Tattaunawar Ilimi Game da Wadansu Sarautu da Tarihin Kasar Hausa Daga Zauren Makada Da Mawaka

    Malam Muhammad Fatihu:

    Kalmar Bunu ta samo asali ne daga  harshen Larabci, Bin wata "da". Kamar ace Aliyu bin Abi Talib.

    Malam Dosara

    Mu a Masarautar Maradun tsatson Masarautar Sarkin Musulmi a duk inda kajji Bunu dan Sarautane kuma Maijiran gado ne
    Bunu
    Durumbu
    Daudu
    Barade
    Chiroma
    S/Kudu
    Sardauna da sauransu.

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji (ÆŠanmadamin Birnin Magaji):

    Daga Tsohuwar Daular Gobir Amirul Muminina Muhammadu Bello É—an Mujaddadi Shehu Usman ÆŠanfodio tagammadahullah birahamatihi ya kawo wannan sarautar zuwa Sakkwato.
    Duka sarautun Gobirawa ne aka aro bayan faÉ—uwar Daular Gobir.

    Malam Imrana:
    Ƙwarai hakane, sarautun Bunu da Kachallah da Zannah da kaigama duk aro su akayi da Barebari aka shigo dasu ƙasar Hausa saboda ƙarewar sarautu sanadiyyar yawan ya'yan sarki masu neman ayi masu sarauta babu. Ko Gobirawa aro suka yi.

    Malam Muhammad Fatuhu:
    Bana jin sarautu masu sunan larabci da ake amfani da su a kasar Hausa suna da alaka da Borno. Wadanda na san an aro sun hada da Galadima (Galtimari) Yarima (Yari Ma) Chiroma (Chiro Ma) Kaigama, Kacalla. Amma a iya nazarin da nayi, sarautu masu alaka da larabci, irin su Matawalle (Mutawalli) Falaki (Falaqi), Waziri (Wazir), Sa'i, Bunu (Bin), Alkali (Khadi) Wali da sauran su, kamar zuwan Maghili ne ya sa Hausawa suka fara amfani da su. Da Fulani suka zo suka kawo litattafai irin su Al Mawardi Ahkam Sultaniyya sai suka kara karfafa abin.

    Malam Dosara
    Ranka dade na ji Birnin-Magaji anacema Sarautarsu Dan-ali, ina asalin wannan suna yafito sir?

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji (ÆŠanmadamin Birnin Magaji):
    "Za mu Garin can/ Tungar can ta Malam Bayero, wane Bayeron? Bayero Ɗan Ɗan Ali", haka mutanen wancan lokaci da suka rayu tsakanin Duwatcun Aya da Na Kamani da wasu garuruwan dake Maƙwabta ka dasu a cikin Dajin Rugu na Tsohuwar Daular Katsina ke cewa idan zasu mazaunin waɗan nan Fulani Alawa da suka ƙirƙiri wannan Masarauta ke cewa a daidai lokacin da suke zaune a Dutcin Aya dake Tsallaken Kogin Bunsuru dake gabashin/gabascin Garin Birnin Magaji, hedikwatar Masarautar ta yanzu. Wannan bayan rasuwar Jagoran su ne, Malam Muhammadu da aka fi sani da Malam Muhammadun Aya wanda shi ne ya taho dasu daga wajen su na asali dake Jamhuriyar Mali ta yanzu zuwa wannan wuri a cikin ƙarni na 18.

    Bayan rasuwar shi a wannan wuri (Dutcin Aya) Aminin shi, Mai Martaba Sarkin Gobir Malam Ummaru Bawa Jan Gwarzo É—an Sarkin Gobir Ibrahim Babari ne ya jagoranci raba masu gado. Malam Muhammadun Aya ya bar É—iya 40 dukan su Maza da dukiyar dabbobi da ta kayan gona da yan uwan shi waÉ—an da Ƙanen shi ne. Bayan raba masu gado, ya dubi É—iyan nan 40  ya ce masu "Kukan gani nan, bari nan Dukiyar Alawa" daga wannan ne aka samu wannan karin magana da ake yi ma wannan jinsin Fulani da ake kira "Alawa", watau "Gani nan bari nan Dukiyar Alawa".

    Bayan Bayero ɗan Malam Muhammadun Aya ya zamo jagora bayan wafatin Mahaifin su anan Dutcin Aya ne aka samar da laƙabin Sarautar da har ya zuwa yanzu ake amfani da ita a wannan Masarautar ta Birnin Magaji watau "Ɗan Ali" ta sanadiyar wancan bayani da nayi tun farkon fara wannan sharhi. Daga cikin Ƙanen Malam Muhammadun Aya akwai mai suna Aliyu/Alu /Ali. Shi ne ake yi wa sabon jagoran wannan jinsin Fulani /Mazauna wannan wuri (Dutcen Aya) watau Malam Bayero ɗan Malam Muhammadun Aya laƙabi da inkiyar Ƙanen Mahaifin shi, Aliyu. Sai ana kiran shi da Bayero Ɗan Ali, sannu a hankali har laƙabin ya kasance na Sarauta ya zuwa yau. Allah ya jiƙan magabatan mu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    Malam Muhammad Fatuhu:
    Kasan Gobir ta taba zama wata babbar matattarar malamai a kasar Hausa, musamman zamanin Sarkin Gobir Bawa, kila hakan yasa sarautar ta shahara. Ina zaton koda Kano ma daga Gobir suka aro ta.
    Game da aron sarauta, ranka ya dade ban da Chiroma, domin an fara amfani da chiroma a Kano tun kusan shekaru 700 da suka wuce.

    Malam Kabiru Lalaye:
    Madallah da wannan ƙarin bayani. A Cotonou na fara jin ta, in the last century. Na yi shekara da shekaru ina neman ta. Sai a wannan century na yi kichiɓis da ita sanadiyyar social media.

    Malam I. Adamu:
    Mene ne ma'anar "Bunu" a fadar Borno da Gobirawa suka aro. Ba irin masarautar Kano ta da ba da ta yi zama ƙarƙashin daular Borno ba, Daular Gobir bata yi zama ƙarƙashin Borno ba balle has sarautun Borno su yi yawa a cikin ta. Mun san Sarautar Galadima daga Borno take amma sai a gaya muna asalin sarautar Bunu a Borno.

    Malam Mustapha Ƙofar Soro:
    Matawalle Tasamo Asali ne daga MuÉ—awwaf Mal.Wato Mai Hidima da Dukiya(Malu)
    Sai Furucin Ya Hade Mutane na cewa Matawalle.Kamar Treasurer a Englishi
    Allah shi ne masani.

    Malam Muhammad Fatuhu:
    To ni dai a Ahkam Sultaniyya ya ce Mutawalli ne asalin sunan, amma ban san da wannan etymology din ba.

    Dr. Adamu Rabi'u Bakura:
    Tsiga,(1985:17) ya bayyana cewa:" Yayin da Shehu Usmanu ÆŠanfodiyo ya isa AlÆ™awarin tare da almajiransa, ya zauna a wani fili da ke bayan gari.  A lokacin ba a san Fulani ba, sai aka rinÆ™a kiran waje Tungar Malan Janbuzu. Sakamakon wannan zaman ne aka gina masallacin Juma'a a AlÆ™alawa kuma aka ba shi limancin. Daga can ne yake zuwa ya ba da sallah, in an gama ya koma. Ana kyautata zaton har Bawa Jangwarzo ya yi karatu wajen Shehu. Idan ana zancen wurin ya zama matattarar ilimi bai kai kamar Kano da Birnin 'Yandoto ba. 
    Hasali ma idan ana zancen aro ne, sai a ce an aro muƙamin Shehu da na Waziri daga Barno ne. Don ƙarin bayani a duba Waziri (2000: 26-30). A farfajiyar ƙasar Hausa kuwa, in ana maganar matattarar ilimi babu kamar Daular Sharifai, mai cibiya a Birnin 'Yandoto, a nan ne Malan Jibrila, ya yi karatu, wanda shi ma Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya yi karatu gunsa. Hasali ma duk faɗin Afirka nan ake zuwa domin ƙwad da ƙishirwar ilimi. Bayan tarwatsewarta ne malamai da almajirar suka barbazu a wurare kamar: Katsina da Kano da Bena da Barno da Birnin Zariya. Allah ya sa mu dace. Ya arzuta mu da cikawa da imani. Amin.

    Malam Muhammad Fatuhu:
    Gaskiya ina da ja akan wasu daga kalaman Shehin Malami Ismail Tsiga, ya za a ce ba a san Fulani ba, har a kira su da Buzaye bayan a wannan lokaci Fulani sun kusa shekara 400 a kasar Hausa. 

    Zancen ace ba wasu gungun malamai sai a Yandoto wannan ma zance ne, Gobarau a Katsina matattarar malamai ce tun zamanin Maghili, Madabo da Madatai a Kano ma haka, Kurmin Dan Danranko a Katsina ma haka, Kusfa a Zariya ma haka. Ta yaya zai ce mana ba wata matattarar masana sai da aka tarwatsa Yandoto? Dukkan wadannan zan gaya maka malamai da suka shahara a cikin su, ba Nigeria ba, duniya ma ta san su, amma a Yandoto ni ban da Sambo dan Ashafa ban taba jin wani shaharare ba. 

    Sheikh Jibrin Ghaini, ni dai a iya sanina ban taba jin ya halarci Yandoto ba, ban kuma san inda aka samu wannan hujja ba. Nasan dai cikakken bagobiri ne, kuma malami ne na a zo a fada, abinda ya tabbata shi ne, ya yi karatun sa a A'ir da kasashen Agadez da Zamfara da kuma Alkalawa, amma ban san malamin sa daya ba a Yandoto

    Malam I. Adamu:
    Wannan labari na Tungar Malan Janbuzu cewa da Shehu Usmanu Danfodiyo da zaman sa a Alkalawa kuma wai saboda zaman sa a wurin aka gina masallacin juma'a na farko a Alkalawa ba tatsuniyar da ya wuce wannan. Bugu da ƙari kuma wai Malam Umaru Bawa Jangwarzo har ya yi a karatu a wajen Shehu Usmanu Danfodiyo! Kila mai rubutun bai san da cewa Ɗanfodiyo ya fara wa'azi a Gobir a lokacin Bawa Jangwarzo yana Sarkin Gobir ne ba kuma shi Shehu Usmanu a lokacin da ya fara wa'azi shekarun sa ashirin ne kawai ba. A cikin almajiran Shehu Usmanu cikin ƴaƴan Sarkin Gobir akwai Sarkin Gobir Nafata da Sarkin Gobir Yunfa waɗanda Sarkin Gobir Umaru Bawa Jangwarzo ne ya sanya su a makarantar Shehun. To, yaya aka yi uban na su wanda ko da Shehu ya fara wa'azi ya tsufa kuma Malami ne zaman kansa ya yi karatu ƙarƙashin sa? Kuma a ce wai ba a san Fulani ba a Gobir a wannan lokaci bayan Kakan Shehu Usmanu na wajen biyar, Musa Jakollo, a Birnin Ƙwanni ta Ƙasar Gobir ya zauna har aka haifi Usmanu Danfodiyo a Maratta kafin su dawo Ɗegel ƙarƙashin Muhammadu Fodiyo Baban Usmanu Danfodiyo?

    Dr. Adamu Rabi'u Bakura:
    Shi lamarin tarihi abu ne da ya shafi bincike. Ka nemi littafin wanda ya sa wa suna: "Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo". Na Isma'ila Abubakar Tsiga. Zancen 'Yandoto kuwa, wani abu da ba ka sani ba, shi ne masana tarihi sun bayyana cewa, tana ɗaya daga cikin garuruwa 170 da suka bayyana a doron ƙasa bayan ruwan Ɗufana. Hasali ma wasu sun bayyana cewa Malamin Imani Malik shi ya kafa Daular Sharifai a garin. Lamari na ilimi da bincike, musamman abin da ya danganci tarihi, wani wanda bai san shi ba, ba zai fito fili ya yi musun abin da bai sani ba. Maganar Kusfa da ka kawo, ai shi Malam Shi'itu ɗan Abdurra'uf, bayan watsewar 'Yandoto ya koma Birnin Zariya da zama. Hasali masu hikima na cewa, wanda bai san tarihi ba, bai ɗanɗani romon zaman duniya ba. Zai kasance kamar jinjiri cikin tsumma yana ganin abubuwa na faruwa, bai san tushe su ba. Ba wai na yi hasashen abin ba ne na karanta shi a littafi ne.

    Malam Muhammad Fatuhu:
    Ikon Allah! Amma zan so in san wane Malik din, Imani Malik ko Imam Malik dan Anas? Ta ina Imam Malik ya bar Madina ya zo Yandoto? Me ya hada Maliku dan Anas da Sharifai kuma, me kuma ya hada Yandoto da Maliku dan Anas? 

    Ko shakka babu, Yandoto tsohon gari ce, amma magana ta gaskiya bana jin ko shekara 1000 tayi a doron kasa, Zaye ta fi ta dadewa, Durbi ta Kusheyi ta fi ta dadewa, Samri da a yanzu ta bata ita ma ta riga Yandoto. 

    Ya kamata mu yi tattaunawa ta ilmi dan Allah cikin girmamawa, ba daidai bane ka ringa cewa bamu san tarihi ba, kai dai fadi abinda ka sani, mu kuma mu yi maka tambaya

    Malam I. Adamu:
    Dr. Adamu ba haka ya kamata ka amsa tambayoyin da na yi ba. Ko dai ban san Tarihi ba idan na yi amfani da rashin sani na nayi tambaya bayani ya kamata a yi mini ba a ƙara ruɗar da ni ba. Kana ta ƙara rikita min kai. Daga zaman Shehu Usmanu a Alkalawa har aka gina Masallacin Jumu'a na farin a shiyar Malam Janbuzu tunda ba a san Fulani ba a lokacin zuwa karatun da Malam Umaru Bawa Jangwarzo ya yi a ƙarƙashin Shehu Usmanu Danfodiyo sai kuma ga maganar cewa Ƴandoto yana cikin garuwan duniya da suka fara kafuwa bayan ruwan ɗufana. Kuma wani Maliki ne ya kafa garin! Daɗa ko wane Imam Maliki ne aka yi bayan ruwan ɗufana ko kuma yaya aka yi ya kafa garin Ƴandoto?
    A nawa ƙaramin sani ba kome da aka rubuta yake zama gaskiya ba. Akwai shirme iri iri da aka rubuta amma bai zama karɓaɓɓe ba. Karl Marx ya yi rubutu game da asalin halittu har ya ce asalin mutum daga biri ne ya canja zuwa yadda yake kuma ba Allah ne ya halicci Mutum da duniya da abin da ke cikin ta ba; haka kawai suka faru! Kila ka karanta wannan littafin amma ban yi tsammanin ka yarda da abinda Karl Marx ya rubuta ba. Rubutu kawai bai tabbatar da sahihancin abu.

    Dr. Adamu Rabi'u Bakura:
    Ai inkarin da aka yi ne, shi ya sa na faÉ—in wannan maganar. Malamin shi ne Yahaya É—an Nafsal-Zakiyya É—an Aliyu Zainul Abidina É—an Sayyidina Husaini É—an Sayyidina Aliyu Ibnu Abu Talib daga wajen  Nana Fatima, shi ya kafa ta. Sharif Yahaya ya kafa Daular ne a Æ™arni na takwas Miladiyya. Kuma yana É—aya daga cikin malaman Imam Malik. Wannan ne ya sa Mazhabar Malikiyya ta yanke cibi a Æ™asar Hausa (Ibrahim, 2009:16). Allah ya sa mu dace. Ya arzuta mu da cikawa da imani, Amin.
    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.