Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kallon Hoto Acikin Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah.

Duk lokacin da na je yin sujada sai na ga mai shigowa daga bayana saboda bangon akwai tiles. To ko wannan ya yi kamar mai waiwaye a cikin sallah? Mene ne hukuncin sallata?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Al-Imaam Al-Bukhaariy ya riwaito daga Ummul-Mu’mineen A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa: An tambayi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a kan waiwaye a cikin sallah sai ya ce:

هُوَ اخْتِلَاسٌ يَخْتَلِسُهُ الشَّيْطَانُ مِنْ صَلَاةِ الْعَبْدِ

Sata ce da sheɗan yake sacewa daga sallar bawa. (Sahih Al-Bukhaariy: 709)

Wannan dalili ne a kan cewa waiwaye a cikin sallah makaruhi ne, abin ƙyama tun da yana rage natsuwa da ƙanƙan-da-kai ga Allaah. Haka ma kallon duk wani abin da ka iya ɗauke hankali daga cikin sallah, kamar kallon hoton mai wucewa ko mai zuwa ta cikin madubi ko TV da sauransu.

Haka kuma Al-Bukhaariy ya sake riwaito hadisi daga gare ta (Radiyal Laahu Anhaa) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi sallah a cikin wata riga mai alamu a jikinta, sai kuwa ya yi kallo guda ga alamun, da ya yi sallama sai ya ce:

« اذْهَبُوا بِخَمِيصَتِى هَذِهِ إِلَى أَبِى جَهْمٍ وَائْتُونِى بِأَنْبِجَانِيَّةِ أَبِى جَهْمٍ ، فَإِنَّهَا أَلْهَتْنِى آنِفًا عَنْ صَلاَتِى »

Ku kai wa Abu-Jahmin wannan rigar, ku karɓo min ambijaaniyar Abu-Jahmin, domin ta ɗauke min hankali ɗazun nan a cikin sallata. (Sahih Al-Bukhaariy: 373)

(Ambijaaniyyah riga ce mai kauri mara alamu ko hotuna).

A kan haka Al-Imaam An-Nawawiy (Rahimahul Laah) ya ce:

واَمَّا الثَّوْبُ الَّذِى فِيهِ صُوَرٌ أَوْ صَلِيبٌ أَوْ مَا يُلْهِي فَتُكْرَهُ الصَّلَاةُ فِيهِ وَاِلَيْهِ وَعَلَيْهِ لِلْحَدِيثِ

Amma tufar da a jikinta akwai hoto ko gicciye (cross) ko duk wani abin da ke ɗauke hankali, to makaruhi ne a yi sallah a cikinta ko in tana gaba ko kuma a kan ta, saboda wannan hadisin. (Al-Majmuu’u Sharhul Muhazzab: 3/180).

Shi kuma Al-Haafiz Ibn Hajr (Rahimahul Laah) ya ce:

وَيُسْتَنْبَطُ مِنْهُ كَرَاهِيَةُ كُلِّ مَا يُشْغِلُ عَنِ الصَّلَاةِ مِنَ الْأَصْبَاغِ وَالنُّقُوشِ وَنَحْوِهَا

Daga wannan hadisin ne aka zaƙulo karhancin duk wani abin da ke ɗauke hankali a cikin sallah kamar launuka da zane-zane da makamantansu. (Fat-hul Baariy: 1/483).

A kan hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi sallah alhali labule mai hotuna yana a gabansa, kuma ya umurci A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) da ta kawar da shi (labulen) saboda hotunan jikinsa sun riƙa gitto masa a cikin sallarsa, sai Ibn Hajr (Rahimahul Laah) ya ce:

وَهَذَا تَشْرِيعٌ وَإِذَا كَانَتِ الصُّوَرُ تُلْهِي الْمُصَلِّي وَهِيَ مُقَابِلُهُ فَأَوْلَى إذِاَ كَانَ لَابِسَهَا

Wannan ita ce shari’ar haka kuma idan hotunan suna ɗauke hankalin mai sallah a halin suna a gabansa, to ina kuma idan yana sanye da su ne?! (Irshaadus Saariy: 8/484)

Daga waɗannan bayanan ya fito fili cewa ɗaga kai da kallon hoton mai wucewa a cikin bangon tiles bai halatta ba, makaruhi ne.

Amma abin da ya kamata, idan ba a iya kawar da hoton, kamar ta hanyar rufe shi ko lulluɓe shi, sai ya nisanci ɗaga kansa domin kallon hoton. Ya kula da yin aiki da abin da malamai suka nuna, watau ya sunkuyar da kansa zuwa ƙasa kawai. Saboda hadisin A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa

 

« دَخَلَ رَسُولُ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - الْكَعْبَةَ مَا خَلَفَ بَصَرُهُ مَوْضِعَ سُجُودِهِ حَتَّى خَرَجَ مِنْهَا »

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya shiga Ka’abah, kuma idanunsa ba su kauce daga wurin sujadarsa ba har ya fita daga cikinta. (Al-Mustadrak: 1/652).

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments