Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafarkin Kunama

Slm mlm barka da juma at dafatan katashi lfy mlm muna godiya Allah yasaka da alkairi mlm nayi mafarkin naga kunama amakaranta munazaune sai na ga kunama yahuce Amma yan ajin basuganiba sai yabuya tajikin wani kujera sai natashi dan in yafito inkace saiga kanina yazo karban abu awajena sai kunaman yafito dagudu sai yashige rigan kanina saina fara ihu inakunama kunama sai malamimu ya tashi ya ce aina sai kanina yafa kuka sainace yashi rigan adnan sai aka fara guduwa sai malamin yamaso kusan da shi sai yadaga rigansa saiyaga kunaman yamutu saina farka a baccin amma kafin nafaka naga yadena kukuka kamar babu abin da yasamaishi mlm nasha kashe kunama agidanmu amma bantaba ganin mai girma kamar wanda nagani amafarkinaba mlm dan Allah mai hakan yake nufi

AMSA

Waalaikumussalam. Warahmatullahi. Wabarakatuhum.

Imam Muhammad Ibn Seerin (Dalibin Imam Maleek) a cikin littafinsa "Kamus din Mafarki" ya ce:

Mafarkin kunama ta hau kan mutum na nufin luwadi, mafarkin kunama ta shiga riga ko kantin mutum na nufin musiba a rayuwar mutum, ganin kunama na nufin  magulmaci ko maqiyi a cikin dangi, ganin kunama ta fito ta inda mutum yake kashi na nufin haihuwar yayan da zasu zamo maqiyansa, kashe kunama a mafarki na nufin mutum zai gano maqiyansa kuma zai ga bayansu ta fuskar qiyayyar da suke masa, harbin kunama a mafarki na nufin harshen mutum

SHARHI:

A shawarce ku sa ido sosai akan yaron ta hanyar nesantashi da abokan banza wadanda ka iya janyoshi zuwa ga mummunar dabi'ar mutanen Annabi Lud AS

Sannan kuma duk sanda kunama ta harbi wani a lokacin kina kusa da wanda ta harba saiki tuno da addu'ar da Annabi SAW ya koyar wadda mutum zai dafa wajen da ta harbeshi ya karanta "Bismillah" sau 3 sannan ya ce "Audhu biqudratihi min sharri ma'ajidu wa'uhadhiru" sau 7 a tofa a wajen, in sha Allahu za a samu sauqi

(Hadisin yana cikin Sahih Muslim mai lambata 2202)

Sannan ki dinga koyawa qannenki da yan uwanki addu'ar har sai sun haddace kuma kice kada su dinga wasa da adhkar na safiya da maraice

Sannan kuma a lazimci addu'a domin kuwa tana sauya qaddara kamar yanda aka rawaito

An karbo daga Abu Hurairah RTA, Annabi SAW ya ce: "Babu abin da yake canza qaddara sai addu'a"

Tirmidhi 3573

Subhanakallahumma wabi hamdika, ash-hadu anla ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilay

Amsawa:

✍️Usman Danliti Mato Usmannoor_As-salafy)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments