Taimako A Cikin Aikin Lada

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mutum ne yake ɗaukar nauyin wata makaranta tun yana raye, bayan rasuwarsa sai wani ya zo ya roƙi a ba shi daman ɗaukar wannan nauyin na wata guda kaɗai shi ma. To, wai ko hakan ya halatta?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    Allaah Madaukakin Sarki ya ce:

    وَلَا یَجۡرِمَنَّكُمۡ شَنَـَٔانُ قَوۡمٍ أَن صَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ أَن تَعۡتَدُوا۟ۘ وَتَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَ ٰ⁠نِۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِیدُ ٱلۡعِقَابِ

    Kuma ku taimaka wa juna a kan alheri da taqawa, kuma kar ku taimaka wa juna a kan zunubi da ƙetare iyaka, kuma ku ji tsoron Allaah. Lallai ne Allaah Mai Tsananin uƙuba ne. (Surah Al-Maaidah: 2).

    Wannan dalili ne a kan cewa:

    1. Taimakon juna a kan ayyukan alkhairi da ayyukan ƙarin taqawa da tsoron Allaah umurni ne na Allaah Taaala.

    2. Kuma bin umurnin Allaah wajibi ne a asalinsa, in dai ba an samu wani dalilin da da ya rage masa ƙarfi ba.

    Kuma da maganar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    « لا يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ حَتَّى يُحِبَّ لأَخِيهِ مَا يُحِبُّ لِنَفْسِهِ »

    Ɗayanku bai yi imani ba har sai ya so wa ɗan’uwansa irin abin da yake so ga kansa. (Sahih Al-Bukhaariy: 13, Sahih Muslim: 179).

    Malamai sun nuna cewa:

    1. Abin nufi da ‘ɗan’uwa’ a nan shi ne: ɗan’uwa musulmi.

    2. Imani ba ya cika sai mutum ya so wa ɗan’uwansa duk alherin da yake so ga kansa.

    Ko shakka babu! Ya shiga cikin wannan alkhairin a bayar da dama ga wani musulmi ya sanya hanun jarinsa a cikin irin wannan aikin na ɗaukar nauyin makaranta, kamar yadda ya zo a cikin wannan fatawar. Domin ko babu komai wannan ba zai hana wancan na-farkon samun cakakken ladansa ba.

    Allaahumma! Sai dai ko in an fahimci akwai wata mummunar manufa a ƙarƙashin wannan neman da ya yi, kamar ta siyasar duniya kawai ba domin neman fuskar Allaah Taaala ba.

    Allaah ya taimake mu.

    Wal Laahu A’lam.

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒��𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.