Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Aure Da Tayi Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mace Ce Mai Aure Tayi Zina Dawani Alokacin Sai Ciki Ya Shiga Kuma Tasani Saita Haife Yaron, Shin Yaron Na Mijin Aure Ne Kona Zinar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Babu makawa abun da ta aikata na zina tana matar aure yana cikin manyan laifuka, koda zina zunubi ce mai girma ita kaɗai to girman zunubin nakaruwa idan akace mai aure tayi zina, shiyasa ma hukuncin mazinacin da bai taɓa aure ba shi ne bulala ɗari (100) wanda kuma yake da aure ko ya taɓa aure shi ne ajefeshi harsai ya mutu.

Allah Mai girma da ɗaukaka Ya ce:

وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا ٢٣۝

Kuma kar ku kusanci zina. Haƙiƙa! Ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israa’i: 32)

Kuma acikin wani hadisin da Zahabiy ya kawo acikin Kitabul Kaba'ir, Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya ce "BAYAN SHIRKA BABU LAIFI MAFI GIRMA KAMAR NAMIJI YA SANYA MANIYYINSA ACIKIN MAHAIFAR DA BATA HALATTA GARESHI BA".

Kuma Manzon Allah ya ce "Mazinaci ba zai yi zina alokacin da yake yin zina alhali yana mumini ba... Ɓarawo ba zai yi sata alokacin da yake sata alhali yana mumini ba. Mashayi ba zai sha giya alokacin da yake sha alhali yana mumini ba".

Bukhariy da Muslim da Abu Dawud da Nisa'i ne suka ruwaito ta hanyar Abu Hurairah (radhiyallahu anhu).

Hakika cikin yin zina kinci amanar iyayenki bisa kyakkyawar tarbiyyar da suka baki, Kin ci amanar mijinki, kinci amanar aure, Kuma kin ci amanar zuriyarki ma waɗanda kika haifa. Don haka ki cigaba da istigfari da tuba zuwa ga Allah (SWT). Domin shi mai gafara ne mai jinkai.

Tare da girman laifin data aikata da muninsa a al'ada da kuma hankali, babu wanda zai shiga tsakanin Allah da bawansa Allah yana farin ciki da tuban bawa kuma yana karɓar tuban, Allah maɗaukakin sarki ya ce:

قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ ٣٥۝

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." (Suratul zumar: 53)

Ibnu kasir rahimahullah ya ce: Wannan aya tana kirane ga dukkan masu saɓo harda kafirai su tuba su koma zuwa ga Allah , tana kuma bada labarin Allah yana gafarta zunubai baki ɗaya ga duk wanda ya tuba yadawo daga aikata laifukan, komai irin yawansu da girmansu koda sunkai yawan kumfar kogi, matukar anyi tuba nagaskiya Allah yana gafarta su.

Amma nasabar ɗan za a jingina shi ga mijinki na aure ne, matukar yasadu dake , saboda faɗin Annabi daya ce: ,( Ɗa na me aurene,) ma'ana ɗan na mijin dakike aure da shi ne koda ba'a saduwa da shi cikin ɗan ya shiga ba, indai kin kwanta da mijin bayan zinar ɗan nasane.

An tambayi shaik bin baaz dangane da matar datake da aure kuma tanada 'ya'ya uku, ɗa na huɗun saita samu cikinsa ta hanyar zina, shin ya halatta ta zubar da cikin ɗan? ko zata kyaleshi idan ta kyale cikin (juna biyu) shin zata baiwa mijinta labari ko bazata bashi ba? sannan menene yake wajibi a kan mijin a wannan halin?.

Sai ya amsa dacewa: Bai halatta agareta ta zubar da wannan cikin (juna biyu) ba, abun da yake wajibi akanta shi ne tuba zuwa ga Allah maɗaukakin sarki, da kuma kin bayyana al'amarin, ɗan data haifa kuma za a jinginawa mijinta ma'ana ɗansane, saboda faɗin Annabi ( Ɗa na mai aure ne mazinaci kuma uquba ce kawai tasa) Ma'ana wanda yayi zina baida hakkin ajingina ɗan gareshi, shi kawai uqubar zinarce akansa.

Fatawa bin bãaz (21/205).

Da wannan majalisar fatawa ta kasar saudiyyah tayi fatawa, Allah yagyara halayen mu gaba ɗaya.

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments