Ticker

6/recent/ticker-posts

Aikatau

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa  

387.  Aiki na nufin abin da ka kaddarta,

 Za ka yi, ko ka yi shi nan har ka rubuta,

 Shi ne aikatau, ga hujjar manazarta,

Aiki kowane iri za ka rubuta,

  Ka kiyaye da shi ga tsarin zanawa.

 

388. Za a rubuta kowane aiki ware,

 Matuƙar ya taho ga kalma jejjere,

 ‘Yanci ag garai rubuta shi a ware,

 Tabbata ka cire shi ka ware bare,

  Ba a raba shi tarsashinsa ga tsarawa.

 

389. Yanka, yanke-yanke ko yayyankewa,

 Sara, sare-sare ko sassarewa,

 Datsa, datse-datse ko daddatsewa,

 Ɗinki, ɗinke-ɗinke ko ɗiɗɗinkewa,

 Girka, girke-gireke ko giggirkawa,

  Zanawa, karantawa da rubutawa.

 

390. Jifa, jefe-jefe ga jejjefawa,

 Kamu, kame-kame ga kakkamawa,

 Ɗauri, ɗaure-ɗaure ko ɗaɗɗaurawa,

 Damu, dame-dame ga daddamawa,

  Dubi, dube-dube ga duddubawa.

 

 

391. Darkake da daddaƙewa da dakewa,

 Ka ga niƙa da ninniƙawa da niƙewa,

 To yage da yakucewa, yagewa,

 Mammatse da lanƙwashewa, miƙewa,

  Matsetseniya ka sa ƙwai murjewa.

 

392. Kalma kowace iri in aiki ce,

 A gajera ta zo a duba a rubuce,

 In ma doguwa a kalma ta kasance,

 Duk yada tat taho rubutu a taƙaice,

  Haɗe ake sa ta can ga dokar zanawa.

 

393. Komi an ka aikata nan a rubuce,

 Ko kuma za a yo shi ba ko jinkirce,

 Za a yi, an yi shi wanga kwatance,

Matuƙar an ka ce da kalma aiki ce,

  Ta zama aikatau ka lura da ganewa.

Post a Comment

0 Comments