𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Menene
hukuncin bi ta gaban mai sallar nafila, kamar a masallacin Jumma’a? Kamar
tsawon yaya ya kamata mutum ya wuce ta gaban mai Sallar Farilla ba tare da yin
laifi ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
Haramun Ne Wucewa Ta Gaban Mai Sallah Matukar dai
Bai Saka Sitira a Gabansa ba. Wanda Wucewa Ta Gaban Mai Sallah Wani Lokaci
Yakan Haifar da Lalacewar Sallar Wanda Aka Ketarewa Sallar. Hadisi Ya Tabbata
Manzon Allah (ﷺ) Yana
Cewa:
An Kar6o Daga Abu-Juhaim (ra) Ya ce: Manzon Allah
(ﷺ) Ya ce: “Da Mai Wucewa
Ta Gaban Mai Sallah Yasan Abinda Yake Kansa (Na Zunubi), Da Ya Gwammace Ya
tsaya Har tsawon Shekaru Arba'in. Hakan Yafi Alkhairi a Gareshi a kan Ya Wuce
ta Gaban Mai Sallar”.
{Bukhari: 510}
Babu wani bambanci ko sallar farilla ce ko kuwa
nafila duk hukuncin ɗaya
ne. Saboda hadisin da Sahabbai suke gaggawan samun wurin tsayuwa a bayan ginshiƙan
masallaci domin yin nafilar maghriba a bayan kiran sallah. (Sunan Al-Baihaqiy: 2/476).
Don haka sanya sutura don hana wani wucewa ta
gaban mai sallah wajibi ne a maganar da ta fi inganci a wurin malamai, kamar su
Ahmad Bn Hambal da Shaikhul-Islaam da Al-Albaaniy (Rahmatul Laahi Alaihim).
(Mausuu’atul Fiqhiyyah: 2/280-281).
Sannan kuma bai halatta shi wanda yake sallar ya
bari ana gittawa ta gabansa ba. Sahabi Abu-Sa’eed Al-Khudriy (Radiyal Laahu
Anhu) ya riwaito hadisin da Al-Bukhaariy (509) da Muslim (507) suka riwaito
daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
Idan ɗayanku
yana sallah a bayan wani abin da ke kare shi daga mutane, sai kuma wani ya so
ya gitta ta gabansa, to ya tunkuɗe shi
a ƙirjinsa, ya yi ƙoƙarin hana shi gwargwadon iyawarsa. Idan kuma ya ƙi, to
ya yi faɗa da
shi, domin kuwa shi shaiɗani ne
kawai.
Ma’anar: ya
yi faɗa da
shi, shi ne: Ya tunkuɗe shi
da ƙarfi fiye da tunkuɗewa ta
farko.
Kuma idan mace baliga ko jaki ko baƙin
kare ne ya gitta ta gaban nasa, to sallarsa ta ɓaci. Saboda hadisin Abu-Zarr (Radiyal
Laahu Anhu) da ke cikin Sahih Muslim (510) cewa, Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
Idan ɗayanku
ya tsaya yana yin sallah, to zai yi masa sutura (kariya) idan ya zama akwai
misalin sandar da ke bayan sirdin raƙumi a gabansa. Idan kuwa ya zama babu
kamar misalin wannan sandar ta bayan sirdin raƙumi a gabansa, to jaki
da mace da baƙin kare suna yanke masa sallarsa.
Malamai sun ƙiyasta tsawon wannan sandar kamar sulusi
biyu (2/3) na tsawon zira’in
hannu ne, watau kamar daga gwiwar hannu zuwa wuyan hannun.
Amma a kan nisan wurin da mai wucewa zai iya
wucewa ta gaban mai sallah ba tare da ya yi laifi ba, ga bayaninsa a taƙaice:
Idan akwai sutura (kariya) a gaban mai sallar, to
duk yadda ya wuce a bayan suturar - watau ba a tsakanin mai sallah da suturar
ba - babu komai, in shã Allãh.
Amma idan mai sallar bai sanya sutura ba, mafi
kyau dai kar mutum ya wuce ta gabansa. Idan kuma ya buƙatu ko tilastu ga
wucewan, to ya zama daga bayan inda mai sallah ke ɗora goshinsa ne, da gwargwadon yadda hanun
mai sallar ba zai iya taɓo shi
ba idan yana tsaye:
Al-Bukhaariy (506) ya riwaito cewa: Abin da ke a
tsakanin matsayin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da
bangon da ke gabansa kamar zira’i uku ne. Watau, idan yana tsaye kenan.
Sannan kuma Al-Bukhaariy (496) da Muslim (508) sun
riwaito hadisin Sahabi Sahal Bn Sa’ad As-Saa’idiy (Radiyal Laahu Anhu) da ya
ce:
Tsakanin wurin da Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yake sallarsa da bango, daidai yadda ’yar tunkiya
take iya wucewa ne. Wannan kuma a lokacin sujada ne.
To, tun da a cikin hadisin Abu-Sa’eed (Radiyal
Laahu Anhu) da ya gabata ya faɗi cewa
‘…ya tunkuɗe shi
a ƙirjinsa…
wannan kamar ishara ce ga cewa: Idan har hanunsa ba zai kai inda yake ba,
shikenan mai wucewan bai yi laifi ba, in Shã Allãh.
Amma dai shi mai sallar da ya ƙi
sanya sutura ce yake da laifi, tun da ya bar wajibi, kamar yadda ya gabata.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.