𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ina tambaya a
kan hukuncin mace ta sanya sarƙa a ƙafarta domin ado, ko hakan ya halatta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.
Asali babin kwalliya ƙofarsa a buɗe ta ke a matsayin halacci, ba a hana
komai daga cikin hakan sai abin da Allaah Ta’aala ya hana da Manzonsa (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:
قُلۡ مَنۡ حَرَّمَ زِینَةَ ٱللَّهِ ٱلَّتِیۤ أَخۡرَجَ لِعِبَادِهِۦ وَٱلطَّیِّبَـٰتِ مِنَ ٱلرِّزۡقِۚ
Ka ce: Wanene ya haramta kayan ado da kwalliya waɗanda Allaah ya fitar domin bayinsa, da daɗaɗa na kayan arziki? (Surah Al-A’raaf: 32)
Ba a hana komai daga cikin hakan ba sai abin da
Allaah ya hana a cikin Alqur’ani ko ta harshen Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam), ko kuma wanda ya saɓa wa wata ƙa’ida daga cikin ƙa’idojin shari’a.
A nan tun da babu wata ayar Alqur’ani ko wani
hadisi sahihi da a kai-tsaye ya hana mata amfani da wannan kayan kwalliyan, sai
a bar musulma ta cigaba da amfani da shi a matsayin halal.
Musamman kuma dayake ayar Suratun Nuur ta yi ishara
ga haka, inda Allaah ya ce:
وَلَا یَضۡرِبۡنَ بِأَرۡجُلِهِنَّ لِیُعۡلَمَ مَا یُخۡفِینَ مِن زِینَتِهِنَّۚ
Kuma kar su riƙa buga ƙafafunsu
domin a san abin da suka ɓoye na
kwalliyansu. (Surah An-Nuur: 31)
A wurin fassarar wannan ayar, Ibn Jareer
At-Tabariy ya riwaito da isnadi hasan daga Sahabi Ibn Abbaas (Radiyal Laahu
Anhumaa) ya ce:
هُوَ أَنْ تَقْرَعَ الْخِلْخَالَ بِالْآخَرِ عِنْدَ الرِّجَالِ ، وَيَكُونُ فِي رِجْلَيْهَا خَلَاخِلُ ، فَتُحَرِّكُهُنَّ عِنْدَ الرِّجَالِ ، فَنَهَى اللهُ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى عَنْ ذَلِكَ ، لِأَنَّهُ مِنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ.
Shi ne mace ta riƙa bubbuga sarƙar ƙafarta
da wata sarƙar a wurin maza, ko ya zama akwai warwaro ko sarƙoƙin a ƙafafunta
sai ta riƙa karkaɗa su a
wurin maza, shi ne Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala ya hana hakan, domin yana daga
cikin aikin sheɗan ne.
(At-Tafseerus Saheeh: 3/465).
Haka sauran malaman Tafsiri suka ambata, kamar su
At-Tabariy: 19/164 da Ibn Katheer: 6/49 da Al-Qurtubiy: 12/237, da sauransu.
Ma’ana dai abu ne sananne a cikin Larabawa tun a
Jahiliyyah cewa mata suna amfani da warwaro ko sarƙa a ƙafafunsu.
Kuma ko a cikin Musulunci ba a hana su cigaba da hakan ba, sai dai kawai aka
hana su buga ƙafafu a ƙasa domin kar su janyo hankalin mazan da
ba muharramansu ba har su san hakan.
Bayan duk wannan, malamai suna iya yin suka da
nuna ƙyamar wannan abin idan ya zama a cikinsa akwai wani abin da ya saɓa wa sanannun dokokin shari’a, kamar idan
ya zama akwai koyi da waɗanda
ba musulmi ba a cikinsa ko idan ya zama amfani da shi ya shahara a wurin waɗansu fasiƙai ko mushirikai ne. Tun
da a ƙa’idar
shari’a an
hana koyi da su. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ »
Wanda ya kamantu da waɗansu mutane to shi yana cikinsu.
(Abu-Daawud: 4033 ya fitar da shi, kuma Al-Albaaniy y ace Hasan Sahih ne a
cikin Al-Irwaa’u: 1269)
Al-Imaamul Mujaddidul Albaaniy ya ce:
فَثَبَتَ مِمَّا تَقَدَّمَ أَنَّ مُخَالَفَةَ الْكُفَّارِ وَتَرْكَ التَّشَبُّهَ بِهِمْ مِنْ مَقَاصِدِ الشَّرِيعَةِ الْإِسْلَامِيَّةِ الْعُلْيَا ، فَالْوَاجِبُ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ رِجَالاً وَنِسَاءً أَنْ يُرَاعُوا ذَلِكَ فِي شُؤُونِهِمْ كُلِّهَا ، وَبِصُورَةٍ خَاصَّةٍ فِي أَزْيَائِهِمْ وَأَلْبِسَتِهِمْ
Ya tabbata kenan daga abubuwan da suka gabata
cewa: Saɓa wa kafirai
da barin kamantuwa da su yana daga cikin manufofin wannan shari’ar ta musulunci
masu girma. Don haka abin da ya wajaba a kan dukkan musulmi maza da mata shi
ne: Su kiyaye wannan a cikin dukkan al’amuransu. A surah ta musamman kuma a
cikin shigarsu da tufafinsu. (Jilbaabul Mar’atil Muslimah, shafi: 206).
Allaah ya ƙara mana shiriya.
WALLAHU A'ALAM
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎��𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.