Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ribá Yana Da Iyaka Sananne A Kasuwanci?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Gafatta malam ni ne na siya kaya naira ɗari (100), sai na siyar naira ɗari biyu (200), shin na ci haram ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam. Lallai ɗan'uwa ba haramun ka ci ba, saboda babu wani dalili a littafin Allah ko a sunnar Manzon Allah ko a ijmá'in malamai da ya iyakance iya riba a kasuwanci. Sai dai fa hakan bai zama hujja na gallazawa bayin Allah farashin kayayyaki ba, saboda Allah na sa wa kasuwanci albarka matuqar an sauqaqa, kuma an yi gaskiya.

Kawai dai a tabbatar mai sayen kaya ya san qimar kayan da zai saya, bai jahilci kayan ba, saboda wani akan buga masa tsada ne ta hanyar la'akari da bai da ilimin wannan abu da zai siya, Allah ya shiryar da mu.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments