Ticker

6/recent/ticker-posts

Sadaka Saboda Mafarki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Surukarsa ce ta yi mafarkin wai wani abu mummuna zai same shi, don haka maganin hakan shi ne ta umurce shi da yin yanka da sadaka. Shi ne shi kuma yake tambayar matsayin hakan a shari’a?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Hadisi ya tabbata a cikin Sahih Al-Bukhaariy (7044) da Sahih Muslim (6040) daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa shi ya ce:

« الرُّؤْيَا الصَّالِحَةُ مِنَ اللَّهِ فَإِذَا رَأَى أَحَدُكُمْ مَا يُحِبُّ فَلاَ يُحَدِّثُ بِهَا إِلاَّ مَنْ يُحِبُّ وَإِنْ رَأَى مَا يَكْرَهُ فَلْيَتْفِلْ عَنْ يَسَارِهِ ثَلاَثًا وَلْيَتَعَوَّذْ بِاللَّهِ مِنْ شَرِّ الشَّيْطَانِ وَشَرِّهَا وَلاَ يُحَدِّثْ بِهَا أَحَدًا فَإِنَّهَا لَنْ تَضُرَّهُ ».

Kyakkyawan mafarki daga Allaah ne. Don haka idan ɗayanku ya ga wani abin da ya yi masa daɗi kar ya gaya wa kowa sai wanda ya ke so. Idan kuma ya ga wani abin da bai masa daɗi ba, to ya yi tofi a gefen hagunsa sau uku, kuma ya nemi Allaah ya tsare shi daga sharrin sheɗan kuma da sharrin abin  da ya gani, kuma kar ya bai wa kowa labari. Idan ya yi hakan ba zai cutar da shi ba.

Haka kuma ya tabbata a cikin Al-Jaami’u (2449) na Al-Imaam At-Tirmiziy cewa, Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« الرُّؤْيَا ثَلاَثٌ فَرُؤْيَا حَقٌّ وَرُؤْيَا يُحَدِّثُ بِهَا الرَّجُلُ نَفْسَهُ وَرُؤْيَا تَحْزِينٌ مِنَ الشَّيْطَانِ فَمَنْ رَأَى مَا يَكْرَهُ فَلْيَقُمْ فَلْيُصَلِّ ».

Mafarki iri uku ne: Akwai mafarki na gaskiya, kuma da mafarkin da yake labarin zuciyar mutum ne, sai kuma mafarkin da sheɗan ne yake cusa wa mutum baƙin ciki da damuwa. To, duk wanda ya ga abin da yake ƙyama sai ya tashi ya yi sallah.

Daga tattaruwan waɗannan irin riwayoyin ne malamai suka samo cewa:

Mafarki iri uku ne ta fuskar yadda ya ke a asalinsa: Mafarki daga Allaah, da labarin zuciyar mutum, da kuma sharri da makircin sheɗan.

Ta fuskar yadda yake shafar mutum mafarkin iri biyu ne: Ko dai mai kyau mai daɗi, ko kuma mummuna mara daɗi.

Ayyuka uku ake nema daga wanda ya yi kyakkyawan mafarki: Godiya ga Allaah, murna da jin daɗi da hakan, ya sanar da wanda yake ƙauna kaɗai.

Idan kuma mummunan mafarki ne ya yi, to ayyukan suna da yawa, kamar haka:

1. Addu’ar neman Allaah ya tsare shi daga sharrin sheɗan da sharrin abin da ya gani.

2. Ya yi tofi sau uku ta gefen hagu a lokacin da ya farka.

3. Kar ya gaya wa kowa labarin mafarkin.

4. Ya juya daga sashen jikin da yake kwance zuwa wani sashen.

5. Ya tashi ya yi sallar nafila.

Amma game hanyoyin kare kai daga sharrorin sheɗanu da ƙulle-ƙullen maƙiya da mahassada da sauran masharranta, matakai ne kamar haka:

1. Kyautata imani da tsoron Allaah da biyayya ga dokokinsa a ɓoye da bayyane.

2. Nisantar saɓo da dukkan nau’ukan zunubi manya da ƙanana a ɓoye da fili.

3. Yawaita zikirori da addu’o’in neman tsari da kariya daga Allaah, kamar na lokacin kwanciyan barci da na farkawa, da na yammaci da wayewar gari, kamar wannan zikirin

« لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، يُحْيِى وَيُمِيتُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ »

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Duk wanda ya maimaita shi sau goma a bayan sallamar sallar Asubah tun kafin ya warware ƙafafunsa, za a rubuta masa lada goma, a goge masa zunubai goma, a daga masa darajoji goma, kuma a cikin wannan yinin yana cikin tsaro daga dukkan wani abin ƙyama, kuma yana cikin samun kariya daga sheɗan, kuma babu wani zunubin da zai iya riskarsa a wannan yinin sai dai idan tarayya da Allaah ne. Haka ma idan a bayan Maghriba ce ya karanta. (As-Saheehah: 113-114).

WALLAHU A'ALAM.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments