Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta yaya karatun littattafan kagaggun labarai zai inganta zamantakewar al’umma?

Ta yaya karatun littattafan ƙagaggun labarai zai inganta zamantakewar al’umma?

DAGA

BASHAR ABDULLAHI

1.0 GABATARWA

Al’adun al’umma su ne hanyarta da take gudanar da rayuwa a kai. Adabin al’umma kuma shi ke bayyana yadda al’ummar take gudanar da rayuwar. Adabi shi ne hoton rayuwar al’umma. Zamantakewa kuma abu da ya shafi al’adun al’umma. Kuma ya fi ta’allaƙa ne a kan zaman tare, kyautatawa, maƙwabtaka, da sauransu. Wannan jinga ta duba yadda karatun ƙagaggun labarai suke inganta zamantakewar alumma. Kafin wannan lokaci Hausawa suna amfani da tatsuniyoyi wajen ilimantar da yaransu. Tsofaffi ne ke shirya labarai domin saita tunanin yara daidai da al’adunsu da abin bautar su, da tsarin zamantakewarsu. Da zamani ya zo da hanyar karatu da rubutu kuma wasu masana kamar su Dr. R. M. East da suka yi ƙoƙarin sanya gasa ta ƙagaggun labarai. Wannan gasa ta samar da littattafan karatu da dama, wanda har a yanzu akwai littattafai da ake rubutawa daban-daban. Wasu a rubuta su don jarunta, wasu don faɗakarwa, wasu don nishaɗi, wasu kuma don tsare gaskiya, wasu don zamantakewa, wasu don soyayya da dai makamantan su.

1.1 ƘAGAGGUN LABARAI

 Sanin jama’a ne cewa wasu masana sun yi tsokaci a kan ƙagaggun labarai na zube daga cikinsu akwai:

 Ahmad Magaji (1982) cewa ya yi, “Zube labari ne da mutum ya shirya da ka, sannan ya rattaba a zube”

 Shi kuma Isah Mukhtar (2002), yana cewa, “Zube wani irin zance ne wanda aka faɗarsa da baka ko kuma a rubuce, wanda yake bayyana yiwuwar wani al’amari, wanda zai iya yiwuwa a zahiri, amma bai faru ba ko kuma ba zai taɓa faruwa ba. Irin waɗannan abubuwa ba dole ne a ce sun faru ba, amma duk da haka sukan sa ɗan Adam ya yi tunanin ya ƙirƙiro waɗansu halaye masu kyau ko akasin haka.

 Wani dalili da ke sa ɗan Adam ya ƙirƙiro wa kansa labarai su ne, ƙoƙarin fito da wasu abubuwa musamman waɗanda suka shige masa duhu. Misali makeken ruwa kamar kogi, ko rana da wata da taurari, ko waɗansu bishiyoyi masu ban al’ajabi da ban mamaki. Akwai waɗannan abubuwan daban-daban da suke fitowa a cikin labarai wani lokaci su ne ke zama tuballan gina labarin.

 Ire-iren rubutattun labarai na Hausa kan ginu ne ta hanyoyi daban-daban misali.

  • Ana iya samun labaran baka a tattara su a rubuta su.
  • Ana kuma samun wasu labarai na wata ƙabila a fassara su a rubuta su.
  • Ana iya yin tsokaci dangane da halin da wata al’umma ta shiga na rayuwa ta zahiri sai a rubuta shi a matsayin labari.

A ɓangaren jigoginsu kuwa ya ce, ƙagaggun rubutattun labaran Hausa, yawanci adabin Larabci da na Turanci ya yi tasiri ƙwarai gare su.

Hausawa musamman marubuta na farko sun kwaikwayi rubuce-rubucen adabin Larabawa da na Turawa suka haɗa su da nasu. Don haka jigon ƙagaggun rubutattun labaran Hausa, bisa jimla za mu iya cewa sun ƙunshi muhimman abubuwa guda uku.

·         Adabin gargajiya na Hausa

·         Adabin Larabawa da tasirin addinin musulunci

·         Adabin Turawa da na addinin Kirista

Bisa ga waɗannan bayanai za mu iya cewa, lallai ne waɗannan littattafan cike suke da tasirin zamantakewar Hausawa a cikinsu kuma waɗancan dalilai su ne suke ba ɗan Adam damar ƙirƙirar labari.

2.1 ZAMANTAKEWA A LITTAFIN SODANGI

Marubucin wannan littafi ya yi ƙoƙarin fito da zamantakewa a wannan littafi tun a farkon littafin, a kashi na ɗaya kuma fitowa da ɗaya. A shafi na sha uku (13) a kofar gidan malam Ɗanjuma, inda mai shela yake gabatarawa ga dai abin da yake cewa:

 “masu iya Magana ne cewa wanda jiya bay au ba, wanda yasan darajar goro shi, yak e adana shi a algarara, har ma ya dinga yayyafa masa ruwa. A yau dai ba abune boyayye ba irin mawuyacin halin da guguwar zaman ta jefa zumunta musamman a rsakanin makwabta, ko irin na mai hakan rijiya ya shafi rayuwar arewa rin tad a ?

Haka kuma zamantakewa a littafin ta ƙara fitowa a lokacin da su malam Adamu suka sauri a kawo abinci don su ci su je duba mara lafiya, shi ma zumunci ne ga dai abin da malam Umar ɗin yake cewa.

“A’a maza shiga ka fito mana da shi ko ma yi sauri mu je gidan malam Iro dubiya (Hafizu na shiga gida) in ce dai an taso daga makarantar boko, ga dai yadda take cewa:”kwarai! (jinkiri) kai da ka ke wannan batu malam Adamu in ban da makarantar bokon da ake yi ai mu ba mu kai shekarunsa na iyayenmu suka yi mana auren ari. (ya jawo kwanon abincin malam Adamu) Allah dai ya saka wa Malam Iro domin ilimin zamani da ya sanya ‘yayanmu”

Imam ya ci gaba da bayyana zumunta wadda ita ce ginshiƙin zamantakewa a fitowa ta uku shafi na ashirin da huɗu (24) inda Inna Shekara take ba Hafizu saƙo zuwa ga gyatumarsa ga abun da take cewa:

“Don Allah in ka je gida, ka fada mata cewa gobe zan zo ta raka ni barkar ‘yar aminiyata Hajiya Mairo da ta haihu shekaranjiya. Kar fa ka manta (ya amsa) sai da safe. Allah Ya kai mu”

Idan mu ka lura da maganar Inna Shekara, zamu ga cewa zumuncin da ke tsakaninta da Hajiya Mairo ya wuce ƙawance ya zama zumunta kuma ita kanta barka da za su je zumunci ne.

2.2 ZAMANTAKEWA A LITTAFIN ILLAR GATA NA AMINA ABDULLAHI SHARAƊA

Wannan littafi ne da aka gina shi a kan zamantakewa, ko da yake dukkan abin da yake cikin wannan littafin akwai tsura. Amma dai dukkan abin da littafain yake ɗauke da shi rayuwa ce ta aure tsakanin Ummi da Abdulhakim. Dukkansu suna ƙaunar juna kuma sun yi aure amma ba mai son a ce shi ya fara son wani. Wani hanzari ba gudu ba, duk suna kula juna kuma suna tsare haƙƙin aure gudun kar wani ya ji ba a yi masa daidai ba. Akwai kuma tsura da shagwaɓa wanda ita matar take yi sakamakon ta fito a gidan masu kuɗi. Zamantakewa a wannan littafi ta bayyana inda suka fita sayayya a babban shagon sayar da kaya misali:

“Ummi ta ci gaye ta saka leshi mai ruwan tsanwa, shi kuma hakin yana saye da kaftani fari ya saka hula mai ruwan tsanwa. Suna fita mota sai wasu mata suka fara kallonsa suna cewa “kai wannan ya haɗu, amma kuma ba su dace da wannan ba. Da zan samu wannan a matsayin miji da babu wadda ta fi ni. Kin ga fa wannan tana biye da shi zalan-zalan kamar dai baƙauya. Nan take Ummi ta juyo ta kai mata naushi domin ta ji zafin abin da ta ce”.

Hakim ya juyo ya ɓamɓare Ummi da ƙyar, ya ce me ya haɗa ku ne? “zagina ta yi wai har da cewa tana sonka.” Sikiriti da suke a wajen suka taso da yake shi Hakim dama soja ne sai ya shiga lamarin ya kashe wannan wutar. Bayan koma gida sai ya shiga yi wa Ummi faɗa cewa daga yau ba zai ƙara fita da ita ba. Ita kuma sai ta ce, Ka yi haƙuri sharrin shaiɗan ne. Ya ce to ke da ba kya so na ai ba kya hana wata ta so ni ba. Ta ce ai ban hana ta so ka ba, amma meye na zagi na?” Nan ko ba don zaginta ta yi faɗa ba sai saboda wata ta ce tana son mijinta. Ummi dai tsananin kishin mijinta take yi....

wannan ya nuna zamantakewa aure da ke tsakanin Ummi da Hakim. Wadda kuma akwai soyayya a tsakani tare da kishinsa da take yi.

SAKAMAKON BINCIKE

A wannan jinga an gano cewa, ana samun zamantakewa a cikin littattafan ƙagaggun labarai na Hausa. Kuma su marubutan sukan yi amfani da zamantakewa irin tasu a yayin isar da saƙonsu a cikin littattafana. Marubuci kan iya yin imani da abin da ya karanta daga cikin littattafan, wannan kuma kan taimaka masa wajen gyara zamantakewarsa ta yau da kullum. Manyan jigogin da suka gina zamantakewa kamar zumunci, aure, maƙwabtaka, abotaka da sauransu, idan mai karatu ya lizimci littattafan da suka yi tsokaci a kan su ya kuma yi imani da abin da ya karanta wannan na taimaka masa wajen ingata zamantakewarsa da abokan zama.

3.0 KAMMALAWA

Zamantakewa al’ada ce wadda ta ƙunshi zaman tare da zumunci da abokantaka da makamantansu. Karatun littattafai kuma yana taimakawa wajen inganta zamantakewar musamman idan mai karatu ya yi imani da abin da ya karanta daga litattafan. Akasari masu karatun sukan ɗauki halaye da ɗabiu na wani jarumi da yake a cikin littafi. Idan suka saka haƙuri kuma kamar yadda jarumin littafin ya yi, to wannan yana kai su ga nasara a cikin zamantakewa da abokan zama.

Manazarta

Ibrahim Y.Y (2002) Tarihin Rubuce-Rubuce A Cikin Hausa. NNPC Zariya.

Imam, K. (2015) Sodangi Wasan Kwaikwayo. Gidan Dabino Published Kano state Nigeria.

Malumfashi I. (2009). Adabin Abubakar Imam Garkuwa Media Services, Ltd, Sokoto.

MuKhtar I (2002), Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labari, (Tsari Na Biyu), A.J Publishes

Umar B.D (2010) “Matsayin Karin Magana A Cikin Ƙagaggun Labarin Hausa, Na

Gasar Farko (1933). Kundin Digirin Na [aya, Sashen Harsunan Nijeriya, Jama’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Umar J.T. da Wani (1933), Jiki Magayi, NNPC Zariya.

Post a Comment

0 Comments