Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Tufafin Da Maniyyi Ya Taɓa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam ya karatu ya dalibai, Malam tambaya ce idan Maniyyi ko maziyyi ya zuba atufa ko jiki najasa ne ko ba najasa bane? Allah Kara ilimi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Farko dai akwai saɓanin malamai game da hukuncin shin maniyyi najasa ne, ko ba najasa bane?.

Kuma saɓanin ya samo asali ne daga fahimtar da malamai suka yiwa wasu hadisai guda biyu waɗanda aka riwaitosu duk daga Nana A'ishah (rta).

Tace : "Na kasance ina wanke janabah (wato maniyyi) daga tufafin Manzon Allah sai ya fita zuwa sallah alhali gurbin ruwan yana jikin tufafinsa".

Da kuma hadisin da tace "Na kasance ina kankareshi (da farcena) daga tufafin Manzon Allah kuma yayi sallah acikinsa".

Duk wadannan hadisan akwaisu cikin Bukhariy da Muslim da wasu litattafan.

Maluman Mazhabin Shafi'iyyah da Hanbaliyyah da kuma Sufyanuth Thauriy da Abu Thaur sunce maniyyi ba najasa bane. Hujjarsu ita ce Nana A'ishah tace tana kankareshi daga tufafin Manzon Allah . Kuma da ace maniyyi ba tsatsarka bane, da kankarewa Kaɗai bazata isar ba.

Kuma wannan ita ce fatawar manyan Sahabban Manzon Allah irin su Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib, da Abdullahi bn Abbas, da Abdullahi bn Umar, da Sa'adu bn Abi Waqqas da ita kanta Nana A'ishah (Allah ya yarda dasu baki ɗaya).

Imam Malik da Imam Abu Hanifah (Allah ya jikansu) sun ce maniyyi najasa ne. Hujjarsu ita ce   hadisin da Nana A'ishah (ra) tace tana wankeshi daga tufafin Manzon Allah . Kuma sun ce saboda yana fita ne daga mafitar fitsari. Kuma tunda fitsari najasa ne, don haka shima najasa ne.

Amma gaskiya waccen fatawar ta farko (fatawar Shafi'iyyah da Hanbaliyyah) tafi Qarfin hajjah mai karfi tare da cewa ta  samu tushe daga sahabbai (Allah ya yarda dasu).

Amma babu saɓani cikin wajibcin yin wanka saboda fitarsa ta hanyar mafarki ko a farke ta dalilin jima'i ko motsuwar sha'awa ko shafa, ko kallo.

Shi kuwa maziyyi, dukkan maluman fiqhu sunyi ittifaki akan cewa najasa ne shi. Kuma idan ya taɓa tufafi wajibi ne sai an wankeshi.

Don karin bayani aduba littafin Ta'aseesul Ahkam na Shaikh Ahmad bn Yahya Annajmiy (juzu'i na daya shafi na 86 zuwa na 87)da kuma shafi na 62 - 63.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CQ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments