Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mutum Mai Yin Gaba Da Ɗan'uwansa Musulmi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum warahamatulla wabarakatuh, mlm tambayata shine meye matsalolin da mutum yake fadawa a cikinsu idan ya kasance yana yawa yin gaba da muslimi Ɗan'uwansa, shin ya halatta kayi gaba da musulmi ! Koda shine da kuskure? Allah ya taimaki malam

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuh.

Allah ta'ala shine wanda ya halicci Annabi Adam kuma ya sanya masa zuri'a masu adadi mai yawan gaske, wadanda ya turo su duniya domin suyi masa bauta, kuma yayi su mabanbanta harsuna don su dika fahimtar juna, suna sadar wa juna da zumunta!

Hakika kalma wacce take tattare da gaba acikin ta wata dabi'a ce da wasu daga cikin halittun Allah ta'ala suka ɗauka suka rataya ta akansu alhali sun san illar da yake tattare da ita sai Shaiɗan ya samu rinjaye akansu suka dika ganinta a matsayin babu komai aciki idan sunyi gaba da juna, wasu kuma basusan illar da yake a tattare da ita ba sai sheɗan yaci gaba da yaudararsu yana kara zaburar dasu wajen ganin sunyi gaba da juna, Allah ta'ala ya tsare mu.🤲

Magana ta gaskiya itace yin gaba tsakanin musulmai abune da Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yayi hani da shi acikin Hadisai mabanbanta kuma ingantattu, hakika ita zuciya tana son mai kyautata mata, kuma ka'idah ta mutumin kirki itace shi yakan kasance duk abin da akayi masa yakan ajiye shi a matsayin ba komai ba saboda ya rigaya ya sani tun kafin a halicce shi, Allah ta'ala ya rigaya ya rubuta hakan zata faru da shi sai ya kasance kullum babu abin da yake tattare da shi sai aminci.

Hadisi ya tabbata daga Abu-Hurairah Yardan Allah ta'ala ta kara tabbata a gare shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya ce: "KADA KUYI FUSHI KADA KUYI HASSADA KADA KUJUYA MA 'YAN UWANKU BAYA KU KASANCE BAYIN ALLAH 'YAN UWAN JUNA"  

An samu wata riwayar daga Annabi ya ce: "KADA KUYI FUSHI KADA KUYI HASSADA KADA KU JUYA MA 'YAN UWANKU BAYA KADA KU YANKE ZUMUNTA, KU KASANCE BAYIN ALLAH 'YAN UWAN JUNA BAYA HALASTA GA MUSULMI DAYA KAURACE MA ƊAN'UWANSA FIYE DA KWANA UKU"

Wadannan hadisan gaba ɗayansu Imam Bukhari da Muslim sun fitar da shi acikin Swaheh nasu.

Yin gaba yana gadar da fushin Allah ta'ala da kuma nisantar rahamar sa, kamar yanda hadisi ya tabbata wanda imam Muslim ya fitar da shi acikin Swaheh nashi cewa, Annabi ya ce: "TSAKANIN JUMA'A ZUWA JUMA'A GAFARA NE (ana gafarta abin da mutane suka aika na zunubi) IDAN JUMA'A TAYI SAI ALLAH ya ce A GAFARTA MA BAYINSA, AMMA BANDA WANDA YAYI SHIRKA DA KUMA WANDA YAKE GABA DA ƊAN'UWANSA, ALLAH ZAICE WANNAN KU KYALESHI HAR SAI YA DAWO"

Kunga wannan hadisin yana nuna mana kyama da kuma Illar GABA a tsakanin Al'ummah kuma wallahi kusani duk Al'ummar da tadauki GABA tasanya acikin ta to bazata taɓa ci gaba ba, kuma ko meye kagani acikin ta na cigaba wallahi matukar suna GABA a tsakanin su to har wayau suna acikin DUHU, Allah ta'ala ya tsare mu.🤲

Don anyi maka laifi hakan baya baka dama cewa kayi gaba da mutum, a'a kayi kokari wajen danne zuciyar ka ta hanyar katange ta da sanya mata hakuri, kamar yanda Allah ta'ala ya ce: "LALLAI ALLAH YANA TARE DA MASU HAKURI"        

Ɗan uwa ka jajurce wajen tausasa zuciyar ka ta hanyar koyi da ma'aiki , domin samun kyakkyawan rabo.

Wanda yake gaba da ɗan'uwansa musulmi to lallai ayi masa nasiha cewa wannan ba halin mutanen kirki bane, muna rokon Allah ta'ala ya kara shiryar damu akan tafarki madaidaici, wannan itace amsar ka in shaa Allah, Allah yasa mu dace 🤲

WALLAHU A'ALAM

Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah (Abu-Nabeelah) Kuriga

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments