𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam, menene hukuncin mutum ya
ciwo ko ya sa a ciwo masa bashin banki domin ya yi business?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
A farkon mun amsa irin wannan tambayar, mun ambaci
cewa:
Haramcin bayarwa ko karɓar bashi-da-ruwa (interest) abu ne sananne
a wurin dukkan masu addini ma, ba wai addinin musulunci ba. Dalilin haramcin a
musulunci yana nan a cikin Ayoyi da Hadisai Sahihai da suka zo a kan haka.
Sannan kuma ga maganganun manyan malamai masana a kan batun, tun daga zamanin
Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) har zuwa yau.
Don haka musulmi ba zai nemi bashi daga irin waɗannan bankuna masu ta’ammali da riba
(interest) ba, sai in ya zama masa tilas, kuma ya shiga takura sosai. Musamman
kuma idan har ya zama rashin karɓar zai
janyo wani abu daga cikin haƙƙoƙinsa ɗan ƙasa ko
na sauran musulmi zai salwanta, ko ya bai wa arna da fasiƙai iko da dama har su
cigaba da danne musulmi.
Amma a lokacin da ake da bankunan da ba su yin
ta’ammali da riba, to ya wajaba musulmi ya yi ƙoƙarin mayar da harkokinsa
a can. Sai dai ko in an gano cewa su ma ɗin ba da gaske suke yi ba, ungulu ne da kan zabo
suke yi ko yaudara ce kawai suke yi domin neman yawan masu ajiya.
Allaah ya kiyaye.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.