Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Sallah A Gaban Liman

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, wai da gaske ne ba a yin sallah a gaban liman?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Malamai sun saɓa wa juna a kan wannan. Amma maganar da ta fi daidai kamar yadda Shaikhul Islaam Ibn Taimiyah (Rahimahul Laah) ya kawo ita ce: Sallah a gaban liman tana inganta ne kaɗai idan akwai uzuri. Ma’ana: Idan masallaci ya cika maƙil da jamaa, shi kuma bai samu wurin da zai tsaya domin yin sallar Jumma’a ko jana’iza ba sai dai a gaban liman, a nan sai a ce: Yin sallarsa a gaban liman ya fi ya bar yin sallar gaba-ɗaya.

Wannan ita ce maganar waɗansu daga cikin malamai, kuma ita ce magana ɗaya daga cikin mazhabar Ahmad da waninsa daga cikin limamai. Ita ce kuma maganar da ta fi adalci kuma wacce ta fi rinjaye. (Majmuu’atul Fataawa:23/221).

*** 

HUKUNCIN YIN SALLAH A GABAN LIMAN

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam mene ne hukuncin yin sallah a gaban liman a wajEn masallaci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Asali Sallar jam'i shi ne Mamu ya kasance A bayan liman, Malamai Sun yi Saɓani akan sallar wanda yayita Agaban liman, Mafi ingancin Zancen shi ne ta Inganta idan Akwai uzuri.

Shaikul Islam Ibnu Taimiyyah Rahimahullahu ya ce: Sallah agaban liman akwai zantuka guda uku na Malamai akai..

1. Ta inganta kai Tsaye, duk da sun ce Makaruhi ne, Shi ne zance shaharre a Mazhabar Malikiyya.

2. ba ta Ingantaba, Kamar Mazhabar Hanafiyyah, da Shafi'iyyah, da Ahmad.

3. Ta inganta idan akwai Uzuri, Kamar babu sauran gurin da mutum zai yi Sallar sai gaban liman ɗin, Sai ya zama yin Sallar agaban Liman shi ne ya fi Alkhairi akan ƙin yin Sallar a lokacin.

Wannan shi ne zancen wasu malamai, shi ne Mazhabar Imamu Ahmad da waninsa, shi ne mafi Adalcin zance shi ne ya fi hujjah Mai ƙwari, domin barin shiga gaban liman Maƙurarsa shi ne wajabcin barin hakan, su kuma wajibai suna gushewa idan aka samu uzuri, ko da wajibi ne a asalin sallah, da rasa jam'i gwara rasa wajibi, Saboda haka wajabcin Abin da mutum yakasa yana faduwa a gareshi, na Tsayuwar Sallah, da karatu, da tufafi, da Tsarki, da sauransu. Fatawa Kubra (2 / 331 - 333).

Saboda haka Bai halatta yin Sallah Agaban liman ba, idan Mutum ya yi sallah agaban liman sai ya sake sallah, sai dai idan Akwai uzuri Masallaci babu sauran filin dazaka iya tsaiwa damansa ko hagu ɗinsa. Kamar Yanda Ibnu Usaimeen Ya faɗa a cikin Maj- Mu'u fatawa dinsa (13 / 44).

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa... 

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments