In kin Karanta ki yi sharing please
Follow this
link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HWOGchc0ANFGLcqBcKeYhH
Yau cike da farin ciki Muktar ya fito daga makarantar sakamakon alba shin da aka biya da kuma extra bonus na extra lesson da suka fara, kai tsaye motar da za ta kai shi Mariri ya hau tun da ya fara aikin nan yake son zuwa gidan ƙanwar sa bai samu yaje ba sabida tsoron kar ya yi kuɗin mota gobe kuɗi ya masa short.
Shinkafa kwano
uku ya siya tare da wake kwano guda sai mai kwalba guda da magin ɗari biyu ya nufi layin nasu
fuskar sa ɗauke da
nushaɗi.
"Ga kawu
ga Kawu" yaron ɗan
kimanin shekaru shida ya rugo yana faɗa
murmushi Muktar ya yi tare da aje kedar hannun sa ya ɗaga yaron ba tare da la'akari da dattin da ke
jikin yaron ba"Noor ashe za ka ganeni?"
Nana ce ganin
an ɗaga ɗan uwan nata ta rugo da
gudu tumbur ba riga bare wando tana fadin "nima" dire Noor Muktar ya
yi tare da ɗala mata
duka kafin ya daka mata tsawa "jeki gida ta sa miki wando da riga"
yarin yar ta tsanyara ƙara tare da rugawa da gudu zuwa gida shi kuma ya kama hannun
Noor suka nufi gidan.
Kafin su ƙarasa
Rashida ya hanga ta fito ko ɗan
kwali babu kanta sanye da ɗaurin
ƙirji
tana faɗin "muje
uban waye ya da ke ki" ƙarasawa ya yi ta yi turus lah yaya
hararar ta ya yi ta koma ciki tana faɗin
"walllahi na ɗauka
wani azzalumin ne ya da ke ta"
"Ni ne
nan azzalumin" tsit ta yi ta shige ɗaki
takaici ne ya kama Muktar lokacin da ya yi karo da fo ɗauke da kashi wanda da alamu tun safe aka yi
dan har ya fara bushewa, ya mutsa fuska ya yi tare da juyawa da zummar zubda
miyau sai dai tarin kwanukan da ƙuda kebi ya sa shi daurewa ya hadiye abin
sa kafin ya shiga ɗakin,
ƙoƙarin
tattare kaya take dan sama masa inda zai zauna, girgiza kai kawai ya yi ya zauna
tare da aje ledar hannun sa.
"Yanzu
fisabilillahi Rashida kina kyautawa ke nan jibi gidan ki, ke kanki jibeki waye
zai ce ke ƙanwa
ta ce ba yaya ta ba?"
Ya tsina fuska
ta yi " yaya dan Allah ya zan yi da rayuwa ta ga yunwa ga ciki walllahi ba
ni da lafiya shi kuma bazai gyara ba sai randa na samu ɗan sauƙi in gyara" numfashi ya furzar
"anma yanzu shi fo ɗin
can ko Noor kika sa ai zai iya zubdawa"
"Wallahi
yaya ban san da shi ba, in banda yanzu da Nana ta shigo ban fito tsakar gidan
ba, ya aikin ta tambaya a ƙoƙarin ta son kawar da mitar rashin gyaran gidan da yake"
"Aiki
Alhamdulillah, yanzu ma daga can nake nace bari in zo mu gaisa ga wannan"
ya tura mata ledar gaban sa.
Da murna ta
hau buɗewa kai anma ka
kyauta Allah ya buɗa,
ya ɗaga arziki bari
kaga in ɓoye wannan
rabi rabi zan nuna masa shi ma in ya ce mun kun haɗu in bai ganka ba sai dai ya dinga gani a
faranci dan idon sa idon abincin nan zai kwashe ya siyar"
Muktar bai ce
komai ba ya miƙe " ungo wannan ya miƙo mata dubu ɗaya kya dinga siyen ice ni bari in je in yamma
ta yi liss tsadar abin hawa" har soro ta rako shi tana ta godiya ya yi
titi.
A bakin titin
suka Haɗu da Nura
mijin Rashida "lah Yaya barka da yamma ya faɗa
lokacin da ya ɗan
rissina da kai" hannu Muktar ya miƙa masa suka gaisa.
"Har ka
fito ke nan nima yanzu na fito daga gidan naje sayo gari tun safe Bamu samu mun
ci wani abin kirki ba" ya faɗa
lokacin da yake ɗan ɗaga ledar hannun sa yana
nunawa Muktar.
" Ayya
Allah ya ci gaba da dafa mana" ya faɗa
tare da zaro ɗari
biyar ya miƙawa
Nuran, ya amsa yana faman zuba godiya tamkar ya ba shi millions.
Cike da gajiya
ya koma Unguwar su kai tsaye wurin Malam audu mai lemo ya wuce fuskar sa ɗauke da annuri, " Lemo
za a ban ya miƙa dubu guda"
Mai lemon ya
amsa ya "anya ina da ɗari
tara kuwa?"
Murmushi
Muktar ya yi "ai yau na du zan siya anma a haɗamun da ayaba"
"Kai
Alhamdulillah, yau da raina naga addu'a ta ta amsu" mai lemon ya faɗa tare da miƙowa
Muktar lemon ya amsa yana murmushi.
Kasancewar
yanma ce ya sa shi tarar da ƙannen sa biyu na wanke wanke, Inna zaune
tana ferayar kabewa Juwairiyya na tsifa tausayin mahaifiyar tasa da ‘yan
uwan nasa ya cika shi shikam zaiso ko sau guda ne wataran ya zo ya tarar da su
suna hutawa sai dai in har suna son rufawa junansu asiri dole su aikatu.
Sannu da zuwa
suka masa ya zauna gefen Inna, "wash Allah na gaji yau ɗinnan" inna ce ta dube
shi "gashi nan kuwa ka yi zuru zuru, yanzu nake cewa ko lafiya yau ka kai
dare"
"
Walllahi nima nagani, da aka tashi ne na biya gidan Rashida duk tana gaishe
ku"
Washe baki
Inna ta yi jin ya ambaci ‘yar uwar tasa " kai amma ka kyauta walllahi, Allah ya bar
zumunci"
"Amin"
ya ce tare da miƙa mata lemon da ya siyo ga wannan ba yawa an mana alba shi
sannan ya ba ta dubu uku ya miƙawa kannen nasa dubu guda guda, suka hau
murna da godiya.
Daki ya shige
tare da faɗawa katifar
sa Juwairiyya ta shigo masa da abincin sa "Allah dai ya sa baki sa mun
gashi ciki ba?"
Murmushi ta yi
"kai yaya wane gashi abu a rife" bai ce komai ba ya buɗe ta yi waje.
Washe gari sai
da ya zauna ya kasa kuɗin
sa yadda za su ishe shi sannan ya wuce shagon Bala ya biya shi ba shin sa kafin
ya wuce makaranta.
***""
Maganar da
sukai jiya da Bilkisu lokacin da take cewa ita ba ta son hutun nan na mid
semester da za a fara yau Bilkisun ke ba ta shawarar mai zai hana ta dinga Bin
Abba sch ko ba ta shiga aji tun da tsakiyar term ne ta dinga ganin yara tana
jin ɗebewar kewa
wannan ya sa yau ta tashi da wuri ta nufi farfajiya dan jiran Abba ya fito.
Tana tsaye a
veranda lokaci lokaci suna hira da Baba mai gadi Abba ya fito yana gyara Babbar
riga turus ya tsaya " Hajiya Hansatu ba hutu kuke bane naga kin tashi da
wuri haka?"
Ya mutsa fuska
ta yi "Abba Hajiya Hafsa nake"
"Ok koma
dai mene?, Baki ba ni amsar tambayar da na yi ba"
Dariya ta yi
" munyi hutu shi ne nake son binka reading at home is boring," furzar
da iska ya yi "rikici dai Hansatu muje to"
"That's
my Abba, leƙawa
ta yi falon cikin ɗaga
murya ta ce Mum na bi Abba sch"
Sai da ta fara
zuwa ta gaida tsoffin malaman ta da ke makarantar sannan ta koma can ƙarƙashin
wata bishiya da ke nesa kaɗan
filin wasan ‘yan
makarantar ta zauna.
Tana zaune aka
fito break masu wasa suka zo suka hau lilikan da ke makale a filin da take iya
hanga nesa kaɗan da
ita, murmushi take lokacin lokaci dan tana iya fahimtar wasan da yaran suke.
Kamar daga
sama ta tsumayi muryar sa yana faɗin
"towo yau an rigani ke nan?" ɗagowa
ta yi sukai nasarar haɗa
idanu ya sakar mata murmushi itama murmushin ta yi, kafin ta ce "ina
kwana, Mai aka rigaka?"
Kujerar da
take kai ya nuna mata "lafiya kalau, nan wuri na ne kullum nake zama akai
during break"
Murmushi ta yi
"a'a da kujerar nan na magana da za ta faɗa
ma kujera ta ce kullum kanta nake zama tun muna student"
"Ah yanzu
ai kin bar makarantar bama kujerar ba, yanzu tawa ce" dariya tasa
"aikam dai bana tashi a gurin nan, ba dai laifi za mu iya sharing shi ma
dan ina ganin girman ka" ta faɗa
tare da ɗan matsawa
gefe.
Dariya ya yi
"toh ya zan yi tun da an mallakemun guri, wai da gaske kina ganin mutunci
na"
"Ga sheda
na matsama ka zauna a kujera ta" dariya ya yi ba tare da ya ce komai ba ya
hau makin ɗin
littattafan da ya zo da su in da ta mai da hankalin ta kan yaran da ke wasa....
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
Domin samun
littattafan Hausa shiga link ɗin
group, sai dai group ɗin
ba wai specifically na littafin Ko da so bane, tallan sa kawai aka sa a shafin
littafin, zaki iya turo littafin ki, ko tambayar littafin da kike buƙata in
Allah ya sa akwai a turo miki.
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.