Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Baya Gamsar Dani Wajen Mu'amalar Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam. Malam dan ALLah wata matsala ce da wata kawata nakeso inyi tambaya akanta wallahi malam ita yarinya ce sai Allah yasa ta aure miji babban mutum to shi kuma baya iya biya mata bukatarta ta aure, daga ya fara jima'i shikenan har ya biya bukatarsa ita kuma kullum kamar wanda ake kara mata bukatarta. Idan har ya biya tasa bazai kara amfani da ita ba. Ta kai inhar taga wani namijin da ya burgeta sai tana kiyasta yadda zatayi rayuwar aure da shi (alhali fa ba mijinta bane). kuma har suna da yara da shi wannan mijin nata, shi yasa mukeso muji menene mafita acikin wannan abun. Dan wallahi tana cikin wata babbar matsala tana bukatar mafitar wannan abun.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Mafita ta farko acikin al'amari irin wannan ita ce jin tsoron Allah. Wajibi ne duk matar da ta tsinci kanta a irin wannan yanayin ta sanya tsoron Allah azuciyarta, ta guje ma kalle-Kallen duk abin da zai tada mata sha'awa, tun daga kallon fina finai, har karanta irin novels ɗin nan na hausa.

Sannan ta guji shiga shafukan dake nuna batsa a internet, da groups ɗin batsa a facebook ko whatsapp ko duk wata kafar sadarwa.

Sannan ki dubi mijinki amatsayin wani jagora ne na musamman wanda Allah ya haɗaki da shi domin ya jagoranci rayuwarki tanan duniya, da kuma samun dacewa arayuwar lahira.

Sannan wajibi ne ki amince wa zuciyarki cewar Allah bai halicci ɗan Adam don cin abinci da shan abin sha da kuma jima'i ba. A'a Allah ya yimu ne domin mu bauta masa mu samu dacewa da rahamarsa. 

Shi Ɗan Adam abu biyu ne. Wato jiki da ruhi. Shi jiki yana ginuwa ne ta hanyar ci da sha, da kuma biyan bukatar sha'awa. Shi kuwa ruhi yana ginuwa ne ta hanyar ibadah da yawaita zikirin Allah da kuma tsaftace zuciya.

Idan kika rinjayar da bukatun jikinki akan bukatun ruhinki, to kin hallaka. Domin babu abin da hakan zai haifar miki sai nadamar duniya da lahira. Amma idan kika rinjayar da bukatun ruhinki bisa bukatun gangar jikinki, to in Shã Allahu zaki samu dacewa da tsaftacecciyar rayuwa aduniya da lahira.

Allah ya umurci Annabinsa cewa "Kuma ka gaya wa muminai mata cewa su runtse idanuwansu, kuma su kiyaye farjojinsu, kuma kada su bayyanar da adonsu......".

Sannan Manzon Allah ya ce "Shi Kallo, wata kibiya ce mai dafi (wato poison) daga kibiyoyin Shaiɗan. Duk wanda yabar shi dan tsoron Allah, Allah zai sanya masa wani hasken imani wanda zai ji ɗanɗanonsa acikin zuciyarsa".

Ki gode wa Allah da ya baki lafiya kuma ya baki miji nagari, kici gaba da kyautata mu'amalarki da shi domin shine kaɗai rabonki daga cikin mazaje. Ki dena hangen wasu mazan domin yin hakan bazai haifar miki da alheri ba.

Awajen jima'i kuma, ki yawaita yin wasanni da mijinki kafin jima'i, sannan idan da hali ki rika haɗa mishi wasu nau'o'in kayan marmarin dazai rika sha da yamma ko bayan isha'i domin samun nishaɗi wajen kwanciyar aure. Misali kamar ki haɗa masa irin su abarba, kankana, da ayaba yaci yasha.. In shã Allahu zai sami Qaruwar Qarfi da nishaɗii.

Idan kuma yana da wata larura ta musamman kamar hawan jini ko ciwon sugar (Diabates) to sai ku kiyaye dokokin kula da chutar, kuma arika amfani da magani yadda ya dace da umurnin likitoci.

Daga karshe zaki iya neman Saki akan wannan matsalar. Saboda za a Kalli yanayinki, ma'ana bukatuwarki da namiji, dan Kar ki fada cikin Halaka (zina).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments