Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Yin Sallar Farillah A Bayan Wanda Yake Yin Sallar Nafila?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Jirginmu zai tashi da ƙarfe 6: 30pm na yamma ne, ko zan iya yin sallar Maghrib da Ishai? Yaya zan yi sallar Ishain: A qasaru ko sallar zaman gari? Ko zan iya yin sallar Farilla a bayan wanda yake yin sallar nafila?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

1. Ana yin kowace sallah ce kawai idan lokacinta ya yi. Don haka, sallar Maghriba ba zakuyita ba sai a bayan rana ta faɗa, ko dai a gida kafin ku fito zuwa tasha ko kuma a tasha kafin tashin jirgin. Sallar Isha’i ita ma sai idan lokacin ta ya yi, a lokacin da shafaƙi (ruɗa-kuyangi) a yamma ya ɓace.

2. Ana yin sallar qasaru ce kawai idan an fara tafiya. Don haka idan a cikin gari tashar jirgin ta ke, to ba za a ce kun fara tafiyar ba a lokacin. Idan kuwa ba a cikin gari ta ke ba, to za ku iya yin sallar Maghriba da Isha’a a farko lokacin Maghriba a tashar, idan kun samu hali yi kafin tashin jirginku. Idan kuwa ba ku samu hali ba, sai ku bari har sai kun sauka daga baya, sai ku haɗa sallolin biyu a lokacin sallar Isha’in.

3. Yin sallah a cikin jam’i ga maza wajibi ne a maganar da ta fi inganci a wurin malamai. Don haka ya halatta kowane mai sallah ya yi koyi da kowane limami a cikin kowace irin sallah, a fahimtar waɗansu malaman. Suka ce: Musulmi zai iya yin sallar Azahar a bayan limamin da yake yin sallar La’asar haka kuma akasi, saboda mashahuriyar maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:

وَإِنَّمَا لِكُلِّ امْرِئٍ مَا نَوَى

Kuma kowane mutum yana da irin niyyarsa ne.

Kamar yadda kuma suka ce: Yana iya yin sallar Maghriba a bayan limamin da yake yin Ishaa’i, ya yi sallama daga raka’a ta uku, kuma ya miƙe ya samu rakaarsa ta farko a bayan limamin.

Wannan shi ne fahimtar malamai irin su Ibn Hazm Az-Zaahiriy (Rahimahul Laah)

Haka kuma mai farilla ya yi sallah a bayan mai nafila ma ya halatta, saboda dalilai sahihai kamar waɗannan:

1. Limancin sallar Isha’i da Sahabi Mu’azu Bn Jabal (Radiyal Laahu Anhu) ya riƙa yi wa mutanen unguwarsu a bayan ya yi sallar a bayan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin masallacinsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 700; Sahih Muslim: 465)

Watau shi yana yin nafila, su kuma suna yin farilla. Kuma in da ba daidai ya yi ba da kuwa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hana shi, irin yadda ya hana shi tsawaita musu karatun sallar.

2. Sannan kuma ga limancin sallar tsoro da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi, inda ya yi raka’a biyu tare da jama’ar farko, kuma ya sake yin raka’o’i biyu da jama’a ta biyu. (Sahih An-Nasaa’iy: 836)

Abu ne sananne kuwa cewa ba a yin sallar farilla guda ɗaya a rana ɗaya sau biyu. Don haka na ƙarshen suna matsayin nafila a wurinsa, su kuma suna yin farilla.

Allaah ya ganar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy,

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments