Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsatsube-Tsatsube Da Sihirce-Sihircen Wanzamai Jiya Da Yau

Published in Danmarna: International Journal of Islamic Culture and Heritage, Vol.1 No.1, July 2009, Faculty of Humanities, Umaru Musa Yar’adua University, Katsina, page 173 – 186.

Tsatsube-Tsatsube Da Sihirce-Sihircen Wanzamai Jiya Da Yau

English Rendition as “Sorcery as Performed by the Practitioners of Hausa Barbers Tradition Past and Present” 

BASHIR ALIYU SALLAU
Department of Nigerian Languages
Umaru Musa Yar’adua Uniɓersity
Katsina – Nigeria

TSAKURE

Babu shakka, idan muka kalli waɗannan ayyuka na wanzamai za su saka mu cikin tunani da mamaki domin an wuce hankalin tuwo an gagari kimiyyar boka a mayar wa mutum da kaciyarsa ta koma da loɓarta, wato kamar ba a taɓa yi masa kaciya ba, ko kuma kaciyar ta koma kamar a wannan rana aka yi har ma a ga jini yana zuba. A sakar wa mutum belun-wuya yadda cin abinci ko shan ruwa zai gagare shi. Ana kuma ɓata aikin wanzami yadda idan ya yi kaciya ta ƙi warkewa, ko kuwa idan ya yi aski sai ƙuraje su fito a kan wanda ya yi wa askin, ko kuma idan ya zo yin aski, sai hannunsa ya riƙa kyarma ya kasa yin aski, ko a mayar da shi kuturu, ko kuma ya makance. Ko kuma a yi wa mace magani ƙofar farjinta ta toshe yadda ba za ta iya saduwa da namiji ba, ko kuwa ta yi ta zubar da jinni ba ƙaƙƙautawa. A kira zabira tana wani wuri ta tarar da wanda ya kira ta a duk inda yake, ko kuma a kafa wa wata halitta marar rai kuma marar jinni ƙaho ya kame a jikinta, a kafa wa bango ko turmi ko tulu ƙaho ya kame a tsaga jini ya fita daga gare su kamar daga jikin ɗan Adam. A ɗauko askar aski a sanya ta cikin baki a yi ta burkawa, amma duk da kaifinta ba za ta yanka ba, ƙarshe dai, sai ta dakushe ko ma ta lalace, da dai sauran abubuwa masu ban mamaki waɗanda wanzamaai suke yi ta amfani da tsatsube-tsatsube da sihirce-sihircen da suke yi da taimakon iskoki da tsafe-tsafe.

 

1.0     Gabatarwa

Kafin shigowar wani saukaken addini daga Allah (mai girma da ɗaukaka), kowace al’umma a wannan duniya tana da hanyoyin da take bi domin neman biyan buƙatu da nuna bajinta da buwaya da ɗaukaka a kan idon sauran al’ummomi da suke kusa ko nesa da ita. Wannan hanya ita ce ake kira addinin gargajiya ko addinin da aka gada iyaye da kakanni na bautar iskoki ko gumaka ko tsafe-tsafe ko bautar yanayi ko wasu halittu ko magabata da sauransu. Wannan al’amari ya shafi yadda Hausawa suka riƙa gudanar da rayuwarsu kafin shigowar addinin Musulunci a wannan ƙasa, kai a ma iya cewa har bayan shigowarsa.Al’ummar Hausawa sun riƙa gudanar da addininsu na gargajiya ta hanyar bautar iskoki ko mutanen ɓoye da yin tsafe-tsafe da bori domin neman biyan buƙatun rayuwarsu na yau da kullum. Wannan dalili ne ya sa a wancan zamani da ya gabata, kowace al’umma tana da irin hanyar bautar da take gudanarwa domin kare kanta da ‘ya’yanta daga kowace irin barazana. Haka kuma, kowane rukuni na masu yin sana’o’in gargajiya sun naƙalci wasu nau’o’in tsatsube-tsatsube da sihirce-sihirce da suka shahara a kansu domin kare mutuncinsu da mutuncin sana’arsu a idanun sauran mutane. A kaƙiƙa, matuƙar ana maganar tsatsube-tsatsube da sihirce-sihirce irin waɗanda masu sana’o’in gargajiya na Hausawa suke yi, ya zama dole a kawo ire-iren waɗanda wanzamai suke yi, don kuwa suna daga cikin waɗanda suke riƙe da tutar fako a wannan harka.

Riƙo da al’adar tsatsube-tsatsube da al’ummar Hausawa suka yi kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa wani al’amari ne da ya zame masu dole, don kuwa a wancan zamani, babu wata hukuma ko shari’a wadda take yin hukunci idan aka aikata wani laifi. Ta hanyar yarda da abubuwan bautar su ne kawai suke iya yin hukunci a kan wani abu wanda al’ada ba ta yarda shi ba, kuma ta wannan hanya ce mai ƙarfi yake taushe na ƙasa da shi. Wannan dalili ne ya haifar da abubuwan bautawa iri daban-daban don su kare al’umma daga abokan hamayya da gaba da nuna ɗaukaka da buwaya.

 

1.1 Shigowar Addinin Musulunci Ƙasar Hausa

Ana cikin irin wannan rayuwa ce, Allah (mai girma da ɗaukaka) Ya aiko da addinin Musulunci ta hannun Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare) wanda ya yi horo da a bauta wa Allah shi kaɗai kuma kar a haɗa shi da wani wurin bauta, a kuma yarda da cewa, Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) Annabinsa ne kuma Manzonsa. Sannan a tsayar da sallah, a ba da zakka a yi azumin watan Ramalana, a kuma yi aikin Hajji ga wanda Allah ya ba iko. Dukkan wanda ya yi biyayya ga waɗannan dokoki ko shika-shikan addinin Musulunci, a ranar gobe lahira sakamakonsa shi ne Aljanna, amma idan ya yi tawaye, wato ya ƙi bin su wuta ce sakamakonsa.Wannan horon shi ya karya alkadarin addinin gargajiya.

Shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa ya kawo muhimman sauye-sauye dangane da yadda Hausawa suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.Wannan kuwa ya faru ne saboda koyarwar addinin ta saɓa da yadda Hausawa suke gudanar da rayuwarsu kafin shigowarsa, misali, bautar iskoki da tsafe-tsafe. Karɓar addinin Musulunci wurin Hausawa ya sa wasu sun yi watsi da hanyar bautar addinin gargajiya da suka gada, suka koma bautar Allah shi kaɗai ba tare da haɗa shi da wani abin bauta ba, kuma idan suna neman biyan wata buƙata, gare shi suke nema ta hanyar roƙonsa kamar yadda shari’ar addinin Musulunci ta tsara. Wannan kuwa ya faru ne saboda kwaɗaitar da su da addinin da wata rayuwa mai kyau da jin daɗi bayan ta duniya ga dukkan wanda ya bi dokokin shari’a ya yi aiki mai kyau sakamakonsa Aljanna, amma wanda ya ƙi bin su, sakamakonsa wuta. Domin a sami biyan buƙata a duniya da lahira ya sa wasu al’ummar Hausawa barin bautar addinin gargajiya suka koma bautar Allah shi kaɗai.

 

 

1.2 Sana’ar Wanzanci

A Hausance,sana’ar wanzanci tana nufin amfani da askar aski don yin aski da gyaran fuska da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da ƙoshiya don cire belun-wuya. Sana’ar wanzanci ba ta tsaya a nan ba, don kuwa ana amfani da ƙahon bajimin sa da askar tsaga don yin ƙaho.Ana kuma cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta kwalliya da ta magani. A sana’ar wanzanci dai ana yin hujen kunne da yanke yatsan cindo (shiddaniya) da yanke linzami cikin bakin jarirai da wasu ayyuka da dama. Haka kuma masu yin sana’ar wanzanci suna ba da magungunan gargajiya ga waɗanda suke buƙata (Suleiman,1990:26).Bayan waɗannan ayyuka, wanzamai suna yin tsatsube-tsatsube da sihirce-sihirce don kare mutuncinsu da mutuncin sana’arsu.

Bisa ga al’ada wanzaman gargajiya suna aiwatar da ayyukansu a kan wata shimfiɗaɗɗar ƙa’ida, wato kowane wanzami yana da gidajen da yake zuwa don yin ayyukan wanzanci.Wani wanzami ba ya zuwa gidan da wani yake yin aiki ya yi, sai kuwa idan wadda ta haihu ta zo ne daga gidan da yake yin aiki, misali matan Fulani da Hausawa suka auro sukan koma gida su yi haihuwar farko, a lokacin da suka haihu, wanzamin da yake yin aiki a gidan da wannan mata take aure ne zai yi ayyukan wanzancin, ba wanzamin da yake aiki a nan gidan mahaifanta ba. Idan wani wanzami ya shiga gidan da ba nasa ba, yakan haifar da hamayya a tsakaninsa da wanzamin wannan gida. Irin wannan hamayyar ce take sanyawa waɗannan wanzamai su yi ta harbin juna da tsatsube-tsatsube don ƙoƙarin ɓata ayyukan junansu.

2.0 Ma’anar Tsatsube-Tsatsube

Tsatsube-tsatsube ko sihiri al'amari ne wanda masana da manazarta al'adu suke kallo ta fuskoki daban-daban. Wasu na kallonsa a matsayin wata hikima da Ɗan'adam yake yi ba tare da amfani da wani magani ba don yin wani abu mai ɗaukar hankali yakan saka mutum cikin kogin tunanin yadda aka yi wannan abu. Wasu kuma suna ganin tsatsube-tsatsube a matsayin amfani da wani magani don yin wani abu na gwada bajinta da ƙwazo da buwaya wadda za ta sanya wanda aka yi wa ko wanda yake kallo zai shiga cikin kogin tunani da mamakin yadda aka yi wannan abu. A saboda haka, a iya cewa, tsatsube-tsatsube na nufin dabara da azanci da ‘yan jarrabe-jarrabe don ɓatar da hankalin mai kallo ko don cuta wa wani ko kuwa don nuna buwaya da ɗaukaka a idon abokan hamayya ko gaba (Bunza, 1990:101-104).

Bayan shigowar addinin Musulunci Hausawa sun ƙirƙiro wani fannin a tsatsube-tsatsube wanda a wannan zamani aka fi sani da sunan sihiri. Wannan fanni na tsatsube-tsatsube malaman tsibbu ne suka fi shahara wajen yin sa, don kuwa ana haɗa koyarwar addinin Musulunci ne ko addinin gargajiya na Hausawa da ayoyin Al'ƙur'ani mai girma ko wasu daga cikin hadisan Annabi (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) don yin maganin wata cuta ko don neman biyan wata bukata daga Allah Mai girma da ɗaukaka ko kuwa don a cuta wa wani.

Kowace al'umma a wannan duniya tana da ire-iren tsatsube-tsatsuben da take yi ko dai don ta kare kanta daga barazanar abokan hamayya ko don nuna bajinta da buwaya ko don cuta wa wani ko kuwa don yin nishaɗi. Dangane da haka a wannan fanni ba a bar al'ummar Hausawa a baya ba, don kuwa daga cikin Hausawa akwai waɗanda suka shahara wajen yin tsatsube-tsatsube da sihirce-sihirce ko kai don su kare kansu da mutuncinsu ko don nuna buwaya da bajinta ko don cuta wa wani ko kuwa don yin nishaɗi a lokutan bukukuwa. Cikin al'ummar Hausawa waɗanda suka fi shahara a wannan fanni sun haɗa da 'yan bori da bokaye da masu sana'o'in gargajiya waɗanda suka ƙunshi manoma da maƙera da masunta da maɗora da mahauta da wanzamai da sauransu.A wannan nazari za a duba ire-iren tsatsube-tsatsube da sihirce-sihircen wanzaman Hausawa a jiya da kuma yau.

 

2.1 Tsatsube-Tsatsuben Wanzamai a Jiya1

Kafin shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa, da ma bayan shigowarsa, hanyar da ake bi wajen samun ɗaukaka da nuna buwaya da maganin wasu cututtuka ko haddasa cututtuka ga wasu mutane da sauran abubuwan mamaki, ita ce ta bin addinin gargajiya wato yin tsafe-tsafe da tsatsube-tsatsube da hikimomi. A irin wannan hanya ana yin tsatsube-tsatsube da hikimomi don samun ɗaukaka da nuna buwaya da kuma cuta wa wasu mutane. Daga cikin waɗanda suke tafiyar da wannan hanya akwai wanzamai waɗanda a iya cewa suna cikin na gaba-gaba wajen yin ire-iren waɗannan tsatsube-tsatsube. Wannan dalili ne ya sa wasu mutane idan suna neman wani asiri na samun ɗaukaka ko na nuna buwaya ko wanda za a cuta wa wani, sai su je wurin wanzamai.

Dangane da wannan nazari tsatsube-tsatsube na nufin amfani da magungunan gargajiya ko wata hikima domin yin wani abin mamaki da ya saɓa al’ada na ban tsoro ko cutarwa ga mutum ko dabba ko wata halitta. A al’adar Hausawa kowace sana’a ta gargajiya tana da ire-iren tsatsube-tsatsuben da ma’abota yin wannan sana’a suke yi don ƙoƙarin kare mutuncinsu da na sana’arsu. Ta wannan fuska a iya cewa sana’ar wanzanci na daga cikin sana’o’in da suka shahara wajen yin ire-iren waɗannan tsatsube-tsatsube.

 Daga cikin ire-iren tsatsube-tsatsuben wanzamai akwai waɗanda ake yi a lokacin bukukuwa domin a nishaɗantar da masu kallo.Ire-iren su sun haɗa da burka askar aski cikin baki, kuma duk da kaifinta ba za ta yanki wanda yake yin wasa da ita ba. Lokacin wannan biki makaɗa da maroƙa suna daga cikin waɗanda suke ƙara tsima wanzami ya yi waɗannan tsatsube-tsatsube don kuwa za su yi ta zuga shi ya kiɗima sosai, sai ya ɗauko askar aski ya saka ta cikin bakinsa ya rufe bakin ya yi ta burka ta cikin bakinsa duk da kaifinta ba tare da ta yanke shi ba. Wanzamin zai yi ta yin haka har sai an dakatar da shi, amma duk daɗewar da ya yi yana burka wannan aska ba za ta yanke shi ba, sai dai a lokacin da zai fito da ita daga cikin bakinsa za a tarar kaifinta ya dakushe.

Domin kashe kaifin aska wanzamai suna amfani da hakin gadon maciji da ganyen ƙirya a haɗa su a daka.Lokacin da wanzami za shi wurin biki sai ya ɗebi garin wannan magani ya sa cikin baki yana taunawa yana haɗiye ruwan maganin, sannu-sannu zai kama jikinsa yadda duk kaifin aska idan ya burka ta cikin bakinsa ba za ta yanke shi ba a duk tsawon wannan rana. Wannan dalili ne ya sa Hausawa suke kiran sa "taurin-ɗaya-rana" ko “shafi”.

 Ana kuma iya kiran zabira ta tarar da wanzamin da yake amfani da ita a duk wurin da yake. Wannan irin tsatsube-tsatsube ana yin tsafi ne da yi wa iskoki yanka don a sami biyan bukata. Wanzaman da suke yin irin wannan tsatsube-tsatsube suna samun baƙin tsumma na saƙi a saka ɗan kunkuru ko ƙififiya mai rai wanda ba a daɗe da ƙyanƙyashewa ba cikin baƙin tsumma a haɗa da yanar gizo wadda ta haɗe wani icce da wani a naɗa ta wurin wannan ɗan kunkuru ko ƙififiya a sa baƙin zare a ɗunke su wato a yi laya ke nan. Wanshekaren da aka ɗunke ta tun da sassafe wannan wanzami zai sami jan zakara ya yanka mata don ta sha jini, zai yanka wannan jan zakara ne a saman wannan laya yadda jinin zai zuba a samanta. Daga nan wanzamin zai sanya wannan laya cikin zabirarsa, amma kuma duk bayan wata ɗaya, tun da sassafe sai ya sake yanka mata jan zakara ta sha jini.Wanzaman da suke yin irin wannan tsafi sun amince kuma zuciyarsu ta yi imani da a duk lokacin da suka kira zabira a duk wurin da suke za ta same su ba tare da ɓata wani lokaci ba. Wannan al’amari yana faruwa a lokacin da makaɗansu ko maroƙansu suka zuga su hankalinsu ya tashi, haka kuma yana tafiya da imaninsu kan duk abin da suka ƙudurta a cikin zuciyarsu zai tabbata yadda suke son ya kasance. 

Haka kuma, ana yi wa turmi ko bango ko tulu da makamantansu ƙaho ya kame a jikinsu, idan kuma an tsaga jini ya fito kamar a jikin mutum. Irin wannan tsafi iri biyu ne, akwai wanda ake amfani da hikimomi wajen yin sa da kuma wanda ake amfani da tsafi wajen yin sa. Kowane daga cikin su ana yin sa don a burge masu kallo a lokacin da wanzamai suke bukukuwa.

Akwai kuma tsatsube-tsatsuben da wanzamai suke yi domin su kare mutuncinsu da na sana’arsu.Wannan yana faruwa ne a lokacin da wani kuskure ya faru ko saɓani a tsakanin su da waɗanda suke yi wa ayyukan wanzanci ko kuma da abokan sana’arsu. A irin wannan tsafi wanzami zai yi duk wasu tsatsube-tsatsube da ya sani don ya kare mutuncinsa da na sana’arsa. Misali, idan aka yi wa wanzami gatse yana iya mayar da kaciya wadda aka daɗe da yi matuƙar ba ta wuce shekara sittin da yi ba ta koma da loɓarta ko ta koma sabuwa kamar a wannan rana aka yi ta. Idan kuma mace ce, yana iya sakar mata da jini ya yi ta zuba ba tsayawa. Haka kuma a lokacin da aka yi kuskure wajen yin aiki ana iya amfani da tsatsube-tsatsube don gyara aikin. Misali, idan ana yi wa mutum gyaran fuska aka manta aka aske masa gemu, ta wannan hanya ana iya mayar da gemun2. Ko kuma idan ya yi tsagar gado wadda ba irin ta ake yi a wannan gida ba, ta hanyar tsatsube-tsatsube yana iya ɓatar da wannan tsaga yadda fuskar za ta koma yadda take ba tsaga ko kuma tsagar da aka yi ta koma irin ta gadon gidan da aka yi wa kuskure don ya kare mutuncinsa da na sana’arsa3.

Wanzamai suna kuma amfani da maganin kurkurar baki domin isar da muguwar niyya.Amfani maganin kurkurar baki shi ne, dukkan wanda ya ci maganin idan ya ƙudurta wani abu na mugunta cikin zuciyarsa a kan mutum ko dabba ko wani abu marar rai, to abin zai tabbata. Irin wannan tsatsube-tsatsube ana yin su ga mutanen da kan yi wa wanzami gatse. Misali a ce wa wanzami "idan kai cikakken wanzami ne ka mayar min da kaciya ta koma sabuwa da sauransu. Idan wanzami yana da irin wannan asiri ba sai ya je wani wuri ba, nan take kaciyar za ta fara zubar da jini ta koma sabuwa kamar a wannan lokaci aka yi ta.

Wasu tsatsube-tsatsuben wanzamai na yin su ne ta hanyar jifar abokan sana’arsu waɗanda hamayya ko saɓani ya shiga tsakaninsu. A nan wanzami na iya jifar abokin hamayyarsa da wata cuta wadda za ta iya nakasa shi ko ma ta kashe shi.Ko kuma ya ɓata ayyukan wanzancin da wannan abokin hamayya nasa ya yi. Misali, idan ya yi aski, sai ƙuraje su fito a bisa kan wanda aka yi wa askin.Haka kuma idan wannan abokin hamayya ya yi kaciya, sai ta yi ta zubar da jini ko kuma ta ƙi warkewa ko kuma idan ya zo yin ayyukan wanzanci, sai hannunsa ya yi ta kyarma da dai sauran abubuwa da dama.

 

2.2 Tsatsube-Tsatsuben Wanzamai a yau4

Idan ana maganar al'amarin da ya shafi tsatsube-tsatsuben Hausawa a yau ciki har da irin waɗanda wanzamai ke yi dole a danganta su da addinin Musulunci.Wannan kuwa ya faru ne saboda irin yadda ya yi naso cikin al'adun Hausawa a yau. Dalilin haka a iya cewa addinin Musulunci ya yi naso dangane da yadda Hausawa, ciki har da wanzamai, suke tafiyar da al'amuran da suka shafi yadda ake yin wannan harka.

 

2.2.1 Matsayin Tsatsube-Tsatsube a Addinin Musulunci

Kamar yadda aka yi bayani a baya abubuwan da Hausawa suke kira tsatsube-tsatsube a al'adarsu, a fuskar addinin Musulunci su ake kira da sunan sihiri, wato yin wani abu na ban mamaki ko tsoro ko nuna bajinta da buwaya. A saboda haka kamar yadda wani masani ya bayyana, a harshen Larabci "sihiri na iya zama abubuwan al'ajabi ko bayani mai kaifin hikima da kama jiki sosai, ko wata magana da ba a taɓa jin ta ba kuma an kasa samo hujjar soke ta" (Bunza, 1990:110).

A tsari na shari'ar addinin Musulunci ana amfani da wasu kalmomi don bayyana darajojin Annabawa da waliyan Allah, waɗanann kalmomin sun haɗa da karama da mu'ujiza. Yanzu za mu bi su don ganin irin yadda masu ilimi suke amfani da su da kuma waɗanda suka shafa da kuma matsayinsu a yau.

 

i) Mu'ujiza

Wannan kalma ta mu'ujiza ana amfani da ita don bayyana wata daraja ko muhibba mai ban mamaki da ta fi ƙarfin hankali ya yi bayaninta wadda Allah ya ba Annabawansa. Irin wannan daraja da ɗaukaka su kansu manzanni da Allah ya aiko ba su san suna da ita ba, amma saboda imani da suka yi da shi, ba zai kunyatar da su ba a lokacin da suka shiga wani tsanani. Allah na bayar da waɗannan mu'ujizoji ga annabawansa domin su ƙara samun natsuwa ga aikin da ya ɗora masu, kuma mutane su ƙara yarda da ba da gaskiya ga wannan saƙo da aka aiko su da shi.

Allah ya ba da mu'ujizoji masu yawa ga annabawa waɗanda suka haɗa da Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) wanda aka saukar masa da Alƙur'ani wanda har zuwa yau babu wanda ya ci gyaransa ta fuskar nahawunsa da balagarsa da labaransa, kuma ba a sami wanda ya yi makamancinsa ba. Haka kuma, wasu daga cikin mu'ujizojin da aka ba Annabi Muhammadu sun haɗa da yin magana da damo inda ya tambayi damon "Wane ne Ubangijinka"? Ya amsa masa da cewa "Allah ɗaya", ya sake tambayar sa "Wane ne annabinka"?Ya sake amsa masa da cewa "Annabi Muhammad" (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi).Haka kuma, Annabi ya kira wata, wata ya zo ya tsage biyu da sauran mu'ujizoji masu yawan gaske (Bunza, 1990:111).

Haka kuma Allah ya bai wa Annabi Musa sanda wadda ta kasance babbar mu'ujiza gare shi a lokacin da Fir'auna ya tattara masu sihirin ƙasarsa don su ƙure shi, amma daga ƙarshe saboda mu'ujiza da Allah ya ba shi ya ƙure su suka ba da gaskiya ga Allah ɗaya. Misali, a cikin Alƙur'ani mai girma, wanda Abubakar Mahmoud Gumi ya fassara, Allah mai girma da ɗaukaka na cewa:

"Ya ce, Ka yi jifa da ita (sandarka) ya Musa.

Sai Ya jefa ta sai ga babbar macijiya, tana tafiya da gaggawa".(Sura ta 20 aya ta 19-20).

 

ii) Karama

Kamar yadda aka yi bayani a baya ita wannan kalma ta karama an fi danganta ta ga salihan mutane, kuma ta samo asali ne daga kalmar Larabci "Karrama" wato girmamawa wadda daga baya sai ta koma wata ɗaukaka da Allah yake ba wasu salihan mutane. Ire-iren salihan mutanen da Allah ya ba karama ba sa gaya wa sauran mutane irin baiwar da Allah ya ba su. Ana fahimtar suna da wannan baiwa ne idan suka roƙi Allah sai ya biya masu bukata, kuma ba sa yi don a biya su ko don a san suna da irin wannan baiwa.A cikin kowace al'umma akwai salihan bayin Allah waɗanda suke da karama kuma suna yin abubuwan al'ajabi da ban mamaki amma ba sa son a riƙa faɗa.

A shari'ar addinin Musulunci idan wani mutum wanda ba annabin Allah ne ba, kuma shi ba ya cikin salihan mutane waɗanda suke yin aiki don Allah ya riƙa amfani da wasu hikimomi, ya yi wasu abubuwa makamantan waɗanda aka keɓance su ga waɗanda Allah ya ba mu'ujiza da karama, to ya aikata laifi. Misali, a cikin Alƙur'ani (mai girma) Allah (mai girma da ɗaukaka) na cewa:

"Kuma suka bi abin da shaiɗanu ke karantarwa a kan mulkin Sulaimanu, kuma Sulaimanu bai yi kafirci ba, kuma shaiɗanun, su ne suka yi kafirci suna karantar da mutane sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan Mala'iku biyu ba a Babila; Naruta da Maruta. Kuma ba su sanar da kowa ba balle su ce: "Mu fitina kawai ne, saboda haka kada ka kafirta", balle har su yi ta neman ilimin abin da suke rarrabewa tsakanin mutum da matarsa da shi daga gare su. Kuma su (masu yin sihiri) ba su zama masu cutar da kowa da shi ba, face da izinin Allah. Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma ba ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sami tabbas, wanda ya saye su ba shi da wani rabo a cikin lahira.Kuma tir da abin da suka sayar da rayukansu da shi da sun kasance suna sani" (Gumi: 1979/1399A.H, sura ta 2 aya ta 102).

Idan muka nazarci wannan aya za mu fahimci matsayin sihirce-sihirce irin waɗanda wanzamai suke yi ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci don kuwa yin su kafirci ne ta kowace fuska. Wannan aya ta ƙara bayyana koyar da sihiri, ko neman iliminsa don yin sa ko don sha'awarsa kafirci ne.

Bugu da ƙari sahabban Annabi sun yi ƙarin bayani a kan illa da hukunci da matsayin yin tsatsube-tsatsube da sihirce-sihirce a shari'ar Musulunci. Wannan kuwa ya faru ne saboda shi addini Musulunci abu ɗaya ne wanda babu saɓani tsakanin abubuwan da ke cikin Alƙur'ani da hadisan Annabi da fahimtar sahabban Annabi da malaman sunna. A haƙiƙa sahabban Annabi da malaman sunna sun hana aikata ayyukan tsatsube-tsatsube da sihiri. Misali, a wannan hadisi da zai biyo an bayyana yadda sahabban Annabi suka yanke wa tsatsube-tsatsube da sihiri hukunci a zamaninsu kamar haka:

"Bukhari ya ruwaito daga Bijalata ɗan Abdata yana cewa: Sayyidina Umar ɗan Khaɗɗabi (Khalifa) ya rubuta musu wasiƙa cewa, ku kashe duk ɗan sihiri da 'yar sihiri. Da wannan hukuncin Umar muka kashe 'yan sihiri uku" (Abdulwahab, 1258 Hijra: 286).

Wannan hadisi kamar yadda ya zo ya bayyana, kisa ne hukuncin dukkan mai yin tsatsube-tsatsube. Domin yin biyayya ga Khalifa ya yi horo da sahabbai suka kashe masu yin tsatsube-tsatsube da sihiri.

Wani hadisin ma ya ƙara bayyana cewa, kisa shi ne hukuncin dukkan mai yin sihiri.Ga yadda wannan hadisi ya yi ƙarin bayani kamar haka:

"An ruwaito daga Bukhari a cikin Tarihi daga Usmanu Nahdiyyi ya ce: Wani mutum ya kasance a wurin Walidu yana wasa (a dandali), sai ya yanka kan mutum ya sake mai da kansa.Sai muka yi mamaki (wannan abu) sai Jundabu azdadi ya zo ya kashe shi (wannan ɗan sihirin). Domin hukuncin ɗan sihiri kisa (Abdulwahab, 1258 Hijra: 287).

A wannan zamani malaman sunna sun yi ayyuka masu tarin yawa don wayar da kan mutane kan illolin da ke tare da tsatsube-tsatsube da sihiri. Misali, a ƙasar Hausa har abada ba za a manta da ayyukan Mujaddadi Shehu Usmanu ba, don kuwa ya yi rubuce-rubuce da wa'azi waɗanda suka nuna aibi da illoli da hukuncin dukkan mai yin tsatsube-tsatsube da sihiri. A wani littafinsa mai suna "Wasiƙatul Ikhwani" shafi na 20 yana cewa:

"Ya 'yan uwana, hayyanku da aikata sihiri kamar ɗalasummai da aza'immai da rubuta haruffan da ba a san ma'anarsu (kamar hatimi) da rubuta sunan Allah ko Alƙur'ani ko sunan Annabawa don jawo (hankali) soyayya, ko don sa adawa balle a buɗe baki a saka sunan wani ko wata a ciki. Duk abin da ya kasance cikin babin sihiri domin jawo wani amfani ko don tunkuɗe cuta duk kafirci ne…."

Haka kuma a wani bayani daga Shehu Usmanu Ɗanfodiyo a wani littafinsa mai suna "Sirajul Ikhwani" shafi na 29 yana cewa:

"Duk wanda ya riya cewa zai iya rubuta abin da ke jawo arziki ko soyayya, da tunkuɗe ɓarna kamar kore ko rinjayar abokan gaba ga yaƙi, da hana ƙarfe ko takobi ya yanka shi ko ya cuce shi ('yan tauri) da makamantansu, duk suna daga cikin nau'o'in sihiri da aikace-aikacensa".

A rubuce-rubucen Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi ya raba tsatsube-tsatsube da sihirce-sihircen Hausawa zuwa gida shida kamar haka:

1.      Akwai sihirin Kawanin da Kashdadin, wannan nau'in sihiri ana yin sa tun zamanin Annabi Ibrahim.

2.      Akwai sihirin neman taimakon aljannu wanda mafi yawa da surƙulle ake haɗa shi. Irin wannan nau'i na sihiri Hausawa sun ƙware sosai wajen yin sa.

3.      Akwai sihirin rufa-ido, kana ganin abu ƙiri-ƙiri amma sai a ɗauke ruhin ganinka ga wani abu daban ba shi ba.

4.      Akwai sihirin da Hausawa suke jingina wa karamcin ƙarya ga wasu mutane salihai ko magabata ana kafa hujja da hadisan ƙarya.

5.      Akwai kuma masu cin magani a cikin abinci ko shafawa don su yi sihiri a dandali. Kamar wasa da maciji da makamantansu da suka saɓa da hankali.

6.      Akwai kuma wasu 'yan sihiri masu laɓewa da addini su ce sun san Ismul Lahil a'azam wanda duk ya san shi duk abin da ya nufa Allah zai biya masa buƙata. Kuma yana riya cewa aljannu suna taimaka masa yana zance da su (Gumi, 1982:31).

 

2.2.2 Nason Addinin Musulunci Kan Tsatsube-Tsatsuben Wanzamai

Shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa ya kawo babban sauyi wanda ya yi naso a kan rayuwar Hausawa dangane da yin ire-iren waɗannan tsatsube-tsatsube.Haka kuwa ya faru ne saboda shari’ar addinin Musulunci ta yi hani ga aikata ire-iren waɗannan tsatsube-tsatsube.Maimakon yin su sai shari’a ta bayyana yadda ya kamata a nemi biyan wata buƙata daga wurin Allah Maɗaukaki. Daga cikin irin waɗannan hanyoyi waɗanda shari’a ta kawo akwai yin addu’a da yin wuridi da zikiri da tofi da dai sauransu. Waɗannan hanyoyi sun yi naso sosai a kan rayuwar Hausawa don kuwa mafi yawancin Hausawa waɗanda suka karɓi addinin Musulunci sun ɗauki wannan koyarwa suka yi watsi da hanyar tsafe-tsafe da tsatsube-tsatsube irin na wanzamai waɗanda aka riƙa yi kafin addinin Musulunci ya yi naso cikin rayuwarsu. Dangane da haka ga bayanin yadda shari’a ta yi horo ga mabiya addinin Musulunci kan yadda ya dace su nemi biyan wata buƙata daga wurin Allah Maɗaukaki. 

 

a) Addu’a da Yadda ta yi Naso a kan Wanzanci

Addu’a na nufin yin ƙas-ƙas-da-kai cikin ladabi da miƙa wuya ga Allah, Maɗaukaki, don yin roƙo a wurinsa na neman biyan wata buƙata. Dangane da haka a iya cewa addu’a wata hanya ce da mabiya addinai, tun ma ba addinin Musulunci ba, suke amfani da ita. Ana yin addu’a domin neman biyan buƙata ko yin roƙo wurin Allah, Maɗaukaki, a kan wani abu da ake so a samu na rayuwa.Sannan kuma akan yi addu’a domin neman falalar Allah, Maɗaukaki, a lokacin da aka shiga wani hali na takura ko zalunci ko rashin lafiya ko domin neman biyan buƙatun duniya da lahira. A tsari na addinin Musulunci, addu’a ita ce hanya ta farko wadda shari’a ta ƙarfafa a dinga yin ta don magance cuta. Tun kafin zuwan Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, annabawa da yawa waɗanda suka zo kafin shi, Allah ya hore su da yin addu’a domin maganin cututtuka iri-iri da kuma samun ijaba a kan dukkan al’amuran da suka sa a gaba (Bunza, 1990: 209).

A saboda haka ne a wannan zamani da mafi yawancin Hausawa suka karɓi addinin Musulunci suke amfani da addu’a domin magance cututtuka irin su ciwon kai da harbin kunama da cizon maciji da dai sauransu.Haka kuma suna amfani da addu’a domin maganin tsari da tsoro da zalunci da talauci da haɗari da kwaɗayi da sauransu. Bayan waɗannan lalurori, ana yin addu’a domin neman tsari daga sharrin mutane mahassada da aljannu da dai sauransu. Mafi yawancin addu’a ana yin ta don tuba da neman gafarar Allah Maɗaukaki.

 

b) Wuridi da Zikiri

Wuridi da zikiri abubuwan ne guda biyu waɗanda suka yi kamanni da juna ta fuskar ma’ana da yi a aikace. Abin da wuridi yake nufi shi ne, mutum ya keɓanta a wani wuri na musamman, misali, a cikin masallaci ko gidansa don yin wata addu’a ta musamman a wani lokaci na musamman domin neman wata biyan buƙata daga Allah Maɗaukaki. A mafi yawancin lokaci an fi yin wuridi da dare musamman sulusin dare na ƙarshe.A lokacin yin wuridi ana zaɓar wasu ayoyi daga cikin Alƙur’ani mai girma, a yi ta karanta su, ana kuma maimaitawa.A lokacin da ake yin wuridi, mai yi yakan nisanci iyalinsa, kuma ba ya magana da kowa. Wannan dalili ne ya sa aka fi yin wuridi a cikin masallaci. Amma kuma duk da haka akwai waɗanda suke yin wuridi cikin ɗakunansu tare da gindaya sharuɗɗin kar wanda ya je wurinsu. Mai neman biyan buƙata daga wurin Allah Maɗaukaki, kan yi wuridi da kansa, ko kuma ya sa wasu malamai su yi masa wuridin. Bayan an gama wurudin, malamai sun bayyana cewa yana da matuƙar kyau a yi sadaka da abin da ya sauwaƙa. Wasu malaman kuma sukan sanar da wanda suke yi wa wuridin ire-iren abubuwan da suka dace a yi sadaka da su.Wannan ya danganta da irin girman buƙatar da ake son a samu falala a kanta. Misali; ana yanka sa ko rago ko kaza ko kuma a ba da waina ko ƙosai ko ƙuli- ƙuli da sauransu don a yi sadaka. A mafi yawancin lokaci, an fi son a ba yara wannan sadaka, don kuwa addu’arsu na daga cikin addu’o’in da Allah Maɗaukaki yake saurin amsa (Bunza, 1990: 22-4, Bunza, 1995: 476).

Idan muka juya ta fuskar zikiri za a ga ya ƙunshi keɓanta a wani wuri na musamman domin ganawa da Allah Maɗaukaki, domin neman biyan wata buƙata tsakanin bawa da mahaliccinsa (Bunza, 1995: 476).

A ƙasar Hausa waɗannan nau’o’in biyu na neman biyan buƙata daga Allah Maɗaukaki, an yi masu wata fahimta ta musamman.Idan muka dubi wuridi, za a ga kowane malami na yin sa, haka kuma ana iya ba kowane mutum wuridi ya yi da kansa domin neman biyan wata buƙata, sai dai kafin a ba shi, sai an shimfiɗa masa wasu sharuɗɗa da ƙa’idojin gudanar da shi. Shi kuwa zikiri a ma’anarsa ta asali yana nufin ambato. Wannan ya nuna kowane mutum na iya ambaton Allah Maɗaukaki, domin neman biyan wata buƙata daga gare shi yadda zai sami nasara.

 

c) Tofi

Tofi wata hanya ce wadda ake amfani da ita domin yin wasu magunguna da ake amfani da wasu ayoyin Alƙur’ani Mai girma, a yi addu’a da su a tofa wa marar lafiya a wurin da ciwon ko matsala take5, ko kuma a yi tofin cikin ruwa a sha ko a shafa wurin da matsala take don yin magani.Ana amfani da ayoyi da dama domin yin tofi. Wasu wanzamai suna amfani da tofi wajen yin kaciya da kuma bayan an gama yi wa mutum aski ana karanta wasu ayoyin Alƙur’ani a tofa domin neman kariya daga dukkan sharri da kuma neman albarka.

 

Kammalawa

Kamar yadda aka gani, wannan takarda ta yi bayani ne a kan tsatsube-tsatsuben da wanzamai suke yi da yadda suke yin su da kuma matsayin yin su a addinin Musulunci. A haƙiƙa, idan aka dubi bayanan takarda za a iya cewa, wanzaman Hausawa sun taka rawa sosai wajen yin tsatsube-tsatsube kafin Hausawa su karɓi addinin Musulunci. Wannan dalili ne ya sa wanzamai suka zama abin tsoro, kuma ba a yi masu gardama ko gates dangane da yadda suke tafiyar da wannan sana’a. Sakamakon karɓar addinin Musulunci wannan al’amari ya sami cikas, don kuwa wannan addini ya kawo sabuwar rayuwa wadda ta yi horon a bauta wa Allah shi kaɗai, kar a haɗa shi da wani wurin bauta, sannan kuma a yarda da dukkan abubuwan da Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ya da su domin a sami sakamako mai kyau a ranar lahira. Wannan al’amari ya taimaka matuƙa gaya wajen sauya rayuwar wasu wanzamai suka yi watsi da al’amarin tsatsube-tsatsube domin yin biyayya ga koyarwar addinin Musulunci. Sai dai daga ƙarshe muna roƙon Allah Ya gafarta mana kurakuran da muka aikata a baya.Amin!

ƘARIN BAYANI

1.      A wannan takarda an yi amfani da kalmar ‘jiya’ don a bayyana yadda wanzamai suka riƙa yin tsatsube-tsatsube kafin shigowar wasu baƙi cikinsu kamar Larabawa da Turawa da sauransu waɗanda suka kawo masu wata sabuwar rayuwa wadda ta kawo wani sauyi dangane da yadda suke aiwatar da wannan sana’a tasu Wafin zuwan waɗannan baƙi.

2.      A cikin shekara ta 1990 a garin Dutsin-ma ta Jihar Katsina wani wanzami mai suna Ali Wanzam ya yi wa wani dattijo mai suna Malam Usman na Tabkin Alƙali Dutsin-ma aski, sai ya manta ya aske har da gemu. Lokacin da wannan dattijo ya fahimci an aske masa gemu, sai rikici ya tashi, ya nuna wa wannan wanzami cewa babu yadda za a yi ya koma gidansa cikin iyalinsa da 'yan uwansa waɗanda suka san yana da gemu shekaru da daɗewa amma yau ya aske shi. Daga nan sai wannan wanzami ya yi ta ba wannan dattijo haƙuri, amma sai ya ƙi yarda, ya tafi ya yi ƙararsa wurin Alƙali Lawal na “Upper Area Court” Dutsin-ma. Da alƙali ya kira wannan wanzami ya tambaye shi wane dalili ya sa ya aske wa wannan dattijo gemu?Sai wanzami ya amsa da cewa, shi bai aske masa gemu ba, idan kuma ana gardama a duba. Da Alƙali ya dubi wannan dattijo, sai ya gan shi da gemunsa lafiya lau ba a aske shi ba, amma da aka fita kotu sai gemu ya ɓace, idan an dawo cikin kotu sai ya dawo.Haka aka yi ta yi har gemun wannan dattijo ya sake tsirowa.Daga ƙarshe saboda rashin hujjoji alƙali ya sallami wannan ƙara. Wannan wanzami ya yi wannan tsatsube-tsatsube ne don ya kare mutuncinsa da mutuncin sana'arsa yadda ba za a ci mutuncinsa ba.

3.      Irin wannan al'amari ya taɓa faruwa a gidanmu shekara arba'in da ta gabata.Wannan kuwa ya faru ne saboda mantuwa da rashin sani wanda ya yi dalilin ɗan'uwana Abdulƙadir Gawo ya je wani gida da aka haihu ya yi tsagar gado wadda ba irin ta ake yi wa zuri'ar jaririn da aka haifa ba. Bayan ya cire wa jaririn mai suna Mannir belun-wuya, sai ya yi masa tsagar gado ta Dauranci wadda ita ce tsagar gadon mutanen wannan gida mai suna Alhaji Cikada na ‘Yarƙwarya, shi kuma jaririn da aka haifa ba irin ta ake yi masu ba. Da aka gaya wa iyayen wannan yaro ga abin da ya faru, sai suka zo wurin mahaifina suka gaya masa, sai ya amsa masu da cewar, a je a duba a gani idan wannan yaro yana da tsaga, da aka je, sai aka tarar wannan tsaga ta ɓace, kuma har yau wannan wanda aka yi wa tsagar yana nan da rai amma ba tsagar. An yi waɗannan tsatsube-tsatsube ne don kare mutuncin wannan wanda ya yi kuskure da sana'ar yadda ba za a sami wani saɓani ba tsakanin iyayen wannan jariri da gidanmu.

4.      Kalmar ‘yau’ kuma, an yi amfani da ita domin nuna yadda al’adun baƙi suka kawo sauyi a kan yadda wanzamai suke aiwatar da ayyukansu musamman abubuwan da suka shafi tsatsube-tsatsube da sihirce-sihirce.

5.      Akwai wani wanzami wanda aka yi hira da shi a Gidan Radiyon Tarayya na Kaduna a ranar 5 ga watan Maris shekara ta 2005 mai suna Alhaji Yahaya Nasara, wanda yake zaune a garin Gwargwaje ta ƙaramar hukumar Igabi cikin jihar Kaduna. Ya bayyana cewa, shi idan ya yi wa yara kaciya ba ya barbaɗa wani magani don hana zubar jini da kuma saurin warkewar kaciya.A maimakon garin magani ko wani abu, addu’a yake yi ya tofa a wurin da ya yi yankan kaciyar. Daga nan sai jini ya tsaya, kuma kaciyar ta warke cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Wannan ya bayyana addinin Musulunci ya yi naso a kan yadda yake tafiyar da ayyukan wanzanci. Dalilin haka ne ɗan jaridar da yake yin hira da shi mai suna Alhaji Ladan Kwantagora ya bayyana cewa, "na so in yi maka tambaya kan ire-iren tsatsube-tsatsubenku na wanzamai, amma saboda ka bayyana cewa kome kake yi kana yin biyayya ga shari'ar addinin Musulunci, a saboda haka ba zan yi maka wannan tambaya ba". Wannan bayani ya ƙara nuna addinin Musulunci ya yi matuƙar naso a kan yadda wasu wanzamai suke tafiyar da ayyukansu na wanzanci wanda ya taimaka masu barin yin waɗannan tsatsube-tsatsube.

 

Manazarta

Abdulwahab, M. (1258 Hijra) Fatahul Majid, Sharhin Kitabul Tauhid, Ba Wurin Bugu.

Bunza, A.M. (1990) “Hayaƙi Fid da na Kogo (Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe Al'ada, Jerin Litattafan Cibiyar Nazarin Al'adun Hausawa, Lagos: TIWAL.

Ɗanfidiyo, U. (1407 Hijra) Surajul Ikwani, Bugun Sakkwato.

Ɗanfodiyo, U. (Ba Shekarar Bugu) Wasiƙatul Ikwani, Bugun Sakkwato.

Gumi, A.M. (1979/1399A.H.) Tarjamar Ma’anonin Alƙur’ani Zuwa Harshen Hausa.Beirut-Lebanon: Dar-al-Arabia.

Gumi, A.M. (1982) Al-Aƙidah al-Sahihah bi Muwafiƙah al-shari'a, Turkey.

Sallau, B.A.S (1994) “Tsafi Gaskiyar mai shi: Tasirin Addinin Gargajiya kan Sana’ar Wanzanci ta Hausawa”, Takarda da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilimi na Ɗalibai Masu Karatun Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sallau, B.A.S. (2000) ”Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sallau, B.A.S. (2009) “Sana’ar Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani Jiya da Yau”, Kundin Digiri na Uku (Ph.D). Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sheriff, B, (2000) “The Kanuri Barber And His Art”, in Borno Museum Society Newsletter, No. 42 and 43. Maiduguri: The Ƙuarterly Journal of Borno Museum Society.

Suleiman, A.H. (1990) “Tsagar Gargajiya a Ƙasar Kano: Nazarin Ire-Iren Tsaga da Muhimmancinsu ga Al’ummar Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Post a Comment

0 Comments