake dakin.

Aminu ya ce basu Daga bane yana tambayar ta.

Eh be Daga ba kila ya kwanta ne amma bari inkara mama ta.

Takarashe zancen tana mai dannawa anty kira.

Bugu daya anty ta Daga.

Cikin sheshekar kuka ta ce anty dafatan kuna lfy dan Allah nombar docto ishaq zaki ba mu nakira Abba na be Daga ba.

Anty cikin kidima ta ce subuhannalah daughter meyake samun ki ne bakida lfy ne wayyo gayamin kinyi shiru cikin gigita take magana duk tabi ta rude.

Rahama cikin sassauta murya ta ce ba ni ba ce.

Shi ne beda lafiya.

Idanun ta na

Shiru ta yi Jin yana motsa hannun sa na dama.

Jefar da wayar ta yi ta nufesa hannun ta Daga cikin kuka ta ce Faruk dan Allah kabani ruwan zam_zam in akwai agidan nan in babu kaban ruwa pls tafada cike da bukatuwa..

Faruk cikin hanzari yatafi dan cika umarnin ta.

Anty sai hello hello take ta fadi amma shiru take ji sai tashin maganar da suke yi a falon take ji.

Hakan ya sa ta kasa kunnen ta..

Ganin Rahama ta ma mance da ita hakan ya sa ta katse wayar tare da lalubar lambar docto ishaq.....

Faruk hannun sa dauke da ruwan zam zam ahannu cikin hanzari yakaraso falon yana mai kokarin mika mata..

Bata karba Daga hannun sa cikin sanyin murya ta ce dan juye mun a kofi.

Adu'oi take ta karantowa tana tofah masa a ilah'irin jikin sa..

 Samad Idanun sa a lumshe.

 Ajiyar zuciya ya soma saukewa ahankali yake kokarin Daga hannayen sa.

 Ganin haka ya sa Rahama ta yi saurin Daga shi tare da daura kansa kan cinyar ta.

Faruk miko mata ruwan ya yi ta karba cikin sauri.

Nan m'a ta shiga karanto adu'a sossai take yi wanda saida ta dauki minti shabiyar.

Sannan ta dan dan Daga shi da taimakon Farruk.

Cikin sanyi murya ta ce Amjad ga ruwa na kawo maka kasha dan Allah..

Ahankali yake bude Idanun sa yana kallon yanda duk tabi ta susu ce.

 Hannun ya yi mata Alamun ta ba shi dan shi kansa kishi yake ji sossai..

Mika masa ruwan adu'ar ta yi tana kallon yanda hannun sa ke rawa ya kasa rike kofin cikin hanzari tasa hannayen ta cikin nashi tare da kai masa kofin abaki.

Shanye shi ya yi tass.

Yunkurin Amai yasoma cikin hanzari ta ce Aminu dan ba mu roba a bandaki.

Ganin Aminu ze ba ta mata lokaci hakan ya sa ta tashi aguje ta tafi tadauko tana kokarin tara masa agaban sa daidai da saukan Aman.

Amai yake yi ba kakkauta har Idanun sa sunjuye.

Wani ciwon ciki mai uban Azaba ya turnuke shi tun daga kan mara zuwa cikin izuwa kirjin sa

Nishi Nishi mai wahala yake fitar wa.

Rahama na kokarin tashi taje ta zubar da Aman wani riko ya yi mata yanda Ka san mace tana nakuda irin haihuwa tazo Gadan Gadan.

Sabon yunkurin Amai ne yataso masa.

Yanayin Aman 'hankalin su ya yi mummunar tashi ganin bakaken zare da Allurori hade da bakaken kyankyasai ya amayo.

Nan da nan.

Ya fara sauke Ajiyar zuciya akai akai.

Rahama da su Faruk kallon abun da ya amayo suke da mamaki.

Faruk ya ce innaliahi wa'inna il rajun.

Samad me wannan kuma nashiga uku ni Umar wayyo Allah na

Aminu cikin tashin hankali ya ce wannan abun sai mun dauki hoton sa dan wlh ba mu yarda ba.

Nida ataba Samad wllh gwamma ni aka taba.

Daukar wayar sa ya yi yadau hoto.

Rahama gabadaya bakin ta yamutu Idanun ta sun kada jajir '' kallon Samad take saita ji yabata tausayi.

 Cikin aro jarumta ta ce Faruk ku taimaka mun inshigar da shi daki ya yi wanka yakwanta kai kuma Faruk Zam _zam za ka karo mun su.

An gama Ranki ya dade yafada daukar roban Aman Samad ya yi tare da fita da shi Daga falon zuwa bandaki na baki

Dan ya zubar ya tsafta ce falon..

Aminu ya taimaka mata wajen shigar da shi daki.

Duk abun da ake Samad yana Jin su saide babu wani kuzari a tattare da shi bare ya taimaka wa kansa..

 Kallon Aminu ta yi cikin sanyi murya ta ce kana iya fita dan ya samu ya yi wanka.

Aminu ya ce babu damuwa inda abun da kike bukata ki sanar muna.

Kallon shi take harya fice Daga dakin

Tunani take taya zata taimaka masa ya yi wanka.

Cikin tausayin sa daya darar mata lokaci daya tasoma kiciniyar cire masa riga '' lafaffen cikin sa take kallo yanda gashi ya kwanta luf a jikin sa...

Tunani take to taya zata cire masa duka kayan jikin sa.

Wata zuciyar ta ce anya zaki iya yiwa wannan wanka kedai akwai sa kai rigima..

Barin wani Tunani ta yi cikin hanzari tasoma kokarin tadashi.

Duk ya sake mata nauyin shi kallon ta yake yanda yanayin ta ya canza sossai..

Tana kaishi bandaki taimaka masa ta yi wajen cire dogon wandon nasa.

Ƙaramin wando dake jikin sa tabar masa.

Ahakan m'a ta kasa jure kallon sa..

Ganin banda kallon ta babu abun da yake yi kuma ya kasa yin komai.

Uhmm Allah mai iko wannan wankan ma ba zaiyi ba saina masa...

Barin wani tunanin ta yi tare da yi masa wanka.

Babu ba ta lokaci tadawo da shi cikin daki.

Kaya masu dan nauyi tasaka masa Saboda tsabar sanyin da ake yi.

Kwantar da shi ta yi cikin muryan rarrashi ta ce inhada maka coffe ne kasha.

Shiru babu Amsa sai kallon ta da yake yi.

Hakann ya sa tafita tare da zuwa kitchen ta daura ruwan zafi coffe ta hada masa.

Tana kokarin kai masa a daki taci karo da Faruk da Aminu.

Ganin Docto Ishaq a gefen su zaune..

Cikin yanayin damuwa ya ce Rahama yakike ya mai jiki Alhmdulilah ta ba shi amsa dasauki. ta ce Docto a tsohon daren nan kazo.

Mun saka ka aiki nasan kila kana hutawa ne anty takira ka tafada cike da kulawa.

Docto Ishaq ya ce karki damu ai ɗare beyi ba sossai ina pection din yake.

Ganin Abdul jalil na kokarin shigowa da mamaki take kallon sa ta ce kaikuma daga ina.. Murmushi ya yi mata ya ce antina aini na rako Docto na tsaya Daga waje ne ina waya.

Rahma ta ce kash nade taso ku babu shiri my kani sannu da zuwa.

Kallon Docto ta yi ta ce mu je ta yi gaba suka take mata baya dukan su.

Dakin tashiga bakin ta dauke da sallama ganin har ya yi barci.

Ta karaso wajen gadon ahankali take shafa fuskar sa wanda ya sa ya bude Idanun sa..

Yasauke su a kan ta yana kallon coffe dake hannun ta yana turiri..

Shigowar su Farruk da Docto ya sa tafara kokarin mika masa coffe..

Babu musu yakarba ahankali yake sha.

Yana lumshe Idanun sa Alamun yaji dadin sa dan cikin sa ya yi dumi sossai.

Kokarin ajiye kofin yake hakan ya sa Rahama ta yi sauri karba Daga hannun sa sannu take ta jero masa akai akai cikin tsananin damuwa.

Docto Ishaq matsowa ya yi kusa da shi tare da duba sa cike da kulawa.

Kallon Docto suke yanda yake ta abu daya tun dazu.

Faruk cikin Kosawa ya ce Docto ka gano matsalar dake ɗamun sa ne har Amai ya yi hade da mugun abu acikin sa

salati Docto ya fara ya ce subuhannalah acikin nasa..

Aminu ya ce kwarai kuwa tare da kunna masa hoton daya dauka..

Cikin tashin hankali Docto ke kallon hoton cikin damuwa ya ce ni dai gaskiya a iya fahimta ta wannan ciwon bana asibiti bane..

Zan masa allurar daze ya samu barci sossai yatashi da karfin jikin sa.

Magunguna ya fiddo Daga jakar sa.

Ya mikawa Rahma...

Hannun biyu biyu ta karba..

Wayar ta ne yasoma ring tana dubawa taga Abba ne..

Cikin hanzari ta Daga wayar tare da karawa a kunne cikin sanyi murya tagaishe shi Daga can ɓangaren ya ce kin kira harna kwanta barci yau da wuri na kwanta..

Sa'adatu ta ce Mijin ki babu lafiya har Abdul jalil yaraka docto gidan naku..

Rahama ta ce eh Abba sunzo jikin ma dasauki tana son ta yi wa Abba bayani ganin mutane a dakin ya sa tafasa...

Abba ya ce Allah yakara lafiya ku kula da shi dan Allah kinji yata.

InshAllah ta furta tare da yin sallama ta ajiye wayar.

Docto da Abdul jalil sallama suka yi masu a kan za su koma..

Rahama godiya ta yi musu '' su Faruk da Aminu rakiya suka yi masu.

Kudi Faruk yadauko da niyar sallamar docto amma fur yaki ya ce ai yiwa kaine karsu damu.....

Rahama gyarawa Samad kwanciya ta yi tare da rufa masa blanket a jikin sa..

Zaune takoma ta yi tagumi tuna abun da ke gabanta ya sa ta tashi tare da dauro Alwala ta yi shafa'i da wutri..

Alkur'an mai girma ta dauko ta bude tafara karanta shi cike da nutsuwa muryan ta na tashi tana karatun tana kallon Samad dake motsawa a gadon sa.

Faruk da Aminu sake dawo wa cikin dakin suka yi ganin Rahama na karatu shikuma barci yake hakan ya sa suka juya dan zuwa nasu dakin..

Aminu ya ce ka ga ikon Allah Ko badan yarinyar nan ba ya zamuyi da shi wlh iyaka mukai shi Asibiti ayi ta magani daban cuta daban..

Faruk ya ce ka san kwanakin baya sanda ba ka gari wlh ya yi ciwo sossai dan har nacire rai a kan ze tashi.

Ba ɗare ba rana haka muke kuka nida Mamy da kannen sa.....

Aminu ya ce subuhannalah andade ana ruwa kasa na shanyewa kenan.

Yakamata mu kira Mamy a sanar mata da abun da ke faruwa cewar Aminu..

Faruk ya ce haka ne kuma tare da lalubo wayar sa ya dannawa Mamy cikin sa'a kuwa ta Daga hakanan ta ji ba ta da nutsuwa banda bugawa babu abun da zuciyar ta take yi.

Cikin rawar murya ta ce Faruk ina fatan dai lafiya Ko.

Farruk yabata labarin abun da ke faruwa cikin tsananin tashin hankali tafara kuka ta ce shi ke nan ɗana ze mutu.

Hawaye shar a Idanun ta.

Farruk ya ce Mamy hakuri zakiyi ai ya samu kulawa sossai gun matar tasa kinga ita ce silar fitar mugun ajiyar dake cikin cikin sa.

Mamy ta ce ina matar tashi take 'Faruk ya ce tana dakin su inkai mata wayar ne ?

Eh kai mata wayar nan dan Allah.

Cikin sauri sauri ya nufi dakin iske Rahama ya yi zaune inda yabarta karatu take yi hartayi nisa tsitt kake Jin dakin banda sautin muryan ta da kamshi turare babu abun da ke tashi a dakin...

Cike da kulawa ya ce Madam Samad mamy za ta yi miki magana yafada yana me mika mata wayar.

Amsa ta yi tare da ajiye Alkur'an a gefen ta cike da girmamawa ta gaida Mamy ta amsa da lafiya lau ya me jiki.

Ta ce yaji sauki Alhmdulilah.

Mamy shiru ta yi tana nazarin tayanda zata bullo mata..

Cikin sassaita murya ta ce diyata Rahama ta amsa da naam tana me maida hankalin ta a kan abun da take shirin fade.

Mamy ta ce dan Allah kisa idanu sossai a kan sa '' ki taimakeni yanda Allah yataimake ki Rahama.

Dan Allah karki ringa nesa ɗashi indai yana gida Ko baya gida ki ringa bin diddigin sa.

Rahama cikin sanyin jiki ta ce InshAllah Mamy zan kula.

Cikin Jin dadin Amsar ta Mamy ta ce Allah ya yi miki Albarka nasan dai ya yi barci Ko

Rahama da Idanun ta na a kan sa ta ce eh ya samu barci sossai ma.

 To dan Allah karki kiyi nisa da shi koda cikin ɗare ne.

Maganar Mamy ba ƙaramin tada mata hankali ya yi ba ita da take shirin ta shimfida bargon ta akasa tun da yau kwana ya kamata a dakin sa..

Mamy ta ce dafatan dai kingane abun da nake nufi..

Rahama ta yi shiru ba ta bata Amsa ba..

Mamy tsab ta lura Rahama tana Jin kunyar ta sossai Daga haka suka yi sallama.

Ajiye wayar ta yi gefen gado ganin Faruk yafice..

Cikin sanyin jiki taje ta murzawa dakin key tare da dawowa cikin dakin.

Samad da yanzu yafarka amma be bude Idanun sa ba. Kallon ta yake yanda take ta safa da marwa acikin dakin.

Zam Zam na hannun ta wanda ta juye a kofi yaga sai adu'oi take yi ba kakkautawa tana gamawa ganin ta nufo inda yake lumshe Idanun sa ya yi kamar me barci.

Yana Jin yanda take shafa masa ruwan adua a jikin sa har zuwa fuskar.

Taci gaba da shafa masa har zuwa wajen marar sa daidai hannun ta na kokarin..............

Ta ku har kullum kyauta Daga AllahUhmm masu fitar da novel.

Masu jiran na sata ayi ku sha zaman Jiraa dakyau fa.

😏

5️0️

Hannun ta na kokarin taba Samad din ta yi saurin zame hannun cikin Jin tsoro Kallon ta yake jiyayi kamar su shekara ahaka dan duk da ciwon da yake ji hakan be hana shi Jin felin na taso masa.

Kallon ta yake yanda take kokarin ajiye ruwan hannun ta.

Blanket ta rufa masa.

Kallon fuskar sa take taga eh lallai barci yake..

Uhmm ka ga mutum dan beda lafiya duk ya saki jikin sa saikace ƙaramin yaro '' komai sai an yi masa ni yanzu inama zan kwanta ne tafada afili kallon bakin gadon ta yi ta ce uhmm bara indan kwanta anan kafun ya tashi

 na farka karya ganni tana me kokarin sauka Daga kan gadon ta yi dan canza kayan jikin ta zuwa na barci.

Kayan barcin ta dauka direct bandaki tashiga dan saka su.

Murmushi ya yi ganin ta tafi bandakin yana cikin tunanin maganar yarinya nan da suka hadu a rijiyar lemu yake

so yake ya tambayi Faruk a kan tabbacin zancen nata

Wata zuciyar ta ce masa tokai Samad idan ka ga zanen hoton ka da ka dade kana nema ya zakai da Rahama.

Murmushi ya yi azuciyar fadi yake ita Rahma *KYAUTA DAGA ALLAH* CE.

Wancen muradin raina ce.

Ahaka har barci barawo yai gaba dashi..

Tana fitowa Daga bandaki cikin sauri sauri taje tasamu wajen cen karshen gadon takwanta.

Tunanin mafita take yi so take ta ji tarihin Yarima Samad '' kasa kwance ta yi tare da zama ta zabga uban tagumi lallai abun da tagani ba ƙaramin tada mata hankali ya yi ba.

Koma wanene tana tabbacin asiri akai masa.

Oh lissafi ya kwace mata so take tasan tasan komi game da Yarima Samad wa zan tunkara kenan take tambayar kanta.

Wata zuciyar ta ce haba Rahama ke kuwa kike da waɗanda za su baki labari tiryan tiryan.

Khadija ce ta fado mata arai Girgiza kafafun ta take yi lallai ba shakka badan ɗare ya yi tabbas da na kira khadija dan in ji Ko tasan wani abu game da yayan nata.

Ahaka barci barawo yai awon gaba da ita..

***********************

Alarme din wayar sa ne yasoma kara '' ahankali ya bude Idanun sa tare da sauke su a kan ta barci take amma da ka kalle ta sai kayi zaton Idanun ta biyu.

Harda gajiya suka dirar mata lokaci daya...

Sauka Daga kan gadon ya yi yana tafiya babu kuzari a tattare da shi amma tabbas yaji sauki sossai a kan jiya..

Jin karar bude kofar bandaki ne ya sa arazane ta farka.

Cikin hanzari ta nufo sa.

Cikin muryan barci ta ce ina za ka je ne tana murza Idanun ta.

Kallon ta yake cikin yin kasa da murya ya ce bakiga time din Sallah ya yi bane ba tare da yajira cewar ta ba ya shige.

Ta kai minti biyar tsaye inda yabar ta kallon kofar bandakin take.

Ko me ta tuna tajuya zuwa dakin nata.

Acen ta yi sallah tana idarwa ta tazauna yin azkar saida haske ya fito Sannan ta fada bandaki ta yi wanka da ruwa mai zafi dan sanyi ake yi ba kadan ba..

Shiko Samad yau a dakin nasa ya yi sallah anan kan darduma barci ya yi awon gaba dashi.

Faruk da Aminu sanye suke cikin farar jallabiya hannayen su cikin Aljihun rigar su.

Daga massalaci suke.

Aminu ya ce anya Samad ya tashi kuwa.

Yakamata mu kyaleshi zuwa anjima tun da matar sa tana nan.

Takun tafiyar Rahama ya sa hankalin su yadawo a kan ta.

Ina kwana ta ce musu a mutunce suka amsa mata da lafiya lau.

Faruk ya ce ya me jiki.

Amsa masa ta yi da yaji sauki har ma ya yi sallah yakoma yakwanta kokarin wuce wa kitchen take cikin dan saurin ta.

Kayan break take kokarin hada musu '' ruwan zafi ta dafa hade da citta da kanumfari' ganyen shayi da lipton sai dan lemun tsami data matsa kadan ya yi '' ruwan na tafasa ta ta ce shi hade da juye shi a flask.

Cikin hanzarin ta soya musu kawai duk ta zuba a babban kula ka sancewa abincin da sukafiso suyi break da shi kenan '' kan dîner table ta jera komai a natse take aikin ta cike da nutsuwa..

Na Yarima Samad gèfe daya ta ajiye kallon kofar dakin nasu take tana tunanin takai masa koko taje ta fito da shi dan ya yi break..

Wata zuciyar ta ce je ki kai masa kawai.

Cike da wannan tunanin ta tafi da su har cikin dakin nasu.

Iske shi ta yi ya fito Daga bandaki Alamun wanka ya fito.

Ajiye kayan hannun ta cike da ladabi kanta akasa ta ce ina kwana ya jikin naka ?

Kallon ta yake yana son gano wani abu amma abun ya ba ce masa.

Lafiya lau yabata amsa.

Zama ya yi bakin gadon nasa.

Kallon ta yake ta ja tebur tare da daura kan brek din.

Kokarin hada masa shayin take har ta suga tadauko madara zata zuba ta ji ya riko hannun nata yana kallon kwayar Idanun ta cikin kasala.

Ya ce kin san bana son madara a shayi.

Yi hakuri na mance ne ta fada tare da miko masa shayin.

Kwai data soya ta matso da shi gaban sa.

Kallon kwan yake ya ce ah ni ba zanci ba.

Dago kai ta yi kamar za ta yi kuka ta ce dan Allah kaci koda kadan ne pls...

Kallon yanda take magiya ya sa shi cewa stop zanci amma a baki zaki ba ni Inkin yarda.

Kalamin nasa Jin sa ta yi a bazataba shiru ta yi kamar me nazari kalaman anty dana Mamy sune suke yawo mata akai.

Cikin yi kasa da kanta ta ce na ji zan ba ka dan gyara zaman naka.

Kallon ta yake ya ce kidan cire hijab din ki kada ya barar mun da shayi yafada cike da bukatuwan haka.

Kamar bazata cire ba

 to tanason yaci hakan ya sa ta cire hijab din ta.

Durkushen da ta yi ya fito da saman boob din ta..

Mika masa shayin take amma shi hankalin sa baya kan abun da take miko masa.

Amsar shayin ya yi Daga hannun nata yana sha Idanun sa nakan boob din ta.

Har ya shanye shayin ba tare da ya sani ba be ajiye kofin shayin ba...

Kokarin tashi dan bashi kwan abaki take.

Cikin takura ta ce yawwa dan bude bakin naka inbaka tafada cike da kunya.

Shikuwa bemasan me take fadi ba ya yi nisa baya Jin kira a kallon Boob din ta..

Kallon shi take ta ce lafiya kuwa shiru kake ji banda sautin numfashi sa babu abun da take ji.

Batai aune ba sai jiya ta yi ya saka hannun kai tsaye cikin boob din ta..

Za ta yi magana ya ce mâta shiiiiiii.

Shiru ta yi cike da tsoro da Fargaba ta ce am zanje indan sawa Faruk da Aminu break.

Kallon ta yake ya ce Faruk da Aminu kuma meye hadin ki dasu badai kin ajiye ba sun zuba da kan su..

Ina nufin basu San na ajiye ba zan sanar dasu ne.

Kallon ta yake ya ce ni kibari inna fita zan sanar dasu.

Taso nace umarni nabaki inkinaso Albarkan aure..

Jikin ta na rawa ta hau gadon ta zauna ganin ya ture tebur din shayin gefe hankalin ta ya yi mugun tashi.

Innaliahi take ta m'aimaitawa.

Shiko kashe mata idanu ya ce Rahma yau nakeson in tabbatar dake cikakkiyar mace dan haka kishiga bandaki kiyi wanka ki ɗauro Alwala.

Tashi ya yi tare da nufar kofar dakin nashi yarufe tare da cire key din..

Hannun ta yakama ya je mu je muyi wanka muyi Alwala Ko.

Kin san kazar nan na kawo shi tun ranar da kika tare inwani kike bukata to..

Zansiya sai bayan komai yatafi yanda nakeso..

Kukan zuci take tana tunanin ya za ta yi babu mafita Samad yau soyake sai ya cimma Burin nasa..

.....

************************

Baba salihu zaune cikin dakin nasa kamar yanda ya saba kallon camera yake ya yi dan kwata kwata tun da yaga hassana a masarautar su beda sukuni......

Waya yake yi dame bashi labarai ya ce ya ce ya'akai ne kasamo mun dalilin ta na zuwa cen..

Me bashi labarai ya ce ya shugaba NA ance aiki taje nema kuma Mamy ce ta dauke ta aiki.

Cikin tsoro da Fargaba baba salihu ya ce yanzu wace hanya zanbi in gana da ita.

Me ba da labarai ya ce eh to inka san gidan nasu kaje kabar musu sako Ko kuma kazo da kanka a sirrince nasan inkazo to matsala yazo karshe kenan.

Baba salihu ya ce zan duba maganar taka intayi daidai zan dauka Daga haka suka yi sallama.....

*****************, ******

Sheik da Aminin sa Isa suna ta hada kayayyakin amfanin su na tafiyar da za su yi zuwa Gabon..

Aminin sheik ya ce Allah ya yi tafiyar tamu gobe ce..

Sheik ya ce haka daman rayuwa take duk abun da akasawa rana tabbatas.

Sai yazo.

Salma ce tazo cikin kyakkyawa shiga tana sanye da habaya Pink sossai ta yi kyau tana ta baza kamshi.

Durkusa ta yi ta ce Abba zanje gidan Rahama ne..

Kallon ta yake cikin Sakin fuska ya ce kin san gidan ne..

Eh anty tamun Kwatance zangane.

Kingayawa mijin naki ya jefo mata tambaya.

Kallon shi take cikin yin kasa da murya ta ce na gaya masa ya ce inje.

.

MashaAllah tun da ya amince Allah yatsare napep zaki hau ne.

Eh napep zan hau Abba.

Kudi yaciro Daga Aljihun sa ya Mika mata.

Ko godiya batayi ba ta tashi ta wuce.

Aminin sheik ya ce Allah yabaka yaya kyakkyawa wlh amma. Halayen sun banban ta.

Sheik ya ce ai Salma sai du'ai..

Allah dai yashirya.

Ameen suka. Furta tare...

.

************, *************

Samad yana rufe kofan dawowa dakin ya yi ganin yanda jikin ta yadau rawa.

Sossai..

Kamo hannun ta ya yi ya ce Rahama rabo ya rantse hakuri zakiyi babu abun da zakiyi ni yau Samad ba zan iya kyaleki ba wlh..

Amma in komai ya tabbata na miki Alkawari zanbarki ki sarara..

Cikin kuka ta ce kayi hakuri ka fadi duk abun da kake so zan maka dan Allah wlh jikina ciwo yake...

Kallon ta yake yanda take kuka da gaskiyar ta..

Uhmm Rahama kenan.

Kinada masaniya a kan me kikazo yi gidan miji..

Ko kin dauki auren ne azo azauna ayi ta safa da marwa acikin gida.

Kada kai ta yi Alamun A'a.

OK tashi mu je muyi wankan tare.

Cikin yin kasa da murya ta ce kai kaje kayi wanka danni nayi nawa.

. Ba na son musu Ko Rahama ta

Yana kallon ta yana kokarin kusanto inda take.

Hannun ta yakama ya hade da nashi.

Bara incire miki kayan tun da kin kasa cirewa.

A'a kabarshi zan iya.

Rufe Idanun ta Jin harya fara cire..............

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

Ankai rabin littafin..

Zanje hutu sati daya InshAllah ina dawowa hutu babu ba ta lokaci za a ci gaba...

Sai munhadu a ƙanwata book 2ƘANWATA.

Barkan mu da dawowa Daga hutu.

5️1️

... Jin har ya fara cire mata riga ya sa cikin tashin hankali ta ce dan Allah Amsad ka bari wlh tsoro nake ji cikin tsananin tashin hankali jikin ta ya ɗau rawa sosai kamar mazari, kallon ta yake cikin yin kasa da murya

ya ce "haba Rahma wai me kike so in yi miki ne so kike in zuba idanu ina kallon ki?

 ba na son na shiga hakkin ki ya ƙarashe zancen tare zagaye hannayensa wajen kugun ta yana

ƙara matsowa da ita kusa da dashi.

Sumbata yake kokarin kai mata tana zame wa sai girgiza kai take ta san sarai abun da take yi ba dai-dai bane amma haka kurum baza taba yarda wanda besan darajan auren ta ba.

Da wannan tunanin ta fara kiciniyar kwacewa daga hannunsa ina sai dai karfin ba daya ba ne dan ya gama gano lagon ta so take ta bijire masa.

Cikin niya da kudiri ya fara aika mata da zafafan sakonni motsa sha'awa wanda hakan ya sa ta yi sanyi har ta fara mance niyar ta.

 kokarin sa yake yaga ya rabata da kayan dake jikinta wanda ita a halin da suke ciki yanayin wasanni da yake mata ba ƙaramin tafiya da tunanin ta ya yi ba.

Kwantar da ita da ya yi yana kokarin mata rumfa yaji karar buga kofa da karfi,

 kallon kofar yake da cike da jin haushin haka amma a hannunsa yana cikin boob din ta yana wasa dasu.

Tsaki ya ja yana kallon Rahama yanda mood din ta ya canza,

Idanunta a lumshe yake sam ta mance gaban Yarima take.

Soma bubbuga gadon ya yi firgit ta dawo hankalin ta cike da mamaki take kallon kan ta babu kaya cikin razana ta ce ina kayana suke ne?

Saurin rufe mata baki ya yi da hannunsa ya ce mata "shhii"

Tare da nuna mata kofa da hannun sa a'lamun akwai wani a wajen kofar.

Cikin zazzare idanu da kunya da ya cikata ta sauko hade da zanin gadon kasa dan kada ya ganta ta manta ya gama kallota mai dauka ne kawai beyi ba.

 Cikin hanzari ta maida kayan jikinta.

Shiko sai tsaki yake ta jerowa akai akai jallabiyar sa dake gefen sa ya ɗauko tare da zira ta.

Jin Ankara buga kofar da karfin tsiya ransa ya ba ce yanufo kofar cikin da bacin rai ya bude.

Sakaka yake kallon Salma dake tsaye bakin kofar Idanun ta dauke da glass taci abaya.

Cikin hada fuska "ya ce baiwar Allah Daga ina hk kuma wa ya baki izinin shigo min gida har kina kokarin ballamin kofa? Ya ƙarashe zancen yana mai nuna mata hanyar sauka daga kan matakalan (steps) ɗin.

Da mamaki take kallon sa da ita ba fadan da ya keyi ya dame ta bakin sa take kallo ji take kamar taje ta l'ashe dan ba ƙaramin Jan hankalinta ya yi ba.

Tsawar daya daka ta mata ya jawo hankalin Rahama dasu Faruk da Aminu dake kasa.

Cikin hanzari suka karaso saman ya yi daidai da fitowar Rahama Daga dakin,

cikin sakin Fuska Rahama "ta ce my kanwaty kece?

Cikin hanzari ta rungume ta

Faruk ya ce wai kai har kaji sauki ne da ka ke ihu ba ka san zai taba lafiyar ka ba,

Meye ya hada ka da kanwar matar ka?

 

Yarima Samad da ransa yake aba ce ya ce kanwar matar tawa ita dabba ce,

kokuwa mahaukaciya ce ?

Dan ba ta da tarbiyya an bata, ta zubar a titi ya za ai tazo ta ringa buga mun kofa ina barci ta tashe ni ita ba ta Jira ne?

Rahama mutuwar tsaye ta yi ganin yanda ya rufe Idanun sa yana zazzaga ruwan masifa dan sosai yaji haushin ta inda ze iya Zane ta tabbas daya Zane ta.

Cikin rawar murya Salma ta yi kasa da kanta a duke ta ce dan Allah kayi hakuri ban san kana barci ba.

 Kallon banza ya watsa mata tare da yin tsaki.

Yabar wajen a zuciye tare da komawa dakin nasa zuciyar sa na tafasa.

 

Faruk da Aminu kallon Rahama suka yi Amma basu ga a'lamun bacin rai a tattare da ita ba wannan yana Daga cikin dabi'ar ta ba ka gane fushin ta sai inhar ta bude baki ta yi lafazin da zai sa a gane Ranta ya baci ba.

Faruk ya ce" Madam Samad kiba kanwar ki hakuri muma mun dauka yana farke ne shi ya sa da ta ce ba ta iya jira muka nuna mata dakin naku.

 

Salma ba ƙaramin bakin cikin wulakancin da Samad ya yi mata takeji ba.

Rahama cikin cool voice din ta ta ce "My kanwaty am sorry bai san ki bane shi ya sa amma zan mai bayani"

Kusan a tare suka sauka Daga kan matakalan( Steps) ɗin.

Farruk ya ja Aminu suka fita compound din gidan dukansu wayoyin su na hannun a rike sukabar falon.

Itakuwa Rahama zama ta yi cikin muryan rarrashi ta ce haba ƙanwata kiyi hakuri na kin hade rai tun dazu.

Salma kallon Rahama take tana jin mugun tsanar ta a cikin rain ta ayyana a ranta dole saita raba Rahama da Samad daman cikin wannan daulan take jibi fa dakin sa ta fito Girgiza kai tashiga yi.

Rahama dake kallon ta ta ce haba Salma har yanzu baki huce bane?

Murmushin yake ta yi cikin salo na bariki ta ce ayya karki damu ai yana da ikon yamin fada yayana ne shima.

Rahama murmusawa ta yi tare da tashi zuwa gaban TV ta kunna mata kallo.

Remote ta miƙawa Salma ta ce gashi ki canza tashar da kike so bara inje kitchen in daura mana girki Ko Salma ta ce Tom maza ki je tana yatsine fuska.

Kallon Rahama take yanda take tafiya cikin saurin ta.

Harara tabita da shi ta ce wahalalliya mai bakin hali irin na Anty sai kinyi kuka wlh InshaaAllah ba dai ni ba ce zaki sani ne.....

Samad yana komawa cikin dakin zaune ya yi bakin gado rike da kansa dake Sara masa hade da wani zazzabi banda haushin Salma ba abun da yake ji tabbas ita ce silan wargaza mishi cikar Burin shi.

Agogon dake makale jikin bangon dakin ya kalla ganin time yatafi ya sa cikin kasala ya shiga bandaki rage kayan jikin sa ya yi ya sakar wa kansa shaya wannan ruwan dake sauka bisa kansa izuwa gangar jikin sa ba ƙaramin tasiri suka yi ba wajen rage masa abun yake ji ba.

Lumshe Idanun sa ya yi abun da ya faru tsakanin da Rahama ne ya fara dawo masa ji yake kamar ya yi tariya ya koma baya cike da takaicin Salma ya fito daga bandaki tare da sane jikin sa da towel.

Gaban miror ya je yana kallon kansa ta cikin madubi Murmushi ya yi cikin maganar zuci ya ce ya Allah kanuna mun cikar burina na tabbatar inna same ta zata kula dani yanda ya kamata,

tsaki ya yi a ransa ya ce to ya'akai ne duk aji na amma gaban wannan yarinyar sai in kasa rike shi?

Barin wanan tunanin ya yi tare da dauko mayukan sa ya fara bin jikin sa dashi,

wasu tsadaddun kayan sa ya dauko Daga wadrobe ɗin sa kallon kayan yake yana tunanin Ko ya canza su ne wata zuciyar ta ce tun da ba ka taba saka su ''l

sa abunka kila rabo ya yi yau ka hadu da zanen hoton ka.

Da wannan tunanin ya yi maza ya saka wannan babban shaddar daya haddaden dinki Daga gun kwararen tela sossai rigar ta zauna masa a jiki,

ka sancewa bleu ne shaddar hula bleu ya saka ya dauko wanda ya yi macin sosai da kayan jikin sa.

Cikin dan hanzari ya zura agogo tare da saka takalmin sa half cover.

Sosai shigar ta yi masa kyau kara koma gaban miror ya yi yana kallon kansa tare da dauko turaren one love ya feshe jikin sa dashi.

wayar sa dake ajiye kan miror ya dauka tare da yiwa kansa hoto.

Kallon kayan break din Da Rahama ta kawo masa ya yi wanda ga sunan ba ta kwasheba kwabe baki ya yi ya ce uhmm badai an hadani da aiki ba,

In ba haka ina ni ina aure garin kano kuma a kanon ma wacce ban taba mafarkin samun ta ba.

Rahama dawowa falon ta yi ganin Salma ta daura kafa daya kan tebur din tsakiyar falo Kuma tasan Yarima in yagani to sai ya yi magana musamman da yake jin haushin su.

Su Faruk ma baya barin su daura kafar su akai ce musu yake suje su nemo nasu wannan nashi ne.

Cikin sanyi murya da dabara ta ce uhmm Salma zo mu danje kitchen ki tayani aiki mana?

Salma cikin hada rai ta ce au har wani aiki zan tayaki inzo gidan naki ni dai ki dafa kiba ni.

Kalamin Salma caraf a kunnen Samad dake saukowa kan matakalan (steps)din Jin karar tafiyar sa ya sa Salma da Rahama kallon sa.

Salma tabarakallah Masha Allah take ta furtawa ji take kamar taje ta rungume shi wanda haddaden gayen shi ne mijin Rahama ah lallai tana girgiza kai.

Rahama kasa da kai ta yi ganin ya karaso falon.

Fuskar sa a hade babu ya hada rai kallon Salma yake yanda kafafun ta ke yawo a kan wannan tebur din nashi.

Karasowa wajen ya yi yana kallon ta cikin idanu ya ce keee!

Da kakkausar murya yake magana wanda ya sa gaga Rahama har Salma tsorata.

Cikin bacin rai yake magana ya ce "ke waya baki damar ki daura kafafun ki anan?

Rike da kugun sa ya fara zazzaga mata ruwan masifa

wanda ya jawo hankalin su Faruk da daki suka fito dan Jin ba asi.

Cikin sauri Salma ta sauke kafafun ta.

Ta boye bayan Rahama dan gani take kamar bugun ta zeyi.

 Faruk ya ce" Yarima wai me yake damun ka ne?

Tun da ka kwanta ciwon nan shi ke nan sai ka fara dawo da halin ka na baya"

"Wannan fa kanwar matar ka Rahama ce ba ka ga suna kama bane haba dan Allah ka sassauta mata"

Yarima Samad da yakai wuya wajen bacin rai ya fuskanci Faruk cikin muryan sa dake nuna zallan bakin ciki ya ce.

"Ina ruwana da ita wacece Ko da tare suka zo duniya da Rahama karshe kenan ba abun da ya dameni a kan me zata zo mun gida irin wannan lokacin kuma tazo da hauka ace ba zan magana ba"

Kallon Rahama ya yi wacce ta yi kasa da kan ta.

Ya ce ki bude kunnen ki da kyau ki saurareni,

Wannan yarinyar in har tazo gidan nan ki ringa sauke ta a dakin ki Ko dakin baki ba na son in yi tozali da ita"

Rahama cikin kasa da murya dan yanzu ya fara ba ta tsoro ta ce" Insha Allah zan kiyaye"

Kallon sa ya maida a kan su Faruk ya ce kuzo mu je aina ga ku shirya Ko?

Aminu ya ce ai dole kace haka jibi yanda ka kure adaka shi ne za ka ja mu kamar wasu raguna babu kyaun gani.

Samad gaba ya yi ya ce to ina compund din gidan da kun gama ku same ni bai san me ya sa kwata-kwata baya son zaman falon tun da yaga Salma inda khadija ce daya zane ta wannan abun haushin ka.

Niko nace Yarima ya da daukan zafi haka daga ta buga maka kofa shi ke nan sai ka sa ta a gaba.

Kallona ya yi ya ce ke kuma Daga ina haka cikin yin kasa da Murya nace suna na *kyauta Daga Allah* wani kallo yabini da masu tarin ma'anoni ya ce suwaye ba na Allah ba?

Ganin kansa na hayaki ya sa na wuce sadaf sadaf ba tare da ya ganni ba na boye wani lungu dan cigaba da kawo maku labari.

Kallon agogon hannunsa yake ya na buga uban tsaki

Har ya zangaya ze shige motar ya sa Su Aminu har, sun fito suna ta buga uban sauri suma.

Samad ya ce yawwa Faruk wannan yarinya nan ya ma sunanta ?

Faruk ya ce Samira kenan kake nufi?

 

Eh ita ya bashi amsa a takaice.

"Dan kira ta ka tambaye ta yaushe zata raka ka?

Faruk zaro wayar sa Daga cikin Aljihun sa ya yi tare da dannawa Samira kira.

Wayar ta yi ring har ta yanke ba ta Daga ba.

Aminu ya ce" tun da ba ta ɗaga ba muna iya tafiya unguwar da ta ce"

"Amma fa kamar unguwa sheik Imam ne"

Samad ya ce "au haba unguwar ce aikuwa tazo gidan sauki"

Samad ya ce, " kamar ya kenan?

Aminu ya ce, "akwai wata kawar Rahama mai suna Asiya unguwa take inada nombar ta sai intura mata zanen ta whsap zata bincika mana basai mun;sha wahala saka yarinyar nan agaba ba"

 

Ajiyar zuciya Samad ya sauke" ya ce to dan gwada tura mata"

Bude datar shi Aminu ya yi ganin kamar Asiya ba ta online yau kwana hudu kenan.

Samad da Faruk da suka tsaresa da idanu suka ce ya ne katura mata.?

Aminu ya ce "eh natura mata saide ta kwana biyu ba ta hau ba"

Faruk ya ce kar ka damu da ta hau zata gani.

Samad shiga motar ya yi yana kokarin shiga mazaunin drever.

Faruk ya tareshi cikin hada fuska a wasa ya ce tabe tabe ya da haka ne

Wai?

Da mamaki Samad yake kallon sa ya ce waye tabe_tabe ne wai rannan na ji kuna fadi kuma yanzu naga kuna yawan fadin haka.

Aminu ne ya tuntsire da dariya ya ce" haba Samad dani yake fa wai ni ne tabe tabe.

Samad dake masu kallon rashin yarda da zancen Aminu ya ce "ku gaya min Ma'anar tabe tabe nace tare da hade fuska tamau.

Faruk kokarin shiga mota yake Samad ya jawo shi ya dawo da baya suna face din juna.

Murmushi Faruk ya yi ya ce ka basar wani film ne muka kalla nida Aminu sosai wannan shirin ya kayatar damu kuma sunan film din tabe tabe shi ya sa nasawa Aminu sunan ya karashe zancen yana Murmushi tare da bude mota yashige.

Samad tsaye ya yi yana nazarin wani Daga bisani shima shiga motar ya yi shida Aminu suka bar unguwar cikin gidan.

************************

🇧🇯

Mamy zaune falo Ahmad na kusa da ita.

Cikin Fada take magana ta ce "haba Ahmad meye hujjar ka na fadin kai ba ka yarda da wannan matar ba?

Ahmad fuskantar Mamy ya yi cikin yin kasa da murya ya ce

 "Mamy wannan matar fa na hadu da ita a zongo rannan dan ta ji ance Daga gidan sarauta nake shi ne fa ta biyo ni har da cemin in kai ta gidan mu"

Mamy tsarkan dake wuyar ta gold ce Hatta agogon hannun ta na gold ne kallo daya nayi mata tsab nagane bawai taimako take nema akwai wata manufa akasa"

Sossai Mamy ta gamsu da bayanan sa.

Kara matsowa ta yi kusa da shi tare da kama hannun sa cikin nata tana murzasu, kallon shi take ta ce maganar ka gaskiya ce wani lokacin tunanin ka sai ya fi nawa zurfi.

Amma kuma matar nan bana tunanin tana da wani mugun nufi amma zan sa idanu sosai a kan ta kai kuma karage tsanar da kake nuna mata pls"

Ka ringa gaishe ta kaji my son?

Murmushi ya yi wanda ya bayyana zallan kyawun sa ya ce "InshAllah Mamy zan kiyaye"

Tashi ya yi ya ce "to ni dai zan fita"

Fatan Alkhairi Mamy ta yi masa.

Tana kallon sa har ya bar dakin Girgiza kai ta ke yi ta ce "uhmm ko shi Samad ya zamantakewar sa da iyalin sa?

Daukar waya ta yi ta kira Samad.

Cikin hanzari ya ɗaga yana zaune kan kujerar office din sa a'lamun tarin aiki gaban sa.

Mamy ta ce ɗana ya kake ya gida.?

Lafiya lau ya ba ta amsa still dai hannun sa dauke da biro wayar hans free ya sata tare da ajiye ta kan tebur yana rubuce rubucen sa.

Mamy ta ce "ina diyata Rahama?

Kalau take ya ba ta amsa.

Mamy cikin zakuwa ta ce Samad wai ME maman maryam ta ce maka ne?

Cikin raba hankalin sa gida biyu ya ce" Mamy cewa ta yi inzo da Rahama dan su ganta"

Gaban Mamy ya yi mugun faduwa ta ce "tokai amsar me kabata ne?

Samad ajiye biron hannun sa ya yi tare da daukar wayar yacire hans free ya kara ta a kunne.

Ya ce nace mata zamu zo tare in har zan zo zaman kotu Inshaa Allah.

Nifa mamy na kusa komawa kwatanon da lokaci kadan yarage..

Mamy da gaban ta ya tsanan ta bugawa ta ce "bangane ka kusa dawowa ba?

Ajiyar zuciya ya sauke ya na mai shafa sajen shi da suka kwanta lub lub a fuskar sa ya ce "Mamy naga ai har yanzu Burina be cika ba dole zamu cigaba da adu'ar Allah ya bayyana shi"

.

Barin kanon ba zai tsaida kamfanin ɗana bude ba komai zecigaba InshAllah dan zan ringa zuwa duba abubuwa kuma inacen ma ina tafiyar da komai kar ki damu..

Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce Allah ya taimaka ya kuma kawo ku lafiya ka gaidamun Rahama"

Cikin Jin dadi ya ce" za ta ji mamy Daga haka suka yi Sallama"

Sai karfe hudu suka baro kamfanin Samad.

Kai tsaye babban super market Aljazeera suka nufa,

Suna parking din motar nasu ya yi dai-dai da wata bakar mota ta paka.

Wanda ke cikin motar ta cikin madubin motar take kallon Samad.

Samad kokarin shiga wannan Super market din ya yi Idanun sa ya yi masa tozali da wannan matar da take kokarin boye kan ta a cikin motar.

Mutuwar tsaye ya yi ya kasa tafiya cikin zafin nama ya juyo.........

 

5️2️

Cikin zafin nama yajuyo zeyi wajen wannan bakar motar '' hango Yarima Samad ya sa wannan dattijuwar fisgan motar ta aguje cikin sauri tabar wajen, aguje ya karaso amma ina har tana kokarin hawa titi.

Cikin ihu yake kiran Faruk da Aminu wanda tuni sun shige super market din..

Ba tare da yajira fitowar su yashiga motar a 360 ya fisgi motar ya take mata baya '' yana tuki cikin zakuwa daya cimma ta...

Wannan dattijuwar lura da yana bayan ta ya sa ta canza hanya wacce bana gidan su ba '' kwana ta rinƙa bi da shi har ta yi sa'ar ba ce masa da gani.

Su Faruk da Aminu aguje suka yi waje 'ikon Allah Faruk ya furta ya ce" Yakira mu Ko ina yatafi ne?

Aminu zaro wayar sa Daga Aljihun rigar sa ya danna Yarima kira.

Samad da ransa yake ɓace ya daga cikin Kosawa ya ce ku jirani gani nan tafe tare da katse kiran...

Aminu rike da baki ya ce" ka ga nine nakira shi amma beban daman magana ba, amma yafadi nashi ya katse..

Faruk ya ce meya ce maka ne? Yatsare shi da idanu...

 Cewa ya yi mu Jira sa yana yarfe hannayen sa cikin takaici..

 Isowar Yarima ya sa suka yi gunsa tun kan yagama parking din motar.

Daga zaune cikin motar ne ya leko kansa waje cikin dan ɓacin rai ya ce" Kungama ne kufito da kayan Muje.

Faruk ya ce" Inafa muka gama nagadai kaine kayi ihun kiran mu.

Dafa kai Samad ya yi ya ce" Oh My god babu ba ta lokaci ya fito cikin motar gaba ya yi suka take masa baya har cikin super market din..

*************************

Salma kallon a gogo ta yi bayan ta idar da sallah tana me kara bin gidan da kallo '' kowa ina tsaf yake cikin kwabe baki ta ce" Wai Anty Rahama kinada Y'ar aiki agidan nan ne?..

Kallon Rashin fahimta Rahama ta bita da shi tana kokarin kwashe kwanukan da suka ci Abinci..

 Salma numfasawa ta yi ta ce eh naga gidan nan yamiki girma sossai ya kike yi wajen aikin gidan nan ke kadai? Nasan ba za ki iya ba ko kinada masu yi ne?..

 Murmushi Rahama ta yi ta ce" kanwaty ai ba wani aiki bane agidan nan me wahala.

 Kwabe baki Salma ta yi tana taunan chiugum karas karas a bakin ta.

Yayi dai-dai da shigowar Samad da su Aminu cikin dan sauri sauri Yake tafiya. '' Caraf Idanun sa ya tsarke ɗana Salma tsuke fuska ya yi tare da barin wajen cikin dan hanzari.

Salma kallon shi take tana Ayyana to laifin me taimishi ya tsaneta..

 Faruk da Aminu falon suka karaso cikin sakin Fuska suke kallon Rahama da Salma tare da yi musu sannu,

 Suma sashin su suka nufa ba ɓata lokaci.

 Salma dake kallon ikon Allah ta ce uhmm kedai Anty Rahama kinada aiki babba Wallahi.

 Rahama ta ce name kenan? Cikin son Jin abun da zata ce..

 

 Ai dole ince haka gida duk katti ke kadai ce Mace a cikin su '' Sannan da dukan Alama Mijin nan naki dan bakin rai ne Wallahi, jibi tun da nazo yanda yake ta Jin haushina....

Hadiye sauran maganar ta yi Jin takun saukowa Daga kan matakalan step.

 Gaban ta ya shiga dukan uku uku ganin Yarima azuciye ya sauko kasa yana kokarin kaiwa Salma mari, Aminu ya yi caraf ya kama hannun.

Hannun Yarima rawa rawa yake Saboda tsabar bakin cikin bekaiwa Salma mari ba.

Aminu cikin kasa da murya ya ce" Waime Yarinyar nan ta yi maka ne haka?.

 Cikin ɓacin rai ya kalli Salma bakin sa na rawa ya ce suwaye Katti agidan nan?

 Faruk shima zare idanu ya yi ya ce katti kuma ? Yana kallon Yarima.

 Samad ya ce" Wannan Yarinyar ba ta da mutunci wai mune katti acikin gida...

Bakin Rahama na rawa ta ce" Yi hakuri ba da kai take ba wani firan muke.

 Samad Beko bi takan Rahama ba dan ita kanta haushi take basa.

 Direct kitchen yazarce.

Rike da kugun sa yana kallon yanda aka gyara wajen tsaf kamar ba ai aiki cikin ta gaba.

 Frij ya bude yadauko lemun champagne, 🥂 kwalba guda, ya karaso falon iske Salma ya yi har ta fice Rahma zata bi ta dan rakiya, '' muryan shi ta ji yana Fadin Inkika kuskura kafarki tabar falon nan da sunan Rakiya uhmm sauran basai na fada ba..

 Cak Rahama ta tsaya Idanun ta cike da kwalla tadawo itako Salma Jin furucin sa ya sa tabar gidan cikin saurin ta..

 Tana buga uban sauri wanda ya ja hankalin mai gadi, kokarin bude mata gâte yake amma koda ta Iso bankade shi ta yi yana kokarin faduwa.

Subhanallahi ya furta, wannan Mahaukaciya kuma Daga ina? Tsuke bakin sa ya yi kada aji shi tare da zama kan kujerar sa yana Girgiza kai...

 Salma tarar me napep ta yi Unguwar Malam isa ta yi masa Kwatance.

 Babu ba ta lokaci akai Unguwar da ita, yana sauke ta ta sallame shi tare da fadawa kai tsaye Gidan malam isa.

 Sa'a taci Malam isa ya fito zeje Unguwa, yana Ganin Salma ya gane ta ya ce" Amarya bakwa laifi mu shiga Daga ciki..

 Suna shiga dakin malam isa ya zauna itama zaman ta yi dirshan Idanun ta cike da kwalla.

 Kallon ta yake ya ce" Nasan mèke tafe dake.

Cikin mamaki ta ce" Ina ga ba muyi maganar damuwa ta da kai ba yanzu nashigo...

 Malam isa bushewa da dariya ya yi wanda saida dakin ya amsa ya ce" Tun jiya nasan da zuwan ki a yau

 Kuma matsalar ki daya ne kina son mijin yayar ki.

 Kinje gidan yaita miki wulakancin Ko ba haka bane?

 Haka ne ta furta cewa Salma..

 Malam isa yabuga kasar dake gaban sa ya ce" Ke Salma wannan auren ba zamu iya raba shi ba kamar yanda muka raba wancen ba.

 Cikin rashin fahimta Salma ke kallon shi ya za ai kace bazamu iya ba malam?

 Cikin kuka take magana ta ce" Malam ba ka san radadin danakeji ba inna bude idanuna naga wai yaya ta ce take auren wannan balaraben sai in ji kamar in kashe kaina malam..

 Kallon ta yake yanda take zaro zancen ya san har cikin zuciyar ta take fiddo zance..

 Salma yakira sunan ta atausashe !!

Na'am ta ba shi amsa tare da dago kai suna kallon juna.

 

Hanya biyu ce inma zaki kashe yayar ki ta hanyar sa mata guba a abinci, Ko kuma ayi amfani da Mijin nata wajen dauke hankalin sa a kan Yayar ki, amma fa ba zai sake ta ba duk rintsi kuma akwai haihuwa tsakanin su.

 Firgit Salma ta zare Idanun ta ta ce" haihuwa fa kace ya za ai a toshe wannan hanyar, Wallahi banson ta hada shimfida da shi inma ta hada banson taci gaba.

 Malam isa ya ce" Keko Salma ai kinga munyi nasaran hana wancen auren to wannan ya fi karfin mu domin shi kansa bibiyar ransa ake Daga cen ɓangaren dangin sa.

Salma bibiyar ransa kuma koda yake ai kyaun dan maciji ne beda mutunci.

Malam isa ya ɗara ya ce" Au kyaun dan maciji ne ni dai kam banga haka ba amma yana da zafin rai bayason takura da raini duk na gani dana buga kasa.

 Salma ta ce uhmm kaide asamu mafita Wallahi dan dagaske na kamu da son sa, kuma so na hakika wancen na baya kudin sa nakeso wannan Ko beda kudin zan iya zama dashi, pls ka taimaka mun harda matso guntun hawayen ta.

 Malam isa tashi tsaye ya yi yana kallon agogon hannun sa.

Kinga Salma akwai Inda zanje na lura bakya fahimtar abun da ake fadi haba tun dazu muyi ta maimaita zance daya, nagayamiki mafita ki je kiyi shawara wacce kika ga ze miki sauki ki dawo ki fadamun" Ya ƙarashe zancen tare da barin dakin cikin sauri.

 Ita Ko bayan sa takebi da kallo tare da tashi jiki asanyaye ta fito, dakin lissafi ya fara kunce mata wanne za ta yi a ciki ne dan gaskiya bazata yarda ta rasa Samad ba..

 Al'amin ne yafado mata wata zuciyar ta ce Kekuwa Salma kiyi yanda zakiyi ya sake ki Sannan Burin naki ze cika...

 **********************************************

Gabon

Baba Salihu zaune kamar yanda saba gaban computer yana kallon abun da ke faruwa a agidan Samad.

Rike da baki yake kallo yana cizza labban sa yaga dai Salma tambayar kansa yake to laifin me tayiwa Samad, yanda yake kallon Samad na yarfe hannayen sa ya tabbatar faɗa yake musamman daya kalli yanda fuskar sa take.

 Rufe ɓangaren Samad ya yi yana Girgiza kai yakoma ɓangaren Masarauta.

 Nan m'a kallo yake yanda hassana ke manne da Mamy, ɗâfe kansa ya yi cikin takaicin wannan Matar tambayar kansa yake wai ana so dole wai in banda hauka ma ya za ai taje wajen Matar shi duk da besan har yanzu meya kaita ba, amma ya tabbata wani ne yabata labarin sa harya ba ta adireshin sa tunani yake kodai canza kasa zeyi dan bayason kwata kwata abun da zai sa yadawo Masarautar duk da Mahaifin sa yana cikin waɗanda suka goyi bayan karya a kan sa..

 Kuma yahana yatafi da iyalin sa '' kukan zuci yake ya ce" Mamy ancutar dake baiwar Allah zuciyar sa tana kuna.

 Tashi ya yi Daga zaunen yakashe computer.

Kiran me bashi labari ya yi bugu daya ya Daga.

 Me bashi labari ya ce" Ya shugaba na har yanzu ina nan inasa idanu a kan Samad Yarinyar nan babu abun da ya taba shiga tsakanin Su na mu'amala.

Nan yaba baba Salihu labarin zuwan Salma gidan da abun da ya faru.

Baba Salihu ya ce Ayya wai yaushe Samad ze rage zafin rai ne.

 Me bashi rahoto ya ce" Inafa ya shugaba na sai dai Addu'a amma dai haryanzu fulani na bayan Samad da kanin ka.

Sossai ran sa ya sosu cikin kuka ya ce" Allah yakawo karshen wannan bala'in.

Ameen ya amsa yana kokarin katsewa ya ce" ya shugaba na akwai wani motar, wata dattijuwa da Samad yabi amma be gayamana wacece ba.

 Baba Salihu rike da habarsa ya ce" To kayi kokarin ya gayamaka abun da ya gani koma wacece ina sauraren ka.

Daga haka suka yi Sallama.

***********************

Salma jiki a sanyaye tadawo gida dai-dai mashigar gidan taci karo da Al'amin tsaye sai kallon agogon hannun sa yake yana Girgiza kai.

 Gaban ta ne yafadi ganin sa shima stil ita dai yake kallo, ya kura mata idanu ganin yanda ta yi masa kyau ta yi wani haske da kiba fatar ta ta yi fresh 'cikin sassauta murya ya ce" daga ina kike ?

 Bakin ta na rawa ta ce gidan Rahama naje.

Kallon ta yake yana nazartan kalaman ta.

Amma kin san inada hakkin ki gayamin duk inda zaki je Ko ?

Bakomai na rufa miki asiri wajen Mahaifin ki.

Dana nuna masa nasan da fitan ki '' tun da tafiya zeyi gobe ki tattara gobe kema ki dawo gidan naki, na canza miki gida zuwa cikin gari kuma kusa da gidan antyn ki na kama haya yana shu'umin Murmushi.

 Salma Zare idanu ta yi ta ce" Da gaske kake koda wasa?.

 Dagaske nake ai nayi maki surprise ne dan haka gobe ki shirya zanzo indauke ki..

 Cikin Jin dadi ta ce" Ai babu matsala zanbika bara in shiga in gayawa su Mama.

 No pls ki tsaya ina son mu je koda hôtel ne indai rage zafi dake kingane Ko.

 Wani kallo take binshi da shi na rainin hankali cikin kwabe baki ta ce" Amma kai Al'amin kai badahume ne kana tunanin zankara yarda kamin abun da kamun wancen lokacin ne? Ka cutar dani a banza dan kasamu Mahaifina mutum ne mai hakuri da kawaici, da wallahi ba za ka sha ba.

 Wallahi inma dan wannan ne kake son in koma toka canza tunani dan ba yanzu ba Wallahi kaji na gayamaka.

 Tun da tafara magana bakin ta kawai yake bi da kallo yana ayyana aransa irin rashin mutuncin daze shuka mata kafun ya sake ta.

 Wata zuciyar ta ce kaiko ai Salma ba irin Matar da za ka aura ka saka bane kaci gaba da kwasar ganiman ka har ta yi expire kafun nan kayi waje da ita.

 Dawo da hankalin sa ya yi a kan ta ya ce" Haba Salma taya za ai kice haka Inkin ce bakiso ni ba zan miki dole ba, aike nake so ba jikin ki Ko kin manta ni ne Al'amin din ki ne.

 Murmushi ta yi ta ce" To na ji zankoma din.

 Hannun ya sa Aljihun sa ya zaro dubu daya yana kokarin mika mata.

 Kallon kudin take da rainin wayau tadawo da kallon ta a kan sa tana yatsine fuska wannan kudin na mene ne ?

 

 Kudin kashewa ne nabaki Ko mata ta.

 Tsaki ta yi ta ce" Allah ya kiyaye aiko Ubana ba zai ban wannan ba..

 Dazun ma dazanje gidan antina dubu biyar yaban.

 Al'amin ya ware idanu ya ce" Dubu biyar fa kudin mota napep dinne ?dubu biyar ai Wallahi in'nine ba zan iyaba ina laifi dari biyar..

 Ganin ze ba ta mata rai wuce shi ta yi tabar shi tsaye rike da kudin sa ahannu.

 Maida kudin ya yi a jikin sa yana Girgiza kai tare da sa kai yafice.

 

 Anty zaune kofar dakin ta tana waya da Asiya cikin damuwa ta ce" Asiya.

Daga can ɓangaren ta ce" Na'am maman Rahama.

 Ina son ki je gidan Rahama dan Allah kin san Rahama ba ta da wayewa sossai a kan rayuwar aure, duk da zamani ya canza amma tana bukatar mai daurata a kan hanya.

Cike da damuwa take magana.

Asiya ta ce" Maman Rahama karki damu Insh Allah zanje har gidan nata naji, Abokin Mijin nata yana cemin wai za su tafi garin kwatano tare da da Rahama za su je.

 Anty ta ce" tare da Rahama kuma amma ta sani kuwa ?

Asiya ta ce" bana tunanin tasani dan bamuyi hiran da ita ba.

 Anty cikin ba da umarni Sam haka nan ta ji ba ta da nutsuwa, a kan zaman Rahama gidan Mijin nata '' ta ce kizo gida Asiya yanzu in ba abun da kike yi.

Asiya ta ce" Zan shigo InshAllah.

Tana katse wayar direct dakin Sheik ta nufa iske Mama ta yi a dakin zaune.

Da sallama bakin ta tashiga dakin.

 Tare da neman waje ta zauna cikin sakin fuska ta ce" Maman Salma ashe kina nan ?

Mama ta ce" eh ina nan cikin Kosawa da maganar ba ƙaramin haushin ganin ta ta yi ba..

 Sheik dake kokarin kulle ƙaramin a kwatin sa dago kai ya yi yana kallon anty cikin sakin fuska, ya ce" Sa'adatu ya jikin naki?

 Anty ta ce lafiya lau alhmdulilah.

 

Yawwa gwamma da kuka taru Anan gobe ne tafiya ta nida Aminina, dan Allah ku tsare gida da mutunci.

Har Allah ya dawo dani.

Ke kuma Anty yakamata ki je asibiti su dauraki a kan magani kin san mata irin ki na bukatar hakan.

 Insha Allah zanje anty ta furta ta ce" daman nazo muyi magana a kan Rahama.

Jin ta Ambaci Rahama ya sashi maida hankalin sa a kan ta..

 Mama dake kallon su Ranta yakai kololuwa wajen baci.

 Anty cike da nutsuwa take ba sheik labarin lefen da ke gidan Rahama.

 Sheik ya ce" To ai inhar Saboda ita aka kai tana iya amfani dasu tun da dai ba ita ta nema ba, Iyayen Adamu ne suka aiko.

 Maganar gold dasuke cikin akwatunan ta tazuba a wadrope din.

 Anty ta ce saura daya.

Murmushi ya yi ya ce" fadi inajin ki.

 Cikin yin kasa da murya ta ce" Gidan Rahama nake son zuwa Insha Allah Ko nan da jibi ne.

 Sheik ya ce" Masha Allah zaki je dubo Y'ar taki Allah yakaimu, inzaki je kisa drever yakaiki yadawo dake..

 Cikin gamsuwa da bayannan sa ta ce to.

Sheik kallon Mama ya yi da kiris yarage ta fashe ya ce" ki gayawa Salma ta rike mutunci auren ta tazauna waje daya banda yawo da auren wani a kan ta..

Mama cikin bacin rai ta ce kullum ba ka kyawawan zato a kan Salma, wai me ta tsare maka ne haba ai wannan tsana ce, Ko ince kiyayya ce.

Tun da take zazzaga ruwan masifa sheik ya mike tsaye yana kallon Anty, ya ce" Sa'adatu yau dakin wa nake acikin ku..

Anty ta ce dakin ta yake OK to saina dawo yafice a dakin dan kwata kwata beson biye mata.

 Ita Ko Anty fuskantar mama ta yi ta ce haba Aishatu kina ban mamaki Wallahi Rahama diyar ki ce ta cikin ki amma kike nuna mata rashin kauna..

 Me laifina dan Rahama tana Y'ar daki na?

Wallahi duk abun da zakiyi saide kiyi Wallahi ba zan taba Jin ina tsanar Rahama ba, koda kuwa ita Rahama ta nuna ba ta yi Uban ta ya damka mun Amanar ta karkiyi tunanin kinayin haka ne dan na ji haushi, Ko yau Allah yabarni ban haihu ba ba zanyi bakin ciki ba tun da ina da Rahama...

 Tsaya kiji dakyau Wallahi tallahi rantsuwar musulmi nafison Rahama a kan Abdul jalil kinko san da cikina na haife shi..

 Wallahi zakiyi kuka da idanun ki kirubuta ki ajiye.

 Tun zuwana gidan nan nakebin ki da lalama burina mu zauna lafiya.

Sheik dai yana mutunta ki sossai dan na lura ya fi sonki akaina hakan be taba batamin rai ba Saboda nasan tare naganku, amma kuma mutuntuwa fa ya fi ganin mutuncina a kan naki, Saboda kin zubar da girman ki antake shi.

 Kinba Y'ar ki mummunar Tarbiyya Wallahi da hannuna Salma ta zauna nasan Allah shi ne mai shiryawa da Wallahi ansamu saukin tabarar da take yi " Ta ƙarashe zancen tana kokarin barin dakin.

 Mama ce ta dakatar da ita cikin isa ta ƙaraso gaban ta ta ce" ke Sa'adatu kike Ko tsiya.

 Ai ke baki isa kice banda Tarbiyya ba shi ya sa Yata Salma ba ta da shi ba.

 Mu bama bin bokaye da malamai ba dole sheik ya mutuntaki ba

Kuma....

 Sallamar Salma da Abubakar ne ya sa Mama yin shiru.. Cikin ɓacin rai taga Abubakar tasan wa'azi ze tsaya musu barin wajen ta yi kamar zata bangaje Anty....

Salma banda harara babu abun da take jifan Anty dashi.

Har zata juya Abubakar cikin tsawa ya ce Salma zo nan.Jiki babu kwarai tazo cikin tsoro..

 Kallon banza yake binta da shi ya ce" Wannan ba Uwar Ki ba ce kike hararen ta, Matar da duk wata matsalar ki tazo ita ce kan gaba ita ce me nuna jajircewa a kan ki, duk da rashin hankalin da kike nuna mata.

Maza ki duka ki ba ta hakuri Ko in yi kasa kasa dake.

 Anty Murmushi ta yi ta ce" Haba Abubakar Yarinya ce fa haryanzu ka kyaleta kar ka damu Ko taki taso ni uwar ta ce.

 Cikin zumbure zumbure baki ta dur kusa cikin muryan takura ta ce" Anty kiyi hakuri Daga haka ta Mike ta yi sashin Uwar ta..

 Abubakar hakuri yake ta ba Anty ya ce" ta yi hakuri shibesan irin Mama ba.

Amma wataran zata gane gaskiya.

Anty ta ce" kar ka damu ɗana Allah yadada shiryamu dukan mu..

Da ameen suka amsa dukan su....

************************

Samad kwance yake kan kujerar falo 3str Idanun sa a lumshe zakai tunanin kallo yake, amma Sam ya yi zurfi a tunani har barci ya fara daukan sa nan take wajen ya yi barci.

Cikin barcin ya fara mafarkin wannan zanen tashi daya zana.

Tafiya yake cikin ciyayi inda wajen zagaye yake da fulawowi masu ban sha'awa gwanin burgewa.

Sai fadi yake ina kike ne hasken zuciya ta yau raina a ɓace yake, pls dan fito mana kidaina boye mun wannan kyawawan fuskar taki kullum cikin nikaf kike, amma bankasa kazo zanen naki a nikaf din ba.

 Dariyar yaji wanda ya sa shi juyowa yana kallon ta tana tahowa cikin wani irin tafiya mai daukar hankalin, tasha ado kamar Matar basarake stil dai wannan nikaf din na fuskar ta..

 Fuskar ta dauke da Murmushi ta ce........

 

5️3️

Ta ce yakai Amjad din zuciya madubin dubawa ta hasken idaniya ta.

Tabbas ni ta kace kuma uwar yayan ka haryanzu ba ka gamsu bane tana Murmushi mai kayyatar da masoyin ta.

 Samad cikin shakuwa yake nuna mata ta kalli sama kusan a tare suka Daga kai suna kallo.

Ya ce kinga yanda sararin samaniyar nan ke haskawa haka kaunar ki take karuwa acikin zuciya ta '' pls Abar sona ki gayamin gidan naku Ko ince inda zan same ki.

Kinmin Alkawari zaki tsaya mun a kan komai na rayuwa ta.

 Kwabe fuska ta yi cikin wasa ta ce kai Amjad dîna ka san dani kaje kayi aure.

 Kallon yake cikin kasa da murya ya ce nayi aure kisani ba ta da gurbi acikin zuciyata kece muradina ita Zabin iyayena ce ki fahimce ni.

 Kallon shi take kallo mai daukan hankali Kallo mai nutsar da zuciyar ma'abota soyayya.

 Wacce ka aura ba zan iya zaman kishi da ita ba.

 Yarinya mai kamala ma'abociya addini ce saurin katse ta ya yi da fadin kamarke haka take !!

 Ki faɗa min sunan ki da unguwar kinada ga cikin dalilin zuwa na kano.

Kince innazo zanga mahaifina nazo Amma shiru ne bangan shi ba..

 Kallon shi take tana nazarin kalaman sa.

 Ahankali take motsa labban ta ta ce kaine kake ganin bakaga mahaifin ka ba.

amma shi ya san da inda kake kuma yana da labarin ka.

Alkawari daya za ka min duk rintsi kar ka wulakan ta matar ka.

Koda kuwa bakason ta.

Ba na son ka aikata aikin ɗana sani InshAllah nakusa bude maka wannan kyawawan fuskar da kake ambata kana son gani..

 Tashi ta yi zata fice.

Da sauri Samad yasha gaban ta ya ce yau ba zamuyi yawo cikin jejin nan bane.

 Girgiza kai ta yi Alamun A'a.

Ganin tana ta zuba uban sauri yana ihu dan dakata mana.

 Faruk tsaye a kan sa rike da kugun sa hannun ya sa yasoma bugun kafar sa firgit ya farka Idanun sa ya sauka a kan Faruk..

 Faruk ya ce haba yaushe rabon da kayi mafarkin nan tun kan kayi aure.

Shi ke nan mun shiga uku mafarkin yadawo wlh Samad harda Aljanu ke damun ka..

Tashi Samad ya yi Daga kwance yana mika hade da hamma cikin muryan barci ya ce nifa ba na son sa'idanu ina ruwan ka da mafarkin inbanda gulma na cinka.

 Faruk rike da baki ya ce wallahi matarka saida ta toshe kunnen ta yanda kake ta ihu kana fadin ki tsaya karki tafi dan iska tashi kabita mana amma ba anan za ka baje mana kana kashe mana kunnuwa ba.....

Aminu ne yakaraso falon ya ce Faruk dafatan dai ya farka Ko caraf Idanun sa suka tsarke cikin juna shida Samad dake hararan sa yana tsaki.

Barin su ya yi cikin sauri yake hawa kan matakalan step direct dakin sa ya nufa...

 Faruk da Aminu kallon shi suke harya shige dakin.

 Faruk ya ce gaskiya mu nemo masa magani karya Aljana ta aure shi..

Aminu ya ce kuma haka ne amma dole ne mu nema mishi magani....

 Samad na shiga dakin kan gadon sa yafada yana mika hade da kara rufa lausasan bargon sa ajiki..

 Adu'oi kariya ya fara karantowa yana gama adu'a ya tofe jikin sa..

Kallon inda Rahama ke kwanciya ya yi ganin wayam babu ma kayan ta awajen Abun da ya faru dazun ne ya fara dawo masa cikin kan sa.

 Jikin sa a mace ya furta ya Salam wai me damun sa ne meyasa yaci zarafin wannan kanwar Rahama wata zuciyar ta ce yarinyar ce ba ta da hankali '' amma duk da haka yana ganin kamar ya yi kuskure hana Rahama rakiya cike da tunani barci ya yi awon gaba dashi...

 Itakuwa Rahama zaune kan dadduma tana waya da Asiya cikin Jin dadi ta ce kice gobe ina manyan baki.

Asiya ta ce kwarai kuwa gayamin me zaki dafa mun me dankaren dadi.

Rahama jujjuya Idanun ta ta yi wanda ya bayyana cikar Idanun ta ta ce uhmm ke ai nidake babu shamaki tsakanin mu duk abun da kike so zan dafa miki ko ki dafa da kan ki..

 Asiya ta ce ke dai Allah yakaimu Aminiyata.

Da ameen ta amsa mata.

Asiya ta ce Rahama wai meyasa bakya yawan hawa online ne Ko mijin naki beso ne ?

Rahama ta ce ni dai ce banda lokaci Asiya ga karatu ga aikin gida '' be zama lallai inba whsap lokaci na ba.

Amma in ina free Tabbas zan hau ayi hira..

Asiya ta ce haka ne kuma Allah ya samu adanshin ku.

 Ameen tabata amsa cikin muryan dake nuna kasala ta ce Asiya ni zan kwanta Daga haka suka yi Sallama.

Kokarin hayewa gado take ta ji ring din wayar ta hakan ya sa ta saurin dubawa ganin nombar Sheik ne ke yawo kan screen din wayar..

Cikin hanzari ta Daga.

Bakin dauke da sallama.

Sheik cikin Jin dadin Jin muryan ta ya ce diya ta dafatan dai kina lafiya.

Lafiya lau ta ba shi amsa.

Abby nayi miss dinka ina son inzo gida inkawo maku ziyara.

Murmushi ya yi ya ce Rahama ta basai kinzo ba kisha zaman ki ni gobe ma tafiya zanyi nida Amini na..

Rahama ta ce Abby tafiya kuma ina za ka je tafada cikin yanayin damuwa.

Sheik ya ce walimar aure ne a kasar Gabon kedai kiyi muna adua dalilin kiran naki kenan..

 Rahama numfashi ta fesar ta ce Allah ubangiji yakaiku lafiya yadawo daku lafiya..

Ameen summa Ameen suka amsa...

Daga haka sukaci gaba da hiran su yana kara mata haske kan abubuwan da suka shige mata duhu......

Kashe Gari.

Bayan ta idar da Sallah Asuba zaune takoma kan sallayar ta tana azkarai.

Alkur'an tadauko zata fara karatun ta ta ji karar buga kofa..

Hakan ya sa ta ajiye a kan dardumar ta tare da nufar kofar dakin a hankali ta murda handle din kofar.

Tare da budewa kallon shi take yana sanye cikin farar jallabiya da hula a kan sa.

Tsintar murya ta yi yana Fadin lokacin Sallah haryawuce na mance ban tashe ki ba.

 Cikin sanyi murya ta ce ai nayi sallah.

 Durkusawa kayi ta yi cikin ladabi ta ce ina kwana ya karfin jiki..

 Ciki ciki ya amsa mata da lafiya lau.

 Kokarin rufe dakin take ya zuba mata zararan Idanun sa masu kashe garkuwan jikin yan mata..

 Ya ce ina tsaye bakin kofar zaki rufe ?

 Yi hakuri na zata za ka wuce ne kara bude kofar ta yi tana nuna masa hanya ya shiga.

 Shiga dakin ya yi sai bin dakin da kallo yake har Idanun sa suka sauka kan wannan akwatunan lefen..

Kallon su yake yana ciza labban sa.

Cikin isa da izza ya ce wannan kayan kinfara Amfani dasu ne ?

Girgiza masa kai ta yi Alamun A'a.

 To karki kuskura kiyi Amfani da nasan kina jin dadin zaki saka kayan da wani kato yasiya to ni agida na ba a wannan tsarin ina fatan kin fahimce ni.

 Gyada masa kai tayi.

Ya ce wannan kayan zan adauke su Aba mabukata.

Su kuma gold din saida su zanyi inkai kudin gidan marayu.

Rau Rau take kallon sa a zuciyar sai fadi take to saime daman akwatunan basu dameni ba.

Kallon ta yake ya ce kina magana ne ?

Naga labban ki na motsawa...

 Girgiza kai ta yi Alamun A'a gaskiya ba abun da nace..

 Good ya furta kindaiji abun da nace lefe da kaina zan hado miki kwanan nan ki shirya anjima mu je super market ki duba kayyayakin da kike so..

Daga nan mu je kasuwa insaimiki atamfofi da lace material.

Kin san zamu ta yi Ko.

 Tafiya ta maimaita a fili.

Tana mai kallon sa..

Daga mata gira ya yi Alamun haka ne.

 Shiru ta yi tana tunanin to ina za su je ne wai Allah batason barin garin su...

Dawo da ita cikin tunanin ta ya yi ta hanyar fadi zamuje garin kwatano dake ki shirya nan da kwana uku masu zuwa..

Kallon reaction din yake yanda yaga zallan damuwa..

 Cikin yin kasa da murya ta ce Allah yakaimu.

 Ameen ya amsa mata cen ciki tare da baro dakin nata.

Itako Rahama tunani tashiga meyasa sai yau ze gayamata zasuyi tafiya ''

 Tafiyar mai ba ta kusa ba oh Allah yazanyi rayuwa garin da ba nawa ba ban taɓa fita kasar nan ba.

Iyaka ta Lagos.

Yau gashi anzo mun da bakon Al'amari.

 Daukar wayar ta ta yi tare da kiran anty ta sanar mata anty nuna mata ta yi bama tasan da zancen ba ta ce kwatano kuma zakije Rahma kiyi hakuri aure ne babu inda bekai ya mace amma InshAllah gobe da kaina zanzo karki wahalar da kanki kice zakizo gida nafison sai kin shekara Sannan kizo kinji Ko daughter.

 

Gyada kai ta yi cikin gamsuwa da bayanan anty sallama suka yi.

Inda Anty ta ajiye wayar Domin zuwa hadawa sheik break da dawuri za su tashi...

Bayan kowa ya karya agidan sheik ya tara s'u ya ce to Allah ya yi zan tafi dan Allah azauna lfy da juna.

Kallon Salma ya yi ya ce ke banson yawo inbada izinin mijin ki ba.

 Abubakar ya ce Abba kaide gayamata fa dan naga tafita wlh zan gyara ta sai dai in mijin nata ne yabata damar fita yakarashe zancen yana mai daukar jakar sheik ze fice waje.

Mama ta ce amma dai Abubakar bakada kunya kenan ni ka daukeni uwar banza kenan kana nufin zanbar Salma ta yi abun da taga dama ne kaine me hankali kaika iya magana Ko ?

Rike da baki Abubakar ke kallon uwar sa ya ce haba Mama wai ina ruwan ki da sha'anina da kannena ne naga dai bake kadai ba ce agidan nan akwai anty ita bataji zafi ba saike.

Mama ta ce taya za ai ta ji zafi tasan zafin haihuwar ya mace ne akasa ta tsinta.

 Sheik yaji haushin kalamin ta hakan ya sa ya fi ce Daga gidan.

Bin bayan shi Anty da Abdul jalil suka yi suka bar Mama da Salma.

 Kofar gida sheik ya ce to sa'adatu mun tafi Allah ya kaddara saduwar mu

Adu'a ta fara masa cikin sanyi murya ta ce Allah yakaika lafiya yadawo da kai lfy yatsare ka.

Ameen suka amsa tashi yayin da drever ya bude masa mota ya shiga...

Abubakar da Abdul jalil shiga motar suka yi suma.

Anty na tsaye tana kallon su har motar yabar unguwar tana ta Daga musu hannu.

Komawa Daga cikin gidan tayi.

Nan inda tabar mama da Salma nan ta same su mama na ganin ta takara sautin muryan ta.

Ta ce ke Salma ki abun da ranki yake so tun da baya nan duk inda kike so ki je wlh banga uban da ze hana ba kuma wata munafukar taje ta gayamasa zata fuskanci hukunci Daga gareni.

Salma shewa ta yi tana taba hannun ta ta ce yawwa mama shi ya sa nake sonki.

 Kada kai Anty ta yi tare da barin wajen cikin hanzarin ta...

Cen airport Aminin Sheik zaune yana jiran sa ganin karasowar ya sa ya nufi inda su sheik suke.

Babu ba ta lokaci aka fara kiran suna hakan ya sa sheik bin bayan Aminin sa cikin sauri.

Abdul jalil da Abubakar kallon su suke suna Daga musu hannu har suka shige jirgin....

Kasar Gabon.

Yau tun safe baba salihu yake ta faman hada kayan sa.

Ze bar kasar zuwa kasar Nigeria kano..

Duka wata daya zeyi yakoma Gabon..

Sai kiran su yake airport din suna kara jaddada masa jirgin kano besauka ba.

Data sauka za a sanar masa yazauna cikin shiri..

*************************

Masarautar gheuzo.

Mai Martaba zaune cikin shigar sa na sarakuna gefen sa waziri ne.

A damar sa Abban Marwan ne zaune dirshan cikin muryan roko ya ce Allah ya taimaki Sarki ataimaka ayiwa Marwan aure yaga wacce yake so..

Mai Martaba kallon sa yake cikin dattako ya ce Marwan ne za ai wa aure yaron da Ko aikin yi beda shi.

 Abban Marwan ya yi kasa da murya ya ce cikin tsoron mahaifin sa ya ce mai martaba aiyasamu aiki Samad compagny a kano tare suke aiki nan ze koma yaci gaba da aiki.

Mai martaba ya ce A'a ya je ya nemi aikin kansa ya yi inda gaske ne meyasa Abdul Samad be faɗa min ba.

Abban marwan ya ce kila ya Manta ne amma tabbas tare suke aikin da shi aka bude kamfanin.

Mai martaba ya ce na ji zanyi magana da Samad in ji kanun labarai.

Ba ƙaramin haushi Abban Marwan yaji ba yafadi magana amma ace masa sai anbincika cikin dan bacin rai ya ce nina tafi mai martaba saina jika.

Daga haka ya fi ce cikin Jin haushin su..

Mai martaba kallon waziri ya yi ya ce ina son afara tarawa gidan nan Saboda ayi shela domin sanarwa jama'ar masarautar nan gangarumin taron da za a hada na tarban Matar Samad 'sashin da zata zauna ita da mijin nata agyara musu a canza furniture komi na dakin.

Sannan lefen da masarautar ta hada akwatuna 24 su zama ready.

Zamuyi taron bikin namu na musamman nan da sati biyu InshAllah kafun nan ɓangaren mamy zata zauna.

 Waziri cikin bangirma ya ce ya shugaban Adalai InshAllah yanda kace haka za ai.

Jakadiya ce ta shigo cikin bangirma ta ce ya shugaba Mama karama tana neman ai mata iso wajen ka.

Allah ya taimakeka Sarki mai ran karfe.

Kallon ta yake.

Waziri ya yi caraf ya ce Jakadiya sarki yabada dama a shigo da ita.

Cikin rawar jiki tabar fadan.

Kalllo bayi da kunyagu take kowa na hidimar gaban sa sanye suke da uniforme din masarautar.

Ganin Jakadiya ya sa suka fara gaishe ta.

Tare da rusuna kai.

Hajiya Hassana cin karo suka yi ita da Jakadiya.

Kallon kallo suka Shiga yiwa juna.

Hassana da Murmushi ta gaida jakadiya ta amsa mata cikin sakin fuska tana tambayar kan ta Ko wannan ce bakuwar da Akace masarauta tayi..

Jakadiya ta ce dan Allah Ko kece bakuwar gimbiya Mamy.

Murmushi ta yi ta ce eh Nice, Sunana Hassana dafatan na sameku lafiya ina son abokiyar hira a masarautar nan...

Jakadiya ta ce ai indai wannan ne kinsamu zan ha daki da baiwar Samad Karima..

Hassana cikin Jin dadi ta ce dan Allah hadani da karima.

Jakadiya ta kalli cikin kunyagu dake kai kawo cikin masarautar ta ba da umarnin a rakata gun Karima tare da yin gaba dan isar wa Mama karama sakon mai martaba...

Kunyaga takai hassana har dakin Karima iske ta suka yi zaune Alamun wani muhimmin abu take ganin su ya sa ta zabura.

Tafara in na in na ciki yake ta ce ke Daga ina haka ai wannan bakuwar Mamy ce.

Hassana Murmushi ta yi ta ce eh nina ce akawoni.

Kuyanga ta ce jakadiya ta ce a kawo ta gun ki Daga haka tawuce.

Karima ta ce bismillah tare da ba ta wuri ta zauna.

Shiru ne ya ratsa dakin na wani lokaci.

Hassana ta ce Karima ance ke baiwar Samad ne.

Eh 'ni baiwar sa tabata amsa ataikaice tare da yin shiru na rashin sabo da ita..

 Murmushi ta yi tana kallon Karima tana nazartan yanayin ta.

Ta ce yawwa Karima ina son in zama abokiyar hirar Ki inbabu matsala.

Karima ta ce wannan me sauki ne.

Fita nake shirin yi dan Shugaba na yakusa dawowa kuma tare da Matar sa Amaryar sa..

 Hassana ta ce kina nufin daman Matar tasa ba ta taba zuwa masarautar nan bane..

Karima gyara zama ta yi tana fuskantar hassana.

Ta ce eh betaba kawo ta ba Asalima wannan matar da ya aura gidan nan babu wanda ya san ta sai Mamy da mai martaba da Abban Marwan..

 Hassana rike da baki ta ce Ko zaki gayamin ya haka ta ka sance kuwa da mamaki Yarima dan Sarki jikan ace ya yi aure ba tare da duniya ta ji ba..

Karima ta ce ai wannan karan duniya zata ji dan zuwan ta ba ƙaramin Girgiza masarautar nan zeyi ba....

Hassana ta ce kamar ya kenan ?

Karima ta ce zan miki bayani bakuwa ki bari anjima inna nutsu.

************************

Fulani ta shiga babban tashi hankali bokan jeji ya tabbatar mata kada su bari Rahama ta tako kafar ta cikin Masarautar nan yin haka ze wargaza komai sabanin da da ake so tazo...

Yanzu kuma ya lura zuwan ta ze ba ta komai ne ba gyara ba dan yarinyar tanada taurin kai.

**************************

 Maman Maryam cikin tashin hankali take magana da Abban Maryam dake fadi mata maza maza ta dakatar da Yarima tun da ita ce ta ce yakawo ta.

Maman maryam cikin zafin nama tadau wayar ta ta dannawa Samad kira...

Har wayar takusa tsinkewa ya Daga.

Cikin bangirma ya ce mommy na dafatan kina lafiya.

Lafiya lau ta ba shi amsa atakaice.

Ta ce Samad naam ya furta tare da gyara zama a kan kujerar 1str na falon sa yana sauraren ta.

Ina son kafasa zuwa da matar ka ?

Zumbur ya Mike tsaye ya ce banji dan........

 

5️4️

ZUMBUR YA MIKE TSAYE YA CE BANJI BA MOMMY KIKACE KADA INZO DA ITA.

MOMMY TA CE EH HAKA NAKE NUFI YARIMA KA FAHIMCE NI.

Maryam ce take kuka a kan son da take maka ta ce ba ka Daga wayar ta kwata kwata ina tsoron kazo da matar ka Jinin ta yahau takarashe zancen tana kukan karya.

 Samad dake sauraren ta lumshe Idanun sa ya yi ya ce mommy naam ta amsa cikin tsai gaita kukan ta.

Ina son kisan cewa na haramtawa kaina auren Maryam hakuri za ta yi Inde a kan Maryam ne ba zan iya fasa zuwa da ita ba.

MOMMY kiyi hakuri dan Allah nariga na gaya mata tare zamu tafi ba na son raini ya shiga tsakanina da ita dan tana ba ni respect daidai yanda Allah ya ce.

MOMMY ta hada rai kamar yana gaban ta '.

Ta ce yanzu Samad duk kukan nan da nake yi dan yata Ashe ba za ki ji tausayin ta ba

Samad sassaita muryan sa ya yi ya ce mommy ina me baki hakuri nariga nayi kudiri da niya kuma har mai Martaba ya san da wannan batun.

 Tun farko kece kika samun sha'awar zuwa da ita sabanin da.

Da ban kawo hakan araina ba..

MOMMY cikin Jin haushin sa ta ce Samad kaban mamaki yanzu in Mamy ce za ka ce mata ta yi hakuri.

Cikin gyara zaman sa ya ce kwarai kuwa har Mamy zan fadawa ta yi hakuri shari'a ba ta yarda kaci zarafin iyayen ka ba.

Yi musu biyayya abu ne mai kyau.

Amma Saboda ke kadai ba zan ba ta ran mutane dayawa ba.

Yi hakuri mommy Daga hk ya katse wayar ransa aba ce cikin Daga murya ya ce wai ita wannan matar meye matsalar ta ne.

Murmushi ya yi uhmm koda yake batasan kallon ta nake ba mu je zuwa.

Ita Ko maman maryam tsine masa ta rinƙa yi ta ce shege dan akuya ni ze gayawa zancen banza.

Abban Maryam ya ce Kinga matsalar yaron nan Ko ya zamuyi ne.

Maryam ce ta fito Daga dakin ta sanye take da riga da wando cotton sossai yakama jikin ta kowani sassa na jikin ta yana motsawa.

Cikin hanzari takaraso Idanun ta cike da kwalla ta ce Mommy ya amince ba zai zo da ita ba Ko ?

Kallon Maryam take ta ce inafa ya Amince dan iskan yaro.

Maryam ta ce haba mommy kidaina ce masa dan iska agabana inajin ciwon haka.

Abban maryam ya ce ke shasha ce duk wannan abun munayi dan ke ne.

Inkin ce kin fasa baki son sa.

Zamu cire hannu a kan lamarin sa '' kema kin san babu abun da matar sa ta tare muna Ko.

 MOMMY TA CE gayamata shasha kawai.

Maryam cikin kuka ta ce mommy ku yi hakuri wallahi ina son Samad duk abun da yadace ku yi.

Nabishi ta lala m'a yaki kulani nazo ta kar kashin kasa nan m'a abu be canza ba..

Abba zama ya yi kan kujera tare da zaunar da Maryam din.

Cikin muryan rarrashi ya ce ki barta tazo din InshAllah Ko babu boka babu mallam akwai tugun da zamu kulla mata wanda zai sa akore ta Daga masarautar gheuzo.

Cikin Jin dadi takwanta jikin Abba ta ce wai dagaske kake Abba na..

Kwarai kuwa Maryam dita.

Kisha kurumin ki yata sai inda karfi na yakare InshAllah zaki zama uwar yayan Samad.

Murmushi ta yi ta ce Abba nagode Allah yabaka sa'a.

Da Ameen mommy da Abba suka Amsa.

Mommy ta ce ina nan fa ina neman wani malami da akace mun yana aiki kamar yankan wuka.

Kawata keban labari InshAllah zanje cen mugani..

Abban Maryam ya ce wannan shi ne daidai in hagu taki a koma dama....

_________________________

Mamy cikin dakin ta take tana dan gyara kayan wankin da suka bushe da tafiso ta gyara su da kanta kafun tabayar ayi mata guga...

Shigowar khadija yajawo hankalin ta a kan kallon ta take cikin sakin fuska ta ce daughter har kin gama kallon ne ?

Cikin turo baki gaba ta ce bashi bane ba.

Mamy ta ce wa kenan ?

Sallamar Yarima Ahmad ne ya sa ta fadin ke da shi ne kuke fada Ko.

Yarima Ahmad zama ya yi kusa da Mamy tare da cire hulan kan sa ya ce wallahi Mamy yarinyar na n taraina ni dayawa kiringa ba ni daman ina dan casa ta.

Mamy rike da baki ta ce chabdi Amma ɗai wuyan ka ya yi kauri duka da nawa ka girme ta.

Wai ma tukunna ma laifin me ta yi maka ne..

Gyada kai khadija ta yi ta ce atoh shi ne abun da ya kamata kiji.

Tana hararan sa ta ka san idanu.

Shiko cikin isa ya hada rai Alamun babu wasa cikin maganar sa.

Ya ce Mamy koda tare muka zo duniya nida ita dole ne fa in gayamata mata gaskiya.

Wayar ta nadauka wlh ba ta da kawaye sai zallan Arna.

Whasap din ta nashiga bakiga irin fitsarrarun kawayen nata ba.

Cikin su harda wata wai ita salomon shegiyar kafura wanda rabin nonon ta awaje hoton data daura a kan Dp din ta..

Gasu nan dayawa basai na fada.

Tashi ya yi Daga zaune yana fuskan ta khadija cikin bacin rai ya ce wallahi Mamy wayar khadija ba zan ba ta ba sai ta yi hankali.

Boko hauka ne Ko wacce intazo da rashin kunyar ta sai ace ai yar Boko ce

Ni dai ba zan zuba idanu ba Allah ya gani hakkina na ne inkula da ita.

Samari m'a haka kowani kare yana da nombar ta.

Kai har m'a kawayen ta musulman bakiga fitsarrarun da take hulda dasu ba.

Ni dai banaso banaso banaso yakarashe zancen kamar ze take khadija da kafafun sa wanda haka ya sa aguje ta Haye gadon....

Mamy cikin sanyin jiki ta ce yi hakuri baba na kanada gaskiya kanwar kace kanada iko a kan ta '' fuskantar khadija cikin bacin rai ta ce baki isa indaura a kan hanya madaidaiciya ba wasu Arna da fitsarraun yaran musulmai susa ki kauce hanya ba..

Ki nutsu ki maida hankalin ki a kan karatun ki.

Jiki magayi ba zan kara hanashi ba inhar zebuge ki yana son ki bakowani dan uwa bane yake kula da sa'idanu a kan dan uwan sa ba.

Wasu inkinga sunyi magana sai ta baci.

Khadija kuka take Daga zaunen.

Ahmad da kukan ta yana kara hasala shi ya ce Mamy da kinbarni na dan gyara ta koda na minti daya ne kinga ai ta yi kukan da hujja Ko..

Mamy ta ce A'a kyaleta ai akwai gaba inhar ba ta gyara ba kayi mata yanda kaso.

Kara zama ya yi kusa da Mamy ya ce yawwa Mamy Samad yakusa zuwa naga ana ta shirye shirye har katuna aka buga na ganarumin taro da za ai na auren Samad.

Mamy Murmushi ta yi ta ce to nacewa Mai martaba basai an yi ba tun da amma ya ce Sam ba wannan zancen dole ne ya yi cewar shi jikan Fari abun soyuwar sa.

Ahmad ya ce oho kenan in mune ba zai mana wannan gatan ba.

Mamy ta ce ina zan sani kana iya zuwa fadar shi ka tambaye shi.

Ahmad Murmushi ya yi ya ce ayi Samad ne kadai yake shiga fadar sa ba tare da an yi masa iso ba.

Mune aka raina Ko tonima auren nan zan nema gaskiya dan kada mu rasa gatan da ake yiwa masu auren.

Jin muryan khadija ya yi Daga bayan sa cen karshen gado ta ce uhmm wace mata ce zata aure ka sai dai a rashin Sani.

Juyowa ya yi yana kallon ta ya ce idan na kawo ta ki hanata zama yar rainin wayau ai Saboda ke zan siye bulala na ajiye.

Tashi ya yi Jin wayar sa na ring ya ce Mamy zanje indawo Daga haka yafice cikin tafiyar sa mai daukan hankalin yan mata..

Yana fita Mamy ta fuskanci khadija ta ce kinga ba na son kina masa rashin kunya kin san dan yana ganina ne yake shanye wani abun ''badai kin rainasa ba ai ga uban gayyan nan zuwa zamu ga yanda zaku kare da shi kin san halin sa babu sauki sai wajen Allah..

Khadija ta ce Mamy InshAllah zan canza kodan Mala'ikan mutuwa nan Yaya Samad..

Murmushi Mamy ta yi ta ce Ko ke fa Dadina dake kina daukan shawara Allah Yayiwa Rayuwar ku Albarka da Ameen suka amsa a tare.

______________________________

Karima a Nutse ta yi aikin ta tagama tare da taimakon hassana sossai ta taya aiki suka yi komai tare..

Hassana ta ce woww gaskiya dakin shugaban ki yahadu sai kace ba a duniya ba Allah kasa ta Aljanna tafi wannan haduwa.

Ameen Karima ta amsa tana dariya ta ce ai Samad ne fa uban gidan nawa na daban ne antina..

Kusan âtare suka dawo sashin Karima tare da zama ka san dakin dirshan.

Karima ta ce antina zauna kan bakin gado mana.

Hassana ta ce A'a nima ka san tafimin dadi.

Kallon Karima take cikin zakuwa ta ce yawwa kin ce zakiban labarin Samad Ko yanzu tun da mun gama kidan ba ni labari mana tana me gyara zaman ta..

Karima ta ce kin san nama mance munyi haka dake bakida mantuwa.

Murmushi hassana ta yi ta ce taya zan manta nida na zaku in ji labarin nan.

Karima gyara zaman ta ta yi ta ce Samad da kike gani guguwa yake mai tada taro.

Hassana ta ce inajin ki Karima ba ni Insha mana..

Karima numfashi ta fesar ta ce uhmm ta ce wannan matar da Samad ya aura ai Daga gun daurin auren wani dan abokin mai martaba ne aka fasa da wancen yaron aka ba Samad.

Hassana ta ce kam buhu ya Samad din ya yi Ko ita yarinyar da Aka hadasu ba tare da sanin juna ba.

Karima ta ce ai yanzu bazamu San haka sai sunzo garin nan amma da dukan Alamu yana rike da ita dakyau dan na lura da hakan beda wulakanta ɗan Adam indai ba ya canza ba ne.

Hassana ta ce wai mahaifin nasa yana ina ne ?

Karima cikin tsoro wannan tambayar ta ce gaskiya nasan mahaifin sa baya garin nan..

Sai ta yi shiru tana wasa da yan yasunta.

Hassana ta ce kiban labari mana naga kinyi shiru Ko sirrine

Karima ta yi shiru cikin yin kasa da murya ta ce antina gaskiya ba za kiji wannan labarin abaki na ba..

Cikin razana hassana ke kallon ta ya ce kamar ya kenan ?

Karima cikin yin kasa da murya ta ce '' gaskiya na fada miki ba zan iya gayamiki komi a kan shugaban adalai ba wannan sirrine tsakanina da ubangidana.

Amma meyasa kike son sanin abun da be shafe ki ba ta jefo mata tambaya cikin tsareta da idanu..

Hassana Murmushi ta yi ta ce na de tambaya ne dan sainake ganin kamar mun zama daya tun da nima gani a cikin masarautar gheuzo tun da kin ce haka babu matsala.

Karima ta ce uhmm kedai bari Nina baduka nasani Ba a kan rashin zaman sa a masarautar ba wannan sai jakadiya ita ce tasan komai sai Mamy da mai martaba da Samad wallahi Ko Ahmad da khadija basu San komi ba dan an sirrin ta abunne duk da maganar ta fita waje har duniya ta dauka.

Amma Daga baya mai martaba ya dakatar da yaduwar wannan mummunar labarin.

Hassana cikin yin kasa da murya ta ce Karima wani mummunar labari ne wannan da baki son naji.

Karima tashi ta yi Daga tsaye tana kokarin shiga bandaki.

Hassana ta ce haba Karima muna magana kin tashi ?

Cikin muryan kuka Karima ta ce Alwala zanyi Daga hk tashige bandaki..

Hassana tashi ta yi jiki asanyaye ta yi ɓangaren Mamy tana Girgiza kan ta Alamun duk yanda ta dauki samun labari da sauki gashi yana neman gagarar ta....

_________________________

Kano

Rahama cikin rawar jiki ta ce ta rumgumi Asiya itama Asiya kara manne wa juna suka yi suna kukan Farin cikin haduwar su.

Cikin zumudi tasa ke tare da Jan ta suka iso falon kayan dake hannun Asiya take kallo tare da sa hannu ta karba ta ajiye saman kujera..

Zama suka yi cikin Jin dadi da Begen juna Asiya ta ce Rahama kinko ganki kuwa ?

Rahama ta ce kamar ya kenan na rame Ko tana kwabe fuska.

Murmushi Asiya ta yi tana gyara zaman ta a kan kujera ina fa Rama anan wajen ji yanda cika ciko fa kinyi kiba sossai fa kirjin ki yacika komai hip din ki kardai kina kashe bawan Allah nan Yarima da kayan kallo.

Rahama dariya ta yi sossai da rabon ta da haka tun tana gida..

Ta ce kinga Asiya har yanzu kina nan dai da halin ki Ko.

Kijimin zancen banza tafada cikin cool voice din ta

Asiya ta ce ina fa zancen banza anan wajen na tabbatar magana ta gaskiya ce..

Rahma kinyi kyau kinyi fresh aure fa ya Amsheki kawata tashi Daga zaunen ta yi tare da zuwa gaban Rahama ta manna mata kiss a goshi ta ce nayi miss din kamar in gudu dake da kewa.

Rahama ta ce ai basai kin fada ba kalaman ki da actin dinki sun nuna haka.

KADA in cika ki da surutu bara in shiga ciki inhada inkawo miki abun sha.

Asiya ta ce A'a ki barshi ba yanzu ba in ina bukata da kaina zanje indauka saikace bakuwa muda gidan mu tana mata hararan wasa.

Rahama ta ce au haka ne fa Sam namance tare da yin shiru suna fuskantar juna..

Shigowar Samad ne yajawo hankalin su a kan sa.

Da sauri Asiya ta sauke Idanun ta kasa dan ba ta fiya son kallon mazan mutane ba.

sanye yake cikin farar shadda dinki zamani sossai shigar ta yi masa kyau.

Karasowa falon ya yi yana kallon Asiya da mutuntaka tun lokacin daukan Amarrya ya yaba hankalin ta.

Inawuni ta furta ta ce yayin da take kallon le dan da Rahama ta ajiye kan kujerar.

Kamar ba zai amsa ba.

Saita ji yana fadin lafiya lau yau baki ne damu a gidan nan.

Asiya cikin Jin dadin kalaman sa ta ce eh mune tun da bakwa neman mu ai ni nazo muku ziyara..

Samad Murmushi ya yi tare da zama kan kujera 1str yana kallon Asiya ya ce haba aminiyar mata ta karki damu zamu zo miki ziyara dazaran mun dawo Daga kwatano yawwa inbabu damuwa ina gayyatar ki rakiyar mu zuwa cen garin kwatanon..

Rahama da Asiya kusan a tare suka kalli juna.

 Samad dake kallon reaction ɗinsu ya ce Asiya ki fada agidan naku dan Allah nasan dawuya su hana.

Rahama maganar zuci take ta ce wannan mutumin inyaga mutane sai ya koma na Allah kamar duka kenan Alhalin tsiya da wasali ne..

Asiya ta ce ni me zanje in yi daga za ka je da matar ka saina biku.

Yarima ya ce eh mana akwai wani taro da za ai acen ne kinga babu Kowa nata shi ya sa na zabe ki..

Asiya ta ce meze hana ku tafi da Salma.

Cikin dan ba ta rai Rahama ta ce haba Asiya kina nufin Salma ita ce nawa yanda nake kusanci dake banayi da Salma..

Samad ya ce Rahama ki tashi ki je kitchen ki dauko mata abun tabawa kinbar bakuwa hakanan.

Cikin sauri Rahama ta tashi dan cika umarni sa..

Ganin Rahama ta tafi.

Fuskantar Asiya ya yi cikin isar sa da kamalar sa ya ce Asiya ki taimaka ki je wannan yarinya ce haryanzu kinfita sanin Rayuwa InshAllah Daga an yi taron nan zansa a dawo dake koda mu ba mu tashi dawowaba

Asiya cikin sanyin murya ta ce zanfada agidan mu insun amince zakaji Amsa abakin Rahama..

Dawowar Rahama ne ya sa shi yin shiru yana kallon ta.

Ta kasar idanu yanda durkushen da ta yi wajen siyaya wa Asiya lemu a kofi hakan ya sa rigar ta sauka caraf Idanun sa a kan rabin boob din ta.

Tashi ya yi dan be iya juran kallon wannan sakacin nata.

Sai Anjima ya furta tare da fita compound din gidan.

Rahama zama ta yi tana kokarin bude ledan da Asiya tazo dashi.

Yayin da Asiya Kofin lemu na hannun ta a hankali take sha.

Samad sai. Safa da marwa yake yi a compound din gidan yana tunanin wannan abun daya gani.

*******************...

Gabon

Baba Salihu a filin airpot din shida dattijo suna zaman jiran waɗanda jirgi ya sauke su fita Sannan afara kiran sunayen waɗanda za a diba zuwa kanon..

Kallon jama'ar dake sauka Daga cikin jirgin yake yana Murmushi ya ce ka ga kullum mutane cikin yawan tafiye tafiye suke suzo suyi kasuwanci su koma yana murmushi.

Dattijo ya ce haka ne ya shugaba na anjima za su sake dawowa daukan wasu.

Baba Salihu ze bude baki ya yi magana...

Tashi ya yi Daga zaune da yake yayin da yaga sheik yana kusanto inda yake shida Aminin sa

Cikin........

 

5️5️

Cikin sauri yake kokarin barin wajen har yana neman tuntube Jin andafa bayan shi ya sashi tsayawa cak ba tare da ya waigowa.

Sheik ya ce bawan Allah lafiya kuwa kake buga uban saurin nan harkana tuntube kamanni naga kana mun da wani bawan Allah.

Dan uwa na dan juyo mana.

Aminin sheik ya ce nima dai kamanni naga ya yi yawa ne shi ya sa nace mukaraso wajen mu tabbatar da Idanun mu ne ke mana gizo koko dai shi dinne.

Baba Salihu waigowa ya yi Idanun sa cike da kwalla.

Sheik da Aminin sa kallon sa suke sake da baki.

Girgiza kai sheik ya yi ya ce Ah Ah wannan ba baba salihu bane me ze kawo shi Gabon shida yatafi gun iyalin nasa ba mu San abun da ya hana shi dawowa ba.

Aminin sheik ya ce nima dai gaskiya ina tantama dan wannan Attajiri ne babban hamshaki.

Baba Salihu kuma mai nema ne kamar mu.

Baba Salihu tun da suke ta magana kallon su yake Idanun sa cike da hawaye.

Sheik ya ce yi hakuri bawan Allah mun ba ta maka rai Ko wlh munyi zaton dan uwan mune.

Har sunsa kai za su wuce.

Sheik yaji ankira ainihin sunan sa

Abdurrazak Abdurrazak Abdurrazak.

Waigowa ya yi yaga wannan dai mutumin ne da suke kama da baba Salihu.

Sheik ya ce Salihu Salihu kaine ?

Aguje ya je ya rungume shi yana kuka sossai iya karfin sa.

Sheik ya ce Salihu kai dinne dana sani koko kama ce.

Baba Salihu ya ce Sheik nine mai gadin gidan ka.

Mutuwar tsaye sheik ya yi kamar andauke wuta andawo dashi.

Aminin sheik Malam Isa ya ce Salihu a Gabon bakin sa na rawa..

Sheik dasai a yanzu yadawo hayyacin sa cikin bacin rai yakama hannun Aminin sa ya jashi cikin sauri suke tafiya tare da nufar motocin da za su dauke su...

Baba Salihu bin bayan su ya yi cikin Azama shida dattijo.

Koda suka iso wajen nasu ganin Sheik suka yi anbude masa mota ze shiga.

Cikin masu bude motar ya Kalli baba Salihu ya ce.

Ya shugaban Adalai kaine nan da kanka ba za ka bari wani ya rakoka ba.

Sheik Sake da baki yake maimai ta kalmar shugaban Adalai.

Baba Salihu cikin yanayin damuwa yake kallon me masa magana ya ce.

Inka Kaisu ma sauki kazo har gida ka dauke ni ka kaini gun su..

Sheik zeyi magana ya ce A'a be yarda ba Aminin sa ya rufe masa baki da tafukan hannayen sa.

Baba salihu na tsaye motar tabar filin aiport din dasu Sheik.

Dattijo rike da kugun sa ya ce ya shugaba na.

Wannan ai shahararren Malamin Addinin nan ne muna kallon wa'azizunka sa

ka san shi kenan da dukan Alamu..

Baba Salihu kallon shi yake da rinannun Idanun sa da suka kada zuwa ja.

Ya ce eh nasan shi mana shi ne wanda nake ba ka labarin sa nazauna gidan sa a kano.

Dattijo ya ce gaskiya shugaba na dole ne yadau zafi duk da besan dalilin ka ba..

Baba Salihu ya ce haka ne kana tunanin ze sauko ta ruwan sanyi ne.

Dattijo ya ce kwarai kuwa inka hadashi da Allah da manzon sa ze saurare ka.

Murmushi Baba Salihu ya yi ya ce nagode da shawara zo mu koma gida tafiya tasha ruwa..

Kai tsaye wajen motar sa suka nufa.

Suna shiga sukabar airport din..

****************************

Asiya kama hannun Rahama ta yi suka je dakin nata rike da ledan da tazo dashi.

Rahama cikin Jin dadi ta ce kinje super market ne kinsiyo mun biscuit ne kin san ina son cin sa Ko.

Uhmm wanda ake ajewa a gidan nan Sam bayamin dadi.

Asiya kallon ta take tana Murmushi ta ce Rahama kenan kedai haryanzu kinki ki girma Ko.

Wai intambayeki mana.

Rahma ta ce inajin ki

In kika kuskura kikamin tambayar banza zaki sani ne..ehee tana turo baki gaba.

Murmushi Asiya ta yi ta ce na ji dai koma meye ai sai ki tsaya ki saurara Ko ?

Gyara zaman ta Rahama ta yi tare da baza kunnuwa dan Jin abun da zata ce..

.

Asiya ta ce Rahama nalura kamar babu shakuwa keda mijin nan naki kallo daya nayi muku na fahimci hakan banson ki boye mun komai takarashe zancen tare da hada rai tamau babu Alamun wasa..

Rahama ganin Asiya ta daure ya sa ta daukan maganar ta serious.

Cikin yin kasa da murya taba Asiya labarin komai tun zuwan ta gidan.

Asiye zare Idanun waje ta yi da Rahma takai karshen labarin.

Ta ce yanzu kina nufin tun zuwan ki gidan nan babu abun da ya taba shiga tsakanin ku keda shi.

Rahama shiru ta yi tarasa Amsar da zata bata..

Asiya tashi Daga zaune ta yi tana ta buga hannayen ta..

Ta ce uhmm Rahama kinban mamaki fa da karatun da sanin ki da komai amma kike take sani..

Rahma cikin kunan rai ta ce Asiya eh da karatuna nasan abun da nake.

Taya zeringa Fadin auren Sadaka ce kinkosan yanda kalamin nan yake min ciwo acikin zuciyata kuwa banda wanda zan iya gayama abun da ke ba ta mun rai saike Asiya...

Da wannan kalamin nasa na gwammace yabugeni zefimun sauki.

Sannan niban hanashi kaina ba kin san banda karfin sa duk da ba ni so.

Shima kamar yana zama dani dan dole ne.

Asiya Ki fahimceni cewa ya yi auren biyayya ne banzo gidan nan ba dan in kuntata masa ba.

Nadauki aure na da shi Kaddara ce.

Asiya cikin Jin tausayin Rahama ta zauna gefen ta rike da hannayen su cikin juna.

Ta ce Rahama kema kin san Allah ya yi miki canji mafi Alkhairi shi ne ya mallaka miki Yarima.

Wallahi kundace kedashi duk wanda ya ganku.

Ki saki ranki ga kayan gyaran jiki nan Anty ta hado miki dan batasan cewa har yanzu a leda kike ba ba a bare ba.

Nasan dasai ta kusa Zane matar Samad.

Rahama Murmushi ta yi tana fiddo kayan dake cikin ledan.

Wani roban Zuman yaji hadi sossai ta fiddo ta ce wannan Zuma ce.

Asiya ta ce kisha kiji mana abu yana hannun ki amma kina tambaya ta..

Bude murfin roban Rahama ta yi tare da da dan lakutowa da hannun takai bakin ta.

Lumshe Idanun ta ta yi ta ce Asiya wannan Zuman badai dadi ba har wasu kwa kwa nake ji a ciki...

Asiya ta ce uhmm nasan ke uwar kwadayi ce saiki shanye tas yanzu amma fa kibi a hankali kisha Rabi yanzu.

Sauran kibarshi sai munje kwatano kinsha.

Rahama ta ce haba wlh ni duka zan shanye ba zan iya bari sai munje cen ba.

Dariya Asiya ta yi sossai harda rike ciki ta ce ina ruwana ki shanye mana Ai Samad yana gari kika matsu ze rage zafi cikin ruwan Sanyi ba tare da yasha wahala ba...

Hararan wasa Rahama tabita da shi kinga ba dakin mu daya ba nidashi ba.

Yana tashi ina tawa.

Kidaina mun mugun baki banaso.

Kafa roban Zuman ta yi a bakin ta saida ta shanye shi tass ajiye roban.

Asiya rike da baki ta ce wlh zaki gane bakida wayau au wannan ba simple din Zuma ba ce kema kin sani Ko amma Saboda tsabar kwadayi kin shanye jiki magayi ina ruwana..

Rahama cikin turo baki ta ce nafa gayamiki ba dakin mu daya ba.

Kuma ba zaimun komai ba banson kina mun mugun baki fa..

Asiya ta ce Tom nayi shiru yanzu dai kinga sauran kayan harda su gumba garurruka duk yanda zaki sha su ga sunan anty ta rubuta a papper.

Rahama ta ce uhmm nifa duk ba zan sha ba Zuman ce kadai ta mun dadi.

Asiya ta ce wlh inbaki sha ba a gabana ba saina gayawa Anty wlh...

Asiya da kanta tadauko madarar peak a frij din kitchen tazo ta hada mata magunguna tabata ta shanye.

Sai yamutsa fuska take kamar za ta yi Amai.

Asiya ta ce kardai ki kuskura kiyi Amai kamar yanda kikai kafun bikin ki dan anbaki magani saiki amayo

 Rahama ta ce ni dai wlh magungunan nan sun cika min cikina haka zan kwanta banci komai ba..

Nan da suka je kitchen tare da da taimakon Asiya ta yi girki.

Tuwon semovita da miyan ganye wai wannan girkin ba ƙaramin daukan ido yake ba abaki ma ba a cewa komai.

Asiya ce ta bude miyan dayaji kifi manya manya ta ce uhmm Rahama ni dai girki zaki koyamin dan anan wajen ban kamo kafar ki ba.

Dibar miyan ta yi takai bakin ta tare da lumshe Idanun ta wani dadi ne ya ratsata sossai.

Asiya ta ce Rahama in babu damuwa ki koyawa fans din KYAUTA Daga Allah yanda kika hada miyar nan dan wlh tahadu iya haduwa sai ma Yarima yaci ze baki note..

Rahama ta yi Murmushi ta ce wai fans din KYAUTA Daga Allah insunce suna so zan fada musu meye aciki ai karuwa ce..

Kusan a tare suka fito da manyan Wamer flask cike da abinci suka jera komai a dîner table.

Faruk Da Aminu cikin sauri suke saukowa Daga kan matakalan step din.

Aminu ya ce Ah ashe manyan baki gare mu.

Asiya ta murmusa tana kallon su cike da ladabi ta gaishe su.

Suka Amsa cikin sakin fuska.

Faruk ya ce Madam Samad wai ina Yarima yake ne ?

Rahama ta ce uhmm yadai fita amma ban san inda ya yi ba...

Takun shigowar sa ya sa ta yin shiru karasowa falon ya yi ya ce daman ina zaki San inda naje yana kallon ta kauda kansa ya yi Daga kallon ta yadawo kallon Aminu da Faruk ya ce sai yanzu kuka fito nasan yanzu ma yunwa ce ta sauko daku.

Faruk ya ce wlh kuwa kamar ka sani amma naga ga abinci nan madam ta girka mana..

Dîner table suka nufa Faruk da Aminu.

Shiko Samad kallon su yake ganin Rahama da Asiya awajen ya kasa motsawa Daga inda yake..

Asiya daukar abincin nasu suka yi suka yi dakin Rahama dan su basu waje.

Suna barin wajen Samad ya isa kusa da su Faruk ya ce yan iska kawai waya hanaku ku yi aure..

Faruk dayanzu yakai loma daya a bakin sa ya ce wai wai kaji wani gardi da dadin abinci nan kuwa.

Aminu ya ce tun da nake ban taɓa cin abinci me dadin wannan ba.

Samad dake kallon su ya ce uhmm ku yi aure mana gwaurayen banza kawai.

Faruk ya ce ai banbancin mu da kai daya ne.

Samad ya ce bangane banbancin mu daya bane meye nufin ka.

Zama ya yi kan kujerar yana kokarin zuba abincin a plate..

Faruk ya ce eh mana Saboda kai da sunan kanada aure ne amma ba ka san Dadin auren ba..

Aminu ya ce tabe tabe.

Faruk ya yi Murmushi shima ya ce tabe tabe mana na gasken ma..

.

Samad ya ce ai duk wani dan iska acikin ku kar nake kallon sa.

Nasan dani kuke tabe tabe meye ma'anar haka ?

Aminu ya ce zato zunubi ne koda ya ka sance gaskiya ne.

Kawai dai ka tsargu ne tokai kana tabe taben ne.

Mun ce maka film ne muka kalla kaki yarda Ko in kunna maka ne..

Samad ya ce dan iska kunna mana mugani.

Murmushi Aminu ya yi ya ce to bara ingama cin Abincin kar ka bari na kware.

Sossai suka ci Abinci yayinda Samad yanaci yana lumshe idanu ji ya yi kamar taita girka masa irin wannan abincin yanacin sa dan yanason irin abinci haka..

Kusan Magrib Asiya tasauko da niyar tafiya gida.

Sossai Rahama tashiga damuwa a kan tafiyar ta dan wunin da suka yi ji ta yi kamar su dawwama tare.

Aminu da Faruk zaune suna kallon Ball.

Asiya ta ce to ni zan tafi ina angon Rahma yake ne ?

Daga can zaunen kan dîner table yana chat yadago kai yana kallon ta.

Ya ce kice ina Abdul Samad yake aini bankai matsayin ango ba..

Daga Asiya har su Faruk darawa suka yi.

Ajiye wayar ya yi ya iso wajen Asiya ya ce ki bari Farruk yakaiki har gida..

Aminu ya ce kwarai kuwa bari mukai ki kinga mun samu mu nuna miki wani abu da muke nema a unguwar ku.

Asiya ta ce babu matsala Muje.

Gaba suka yi ita da Rahama.

Samad ganin Rahama na kokarin fita Daga Falon ya yi saurin fadin.

Ashe banhanaki wuce iyakar falon nan ba inkikai baki ba indai ba ni ne nace ba

Cak ta tsaya cikin Jin zafin haka tarasa dalilin sa.

Asiya ta juyo tana kallon Rahama ta ce ki koma ai yana da gaskiya babu hijab zaki fito haraban gidan..

Murmushi Samad ya yi dan ya lura Asiya akwai ganuwa a fili ya ce.

Asiya kiyi hakuri fa karki ga laifina..

Asiya ta ce ba komai InshAllah zakaji amsa ta wajen Rahama..

Daga haka tasakai tafita '' Faruk da Aminu suka bi bayan ta dan kaita gidan su..

Rahama dawowa falon tayi.

Jin yanayin ta yasoma canzawa saman kujera ta zauna 3str idanunta a lumshe wani bakon yanayine yake ziyartan ta.

Mutsu Mutsu tasoma Daga kwance wanda yajawo hankalin Samad dake kokarin hawa kan matakalan step din..

Dawowa ya yi a falon yana tsaye a kan ta kallon ta yake yanda Idanun ta arufe suke amma sai nishi take fitarwa mai fidda sauti.

Hannu ya sa ya taba jikin ta yaji jikin nata harya ɗau zafi sossai.

Subuhannalah ya furta yana kokarin.......

Post a Comment

0 Comments