Ticker

6/recent/ticker-posts

RABO DA MAZA (Ta'aziyar Shaikh Giro Argungun RH)

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

Kuka muke jama'ar gaba ɗai Duniya.

Kukan idanun munyi kai har Zuciya,

Na rashin karimi haziki a mazan jiya.


Shaikh gero fata muke ɗaɗa yi maka,

Allah ya gafarta ya sa da ka ɗaukaka,

Dukkan du'a'i karin duk dai mun biya.


Allah ka sa shi cikin wasiliyyai talikai,

Duk duniya sam bata mantawa da kai,

Ka yaɗa kairi ko ina duk tun can jiya.


Tun shakarun kafin na san shi a fuskanma,

Maganarsa kunne ta shege ta fantsama,

Wa'azinsa kullum ji nake ban gajjiya.


Malam da ya hau mimbari sai kabbara,

Har wanda ke bacci a nan ya haƙƙura.

Don za ya farko ba batun wata gajjiya.


Domin fasihi ne akwai shi da hikkima,

Maganarsa rai-rai ko kaɗan ba gardama,

Wani lokacin maganarsa ce bulaliya.


Duka rayuwarsa fagen kira haka ta-ttafi,

Ya sauke nayi ni garan ban ƙorafi,

Sai dai du'a'in kairi sam ba Tankiya.


Jama'a na hanga can gabas har yamma duk,

Hakan nan kudu da arewa na hange su duk,

Sun zo janaza ko ina duk duniya.


Tarin tulin jama'ar da sunka taho garin-

Argungun don salla hakan ya zam ƙari,

Gun dukkanin wani ɗan ta'adda jan wuya.


Wasu can na ji su sunata zance sai guda-

Yacce abokina Muzo da guda-guda,

Sunna mu kama kar ayi mana Dariya.


Taron tulin jama'ar ga yasa na nustu,

Sunnarga zan koma fa don har na mastu,

Ko na rabauta a lahira har Duniya.


Jama'a ka duba ko ina sun gangaro,

Fata na kairi sukewa malam na ƙyaro,

Sunna na koma babu Ni ba Zamiya.


Ƙarshe a baiti na ina Roƙon gwani,

Allah ka sa na zamo abin koyin wani,

Haka ban sabati kar na hau motar tsiya.


Allajjiƙan Malam kayi masa Gafara,

Har ma da malam Sani kai masa Gafara,

Baba gareni guda abin yin Tutiya.


Dukkan batu in zan yi ban mance shi ba,

Mutuwa ta Ɗaukar Tuntuni bata barshi ba,

Yau ga ya ta ɗau Geru ya bar Duniya.

Sheik Giro Argungu

Daga Alƙalamin✒️✒️

Aminu Sani Uba
Abu Isah Asshanqedy
08162293321
aminusaniuba229@gmail.com
07/Satumba/2023m

Post a Comment

0 Comments