Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina ya ce Idan Na Bayar Da Shaida A Bakin Aurena

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Maƙwabta ne guda biyu suke faɗa, sai ɗaya ta ce wa ɗayar: Ni ce ajalinki! Kuma ta daga hannu ta mare ta, sai kuwa nan take ta faɗi ta mutu! Wannan abin kuma a gaban mu takwas (8) ya auku. Mutum bakwai (7) duk sun ba da shaida, saura ni kaɗai ce ya rage a yanke hukunci. Amma mijina ya tabbatar min cewa: In har na faɗa to a bakin aurena! To, malam, menene mafita?!

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Da farko matar da ta yi haka ta aikata kisan-kai, wanda ake kira: Shubuhu Amdi , watau: Mai kama da gangar. Domin a fili ya ke cewa a asali mari ba ya kisa, tun da shi ba kamar suka da wuƙa ko bugu da sanda ko harbi da kibiya ko harsashi ba ne, wanda ake ɗaukarsu: Kisa na gangar .

Hukuncin wannan aikin, idan ya tabbata shi ne kamar yadda Allaah Ta’aala ya faɗa:

وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ أَنْ يَقْتُلَ مُؤْمِنًا إِلَّا خَطَأً ۚ وَمَنْ قَتَلَ مُؤْمِنًا خَطَأً فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُؤْمِنَةٍ وَدِيَةٌ مُسَلَّمَةٌ إِلَىٰ أَهْلِهِ إِلَّا أَنْ يَصَّدَّقُوا ۚ  ... ٢٩۝

Kuma bã ya kasancewa ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya ´yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutãnensa, face idan sun yafe ... (Surah An-Nisaai: 92)

Sannan kuma Al-Bukhaariy (5758) da Muslim (1681) sun fitar da hadisi da isnadinsa zuwa ga Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya ce:

Wasu mata biyu daga ƙabilar Huzail suka yi faɗa da junansu. Kuma sai ɗaya ta jefi ɗayar da dutse kuma ta kashe ta tare da jaririn da ke cikinta, sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yanke hukuncin diyyar jaririn shi ne: Cikakken bawa ko baiwa guda. Sannan kuma ya yanke hukuncin diyyar matar a kan dangin mai kisan.

Don haka, wajibin abin da ke kan wannan matar shi ne ta ’yanta baiwa guda ɗaya mumina. Idan kuma babu hali, to sai ta yi azumi na watanni guda biyu a jere, sai dai ko in dangin matar da aka kashe sun yafe.

Sannan kuma danginta su taimaka mata wurin biyan diyyar raƙumma guda ɗari (100) ko shanu ɗari biyu (200) ko tumaki dubu biyu (2000) ko dinare dubu ɗaya (1000) ko kuma azurfa dubu goma sha-biyu (12000). Haka Abu-Daawud (4542) da Ibn Maajah (2630) suka riwaito daga hukuncin da Umar Bn Al-Khattaab (Radiyal Laahu Anhu) ya yanke a zamaninsa, kuma Al-Albaaniy ya hassana shi a cikin Al-Irwaa’u: 2247 .

Malamai sun yarda cewa daga cikin hanyoyin da ake tabbatar da laifi kamar irin wannan na kisan-kai akwai:

1. IƘIRARI : Watau musulmi baligi mai hankali ya tabbatar da aikata laifin ga kansa a gaban alƙalin musulunci.

2. SHAIDA : Watau musulmi baligi mai hankali ya yi shaida a gaban alƙali cewa wannan mutumin ya aikata wannan laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Duk lokacin da aka samu mutum baligi mai hankali ya tabbatar da aikata laifi irin wannan ga kansa, to alƙali ba ya ma buƙatar wata shaida daga wasu shaidu a kan hukuncinsa. Yana buƙatar shaidar masu shaida ne kawai a lokacin da mai laifin ya yi musu, watau bai amince da cewa shi ne ya aikata laifin ba.

A irin wannan laifi na kisan-kai malaman sun zaɓi cewa dole sai dai shaidu sun zama maza guda biyu kawai, saboda ana buƙatar ƙarin tabbatarwa a wurin zartar da haddi. Idan kuma abin yana da alaƙa da kuɗi ko dukiya ne to a nan ne ake iya karɓar shaidar namiji ɗaya da mata biyu.

Sannan a duk lokacin da aka kira mutum don ya zo ya bayar da shaida a kan abin da ya sani, to bai halatta ya ƙi zuwa ba. Domin yanzu shaidar ta zama Fardu Ainin ce a kansa. Allaah ya ce:

... ۗ وَلَا تَكْتُمُوا الشَّهَادَةَ ۚ وَمَنْ يَكْتُمْهَا فَإِنَّهُ آثِمٌ قَلْبُهُ ۗ  ... ٣٨٢۝

Kuma kar ko ɓoye shaida; duk kuwa wanda ya ɓoye ta, to haƙiƙa! Shi zuciyarsa mai laifi ce. (Surah Al-Baqarah: 283)

A ƙarƙashin wannan bai halatta miji ya hana matarsa zuwa bayar da shaida a kan abin da zai taimaka a fitar da haƙƙin waɗanda aka kashe musu ’yar uwa ba. Kuma bai halatta ya sanya wannan abin ya zama wata matsalar rayuwa ko mutuwar aurensa shi da matarsa ba.

Amma idan shaidar ba ta zama farilla a kanta ba, kamar idan alƙali ya wadatu da shaidar sauran mutanen guda bakwai kamar yadda ya zo a cikin wannan tambayar, to babu dalilin da zai sa ita matar ta nace a kan cewa sai ta je ita ma ta bayar da tata shaidar. Ta yi haƙuri ta bi maganar mijin aurenta, kar ta aikata duk abin da zai janyo aurenta da mijinta ya shiga matsala. Domin dai shi ne Aljannarta kuma shi ne Wutarta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi sahihi.

WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments