In kin karanta ki yi sharing please
Juyawa ta yi ta re da yin ƙunƙuni lokacin da ta ji Muryar Momy tana magana daga bakin ƙofa ita dai tasan ba ta rufe ƙofar ba, wannan ya sa ta juyawa tare da jan maya fin rufar ta dan zaton ta mafarki take sai dai jin muryar Momy ta yi a kan ta tana fadin " wai Hafsa ba zaki ta shi ba sai na ɗala miki duka"
A hankali ta
tashi tana miƙa, "Mum bafa mu da lecture yau dubi agogon yanzu fa 7 ta
yi?"
"Kina jin
ta ko" abin da kawai Hafsa ta ji momy ɗin
ta ce kafin ta saka mata waya a kunne, muryar yayar ta ji tana faɗa "Hajiya ki shirya
kije gidan kakan nin su Kalil ki ɗauko
su ki kawo su nan su ƙarasa sati guda ɗin
kan a koma"
Mum ba ta jira
amsar Hafsa ba ta fice tana ci gaba da wayar ta " ai ke kika kyale su
mutane sunbi sun mallake miki yara"
" To Mum
ya kike so in yi Mansur ya nuna dole sai an kai su, yau ɗinma tun jiya na dira masa mitar nawa iyaye ne
baya son su dinga shiga shi ne fa ya ce to in ɗauko
su siyi sati"
" Ai kuwa
zaiga sati ki haɗa ma
Kalil ɗin uniform ɗin sa in an koma sch din
Usman ya dinga Kai shi ita kuma ki haɗomin
kayan ta in ga in yana da kunyar zuwa ya ce in ba shi su"
Dariya Farida
ta sa " thats my Mum" suna gama tattaunawa bayan ta katse wayar
"Hafsa!" Momy ta kuma kwala kira bayan aje waya.
Rai a cinkushe
Hafsa ta fito tana miƙa da hamma, kai tsaye wurin aje abinci ta nufa tasan tun da
Mum ce ta ke son ta fita da wuri ta dafa breakfast, kamar yadda ta za ta ta
kammala komai tea ta haɗa
ta ɗebi chips da
soyayyen kwai ta yo falon dan ba ta son cin abinci kan dining table, cak ta
tsaya lokacin da taga Yaya Usman sam ba ta yi tsammanin ganin sa ba a yanzu,
daurewa ta yi ta ce "yaya ina kwana"
Tsaki yaja
"mene wannan?" ya nuna mata kayan jikin ta.
"wai ke
Hafsa Sau nawa kike son in faɗa
miki ki daina fitowa falon nan da kayan bacci"
Kallon kanta
ta yi " but yaya mene ne matsalar kayan nan?"
Hannu ya kai zai make ta ta yi saurin kaucewa
tana dariya, ɗakin ta
ta koma mintina baifi ashirin ba ta fito tsaf da ita har lokacin Momy na zaune
tana kallo " yawwa Mum ni na wuce Bala ne zai kaini ko?"
"Eh ki
biya ta gidan yayar taki za ta baki kayan su"
"Tom"
kawai ta ce ta fice
A bakin gate
ya parker motar bugu biyu mai gadi ya buɗe
ta shiga da Mijin Faridan ta fara cin tozali.
"lah yaya ashe ma kana gida?"
Dariya ya yi
"yau sarkin rikici ce a gidan namu mukan munyi fushi"
Murmushi ta yi
" a'ah dan Allah, in kun fushi dani ai da matsala, sai in shiga ruɗani, Mun ta shi lafiya ta
faɗa lokacin da ta ɗan risina"
"Lafiya ƙalau Alhamdulillah,
muje ciki ya ce"
"Ai na ɗauka fita zakai?"
"Ah ai
sai nayi wa autar Abba rakiya zuwa falo, kafin in fita" dariya ta yi
"woni" suka sa dariya
A falo ta
zauna inda ya shiga ciki, sai dai wanka ya tarar da matar tasa na yi wannan ya
sa shi komowa suka ci gaba da hira da Hafsan suna ta dariya Farida ta fito tana
taku dai dai tamkar amarya kamshin ta ya mamaye falon, cike da fara'a Mansur ya
ɗaga ido ya kalli
matar tasa
"eyye sai anci tarar ki wato da a ce Auta
ba ta zo ba duk wannan wankan haka zan missing kike nufi?"
Murmushin da
tasan yana rikita shi ta masa cikin salon tata yaudarar ta ce kaima dai ai sai
kasa ayi tunanin bana ma gayu fisabilillahi mene cikin wannan shigar kofa mai
ban shafa ba" ta faɗa
lokacin da taɗan juya
idanun ta bayan ta ɗan
kalli jikin ta"
Miƙewa ya
yi yana dariya " ke ko Allah in mutin ya biye miki sam ba zai fita ba, ƙanwar
mu agaishe mun da su Abba," dariya ta sa ta bi shi sai ka dawo min tina kaɗan ta dawo tana murmushi.
Sun jima suna
hira da Hafsa kafin ta ɗauko
mata kayan yaran ta bar gidan zuwa gidan surukan nasu, tamkar wata babba ce ta
zo haka sukai ta nan nan da ita ya yin da Khalil ke ta faman murna da tsalle
tsakanin jikin Hafsa da Gwaggo wato kakar sa.
Khairat Bacci take
Gwaggo da kanta ta saɓata
a kafaɗa tasanya ta
cikin mota tana faɗin
" Allah dai ya sa ta zauna dan tun da aka kawo ta yayen nan ba ta yadda da
kowa sai ni"
"In taƙi
yadda ba sai a mayar wa da Babar ta ba" Hafsa ta faɗa suka sa dariya duka inda suka shiga mota
Khalil na ɗagawa
gwaggo hannu aka ja motar.
*****
Duk da cewar
an musu orientation haka kawai tsoro ya cika shi tunanin yadda za ta kasance
masa da da ɗaliban ya
sa gaban sa ke ta faman faɗuwa,
yau shigar manyan kaya ya yi sosai haibar sa ta fito, nutsuwa da kyansa suka
kuma bayyana, kallo ɗaya
za ka masa kasan shi ɗin
nutsattse ne.
Inna na bakin
wuta tana mulmula tuwon siyar wa na safe ya fito, ɗauke da kwano da alamu na abin cin da ya yi
kari ne, Inna ni zan wuce asamu a addu'a walllahi tun ɗazu gaba na ke faɗuwa ji nake tamkar bazan iya ba.
Ɗagowa
ta yi tana murmushi " kaima dai Muntari yo ai in Sha Allah tinda ka samu
damar tsallake ɗaukan
aikin za ka iya ne shi ya sa suka ɗauke
ka"
Ajiyar zuciya
ya yi " kin san yaran masu kuɗi
koyar da su sai anyi haƙuri"
"Ba fa su
da matsala ba ga sunan ko ina muna ganin su ba, in zanma misali da yaran gidan
Alhaji Sani in ka dubi yadda suke da nutsuwa da tarbiya yaran talakawan ma ba
su da ita"
Murmushi ya yi
" wallahi Inna har kin kwantar min da hankali bari in je kar in
makara"
Miƙewa ta
yi har soro ta biyo shi, "Allah ya tsare min kai ya bada sa'a ya sa a fara
a sa'a"
Cike da kwarin
gwiwa ya fice bayan ya ce "amin"
Da kwarin
gwiwa ya tura gate ɗin
makarantar ya shiga ɗauke
da littattafan da aka ba shi dan zuwa ya yi nazari ya kuma haɗa lesson plan dan David yaƙi
yadda ya bada lesson plan in wurin sa.
Kai tsaye SS 3
ya wuce nan yake da period ɗin
farko, sam baiyi tsanmanin ganin ajin da ɗalibi
ko guda ba, dan yadda ya sha ji ana faɗe
shi ne yaran masu kuɗi
makarar su ta yi yawa.
Cike da
girmawa suka gai da shi ya gabatar da kansa matsayin sabon malamin Physics
kafin ya koma kujerar zaman malami ya zauna, ya hau tambayar sunayyen su duk
cikin jiran takwas ɗin
ta yi a Kaɗa
kararrawar fara lesson, kafin takwas ɗin
har hankalin sa ya kwanta har son yaran ya shiga ransa sosai suke ɗan taɓa hira ana kaɗa kararrawa duk suka nutsu
suka hau fiddo da littattafan su, tsarin yaran ya birge shi sosai ba yau ya
fara koyarwa ba domin yana voluntary a unguwar su, nan Makarantar ‘yan
mata ayi shiru ma kawai ya ishi malami.
Motion shi ne
topic ɗin da aka ce ya
ƙara
yi musu da alamu malamin su na da ya iya koyarwa dan kuwa bai wani sha wahala
ba dan sun gane topic din sosai tun daga yadda suke watso masa tambaya da kumma
ba shi amsar tambayar da ya mu.
Lokacin bada
class work aka kaɗa
wannan ya sa shi rubuta tambayoyin sa ya koma ya zauna lokacin lokacin wa su na
masa tambaya.
Rike da
littattafan na su ya fito dan malamar Chemistry tuni ta hallara har ya fita
wani ɗalibi ya ce "
Sir pls Mai ka karanta?"
"Juyowa
ya yi yana murmushi abin da ka ce ɗazu
kanasonn karanta"
"Wow ɗalibin ya ce u mean engineering
no wonder na ji Ina son ka"
Dariya kawai
Muktar ya yi ya bar ajin sai da ya kai takardun nasu office sannan ya dawo zuwa
SS 2, tun a wurin orientation aka faɗa
musu ‘yan
SS 2 sai sun yi haƙuri da su, sai dai sam bai ga matsalar ba in ka ɗauke surutu ƙasa ƙasa
wanda shi tun a GGSS Dala ya saba da wanda ya fishi yadda ma ya fahinta sun fi
SS 3 ɗin ƙoƙari...
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.