𝐓𝐀𝐌𝐁A𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mallam, Ina da tambaya, shin yin
Alwala sau biyu biyu ya halasta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam.
1. Tabbas ya halasta mutum ya wanke gaɓoɓin alwala sau ɗai-ɗai, kamar yadda Abdullahi ɗan Abbas ya ruwaito cewa Annabi ﷺ ya yi. Bukhari 157.
2. Kuma ya halasta a wanke sau biyu-biyu, kamar
yadda Abdullahi ɗan
Zaidu ya ruwaito cewa Annabi ﷺ ya yi
hakan. Bukhari 158.
3. Sannan kuma ya halasta a wanke sau uku-uku,
kamar yadda mafi yawan hadisan da aka ruwaito game da siffar alwalar Annabi ﷺ suka nuna yana yi. Bukhari 159.
Wannan ya nuna cewa Manzon Allah ﷺ yana caccanjawa ne domin nuna halasci,
wani lokacin ya wanke sau ɗai-ɗai, wani lokacin sau biyu-biyu, wani
lokacin kuma sau uku-uku.
Duk wanda aka yi alwala da ita alwala ta inganta,
saboda wanki na farko shi ne wajibi, abin da ake so a tabbatar ruwa ya game
ko'ina, sai dai kuma wanke gaɓoɓin alwala sau uku-uku ya fi kamala fiye da
sau ɗai-ɗai ko sau biyu-biyu, saboda shi ne abin da
aka fi yawan ruwaitowa daga siffar alwalar Manzon Allah ﷺ.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
Post your comment or ask a question.