Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Satar Amsa A Jarrabawa (Exam)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam

Menene hukuncin wanda

yai satar jarabawa domin

ya sami aiki??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

An Karɓo daga Abu Hurairah R.A Manzon Allah yace. Duk wanda ya Ha'incemu to baya daga cikin mu. (Muslim hadisi na 103)

To faɗin wannan Hadisi na nuna karara haramcin ha'inci ko da kuwa a Exam ne ko Test haramun ne mutum yayi satar amsa.

Sheikh Muhammad Saaleh al-Uthaymeen yace; Satar amsa a jarrabawa haramun ne kuma yakan shafi rayuwar mutum. Domin in ka samu aiki da wannan certificate na (Diploma ko Degree) da kayi satar amsa a Jarrabawar to haramun kake ci (ma'ana Salary naka zai zama haramun domin sakamakon da ka samu aikin da shi na sata ne.).

(Fataawa Noor ad-darb_24/2).

Haka kuma Sheikh Bin Baaz yace; Satar amsa a jarrabawa haramun ne

(Majmoo al Fataawa Ibn Baaz_6/397).

Dan haka satar amsa haramun ne musamman ma exam irinsu WAEC, NECO, NABTEB da sauransu.

Gaskiya kaɗan ne cikin dalibai masu rubutawa da basa Satar amsa. Dan haka ko wani yana sata to kai ka rabu da shi kada ka biye masa kuyi satar tare.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments