Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mace Ta Shayar Da Ɗanta Nono A cikin Janaba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mlm tambayata ita ce, mlm idan miji ya sadu da matarsa kuma tana shayarwa yaronta ya tashi a bacci to mlm sai tayi wanka ta bashi nono ko zata iya bashi haka, sannan kuma wani lokacin idan tana bashi nonon mijin yana amfani da gabanta ta baya hakan babu mtsala. Allah ya sakawa mlm da alkhairi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Al-imamul A'imma Maliku Ibn Anas Yace, Bai Kamata ga Mace ta shayar da danta Nono Alhalin Akwai Janaba a Jikinta ba. Sabida Wannan yaron zai sha Wannan Nonon Nata tare da Shaiɗani. Shaiɗani yana Kusantar Mutumin da yake da Janaba a Jikinsa. Wanda kuma idan Shaiɗan ya sha Wani Abu Ko ya Ci Wani Abu tare da Mutum, Zai cutar da shi. Musamman Yaro. Shiyasa Manzon Allah ya ce idan ɗayanku zai Ci Abinci yayi Bismillah a farkon Farawarsa, idan ya manta Baiyi Bismillah a Farkon Laumarsa ba, to ko da a ta Karshe ne ya yi Bismillah. Sakamakon Rashin Yin Bismillah, yana Ci da Shaiɗani. Idan Yayi Bismillahi. Wannan Shaiɗanin zai Amayar da Abinda ya ci tare da Wannan Mutumin da Baiyi Bismillah a karon farko wajen cin Abincinsa ba. Ko dai yaron nan ya Haɗu da wata Jinya, ko kuma ya dabi'antu da Dabi'u irin Na Kangarewar Shaiɗani da Sauransu.

Sabida haka Kenan sai dai tayi Wanka Ko tayi Alwala kafin ta shayar da wannan yaron.

 Zama Da Janaba haka Kawai ba shi da Amfani. Amma dai ba Lefi bane a shari'ah Mutum ya dan Zauna da Janaba kafin ya samu yayi Wanka na ɗan Wani Lokaci. Sabida wani Lokaci Manzon Allah Ya Haɗu da Abdurrahman Ibn Sakarin Addausiy Al-yamaniy, shi ne Abihuraira a wata hanya. Sai Abu Huraira bai zo ya gaisa da Manzon Allah ba. Ashe ya tafi ne yayi Wanka wanda a wannan Lokacin Akwai Janaba a jikinsa. Sai da ya dawo sai manzon Allah ya ce ina ka shiga ya Abuhuraira? Sai Abuhuraira Yace, Akwai Janaba ne a Jikina, shi ne na kyamaci Gaisawa da kai ina Cikin halin janaba. Sai manzon Allah ya ce SUBHANALLAH AI MUMINI BA YA ZAMA NAJASA.

Duk da Cewar Manzon Allah ba ya gaisawa da Mutane, ba ya Maida Sallama kuma ba ya yiwa kowa sallah idan da janaba a jikinsa. Har sai yayi Wanka. Sannann Kuma Yana Cewa, Mala'iku ba sa Shiga Gidan da ya ke da Mai Janaba a Jikinsa.

Allah Shi ne Masani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments