In kin Karanta ki yi sharing please
Tsaye take gaban notice board din kamar yadda sauran dalibai suke tsaye da littafan su da biro suna kwafar draft timetable ɗin da aka kafe dazu. Ita kaɗai ta zo makaranta a cikin kawayenta yau shi ya sa ma take tsayen ita kaɗai.
Hannunta ta
kai kan layin course din farko tana karanta da code ɗin cike da damuwa.
“Eh
electricity ne. da shi za mu fara.” wani da ke bayan ta ya faɗa, A nan take ta ji kafafuwanta
sunyi mata nauyi. Ita fa ba ta shiryawa exam ɗinnan
ba. A bazata ta zo mata kuma a ce course din da ba ta iya ba da shi za a fara.
Test dinma da aka yi kwafa ta yi kuma malamin bai ma kawo musu sunga nawa suka
ci ba.
Jiki a sanyaye
ta bar tsakiyar jama’ar da suke ta faman tofa ra’ayinsu. Idanunta suka ciko da
hawayen fargaba. Nan da nan ta kara sauri ta bar wurin. Female rest room kawai
ta nufa. Tana shigo ta fara hawaye. Sai da suka gama zuba sannan ta wanke
fuskarta ta fito. Driver dinta ta kira kawai sannan ta shiga masallaci ta
kwanta tana jiransa. Tunaninta bai wuce yadda zatayi ta tsallake jarabawar nan
ba.
Tana kwance
kiran dreba ya shigo. Jiki ba kwari ta tashi ta tafi in da ya yi fakin.
Ko da suka isa
gida babu wanda ta tsaya gaisarwa kamar yadda ta saba. Ji take abubuwan sun
cunkushe mata a lokaci guda kuma ba ta san ta inda za ta fara ba.
Dakinta ta
fara shiga ta yi jifa da jakarta sannan ta fada bandaki inda ta yi wanka, tana
wankan tana hawaye har sai da ta ji saukin abun da ya tsaya mata a rai sannan
ta yi alwala ta fito.
Sallar la’asar
ta fara yi sannan ta kwanta. Kugin da cikinta ya fara ne ya sa ta tuna ba ta ci
abinci ba. ba a son ranta ba ta nufi kitchen. ta yi sa’a babu kowa balle a sakata
ciwon bakin magana. Tana buɗe
flask taga dambun shinkafa, nan take mood dinta ya fara chanjawa ta diba ta
koma daki.
A hankali take
cin abinci wanda duk wanda ya hangota cewa zai yi wasa take da abincin. Sai da
ta gama ta sha ruwa sannan ta dauki wayarta ta kira Bilkisu.
Sai da ta yi
ringing din farko Bilkisu ba ta dauka ba. Duk da ba son yin magana take ba haka
ta sake kiran wayar. Sai da ta kira kusan sau uku sannan kaninta ya daga.
“Bata da
lafiya, kuma ta kulle kanta a daki.” Gaban Hafsah ya fadi, ta rasa abun cewa.
“Hello?” Ta
fada don ya maimaita abun da ya ce ta tabbatar ta ji daidai.
“Yaya Bilkin
ta rufe dakinta kuma taqi magana dani.” Duk da haka Hafsah ba ta fahimci abun
da dan shekara bakwai dinnan yake cewa ba. Mikewa ta yi ta nemi abaya ta saka
cike da tashin hankali da tunanin me ya sami aminiyarta ta. Banda wayarta babu abun
da ta dauka ta fito. Jin shiru sosai har yanzu ya sa ta fahimci Mumy ba ta nan
yau. Watakila fitar yamma ta yi. Gate kawai ta nufa ba tare da tabi takan dreba
ba taga me gadi yana zaune.
“Hajiya Karama
sannu da fitowa.” Fuskarta babu fara’a kamar yadda ta saba ta ce,
“Don Allah ara
min dari biyu in na dawo zan dauko maka. Bana son komawa ciki ne, sauri nake.”
Ba musu ya
zura hannunsa a aljihu ya mika mata ita kuma ta yi gaba tana godiya. A ransa
yake tunanin ko me ya sameta. Ko me yake damunta. Yarinyar tana da mutunci
sosai da girmama manya. Ba ruwanta da bambancin da ke tsakanin su na nauyin
aljihu. Sosai yake jin dadin aiki a gidan sabanin gidan da ya baro inda yaran gidan
suke masa kallon raini da rashin sanin darajar dan Adam.
“Allah ya sa lafiya.”
Bai ma san sanda ya fada ba a fili saboda abun ya dame shi.
Ko da Hafsah
ta isa titi kafar ta ta yi budu budu saboda saurin da take yi.
Me adaidaita
sahu ta tsayar ta shiga sannan ta fada mishi unguwar da zai kai ta. Sauri yake
amma gani take kamar ya rage saurin adaidaitar.
“Malam dan
Allah ka kara sauri.” Ta fada tana kallon gefen titi. A ranta take tuno wacece
Bilki. Ta san duk abun da zai hana Bilkisu zuwa makaranta ba karamin abu bane
domin ita din jaruma ce kuma mutum ce mai kwazo da yarda da kanta. Ko kadan ba
ta da wani weakness da Hafsah za ta iya cewa gashi. Komai nata a tsare yake,
komai nata a lissafe take yin sa. Komai Bilki ta kan kalle shi da zuciya me kyau.
Abun da zai karya ta ba karamin abu bane.
Duk da ta
kasance a hannun kishiyar maman ta tashi wadda take tamkar uwa a gareta,
Bilkisun ba ta taba kallon cewa rayuwarta nada wata tawaya ba saboda rashin
uwa. She was always positive about her life. Komai zafin abun da ya same ta
alhamdulillah za ka ji ta fara fada. Ko mitaar dan Adam yau da gobe Hafsah ba
ta jin Bilkisu tana yi.
Tayi nisa a
tunani ta tsinci muryar me adaidaita sahun yana tambayarta ina zai yi. Hanyar
ta kalla taga har an wuce kwanar tana ta faman tunani.
“Mu koma baya
dan Allah. Yi hakuri. Kwanar ita ce kafin wannan.” ta yi sa’a ba masifaffe
bane, ba musu ya koma bayan. Suna shiga ta ce ya yi ta sauka tana mika masa
kudin. Ko chanjin da yake nufin ba ta ba ta tsaya karba ba.
Ko da ta isa
gate din gidan nasu turawa kawai ta yi ta shiga. Directly part din yaran gidan
ta nufa. Bakinta dauke da sallama ta shiga falon amma babu kowa. Corridor din
falon tabo inda ta samu yayyin Bilkin suna zaune suna hira kamar babu wani abu
da ya faru.
“Ya Iftee ina
wuni…” ta gaishe ta. Sai da taja aji sannan ta amsa. “Lafiya. Ta kira ki ke nan?
Tana sama.” Da haka ba wanda ya kara magana. Akwai rashin jituwa tsakanin
Bilkisu da yayyan nata wanda suka hada uba daya. Bilkisun ta taba gaya mata
cewa suna jin haushin ta kan cewar baban su ya fi kula da lamarin ta.
Yanzu ma abun
da take wa kuka haushi suke ji.
Hafsah ta kai
minti biyu tana buga kofar amma ba ta buɗe
ba.
“Bilkisu ki buɗe min this minute. Wannan
wani irin abu ne? In kuma in koma toh?” Ta tambaya tana hararar kofar. Karar
mukulli da ta ji ne ya sanar da ita da Bilkisun za ta buɗe mata.
Tana budewa
taja Hafsah ciki ta rufo kofar gami da sake rushewa da kuka.
Rungume ta
Hafsah ta yi tana jin tausayin Bilkisun. Kuka takeyi da dukka zuciyarta wanda
ya sa Hafsahn ita ma ta fara tayata. Sai da ta yi me isarta sannan sukayi shiru
ta goge hawayen, idanta jajir.
“Abba ne. Aure
zai min wai. Tariq zai aura min…” Ita kanta Hafsah sandarewa ta yi. ba ta san
waye Tariq din ba amma dai tasan Bilkisun tana da crush duk da sam babu auren a
plan dinsu.
Shiru sukayi
ba wanda ya yi magana.
“Tariq fa ex
din Ya Iftee ne. This union is as good as nothing. Kuma wai auren hadi. Abba
bai tsaya ya ji ta baki na ba fa…”
Ta sake
fashewa da kuka. Janyowta kawai Hafsah ta yi tana bubbuga bayanta alamar
rarrashi in da a ranta take tunanin makomar da kuma dalilan tashin hankalin
Bilkisun.
**
“Nace ba,
Muntari ka cire wani abu a kaiwa Baffan ku.” Inna ta fada tana samun wajen zama
kusa da inda yake marking.
Sai da ya ba
ta fuska sannan ya ce,
“Haba Inna ni
fa ba ni da wani Baffa. Haka kawai sai ki yi ta makala mana mutanen da ba son
mu suke ba.”
Kalaman nasa
suka ba ta mata rai saboda sam baya jin fadan da take yi masa shekara da
shekaru. “Ahir din ka! Baka da wasu yan uwa sama dasu. Dangin mahiafinka ai
sune dangi.”
Rufe littafin
ya yi sannan ya lumshe idanunsa yana tuno wasu abubuwa da suka faru wanda ba
zai taba mantawa ba.
“Inna…”
Ba ta jira ya
ce komai ba ta tare shi da amsa. “Ko dubu biyu ce ka kawo ni zan kai musu.
Zumunci ba zai ba ta dorewa ba in har za ka dinga duba abun da ya faru a baya.”
Shiru kawai ya
yi saboda ba zai iya musa mata ba. Har zaice sai wani watan toh amma saboda
gudun bacin ranta ya ce toh zai bayar sannan ya dauki littafin ya ci gaba da
maka wa yana jinjina hazakar daliban makarantar.
***
Bayan kwana
biyu Bilkisu ta ware ta ci gaba da harkokinta bayan Hafsahn ta yi ta faman zuwa
gidan nasu kullum tana ba ta baki ko dan exam din da take tunkarar su. Yau ce
ranar farko da za su rubuta physics duk da Objectives ce. Suna zaune suna amsa
past questions Bilkisun ta yi shiru har sai da Hafsah ta yi snapping fingers
before her face.
Ajiyar zuciya
ta yi. “Kin san me? Tariq din ya zo jiya and he seems nice. Ni matsalata bai
wuce yadda Umma ta fara min acting ba ita da Ya Iftee. They turned their backs
against me bayan they’re my rocks. I bask in their glory.”
“Hakuri zakiyi
har su fahimci ba laifin ki bane.”
Bilkisun ta
mai da kwallar da ta zo idonta. “Sun sani. Cewa sukayi haka jinin mu yake ni da
mahiafiyata, snatching mazajen mutane muka iya. He was her ex fa for God’s
sake.”
Takardar
hannunta Hafsah ta ajiye sannan ta kama hannun Bilkisu. “It’s not just about
that. Akwai wani dalilin da ya sa suke miki haka kuma shawarata a gareki shi ne
ki zama Billyn da na sani. Grow a thick skin…”
Kafin Bilkisu
ta bada amsa wani lecturer ya zo wucewa da booklet da answer sheet.
“Innalillahi…”
Hafsahn ta furta tana mikewa ta ci gaba da duba takardun hannunta. Ita ba ta yarda
ba sai cramming answers take saboda ance su ɗin
ne dai ake maimaitawa a hargitse duk shekara.
Har dalibai
suka fara shiga halls Hafsah ba ta nufi kofa bama. “Hafsah drop the papers kar
a hana mu shiga.” Bilkisun ta yi gaba Hafsah na binta a baya tana ta cramming.
A karshe dai
ita ta shiga last aka raba musu papers din. Sai dai me? Wannan karan ko
question daya bai dawo daga past questions ba.
Hall din ya yi
tsit, cikin dalibai kamar Hafsah ya debi ruwa tsabar tashin hankali. Sam Hafsah
taki yarda ma question paper din su ce. Watakila mistake aka yi hakan ya sa ta
daga hannunta alamun tana son magana.
“Sir, ina
tunanin question din yan level three ne.” Ta fada tana wuri wuri da idanuwa.
Dariya ya yi kadan.
“Level 100, Electricity and magnetism. Read that again and don’t talk again. In
baki da abun rubutawa you can submit.”
Da haka ya sha
kunu inda Hafsah ta kurawa paper din ido kafin rai a cinkushe…
Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.