Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokutan Amsar Addu’a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malamai suna ta kira cewa a yawaita addu’a a cikin halin da muke ciki na rashin tsaro, to wai a waɗanne lokuta ne suka dace da yin addu’ar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Ubangijinmu Tabaaraka Wa Ta’aala ya ce:

وَقَالَ رَبُّكُمُ ٱدۡعُونِیۤ أَسۡتَجِبۡ لَكُمۡۚ إِنَّ ٱلَّذِینَ یَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِی سَیَدۡخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِینَ

Kuma Ubangijinku ya ce: Ku yi addu’a gare ni zan amsa muku, lallai waɗannan da suke yin girman kai daga yi mini bauta, za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu. (Surah Ghaafir: 60)

Wannan  ya nuna:

1. Addu’a ita ce haƙiƙanin ibada.

2. Allaah yana son a roƙe shi, shiyasa ya yi umurni da hakan.

3. Allaah ya yi alƙawarin amsa wa masu addua gare shi, idan sun cika sharuɗɗa.

4. Masu girman kai daga yin addu’a ’yan Wutar Jahannama ne a Lahira.

5. Masu girman kai daga yin addu’a za su samu wulaƙanci da ƙasƙanci a Lahira

Daga cikin wuraren ko halayen da hadisai sahihai suka nuna ana karɓar addu’a a cikinsu akwai waɗannan:

1. A ƙarshen dare. (Sahih Al-Bukhaariy: 1145; Sahih Muslim: 758)

2. Bayan sallar farilla. (Sahih At-Tirmiziy: 3/167)

3. Tsakanin Kiran Sallah da Iqamah. (Sahih At-Tirmiziy: 212; Sahih Al-Jaami’: 3408)

4. A cikin kowane dare. (Sahih Muslim: 757)

5. Lokacin saukan ruwan sama. (As-Saheehah: 1469)

6. Ƙarshen yinin ranar Jummaa, bayan Laasar. (Sahih Al-Bukhaariy: 935; Sahih Muslim: 852; Zaadul Ma’aad: 2/388-397)

7. Bayan shan ruwan Zamzam. (As-Saheehah: 883)

8. A cikin Sujada. (Sahih Muslim: 479)

9. A bayan farkawa daga barcin da ya kwanta da tsarki a farkonsa. (As-Saheehah: 3288)

10. Amfani da addu’ar Annabi Yunus (Alaihis Salaam):

 لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ

(Sahih At-Tirmiziy: 3/168)

11.  Addu’ar musulmi ga ɗan’uwansa musulmi a ɓoye. (Sahih Muslim 2733)

12. Istirjaa’i a lokacin aukuwar wata masifa. Watau:

إنَّا للـهِ وإنَّا إلَيْهِ رَاجِعُونَ، اللَّهُمَّ أجُرْنِي فِي مُصِيْبَتي، وأخْلِفْ لِي خَيْراً مِنْهَا

(Sahih Muslim: 918).

13. A halin tafiya. (As-Saheehah: 1797)

14. A kan wanda ya zalunce shi. (As-Saheehah: 767)

15. Addu'a Mahaifi a kan ɗansa. (Sahih At-Tirmiziy: 2741)

16. Addu'ah Ɗa na-gari ga mahaifinsa. (Sahih Muslim: 1631)

Hanyoyin samun ijaaba (amsar addu’a da biyan buƙata daga Allaah) suna da yawa. Ga kaɗan daga cikinsu:

1. Tsarkin zuciya.

2. Farawa da Hamdala da Salati.

3. Sakankancewa da samun ijaaba.

4. Nacewa, da barin yin gaggawa.

5. Godiya a kan ni’imomin Allaah.

6. Amincewa da laifi tare da mayar da haƙƙoƙi, sai tuba da istighfaar.

7. Ƙanƙan da kai tare da kyakkyawar fata da fargaba.

8. Maimaita addu’a sau uku.

9. Ɗaga hannuwa sama.

10. Tawassuli da Sunaye ko Siffofin Allaah ko kuma kyawawan ayyukan da bawa ya aikata.

11. Kulawa da cin halal.

12. Nisantan zunubai da saɓo.

Domin ganin dalilai da hujjoji ingantattu a kan waɗannan abubuwa ana iya duba: Muqaddimar Sharhu Adu’aa’ Minal Kitaab Was Sunnah na As-Shaikh Sa’eed Bn Wahf Al-Qahtaaniy (Rahimahul Laah) wanda Maahir Bn Abdilhameed (Hafizahul Laah) ya rubuta.

Allaah ya ƙara mana taimako, ya ba mu daman tuba da yawaita addua gare shi, ya yi mana maganin dukkan masifu da balaoin da suke damun mu, ya kawar mana da dukkan firgici da tsoro, ya kawo mana aminci da kwanciyar hankali.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments