Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallah Da Matsatsun Kaya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene Hukuncin Mace Mai Sallah Da Matsattsen Kaya, Gashin Ta A Waje?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabinabi Muhammad .

Allah ya umurci bayinsa da yin ado ya yin Sallah:

يَا بَنِي آدَمَ خُذُوا زِينَتَكُمْ عِنْدَ كُلِّ مَسْجِدٍ

ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci. (Suratul Aarafi aya ta 31).

Malamai suka ce mafi karancin ado shi ne suturta al’aura. Saboda haka ne ma suturta al’aura ya zamo sharaɗi a Sallah. Sallah ba ta ingantaba face masallacin ya suturta al’aurarsa. Ba ason musulmi ya yi Sallah da kayan barci, ko kayan aiki, ko kaya masu datti, Allah kyakkyawa ne kuma yana son ado.

1 – Macce dukkan jikinta al’aura ne har gashinta. Wajibi ne ke nan ta rufe shi a cikin Sallah da wajenta. Idan macce tana Sallah sai gashinta ya bayyana (ya buɗe) kuma ta yi gaggawan rufe shi nan take, to babu laifi a cikin hakan, sallar ta ta yi.

2 – Sharaɗi ne macce tarufe dukkan jikinta ya yin Sallah, tun daga kanta har kafan ta. Idan mace ta lulluɓe jikinta da sura wanda baya bayana wata gaɓa nata, to sallarta ta yi. Saidai abin da akafi so shi ne a sanya sutura mai kauri, mai yalwan da baya bayyana surar jikin

3 – Idan macce ta sanya matsatsun tufafi mai nuna suran jikinta ta yi Sallah da su, sallar ta ta yi amma fa ta saɓa umurnin shari’ah na sanyan suturar kamala ya yin Sallah, laifinta na sanya matsatsun kaya kuma na nan a kan ta.

Makaruhi ne yin Sallah da matsatsun kaya ga na-miji da macce. Kuma hakan na iya kai ga Haramci. Sai dai Sallah ta yi.

Allah Shi ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments