Ticker

6/recent/ticker-posts

Wa Yake Da Haƙƙi Renon Yaro Bayan Rabuwar Aure Tsakanin Ma'aurata?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mijine yasaki matarsa tana shayarda yaron, data yayeshi sai babansa ya ce tabashi ɗansa, ita kuma tace musulunci ya ce uwa keda hakkin rike ɗanta natsawon shekara bakwai, inason karin bayani dangane da hakan.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Abun da malamai suka haɗu akansa shi ne uwa ita ce take da hakkin rainon yaro matukar baikai shekarun tamyiziba (shekara bakwai zuwa goma) saboda yaro acikin waɗannan shekaru yana da bukatar jinkai da rahma da tausayi da wani nau'i na kulawa wanda uwace zata iya yimasa uba ba zai iyaba.

Saidai wannan hakki yana faɗuwa a kan mace dazarar tayi aure, domin hidimar yaron zata shagaltar da ita daka yiwa mijinta hidima, za a samu cinkaro wajan maslahar yaron datake raino da maslahar mjinta, ibnu munzir yaruwaito ijma'i a kan faɗuwar hakkin kulada yaro ga mace idan tai aure, Duba Alkafi Na ibnu Abdul barri ( 1/296) da Mugny Na ibnu qudama (8/ 194)

Hadisin Abdullahi bin Amru Allah yakara musu yarda yana nuni dahakan, wata mata tace ya manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam  wannan ɗan nawa cikinane Abuncinsa, nono nane Abun shansa, dakina shi ne inda yake kai komo acikinsa, Babansa yasakeni kuma yazo yanaso yakwaceshi daka wajena Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce da ita, ( Kece kika can-canti kiriqe ɗanki matukar bakiyi Aureba) Ahmad yaruwaitoshi ( 6707) da Abu dauda ( 2276) Albani ya ingantashi acikin Sahihu Abu dauda, Ibnu kaseer ya ingantashi acikin Irshadul faqeeh (2/250)

Abu Nagaba shi ne ciyarda yaro wajibine a kan uba koda sun rabu da uwarsa, Mahaifiyar yaron mai wadatace ko talakace ubansa keda hakkin ciyarda shi.

Idan Uwa tana shayarda da ɗanta bayan sun rabu da babansa zata nemi yabiyata abun da take kashewa yaron.

Ciyarda yaro kuma yahaɗa wajan kwanciya da Abun kwanciyar da tufafi da magani da subulun wanka da wanki, da kuɗin makaranta, da duk Abun da datake bukata wajan kulada yaron, taimasa lissafi dakyautatawa takiyaye hakkin mijin wajan bayyana masa abun da take bukata wajan kulawa dayaronsu.

Saboda fadin Allah madaukakin Sarki:

ﻟِﻴُﻨْﻔِﻖْ ﺫُﻭﺳَﻌَﺔٍ ﻣِﻦْ ﺳَﻌَﺘِﻪِ ﻭَﻣَﻦْ ﻗُﺪِﺭَ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﺭِﺯْﻗُﻪُ ﻓَﻠْﻴُﻨْﻔِﻖْ ﻣِﻤَّﺎ ﺁﺗَﺎﻩُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻟَﺎ ﻳُﻜَﻠِّﻒُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻧَﻔْﺴًﺎ ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﺎ ﺁﺗَﺎﻫَﺎ ﺳَﻴَﺠْﻌَﻞُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑَﻌْﺪَ ﻋُﺴْﺮٍ ﻳُﺴْﺮًﺍ ‏٧۝

Mai wadata yaciyar gwar-gwadon wadatarsa, wanda aka tsuke masa arzikinsa yaciyar daka iya Abun da Allah yabashi, Allah baya dorawa rai wani abu sai wanda zata iya, Tabbas bayan kunci Allah yana kawo sauqi. (Suratul Talaq : 7)

Idan uban yaro mawadacine ciyarwa zata kasance gwar-gwadon wadatarsa, talaka ko wanda yake tsaka tsakiya gwar-gwadon halin arzikinsa zai ciyar, idan iyayen yaron sukai yarjejeniya a kan wani abu nadukiya cewa duk sati zai bata kaza naciyarwa yaron wannan al'amari yana wajansu, amma idan suna jayayya alkali shi ne zai raba wannan rigima.

Ya halatta mace tanemi mijinta daya saketa yabata ladan shayarda yaron datake kula da tarbiyyarsa a ittifaqin malamai, kamar yanda ibnu qudama ya bayyana cikin Almguny ( 11/430) da (11/431) da shaikul Islam ibnu taimiyyah acikin fatawa Kubrah ( 3/347)

Idan uba yaki ciyarda yaron ya aikata saɓo hakkinsa na rainon yaro ya faɗi akansa.

Kamar yanda yazo acikin Rauzatul dhalibeen ( 9/98) da Rauzul murbi'i ( 3/251) da Almugny (8/190) da Zadul Ma'ããd na Ibnul qayyeem ( 5/424) da fatawa Sa'adiyyah na Shaeik Assa'ady shafi na (535)

Abun nufi dai shi ne idan uba yaki ciyarda ɗansa hakkinsa nakulada yaro ya faɗi, koda yaki ciyarda ɗan ne danya cutar da uwar ne, Wannan yana nuna shi bawanda za a amincewa bane, a kan maslahar 'ya'yansa, uwar yaron zata nemi hakkin ciyarda 'ya'yanta awajansa akotu gurin alkali.

Saboda haka babu kuskure cikin zancenki kece kike da hakkin kulada da ɗanki matukar bakiyi aureba, karin bayani kuma shi ne za ki iya neman hakkin ciyarda yaron awajansa koda akotune gurin alkali.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments