𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam dan Allah idan mutum yana
da 'yar uwa Kiristan ta ba shi kayan sawa idan ya karba zai iya salla da shi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa'alaikumus salam, ya halasta mutum ya karbi
kyautar kayan sawa a wurin Kirista, kuma ya halasta mutum ya yi sallah da kayan
idan ya tabbatar da tsarkin kayan, idan kuma mutum yana kokwanto a game da
tsarkin kayan, to ya wanke su ya sa abinsa ya yi sallah da su, sallarsa ta
inganta da ikon Allah, saboda asalin al'amari game da kayan sawa shi ne
halasci, in banda abin da Shari'a ta haramta.
Kayan da bai halasta a karɓa a sa ba su ne kayan da suka keɓanta kaɗai da kafirai, wanda gaba ɗaya ba mai amfani da shi sai su, to wannan
shi ne bai halasta mutum ya karɓa ya
sa ba, ballantana har ya yi ibada da su, saboda addini ya hana mu yin
kamanceceniya da kafirai.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.