In kin karanta ki yi sharing
"Wai dan Allah Hafsa ke wacce irin mutun ce?, kin kira mutun kince ya zo ya taimaka ya koya mana, kuma ya zo kin ce yunwa kike ji" Bilkisu ta faɗa a fusace cikin faɗa fada.
Juyowa Hafsa
ta yi cikin halin ko in kula "Please Hajiya dena mun ihu, kina ji fa ya ce
zai je gun abokin sa ɗan
level five ya jira mu ai ko addini ya bawa yunwa haƙƙin ta, in coke village ɗinne ba zaki ba ki je gun
sa ku fara" ta faɗa
gami da yin gaba ba tare da jiran amsar Bilkisu ba.
Ƙwafa
kawai Bilkisu ta yi tare da bin bayan Hafsa rai ɓace.
Sai da suka
sai lemo da cake sannan suka wuce gun ma su gurasa, Hafsa na son gurasar sosai
tun randa ta fara ci shike nan kullum sai ta siya ada ƙyankyamin ta ma take anma
tana jin ɗanɗanon ta ƙyankyamin
ya bar ta. Suka wuce faculty of engineering ɗin
dan can sukai za su haɗu
bilayi suka hau yi har Hafsa ta ɗauki
wayar ta tana neman Number ɗin
sata jiuryar sa na musu magana.
Shi kuwa zaune
yake suna hira da Umar abokin sa lokaci-lokaci yana duba agogo sam baya son
jira kawai dai dan yaran sun takura masa ne, kullum ya tuna yaddda suka haɗu sai ya yi dariya, yana
zaune yana koyawa Umar Mechanics da yake carrying suka ji muryar ta, ta musu
sallama," Ina wunin ku?" ta ce suka amsa da" lafiya ƙalau,"
ta ɗan sa hannu ta ɗauki takardar gaban su,
mintina kaɗan da
dubawa ta juya " lah Bilki zo kiga ya iya Physics wallahi" wadda aka
kira da Bilkin ta matso "Allah Hafsa ki fita ido na bana son Bilkin
nan"
Dariya Hafsa
ta yi " sorry Bilkisu"
Kallon
takardar Bilkisun ta yi "lah walllahi ya iya kuwa"
Ba tare da
wani tunani ba, Hafsa ta ce " kawo wayar ka in sa ma Number ɗin mu dan Allah za ka dinga
koya mana walllahi bamu iya ba," kasa magana ya yi ya miƙo mata
wayar ta rubuta ta ce " na yi saving Suna Hafsa ita kuma Bilkisu me zan
sa, dariya ya sa "Ba shir zaki sa but ni bance zan koya muku ba
gaskiya."
"Dan
Allah ka taimaka" ta ce
"Oktom ba
yanzu ba kumin message ɗim
sanda kuke da free time zan duba tamu time table in"
"To mun
gode"kawai Hafsa ta ce taja Bilkisu sukai gaba suka bar Umar da Ba shir da
mamaki.
Umar ne ya taɓo Ba shir wanda ke ta
murmushi bayan tuna yadda suka haɗu
"waɗancan ba
yaran da kake jira bane?'" ta taga Ba shir ya leƙo kun gann nan wayar ya Hafsa
ta mayar suka haura saman.
Zaune suke
yana faman bayani ya yin da Bilki ta mai da hankali sosai har tambaya take
jefawa ya yin da Hafsa ta mai da hankalin ta ga gurasar ta da lemon ta, Ba shir
ne ya kalle ta ya girgiza kai kafin ya ce ya ce, “ai sam electricity and
magnetism ɗin nan ba
shi da wuya amma Hafsah tafi mai da hankali kan gurasar.” Bilkisu ce ta fara
dariya " hmm ai in kaga ta mayar da hankali to ta cinye" Bilkisu ta
faɗa, amma duda haka
ko a jikin Hafsah sai ma kafaɗa
da ta ɗage musu, tare
da zuƙar
lemon da ke hannunta tana kallon yadda yake ci gaba da rubutun yana bayani.
Kusan awa guda
ya yi yana koya musu, ba laifi ta dan tsinci wani abun daga ciki. Ita dai
burinta bai wuce ta yi passing ba. ba ta damu sai makin da ta samu ya yi yawa
sosai ba tun da shi kadai ne course ɗin
da ba ta ganewa ko Organic da 1301 da mutane ke tsoro ba sa razana ta. Sam ba
ta so ma ta gayawa Abba cewa ba ta iya ba, yanzu zai ɗaga hankalinsa akan sai ya nemo me nuna mata
ita kuma ba ta so ya nemo. Kusan ɓata
lokaci za ayi don sam ba ta ƙaunar course din balle ta fahimce shi.
Sai da me
tutorial din ya ba su assignment suka masa godiya tare da ba shi lemo da cake ɗin da suka siyo yaƙi amsa
Hafsa ta ajewa Umar gaban sa, sannan suka taso suka tafi.
“Hnmm wallahi
gwara ayi test dinnan mu huta. Duk nabi na gaji da mafarkin course dinnan.”
Bilkisu ta fada suna saukowa daga bene.
“Ke nima.”
Hafsah ta ba ta amsa tana hamma. Da alamu ta gaji sosai. Wajen kujeru suke samu
suka zauna jiran direban Hafsah.
Ba su wani
jima ba ya zo ya dauke su.
**
Tun da Inna
Kulu ta ji labarin ya samu aikin nan wani irin farinciki ya lullube ta tana
gyara kayan miya tana waƙe waƙen farin ciki, Harira da ta shogo ne ta ce towo ka ce yau za
mu yini da yunwa har yanzu ba akai markaɗe
ba, kinga Malam ya aikon in siya masa Taliya da wake sai dai ke nan a zuba masa
da mai.
Ɗagowa
Inna ta yi tana Murmushi "a'a wannan na gobe ne yanzu nake shirin Hajara
ta zo su ɗauki na
kaiwa Bakin kasuwar nan kafin rana ta kwalle"
"Haba
koda na ji to na dari biyu za a ban taliyar sai waken hamsin ya ce karasa
salak" Harira ta faɗa
Amsar kwanon
da kuɗin Inna ta yi
tana ci gaba da ‘yan waƙe waƙen ta, " wai Inna kulu albishir ɗin Hajji aka miki ne?, Tun da na shigo na gane
kina cikin farin ciki"
Dariya Inna ta
yi " Bari kawai Harira, yaron nan ne yasamu ailki a sa masa albarka"
Buɗa Harira tasa oh danma ba
ni da hanci ai da har gidan mu sai anji, Allah ya dafa ya sa duk mu
anfana"
"Amin
kedai Harira Inna ta fada dedai lokacin da take miƙo mata kwanon
taliyar"
Yamma ce lis
iska na ƙaɗawa a hankali, Wanke wanke
sukeyi ita da Saratu bayan sun kammala.
Saratu ce ta
dubi Inna lokacin da ta miƙe dan ɗaukan
kwadon kwanunakan “Inna kuma wai Yaya barin gida zai naga Hotoro da Nisa?”
Shiru Innar ta
danyi kan ta amsa. “To ya za ayi shi canjin rayuwa haka yake ai. Zuwa daga nan
zuwa inda makarantar take ay ya yi masa nisa.”
“Toh wurin wa
zashi?”
“Wannan
saindai ki jira zuwansa ki tambaye shi.” Nan suka ci gaba da wanke wanken wanda
ba yadda basuyi da Innar ba akan ta dena taki sam. ta ce rashin aikin zai saka
ta tsufa da wuri. Girki daman ba wahala yake ba ta ba balle a ce ya ishe ta a
matsayin aiki.
Shiru sukayi
na dan lokaci akan tabarma, iska na kadawa. Suna zaune ne aka kira sallah duk
suka tashi sukayi alwala da tunani barkatai a cikin kawunnan su sam yanzu da
sukai maganar barin sa gida sai Inna ta ji ba daɗi
ba ta shirya rabuwa da Muktar ba. Ko wannen su yana hasashen yadda rayuwa za ta
ci gaba da zuwar musu bayan Mukhtar din ya bar gidan da zama da haka sukai
Sallah. Shi din jarumi ne kuma uba ne a gare su. Shi ne katangar gidan shi ya
sa suke ganin tamkar idan ya bar to wani gata ko lullubi da zai kare su daga
sanyin gari ya bar su. Mutanen unguwar ba kaɗan
ba suka sa musu ido ba musanman yadda shi kaɗai
ne namiji da yadda suke ciniki sosai. Zagi babu kalar wanda ba a musu. Girman
da Mukhtar ya yi ne ya sa ya danyi sauki. Da zarar ya daina kwana kullum a
gidan sun san abun zai dawo.
Su din ana
musu kallo da dama. Inna ba irin sunan da ba a kiranta da shi saboda kawai ba
ta ƙara
aure ba bayan rasuwar mijinta. Kuma sana’ar ta ma ta sayar da abinci da takeyi
ance abu take zubawa a ciki shi ya sa magidanta da yawa suke mata ciniki sosai.
Yaran gidan kuma ko wacce sai a ce yar mace ce ba wata tarbiyya suka samu ba.
Suna tafe ana nuna su a unguwa. Dukka wannan sunyi sauki saboda Mukhtar din da
yake da kwarjini da rashin daukar raini daga jama’a.
**
Tsaye take
gaban mudubi a cikin ɗakin
ta wanda yake madaidaici ne tana kwalliya. Ɗakin anyi masa fenti purple da fari, daga
gefen gado kuma sticker din bismillah ce da frame din ayatul kursiyy. Dayan
bangon kuma stickers din motoci ne wanda suke bala’in burge Hafsah. Dakin bai cika tarkace ba, daga
madaidaicin gado sai drawer sa da mudubin kwalliya. Daga gefe kuma wata kujera
ce ta ado sai dai Hafsah ta cika ta da kaya. Daga kan takalma ne zuwa hijabai
da kayan da ta cire, duk ta loda su a kai. Har jakarta ma da handouts ma anan
suke samun masauki shi ya sa suke saurin yagewa. Da zarar ta shigo dakin abun
da ta fara cirewa akan kujerar za ta wurga shi.
Bayan wannan,
dakin tsaf yake. ta yi shara kamar ko yaushe haka ma gadonta ta gyara shi tsaf.
Daga kasan gadon kwanon abincin da taci ne bayan ta shigo.
Fitowarta ke
nan daga wanka bayan ta tashi daga baccin gajiyar da ta kwaso.
Tana kokarin
zana ‘yar
siririyar jagira aka buɗo
ɗakin. Ta mudubi ta
hango Mummy tana yatsina fuska. Doguwar mace ce, fara mai tsananin kyau wadda a
gunta Hafsah ta ɗauko
kysu. Sanye take da atamfa gold wadda aka mata dinkin bubu da shi an bi zanen
adon da duwatsu masu sheƙi. Hannunta na dama ta ƙawata shi da bangle din gold guda biyu ga
zobunan gold biyu a yatsunta. Hannun hagun ta dauke yake da agogo da kuma zoben
azurfa. Kamar ko yaushe a cikin kamshi take don tafi bawa kamshin muhimmanci
akan kwalliyar fuska. Fuskar ta fayau, sai kyalli da shekin hutu take yi duk da
ko hoda babu.
“Mummy…”
Hafsahn ta yi saurin fada tana juyowa kafin mummyn ta fara mita.
“Hnmm jibi ɗakin mutum kamar ɗakin mahaukata. You should
be ashamed of yourself!” Ta faɗa
tana sake kallon dakin da har ji take kamar yana karnin datti. Ita macece mai
tsafta sosai.
“Mummy dawowa
ta ke nan fa.”
“Hnmm two
hours ago. Toh mutum dai tun da kazanta ya sa a gaba sai ya yi ta yi ai. Ni na fita
zan leka boutique naga cinikin yau da aka yi zuwa Magariba.”
Shiru Hafsahn
ta yi.
“Na san yanzu
zaki fara mita. In kina so kya iya zuwa gidan su Hidaya sai na dauke ki can
idan na gama. Baban ki sai jibi zai dawo.” Da haka ta fice. Jin an ambaci Hidaya
ya sa Hafsahn jin daɗi
sosai. Hidaya cousin dinta ce, yar yayar mummy wadda suke sa’anni. Dama sun
dade ba su hadu ba. Tun dazu kwalliyar da take yi don ta je ta siyo ice cream
ne ta dawo gida ta sha sannan ta duba assignment dinnan taga ko za ta iya. Amma
yanzu da Hidaya za su je.
A gurguje ta
gama shiryawa ta saka atamfa ta kashe dauri. Da sauri ta fito ta gaida driver
suka fita zuwa unguwar su Hidayan.
Suna zuwa ta
kira ta a waya. Da gudu itama Hidayar ta fito zuwa compound din. Suna tsalle n
murna da ihu suka rungume junan su.
“Longest time,
besty!” Ta fada with a strong accent. Hafsah ta tabe baki.
“Iyayi dai
Hidaya. Muje na gaida Ammi.” Da haka suke shige ciki suna hira.
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.