Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko Da So... (Kashi na 24)

“Ashe ma kin iya kika zauna wasa..” Mukhtar ya fadi, yana duba assignment din Hafsah wanda guda daya ne kadai ta yi mistake shi ma daga formula ne. Cike da jin dadi ya sake kallonta ya ce,

“Kawai dai bakya mai da hankali ne.”

Hafsah ta sunkuyar da kai tana murmushi sannan ta ce, “ai malamin ne wallahi abun haushinsa ya yi yawa. Wai kaga mutum ya sako wata yellow din shadda ga bakin glass kamar dan daba.”

Mukhtar ya kasa rike dariyar sa ya dara. “Allah da gaske. Ni gaba daya sai na ji haushi yake ban kuma dama ni ba son physics nake ba.”

Ya kalle ta cike da mamakin yanayin tunanin ta da yadda ta dauki rayuwa. “Toh yanzu me ya chanza? Nima dai kalli kiga silifas na saka.”

Hafsah ta leka kafarsa taga silifas dai da ta sani amma sai ta ji haushin Mukhtar bai kama ta ba.

“Ai kai daban ne, you’re charismatic and just ka hadu kawai…” kamar wadda ta yi sabo, sai ta yi saurin rufe bakinta ta sadda kanta kasa tana ji kamar ta nutse don kunyar abun da ta fada.

Mukhtar kuwa zuciyarsa ta cika fam da farin ciki. Ya rasa inda zai saka kansa a lokacin, fuskarsa dauke da yalwataccen murmushi ya mai da kallonsa kan littafin da ke hannunsa. Sun jima a haka ba wanda ya sake cewa komai. Ko wannen su zuciyarsa tana dokawa da sunan dan uwansa.

Mukhtar ya gyara murya sannan ya yi kokarin ture yanayin da ya ziyarce su. Hafsah ta dago ta kalle shi, kafin ta dauke kai sai da idanunsu suka sarqe suka yi murmushi sannan kowa ya kau da kai.

Ya sake gyaran murya yana nemo jarumtakarsa da ta gama ba cewa a lokacin sannan ya dauki textbook din gefen sa ya bude.

“Tun da kin gane capacitors, inaga yanzu sai mu fara da resistors ko?” Ya fada wanda ya sanya Hafsah ta yi ajiyar zuciya sannan ta kalle shi tana gyada kai. Zuciyarta ba ta daidaita bugunta ba sai ma kara saurin da take yi.

Ta rasa yadda za ta yi ta nutsu ta nuna ba abun da ya faru har sai da kalaman da ba ta san yadda suka hadu ba suka fito ba, ta ce “uncle Mukhtar wasa nake fa kawai dai ka iya koyarwa ne.”

Mukhtar ya gyada kai. “Na gode.”

Bata kalle shi ba ta yi shiru. Tun da ya fara bayani kanta kawai take gyada mishi ba tare da ta furta komai ba har suka gama karatun ranar. Daidai sanda ya zo tafiya ne ya sa ya ce mata ya kawo mata abu ya ajiye a kofar dakin me gadi.

Cuke da jin dadi da manta wancan yanayin kunyar da ta saka kanta a ciki ta bi shi ya mika mata flask madaidaici.

“Wainar gero ce, inji Inna.”

Taji dadi sosai kamar ta yi tsalle.

“Na gode sosai. Bari na koma. A gaishe su dan Allah.” Ba tare da ta jira amsarsa ba ta gudu cikin gida cike da farin cikin da tun kwanaki ba ta san silarsa ba. Kai tsaye kitchen ta wuce don ta zuba wainar in ta huce kuma ta yi warming a microwave.

Bayan Mukhtar ya yi sallama da mai gadi shi ma a hankali ya soma tafiya yana tunanin ta. Wani yanayi yana fusgar zuciyarsa game da Hafsah. Ya sani ya kamata ya dakatar da koma menene. Aiki ne ya kaishi ba sabo ba. Ko bayan haka ma sam ita ba kalar wadda zai yi sabo bane da ita. Watakila kuma shi yake ganin kamar kulawar ta a gare shi ta musamman ce. Watakila kawai kirki take masa with no strings attached. Ya tsaya a bakin titin yana sake maimaitawa zuciyarsa ta daina dokawa Hafsah ko da kuwa dukan da takeyi ba na neman wata alaka ba ce ta kawayence ko na so. Maimakon ya ji komai ya daidaita sai murmushin Hafsah ya sake fado mishi a rai.

A take zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri da sauri tana saka shi shi ma murmushin.

Mota ta zo wucewa ya tsayar ya shiga sannan ya samu hankalinsa ya chanja alkibila.

**

Mummy ta yatsina fuska tana nuna bacin ranta gami da nuna kyama ta kalli flask din da ke zaune a cikin sink. Jikinsa duk ya kode. Ko flask din ma’aikatan gidan bai kai munin wannan ba. Sai ma ta ji kamar har wani wari wari ne yake tashi daga sink din duk dan saboda flask din.

Ta sake kallonsa sannan ta wanke hannunta ta nufi dakinta saboda wayarta da take ringing.

Ko da ta isa ta tarar call din ya tsinke sai kawai ta ajiye wayar ta fita da tunanin waye ya kawo mata wani flask cikin gida.

A corridor suka ci karo da Hafsah wadda mummyn ba ta ganta ba tun bayan sanda ta fita daukar lesson.

“Kin yi wata bakuwa ne bayan kin shigo?” Ta tambayi Hafsah.

Hafsah ta girgiza kanta sannan ta kalli plate din hannunta. “Laa mummy wallahi na manta banyi miki bismillah ba. Wainar gero naci.”

Mummy ta kalle ta unbelievably, “wainar gero kuma? A ina kika samo ta Hafsah?”

Hafsah ta murmusa. “Uncle Mukhar ne… Innar…” ba ta karasa ba mummy ta dakatar da ita.

“Ban gane ba.”

“Innar shi ce…” ta sake katseta da wata tsawa me firgitarwa.

“Innar wa? Meye hadin ki dasu Hafsah? Wato har abincin alamajirai ake kawo miki kina ba ni kunya ko?”

Hafsah ta zumburo baki ta ce, “mummy ni nace fa ya kawo min. Wallahi kinga kuma har na saka wata a fridge.”

Mummy ta dafe kanta da ta ji ya fara sara mata saboda bakin ciki. Ta rasa yadda zatayi da wannan yarinyar. Wato abun Hafsah ya kai har abincin mutane take ci take kawo mata cikin gida. Irin mutanen da ba ta kauna musamman ma wannan Mukhtar din da kallo daya kawai ta mishi ta ji baiyi mata ba.

Bata son Hafsah tana harka da irinsu. Mutane ne masu wani irin tunani kuma ba ta so a gwarayawa Hafsah tunaninta. ba ta kaunar kusanci da irin su Mukhtar shi ya sa ma tun farko ba ta ji dadin yadda zai dinga zuwa ba. Yanzu kuma abun ya kai har da abinci ma aka kawo. Allah kadai ya san me ya zuba a ciki don ya cuci yarta.

Har wani duhu take gani yana gilmawa ta idonta. Ba tare da ta ce komai ba ta nufi part din baban Hafsahn ta shiga. Ta san baya nan amma a nan za ta zauna jiransa don wannan abun ya fi karfinta.

Kujera ta zauna tana rufe idonta. A hankali take kokarin ayyano fuskar Mukhtar amma ta kasa don ba ta wani tsaya ta mishi kallon da za ta gane shi ba. Yanzu kuwa ya zama dole ta saka ido sosai akan sa. Har ma akan Alhaji Muhammad don talakawan nan ba kirki gare su ba yanzu tana zaune sainsu asirce mata miji da ya.

Bari dai ya dawo.

***

Zaune Hajara take suna hira da Inna tana ba ta labarin yadda za ayi bikin kawarta Nafi ba tare da sun kammala karatunsu ba. Nafi kawarta ce sosai da suka shaku har suke lissafin irin burirrikan da suke so su cimma a rayuwarsu bayan sun kammala sakandire. Kwatsam wani Alhaji Gambo ya zo ya ce yana sonta. Ganin mutuncin sa ya sa ta kasa yi masa wulakanci ta ce yaje ya gaida babanta wanda take tunanin kora da hali ne ta yi masa.

Sai dai yana zuwa gidan nasu zance ya chanza musamman ma da ya sakar musu da bakin aljihu kamar bai son ciwon kudin ba. Daga yadda Nafi take ba ta labari, da gaske sonta yake tsakani da Allah amma ita Nafin ba ta son shi. Sam ba kalar wanda take tsara rayuwarta bane. Tun Hajara tana nuna mata ta botsare har ta hakura dai take lallashin ta saboda taga alamar aure dai sai anyi shi.

Inna ta gutsuri goron da take ci jefi jefi ta ce, “toh Allah ya ba su zaman lafiya. Su ma iyayen nata hankalinsu ya fi kwanciya.”

Hajara ta yi shiru tana sake jin haushin Alhaji Gambo sannan ta ce, “ni kam inna sai nake ganin an cuceta wallahi. Nafi fa ita take yin na daya a ajin mu kuma gashi wanda za ta aura yana da mata kuma ya ce ba zatayi karatu ba.”

“Aure ai wata ni’imace musamman in mace ta yi dace da miji me tausayi da sanin kimarta. In dai zai dauke ta da daraja sam karatun ma mantawa zatayi dashi.”

Hajara ta tabe baki. “Tab di jam. Ta dai gamu da wahala.” Inna ta kalle ta cike da mamakin tunanin Hajarar.

“Toh ni Inna wallahi gara min karatun. Gara mutum ya waye ya samu ilimi ya kuma tallafawa kansa kafin auri. Jibi fa Yaya yadda take. Ni ban ga wani amfanin auren wuri ba.”

Inna ta rasa abun cewa sai kawao ta kara volume din rediyonta ta juya gefe alamun ta gama wannan maganar.

Hajara dai taso Inna ta tanka mata amma ta yi shiru. So take ta sako maganar Garba amma ta rasa taya ya.

Sai da ta gaji ta tashi sannan Innar ta bita da kallo.

Zuciyarta ta sosa game da halin da yayar tasu take ciki. ba ta mantawa, ra’ayin Rashida baibai yake da ra’ayin Hajara. Sam taki yarda ta kammala karatu ta nace ita sai aure. A lokacin Nuran zaman jiran shago yakeyi sannan ya kan dan saida abubuwa idan yanayin su yazo. Duk yadda aka so a fahimtar da ita ba shinda sana’a mai karfi da zai rike ta taki fahimta. Haka suka hakura aka mata auren saboda kwanciyar hankalinsu da nata.

Duk da wannan, ba ta son ra’ayin Hajarq da dogoj burinta. Tana so a ce yaranta dai sun danyi karatun su sannan suna da sana’ar hannu kafin suyi aure in yaso in suna da rabo sayi karatun mai zurfi a dakinsu.

Take taken Hajara ya ba ta tsoro. A hankali ta furta addua ga dukkan yayan nata sannan ta ci gaba da jin rediyon tana ayyanawa a ranta ya kamata a ce Mukhtar ya iso gida.

Rubutawa

Aeshakhabir

Fadimafayau

Soyayya
Credit: LuckyTD

Post a Comment

0 Comments