𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam tambaya ce a kan wanda bai yi Azumin Ramadan
ba saboda larurar rashin lafiya, har kuma ya rasu. Yaya za a yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Malamai sun saɓa a kan wannan mas’alar:
1. Waɗansu
sun ɗauki
cewa babu komai a kan magadansa.
2. Waɗansu
kuma sun zaɓi cewa
sai magadansa su rama masa, ko da kuwa Azumi Ramadan ne, ko kuma Azumin Bakance
ne, ba bambanci.
3. Waɗansu
malaman kuwa rarabewa suka yi, suka ce: Idan Azumin na Bakance ne, shi ne
magadansa za su rama masa. Amma idan Azumin na Ramadan ne, to sai dai su biya
masa da ciyar da abinci ga talakawa. Watau sai a lissafe adadin kwanakin da bai
yi azumin a cikinsu ba a ciyar da abinci ga daidai wannan adadin na talakawa.
Wannan maganar ta ƙarshe kuwa ita ta fi
bayyana a gare mu. Domin da haka ne manyan Sahabbai guda biyu: A’ishah da Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhum)
suka bayar da fatawa, kamar yadda Ibn Hazm ya riwaito daga gare su da isnadi
ingantacce a cikin littafinsa Al-Muhallaa .
Kuma wannan shi ne abin da suka fahimta daga
maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce:
مَنَ مَاتَ وَعَلَيْهِ صَوْمٌ صَامَ عَنْهُ وَلِيُّهُ
Wanda ya rasu alhali ana bin sa Azumi, sai
waliyinsa ya yi masa Azumin.
Al-Bukhaariy (1952) da Muslim (1148) suka
riwaito shi .
Musamman ma dayake su suka riwaito shi. Mai riwaya
kuwa shi ya fi kowa sanin ma’anar abin da ya riwaito, kamar yadda Malamai suka
faɗi.
Abin lura: Wannan maganar tana kan mara lafiyar da
ya warke ko ya samu sauƙi ne, har ya samu damar ramawa amma bai raman ba!
Amma shi wanda rashin lafiyarsa ya doge masa har
zuwa rasuwarsa, a kan wannan Malamai sun ce: Babu komai na laifi a kansa: Ba za
a rama masa komai ba, kuma ba za a ciyar masa da komai ba, kamar yadda shi ma
ba za a kama shi da laifin komai ba saboda hakan. (Tamaamul Minnah: 2/174).
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.