Ticker

6/recent/ticker-posts

Ƙanwata Na Ikilima Adam (Kashi na 1)

Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Allah kasa yanda na fara lafiya in kare shi lafiya. Wannan labarin ya faru da gaske dan kusan Book dina da nake yi true life ne sai dai in yi masa kwaskwarima dan abun ya fi ba da citta.

Ku biyo ni ku sha labari.

Ku daure ku yi comment dan in ji ra'ayoyin ku a kan Littafin nan......

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishaɗantarwa tare da faɗakarwa da jama'a bisa harshen hausa}_

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

⚜️©J.A.W📚🖌️

Marubuciyar

* Amince Da Ni
* KAI KA JA WA KANKA

Yanzu kuma gani ɗauke da

ƘANWATA

Paid Book ne

Vip 300
Special 500

Acct No. 3115484026, First Bank, ko kuma Kati MTN (Ba na son VTU)

Idan kin biya ta bank kina iya turo shaidar biyar ki ta wannan 09069080725

kanwata

🌟🌟 ƘANWATA Na Ikilima Adam [Kashi na 1]🌟🌟

Book 0️1️

Tafiya suke a ƙasa Rahama sai zuba Uban sauri take batason ta yi latti.. Waigo war da za ta yi ta hangon ƙanwar ta Salma cen baya tai, tana fira da wani Atiku sai washe baki ta ce cikin jin haushin haka.

Rahama ta ɗaga murya da karfi yanda zata iya jiyo ta ta ce salmaaaaa!

Wacce Aka Kira da Salma ɓata rai ta yi ta ce na'am.

Kin san lecture ɗin mallam Hamza garemu amma kika tsaya surutu tana magana da ɗan ɓacin rai.

Salma turo baki tai Ta ce" kina iya tafiya Kona hanaki ne ehee.

Aikuwa cigaba da tafiyarta Rahama tai ɗan taso ta makara shiga aji.

Mallam Hamza yashigo aji ɗukan dalibai suka tashi dan gaishe shi.

Hannun yai musu da su zauna Kowa ya nemi wuri yazauna tsit kake jin ajin.

Gyaran murya Mallam yai Ya ce" Wa zai gayamin inda muka tsaya wancen satin?

Kowa ya yi tsit shiru kake ji.

Rahama ce ta daga hannu.

Bismillah Ya ce mata...

Cikin muryan ta ɗa nutsuwarta ta fara faɗin awancen satin mun tsaya ne a kan inda kake mana bayanan amfanin ruwa a jikin ɗan Adam...

Mallam Hamza kallon ta yake yana nazarin tarin ilimin Yarinyar Ya ce Ku tafa mata class kowa yadauki taɓi..

Kina iya zama Rahama.

Cikin dan ɓacin rai Ya ce" yanzu tun wancen satin mukai lecture kan amfanin ruwa jikin ɗan Adam, amma wai babu Wanda yarike sai mutum daya.

Meyasa sau dayawa bakwa daukan Abun da ze amfane Ku da muhimmanci?

 Gaban allo ya koma ya soma rubutu kamar Haka

*Amfanin ruwa jikin ɗan Adam ''*

*Ruwa yana taimakawa wajen gudanar da jinin jikin mu*

Da kuma....

Sallamar Salma ne ya dakatar da shi da rubutun da yake yi.. Kallon ta yake yana kallon agogon hannun sa.

Keee daga ina Haka? Ya nuna ta yatsa da hannu wannan ba Yayar ki ba ce? Ya akai ta riga ki zuwa?

Dukar da kanta ƙasa ta yi tagaza magana.

Kowa class sai kallon su suke suna kwabe baki.

Ita ko Salma ganin idanun class kowa akanta turo baki gaba tai ta ce" Mallam ban san lokaci yawuce ba.

Get out.... Ya ce mata ransa aba ce.

Cikin bacin rai ta kalli Malam. Ta ce" Mallam ka kosan waye babana agarin nan kuwa kake korata'?

Rahama ta Mike cikin fushi Ta ce" haba Salma ba za ki bashi hakuri ba 'bayan kinyi laifi! Saiki tsaya zakimasa rashin kunya.!!

Harara ta watsawa Rahama Ta ce" oho dai ai ban kasa dake ba.

Kai kuma Mallam kakiyaye haɗuwa ta da kai!

Tsakiiii ta ja ta fice cikin harabar makarantar ta nemi waje ta zauna ta tana ta gunani Wallahi Mallam Hamza ze san ya ta boni.

Mallam Hamza rike da baki yake mamakin kalamin Salma

Maida hankalin sa ya yi a kan rubutun da yake yi...

Sai kusan karfe 11am yagama musu lecture

Mallam Hamza nafita ajin.

Salma ta shigo ajin, tazauna tana ta cika tana batsewa Wallahi duk wani dan iska a ajin nan na ƙara Ganin Yana min kallon raini Wallahi zai san yata boni, munafukai kawai... Rahama harta buɗe baki za ta yi magana saita fasa, sai kusan karfe ɗaya suka tashi.

Tafiya suke ahanya suna hiran ƙawar su da ba ta da lafiya za su je dubo ta.

Wani matashin saurayi kyakyawa saurayi ajin farko yanata cewa Yan mata ji mana.

Sai suka waigo 'Salma sai fari da ido take yi irin an saida ita ɗin nan.

Ya ƙaraso gaban su. Rahama kanta a duke Ta ce "pls in kana son magana da Ƙanwata ba a titi za ka tsaida ita ba.

Salma turo baki tai gaba irin yau ga rainin wayo.

Ko ina ruwanta da in an tsaida ita din.

Saurayin Ya ce" ni dai 'sunana

Adamsy dan gidan ambassado ɗin Libya ɗazun nazo garin Kano.

Kuma Wallahi na ji kin kwanta min a rai ya nuna Rahama da yatsaya.

Ɗago Kai ta yi ta kalle shi Ta ce" ni kuma ba Ƙanwata ka tsayar ba?.

No kece ɗin nabiyo ba ita ba.

Ran Salma yakai kololuwa wajen baci.

A fusace tai gaba tana ta buga Uban sauri 'har tuntube take yi a hanya 'saida ta taka Kaya 'amma da yake ranta aba ce yake bama ta damu ba.

Rahama Ta ce" ka ga kar ka haɗa ni da Ƙanwata 'in kana son Yarinya gidan iyayen ta za ka je kanemi izini daga Haka ta wuce.

Yan Mata! Yan Mata!!..

Ya sake biyo ta 'baki faɗa min sunanki ba?

Kallon sa, tai takauda kanta gefe cikin gajiya da bin bayanta da yake yi.

Rahma sunana Ta ce" masa a taƙaice tare da cigaba da tafiyar ta cike da nutsuwa.

Kallon ta yake 'Ya ce wow amma wannan Yarinyar sai kace ita ta yi kanta komai Nata na musamman ne, Allah ya sa ta soni daman kyakyawar Mace aji gareta. Cije labbansa yai cikin son ganin yai magana da Rahama Wani dan yaron Unguwa ya gani shima daga makaranta yake na sauri ya je gida.. Tsayar dashi yai Ya ce zo nan abokina

Yaron tsayawa yai yatsareshi da idanu.

Dan Allah wacce Yarinyar c'en datai nisa a tafiya yanuna masa ita da yatsaya koka san Gidan su? Ta ce min sunan ta Rahama.

Yaron yai murmushi au Rahama kake nufi ?

Eh ita ya ba shi amsa yana kallon sa.

Yar gidan Sheik Abdulrrazak hizqeel makarfi ce Wannan shahararren Malamin addinin 'nan Wanda yadawo nan Kano dazama '.

Kai haba Kana nufin Sheik Abdulrrazak hizqeel makarfi da na sani ina sauraran wa'azin sa.

Gayamin layin gidan nasa.

Layi na uku ta hannu hagu za ka ga wani gida me babban Gate kaf cikin Unguwar sune gidan su 'yafita daban.

Nagode sossai ya sunanka.

Sunana Aliya Haidar

To Aliyu godiya nake

Zaro dubu daya daga cikin aljihun wandon sa.

Ya Miƙa masa.

Karba yai'yana masa godiya cike da jin daɗin kyautar mutumin.

............

Salma ta shigo gida kamar anjefota daga sama sai haki take yi dan tasha gudu ahanya

Mama ! mama !!mama!!!

Take Kira

Mama Ta ce"

Lafiya Salma kike kwadamin Kira meya farune ?

Ta tsareta da idanu

Ina Rahma take ne kika dawo ke kadai.

Cikin bakin cikin da ke cinta ta ce Wallahi Mama wani Saurayi ne yajata a mota suka tafi.

Abban su dake zaune yake cin tuwo ya Mike cikin zazzare idanu ya ce mo....me?

Ta ce mota tana turo baki waje.

Innalilahi wa'inna ilai rajun Mama tashiga maimaita wa.

Nan take ta ji ji......

Book 0️2️

Nan take ta yi Allah ya wadai da halin Rahama wallahi Yarinyar nan zata san da Wanda take yi tana yatsine fuska.

Rahama baiwar Allah

 sai Addu'a take jerowa kada Allah ya sa wannan Matashin ya biyo bayan ta.

Tana tafiya tana waige waige ganin ya daina Bin ta a baya

 ya sa Kai tsaye tasha kwanar gidan nasu.

Daidai kofar shiga gidan nasu.

Addu'ar shiga Gida ta fara karantowa acikin zuciyar ta, hannun tasa cike da nutsuwar ta ta buɗe Gate ɗin gidan su.

Mai gadin Gidan nasu ta hango yanashan fura..

Ina wuni Baba Salihu Ta ce "masa tare da risinawa daban girma....

Mai gadi ya amsa da lafiya kalau cikin sakin fuska dason zancen Rahama, dan shi komai nata burgeshi yake harsai yakejin dashi wani' ne ɗa Wallahi sai ya aura wa dan sa.

 Rahamatullah har andawo?

Eh Baba ka ganni duk a gajiye nake

Sannu da hutawa Baba.

Yawwa y'ar Albarka yabata amsa.

Cigaba da tafiyar ta ta yi

Baba salihu murmushi yaketa jerowa shi kaɗai Yana girgiza Kai ya ce" oh Allah me iko me fidda rayayye cikin matacce...

Tofah me Baba Salihu yake nufi da wannan zancen nasa.

Ƙarasowa cikin Gida ta yi 'sallama dauke abakin ta ta shigo ɗakin Ganin babu Wanda ya amsa mata Sallamar ta

Ta ƙarasa shigowa dakin.

Iske Mama da Abban su ta yi kowa A tsaye alamun tarin damuwa kwance a kan fuskar su....

Abba ya ƙaraso gaban ta ɗauketa da Mari yai Wanda ya sa ta ji kunnuwan ta suna neman daukewa, ji tai luuuuu cen ƙasar kunnen ta wani zugi ya shige ta

 kara ta saki Wanda ya sa Baba Salihu dake kokarin shiga wanka yajuyo a razane, ya sallam ya furta Wannan kamar muryar Rahma nake jiyowa!.

Rahama

Batai aune ba!

Mama tafara buga mata muciya duk inda ta samu a jikinta bugawa take yi tana kuka, wallahi Rahama ba zan yafe miki ba...

Shegiya ni Zaki tonawa asiri a garin nan kakaf babu Wanda besan matsayin '

Mahaifin ki ba

shike fada aji..

Cigaba da bugun Rahama tai tana jifan ta da mugayen kalamai....'

Shiko Abba saboda tsabar takaici yama rasa ta inda zai fara magana.

Rahama ya kira sunanta da kakkausar murya...

Bata iya dago Kai ta kalle shi ba '.

Ta amsa saman makoshin ta.

Na'am...

Wani dan iskane ya dauke ki a mota kuma ina kuka je?

Fuskar shi tamau babu Wasa.

Cikin sheshekar kuka daya kwace mata Ta ce" Wallahi Abba ban shiga motar kowa ba.

Ka tambayi Salma.

Salma dake zaune tanajin dadin Abun da akewa y'ar Uwar ta.

Ta buga kirji ni kuma? sanda zaki shiga ban ce kada kibishi ba kika ƙi sauraro na, sai Yan zu Zaki wani Fake dani.

Abba da yakai kololuwa wajen ɓacin rai Ya ce" Rahama duk cikin Ya'ya na ina yabon ki, Kinbi daban cikin su.

Rana tsaka kike son kiyi watsi da yardar da muka baki.

Wane ne shi da yadauke ki a mota gayamin tun ranki bai gama baci ba!.

Tsoro da fargaba ya cika zuciyar ta Allah ya sani tana tsoron duka shi ya sa take kiyaye duk Abun da ze ja mata hakan.

Wata sheda gareta dazasu yarda cewan sharri akai mata?.

Sabon kuka ya kwace mata ta ce" Wallahi banga Mota ya biyo ni ba wani saurayine ya biyo mu 'nida Salma nan takwashi labarin yanda akai tun Farko zuwa Karshen labarin. Narantse da girman zatin Allah in karya nake Abba Allah kada ya ba ni Abun da nake buƙata Duniya da Lahira shine aljanna.

Sannan Allah ya saka muku, tun da kun ba ni tarbiya Abba tana sheshekar kuka Idanun ta Sun kada sunyi jajir....

Zama Abba Ya yi a kan Kujera dirshan Kara gudun AC ya cewa Mama ta yi...

 dan wata zufa ce take sassafo masa cikin Abun da befi minti daya ba 'ya soma sauke ajiyar zuciya.

Sassauta nutsuwar sa Ya yi yana dafe kansa shi dake sarawa, muryan sa dake nuna raunin sa...' Ya bude labbansa ahankali ya furta kowa ya nemi waje yazauna.

Babu musu duk suka zazzauna Kowannen su, zuciyarsa cike da tsoron Meze faru.

Kallon Mama yake cikin bacin Rai Ya ce" Aishatu kin gurbata tarbiyyan da na yi wa Yata Salma harta Kai da zata iya yiwa yar uwar ta.

Ta jini daya kazafi 'mafi munin zance.....

Caraf Mama ta karbi zancen ai wannan zancen Banza ne taya za ka goyi bayan karya Ka san karya ce meyasa ka mareta nifa wallahi infa kacika matsamin sai inkoma gidan Uba na.

Koda yake ma Alfarmata kakeci aka ba ka wannan Gidan da ka keciki ehee ta ja tsukii.mtssss

Aikin banza kiba ga kunne, Salma taso kinji soyake ya dawo da haushin Abun kunyar da Rahama ke shirin aikata wa akanki....

Salma tashi ta yi tana yatsine fuska sai yauƙi take yi kadan ya rage ba ta fada kan Abba ba dake zaune rike da bakin sa ya kasa magana.

Sorry Abba kada in taka ka cewar Salma..

Kallon ta yake yasha Alwashin sai ya nunawa Aishatu Mahaifiyar su shike da iko da Gidan sa..

Wannan karan ba zai kara Yarda da cin mutuncin Matar sa ba.

Rahama da duk jikinta ya yi tsami har susa jikin ta soma tana kokarin tashi kafafuwar ta Sun Gaza daukatan..., Abba dake zaune yana lura da ita tausayin ta ne yacika masa zuciyar sa.

Yasan Rahama kamilar Yarinya ce Ma'abociyan karatun Alkur'ani,, sam- sam rayuwar Duniya ba ta dame ta ba,, da abun da yake cikin ta...

Burin ta kullum shine ta farantawa Iyayen ta.

Tuno irin kyautatawa da Rahama ta yi masa wajen kula da Mahaifiyar sa,, duk da Matar sa tana kyankyamin ta saboda akwance take kashi da fitsari, 'sam hakan bai ɗaga hankalin Rahama ba, saima jajircewa da ta yi ganin ta yi duk Abun da ya dace ga Mahaifiyar Uban ta a Garin Makarfi..

Tsabar shakuwar da ta yi da Mahaifiyar sa, a hannun Rahama Allah ya karɓi rayuwar ta...

Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke

Cikin muryar lallashi Ya ce" inkaiki daki ne?...

Abba zan iya tana kokarin Mike wa. Cije labbanta ta yi cikin jin zafi da ƙuna, ɗuk jikin ta shatin bulala ne........

*Waye Sheik Abdul Razzak hizqeel Makarfi ?*

Shahararren Malami ne Wanda Duniya gaba ki daya suka san da Zaman sa,

anyi gwagwarmaya dashi wajen ƙarfafa kalmar Allah, 'a Sudan ya yi karatun sa, 'inda ya fito da Babban sakamako harya kammala yakarbi diploma, 'be bar ƙasar ba Saida tashar Afrika TV suka ringa gayyatar sa 'yana wayar da kan Al'umma a kan jahilci,,

Daga nan ya koma Saudiya garin Madina Ya yi shekaru biyar, nan ma larabawa 'suka yita jinjina irin tarin ilimin da yake dauke dashi, har suka nemi ya zauna nan za su ringa biyansa Albashi mai tsoka...

Ka san cewa Yana kishin ƙasar sa Yaki yarda da kudirin su,, badan ransu yaso ba ya baro ƙasar inda ya dawo garin su Makarfi Yana ko yarwa da dalibai Yana huɗuba a massalacin juma'a...

Kwarewar sa da iya sarrafa harshe wajen fidda baki inzai yi karatu, ya ja hankulan Manyan Malamai har suka fara damawa dashi....

Mahaifin sa tsohon malami ne Kabeer hizqeel,, 'yataso da burin Duniya tasan shi ta hanyar daukaka kalmar Allah, besamu wannan damar ba, sai ya sa Wannan burin a kan ɗan nasa....

Fatima sunan Mahaifiyar Sheik Abdulrrazak yana ƙanne biyu Hassan da Hussain,, Kullum ba ta da burin daya wuce, taga ya yi aure... A lokacin sam besa aure agaban shi ba, Kullum basu wannan Garin, gata suna wancen garin ahaka dai Allah ya kaisa Garin kwatano Watan sa Daya a ƙasar....

Ya bugawa Iyayen nasa waya a kan zai ɗan kwana biyu kafun sudawo dan kwatano gari ne dake buƙatar wa'azi kusan a Garin za ka ga Ya'yan Musulmai suna yawo kaman a tsirara.

Mahaifin sa yaji daɗin bayanan sa Ya ce" to inka dawo za ka iske Matar ka da zamu aura Maka gobe in Allah yakai mu.

Cikin tsananin tashin hankali Sheik Abdulrrazak Ya ce" Abba Mata kuma'? a iya sanina banda Budurwa Wacece kuke shirin aura min ?.

Mahaifin sa ya amsa masa da Aisha ɗiyar Sani makocin mu.

Sheik yashiga tashin hankali jin wacce Aka bashi amatsayin wacce ze aura, ya gama zaman sa akwatano yabdawo inda ya iske sabon Gidan da Aka basu dan zama shida Amaryar sa Aisha.

sossai yaiwa Iyayen sa biyayya ta hanyar ɓoye rashin Soyayyar da be mata, Allah ya azurtasu da yaya

Abubakar

Rahama

Salma

Tun daga wannan lokacin ba ta ƙara haihuwa ba.

Sheik cikin son ya ƙara zuri'a ya karo aure tun lokacin daya auro 'Sa'adatu

Aishatu ta canja halayen ta nagari ta dauki karan tsana ta daurawa Rahama dan Rahama taki bin mugun kudurin ta.

Bata da burin daya wuce Sheik ya saki Sa'adatu amma fur Yaƙi Ya ce" sai dai in bazata iya zama ba ta wuce.

Shakuwa mai karfine tsakanin Rahma da Sada'atu dan har karatu take koyawa Rahama da abubuwa masu muhimmanci a rayuwar ta.

Aishatu ta sallama Rahama daga cikin Ya'yan ta kawai dan tanason kishiyar ta.

Duk Abun da Salma zata aikata na rashin kyautatawa to dai-dai ne awajen Mama..

Bata Raina laifi komi kankatar sa awajen Rahama.

Sa'adatu haihuwar ta daya Abdul Jalil shine dan data Haifa soyayya datakewa Rahama ya ninka Wanda takewa dan cikin ta.

............

🇧🇯 *Benin Republique*

Kasar Benin Republique kasace wacce acikin afrika tafi kowace kasa Zaman lafiya da kwanciyar hankali,, Domin a tarihi ita ce kasar da ba a taɓa Yaƙi cikinta ba.

Babban Birnin tarayya kasar ita ce *kwatano*

Wanda shine capital.

Gari ne mai yawan jama'a acikin su.

Akwai kabilu iri iri kamar

Hausawa zabarmawa, dandawa, fulani, chabe, yoruba, Yan basilla, fongbe.

French ita ce turancin kasar

 *Masarautar camp guezo*

 Abdul samad ne ya fito cikin shigar sa ta Alfarma sanye yake da suite baki wando da farin rigar, takalmin sa haf cover, Fari ne dogo kyakyawa sangirin ajin karshe, dan inba kaji yai hausa ba zaka dauka balarabe ne, yalwata cen saje ne a fuskar shi hancin sa kaman biro' 'labbansa jajir yake A nitse cikin takun sa dake nuna kwarjinin sa ɗa haibar sa yake tafiya, miskili ne dan ko bedamu da yawan magana ba idan aka cikashi da surutu nan da nan idanun sa kekawo hawaye.

Sallama dauke a bakin sa 'ya ƙaraso fadar sarki

Fadawa suka fara gaisheka dan sarki jikan sarki yarima Samad takawan ka lafiya..

Mai martaba namaka barka da isowa 'fadawar dake bayan mai martaba sanusi turaki 'fifita suke masa ahankali...

Gyaran murya mai martaba ya yi alamun kowa yatashi yabasu waje ze gana da jikan sa.

Hatta waziri Saida suka tashi.

Gyara zaman sa Yarima Samad ya yi.

Kansa aduke Ya ce..

Allah yataimaki mai martaba yau fa nakeson infara cika burina.

Kubiyo ni labari nacen gaba 💃💃

Book. 0️3️

Allah yataimaki mai martaba yau fa nakeson infara cika burina.

Mai martaba *Sanusi *Turaki* kallon sa yake cike da tausayin ya ce Abdul Samad..

Naji dadin jin Haka daga gareka Allah yabaka Sa'a.

Amma wace kasa za ka je ne?

Cikin dukar da kai kasa ya gyara kafafun sa ya tankwashe su waje daya.

Zazzakar muryan sa mai dadin sauraro ya ce wannan karan ( Nigeria kano) zanje ko Allah zai sa indace da abun da nake nema.

Kuka ya kwacewa mai martaba har sautin kukan nafita ya ce Abdul Allah yataimakeka.

Ina son duk halin da ake ciki ka rinƙa sanar dani Domin inringa sani lafiyar ka.

Ya batun Maryam ne Samad ya tsare shi da idanu.

Nan da nan duk wani annurin dake kwance saman fuskar sa ya dauke.

Mikewa tsaye ya yi cikin halin ko in kula da maganar mai martaba cikin ba ta rai ya ce natafi.

Bai jira amsar mai Martaba ya fito Kai tsaye.

Mai Martaba murmushi ya yi Yana girgiza Kai ya san za ai Haka.

Fadawa 'na ganin fitowar sa 'suka fara masa kirari

Tafiya yake cike da kasaitar sa da cikar haibar sa yai ɓangaren fulani yanufa dan ya yi mata sallama bayi ya iske sunata mata hidima yayinda take zaune kan doguwar kujera.

Idanunsa ya sauka a kan baiwar dake goge wa fulani kafa da ruwa da kyalle ahannunta cike da nutsuwa take mata wankin kafar.

Lale lale barka da isowa Samad Yana ga ka shirya kaman Wanda zebar kasar.

Be ba ta amsa ba karasa shigowa dakin yai Yana kallon bayin dake mata bauta 'cikin jin haushin wannan banzar Al'adar su.

Ya kalli inda bayin suke umarni yabasu Dukan su 'sufita kuma beson yakara ganin su a dakin inhar Yana ciki.

Cike da girmama zancen sa

 kowannen su yafita sadaf sadaf.

Kallon sa ya maida a kan fulani wadda shi take kallo cike da mamakin cin fuskar dayai mata.

Daman nazo in sanar dake zanyi tafiya saina dawo daga Haka bekara cemata komi yafita dakin.

Itako fulani ranta yakai kololuwa wajen baci ka gamun dan iskan yaro

Ni zewa cin fuska agaban bayi.

Cije labban ta ta yi cikin zafin rai ta ce wallahi Kaima saina ga bayan ka.

inshAllah inka tafi ba za ka kara tako kafarka masarautar nan, wani dariyar mugun ta saki.

Ɓangaren mahaifiyar sa

Ya nufa

Mahaifiyar sa Kwance ya isketa tana fitar da nishi mai wuyar fassarawa Alamun tana jin jiki sossai

Cikin hanzari yakarasa shigowa dakin 'sannu mamy jikinne yatashi?

Kannen sa ya kalla Wanda duk sunyi tagumi.

Cikin kaduwa ya ce Mamy

 meke samun mamy ne Yana tambayarsu cikin yanayin damuwa.

Ahmad ya ce inaga hawan jinin Nata ne yatashi.

Yaya samad na Lura duk sanda ka kirkiro tafiya to aranar Mamy baa tashi lafiya da ita.

Why ba za ka hakura ba da wannan burin naka.

Yarima samad sakaka yake kallon kanin nasa Yana zaro zance 'cikin dabi'ar sa da yake nuna halin ko in kula.

Yai gaban Mamy be amsa masa ba. hannayen ta yakama cikin nashi ya hadesu waje daya.

Mamy dan Allah kiyafemin wannan karan ba zan iya Zama ba 'saina tafi ɗuk wani kulawa zansa abaki 'cikin gamsuwa da zancen nasa.

Mamy ta dago Kai ahankali ta daura kan pillow Kara matse hannun samad tai cikin Nata.

Ta ce Dana Allah yakaika lafiya na lura duk sanda kake kokarin barin kasar nan da rashin lafiya nake tashi dan haka kar ka damu inshAllah zamu kula da kan mu.

Cikin kuka' da nishi da take yi sama sama ta ce

Duk halin da kake ciki ka rinƙa taboni inajin labarinka

Gyada mata Kai ya yi alamun gamsuwa da zancen nata.

Mikewa ya yi ya ce natafi Allah ya Kaddara saduwar mu 'idanun sa cike da kwalla.

Harabar gidan yanufa iñda Ahmad da Khadija suka take masa baya.

Abokan sa su biyu tun kuruciya suke tare ne suka taso cikin shigar su.

Ta Alfarma laptop ne a hannayen su.

Da jakunkuna bakake

Amma wallahi Kai dan iska ne mai suna faruk ya fada Yana kallon Samad ya za ka wani shanya mun anan tsabar iskanci.

Abdul Samad ko kallon iñda yake beyi ba bare ya sa Ran zebashi amsa.

A daddafe yai sallama da kannensa da suketa kuka musamman Khadija data rungume shi tana mejin kaunar yayan Nata da ƙyar Aka banbare ta a jikin sa.

Badan yaso ba 'suka shige motar daze kaisu aviation (airpot)

Hanyar daze kaisu Aviation cadjehoun suka nufa Kai tsaye.

Yana zaune cikin mota adu'oi yaketa karantowa wannan dabi'arsa ce duk sanda zeje koda nan da c'en ne indai Yana kan abun hawa ya rinƙa karanto adu'a harya isa inda zashi.

Wayar sa mai kirari iphone 13 max tafara ring Kallon fuskar wayar ya yi Yaga ansa Maryam.

Saida wayar ta kusa katsewa ya daga 'shiru kake ji Yaki magana.

Daga can ɓangaren cikin jin dadin ya daga ta buga uban tsalle wayyo inawuni dafatan kawuni lafiya ya aiki ya kokari ya fama da jama'a...

Lafiya kalau yabata amsa atakaice.

Daman na ji ance zakai tafiya banyarda shine nakira in ji ko Haka.

Eh Haka ne yabata amsa

Cikin kosawa da zancen ta

Ya ce sai anjima munyi waya bejira cewarta ya katse mata waya.

Itako Maryam tsalle taketa yi wai yau Samad ne ya amsa mata gaisuwar ta Wanda Ada kwata kwata baya cemata komai' harta gama surutun ta ta kashe.

Rungumar 'mahaifiyar ta dasuke Kira ummy ta yi sam ta manta gaban uwarta take.

Ummy rike da baki ta ce oh ni Karima yaran Zama ni basuda kunya.

Rufe fuskar ta yi da tafukan hannayen ta cikin jin kunya ta tashi tawuce sid dinta.

.......

Abdul samad suna isowa airport gabadaya ma'aikatan wajen suka fara barka da zuwa sir

Me za ai maka ne suna biye dashi abayan sa.

Be basu amsa ba saide cigaba da tafiyar yake yi cike da izza yakaraso wani babban office.

Abokan sa faruk da auwal suka tsaya daga waje 'sai wani dan kawun sa Marwan duk suka tsaya wajen office din.

Secretariat tana ganinsa

*Bienvenue* (barka dazuwa) ta cemasa da harshen french

Merci nagode yabata amsa, file din dake saman table din office din ya jawo su.

Yasoma rubuce rubuce abun da befi minti daya ba.

Mika mata ya yi ya ce wannan shine last din kudaden dazan Bari.

Kiyi copy original kiba Ahmad zezo yakarba.

Kanta aduke ta ce an gama ranka yadade.

Amma ba ka fadi wani kasar za ka je bane in shigar dashi Yanzu a computer dan su sani.

Kano zani yabata amsa atakaice

Mu Hudu ne zamu je.

Fitowa daga office din ya yi inda su faruk suka take masa' baya.

Jirgin da suka shiga

 jikin jirgin anrubuta

Samad personel

Sabanin sauran jiragen da zakuga

Samad air plan

Babu ba ta lokaci drever jirgin sama be ba ta lokaci ba wajen tashi dasu

Sararin samaniya.

**********

Sa'adatu da Rahma bayan Sun idar da sallah 'isha'i Rahama nakwance jikin ta ta ce wai anty in tambayeki mana.

Inajinki yar anty yayinda take shafa kan Rahma tana murmushi ta zaku ta ji me zata ce.

Lumshe idanunta tai tana shakar kamshin jikin sa'adatu wacce suke kira da anty '.

Daman sonake in tambaye wai mene ne aure sunnah manzon Allah Saw ne.

Murmushi kwance a kan fuskar anti tana gyara kwanciyar Rahma a jikin ta ta ce to kekuwa Rahama meyasa kikai min wannan tambayar.

Kawai de na tambaya ne dan sau dayawa saikaji anacewa aure sunnah manzon Allah ni kuma nasan nayi karatu sossai amma baa taba Zama Aka fassara mana ma'anar aure sunnah Manson Allah ba.

Rahama kibari idan kikai aure mijin ki ze gayamiki tana murmushi amma dai kaman yanda kikace ance sunnah Manzon Allah ne, shike nuni da cewar shugaban halitta shima ya yi.

Yanzu kinga dare yakamata ace kin kwanta saboda tashin asuba.

Kara shigewa jikin anty ta yi.

Sallamar Sheik ne ya sa tamike dasauri cikin girmamawa ta ce inawuni Abba dafatan kadawo lafiya?

Lafiya lau yabata amsa

Yana mejin tausayin ta tun ranar datasha duka

Anty tagaishe shi ya amsa mata cikin sakin fuska

Fira akeyi Kenan tsakanin uwa da ya

Yana murmushi

 yayinda yajuya ya yi sashin mama.

Sallama yake mata amma sam hankalin ta be jikin ta.

Saida yakara sallama WAJEN Sau uku sannan ta dawo hankalin ta.

Shan kunu ta yi ta ce baga irin ta nan mutum yadawo babu adalci.

Yanzu saboda Allah kadawo ai dakina yakamata kafara lekowa sannan kaje Nata.

Kallon ta yake yanda take zuba ruwan masifa hartakai karshe...

Salma ya kallah da take shan shayi cikin turo baki gaba kaman anmata dole ta ce inawuni.

Amsa mata ya yi yadawo da kallon sa kan Mama.

Kingama fadar?

Eh nagama tana kada kugu azaune.

Saida safe daman yau ba kwanan ki bane kuma gida na ne duk iñda naga dama zan shiga inada ilimi Niba jahili bane.

Ficewa ya yi Ransa aba ce.

Cijje labbanta ta yi kam buhu gaskiya Sheik ya gama dani waiyau ni yake cewa jahila.

Ze ga jahilci ganin idanunsa.

Salma ta ce ai Mama ni sai Inga kaman baya sona dan duk sanda ze ganni wallahi cikin fada yake min.

Amma banda Rahma ni wallahi na tsaneta tana murguda baki.

Mama kalmar tsana da ta ji Salma tafurta' be mata dadi ba.

Amma gudun kada ran Salma yabaci ya sa takasa cewa komi

Washe gari.

Tun da sassafe Rahma ta tashi tashiga kitchen ta daura musu brek fask sauri sauri take kada suyi latti.

Iske Salma ta yi inda tabar ta ko Sallah batayi ba.

Waike kullum Salma saina ta fama dake a kan Sallah jibi agogo fa karfe bakwai tun karfe biyar na tasheki amma inda kike ko motsawa bakiyi ba.

Salma turo baki ta yi gaba tana hararan ta ce inkece ke karban Sallah idan nayi ki maidomin abuna ta ja tsuki mtss..

Ni dai na ji pls ƘANWATA tashi kiyi Sallah muyi brek kin san yau yau munada lecture din sabon malamin da principal ya ce shize maye gurbin Joseph.

Kin san ba na son yi latti aduk abun da zanyi.

Koma wa falo ta yi tagama hada brek direct dakin Abba taje ta aje masa nasa gaishe shi ta yi.

Ya ce my Rahma har an gama hada Brek

Eh baba kuma.sauri nake ka san a shekarar nan zamu gama karatu befi sauran wata daya ba.

Banson in yi Wasa da Damata.

Gaskiyar ki Rahma Maza kije kishirya ina ita kanwar taki.

Tanacen tana shiryawa.

Abubukar ne yashigo sanye yake da farar jallabiya 'murmushi kwance a kan fuskar shi ganin kanwar sa abun soyuwar sa.

Cike da ladabi yagaida abbansu shafa kan Rahma ya yi ya ce m'y kanwaty ina brek Dina banga kin kawo mun ba

Dariya ta yi Saïda fararen hakoran ta suka bayyana

Ta ce yaya Yana dakin anty bara inkai maka.

Amsa mata ya yi a'a dakin barshi zanje da kaina indauka.

Gaban Abban nasu yazauna rike da Alku'ani ahannun alamun hadda yake yi.

Sun gama shiryawa tsaf kallo daya zakai wa Rahama ka tabbatar Allah ya yi halitta awajen.

Fara ce sol kyawunta baya misaltuwa dan kusan a unguwar ita akaiwa lakani da sarauniyar kyau...

Tafiya suke hanya Dukan su ahanzarce suke har Salma dan yau batason amata cin fuska gaban dalibai.

Sun shigo makarantar cikin ikon Allah malamin da zefara koyar dasu geographie be iso ajin ba.

Kowa sai surutu yake a ajin.

Rahama itada kawarta asiya ke fira.

Asiya ta ce waini Rahma in tambayeki mana

Inajin ki kawalli suna fuskantar juna

Rannan naje gidan Ku na'iske anata bugun ki na ji kaman muryan ki na ji bankarasaba nakoma.

Inafatan bake ba ce.

Rahama cikin son kawar da zancen ta ce kunnenki ne basu jiyo maki daidai ba.

Niko me zai sa abuge ni babu laifin komai.

Sallamar da suka ji an yi

Yasa kowani ɗalibi maida hankalin sa a kan wanda keshigowa

Ganin wanda ke shigowa acikin ajin su Rahma tafara zazzare idanu.....

Book 0️4️

Rahama tafara zazzare idanu ganin wannan saurayin daya bisu rannan tambayar kanta take yi me yazo yi.

Class din Taga kowa yatashi Yana ta welcome.

Karasasa shigowa ajin ya yi Yana kallon daliban cikin shigar shi ta boyel Maroon color ba ƙaramin kyau ya yi ba.

Murmushi kwance a kan fuskar shi yabada umarnin kowa yazauna.

Rahama data lula duniyar tunani batama san ya ce a zauna ba.

Asiya ta buge ta

Ta ce ke Rahama ba za ki zauna ba...

Am sorry ban lura ba Rahama tabata amsa tare zama kan kujerar

Salma data ganshi tsaf ta ganeshi hade rai ta yi tana ta hararan sa ta ka san idanu.

Gyaran murya ya yi ya ce nine sabon malamin Ku me koyar muku geographie dafatan zaku ba ni hadin Kai.

Gabadaya class suka amsa da inshAllah.

Yakara dacewa sunana

Adamu Abdullahi daga jahar katsina...

Idanun sa ya sauka kan Rahama da ganinsa da ta yi ya sa ta dukar da kanta kasa.

C'en kasa kasa takewa asiya magana ta ce asiya wannan mutumin nataba ganin sa.

Murmushi asiya ta yi ta ce kodai ya ce Yana sonki ne Rahama.

Zara zaran idanunta ta ware cikin yanayin tsoro ta ce A'a soyayya kuma ni me hadina da namiji inbanda Yan uwana.

Adamsy tun da yashigo ajin ya lura da Rahama da asiya fira suke kuma ya tabbata akansa ne.

Keeee!

Tashi tsaye keda kawarki

Yanuna asiya da Rahama

Tashi suka yi a tare Rahama kanta aduke takasa kallon sa.

Bakusan class kuke ba kuma malamin Ku na aji

Amma kuke surutu.

Afuwan suka bashi amsa tare da Zama beso suka zauna ba dan begaji da kallon fuskar Rahma ba duk da kanta aduke yake hakan be hanashi ganin zallah kyawunta ba.

Kusan karfe goma yagama musu lecture

Dalibai suka fito dan nema wa kansu abun da za su dan taba.

Asiya da Rahama da Salma tare sukaje cafeteria lemu kadai suka siya dan su ba sa ciye ciye a makaranta.

Salma ta ce zanje wajen Amina kawata kafun a koma aji da to suka amsa mata.

Rahama takai dubanta ga asiya ta ce wannan malamin nan wallahi shine Wanda ya tsaidani nida Salma.

Asiya ta ce gaskiya kinada saa wannan hadadden gayen ya biyo ki.

Harara ta watsa mata ta ce kece kika ga haduwar sa

Amma nikuwa banga komi ba ke mubar zancen sa kawai.

Dariya asiya ta rinƙayi sossai harda rike ciki.

Rahama ta ce kedai kika sani tana jifanta da hararar Wasa.

Asiya tamike tsaye tare Kai dubanta a kan Rahama pls kawata jirani inje indawo cikina kedan murda min.

Ok saikin dawo ina nan ina jiranki!

Ita kadaice zaune inda ta fiddo littafin ta tafara karanta karatun da akai musu dazun.

Tsayuwar mutum a kan ta ta ji dago Kai ta yi ta kalle sa.

Gabanta ne ya tsananta bugawa gab gab gab da karfin nan.

Tsintar muryar sa ta yi yana cewa be dace dake ba ma'abociya kyau ki zauna ke kadai anan anan wajen ba.

Dago Kai ta yi idanun su suka tsarke cikin juna.

Cikin muryanta dake nuna an takura mata ta ce mallam ka tsayamun akai yaya Haka.

Ok to tsayuwar ne bakiso to bara inzauna.

Samun wuri ya yi yazauna kusa da ita.

Ranta aba ce ta ce nan wajen ya yi maka ne.

In tashi in bar maka

Ba zan so ki tashi ba ma'abociya kyau nine yadace intashi tun da Nina sameki anan

A'a kar ka damu ni canja waje ba zaimun wahala ba.

Ba zan so ayi hakan ba dan inkika tashi nima wajen ba zai min dadi ba.

Kuma nashiga hakkin ki.

Kinga tafiya ta amma karki manta fa adamsy ne naki Wanda ze mallake ki har Abada inshAllah.

Wuce wa ya yi Yana tafiya kamar Wanda bayason wuce wa

kallon sa take harya ba ce mata da gani.

Maida hankalin ta ta yi a kan karatun ta.

Kusan karfe biyu suka tashi daga skul.

Neman Salma tashiga yi a makarantar duk inda take tunani zata ganta duk ta leka ba ta ganta ba...

Jiki asanyaye ta fito.

Tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.

Adua' take yi kamar Haka

Ya 'Allah kasa kanwa ta tana lafiya ka karemin ita

Duk inda take.

Karasowa gida ta yi ta iske Sheik da baba salihu suna hira.

Gaishe su ta yi cikin yanayin damuwa ta ce Abba banga Salma ba.

Abba da baba salihu suka yi murmushi keko ai Salma ta dade agida.

Maza kishiga gida kije kiyi wanka kiyi Sallah.

Jiki asanyaye tashige ciki.

Baba salihu ya ce Sheik in babu damuwa zan nemi wata Alfarma mana.

Sheik cikin tsareshi da idanu ya ce fadi bukatun ka aika wuce matsayin mai gadi agidan nan kazama dan uwa dan dai duk kaki kayi wata sana'ar ne kace abarka a gadin.

Baba salihu ya daidai ta nutsuwar sa, ajiyar zuciya mai karfi ya sauke.

Ya ce Sheik maganar da zan fada maka dan Allah karya ba ta Ran ka '

Murmushi Sheik ya yi tare da gyara zaman sa 'yana shafar gemun sa.

Ni dai fadi inajin ka anzama daya.

Baba salihu cikin tsoro da fargaba ya ce Dana nake nema wa auren Rahama idan tagama karatu shekaran nan.

Cikin zare idanu Sheik ya ce dan ka kuma.......

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 0️5️

Dan ka kuma ɗaman Kana da ne kuma ba ka taba gayamin ba.

Baba salihu dukar da ka san kasa ya yi cikin sanyi murya ya ce afuwan firan hakan ne ba ta taba tasowa ba shi ya sa ban gayamaka ba Amma tabas inada iyali harda yaya.

Sheik da mamaki yacika masa zuciya ya kalle shi akaro na biyu cikin takaici ya ce baba salihu kaban mamaki duk Zaman da mukai da kai ba ka taba gayamin ba sai yau...

To yanzu ina iyalin naka suke da ka bar su tsawon shekaru biyar Kana zaune anan Koda kasuwa ban taɓa ganin kaje ba...

Baba salihu ba na son kasawa zuciyata zargi da wasi wasi akanka kafito a mutum ka gayamin gaskiyar ka.

Ajiyar zuciya baba salihu ya sauke ya ce Sheik dan girman Allah kayi hakuri zan sanar da kai hakikanin gaskiya Amma ba yau.

Wallahi Inna fada maka zansamu matsala azuciyata kamin afuwa kuma ni mutum ne

Mai gaskiya kar kai tunanin kozan iya cutar daku kokuma rashin gaskiya ne yakawoni gidan ka.

Numfashi Sheik ya fesar tare da fuskantar shi na ji bayanan ka

 dan naka da kakeso ya auri Rahama ya sunan sa...

Cikin dukar da kai kasa ya ce Abdul samad sunan sa.

Aika wuce neman Alfarma nabashi Rahama

Saide gaskiya suna gama karatu da sati Daya zan daura musu aure.

Murmushi kwance a kan fuskar baba salihu duka wa ya yi kasa Yana godiya harda kukan farin ciki.

Salma ta ce gantalalla sai yanzu Kika dawo

Kin tsaya kina tambada a skul waike kinga saurayi '

Wallahi kikai sake wannan malamin sai ya dura Miki ciki ya gudu ya barki tana turo baki waje.

Rahama da ranta yakai kololuwa ta buga kirjin ta ta ce nice kike gayawa Haka Salma?

Eh anfadamiki kina tunanin banga abun da kikeyi bane waike kamila

Batai aune ba ta ji saukan mari a kuncin ta.

razananne kara Salma ta saki yanda ka san yanka naman jikin ta akeyi.

Wayyo Mama Rahama zata kasheni.

Aguje mama ta fito itada anty tana ta salati.

Kallon Rahama take wacce hawaye ke kwaranya daga idanunta.

Cikin tsawa mama ta ce

Keeee!

Me ta yi Miki ne kike zaluntar ta banza yarinya

Salma cikin kuka' rike da kuncin ta ta ce mama a skul na ganta kebe da wani saurayi sukadai a lungu zaune suke ga kugun sa ga Nata.

Kuma wallahi hannun su cikin juna kinga dalilin dayasa banjirata ba Kenan.

Na dawowa ta gida banson dalibai su ganni aita nuna ni anacewa yar uwata yar iska ce takai karshen zancen tana sakin kukan karya

Rahama da idanunta suka ciko da kwalla tagaza magana.

Kallon Rahama suke mama da anty ganin ta yi shiru ne...

Yasa mama daga hannu ta wanketa da wawan mari Wanda take ta ji walkiya.

Zata kara mata wani marin ne anty tarike mata hannun cikin fushi da bacin rai ta ce.

Ke Aishatu wace uwa ce ke.

Sam bakida Imani Rannan anmata kazafin tashiga motar saurayi yaukuma kuma ance Sun kebe itada saurayi.

Shin baki Auna maganar Salma ne kokin mance wacece Rahama to Bari kiji abun da zan fada miki muddin ina aure gidan nan wallahi ba zan kara yarda dacin fuska duk da kuwa kece kika haifeta.

Nufo Salma ta yi cikin bacin rai tadau hannu ta wanke ta da mari 'mama sake da baki take kallon karfin halin 'sa'adatu.

Salma Takara fasa wani kara ta cakume wuyar rigar anty wai kokuwa zatayi da ita.

Cikin zafin nama Rahama ta jawo Salma ta yi jifa da ita saman kujera kama hannun anty ta yi za su shige ciki...

Mama ta finciko Rahama iccen murhu tadauka tafara kwada mata akai nan take jini yarin ga tsiyaya kara nausa mata icce ta yi akai sabar buguwa Rahama da baya baya ta fado Kasa nan take ta yanke jiki ta fadi sumammiya

*******

C'en ɓangaren Abdul samad ji ya yi jiri na Diban sa yana kokarin faduwa

Magoya bayansa suka yo kansa lafiya kuwa lokaci daya ba ciwo bakomai kake kokarin faduwa banda bugawa babu abun da zuciyar sa keyi

Cikin tashin hankali faruk ya ciccibe shi suka sakasa a mota

Numfashin sa sama sama yake fitarwa

*******

Ɓangaren su Rahma

 

Innalilahi wa'inna rajun anty tashiga maimaitawa shi ke nan ta kashe min ya aguje tafita harabar gidan 'cin karo ta yi da Abdul Jalil daya dawo daga buga kwallon kafa.

Cikin kidima ya ce anty lafiya naganki arude ina zakije Haka ne babu ko dankwali akanki.

Ina Abban Ku yake Maza kirawomun shi wannan azzalumar ta kashe min ya ta.

Innalilahi wa'inna rajun ni sa'adatu wannan wace irin rayuwa ko ince wace irin kiyayya ce.

Cikin hanzari Abdul jalil yakaraso gaban Abban su da baba salihu dasuke CIN abinci tare..

Kamar an jefoshi daga sama suka gansa arikice.

Cikin zazzare idanu ya ce Abba Rahama ce tafadi ba ta numfashi.

Baba salihu da abba azabure suka tashi suka yo gidan gadan gadan cikin sauri.

Cin karo suka yi da anty daketa zuba uban kuka.

Tana ganin Sheik takara sautin kukan ta..

Beko bi takanta ba shida baba salihu direct daki suka nufa inda suka iske mama sai jijjigata take yi tana kuka tana fadin Rahama ki tashi.

Anty takaraso dakin cikin zafin nama ta ture mama ta ce Azzalumar uwa mekike akanta kina son ki karasata ne.

Sheik da ya yi mutuwar tsaye ya ce bangane Me kike nufi ba sa'adatu WANNAN jinin dake malale tsakiyar daki na mene ne ?

Yana kallon sa'adatu cikin kuka ta ce mama ce ta buga mata icce a kan sharrin da Salma taiwa Rahmatullah.

Sheik da baba salihu zazzare idanu suka yi basu ko bi takan mama ba.

Sheik yadauki Rahama cak ya rungumeta cikin sauri ya nufi motar sa 'baba salihu ya take masa baya kusan a tare suka shiga motar.

Sa'adatu saka hijab dinta ta yi a baibai tasaka shi. Kujera bayan motar tashiga rike da Rahma tana kuka mai tsuma zuciya dan ko motsi Rahama batayi.

Direct asibitin *khamec* CLINIC babban asibitin private ne da akeji dashi a kano.

Cikin hanzari Aka bude masa Gate duba ga yanda suketa zuba Horn.

Motar su Abdul Samad shima ya doso asibitin kusan a tare motocin su

Suka shigo asibitin.

Emergency emergency faruk ke fadi Yana ihu

 'muryans ta disashe saboda tashin hankali

Taku har kullum

Kyauta daga Allah*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 0️6️

Emergency.

Likito suka fito cikin sauri dauke da gadaje.

Da ƙyar su faruk da hamza suka daga Samad tare da daurashi kan gadon 'cikin hanzari akai ciki dashi.

Sheik ya daga Rahama sama bedaurata a gadon ba tana hannun sa 'yanata mata tofi adu'oi

Cikin hanzari yashiga ciki anty da baba salihu suna bayan sa.

Kai tsaye likitoci suka amshi Rahama daga hannun sa umergency akai da ita.

Likitan daze duba su Daya ne

Tura musu gado ya yi Aka daura Rahama Kai itama yashiga da ita cikin dakin.

Baba salihu Yana hango Marwan duk ya tsorace lokaci Daya 'mamaki ne kwance a kan fuskar me sukazo yi kuma wa suka kawo dan kwata kwata shibema lura da mutanen da suka kawo dayan umergency ba saboda kowa hankalin sa atashe yake.

Zuciyarsa naci gaba da bugawa da karfi.

Neman hanyar guduwa yake yakoma gida yaji muryan faruk nacewa Allah yaba yarima samad lafiya 'marwan ya amsa da ameen.

Juyowa ya yi kallesu yanason tuno wani abu Amma Brain dinsa yakasa kawo m'asa komai adaddafe ya je kusa da Sheik ya ce yakamata inje gida ka san anbar gida abude saboda tsaro, Sheik ya gyada masa tare da bashi dari biyar yahau mashin.

Likita Yana dakin tare da su nurse masu tayasa Akai ya yi nasaran yiwa Rahama dinki dan sossai wajen kan Nata ya yi Rami sossai.

Cikin abun da befi minti 30 ba yaimata gwaje gwaje dasuka gano tana dauke da ciwon zuciya.

Ya sallam ya furta Yana me kallon ta.

Stil gwaje gwajen da yaiwa Samad resultat Daya ya bayar shima ciwon zuciya.

Likito su dake taimaka masa suka ce wai docto meyake kawo ciwon zuciya ne ga matasan yara?

Docto ya ce abubuwa da yawa amma Bari mugama shawo kan wannan saurayin.

Marwan ne yakoma c'en baya Yana Waya da Dukan alama sirri yake yi.

Daga can ɓangaren ta ce Marwan Kana nufin kuna asibiti da yarima Samad ya ce kwarai kuwa muna tare da Yana umergency Yanzu haka.

Dariya fulani ta yi ta ce Alhmdulillah ka san me nakeso da kai ya ce A'a saikin fada.

Ina son yau Komai dare kaje dakin da aka kwantar dashi pillow kawai zakasa masa ya wadatar.

Zazzare idanu Marwan ya yi ya ce in asirina ya Tonu fa?

Kai meysa kacika tsorone saikace ba jinina ba.

Da ƙyar Marwan ya amince da kudirin fulani daga Haka suka yi sallama.

Kusan Awa biyu shiru

 kake ji duk Sun kagu suji labari 'anty ta ce Sheik nifa na tsorata fa tun da Aka shiga da ita' basu cemana komi ba.

Kwantar mata da hankali ya yi yanuna sudai kara hakuri sugani.

Wata nurse suka gani ta fito daga dakin tana goge zufa...

Aguje suka yi gunta suka tsareta.

Nurse lafiya ya Rahama take ne kinki magana

Nurse ba ta basu amsa ba illa wuce su ta yi.

Anty tagumi ta yi tana ta dua'a Allah ya sa kada mummunan labari yahau kan Rahama.

Fitowar docto ya sa suka maida hankalin iñda yake fadin ina Yan uwan wannan saurayin.

Su faruk suka matso ya yi gyaran murya ya ce zaa bashi daki daya shida wacce suke daki tare.

Amma baa bukatan kowa yashiga dakin da kansu za su Farka.

Indan sun Farka kowan'e zaa bashi daki cikin gamsuwa da Hakan Sheik ya ce docto ina iya zuwa dubata Yanzu kuwa.

A'a bazaku shiga ba bayanda suka iya dole suka hakura.

Anty ta ce Sheik Kana iya zuwa gida ninan zankwana.

A'a karki damu kije gida dan kisamu kiyi girki nasan akwai yunwa tattare dake.

Da ƙyar da lallabawa tayarda ta tafi gida.

***********

Mama tana zaune daki Kana ganinta ka san ba ta cikin hayyacin ta.

Tsoro da fargaba abun da zebiyo baya tsakanin ta da Sheik tashiga yi.

Sallama baba salihu ne ya sa ta Mike aguje ta sameshi.

Cikin kidime wa ta ce baba inafatan Rahama ba ta mutu ba ko.

Ransa aba ce ya ce Taya zansan Hakan tun da Niba Allah bane.

Keda kike neman kasheta baki gano Haka ba saini ne zan gane.

Salma ta fito daga daki tana Mika ta ce amma baba salihu kacika dan rainin wayau wallahi.

Mama ce kake gayawa bakaken maganganu tana turo baki.

Be ba ta amsa saide cemata ya yi yi hakuri uwata.

Fuskantar Mama ya yi ya ce dan Allah kodan abinci ki dafa ki kaimusu nasan suna bukatan Hakan.

Jikinta a sanyaye ta ce to.

*******

Ɓangaren adamsy

Adamsy a hadaddan gidan da gwanati tabasu dan zama.

Toilet ya fito daga shi sai towel a kugun sa.

Abokinsa dake zaune gaban TV Yana kallo sake da bashi ya ce Kai Amma adamsy Kai dan iska ne saboda Allah Kai bakajin kunyata ne jibi yanda sandar ka yaketa tsalle acikin towel..

Murmushi ya yi Saïda fararen hakoran suka bayyana kuncin sa ya lotsa to in banda abunka Aminu Nida dakina wai na gayyato ka ne...

Uhmmm angon Rahama Kenan wallahi in taga wannan abun naka saita suma Alku'an.

Adamsy ya ce suman dadi ba Kai bara in yi sauri in shirya ka san yau nakeson infara zuwa neman iri gidan su.

Katayani da adua Allah ya sa inje a sa'a dan wallahi rasa Rahma daidai yake da rasa rayuwata.

Aminu ya dafashi ya ce ba na son ka zurfafa a son Mace 'sufa mata da kake gani basuda tabbas hakama Maza..

Kuma gaskiya kafadi aminu amma inaji a jikina zan mallaketa inshAllah.

Allah ya sa kasamu sa'a abokina da ameen ya amsa yayin da ya je gaban miro Yana shafa body lotion mai dadin kamshi.

Shiga toilet ya yi da Kayan daze canja.

Aminu dariya yaketayi rike da ciki ya ce oh kaji manya masu boye 'barazanar Yan mata.

*********

Sai Yanzu Aka fito dasu Rahama daga dakin direct dakin hutu Aka tafi dasu.

Gadon Samad na hagu

Na Rahama na hannun dama

Barci suke kowannen su yanata ajiyar zuciya.

***†**

Sheik daki yanema Akaba shi dan kwanciya saboda dare ya yi Yana shiga ya yi wanka ya gabatar da shafa'i da wutir ka sancewa asibitin akwai massalaci anan ya yi sallah.

Adua' yaketayi Allah yaba yarsa lafiya da yayan musulmi.

.......

Faruk yakira wayar Ahmad ya sanar dashi halin da ake ciki.

Cikin tashin hankali Ahmad ya fara kuka dan Allah ina yarima Samad yake ne.

Yana dakin hutu.

Mikawa Mamy waya ya yi...

Cikin tashin hankali ta ce a tarihin Rayuwata Dana betaba kwanciya asibiti ba sai yau kuma da ciwo Mafi muni Aka sameshi nashiga uku.

Khadija dake gefen ta ta ce Mamy kodai mu je ne nida yaya Ahmad ne.

Cigaba da wayar......

Taku har kullum kyauta daga Allah

09069080725*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 0️7️

Cigaba da wayar datake yi ta yi cikin tsananin damuwa ta ce dan Allah Daya Farka ka hadani dashi 'faruk ya ce babu matsla.Hhhh

Daga Haka suka yi sallama...

Khadija sai buga uban tsalle take kaman yar goye tana ta rusa kuka.

Wallahi mamy ni kibarni inje yarima Samad Dina babu lafiya wayyo Allah na.

Gabadaya bayi suka shigo cikin tashin hankalin jin ihun Khadija.

Cike da tsananin damuwa suka ce ya shugaban mu meyake faruwa ne.

Mamy cikin ɗAnne damuwar ta ta ce babu komai kawai dan ta buge ne take wannan sakarcin.

Labari yazowa mai Martaba yarima Samad na kwance gadon asibiti kano.

Cikin tsanin damuwa ya kalli waziri ya ce ina son ka kiramun lambar ambassado libya Yana katsina akace.

Waziri be ba ta lokaci ba wajen lalubo lambar ambassado libya Dr Abdullahi...

Mika masa wayar yayi.

Mai Martaba Sanusi ya kara wayar a kunnen sa yanata ring harta kusa tsinkewa Aka daga.

Sallama ya yi daga can ɓangaren ya ce 'A'a Ranka yadade kaine da kanka yau.

Cikin ban girma ya ce inawuni ya bayan Rabo.

Mai Martaba ya amsa masa da lafiya l'au.

Shirune ya biyo baya Dr Abdullahi ya ce Ranka yadade Allah ya sa lafiya Yana ɗAnna système dake gaban sa eapece na kunnen sa ka sance in Yana aiki beson daukar waya ahannun sa.

Cikin damuwa mai Martaba ya ce akwai jikana Abdul Samad Yana nan kano labari ya sameni wai ya yanke jiki yafadi.

Subuhanallah Dr Abdullahi wani asibitin yake ne.

Ai Dana Adamu Yana kanon zan turashi kafun nikaina in samu zuwa garin

Cikin gamsuwa da zancen NASA mai Martaba ya ce Kai gaskiya godiya nake in dan naka ya je ka sanar min daga haka suka yi sallama.

DR Abdullahi Kiran adamsy ya yi awaya harta gama ring be dagaba.

Kira wajen sau uku be dagaba tsakii yaita jero wa.

Nasan yanacen Yana shashanci haba Dan Allah kaita Kiran mutum.

Mahaifiyar adamu hajiya Sara ta fito dakin ta sanye take doguwar Riga gezner cikin tafiyar ta mai daukan hankalin mijin nata ta iso tana kwarkwasa.

Alhaji yanaga sai tsaki kakeyi Kai kadai ne kuma laptop na gaban ka...

Kallon ta ya yi ba ƙaramin kyau tai masa ba amma yanzu ba lokaci WANNAN bane.

Dan naki ne naketa Kira bedaga wayaba 'jikan sarkin kwatano ne beda lafiya kuma very important.

Ina Kiran sa da ya je ya dubo sa 'amma shiru.

Bedaga ba.

Kayi hakuri Dr yanzu Haka ya je wani aikin ne mai muhimmanci.

*********

Adamsy parking suka yi daidai kofar gidan Sheik.

Kan sufito ya kalli abokin NASA ya ce Kana ganin ba za a samu matsala ba.

Dan wallah ni Aka hanani Rahama ankira ruwa.

Abokin sa ya ce kadai nagayamaka baa daukan son duniya a daurawa Mace ka rinƙa control din kanka in Rahama matar ka ce zaka aureta.

Ok to mu je kusan a tare suka sauko daga motar'.

Knocking suka yi 'Baba salihu dake zaune Yana istigifari yataho yabude Gate...

Kallon su yake ya ce daga ina bayin Allah?

Adamsy sai sunne Kai yake kasa daman wajen Rahama muka zo.

Kuma kafun naganta ina son in yi magana da Sheik ne hannayen sa duka biyun cikin aljihun rigar sa.

Baba salihu kallon su yake daga ganin su ya san Yan Babban gida ne.

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce 'Ya ce Rahama dakuke nema ba sa nan itada Sheik.

Adamsy cijje labban sa ya yi yaji dacin amsar da baba salihu yabasu.

Abokin sa ya dafasa ya ce ka ga mu je goben in Allah yakaimu ma dawo.

Jiki asanyaye suka juya.

Baba salihu Yana ganin Sun fice ya maida kofa ya rufe.

Adamsy da ƙyar yake tuki zuciyar sa na tafarfasa idanun sa Sun kada, cikin bacin rai ya ce Rahama rasa daidai yake da bugawan zuciyata...

Karar wayarsa ce tadawo dashi hayyacin sa ɗakyar yadauko wayar kan screen din wayar Yaga Dad cikin hanzari ya ɗaga.

Inawuni Dad daga can ɓangaren ya ce haba adamsy ban ce maka wayarsa ya daina nisa da kaiba..

Ina WANNAN sarkin kwatano damuka taba Zama gidan sa tun Kana shekara daya a duniya...

Cikin gyada kai ya ce eh nagane Dad kanaban labarin su...

Jikin sa ne Aka kwantar nan asibiti khamec sunan sa Yarima Samad da zaran kaje kaje anuna maka emerngncy...

To Dad yanzu kuwa zamu tafi daga Haka suka yi sallama.

Ya juya akalar motar hanyar asibitin.

*************

Mama ta ce Salma dan Allah kiringa sassauta wa Rahama inada tabbacin sharri kike mata.

Amma abun da ya sa kika ga namata hukuncin nan Raina ne yabaci ganin nice uwarta amma ta ja hannun kishiyata za su shige dakin ta...

Salma da ranta yakai kololuwa wajen baci ta ce au Haka kikace sharri na mata ko?

Bahaka nake nufi ba Salma ina nufin amsamu akasi ne wajen ganin da kikai mata kila ba ita Kika ganiba.

Zumbure zumbure Salma tafara yi babu komai ke yau Zaki fara tsanata Kenan ko.

Sallamar anty ya katse musu hanzari kallo Daya ta yi musu ta kauda kanta ta raba ta gefen su tawuce.

Mama tabi bayanta cikin sanyi murya ta ce kinzo kin wuce mu bakice min komi ba...

Dago Kai anty ta yi tana harararta ai Niko me zance Miki duk WANNAN abun kinayinsa saboda kin tsaneni tun da nashigo gidan laifina ne dan na auri mijin naki.

Koko daze auroni meya Hana ki hanashi karo aure shi ke nan saboda mugun halin ki yar cikin ki...

Kike cutarwa dan in ji haushi kokuma yarinyar dan ta tsaneni kike so ko?

To ahirr dinki wallahi na Gina Rahama kan tarbiyya na gari duk son da Rahama takemin bekai wacce take Miki ba.

Ba dole ta shaku dani ba 'bakya janta ajiki kullum maganar fitsarriyar yarki kike dauka to wallahi Salma saita saki kuka ki rubuta ki ajiye Dan Allah ki ficemin adakina.

Mama mutuwar tsaye ta yi duk maganganun da Anty ke fade sakaka ta sake baki tana kallon ta hartakai karshe...

Cikin sanyin jiki tabaro daki 'abincin dazata asibitin tadauka tare da zura hijabin ta.

Baba salihu ya yi mata kwatance.

Itako Salma komawa daki takwanta ranta aba ce wai ita ala dole anbata mata rai kuma mama zata dawo ta same ta.

Daukar wayarta na sirri da ba ta Bari gidan su 'ansani ba.

Kunna wayar ta yi takawo haske babban waya ce Infinix smart HD

Whasap dinta tabude.

Nan da nan sakonni suka fara shigowa.

Sakon Al'amin wani matashin yaro yashigo inda yarubuta.

Aslm gimbiya sarautar mata wlh kwana biyun nan da Bana samun ki bakiji yanda hankalina yatashi ba.

Wai yaushe zaki zone wallahi inabukatar inkara tsotson boob dinki laushi ga tsantsi.

Reply tai masa da.

Hhhhh Allah ko nawa ka san gidan namu ne wallahi ancika tsaro dayawa yanzu babu kowa gida sai anty itakuma tana dakin ta.

Zan san yanda zanyi nafito ba tare da kowa yaganni ba amma fa ba zan wuce minti shabiyar ba.

Nikawai nono na inkana shansa ina fita' hayyacina.

Reply yai mata dasai kinzo inajiranki.

Bata duba sauran message din ba.

Takara kashe wayar.

********

Adamsy Kai tsaye cikin asibitin suka nufa tambaya suka yi Aka nuna musuɗakin da Abdul samad yake.

Ka sancewa ya yi popular agarin ansan baban shi shi ya sa basu hanashi shiga dakin hutun ba.

Faruk ya ce mallam tsaya mana juyowa ya yi ya kalle shi cikin dan ba ta rai ya ce lafiya ?

Faruk ya ce ance baa shiga kuma Kai daga ina kake ne ai ba mu sanka ba.

Be bi takansa ba yashige dakin.

Yarufo kofa.

Kusa da gadon abdul.samada yatsaya Yana ma kallon tausayi.

Kamar ance waiga ya hango gadon da Rahama ke kwance.

Cikin tashin hankali...

Taku har kullum kyauta daga Allah

Karku manta paid Book

Kubiya free Book yakusa karewa*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 0️8️

Cikin tashin hankali arazane ya furta Rahama muryan sa na rawa zufa ce ta keto masa nan da nan jikin sa yadau rawa.

Da ƙyar ya ja kafafun sa yakarasa gaban gadon ta Yana kallon yanda take fitar da numfashi 'bandejin dake kanta idanun sa ya sauka Akai.

Ya ilaihi hatsari tayine koko wani ne ya yi mata wannan mugun aika aikan.

Inhar ba hatsari bane nadau Alwashin ni adamu saina dau fansa wallahi ko uban waye ba zan raga mashi ba.

Cikin kunan rai ya fito dakin Kai tsaye dakin likita yanufa likita yanata rubuce rubuce wasu ordanance daze ba wasu.

Yaji an bankado kofa da karfi firgit ya Mike tsaye dan ya yi fada sai yaga Adamsy ne.

Komawa ya yi yazauna Yana me kallon ikon Allah.

Adamsy dake huci sama sama cikin tsawa ya ce me ya faru da yarinyar c'en dake kwance dakin hutu kuma me dalilin da zaku hadata daki daya da namiji?

Likita bakin sa ne yasoma rawa ya ce sory oga wallahi dakin hutu yacika da jama'a ne.

Kuma dayan yaron ance jikan sarki ne.

Itakuma diyar babban malamin mune ka ga bekamata a cakudasu da sauran jama'a ba ka sancewa matsalar su babba ce.

Adamsy dake masa kallon tara saura kwata ya ce maza maza adauke Rahama daga wannan dakin abata daki inyaso ta Farka acen...

An gama Ranka yadade likita ya ba shi amsa tare da barin abun da yake yi.

Abdul samad ahankali yake kokarin Bude idanun sa...

Soma jujjuya kansa yasoma yi iñda ya ware idanun sa gabadaya.

Ganin iñda yake mamaki ne yacika shi.

Ahankali yadago Kai 'yanata kallon jikin sa dakuma tambayar kansa meya kawosa asibiti dan da Dukan alamu nan asibiti ne.

Sauke kafafun sa kasa ya yi bega takalman sa awajen ba.

Idanun sa ne suka sauka a kan kyakyawan fuskan Rahama dasai haske da sheki yake yi.

Nan da nan Ransa ya yi mugun baci 'cikin fada ya ce wani dan iska ne yahadani daki daya da Mace.

Ganin babu me ba sa amsa ya sa fito Yana tangal tangal jikin sa babu kwari ya fito daga dakin.

Su faruk na hango aguje suka zo wajen sa shida Marwan da aminu kankace me yarima Samad jiri na Diban sa.

Taro sa suka yi tare da tallafa masa cikin kulawa faruk ya ce haba kaikuwa bekamata kafito ba kamata ya yi kasa Akira mu.

Wani mugun kallo mai cike da ma'anoni yarima Samad yake jifan su dukan su.

Marwan nan da nan yasha jinin jikin sa dan ya san waye Yarima Samad Zaki ne Wanda ya gagari namomin daji guguwa yake me tada Taro

Cikin bacin Rai yakai Duban sa a kan faruk tare da tambayar ya AKAI yazo nan asibitin.

Faruk ya ba shi labari yanda Akai 'shiru ya yi na wasu dakiku Yana nazartan kalaman faruk.

Likita dauke da gado sunzo daukan Rahama a canja mata daki.

Kallon yarima Samad ya yi ya ce Ah Ranka yadade harka Farka tun da ka Farka bara abar waccen yarinyar adakin ita kadai.

Cikin bacin Rai Yarima Samad ya ce bangane Me kake nufi ba tun da na Farka

iñda ban Farka ba to me zan mata adakin ?

Likita ya ce sorry bahaka nake nufi ba 'naga Mace ce shi ya sa.

Mace ce kace fa ?

ya tsareshi da idanun sa masu firgita mutum in ransa yabaci.

Me zandauka inhar ina daki daya da ita angayamaka kowama irin kune mayun mata.

Allah yatsare ni da mugun tunani da kukai akaina.

Su faruk rike da baki suna kallon yanda yaketa zubawa likita masifa ba gaggautawa

 Likita ya ce yau dai nashiga uku 'sadaf sadaf yawuce tare da komawa office dinsa Yana goge zufa.

******

Adamsy rike da ka san dake sarawa har idanunsa suna hasko masa ga yarima Samad nan zekama hannun Rahama zumbur yamike.

Ya ce ya ilahi mai ke shirin faruwa Danine.

Tuno wa ya yi Dad dinsa yaturo sa ne dan yaduba Yarima Samad ya sa ya tako inda suke ganin babu su babu alamun waɗanda suka kawo shi.

Direct dakin likita yatafi ya ce docto ina wannan pection dan gidan sarki.

Likita ya ce am sorry Yaki Zama ya ce wai lafiyar sa kalau ba zai kwana anan ba.

Adamsy ya ce oh M'y God wai me nake yi Haka ne har Wanda nazo Domin shi yabar asibitin ba mu hadu ba.

Likita duba mun file dinsa akwai nomba ko adress.

Likita na dubawa ya ce gaskiya babu kodaya.

Jiki asanyaye yabar dakin.

Sheik ya hango Yana ganin sa yagane ka sancewa Yana yawan kallon wa'azin sa a tashar sunnah TV da Afrika TV3..

Cikin sauri sauri yakarasa gaban Sheik tare da risinawa.

Inawuni Sheik ya mai jiki?

Lfyalau alhmdulillah ya ba shi amsa.

Sosa kansa yasoma yi ya ce daman ni malamin Rahama ne 'naji ance ba ta lafiya shine nazo in gaisheta.

Sheik gyara kwalar rigar wuyar sa ya yi yana me kallon sa murmushi ya yi ya ce au kace malamin Rahama na skul ko?

Amma ban sankaba kokaine me koyar dasu geographie.

Dasauri ya amsa Danine Yana sunne Kai.

Godiya muke da ziyara Allah ya saka da Alkhairi yakamata katafi gida dare yayi.

Adamsy kaman Wanda kwai ya fashewa aciki Haka ya juya

 inda ya je wajen motar sa ya iske abokin sa dayabari kwance a motar Yana Waya.

****

Mama tana shigowa asibitin ta tambayi dakin da Aka Kai umergency.

Nuna mata Akai tana tafiya tana karanta sunayen dake rubuce kan kowace daki harta hango Wanda Aka rubuta emegency.

Jikin kofar ta tsaya tana ta tunanin ta ina zata fara ne.

Hango Sheik ta yi tsaye yajuya mata baya Yana Waya da abubukar

 da ya je restaurant yasiyo masa abinci yazo dashi asibiti dan yunwa yakeji'.

Ahankali take tafiya kamar bataso.

Jin takun tafiya abayansa ya sa Sheik waigowa.

Idanun su ne suka tsarke cikin juna shida mama wani irin bugawa kir........

Taku har kullum Kyauta daga Allah Yan special group A kuna comment sossai 'banda Yan special B Allah ya sa dai suna biye dani.

09069080725*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 0️9️

Wani bugawa da tsoro da fargaba yakamata ganin kallon da Sheik ke jifanta dashi.

Sassaita nutsuwar sa ya yi cikin bacin rai ya ce mekikazo neman nan?

Inda inda tasoma bakin ta na rawa ta ce abun da ya faru sharrin shedan ne...

Sheik ya yi murmushi irin tasu ta manya ya maimaita sharrin shedan.

Ya ce ai babu shedaniyar uwa data wuce ki Aisha.

Nabaki nan da zuwa safiya! ki tattara duk wani dakika san naki ne.

Kibarmun gida na.

Ganin asibiti suke beson hankalin jama'a da keta wucewa ya dawo kansu.

Barin ta ya yi nan tsaye ba tare da ya waiwaye ta ba.

****

Salma ahankali taketa taku harda cire takalmin ta tarike ahannun.

Daidai fita gidan ta haska baba salihu da tochla taga lallai barci yake yi.

Sadaf sadaf ta murda hannun kofar tabude tare da maidawa tarufe ahankali'.

Hango Abdul jalil kaninta ta yi ɗa sauri taje ta Labe bayan wata bishiya tana ta huci sama sama

Kallon sa take yi harya shige gida.

Cikin hanzari aguje tabar wajen.

Tana ta buga uban sauri harta Iso kofar gidan 'Al'amin din.

Turo kofar dakin nasa dake zauren gidan su tayi...

Tana shiga ya maida kofar ya rufe.

Washhh Allah daga ji tare da fadawa kan katifar sa.

Dariya yake cikin shigarsa ta jallabiya fara...

Mezan kawo Miki ne lemu ko juice?

Kwabe fuska ta yi uhmmm ai juice dai nakeso amma kadan zan sha.

Shiga ya yi kitchen din dakin ka sancewa Daki daya ne 'amma akwai kitchen da toilet dan daidai dakin samari.

Juice din yadauko a frij din harya dauko magani ze zuba ciki sai ya fasa tunowa ya yi dare ya yi kar Abban su ya leko Yaga Mace a dakin.

Cup din roba yadauko samun ta ya yi zaune Wayar sa ahannun ta.

Tana kallon picture murmushi kwance a kan fuskar ta.

.

Gimbiya ga juice Yana me jawota jikin sa.

Kara narke masa ta yi ajiki wayar dake hannun ta yafadi ba tare da ta Ankara ba.

Juice din ya tsiyaya mata a cup tare da kurba Abakin sa 'be hadiye ba.

Yabude bakin Nata ya juye mata aciki...

Washhh dadi tafada tana mejin kasala na saukar mata..

Uhmmm wlh lemun Abakin ka ya fi dadi tare da daukan cup din.

Takai bakin ta tashanye tass.

.ta ajiye masa cup.

Kara rungumeta ya yi a jikin sa Kokarin zuke zipp

Din rigarta ya fara.

Ba tare da ta hanashi ba' tana kallon sa harya gama cire mata Riga.

Waouhhh gimbiya kinga yanda boob dinki yakara girma kuwa tare da Kai hannun sa 'ya fara ai mata da sakonni mai firgita tunani....

Tuni ta sakar masa kanta dan kwata kwata tamance dare.

Ji ta yi Yana kokarin cire mata pant ɗa sauri tarike hannun sa please kabari.

Cikin narkakken murya idanun ta Sun kada ka san nace maka Wasa kadai da romance zamu ringa yi banda sex.

Bata rai ya yi ya tashi tsaye cikin fushi ya rike kugun sa.

Haba Salma

Kullum ke bakison ki kyautata min.

.

Yi hakuri m'y love nafi son in mukai aure saimuyi.

.

Cikin bacin rai ya ce bakya min biyayya zan aureki.

Yanzu me kake so ayi ne?

Ina son ki ba ni kanki Salma.

.

Shiru ta yi ta ce ka ga Yanzu dare ya yi amma kabari da wata damar ta samu barin garin zamuyi ka ga hk saimu kwana tare.

Wani tsalle ya ɗOka ya dagata sama.

Allah ko baby na?

Shi ya sa nakeson ki.

Bari inmana selfie yadauko wayar sa.

No kar kai mana selfie please na rokeka.

Ajiye wayar ya yi tare da yin kwafa ok to naji.

Bani Alewa ta inkarasha saimuje inraka ki.

Cikiin gamsuwa da Haka ta ce to matso nan.

********************

Mama saka hannun a kan ta ta yi tana ta Safa da marwa acikin asibitin.

Ganin dakin da Sheik yashiga ya sa tamike tare da daukan abincin ta nufi dakin.

Sallama dauke abakin ta tashiga iske shi zaune ta yi ya tankwashe kafafun sa waje Daya Yana lazimi.

Amsa mata sallama ya yi tare da kauda idanun sa Akanta.

Mama cikin magiya tafara kuka dan girman Allah Sheik kayi hakuri ka yafemun kar ka sakeni inka Rabu dani Waze aure ne.

Dago Kai ya yi ya kalle ta yanda taketa zuba magiya..

Waze aure ki Inna Rabu dake.

Keda kikacemin gidan uban naki Zaki koma Inna cika matsa Miki!

Yanzu ga Dama tasamu Saiki tsaya watsi da ita'.

Cikin kuka' ta ce wallahi banda gidan dayafi naka kuma namaka Alkawarin zan canja halayena a kan Rahama.

Da kowa ma.

Dan kaunarka da manzon Allah (SAW)

Kayi hakuri!

Nauyayyen ajiyar zuciya ya sauke ya ce Allah ya yafe mana baki Daya.

Guntun hawaye take fitar wa tana zuba masa godiya da fatan Allah ya sa yagama lafiya da amin ya amsa mata.

Plate tadauko tana kokarin zuba masa abinci.

Kallon abincin yake ya ce suwaye za su ci?

Kasa da kanta ta yi ta ce ai Kai na kawowa.

Bana jin yunwa yabata amsa ataikace.

Sallamar abubukar ne ya sa yakai Duban sa ga kofar shigowa...

Cike da ladabi yashigo yagaida iyayen nasa.

Abba ga abinci na kawo 'yana me kwance ledar tare da dauko plat da cokali yajuye masa 'yakai gaban sa.

Ruwan faro yadauko ya ajiye masa agaba.

Abba!!

Naam !! Yabasa amsa.

Ya jikin Rahama ko zan iya zuwa ganin ta.

A'a ai likitoci sunce sai gobe maza kaje gida Ku tafi kaida jatimar ka.

Ka san Salma kadaice sai anty ba na son barin mata kadai agida babu babba.

Cikin gamsuwa da hakan abubukar ya ce to Abba Saïda safe.

Kallon Mama ya yi cikin bacin rai abun da tayiwa kanwarsa.

Ya ce Mama tashi mu je ko!

Tashi ta yi jiki babu kwari tadau abincin data kawo.

Suka juya tare itada dan Nata.

*******

Yarimad Samad yashigo baban gidan nasa Daya siya daga zuwan sa kanon.

Gidane kerarre na bugawa a jarida babban gidan bene ne mai hawa Hudu.

Ko'ina na gidan tayis ne gabadaya.

Kofar gidan shuke shuken flowar ne.

Me gadin gidan nasa yanata barka da dawowa yarima.

Hannu ya daga masa.

Tare da shiga cikin gidan.

Su Marwan da 'aminu da faruk nabiye dashi abaya.

Tafiya yake ahankali kamar baya son taka kasa.

Yana shigowa falon kujerun falon sa nasa yakebi da kallo

Royal chair.

Ahankali yatako falon tare da Zama kan 3str Yana maida numfashi.

Faruk dasuka nemi wuri suka zauna cikin yanayin damuwa ya ce

Gaskiya ba ka kyautawa kanka Yarima bakada isassen lafiya amma

Kaki Zama hakan ai bedace ba' kuma katsaya sai masifa kake zubawa likitoci kamar sune suka kaika.

Yarima samad kallon sa yake da idanun na sa mekama da Wanda yake abuge.

Cikin kasallaliyar murya ya ce.

To!! dokeni tun da na ba ta maka rai.

Aminu ya kwabe baki ya ce ka ga Faruk Yarima miskilancin nasa sai cigaba yake yi kaji amsar dayabaka.

Wai ka doke shi.

Marwan ya ce cikin zafin ciwo ne mukai shi daki.

Daya samu barci zetashi da karfin sa.

Kamashi suka yi 'yanata fada da masifa Ku sakeni nace saikace wani jariri saiwani Jana kuke.

Aminu ya ce ai in jaririn ne Kai daukar ka zamuyi ahannu.

Cikin su babu Wanda yaKara tanka mishi bare amsa ta biyo baya.

Suna kaisa daki.

Wani daddan kamshi ya doshi hancin su.

Ya gwauraye da sanyin Ac sai yabada mood mai dadi.

Faruk toilet dinsa yashiga yahada masa ruwan zafi ya sirka masa Dana sanyi.

Tare da dawowa falon yakama shi.

Yarima Samad da barci ke damun sa ya ce.

Wai me Haka ne kunki barina in huta.

Muje dai sarkin masifa cewar faruk Yana janya zuwa toilet din.

Tare suka shiga ka ga ruwan wanka Maza kayi wankan nan.

Kallon Faruk yake ba tare da ya ba shi amsa ba.

Ya kauda kansa gefe.

Fita nace ina son incire Kayan jikina

Faruk ya fito Yana murmushi..

Shidai Yarima ba a iya mishi wai in fita ze cire Kaya.

Matar shi tanada aiki

 yafada yayin da ya fito falon kallon Aminu ya yi ya ce mutafi inya fito zeji karfin jikin sa.

Cikin gamsuwa da hakan suka fito.

Mamaki ne yakama Marwan ganin faruk ya sa Key ta waje ya kulle kofar dakin yarima Samad.

Aminu ya ce yaka rufe '

Eh narufe shine banson adameshi cikin dare Yana kallon Marwan.

Inya tashi akwai wani Key din a dakin zebude da kansa.

Aminu ba tare da yakawo komai aran sa ba.

Ya ce to mu tafi.

Marwan da gabadaya hankalin sa yatashi jin furucin da faruk yayi.

......

Wayar faruk ne yasoma ring Yana dagawa mamy ce cikin damuwa ta ce ina

Yarima samad yake.

Faruk cikin son kwantar mata da hankali ya ce ai anma sallame mu mundawo gida saide yakwanta Yana barci.

.

Zuwa da safe zekira inshAllah cikin jin dadi ta ce Alhmdulillah.

Khadija da Ahmad dake tare da ita hamdala suka yi suna murmushi.

Mai Martaba ya sake Kiran ambassado libya.

Ya ce dafatan dan naka yaje.

Eh ranka yadade ya je amma besamu ganin sa.

Ance har an sallame shi yaji sauki.

Ajiyar zuciya mai Martaba ya sauke ya ce nagode sossai.

Dr Abdullahi ya ce inshAllah asatin nan zanje dubo sa.

Daga Haka suka yi sallama.

******

Abubukar shigowar su gida Kenan shida mama.

Tsayawa gun baba salihu ya yi Yana tambayar sa.

Koya ci abinci.

Baba salihu ya ce ainaci akoshe nake.

Mama tawuce su ta yi cikin gida.

Baba salihu na kokarin rufe gida.

Yaji ana turo kofar.

Cike da mamaki dan atunanin sa ko barawo ne.

Haska tochla dazeyi idanun sa ya sauka a kan Salma.

Abubukar ya ce baba mekake kallone tare da nufo inda yake Wayar dake hannun sa yafadi kasa' ya tarwatse ganin.

Salma dayayi cikin........

Taku har kullum kyauta daga Allah

Karku manta

Kubiya Ku karanta cikin salama

Free Book yakusa karewa*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 1️0️

Salma dayayi kamar tsohuwar mayya.

Keeee.

Daga ina kike ne?

Bakin ta na rawa ta ce wajen Amina naje anmso littafi na ɗanaje na iske gidan nasu' akulle.

Baba salihu dayayi mutuwar tsaye ya ce yaushe Kika fita gidan nan ban saniba.

Kasa magana' tayi.

Shiko Abubukar dukawa ya yi yadauki wayarsa tare da maidawa cikin Aljihun sa.

Kallon ta ya yi yanajin zuciyar sa na tafasa kina iya shiga Ayya karki damu ai tun da kawarki ce yadace sossai ma kije adaren nan dubo ta.

Kamar wata munafuka Haka tazo tawuce sadaf sadaf tana gama shiga gida.

Dakin nasa ya nufa.

Yaje yadauko katuwar bulalar Dorina tsabar haushin ta da yakeji.

Man kadanya yashafe bulalar dashi.

Cikin azzama yayo cikin gidan baba salihu na Abubukar dakata kar ka bugeta ina ko tsaya sauraron abun da yake fade beyi ba.

Zaune ya iske mama na tambayar ta inda ta fito.

Fincikota ya yi ta zuba uban kara bakin ta na rawa.

Bulalar Dorina ya rinƙa zabga mata duk inda ya samu ajiki ta har akanta tun tana ihu har muryan ta ya disashe.

Anty ta fito cikin sauri ba ta so fitowa ba amma ganin dukar KAMAR baaza daina ba ya sa cikin hanzari taje tarike hannun Abubukar.

Dan girman Allah ka kyaleta Haka ba ka san inda rai yake ba.

Cigaba da bugun ta yake bakin Nata Saïda yafashe da jini jikin ta ko ina shatin bulalar ne.

Mama takasa magana dan tana tsoron ta ce wani Abu abubakar yahuce fushin akanta duk da tasan yana da hankali da tarbiyya a kan kannensa baya sauraren kowa Hatta Sheik sa masa idanu yake.

Anty kama hannun abubakar ta yi cikin magiya ta ce dan Allah abubakar ka kyaleta inko ba za ka kyaleta ba.

Ni kamin dukar dazakai mata jin Haka ya sa ya saketa yakoma gefe Yana sauke numfashi sama sama.

Cikin kallon da yake jifan ta dashi ya sake Kai Duban sa akanta.

Zaki gayamin inda kikaje kosaina na yankaki agidan' nan.

Wallahi gidan Amina naje banganta ba Sun rufe gida.

Anty talura indai har ba ta kamashi takaishi dakin sa ba.

Dukan da ze sake mata ita' kanta ba ta iya kwatar ta.

Cikin lallami takama hannun sa ta ce zo nan babban yaya Allah yahuci zuciyan namijin Zaki.

Muje inrakaka da ƙyar tajashi suka nufi dakin sa.

Zaunar dashi ta yi bakin gadon sa.

Ta ce m'y Abubukar kwantar da hankalin ka.

Da lallami za ka iya gano gaskiya inda taje ba da duka ko fada ba.

Cikin gamsuw da bayanan ta ya ce afuwan anti ban saurareki ba wallahi anti ina son kannanen nawa fiye da tunanin ki inajin bakin cikin Inga jini na Yana tafka babban kuskure na tabbata Salma gidan saurayi taje anty.

Rau rau ta yi da idanu tana kallon sa' duk da tasan komai a kan Salma amma ba ta taba fadi ba gudun ace sharri take mata.

Eh anty inada yakinin Haka kuma zankara saka idanu sossai.

Anty ta ce kuma fa ze iya zama Haka amma ka tsananta bincike karta lalata mana tarbiyya gidan nan.

********

Rahama yau kwananta uku a asibiti tasamu sauki sossai har anbasu sallama.

Daidai fitar su daga asibitin adamsy YASHIGO shida abokin sa hamza.

Sheik na ganin sa yagane sa 'murmushi ya sakar mishi.

Au kaine?

Cike da ladabi suka duka Dukan su suka gaida Sheik.

Rahama sai kallon sa take taka san idanu.

Tambayar kanta take meyazo nema 'barin wani tunani ta yi ba tare da ta sake kallon su ta ce inawuni cikin cool voice.

Kallon Rahama adamsy yake yi har Sheik Saïda ya Lura da kallon ya yi yawa.

Hamza buga bayan shi ya yi ya ce za su wuce

Adamsy kazo mu juya.

Allah yakara lafiya suka fada a tare.

Ameen thumma ameen

Yabasu Amsa atakaice tare da budewa Rahama mota kujerar gaba tazauna.

*************

Yarimad Samad yashirya tsaf cikin tsadaddan boyel mai masifan kyau alkyabba yadaura saman rigar sa.

 Maroon daidai da kalar rigar jikin sa.

Agogon diamond dake kaman miro yadauko ya saka, turaren mai dan Karen kamshi *oud collection* ya feshe jikin sa dashi.

Kokarin fita daga dakin yake wayar sa tasoma ring dauko wayar ya yi daga Aljihun rigar sa.

Ba tare da ya kalli wayar ba ya daga.

Muryan Maryam yaji cikin ihunn tana tsalle acen iñda take tana fadin ummy kizo ya daga wayar.

Kallon wayar yake dan bema gane dawa yake Waya ba....

Ganin nombar tane ya sa shi hade rai kaman Yaga kashi.

Inawuni Yarima Samad tun da akace ba ka lafiya nashiga matsanancin damuwa a kan ka.

Pls Dan Allah kacemin lafiya ka kalau kozanji dadi.

Shiko Yarima Samad haushi ne yakama shi rashin duba Kiran dabeyiba harya daga.

Cikin tsawa ya ce keee!

Stii ta nutsu kamar yana gaban ta.

Kinga Bana son shashan ci, wai meyasa kullum bakida nutsuwa kina abu kamar me kwakwalwar kifi...

Kalaman nasa Sun ba ta mata rai sossai amma ta dake tana share hawayen da suka zubo mata lokaci Daya da batasan na mene ne ba.

Tsintar kanta ta yi da cemasa yi hakuri Yarima Samad ba zan kara ba.

Amma Dan Allah kafaɗa min abun da nake yi da bakaso.

Tsakii yaketa jerowa akai akai shi dabi'ar sa beson wulakanta ɗan Adam amma kuma beson aimasa shishigi..

Kinga yanzu ba lokacin magana bane ina ummy take?

Tana kitchen bara inkai mata...

Cikin tsauri ta isa kitchen ta mikawa ummy wayar.

Ummy Takara wayar akunne cikin so da kaunar dan yayar ta.

Ta ce

Dana yakake ya jikin naki.

Dasauki alhamdulillah ummy.

Cikin so da begen dan Nata ta ce ka ga Maryam kullum wuni kuka Yarima Samad ba ta da aiki nikam nace wai wannan wani irin kauna ce take maka Haka.

Yarima Samad ya yi kamar beji abun da take fadi dauko wani zancen ya yi ya ce ummy na inakewar abincin nan naki sakwara fa.

Tare da shagwabe fuska kamar yana gabanta

Tun da Kana kewa kadawo gida sai in ringa dafa maka.

Tom ainakusa inshAllah.

Karki damuwa...

Daga Haka suka yi sallama.

Ran Maryam yabaci harda sakin kuka itada da gaske take iya gaskiyar ta...

Ummy ta ce lafiya kuwa?

Ai kece !! Tabata amsa.

Nice nayi me?

Kika kashe wayar ba tare da kin ba ni wayar ba ban gaji dajin muryan sa ba.

Tana zumburo baki waje.

Ummy sake da baki ta ce yau na ikon Allah.

Hade fuska ummy ta ce kaman ba ta taba dariya ba.

Ta kama kunnen maryamta murda da dan karfi Saïda ta saki kara sossai...

Sannan takama hannayen ta sukaje falo.

Zaunar da ita ta yi kan kujera itama tazauna suna fuskantar juna.

Maryam sam abun da kikeyi banajin dadin Haka.

Abdul Samad dan antina ne.

Kin san aure kedashi babu shamaki sai an yi shi.

Amma ina son ki kama darajar ki ta ya Mace...

Kina sake kanki wlh ba zaitaba ganin ki da mutunci ba.

Kidufa irin zubin sa badan jinina bane kina ganin ko Lambar Drever dinsa ba za ki taba samu ba bare shi kansa.

Dan Allah ki nutsu kidaina rawan jiki in kuna Waya kinji nagayamiki.

Gyada Kai ta yi kaman kadangaruwa.

Ummy na ji inshAllah zan gyara amma ki gayamishi ya rinƙa daga wayata dan girman Allah.

Wallahi zan iya mutuwa Inna rasashi.

Ummy zazzare idanu ta yi jin ta ambaci mutuwa.

Janyota ta yi takwanta kan cinyarta tana shafa sumar kanta.

A'a Maryam ba za ki mutu ba kuma nasan matakan da zandauka kwanan nan ko yanaso ko beso saï andaura auren naku keda shi.

Alhaji bushasha mahaifin Maryam ne yashigo cikin farar shadda da farin hula a kan sa.

Tafiya yake cikin sauri sauri alamun mantuwa ya yi yadawo gida.

Sallama dauke abakin nasa yakaraso falon.

Ummy ta ce sannu dazuwa dadyn maryam.

Yaww Yana me kallon Maryam ya ce yar baba ba za kimin oyoyo ba.

Tare da bude tafukan hannun sa alamun tazo.

Aguje ta tafi tarungume shi tana mai ajiyar zuciya.

Kedai ummy mantuwa nayi dafatan kingama abinci inaci zankoma.

Eh Alhaji nagama bara indauko maka.

Amma Alhaji yakamata kasa baki cikin lamarin nan.

Kallon yake yana kokarin cire hular kansa ya ajiye a kan tebur.

Insa baki a kan me Kenan?

Yarima samad mana

Yanason ya fi karfin mu.

Maryam ta ce in Bashi ba sai mutuwa.

Alh bushasha ya ce subuhanallah.

Keee mairo kin tabbatar kina son Yarima Samad.

Cikin shagwaba ta ce daddy kafi kowa sani.

An gama Maryam kin auri Yarima kingama Nida nake dan siyasa nasan hanyar dazanbi saikin aure shi.

**********

Faruk ke Drever motar sossai cikin kwarewa.

Yarima Samad dake ɗAnne ɗAnne a laptop dinsa acikin mota.

Ya ce Taya zan san sunan

Malamin da akace nanne farin cikin gidan namu yake ?

Kubiyo ni labari nacen gaba

Shin yarima Samad meyake nema.

Ya 'alakar Rahama da adamsy ze ka sance.

Salma......

Saide kun biyo ni karku manta *🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 1️1️

Tafiya suka yi mai dan nisa kafun suje rijiyar lemu.

Daidai wani babban masallaci juma'a suka yi parking motar' nasu.

Yarima kansa aduke yake ba tare da ya san Sun iso ba.

Faruk daidaita parking ɗin motar' nasu ya yi tare da zagayowa yabude wa Yarima Samad mota.

Dago Kai ya yi YA CE am sorry ashe har mun iso...

Laptop dake kan kafafun nasa ya ajiye kan kujerar motar' tare da dauko medical glass ɗin sa ya sa.

Ba ƙaramin kyau shigar dayayi ya amshe shi sajen nashi lub lub kwance a kan fuskar shi Yana sheki.

Cikeda da izzar sa da cikar haibar sa ya sauko daga motar'.

Tsaye yake yanata kallon yanayin unguwar da tsare tsaren gine ginensu.

Kallon massalaci dasuke sallah juma'a ya yi yanayin tsarin massalacin kwarai yaburge shi.

Faruk ya ce Samad mutafi mana ka san akwai ayyukan da zamuyi a kamfanin da kakeson kabude ko.

Marwan dake gefen nasu tsaye ya ce Amma kuma ai yakamata mu koma gida tun da kullum sai munje massalatai amma shiru kake ji babu amsa yanzu kila ma baya kasar nan 'mune muke wahalar banza.

Aminu cikin bacin rai ya ce wlh kaide Marwan ko ya'akai dan bakin cikine kullum bakason ci gaban mu.

Waima dole ne saika fito kazauna gida mana haba.

Duk kasashen da muke yawon zuwa kaine kullum kake mita adaina yawo neman Wanda baya raye.

Taya ka san baya raye Kenan ka san wani abune a kan mutuwar sa.

Haba dan Allah idanunsa Sun kada ji yake kamar yakama Marwan ya shake masa wuya sai ya daina numfashi.

Yarima Samad duk ihun da Aminu yake kan sa harya fara sarawa kwata kwata beson hayaniya.

Ganin Aminu Yaki Bari sai masifa yaketa zubawa

Hannu ya daga alamun ya isa

Shiru kake ji Dukansu babu Wanda ya yi magana.

Mai gadin massalacin ne yazo gaban su cikin girmamawa Yana fuskantar Samad YA CE ranka yadade wani taimako za a baku ne.

Aminu ya amshi zancen da eh wani bawan Allah Muke nema Allah ya sa ka san shi.

Mai gadin YA CE to Allah ya sa nasan sa ya sunan sa.

Faruk YA CE sunan sa.

Alhaji salihu turaki

Jinjina sunan mai gadin massalacin ya yi ya ce gaskiya ban san shi banma taba jin suna me kama da nashi ba.

Yarima samad yakaraso gaban sa cikin idanun sa dasuka kada jajir jin amsar mai gadin yabasu

Amshi wannan Kati nane

Nombar wayata nakai dan Allah duk sanda kasamu labari a kan wannan sunan ka Kira ni.

Namaka Alkawari siya

Maka gida da mota.

Mai gadi ya girgiza kwarai dajin Alkawarin gida da mota kallon Katin dake hannun sa yayi.

Yaga

Anrubuta Yarima Samad salihu Turaki.

Tare da adresse ɗin gidan sa da nombar Waya.

Faruk ya ce muna iya komawa cikin motar direct kamfanin zamu nufa muga Meye tsare tsaren da Aka fara.

Yarima Samad cikin gamsuwa da Hakan yakoma motar nasu...

.

Daidai suna fita layin.

Daidai da isowan Sheik dan gabatar da sallah la'asar.

Kallon motocin Sheik yake.

Jikin Lambar motar anrubata Yarima Samad.

Mai gadi ya ce Ranka yadade wayannan mutanen bincike sukazo yi.

Sheik dake kokarin daukar buta dan yin alwala ya ce a kan mekenan suke bincike...

Nuna masa Kati da yabasu ya yi tare da sunan Wanda suka ce suna nema...

Sheik ya ce basu nuna maka hoton sa.

Kash wlh ban tambaya ba.

Dan nasan Wanda suka nema bama a unguwar nan yake ba.

Daidai da isowar baba salihu shima yana sauri karya rasa Sallah.

Yaji Sheik na fadin

To ai a unguwar nan Kaf.

Babu wani Alhaji salihu Turaki.

Gaban baba salihu ne ya tsananta bugawa cikin dakiya yakaraso wajen nasu yanayin sa ya canja jiki babu kwari.

Buta yadauko ya yi Alwala Sheik ya ce dan hanzarta mallam salihu yanzu zan tada sallah.

************

Bayan kwana biyu.

****

Rayuwa ta sauya sossai agidan iñda mama da Anty suka zama kamar kawaye damacen Anty saukin Kaine da ita mama ce ke nuna mata tsantsar kiyayya duk da boye halin Nata ta yi dan tasamu Sheik ya sauko daga yajin dayai mata.

Duk ranar kwanan ta 'falo yake kwanciya hakan ba ƙaramin bakanta Ran mama yake ba.

Amma ta shanye...

Cikin hanzari Rahama ta fito toilet daure da towel a jikin ta 'agogon dake makale bangon dakin nasu taga Karfe takwas saura kwata.

Ba tare da ba ta lokaci ba '

Tashirya tsaf cikin Kayan makarantar ta 'hijabin makarantar tasu bleu color dashaya guga tasaka cikin hanzari.

Salma sai wani cika take' tana batsewa Ganin yayar tata ta yi shiga me kyau.

Cikin hanzari suka yiwa iyayen nasu sallama Domin yau za su fara jarabawa.

Adamsy yashigo aji ka sancewa yau shine zefara musu jarabawar.

Baza idanunsa yaketayi a makaranta dalibai nashigowa amma sam bega Rahama ko kanwarta ba Rasa nutsuwar sa Yayi.

Harya shiga ajin ya kalli dalibai dakowan su ashirye suke tsaf dan afara.

Asiya kawar Rahama yakira ya ce tasameshi awaje babu musu...

Ta fito tana kallon yanayin sa Daya canja.

Zararan idanun sa masu kashe garkuwan jikin Yan mata ya zuba mata.

Tare da tambayar ta meya Hana Rahama zuwa makaranta ne kuma yau jarabawa ta karshe.

Zata Bude baki tayi magana saika ga

 Rahama Sun kunno Kai itada Salma.

Tafiyarta yake kallo Wanda wasu za su iya cewa na takama ne 'amma itakuma wannan yanayin halittar ne Ko ina na jikin ta na motsawa.

Kafarta sai ta daga Daya Ta tsai gaita sannan tasauke dayan.

Ba ƙaramin tafiya da imanin sa tafiya ba....

Harsuka karaso gaban sa cike da ladabi ta gaishe shi.

Kunya ne yakamashi Ganin ta tsareshi da idanu.

Lfyalau yabata amsa tare da juyawa ajin.

Rahama da asiya da Salma da bakin ciki ya dabaibaye mata zuciya.

Ganin kallon da adamsy kewa Rahama..

Kusan karfe goma Aka fito brek...

Asiya da Rahama zaune suke kar kashin Wata bushiya suna tattauna yanda lecture da zasuyi nex

Tsintar muryan adamsy suka yi tsaye akansu.

Ya ce bedace dake ba Rahama kizauna ke kadai ba tare da masoyin naki ba.

Murmushi asiya ta yi Ganin Rahama tasha mur lokaci Daya.

Zama ya yi gefen su.

Rahama na kokarin tashi.

Asiya tariko hannun ta pls dan girman Allah dawo ki zauna kin san wulakanta ɗan Adam baya cikin dabi'ar ki.

Bawan Allah nan yanason ki Rahama yakamata kibashi dama.

Adamsy yakaraso gaban Rahama tare da durkeshewa akasa Yana kuka mai taba zuciya...

Dan Allah Rahama zuciya ta tana azabtuwa saboda Rashin kulawar dakike ba ni zan iya mutuwa a kan ki dan Allah ki kauna ceni.

Rahama jikinta yagama yin sanyi takalli Asiya ta ce pls kigayamai yatashi kada idanun mutane yataru a kan mu.

Wallahi Rahama ba zan tashi ba agabanki ba saikin ce kin amince dani.

Kallon asiya ta yi tana kwabe fuska ranta aba ce.

Asiya daga mata Gira ta yi alamun ta amince kawai.

Zazzakar muryanta ya tsinta tana fadin katashi na amince.

Wani tsalle adamsy ya ɗOka tare da tashi yabar wajen cikin zalama.

*******

Amina ta ce Salma kinkosan ABUN DA ke faruwa kuwa '

A'a saikin fada inajinki!

 Wallahi Adamsy da Rahama soyayya suke na ban mamaki ke dazun zokiga yanda ya diririce a kan ta harda dukawa akasa.

Wani katutun bakin cikine ya ziyarshi Zuciyar ta Wasu zafafan hawaye ne suka silalo mata a kuncin ta.

Soyayya fa kikace...

Taku har kullum kyauta daga Allah

Karku manta

09069080725*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 1️2️

Ankusa gama free Book

Soyayya fa kikace

Nashiga uku ni Salma me natsaya kallo da har yayata zata samu saurayin da duk fadin kanon nan ban taɓa ganin Wanda yakaishi haduwa ba.

Dafa Amina ta yi cikin kuka' ta ce yazanyi ne Amina wlh ina son shi.

Kuma wallahi ba zan taba barin Rahama ta aureshi ba 'uban kuturu ya yi kadan bare na makaho.

Asiya kwabe baki ta yi ta ce to me Zakiyi bayan aikin gama ya gama ɗa dukan alamu itama Rahama tanason shi wlh.

To ina saurayin naki Al'amin yake ne.

Tsaki Salma ta jero Al'amin fa kikace in ana maganar Mazan kwarai pls kidaina sako shi.

.ni dai kiban shawara yazanyi ne.

Asiya tadan numfasa kamar me lissafin ta ce nasamo mana mafita Daya ce.

Abu daya ne kawai kifito a mutum ki gayamai masa kina kaunar sa.

Inhar be baki hadin Kai ba 'uhmmm munada hanyoyi dayawa.

Tafa hannu suka yi Salma ta ce shegiya kawata shi ya sa nake mugun sonki wlh.

Amma wannan tsinanniya yayar tawa mai farar kafa yo aidole ince mai farar kafa wlh duk inda zata sa kafa to nice da faduwa ina dalili tana Jamin bakin jini.

Wallahi badan mama tahaifeta ba ɗa tuni nasan yanda nayi Aka koreta gidan nan.

Uhmm Salma Kenan yar uwar ki ce ta jini ki sassauta mata mana.

Aji suka koma hankalin Salma sam baya jikin ta ta lula duniyar tunanin adamsy.

Minti arba'i suka dauka kafun da bisani Aka tashi.

Rahama daukar jakar Salma ta yi tana murmushi ta ce m'y kanwaty mu je ko yau naga ko kulani bakiyi ba tun da mukazo skul.

Harara ta watsamata andai ji dashi tun dazun da idanun naki yarufe a kan Adamsy bakisan dani ba saï Yanzu.

Sakaka da baki asiya da Rahama suka yi suna kallon ikon Allah 'amina dariya tabushe dashi tana gyara safar kafarta ta ce anty Rahama ki rabu da Salma fa aljanun ta ne suka tashi.

Kusan Dukan su dariya suka kyalkyale dashi Wanda hakan ya Sosa Ran Salma 'hawaye suka gani idanun shar shar.

Rahama tarufe ta ce my kanwati ke bakisan Wasa bane 'pls kiyi hakuri wallahi zolayar ki muke...

Zumburo baki ta yi waje ta fice gaba abinta.

Rahama ta ce kinga Asiya banga tazama ba tun da Salma ta fice wlh karta kiramun ruwa ban gama warkewa ba.

Dariya asiya take' saï da kuncin ta ya lotsa.

Kallon Amina ta yi ta ce muna iya tafiya ko tun da tagudu tabi yar uwar ta.

. Adamsy yashigo kaman anjefo shi ya ce wai ina Rahama take' ne inata jiran Inga kyakyawa fuskarta.

Ai Rahama Yanzu tabar nan inaga bama ta yi nisa ba.

Cikin hanzari yabar su...

Sauri sauri yake ya hango daga can nesa itada Salma suna tafiya hannun su tsarke cikin juna...

Shan gaban su yayi.

Cikin dariyar sa me bayyana zallar kyawun sa ya marairace fuska.

Ya ce wana kama '! Nace '

Wa na kama.

Rahama murmushi ta sakar masa Saïda kuncin ta ya lotsa.

Pls Adamsy inkana son ganina kazo gidan namu mana '

Ok gayamin lokacin dazan zo yatsareta da manyan idanun sa.

Bayan la'asar lokacin Abba na Yana nan saika zo ka nemi izini.

.waouh yau ni me sa'a ne.

Salma banda wani katutun bakin cikine ya tokare mata mako garon wuya.

Da ƙyar tafurta yaya adamsy kaide kazo anjima tun da anti tabaka dama.

Kama hannun Rahama ta yi sukaci gaba tafiya shiko kallon su yake.

Har suka ba ce masa dagani.

************

Yarima samad

Zaune yake a babban office din sa yanata juyi kan kujerar mai Lilo sai juyawa yake yi yatsar sa Daya Abakin sa..

Scretaria ce cikin shigarta na rike da siket dinki atamfa sossai siket ɗin ya fito da shap ɗin jikin ta.

Rabin nonon ta awaje ka sancewa crista ce...

 Ta shigo office dinsa

good evening mesieur can I help you?

Wani harara ya watsa mata Wanda tuni hantar cikin ta ya kada kallon yake daga sama har kasa ya ce.

What are you looking for at the moment because I didnt allow you to come in here

Sorry sir tafurta tana kar kada mazaunan ta...

Kauda kansa ya yi daga kallon Nata harta fice daga office ɗin.

Jin Kiran sallah la'sar ne ya sashi cikin hanzari shigo toilet ɗin office yadauro Alwala...

Direct motar sa ya ja zuwa babban masallaci rijiyar lemu Haka wa yaji wannan masallacin ya kwanta masa' Arai da ya ringa zuwa sallah anan.

Ba tare da cikin hanzari yaketa gudu kada ya rasa Sallah....

Daga can baya baya ya paka motar daidai lokacin ne Aka tada sallah.

Agaggauce yashiga masallacin Yana sahun baya na karshe daga can karshe Gini.

Baba salihu Yana daidai bayan yarima Samad ka sancewa shima ya yi latti.

Kallon keyar Samad yake yi harsuka idar da sallah.

Ana kokari sallame sallah yaaaa.

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishaɗantar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,, 𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)

Kai dajin sunan labarin ma ka san basai an tambaya ba.

*(ƘADDARA CE)*

*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane ƘADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo ba ta yi magana ba ta damƙi hannun Sultana Ta ce" Ke Sultana mu je ki nuna a hanyar shara-mansoor ɗin Uban waye ya faɗi miki wannan maganar yau saina wuƙance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...

*Dandano!Dandano!!*

Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta ɗago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Ta ce Rahama kiyi Haƙuri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi haɗe da zallar bakin ciki, take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da faɗin. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da ƘANWATA taimun ya Allah ka..

Ga maru buƙatar wannan novels ɗin za su iya tuntuɓar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573

 Nomal. guda ɗaya N 300 ne

guda biyu N 500 ne

Special guda ɗaya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne

Zaki iya biyan kuɗin ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 1️3️

Ana kokarin sallame Sallah ya juya da kansa baya agigice buzun Nadin dake kansa rufe fuskarsa ya yi dashi Yana mai tasbihi.

Yarimad Samad gaban sa ya tsananta buga Gab Gab da ya tsananta bugawa da karfi nan da nan ya nemi nutsuwar sa ya rasa Kokarin waigowa bayan yake ɗaidai da tashin baba salihu cikin hanzari da sassarfa ya fito gaban massalacin duk ya dimauce 'banda bugawa babu abun da zuciyarsa ke tsanantawa.

Tafiya yake da dan sauri sauri kansa aduke.

Cikin hanzari yarima samad ya fito Yanata waige waige ina bawan Allah Daya gani yanzu wala Allah ya san Wanda yake nema.

Daga can nesa ya hango mai rawani da dan karfi yabuda Dukan muryan sa yafurta.

Mallam buzu dan Allah dakata.

Babu ba ta lokaci ya isa gaban mutumin kallon sa yake Yana cije labbansa.

Mutumin yatsareshi da idanu.

Bawan Allah lafiya kake kwadamin Kira

Jikin sa ne ya yi mugun sanyi ganin Wanda yake tunani gani bashi bane.

Afuwan Dan Allah damar tambaya ce dani.

Koka san Alhaji salihu Turaki.

Mutumin girgiza kansa ya yi alamun 'A'a gask ban san Shiba kila ma baya unguwar nan.

Musabaha suka yi shida mutumin iñda yajuya.

Baba salihu dake Labe jikin Wata bishiya ya boye hawaye masu zafi yake silalo masa' idanun sa...

Cike da tausayi yake kallon Yarima Samad harya ba ce masa da gani.

Babu ba ta lokaci ya isa gida 'banda kuka' babu abun da idanunsa suke fitar wa.

Iske Sheik ya yi farfajiyar gidan Yana koyar da dalibai

cikin muryansa me kama da Wanda yake cikin damuwa ya ce.

Ya ce ya Sheik kozan iya zama in saurari kira'ar da kuke yayinda yake kokarin zama kan Capet ɗin dake malale tsakar gidan.

******

Yarima Samad Allah ne kadai yakaisa gida dan tuki yake sam baya sanin iñda ya sa gaba.

Knockin ya yi Aminu yabude masa kofa Rabashi ya yi cikin azama direct ya yi dakin sa ya nufa.

Aminu sake da baki yake kallon sa Yana haurawa sama.

Rage Kayan jikin sa ya yi dagashi sai boxer Yana shiga toilet ya sakarwa kansa ruwan mai mugun sanyi Yana ratsa tun daga tsakiyan kansa zuwa bargon jikin s..

Akalla minti Arba'in yadauka.

Daidaituwan numfashi ya sashi fitowa da towel a jikin sa.

Fadaddan kirjin sa Wanda gashi ya kwanta lub lub gaban miroir yanzauna ta'cikin madubin yake kallon kansa da idanun sa da Suka canja launi.

Oh ni Samad shekara nawa ina yawo' kwaro kwaro duniya yaushe zan samu cikin burina.

Abbana dan Allah ka bayyana nasan gaskiya za ta yi halin ta 'yasaki marayan kuka' rike da rigarsa ahannun Yana kallon kansa ta madubi.

Yanda idanun sa suka canja launi dan kuka'.

Faruk dauke da sallama bakinsa yashigo kallon yarima samad yake ya ce yauma sokake kayi abun da kasaba ne.

Samad inada yakinin bayan wuya saï Dadi kuma InshAllah mafarkin ka sai ya tabbata kaide karmu gajiyawa tare da dafa bayan yarima Samad Daya bashi baya 'suna kallon juna ta cikin madubi.

Yarima Samad tashi.yayi ya rungumi faruk dukansu kuka' suke babu mai rarrashin' sa.

Faruk irin abokan nan n'e

Na amana Wanda azamanin nan damuke ciki samun irin sa yana da matukar wahala...

*******************

Rahama kwance jikin Anty tana ba ta labarin adamsy 'yanda suka yi duk ta fada mata ba ta boye mata komai dangane da Rayuwar ta.

Anty dariya take mai dan sauti'. Ashe dai mun kusa daukan suruki yata.

Shawara Daya zanbaki kirike martaban gidan nan.

Kuma ainaji mahaifin Ku ya ce kuna gama karatu da sati Daya zemuku aure..

Rahama zazzare idanu tashiga yi tare da tashi daga jikin Anty ta maimaita aure ai a iya sanina ban fidda mijin da zan aura ba..

Wanda nakeson gabatarwa ayau din nan zezo gidan nan Kuma kin san me Anty ?

Girgiza Kai ta yi ta ce saikin fada Rahama.

Wallah anty tun ranar Dana fara ganin sa 'naji yakwanta min Arai 'nakamu da sonsa amma banta nuna masa ba...

Saboda kin san Mazan yanzu dole saika kama darajarka za su kama maka. Naka.

Anty murmushi ta yi tana me gyara zamanta sossai cikin so da kulawa ta ce karki damu nasan ke wacece banda matsla akanki.

Idan yazo ki gabatar dashi kinga shi ke nan mallam ba zai baki Wanda bakiso ba.

Cikin shagwaba ta ce anty na Allah yabarmun ke 'amin ta amsa yayinda suka ji wai ana sallama da rahama wani yaro ne da ba zai wuce shekaru goma ba.

Mama ta ce waye ke sallama da ita.

Salma ta karbi zancen au mama baki Sani ba ai adamsy ne abokin dadiron Rahama ne...

Kwabe baki mama ta yi to naga ta iñda zata fita gidan nan.

Rahama dake tsaye jikin kofa duk abun da suke fadi a kan kunnen ta.

Cikeda nutsuwar ta takaraso gaban mama.

Dan Allah mama kibarni inje wallah ba zan wuce minti shabiyar ba nadawo...

Mama banda harara babu abun da take jifan Rahama dashi.

Anty rike da buta ahannun ta kallon Rahama gaban mama tana magiya ya sa Takarasa wajen tare da Kamo hannunnta.

Cikin isa da takama ta ce Rahama sheik tun kina yar karama yabani ke dan Haka hakkin kula dake Yana kan wuyana.

Yarki kirki tafi Allah ya yi maki Albarka.

Da hanzari Rahama tawuce hartana tuntube.

Anty ba tare da ta kula mama ba tajuya tashige ciki.

Mama kasa maganatayi ta ce Amma Sa'adatu yar iska ce.

Shiru shiru fa ba tsoro bane gudun magana' ne.

Salma wani bakin cikine ya ziyarceta fitan da Rahama ta yi shiga daki ta yi ta rinƙa zubar da duk abun da tagani adakin uwarta cikin hasala tadau takalmin ta jefa kan miro dakin nasu' tuni ya fashe wargas.

Karar buga Abu ya sa mama cikin hanzari shiga dakin.

Rike hannu Salma ta yi Wanda tafara buga hannayenta abango har suna jini...

Cikin zuciyar ta dake tafasa ta ce wlh Rahama daki auri adamsy na gwammace in yi ta yawo tsirara.

Mama ta ce haba Salma karki mance Nina haifi Rahama yazaki ringa furta irin wayanna kalaman agabana.

Yi hakuri zansar matakin dazan dauka akai.

*****

Adamsy cikin shiga ta Alfarma kananun Kaya yake sanye dashi.

Ganin Sheik na sallamar dalibai cike da ladabi ya gaishe shi.

Fuska asake ya amsa.

Rahama hango Sheik da tayine da Adamsy ya sa ta Labe bayan kofa tana sauraron su'.

Inawuni ya Sheik daman nine nakeson yar gidan ka Rahama in kaban izinin ina son abani damar tsayawa da Rahama kansa aduke.

Sheik kallon sa yake dama tuni ya dago lagon sa.

Gyaran murya ya yi ya ce.

Adamu agaskiya ka makara dan Rahama harnayi mata miji nanda wata Daya bikin ta ɗa an gama makaranta nanda sati uku.

Adamsy da Rahama kusan a tare wani jiri ya fara dibansa...

Cikin kunan rai da tafarsa da zuciyar sa keyi ya ce

Amma sheikk

Hannu ya yi masa

Dakata.........

Taku har kullum kyauta daga Allah

Karku manta

Free Book kuke karantawa*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 1️4️

Dakata!!!

Nacemaka na yi wa Rahama miji kobaka fahimta ne?

Jikin Adamsy yadau rawa hawaye shar shar wani nabin wani a kan fuskar sa.

Sheik harya juya zeshige gida ya ce dan Allah Sheik kaimin wata Alfarma Daya.

Juyowa ya yi Yana fuskantar shi inajinka ya ba shi Amsa yatsare shi da idanu hannunsa na jan tasbaha.

Adamsy kasa da murya ya yi cikin rauni da kunan da zuciyar sa keyi ya ce dan Allah ina son Inga Rahama kataimaka namaka Alkawari daga wannan Rana ba zan sake zuwa ba.

Cikin gamsuwa da bayanan sa dan matuka yaba Sheik tausayi amma shi ba zai iya canja Alkawari Daya dauka ba.

Rahama najin takun shigowar Sheik aguje takoma gida.

Zuciyar ta namata kuna ta rasa ne mene ne damuwar ta!

 bakin cikin Wanda akace zata aura ne da batasan shi ba koko bakin cikin rabasu da Adamsy da Sheik ke shirin yi ne.

Tunanin ta ne yakatse jin muryan Sheik Yana cemata tashi kije kinada bako awaje.

To Abba ta Amsa masa yayin da tabar gidan cikin sanyin jiki da fargaba

Mama kwabe baki ta yi Ganin Sheik yatsaya Yana kallon wucewar Rahama.

Tsakiiii yaji ta jero masa Wanda firgit ya waigo Yana kallon ta.

Sai hura hanci sama sama take ta ce banda cin amana ai saurayin Salma ne ya za ai kace Rahama taje saboda Allah.

Beko bi takanta ba wucewar sa ya yi dakin anty dauke da sallama Abakin sa yashiga.

Anty murmushi a kan fuskanta ta ce lale lale da sadaukin Maza.

Lemun juice ta tsiyaya masa a cup.

Ta Mika masa Yana sha Yana lumshe idanu.

Kallon kyakyawa fuskantar yake ya ce Sa'adatu yau dakin ki nake ko dakin maman Salma.

Dariya tabushe dashi ta ce au Kai yau ba ka san inda za ka kwana ba.

Yau maman Salma ce da kai angona.

Rahama na ji yau ta ce zata gabatar da surukina 'nasan ma yanzu yazo.

Tana me fuskantar sa.

Sheik gyara zaman sa ya yi Yana fuskantar ta.

Anty na yi wa baba salihu Alkawari zanba dansa auren Rahama

 data ta gabatar da adamu kafun Alkawari Dana dauka tabbas babu abun da zehana inbashi Rahama.

Jikin anty ya yi mugun sanyi cikin yin kasa da muryanta cike da ladabi.

Ta ce ba ka san asalin baba salihu ba shine za ka yarje masa za ka ba dansa

 yarka yarinya mai hankali da nutsuwa ni dai gaskiya ka tsananta bincike Akai.

Sheik yanuna mata Zuciyar sa Haka kawai ya yarda ba mutumin Banza bane Kuma dan NASA kamar garkuwa ze zamewa Rahama.

Kidaiyi fatan Alkhairi dan ni inayawan mafarki a kan Haka InshAllah Alkhairi ne.

Anty tayi jigum cikin tausayin Rahama ba ta iya ja da mijin ta ta ce Allah ya sa Haka shine Mafi Alkhairi.

Amma ni amatsayina na uwar Rahama Ina son ya gabatar mana da dan nasa inko be gabatar ba.

Gaskiya Sheik kayi hakuri ba zan amince ba inbashi yata ba.

Kallon ta yake yau' ne karo na farko dayaga bacin rai kwance a kan fuskarta kuma ya san kowanene indai mai hankali ne irin tunanin zeyi' wayewarta da hikimar ta wajen furta lafazin bakin ta 'ba ƙaramin burgeshi yake ba.

Cikin muryan sa dake Nuna gamsuwa da zancen nata ya ce inshaAllah sa'adatu zan zauna da baba salihu Yanzu fa dudu sati hudu yarage indaura mata aure.

Nibana bukatar lefe ko wasu Al'adun Banza.

Sadaki ya wadatar.

Sa'adatu fadada fara'ar ta tayi ta ce kokai fa ya Sheik Amma....

Shiiiiiii

Basai kince komai ba na ji bukatun ki kuma na dauka.

Murmushi ta sakar masa.

Mama dake Labe kofar dakin ta Kasa kunne Amma ba ta jiyo me suke fadi dariyar su kadai ta ji.

Cikin kunan rai tabar wajen tana ta zage zage maciya Amana yau' kwanan daki nane Amma Yana c'en makale jikin ta Suna shashan ci.

Duk Abun da Abun da take fade sheik najin ta.

Murmushi Yayi..

.....

Rahama jiki asanyaye takaraso kofar gidan.

Ba ba ta lokaci ta iso inda yake tana karemai kallon Ganin yanda ya susuce.

Inawuni yaji ta furta jajayen idanun sa dasuka canja launi zuwa ja.

Yazuba mata.

Ya ce

Rahama dama an Miki miji shine baki faɗa min ba?

Kasa da kanta tayi ta ce nikaina ban san da zancen nan ba Saida ka aika akirani.

Rahama kinkosan zuciyata tare da taki take bugawa kuwa Rasaki daidai yake da rasa rayuwata kiyi wani Abu akai dan Allah narokeki.

Durkusa ya yi da kafafunsa duka biyun akasa.

Hannun tayi masa alamun yatashi.

 Ba musu yatashi.

Zazzakar muryan dake sashi nishadi yaji tana fadin.

Tun Ran Gini tun Ran zane adamsy.

Zamu yo rabuwar kadaici.

Kadau hakuri!!

Kaddara ce tasauka.

Duk mai Imani yakamata ya rungume ta.

Tsawa....

Ya daka mata haba Rahama daman nasan bakya sona na tabbata Wanda zaa bashi ke.

Besan darajarki ba besan mutuncin ki nine nan zankare maki su.

Pls narokeki karki rabu dani ahaka 'askul dan Allah kiringa kulani kozan ringajin saukin abun da ke damuna.

Gyada masa Kai tayi alamun gamsuwa da bayanan sa.

Kaga nizan koma minti goma shabiyar nadauka agida kuma suncika.

Bata Jira cewar shi'' ba tajuya cikin gidan.

Kallon ta yake ya ce inaa....

 Bari zankira hamza Inna koma gida wallahi sai ansan mafita 'yana kokarin shiga mota.

Salma ta dakatar dashi.

Fuskarta akumbure alamun tasha kuka sossai.

Adamsy Dakata kaji ai ingaya maka wani Abu da ba ka sani ba.

Girgiza Kai ya yi ya ce inajin ki my kanwati kamar yanda yaji Rahama tana kiranta.

Wallah antina bin Maza take kuma Wanda Sheik ya ce zata aura shine Wanda ya taba cire mata ciki.

Kai ma ka san adalci irin ta mahaifin mu ya ce tun da shiya Santa ya Mace to lallai shine ze aureta dan ba zai iya abun kunya ba.

Tsawa....

Taji ya daka mata

 tare da dauketa da wawan mari.

Ni Zaki gayawa zancen banza a kan yayarki to Ina son ta Ina son ta Ina son ta Kuma wallahi na tabbata sharri kike mata in gaskiya ne kibani shaida a bayyane mana.

Rike da kuncin ta ta ce Niko Salma InshAllah zan Nuna maka ko wacece Rahama.

Ok yabata amsa tare da shiga motar tasa yajata fuuuuuu yatada mata kura a kan ta.

Jikin asanye ta shigo gidan tunani take meye mafita yazatayi taba adamsy shaida a kan Rahama dan wallahi bazata Bari ta auri dan gidan ambassado libya ba ita ko dan me kanti ba ta samu ba

Sai Al'amin da gidan nasu' ciyar dashi ake.

*********

Kasar kwatano.🇧🇯

Mamy jiki ya warware sossai kaman ba 'ita ce takejin jiki sossai ba.

Ahmad ne zaune agefen Nata Yana chat.

A Badoo

Hotunan Yan mata kala kala yake kallo yana dariya inda Yaga wata buduwar rabin nononta awaje.

Murmushi yake ya ɗAnna mata like.

Khadija data shigo bakinta dauke sallama tana kallon yanayin sa ta ce haba yaya ina sallama hankalin ka nakan Waya.

Beko saurare ta ba.

Mamy cikin tsare gida ta ce waikai Ahmad ba za ka ajiye wayar nan bane.

Kaje airport saboda Abdul samad yamin korafi ba ka kula masa da dukiyar sa.

Duk sati yakamata Kana check balance ɗin kudin ɗasuke shiga.

Kuma abun da suke bukata ka ga daga wajen ka ne za su samu.

Ok mamy amma saï gobe zanje ko 'hankalin sa nakan wayar bedago Kai ya kalle ta ba

Ranta ne yabaci cikin ranta saï fadi take l'alle yakamata insan me yaron nan yake aikatawa awaya.

Afili kuma ba ta kara bin takansa ba.

.

Fulani zaune kan kujera 3ster kaman yanda tasaba kaman ta gado ta sha ado da manyan gold a jikin ta.

Baba nasiru mijin nata ne yashigo fuska dauke da murmushi kinga Yarima samad bedawo ba.

Kafun yatafi ya cemin sati zeyi'.

Murmushi ta yi tana me jujjuya idanun ta ta ce kaima ka san ba zai dawo akusa ba' watakila ma shi ke nan har abada shida masarautar nan.

Ai ina gayamaka ba zan taba barin sa ya yi aure ba shi ya sa kullum nake zuwa gun boka markau.

Yana kara zuzuta masa kiyayyar Maryam aransa.

Haba ai ba zaiyu ba.

Baba nasiru murmushi ya yi ya ce amma fulani ke maciji sari ka noke ce.

Bata rai ta yi ta ce amma aiduk mugun ta, ta kafini.

Yi hakuri ban ce kimun tone tone ba yanzu de ina abincina yake Yana me Mike kafafun sa kan kujera.

**

Mai martaba Sanusi turaki ne zaune adakin sa.

Uwargidan sa tana masa fifita cike da nutsuwa. Kwantar dakan sa ya yi bisa kafafun ta ya ce

Gaskiya kibari mu daurawa Abdul samad aure mana kin san burina ba zai cika ba saï yana da iyali.

Hajiya hauwa ta ce haba ranka yadade baya son yarinyar nan asaurara masa mana dole ne auren zumunci.

Kabarshi yazabo Wanda yake so.

Yaran Zamani baa masu Haka.

Murmushi irin tasu ta manya ya yi ya ce haba hauwa wannan miskilin yaron kina ganin har akwai matar daze gani ya ce yanaso nasan Haka bame yuwa bane.

Mahaifin sa Haka nayimasa duk halinsu Daya 'amma daga baya ba gashi yaci amfanin sa.

Rushewa da kuka ya yi ya ce yanzu ace Dana babu amo babu labari shekaru biyar Kenan.

Idan ban kula da ahlin sa ba dawa zan kula...

Jikin hauwa ya yi mugun sanyi cikin son karfafa masa guiwa ta ce.

Kayi hakuri mai martaba nice na haifi salihu nafika shiga damuwa dauriya ce kawai.

Allah ya bayyana mana shi inda yake amma sainake ganin kaman koda ya bayyana ba zai taba yarda damu ba idanun ta cike da kwalla.

Cikin son kawar da zancen tadau wayar ta.

Ta dannawa yarima Samad Kira bugu biyu ya ɗaga

Daga can ɓangaren murmushi ne kwance afuskar shi ya ce yaudai mata ta tuna da mijin ta.

Dariya mai sauti' ta yi ta ce mijin da babu cefane shi ya sa nakeson ka karomin kishiya.

Uhmmm kodai kasamu wata anan kanon ne infara kishi tun yanzu.

Ransa ne yai mugun baci

Tunanin amsan daze ba ta yake ya san zancen Maryam za ta yi masa.

Amsa mata ya yi aikuwa namiki kishiya kwanan nan zan gabatar miki da ita ta Waya.

Hauwa fadada murmushin ta ta yi tana kallon mai martaba ta ce dagaske kake kuwa ya sunan ta wai Allah dadi kasheni.

Samu kansa ya yi dacemata sunanta baiwar Allah.

Mai martaba cikin zumudi ya amshi wayar hannunta dan ya tabbatar da zancen sa cike da jin dadi suke wayar shikuma Yarima Samad Yana kara lula dasu duniyar karyar shi dansu shafa masa lafiya yahuta.

*****

Kashe gari

Bayan Sheik ya idar da sallah asuba

a babban masallacin juma'a

 'huduba yatsaya yi kafun fitowan alfijir 'cike da nutsuwa yake wa'azi a kan Maza masu cin Amana mata gabadaya masallacin a nutsu inda yake fadin daidai da kwayar zarr namiji ya cutar da matar sa.

Sai Allah yabiye mata hakkin ta.

Banda karar fanka babu abun da kake ji a masallaci kowa ya nutsu.

Bayan yagama wa'azin suka fara musahaba da jama'ar wajen.

Baba salihu zaune kusa da Sheik danshine ke jan aya Sheik na fassarawa.

Cike da nutsuwa yagaida Sheik inakwana kansa aduke alkur'ani mai girma na hannun sa sanye yake da farar jallabiya fara.

Yana kokarin fita Sheik ya dakatar dashi tare da bashi izinin zama dan su tattauna.

Murya asanyaye Sheik ya ce daman magana ne a kan Rahama dakace kana son abawa danka.

Bikin nan ba zai wuce wata Daya ba kacal ba kuma har yanzu ba ka bayyana min asalin ka ba.

Dakuma dan naka daze auri Rahama ba.

Tsareshi da idanu ya yi yanajiran yaji ta bakinsa.

Baba salihu cikin kunan rai ya ce......

Ayimun afuwan rashin typin wlh banda lafiya ko yanzu Haka ban warke ba lallabawa nayi dan hakkin Ku dake kaina.

Karku manta paid Book

Free Book yakusa karewa*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

 

 

IKILIMA ADAM

(Kyauta daga Allah)

 

Book 1️5️

Cikin kunan rai ya ce..

Ya Sheik ni maraya ne banda Kowa sai Allah.

Nataba aure agarin Gombe matar tawa Allah ya yi mata rasuwa tabarni da yaya uku 'banda kowa agarin saï Allah dan iyayena cirani sukaje agarin ban san asalin su ba.

Dana kuma Abdul Samad nasan Yana Gombe da kaina zan gabatar dashi 'inkuma Kana tantama akaina nabaka izinin kaje c'en kayi bincike akaina.

Cikin gamsuwa da bayanan sa Sheik ya ce to yaushe za ka je kataho da dan naka.

Baba salihu yabada amsa da jibi ɗaman tuni ya fara hada Kayan sa dan ya yi hijira daga kasar

Zuwa Gabon.

Tun da Yaga yarima Samad ya nacewa unguwar tasu hankalin sa 'yayi mugun tashi.

Kukan zuciya yake yanda zerabu da Sheik tsawon shekaru dasuka dauka tare harda karya ya yi Masa karo na farko.

Azuciyar sai maimaita astagafirullah yake.

Ya Allah ka san zuciyata ka san dalili ya Allah kayafemin zunubin karya danaiwa babban malami ba Haka na so ba matsamin yayi.

Sheik ya ce MashAllah Allah ya nuna mana..

Rahama da asiya sanye suke da bakar abaya ba ƙaramin kyau shigar ta yi musu ba kansancewa za su je su amso form da ake rabawa na musabaka..

Asiya ta ce laaa amma adamsy kamar maye yake ne gashi nan abayan mu.

Waigowa ta yi idanunsu suka tsarke cikin juna 'fuskar ta ba yabo ba fallasa ta ce inakwana Adamu.

Amsa mata ya ce ina zakuje ne Haka.

Rahama ta yi rau rau da idanu cikin cool voice dinta ta ce.

Wallahi Abba ne yaturani amso Masa forme ɗun musabaka da za ayi ga yaya abubukar baya gari.

Adamsy ya ce form ɗin mene ne.

Na musabaka ne ta ba shi amsa ataikace suna ciki gaba da tafiyar su.

Harda ke za ai musabaka ne ya jefo mata tambayar.

Kashh...

Amma Adamu kacika tambaya saikace gidan redio tana turo dan ƙaramin bakin ta.

Daman Hakan yake so Yaga ta yi murmushi Yana satar kallon ta.

Ni kigayamun hardake za ayi ne.

Asiya ta karbi zancen da gaskiya A'a

bazatayiba Bana

 kullum ita ce kefitowa ana farko Tabarmu mu gwada sa'ar mu tana dariya.

Rahama ta ce daman bayi zanyiba.

Napep suka tara adamsy zeshiga Rahama tadan ba ta rai ta ce yanzu in Abba yaganmu tare zemana fada sossai.

Kin sauka ya yi ya ce inyagani kila yabarmun ke

 in aura kawai.

Kallon me napep ya yi ya ce ka tambayi hajiya iñda zata kaimu.

Rahama ta ce nasarawa.

Tun da suka DAUKI hanyar fira suke itada asiya

Adamsy na saka musu baki cikin zancen su.

Me napep ya ce munzo nasaraw.

Rahama ta ce.

SAMAD INVESTISSEMENT za ka kaimu.

Daidai mashigar kamfanin ya sauke su.

Mai gadi ya Bude masu Gate tare da tambayar su abun da yakawo su.

Rahama ta sanar Masa forme Aka turo ta amsa.

Mai gadi ya ce eh lallai jiya ya kare amma kidan jira oga ze iso Yanzu InshAllah.

Da to Suka amsa inda kowannen su ya samu waje daga cikin compound ɗin gida'n suka zauna Zaman Jira.

Horn ɗin motoci da'akai ya sa mai gadi wangale Gate 'motoci guda biyu suka kunno Kai

parking suka yi.

Boduygad da adamsy yadauka Sune suka zagaya tare da bude masa kofa' Akalla saida yadauki minti daya kafun ya sauke kafafun nasa kasa'.

Kowa ma'aikatan suka fara barka dazuwa ranka yadade.

Su faruk da aminu da Marwan kusan a tare suka fito daga tasu motar.

Yarima Samad dagawa ma'aikatan wajen hannu ya yi alamun kowa yakoma bakin aikin sa.

Rahama da Asiya tun shigowar shi suke kallon sa.

Kwabe baki Rahama ta yi ta ce amma wallahi akwai son barnatar da dukiya jibi fa shi ba zaiyi yawo shikadai ba saida Bodyguard saboda tsabar Albazaranci shi ya sa banda burin auren me kudi tsaki take ta jerowa ta rasa na mènene

Adamsy na ganin shi tsaf yagane shi

 dan lokacin da ya je asibiti be Farka ba.

Cikin hanzari yakarasa gaban sa ya ce Ranka yadade sunana Adamu Abdullahi.

Dan Ambassado libya ne.

Ya ba shi labarin Abban shi Daya turo shi dan yaduba lafiyar sa.

Yarima Samad murmushi ya yi ya ce barka da zuwa Ashe dan uwa ne Kai.

Muje daga ciki ya nunawa Adamsy hanyar office ɗin sa.

Ranka yadade na rako gimbiya ne.

Babu ba ta lokaci yamusu jagora suka shiga office ɗin sa.

Banda bugawa babu abun da zuciyar Samad yake.

Nan da nan Rahama ta nemi nutsuwar ta tarasa gabanta na tsananta bugawa da karfi.

Yarima yasoma kokarin tuno inda yata ba ganin Rahama tuno wa ya yi asibiti ne.

Kauda Kai ya yi daga kallon ta tsaye dasuke itada adamsy.

Bata rai ya yi banda harara babu abun da yake watsamata.

Meke tafe daku.

Asiya ta ce Ranka yadade Sheik Abdulrrazak ne yaturomun kan form ɗin musabaka

da kamfanin nan tasa gasa!

 'ya ce ba zai samu zuwa da kansa ba.

Yarima Samad maida kallon sa ga Rahama ya yi ya ce kekuma fa

Mekikazo nema nan.

Wayar adamsy Yasoma ring yafita dan amsa Kira..

Rahama ta ce to ai tare ka ganmu da ita.

Dan Haka mallam inzaka ba mu form kabamu tun dazu sai Raina mana hankali kake.

Sake da baki Yarima samad yake kallon ta 'cikin bacin Rai ya ce

Keeee

Dan Allah rufemin bakin.

Ko angayamiki nan gidan Ku ne da har zakiyi min rashin kunya.

Eh nan ba gidan mu bane

Daliline yakawo mu.

Ba munzo maula bane.

Tabuga uban tsaki mtsss.

Fita daga cikin office ɗin tayi cikin kunan rai.

Asiya ce ta Tsaya ta ce Ranka yadade kayi hakuri ina zamu samu form ɗin

Bude drawer ɗin office ɗin sa ya yi tare da Mika mata takardun form ɗin.

Tun da ke kinada hankali dan Allah Kija kawar ki Mara kamun Kai da take yawo da saurayi Ku tafi.

Kada infito in same ta anan ma'aikatan.

Cikin gamsuwa da bayanan sa tabar office ɗin.

Iske Adamsy da Rahama ta yi kusan a tare sukabar ma'aikatan.

*********

 

Salma zaune tsakar gida'mama tana mata tsifa sallamar Amina kawarta ya sa ta fadada murmushin ta

Inawuni Mama

Tare da neman waje tazauna 'cike da fara'a mama ta Amsa mata tana tambayarta ya mutan gida lfylau tabata Amsa.

Salma ta ce mama kibari inraka Amina mana tana marairace fuska.

Saikun dawo mama tabata Amsa tare da tashi zataje ta daura girki.

Salma hijab dinta tadauko adaki suka fito cikin hanzari.

Baba salihu dake tsaye bakin kofa Ya ce ina zakuje ne haka.

Salma turo baki ta yi waje tana hararan sa.

Inaruwanka da inda zamu koko ajiyar mu Aka baka.

Allah yabaku hakuri Ya ce tare da bude masu Gate suka fita.

Tafiya suke suna waige waige ganin babu wani' abayansu.

Amina ta ce fiddo wayar nan naki ba ni shi.

Mika mata wayar ta yi.

Kunna wayar Amina ta yi tare da dauko wata yar Takarda copy wasu nombobi ta yi tasa awayar.

ɗAnna Kira ta yi bugu biyu Aka daga.

Amina ta ce assalamu Alaikum malam isa gamunan zuwa Nida kawata babu jama'a wajen naka KO.

Amsa mata ya yi da babu kowa sukadai yake jira.

Babu ba ta lokaci suka tari napep tare da Masa kwatancen iñda zekaisu.

Basu dau lokaci mai tsawo ba a kan hanya suka iso unguwar.

Nikaf Salma tasaka sannan tasauka daga napep DIN direct gidan suka nufa.

Amina ce ta yi gaba Salma nabiye da ita abaya.

Sallama suka yi yabasu izinin shigowa Yana zaune tankwashe da kafafun sa.

Tabarma ya shimfida musu suka zauna.

Amina ta ce malam isa WANNAN sunanta Salma kawata ce.

Kafun takarasa magana malam isa Ya ce dakata nasan Meye matsalar ta.

Zururu da idanu Salma da Amina suke kallon juna.

Gyaran murya ya yi Ya ce a kan wani' saurayine mai suna Adamu kikazo KO?

Dasauri ta girgiza Kai ta ce eh haka ne malam.

Murmushi ya yi Ya ce Salma kinyi sake ɗan Adamu shine ze auri Rahama.

Idanunta nan da nan yakawo ruwa ta ce malam dan Allah mene ne mafita ?

Wani' dariya yabushe dashi Ya ce mafita dayawa fa amma da kamar wuya.

Kallon juna suka yi Amina da Salma suna zazzare idanu.

Amina ta ce fadi koma mene ne zamu iya kar kaji komai'.

Mallam isa Ya ce Abu nafarko shine.......

300 vip

500 special

Acct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

1️6️

Abu na farko shine zaa samu zuciyar kiyashi.

Arazane suka dago kai suka kalle shi

Zuciyar kiyashi kuma salma ta maimaita malam ina zamu samu ?

Dariya yabushe dashi sai suka tsorota.

Ke salma nasan bakisan komai aharkan nan ba.

Amma kawarki Amina tasan komi dan haka basai kin daga hankalin ki ba.

Amina murmushi ta yi ta ce to nawane zamu ba ka asamo ayi mata aikin nan dan wallahi shegiyar yayar tata ta tare komai.

Malam isa dan nisawa ya yi a cikin tunanin sa '.

Yadauko kasa yanata sindabarun sa.

Dago jajayen idanun ya yi ya gimtse kamar be ba ta dariya ba.

Dubu dari zata bayar tabada rabi daga baya tacika sauran.

Hankalin Salma ya yi mugun tashi har wata zufa ce ta keto mata.

Aro kuzari ta yi ta ce to malam nida ban sana'ar komi ina zansamu kudin.

Bata gama rufe baki ba.

Taga Amina ta fiddo dubu hamsin cikin jakar ta tashi ta yi taje gaban malam tare da sa dukanin hannayenta biyu ta mika masa' gashi kayi abun da yadace sauran kudin sai munga biyan bukata zamu cika maka.

Salma da bakin ta yakasa rufuwa dan mamakin ina Amina tasamu kudi.

Barin wani tunani ta yi Jin Amina na Dafata tashi mu je kada Abban mu yadawo besameki agida ba.

Malam isa dauko kullin magani ya yi ya ce kinga wannan garin kisan yanda zakiyi kijata ajiki harta sake dake 'shaka mata wannan maganin zakiyi zata sume maki kaman minti goma daga nan kuma bazata kara tuna wani Adamsy ba.

Namiki Alkawari Rahama kaskantancen mutum zata aura wanda me gadin gidan naku yafishi matsayi.

Hannun biyu salma tasa hannu takarbi maganin tare da yiwa malam godiya.

Sallama suka yi masa babu ba ta lokaci sukafito waje.

Me napep suka tara 'suna kan hanyar su takomawa gida.

Salma duban Amina ta yi tana tambayarta inda ta samo kudade masu yawa.

Amina ta ce wani alhaji ne da yake yawan kaini hôtel shine ke kashemin kudi.

Kema wlh dazakibi dakinyi kudi tayanda zakiga bayan Rahama ta ruwan sanyi.

Rau rau ɗa idanu salma ta yi ta ce nikinga iskancina bekai cen ba.

Me napep dake jansu sai kada kai yake yi zallar mamaki ne kwance a kan fuskar sa Wai matasan yara ke fiddo manyan kalamai ta iskanci abakin su.

Salma kusan tare da suka dawo gida da Rahama ita tadawo daga gidan malam.

Rahama tadawo daga aiken Abba kawayen nasu kowanne yakama hanyar gidan su.

Rahma kallon salma take tana tambayar inda ta fito.

Tunowa ta yi malam ya ce ta ja Rahama ajiki ya sa tasakar matar murmushi antina na je rakiyan Amina ne mu je daga ciko Ko amsar form din hannun Rahama ta yi takai mata dakin Abba.

Baiwar Allah Rahama ba ta kawo komai aranta ba 'cike da nutsuwa tagaida mama.

Zama kusa da ita ta yi ce mama wai ina Abdul jalil ne duk wunin yau banganshi ba.

In akwai abun da maman ta tsana aduniya shine aimata maganar sa' adatu ko maganar Abdul jalil.

Bata rai ta yi nace yana gidan uban kii.

Tsuke bakin rahama tayi.

Sallamar abubakar ne ya jawo hankalinsu akansa.

Rike yake da akwatunan kaya sake da baki Rahama ta ce kardai kace min kawu hussaini ne yazo daga makarfi tana buga uban tsalle wuceshi ta yi aguje ta tafi wa je.

Kawu hussaini shida matar sa zainab tagani sun tsaya suna gaisawa da baba salihu.

Aguje Rahama tafada jikin zainab din har suna kokarin faduwa.

Antina yaushe gari tare da kara rungume ta 'sauke mata goyon dake jikinta ta yi yaron nata ihun kiwuya ba zai zauna hannun Rahama itako kin ajiyeshi dan tsananin son da take yiwa yara har Adua' take yi Allah yaba anty haihu.

Tare suka karaso gidan kawu hussaini daman bawani shiri sossai suke da mama ba amma ahaka ya je suka gaisa.

Mama saiwani daure masa fuska take kaman taga kashi.

Bekulata ba danshi saboda bikin Rahama sukazo.

Anty da fara'a ta karbesu nan da nan tafada musu taliya shap shap.

Dakinta tasauke zainab tare da yiwa dan ta wanka tagyarashi.

Tarba mekyau suka samu Salma da yake da biyu yanzu take mannewa Rahama taje tagaida zainab.

************

Kashe gari.

Baba salihu ne yashirya kayan sa tsaf dabefi kala uku ba.

Zaune yake dirshan adakin sa idanun sa' sun kada.

Ya sheik na so ace dana ze auri yarka Rahama banda zabi dole nayi hijira Kayafemun rashin dawowar da ba zanyi ba.

Dan kawo maka ɗana ba.

Naso ace inada wannan damar ahannuna ne.

Na hada aure tsakanin jinina da naka.

Kuka yake mai fidda sauti.

Goge hawayen sa.

Yayi tare da shiga cikin gidan yayiwa su anty da mama salma'

Rahama banda kuka babu abun da take yi.

Har kofar gida suka yi masa rakiya tare da hussain da abubakar.

Sheik cikin......

300 vip

500 special

Acct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

1️7️

Sheik cikin hanzari yakaraso gaban baba salihu tare da rungumar sa.

Cikin kuka yake fadin na shaku da kai dan uwa kazamo tamkar fitila a cikin ahlina kanada dadin zama kyakyawan zuciya.

Sassauta rungumar dayayi wa baba salihu ya yi tare da kallon sa cikin idanu hannayen su tsarke cikin juna.

Ya ce yanzu inka tafi yaushe za ka dawo kar ka manta dudu bikin bekai sati uku ba.

Baba salihu karfafawa sheik gwuiwa ya yi a kan zedawo nan ba da jimawa ba.

Har bakin titi suka rako sa duk wani kudaden sa aikin gadin da yake musu. sheik yamika masa.

 salihu da ƙyar ya masa kudin saida yaga ran sheik yabaci sannan ya amsa yaita zuba godiya.

Suna kallon sa ya tari me napep yashiga sunata daga masa hannu yana daga musu harya suka yi nisa.

Sheik jiki asanyaye suka koma gida.

Abubakar ya ce Abba yanzu daya tafi wani mutum ne na amana za ka samu ya rinƙa tsare mana gida.

Sheik murmushi ya yi irin tasu ta manya ya ce aiyanzu tsaron gida yadawo hannun ka.

Abubakar ya ce laa !

Abba ni kuma ayyuka na fa ?

Sheik ya ce hakuri zakayine ka ga ba dadewa zeyi ba kafun biki zansamu mana me gadi.

Aishi baba salihu koya dawo gaskiya ba zaiyi gadi ba.

S'aide kasuwanci dan yazama surikina.

Abubakar girgiza kai ya yi cikin gamsuwa da zancen Abba Suna isowa gida ya yi sashin sa.

Sheik yakarasa gida iske salma da Rahama sun shirya cikin kayan su na makaranta za su wuce dan yau shine rana ta karshe zana jarabawan su.

Kiransu ya yi zuwa dakin nasa.

Mama ta ce haba sheik kazo sai magana nake maka kana shareni wa'azi kakeyi agari amma agidan ka.

Akwai gyara wallahi

Zainab matar hussain dake cin abinci saida ta dago kai tana kallon tijara irin na Mama.

Be bi takanta ba yawuce dakin sa yana girgiza kai.

Yana shiga Rahama da salma suka take masa baya.

Sallama dauke abakin su.

Suka shiga samun wuri suka yi suka zauna.

Kallon su yake nawasu dakiku yana nazartan yanayin su.

Yalura salma duk takosa tabar dakin yanayin zaman nata yake kallo.

Gyaran murya ya yi ya ce

Rahama kina sane nabada auren ki ko ?

Kanta aduke ta amsa cikin cool voice nasani abba ta ba shi amsa a takaice.

Ina son pls amatsayin ki na yarinya me hankali ki tsaida hankalin ki.

Waje daya nasan kin san ba zan taba miki zaben tumun dare ba.

Rahama dan Allah karki ba ni kunya nasan akwai wani wanda kike so kidauka yashigo rayuwarki ne bisa kaddara narokeki yata.

Jikin Rahama ya yi mugun sanyi cikin raunin murya ta ce Abba zanmaka biyayya wallahi Ko mahaukaci kaba ni amatsayin miji zan zauna dashi bare ace mutum mai hankali ɗa nutsuwa kar kai yi shakku a kan tarbiyyan dakabani ba zan bari kaji kunya ba InshAllah.

Dadin kalamanta bakadan suka dada ran sheik ba guntun hawayen dake fuskar sa ahankali yake kwaranya Dadi yakeji aransa da Allah ya bashi ya mace mai nutsuwa da hankali.

Fuskantar Salma ya yi ya ce to na dawo kanki.

Nasan halayenki salma na so inmiki zabin mijin aure amma nalura hakan ba zai yuba ina son ki gabatar da wanda kike so dan arana daya nakeson auran daku keda yar uwarki.

Salma kanta akasa banda bugawa babu abun da zuciyarta yake yi.

Cikin tsoro da fargaba ta ce Abba ni Adamu nakeso.

Kusan a tare abba da Rahama suka dago kai Suna kallon ta.

Abba ya ce wani Adamun kenan ?

Cikin tsoro ta furta dan anbassador libya.

Gaban Rahama saida yabada ras wani sashi na zuciyarta ta ce to ai gwara ya auri

 

Tun da yarasani kukan zuci take Ta yanda zata auri wanda bataso.

Abba ya ce Adamu daman saurayin kine.

Turo baki ta yi gaba ta ce ai daman ni ya fara gani yana so.

Rahama tashiga tafita ganin taraba mu.

Gashi ita kanta ma ba auren nasa zatayi ba tana murguda baki da hararan Rahama.

Abba Ransa yaba ce.

Ya ce ke dakata nan bankira ku ba dan ayita faden zancen banzaba.

Kituro adamun yazo ina son ganin sa.

Kuna iya tafiya karku yi latti.

Jiki asanyaye Rahama ta tashi banda kuka babu abun da zuciyarta yake yi.

Akan hanyar su ta makaranta babu wanda yakewa dan uwan sa magana.

Salma tsaki kawai taketa jerowa Sam Rahama taki kulata dan gabadaya hankalin ta nakan makaranta da za su je.

Mai gadin makaranta sai washe baki yake ganin Rahama mutumiyar sa.

Sai magana yake mata da ƙyar ta ba shi amsa tashige ciki..

Suna shiga aji aka fara zana jarabawan Sam Rahama rubutu Take yi amma Sam hankalin ta

Baya kan abun da take zanawa dandai ilimin a kwanyarta yake ɗa sai dai ta yi asarar damarta ta karshe da taimakon asiya tadawo tunanin ta harta gyara inda ta yi kura Kurai.

Har suka tashi break Sam ba ta da tsukuni auren nata daya saura satî biyu kacal shine yake daga mata hankali.

Yazan yi ni Rahama in yi zaman aure ɗa wanda ban san halayen sa ba.

Ban san ya yake ba 'ban san Addininin sa ba.

Murya Adamsy ta tsinta dake tsaye yana kallon ta.

Sanye yake da boyel bleue color hular sa bleue sai baza kamshi yake.

Haba Rahama bedace dake ba kizauna ke kadai anan ba' ba tare da abokin hira ba.

Dago jajayen idanun ta ta yi ta kalle shi tare da kauda kanta gefe.

Tashi ta yi daga Wajen shan gabanta ya yi ya ce haba babu fada meyakawo gaba gimbiya.

Salma takaraso inda suke tana murmushi kai ba ka san dalilin fushin ta ba.

Girgiza kai ya yi yana kallon salma dake wani kashemai idanu karasowa gab dashi ta yi har sunajin numfashin juna.

Abba ya yi mata miji wanda bakai ba bikin saura satî biyu.

Adamsy nan da nan idanun sa suka kawo ruwa Sam ya manta da zancen ba da auren Rahama da Abba ya ce yayi.

Rahama kasa jure tsayuwar ta nan tayi.

Barin wajen ta yi cikin sheshekar kuka mai tsuma zuciya.

Adamsy zebi bayan Rahama salma tasha Gaban sa.

Pls kar ka bita dan bakula ka zatayi ba tayiwa Abba alkawarin haka.

Iname ba ka shawara tun da ka rasa Rahama ka aureni.

Firgit haka yaji kalaman nata kamar saukan guduma kallon tara saura kwata yake jifanta dashi.

Afili yafurta aure ni dake salma yana nuna kansa da yatsa.

Wallahi kin makaro Ko ke ce autar mata nahakura dake non-sens kawai.

Tubar da miyau ya yi akasa tsukii ya ja tare da barin wajen yana mejin tsanarta a cikin zuciyar shi.

Ikon Allah ne kadai yakai adamsy gida.

Awaje ya paka motar sa Kai tsaye gida ya nufa tafiya yake kamar dan maye.

Ko kallon me gadi dake gaishe shi be yi ba.

Hamza dake zaune yana kallon TV arazane yadago kai yana kallon adamsy dake kokarin faduwa.

Cikin hanzari ya tarosa cikin gigita ya ce Adam

Meyake damunka ne Adamu.

Budan bakin adamsy ya ce...

Ta ku har kullum kyauta daga Allah*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

300 vip

500 special

Acct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

Karku manta free book yakusa karewa

1️8️

Budan bakin Adamsy ya ce tawa takare hamza shi ke nan sun rabani da Rahama ta !

Numfashin sama sama yake fitarwa saboda hawan jinin da yake dashi nan da nan yaji bakin sa na neman juyewa wanda harshen sa da ƙyar yake daga shi.

''

Tsoro da fargaba yakama hamza ganin Adamsy ya sume masa ahannu.

Girgiza shi yake yi da dukan karfin sa.

Amma still shiru cikin gigita yakwantar dashi kan kujera ruwan sanyi yadebo ya rinƙa zuba masa stil dai shiru ne.

Kasa kunne sa ya yi a kan kirjinsa yaji Ko yana numfashine ciki gigice wa kardai ace mutuwa yayi.

Aguje yana nufi kofar gidan mai gadin yagani rike da redio hannun sa.

Yana sauraren tashar BBC akidime cikin kuka ya ce Dan Allah zo ka kama Adamu mukai sa.

Asibiti 'babu ba ta lokaci suka shiga ciki da hanzarin su.

Mai gadi Tanko ya ce Ranka yadade suma ya yi inaga basai munje asibiti ba debo ruwa ka gani.

Cikin hanzari haryana tuntube ya je ya dibo ruwan.

Mikawa tanko yayi'.

Tanko ya rinƙa yayyafa masa ruwan a fuska.

Afisge ya ja numfashi.

Tare da ajiyar zuciya.

Kana ya lumshe idanun sa gashin girar sa lub lub Saboda damshin ruwa kana fuskar sa ta yi wasai.

Ramar da ya yi na lokaci daya ya firgita hamza ganin bakin sa harya bushe ya yi fari kal.

Kaman bashi ba.

Tanko sai jero masa sannu yake yi kallon Hamza ya yi ya ce Allah ya sauwake tare da juyawa yafice daga dakin yana mejin tausayin me gidan nasa.

Hamza tagumi yazuba ganin ba zai fisheshi ba.

Yadau waya yadanna wa Abban Adamsy kira.

Daddy ya ɗaga ya ce haba adamu tun dazu nake kiran wayar ka ba ta shiga inafatan lafiya Ko ?

Jin muryan hamza nacewa Daddy ba Adamsy bane nine abokin sa hamza.

Gaban Daddy ne yafadi ya ce to ina Adamun yake yayin da yake kokarin ajiye computer dake kan kafafun gaza zama ya yi tare da nufar dakin mommyn Adamu yana fadin kayi shiru ba ka ban amsa ba ɗaidai lokacin yashigo dakin iske mommyn zaune tana chattin a whsap murmushi kwance a fuskarta.

Daga can ɓangaren hamza ya ce amsorry wlh Adamu yana bukatar taimakon ku.

Nan yakwashi labari tun farko harzuwa yanzu.

Jikin Daddy kamar mazari haka ya rinƙa rawa.

Mommyn ajiye wayar hannun ta yi cikin kidima ta ce tun dazu kashigo sai waya kakeyi kaki magana.

Gayamin meke faruwa ne wani abunne ya samu adamu !

Kallon ta Daddy yake ajiyar zuciya ya sauke kana ya maida hankalin sa kan wayar da yake yi.

Cikin bacin rai da tafasar zuciya ya ce yar gidan uban wacece ita.

Da har zaa hanashi wallahi saina nunawa iyayen ta.

Su matsiyata ne basusan wane ne uban nashi bane.

Hamza ya ce sai hankuri Daddy adai ne mi mafita dan wlh ze iya rasa ran sa.

Akan Rahama.

Daddy cikin fushi ya ce wlh yau dinnan zanzo kanon pls ka kulamin dashi Daga haka suka yi sallama.

Daddy yana ta huci kamar kumurcin zaki.

Bama Mommy labari abun da kefaruwa hankalin ta yakai kololuwa wajen tashi.

Kallon mijin nata ta yi ta ce amma dai talaka talaka ne.

Kamar Adamsy ze je neman aure su hana me suke takama dashi.

Arziki 'boko' kokuma wayewa na tabbata babu kodaya.

Mommy Sam ta mance babu wayewar datafi addinin mu musulunci.

*********

Ɓangaren yarima Samad

Firgit yafarka Daga barcin da yake yi matukar mamaki ne yakamasa a kan mafarkin da kullum yakasa dainawa daga yakwanta barci.

Faruk dake zaune gefen sa yana chat maida hankalin sa kan Samad ya yi dake dafe da kansa.

Ya ce wai lafiya naga ka tashi daga barci.

Cikin muryan barci ya ce wai yaushe ne zandaina wannan mafarkin mai cike da al'ajabi.

Faruk tashi ya yi daga inda yake karasowa kusa dashi ya yi kallon sa yake yana nazartan yanayin hango tsantsar damuwa kwance a kan fuskar sa.

Ya ce gayamin wani mafarki ne wannan yana ya tsareshi da manyan idanun sa.

Yarima Samad dake hamma ya ce wlh kullum sainayi mafarki wai gamu wajen wani taro amma ban san taron mene ne ba.

Faruk ya numfasa ya ce ai mafarki ba gaskiya bane.

Amma tabbas kila akwai taron da za ai ne shine Allah yake nuna maka.

Tambayar shi yake Ko a mafarkin ya yi murna da taron ?

Yarima Samad ya ce ai Ko alama a mafarkin ji nake Kaman atakure nake wajen taron nan.

Numfasawa Faruk ya yi ya ce akwai abokina dayasan fasaran mafarkin gobe zanmai bayanin mafarkin naka muji me ze ce.

Cikin gamsuwa da bayanan sa Yarima Samad yakoma ya gyara kwanciyar sa tare da rufa blanket dan gobe yana da uzuririka dayawa.

*****************

Dare mahutan bawa Allah sarki Rahama kwance take itaba barci take ba itakuma ba ta bude idanun ta ba.

Tuno haduwar su da Adamsy dakuma yanayin databar shi ɗuk ilah irin jikinta ya gama sanyi.

Sallamar anty ya sa ta lumshe idanun ta kamar me barci.

Anty kallon ta take sarai tagane ba barci take ba.

Zama kusa da ita tayi.

Tare da tallabo kanta.

Ta ce haba Rahama nice fa na reneki har kika girma haihuwar ki kadai ne banyi ba.

Yanzu har akwai abun da zedameki yahanaki barci ni sa'adatu ki kasa gayamin Sam ba haka tsarin rayuwata da naki suke ba.

Bude idanun ta dasuke lumshe ta yi tare da gyara zaman ta dukar da kai ta yi alamun afuwa ga anty.

Cikin sanyi murya ta ce anti wlh Adamsy yaban tausayi ina kuka ne halin daze shiga akaina.

Wanda ni zan shiga bedameni ba.

Anti shi ke nan zanbar gidan mu.

 'labarin aurena ban tabaji koda a novel bane ace mijin dazan aura uban sa ya je yadauko sa.

Inada kyakyawan zato a kan baba salihu amma dukan mu'

Bamusan daga ina ya fito ba

Abba kadai ya sani cikin kuka ta ce yanzu anty in yakawo yaron nasa kukaga bamai tarbiyya bane shi ke nan babu wanda zehana a daura auren.

Numfashi ta fesar zataci gaba da magana.

Anty ta dakatar da ita.

Da hannun

Pls Rahama narokeki kicire duk wani tunani aranki Allah yana sa ne dake kuma InshAllah auren nan ze zamo Alkhairi a tare dake karki damu da rashin sanin wanda zaki aura.

Kedai kisa aranki bauta zakije Ko yaya mijin naki yake kiyi masa biyayya.

Kinji Ko ?

Gyada kai ta yi alamun gamsuwa.

Tare da kwanciya jikin anty.

Cikin rarrashi anty keta ba ta shawarwari masu kashe jiki.

Ahaka barci ya yi awon gaba da Rahama ba tare da ta shirya ba.

Gyara mata kwanciya ta yi tare da tofe ta da adu'oi kana ta rufa mata blanket tabaro dakin tare da rufo mata kofa.

Daidai corrido daze sada ta da dakin nata ta ji muryan Salma alamun waya take yi a sirrince.

Ganin anty ya sa ta rikice tare da tura wayar cikin Brezia.

Rau Rau da idanu take kallon anty alamun rashin gaskiya sun bayyana a tare da ita.

Wuce ta anty ta yi tana Girgiza kai tsoron magana take yi uwarta ta ce sharri ake mata.

Abba yazo wucewa tawajen ganin Salma a wajen ba ƙaramin shock yashiga ba.

Wayar ya fara ruri tana kawo haske.

Nan take ta ji hantar cikin ta ya kada ganin sheik na kokarin....

Karku manta Paid book

Kubiya ku cigaba da karatun sa har a gama.

300 vip

500 special

Acct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

1️9️

Ganin sheik na kokarin saka hannun sa cikin rigar ta ze zaro wayar.

Kokarin guduwa take yi ya damko Hannayen ta Wani irin wawan riko yayiwa hannun ta tare da wucewa da ita kai tsaye dakin nasa.

Suna shiga ya ja kofar yarufe wayar yazaro a jikin ta yana kallon yanda take ring saman screen din wayar anrubuta Al'amin.

Daga wayar ya yi tare da sa hansfree kasa kunne ya yi yana sauraron abun da yake fadi.

Daga can ɓangaren ya ce haba salma kinfa yimun Alkawari zaki mallaka min budurcin ki.

Naga yanzu lokaci ya yi da zaki ba ni hadin kai ina son nanda sati daya.

Muje hôtel pls wallahi abukace nake tun da yaketa zuba be lura da Sam salma ba ta amsa masa ba saida yakai ayar zancen nasa kallon wayar ya yi yaga dai baa kashe.

Cikin fushi ya ce Kindaukeni mahaukaci nikadai sai magana nake kinshareni.

Sheik ba ƙaramin tashin hankali ba yashiga t' yanata nanata zancen budurci acikin zuciyar sa.

Afili kuma kallon wayar yake yi yana kallon Idanun salma data fita hayyacin ta lokaci daya.

Gyaran murya ya yi ya ce da uban salma kake magana kajira ka ga abun da zebiyo baya.

Al'amin ba ƙaramin tashin hankali yashiga ba. Kallon wayar yake yi ya ce shi ke nan ze tona mana asiri yazan yi in iyayena suka ji wannan zancen.

Sheik da Idanun sa suka kada jajir kyawawan maruka guda uku yadauketa dashi wanda hakan ya sa ihun ta.

Ya karade ila'irin gidan gabadaya.

Kowa gidan saida suka zabura Jin yanda salma ke ihun neman taimako.

Sheik dorina yaketa zabga mata Ko ina a jikin ta.

Kuka take kaman ranta zefita tana fadin natuba wallahi ba zan sake ba.

Wayyo Abba kirjina zafi.

Wuyana zan mutu !

Mama dasuketa buga kofar itada anty amma ina Ko sauraren su beyi ba.

Hussain ya ce wlh kada fa zuciya ya debeshi yakasheta nasan yaya Abdulrazak akwai hakuri amma fa da ransa ya ba ce baya gudun abun da zebiyo baya.

Zainab matar hussain cikin damuwa ta ce maza kanemo wani abu aballa kofar nan.

Babu musu ya tafi sai gashi dake da gatari hannun sa kokarin buga kofar yake.

Sheik ya ce dakata zan bude yana bude dakin aguje suka shiga ciki.

Mamaki ne yakamasu ganin Sheik sharkaf kaman wanda aka watsawa ruwa zufa ne ke sassafo masa ta ko'ina a jikin sa.

salma nakwance kaman wata gawa takasa tashi sautin kukan da take rerawa ahankali yajawo hankalin su a kan ta.

Mama cikin kuka ta ce Salma laifin me kikai masa da harya zabi yamiki mugun duka.

Zabura ta yi taje gaban ta tana huci sama sama.

Na tabbata da Rahama ce Ko Abdul jalil baza taba musu wannan muguntar ba.

Karfa kamance salma jinin ka ce fa kai ne ubanta.

Tsawar da Sheik ya daka

Mata ba ita kadai duk dakin saida suka razana.

Cikin kunan rai ya ce wallahi nayi nadaman hada zuri'a dake Aisha Sam bakida hali bakida tarbiyya tsawon shekaru nawa nadauka ina hakuri dake wallahi badan umarnin mahaifina bane kada in sake ki duk rintsi duk wuya da bakikai wannan lokacin a gidana ba.

Saboda ke zanje makarfin nan duk yanda zanyi sainayi yaban daman sakin ki.

Sakaryan banza duk abun da salma take yi da sa hannun ki.

Ni uba ne dole ne infita nema Ko harkokin gabana kune iyaye mata tarbiyya Daga hannun ku ake dauka shi uba hakkin sa ne yadaura iyalin sa kan kyakyawan turba kuma Allah ya sani ina yi.

Kallon su hussain ya yi Idanun sa sun kada goge hawayen dake kwaranya kan idanunsa ya yi dawani kyalle ya ce ku duba Rahama dan Allah waze kushe halayenta Saboda tasamu riko hannun uwa tagari.

Kamar ni wallahi salma ta yi kadan ta zubar min da mutuncina a idanun duniya wallahi.

Nan yashiga basu labarin abun da ta yi salati duka dakin yadauka.

Cikin kuka Rahama ta shigo tarike kafar Abba dan Allah kayafe mata.

Kar ka yanke mata hukunci cikin fushi Abba.

Hannun ya sa ya ɗaga Rahama Ta fada jikinsa tana kuka, bubbuga bayan ta yasoma yi.

Ya ce na ji zancenki Rahama zanyi tunani a kan abun da yadace.

Kallon hussain ya yi ya ce ina son ka rinƙa sa mun idanu a kan shige da ficen yaran nan.

Hussain ya ce babu matsala zanyi adaiyi hakuri da ita yaya

 zamani ne da muke ciki yanzu sai du'ai.

Mama cikin kuka ta ce shikenaan yau sheik ya gama cimun mutunci a idanun jama'a.

Har ni kake cewa za ka saka inka sake ni gayamin wa zan aura ai tun kuruciyata zakai haka bayan zu ba.

Kama Salma suka yi da taimakon Rahama suka kaita dakin nasu.

Kowa ya watse zuciyar sa babu dadi.

**************

Daddy Adamsy tare da mommyn sa suka Iso gidan.

Cike da damuwa kwance a kan fuskarsu 'hango Adamsy kwance kan 3ster idanun sa a lumshe.

Cikin kuka momy ta rungume sa mamaki ne yakamashi ganin iyayen nasa agaban sa.

Daddy a jiyar zuciya ya sauke yana kallon dan nasa Cike da tausayawa.

Wai Adamu wannan wace yarinya ce haka da har samun ta zemaka wahala gayamin wane ne ubanta.

Adamu mamakin ganin iyayen nasa zuwan bazatan da suka yi masa.

Fahimtar abun da ke cikin ransa ne Abba ya ce abokin ka hamza shine ya sanar mana dan haka inajin ka yar wacece ?

Cikin yin kasa da kai ya ce diyar sheik Abdurrazak kabeer hizqeel makarfi ce.

What ?

Daddy ya furta yana zazzare idanu kallon mommy yake kin Ko gane wanda yake fade kuwa.

Girgiza kai mommy ta ce Alamun A'a amma kaman nasan sunan a duniyar social media.

Daddy cikin farin ciki ya ce wannan shaharraren malamin addinin nan da yasha gwagwarmaya da kafurai ta dalili sa dayawa sun tuba.

Kuma masani a kan wayewar zamani indai har shine uban nata gaskiya Adamu kaika san abun da ka gani harka nace masa kabari Allah yakaimu gobe za ka kaini gidan nasu.

Adamsy duk da haka be gamsu zai samu rahama dan sarai ya san halin sheik kan Alkawari inya dauka baya canjawa.

Kallon su yakoma kan hamza dake sauko wa kan matakalan step.

Bakin sa dauke da murmushi yakaraso falon cike da ladabi ya gaisheda iyayen Adamsy fuska asake suka amsa masa.

********, ****

Washe gari

Asuban fari sheik ya rinƙa bin dakin kowa yana bubbuga kofa Alamun su tashi lokacin sallah yayi.

Rahama daman idanun ta biyu gyara zaman ta kan sallaya ta yi tare da soma tashin salma dake barcin wahalan dukan da tasha hannun Abba.

Cike da so da kaunar salma tasata agabanta tana kallon yanda take barci ahankali kwance.

Har ta tashi zata je sakeyin sabon Alwala ta tsinkayo muryan salma cikin barci tana fadin wayyo ni fa baku isa ku rabani da Adamsy ba.

Shinake so.

Dawowa Rahama ta yi ganin sai shure shure salma keyi a gadon tana gurnani.

Tashin ta ta yi arazane ta farka tana mika kokarin komawa barcin take Rahama ta hana

Haba salma inzaki kwanta nace kiringa yin Alwala amma Sam bakiyi

Gashi saikiyita mugayen mafarkai kina gurnani.

Salma wani kallon banzai take jifan Rahama tsakii ta yi ta ce banda munafunci ina ruwan ki da barcina..

Rahama kyaleta ta yi tawuce dan gabatar da Alwala.

Bayan ta idar da sallah ne tazauna tana ta azkar.

Kallon salma dake barcin ta Ko sallah batayi ba.

Saida tabi kowani daki tayimusu barka da asuba tare da yin ayyukan da tasan aikinta ne.

Babu ganda Ko kiwuya takama aiki tagyara Ko ina na gidan tsaf tare da kunna turaren wuta har dakin Abba takai.

*****************

Yarima samad wanka ya fito daure da towel iya kugun sa.

Cikin hanzari yakashe wutar dakin domin Al'adar sa ce inze sanya kaya sai ya kashe wutar dakin.

Wani yadi mai masifan kyau ya saka royal bleue ba ƙaramin kyau ya yi da shigar ba takalmin sa harf cover ya sanya tare da zuwa gaban mirrow mai kadan yadan murza a hannayen sa da fuskar sa..

Sauri sauri yake yi dan zeje bauchi kaiwa abokin sa ziyara tare da bincike a kan Abban nasa.

Ahanzarce ya sauko kasa ganin su Aminu da marwan 'faruk kowannen su a shirye yake.

Suna ganin ya sauka faruk ya ce pls Yarima samad dan dakata mana saurin me kakeyi ba ka karya ba.

Kallon agogon hannun sa Yarima Samad ya yi cikin marairaice fuska ya ce am sorry bari in mun isa cen bauchi naci.

Kada mu makara time fa yakusa tare da cigaba da tafiya suna take masa baya...

***********

Abba zaune yana koyar da karatun Alkur'ani agidan nasa.

Rahama ɗa abubakar

Abdul jalil da hussain.

Salma kadaice ba ta zo ba.

Cikeda kwarewa yake karanto surorin Alkur'ani

Dukan su hannayen su dauke yake da Alkur'ani mai girma.

Time to time Rahama tana ta kallon agogo.

Cikin yin kasa da murya cike da ladabi ta ce.

Abba karfe goma ne zamuje airport yin bukin jirgin Lagos.

Haka ne fa yayinda sheik ya ce to maza tashi ki je.

Salma tarakaki.

Ungo wannan wayar tare da mika mata wayar salma daya kwace akwai layi ciki 'nasaka duk yanda ake ciki ki kirani.

Cikin gamsuwa ta tashi tare da zuwa jan salma suka tari me napep a daidai kofar gidan su.

Suna fita layin ya yi daidai da shigowar motar Adamsy da iyayen sa..

Basufi Akallah minti shabiyar ba sai gasu airport.

Cikin sauri sauri Rahama ke tafiya kada time yawuce tasan ba za su karba ba.

Yarima Samad a ujajan yake sauri dan kada su rasa jirgin safiya.

Daidai da wani karfe Rahama tasa kafafun ta.

Karfen makale hijab din Rahama ya yi wanda ya jata da baya baya.

Tana tangal tangal zata fadi ya yi daidai da zuwan Yarima samad a ujajan karo suka yi Ta saki wani kara tare da fadawa jikin sa wanda hakan ya sa shi faduwa dukan su a kasa.

Rahama na saman shi.

Marwan cikin shu'umin murmushi yadau wayar sa hoton su yadauka a haka.

Salma ciki....

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

Karku manta

Free yakusa karewa*🌟🌟 ƘANWATA🌟🌟*

300 vip

500 special

Acct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

2️0️

Salma cikin zargi take kallon marwan da bema 'lura tana kallon sa ba.

Maida wayar sa Aljihu yayi.

Cikin bacin rai Rahama ta dago Daga kan Yarima samad tana yarfe hannayenta.

Yarima samad da duk kunya ya gama kama shi faruk yataimaka masa yatashi sai nishi yake kamar wanda ya je wasan tsere.

Faruk hakuri yashiga basu Rahama wai Yarima samad be kula da ita bane.

Ran Samad yabaci ya ce hakurin me kake ba ta ba ka ganin abun da tamin Ko sannu ba ta cemin ba.

Saima dai hada rai da tayi.

Cikin Jin haushin ta ya ce ka ga mukoma gida nafasa tafiyar nan yau nahadu da rashin sa'a.

Aminu ya ce haba yazaka fasa a kan mace dan ranka yabaci.

Beko bi takansu ba yawuce su hanyar motar sa yanufa cikin tsananin bacin rai dajin haushin Rahama.

Salma wow ta furta tun da taga Yarima samad ta nemi nutsuwar ta tarasa.

A zuciyar ta 'sai fadi take Allah mai halitta ina fadin kyawun Adamsy ashe zanga wanda yafishi haduwa dubi yanda tafiyar sa abun kallo.

Fushin sa kara masa kyau yake yi.

Inama zemin kallo koda dayane tak wallahi dana kwana farin ciki.

Marwan sarai yake lura da kallon da salma keyiwa Samad.

Hakan ya ba shi daman zuwa kusa da ita katin sa mai dauke da nombar wayar sa yabata.

Cen kasa da murya ya ce nasan kingani kin yaba Karki damu hadaku ba zaimin wahala.

Salma ta ce pls hoton daka dauka dazun dan Allah kar ka goge awayar ka wataran zemin amfani.

Cikin gamsuwa da bayanan ta ya ce sainaji kiran ki' suna jirana.

Yawuce war sa.

Yana zuwa wani kallo Samad yabishi dashi..

Saida yasha jinin jikin sa.

Rahama tana cen tayanki ticket din waigowar da za ta yi taga salma ba ta bayanta Sam ba ta lura ba

Bacin rai ya sa tabar wajen ba tare da ta jira salma ba.

Waige Waige Rahama tasoma yi hango salma ta yi tana tafe itakadai murmushi take.

Cikin bacin rai ta ce haba m'y kanwaty ina kika tsaya ne harna gama abun da nake yi.

Kama hannun juna suka yi

Suka juya dan zuwa taran me napep daze kaisu gida.

****************

Hussain yashigo dakin sheik

Iske shi ya yi yana kokarin kwanciya barci dan ya huta kafun azahar.

Cike da ladabi ya ce sheik kayi baki.

Cikin kasalalliyar murya ya ce baki Daga ina kuma.

A jiyar zuciya ya sauke ya ce ka kaisu dakin baki yanzu gani nan zuwa.

Daga haka Hussain yafice Daga gidan.

Komawa ya yi ya Iske su Adamsy da iyayen sa.

Ya sanar dasu abun da sheik yafada 'Cike da Jin dadin karamci irin na sheik Suka biyo Hussain har dakin da aka tanada dan baki.

Samun wuri suka yi Suka zauna dukan su.

Hussain ya sake dawowa hannayen sa' dauke da ruwan sanyi na faro ya ajiye musu hade da cup.

Bismillah ya ce musu.

Da fara'a Suka amsa masa da sun gode.

Daddy kallon yanayin dakin yake yi dan daidai banda kamshi babu abun da dakin yake yi.

Dakin yadau shiru mommy ta kalli Adamsy duk yabi ya diririce ta ce kar ka damu InshAllah ba zai hana auren nan ba.

Sallamar sheik ya katse mata zancen da take yi.

Amsa masu suka yi fuska a sake.

Neman waje. ya yi yazauna yana fuskantar su Daddy musabaha suka yi dashi da Daddy harda Adamsy Cike da girmamawa da mutuntaka Suka kara gaisawa.

Shirune ya biyo baya.

.

Daddy ya ce nasan ba ka sanni ba '

Girgiza kai sheik ya yi alamun haka ne hankalin sa da nutsuwar sa yamaida kan zancen Daddy.

Daddy ya ce suna na Dr Abdullahi Auwal ambassador libya ne ni.

Ina zaune a katsina nida iyalina.

Dana Adamu nan yake bautan kasa.

Har Allah yahadashi da yar ka.

Amma cemana ya yi wai kayi mata miji.

Bayanin abun da ya samu Adamsy ya bashi da dalili zuwan su kanon.

Sheik Girgiza kai yake yi har Daddy yakai karshen zancen sa.

Gyaran murya ya yi ya ce a gaskiya na tausayawa halin da adamu yashiga a kan yata.

Ina me baku hakuri dan Allah.

Akwai wani dattijon Arziki salihu wanda ta dalili sa ne yau nake zaune cikin gidan nan ɗuk dai baibasu labari tsakanin su.

Amma yanuna masa baba salihu ya taka rawar gani acikin rayuwar sa.

Shi ya sa beki amince wa wajen bawa dan sa auren Rahama da zeyiba.

Iname baku hakuri nariga nayi Alkawari kuma harya tafi garin na su dan bikin nan tare da dansa za su dawo.

Mommy ta ce Allah gafarta malam yarka ance tana son Adamsy wanda za ka ba Beko taba ganin Rahama ba itama ba ta sanshi ba.

Yin haka sainake ganin kamar cutar da zukata ne.

Adai duba lamarin nan

Harda sheshekar kukan ta.

Sheik ya numfasa tare da Maida kallon sa a kan ta.

Ya ce biki saura sati biyo kike son a fasa amaida kan dan ki ?

Yin haka babu son kai aciki kuwa.

Daddy ya ce babu son kai sai dai taimakawa yaran zamuyi.

Sheik rasa me zecemusu yake gashi yana musu kallon mutane masu kamala.

Ya ce in babu laifi akwai kanwar ta Salma ta cemin shi takeso me ze hana amaida auren a kan ta.

Cikin kuka Adam ya ce sheik ni babu soyayya tsakanina da salma kanwa na dauketa.

Amma ina neman wata Alfarma sheik guda daya dan Allah.

Sheik ya ce inajin ka Allah ya sa zan iya.

Inhar baba salihu be dawowa ba ana bikin saura kwana uku za ka Maida auren akaina.

Sheik ya ce na amince dan ya san baba salihu befi nan da kwana uku yadawo ba.

Cike da mutuntaka Suka bar gidan suna yaba hankali da dabarun sarrafa harshe da magana cikin hikima irin ta sheik.

.......

Bayan sati daya

Kasar Ghana

Baba salihu a kasar Ghana wani babban hôtel yakama nan yake kwana

Hôtel din da sai yayan sarauta kadai ne sauka ciki.

Motar da yake hawa mercendez ba ƙaramin kyau ya yi ba dan Sam ba za ka taba ganeshi ba.

Fatar shi ta yi fresh hasken Fatar ya fito sossai kana kallon sa za ka tsatsan kamannin da suke yi da yarima Samad.

Wani fili ya je du bawa inda zefara ginin gidan sa.

Tuni yabiya contrat din gidan.

Zaune yake cikin motar sa ya kunna kira a idanunsa a lumshe.

Tunowa ya yi yaufa saura kwana bakwai bikin Rahama hankalin sa ya yi mugun tashi.

Zuciyar sa na masa radadin bakin cikin da sheik zeji inbe ganshi yazo da Samad kuma bekara ganin sa ba.

Wayar sa yadauko kirar iPhone 13 max ya danna kira bugu biyu aka Daga

Daga can ɓangaren ya ce ranka yadade ina nan ina bincike a kan komi sannu a hankali zan kamala maka ayyukan ka.

A jiyar zuciya baba salihu ya sauke ya ce bawanan ba ina Yarima Samad yake ne ?

Mutumin ya ba shi amsa muna nan tare dashi.

OK bude whsap dinka muyi magana yanzu.

Da to. Ya amsa masa tare da katse wayar.

Shiga whsap ya yi ya rubuta masa sako kamar haka.

Gidan sheik Abdurrazak nakeson kuje akwai bikin yarsa da za ayi gudummuwa za su aika masa na million goma.

Da sunan tallafi ne Daga saudiya akabashi dan ya yi zama a kasar kuma kada ka kuskura Yarima samad yagane komi tattare da kai.

Daga haka suka yi sallama.

*****, ********

Kasar kwatano

Maryam ce tazo gaida mamy Cike da farin cikin ganin ta.

Mamy ta rungume ta yaushe rabo yata da gidan nan gaskiya nayi fushi tun da Samad ya tafi shi ke nan kikai mana yaji.

Cike da kunya ta ce haba mamy koba samad dole inzo zama suka yi suna hira yaushe gamo.

Khadija ta shigo fuskar ta dauke da fara'a yau manya baki gare mu tana kallo Maryam.

Dake sakar mata murmushi mamy da kanta takawo mata lemun kwali da pepper soup din kaza.

Ta ce ajiye gabanta bismillah yata kuma surukata nan gaba InshAllah.

Kamshin abincin ya barade dakin gabadaya.

Cikin sakin jiki ta rinƙa ci.

Mamy ta ce bara inkira Mutumin ki.

Waiko kuna waya ke dashi kuwa.

Annuri dake kwance fuskar Maryam yadauke.

Mamy ta ce inajin ki kinyi...........

300 vip

500 special

Acct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishaɗantar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,, 𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)

Kai dajin sunan labarin ma ka san basai an tambaya ba.

*(ƘADDARA CE)*

*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane ƘADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo ba ta yi magana ba ta damƙi hannun Sultana Ta ce" Ke Sultana mu je ki nuna a hanyar shara-mansoor ɗin Uban waye ya faɗi miki wannan maganar yau saina wuƙance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...

*Dandano!Dandano!!*

Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta ɗago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Ta ce Rahama kiyi Haƙuri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi haɗe da zallar bakin ciki, take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da faɗin. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da ƘANWATA taimun ya Allah ka..

Ga maru buƙatar wannan novels ɗin za su iya tuntuɓar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573

 Nomal. guda ɗaya N 300 ne

guda biyu N 500 ne

Special guda ɗaya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne

Zaki iya biyan kuɗin ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

2️1️___2️2️

Mamy ta ce inajin ki kinyi shiru tsareta da idanu tayi.

Maryam cikin kasalalliyar murya ta ce mamy yarima samad baya sona wlh.

Zazzare idanu khadija da mamy suka yi sake da baki suna kallon ta.

Kamar ya baya sonki mamy ke tambayar ta.

Maryam ta ce da bakinsa ya ce besona son yan uwan taka kadai yake min.

Nima bancikin tsarin matan da yake so koda ina ciki shifa ba aure zeyi ba.

Bare asamu damar shi.

Mamy jikinta ya yi mugun sanyi itada khadija rarrashin maryam suka yi ta yi suna ba ta baki a kan ta kwantar da hankalin ta.

Ai aure itada yarima samad kamar an yi an gama.

....

Fulani zaune adaki itada mijin ta suna tattauna tugun da za su shiryawa yarima samad.

Dariya yake yi har sautin na fita yayin da yake kallon hoton da marwan dan sa yaturo masa.

Zoomin hoton ya yi yana kallon yanda Rahama ke kwance a kan yarima samad.

Cikin samun karfin guiwa ya ce Fulani yakika ga aikin dan namu yana kyau sossai.

Shi Samad gani yake ai yatara masoyan sa.

Besan harda makashin sa ba.

Wannan hoton ba ƙaramin Girgiza mai martaba zeyi ba yakike tunanin yan jaridu insuka samu wannan hoton.

Kema kin san za su ce tarihi ya maimaita kansa.

Gyara zaman ta fulani ta yi tana Girgiza kugun ta.

Cikin shewa ta ce rabo na da in ji labari mai dadi harna manta shegen yaro ga fadin rai.

Zamuga yanda za ayi inhar labari ya je wa mai martaba.

Wata baiwar fulani me suna iya firdausi sai kada kai take yi alamun tausayawa yarima Samad haihuwar sa kadai ne batayi tana cikin waɗanda suka raineshi a masarauta.

Fulani umarni taba iya firdausi taje taje ta sanarwa mamy gatanan zuwa yanzu.

Cike da girmamawa iya firdausi ta tafi ce sashin mamy.

Iske mamy zaune ta yi sun sa Maryam agaba sunata rarrashin ta a kan halin Samad.

Cike da girmamawa ta ce ya shugaba ta

 fulani ta ce a sanar miki isowar ta yanzu.

Mamy ta ce to saita zo tare da daukar wayar ta

Ta dannawa dan nata kira.

Bugu biyu ya ɗaga rubuce rucen wani case din shar'ia da zasuyi a kwatano nan da kwanan takwas yake yi ka sancewar shi lauya me zaman kansa.

Baya aiki wa marasa gaskiya duk dukiyan da za ka bashi.

Sannan yana yawan amsar case din waɗanda aka zalunta.

Case dinnan daze kaishi kwatano kan wata baiwar Allah da aka kashe mijinta Sannan aka daura alhakin kashe shi a kan ta.

Kuma aka kwace masu dukiya.

Daga can ɓangaren yana rubuce rubucen sa ya makala wayar da kafadar hannun sa.

Mamy ta ce inawuni Samad Cike da farin ciki ya amsa lfylau ajiye biron ya yi yana mai jingina jikin kujera idanun sa a lumshe ya ce mamy na lafiya kalau nake yasu Ahmed da khadija.

Mama karama da mai martaba su kawu basiru.

Mama fulani.

Lafiya lau suke dukansu ta ba shi amsa ataikace shiru ne ya ratsa tsakanin ganin yanda mamy ta canja murya lokaci daya.

ABDUL SAMAD yaji ta furta sunan sa cikin serious voice.

Wani faduwan gaba yaji dan ya san duk sanda takira full sunan sa magana ce mai muhimmanci take son suyi.

Cike da girmamawa ya amsa da na'am mamy

Mamy ta ce gaskiya kanaban mamaki yaushe kazama mara tausayi ne.

Inace ka karanci lauya ne dan tausayi da jinkan talakawa to meyasa ba ka nuna wa a kan Ahlina SAMAD numfashi ta fesar cikin bacin rai ta ce

Yanzu abun da kakewa diyata Maryam yadace da kai kuwa koka mance alakata da uwar ta ne Samad.

Daga can ɓangaren ajiyar zuciya ya sauke dan ya yi tunanin wani laifi mai girma rasa amsar daze ba ta yayi.

Cikin son kwantar mata da hankali ya ce haba Mamy"

 maryam ai Ƙanwata ce wallahi bana mata son aure saina yan uwan taka.

Yake mahaifiyata kimun hakuri ki yafemin wlh ina son Ahlinki domin nima Ahlina ne.

Mamy kin san komai agabana kina sane lokacin aure gareni beyi ba.

Ba na son in ba ta mata lokaci.

Ya mace lokacin ta kurarre gaban iyayen ta.

Pls ki fahimceni in Allah ya yi mata ta ce zan aure ta.

Jikin Mamy ya yi sanyi ta ce gaskiya ka fada Samad kanada tarin Ayyuka gaban ka.

Allah yaimana zabi na Alkhairi.

Da Amin ya amsa yana me sauke ajiyar zuciya shawo kan mamy da yayi

 ta cikin wayar yake Jin sallamar fulani.

Katse wayar ya yi ganin mamy tamaida hankalin ta a kan fulani.

Fulani cike da kasaita ta shigo dakin sai karewa dakin da abun da yake cikin sa kallo take.

Yatsine fuska ta yi kamar taga kashi ta ce.

Waike Mamy bakida zuciya ne shekara da shekaru kin zauna jiran tsammani mutumin nan koda yana raye ba ta ke yake ballatana inada yakinin baya raye.

Kiyi masa takaba ki lallaba Ko wani ze taimaka aure ki.

Kara takowa cikin dakin ta yi tana kallon khadija da banda hawaye babu abun da suke yi itada Maryam.

Kujera ta jawo ta zauna ta ce uhmm koda baa ce inzauna ba zan zauna.

Kallon banza takebin Mamy dashi ta ce wallahi ke karya ce mara zuciya.

Ran Mamy ya yi mugun baci shekaru biyar kenan ana mata cin kashi ba ta taba tankawa ba sai dai ta yi kuka tashare hawayenta.

Har fulani Ta gama izzar ta zata fice saida takai daidai bakin kofa.

Mamy ta ce dakata fulani !!

Cak ta tsaya cike da mamakin furucin bakin ta.

Karasowa gaban fulani ta yi ta ce.

ai Ta kaba ba ni ba ce zanyi kece zakiyi dan wannan mijin naki.

Bashida Amfani awajen ki.

Maganar rashin zuciya kona samu mai taimakamin ya aureni.

Wannan kece yakamata in gayama Saboda zuciyoyin ku keda mijin naki kafurin zuciya ne.

Gara ki rabu dashi kokin samu mai zuciyar musulunci ki aura kila ya saita ki kidawo kan hanya inhar kinada rabon shiriya.

Sakarya kuma da kikacemin wannan sunan ki lamba daya ne.

Dan haka wallahi ki fita harkata dan inkika sake zakisha mamaki mai halin dabbobi.

Tsakiii ta ja tare da komawa cikin daki tana haki dan bacin rai

sossai khadija da maryam suka ji dadin wankin babban bargon da mamy tayiwa fulani.

Fulani mutuwar tsaye ta yi tana cije labban ta kalaman mamy ne keta dawainiya da zuciyar ta.

Da ƙyar ta ja Jikin ta.

Tabar dakin cikin kunan rai.

***********

Kano ta dabo tunbin giwa

Sheik sai safa da marwa yake yi ganin biki saura kwana shidda Amma babu baba salihu babu babu labarin sossai yake jinjina Al'amarin.

Anty ta ce haba mijina me ya yi zafi haka ka kasa zaune ka kasa tsaye Ko kudin gudumuwar da saudiya tabaka na bikin yayan ka banga kana murna ba.

Kallon ta yake cikin tafarsa zuciya ya ce kina sane fa auren nan saura kwana shidda Amma babu labarin salihu.

Anty ta ce tun da kace in ya rage kwana uku bikin bezo ba zakaba Adamu kadena damun kanka.

Ita salma ta fito da mijin auren nata Ko.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da zama kan kujera suna fuskantar juna.

Dadi na dake Sa'adatu kin iya kwantar da mijin ki hankali.

Maganar salma wannan dan iskan yaron Al'amin dashi zan hada ta nasa akirawo iyayen sa dashi kansa anjima za su zo gidan nan.

Cikin gamsuwa da bayanan sa ta ce ai gwamma ta yi auren barin ta gida beda amfani.

*******

Post a Comment

0 Comments